You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin sauri ya isa inda kausar take yasoma rabata da kayan jikinta, ita kuwa dasauri ta goge hawayenta tana murmushin jin dadi rikeshi tayi tana fadin i love you Aliyu.... Kuramata ido yayi yana kallonta, fisgoshi tayi ya fado kanta tashiga shafashi ta ko ina daidai lokacin Umar Faruq ya bugo k'ofar da karfi yashigo, cak ya tsaya yana kallon ikon Allah Aliyu najinsa amman yayi kamar baijiba, yace kausar kibari kinsanfa ke matar aure ce ko?! Rikeshi takarayi tare da tura masa bakinta cikin nasa, wani irin mugun tsawa Umar Faruq ya daka masu yana fadin tir da halinku masu halin karnuka! "Adan firgice irin ta yan duniya Aliyu ya daga kausar yana wani kauda fuska, " dasauri Umar ya karaso cikin falon kai tsaye kausar yafara fisgowa tare da kifa mata mari ya shaketa yana fadin nizaki cuta kausar ni zaki wulakanta?! "Hawayene yasoma gudu bisa fuskar sa sakinta yayi kafin shiga dukanta yana fadin nasake ki kausar! Na sakeki! Na sakeki bana kaunar ki kausar bana kaunar ganinki! Ganin dukan yayi yawa yasa Aliyu shiga tsakani yana fadin to dama kai sai yau kasan muna irin wannan haduwar da ita, dallah malan bar dukan masu y'a tamkar kasamu jaka kaji ko?! Kausar wacce ke kuka sosai sam ita bama tasan metake ciki meke damun taba,


" fada ne ya kaure a tsakanin Aliyu Haydar da Umar Faruq naushin juna sukeyi sosai suna zage zage, Faisal dayaji shurun yayi yawa ya shigo gidan saboda ai shidai a iya saninsa wannan gidan Aliyu ne kuma ba zama yakeba, dan haka kai tsaye ya shigo har falon dasauri ya karaso ya shiga tsakaninsu yana fadin meye haka meye haka?! Bakuda hankali ne?! Dakyar suka rabu sai a lokacin hankalin faisal yakai kan kausar wacce keta kuka itakam kukan katse masu hanzari da Umar Faruq yayi takeyi wani irin abu takeji tamkar zata mutu, "dasauri Faisal ya kauda kansa izuwa yanzu yagama fahimtar komi, hannun Umar Faruq ya kama suka bar gidan, dasauri shima Aliyu ya maida ma kausar kayanta yaja hannunta suka fice daga gidan tana kuka tana tirjewa......






Fido sodangi🍃




Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 5:41 PM] ‪+234 813 502 2313‬: 🍃KAINE GATANA🍃


1⃣1⃣0⃣to1⃣1⃣5⃣






NA FIDDAUSI SODANGI






©TASKAR MARUBUTA📝








Note
Afuwan pls, naji k'orafinku dangane da last page dina! Kuyi hakuri banyi daniyyar cin zarafin aure ba ko makamancin haka ba sam! "Yakamata kuyi min uziri kuji k'arshan lbrn.
****************************






"A lokaci daya suka k'araso gida inda mai gadi ya wangale masu gate Aliyu ya faka motarsa inda shima faisal ya paka tasa, a lokaci daya suka fito d'ukansu, idanuwan Umar Faruq sam babu kyawun gani sun kada sunyi jawur, ahaka ya doshi falon abba, Aliyu na ganin haka ya juya yai tafiyar sa, kausar tabishi da kallo tanason tuno wani abu amman ina tunaninta ya tsaya cak! " dasauri tabi Umar Faruq da gudu wanda harya kusa shiga falon abba,


"A lokaci daya suka shiga falon yana gaba tana bayansa, mummy da abba ne tsaye cirko cirko a falon dukkansu sun tsura ma kofar shigowa ido, " wani irin tsawa abba ya daka masu yana fadin daga ina Kuke?! "Umar da zuciyar sa ke tafasa kai tsaye yace daga barhim muke! " wani irin mugun kallo mummy ta watsa masa hade dacewa dan iskanci amman umar ka kyauta mana kenan mutara jama'a sai ka dauketa ku fice abinku?" Wannan wani irin rashin kunya ne ni tunda nake bantaba jin irin wannan tantirancin ba kawai dai dukkan ku kunnuna mana bamuda cikakken iko akan ku shiyasa kukayi mana ahaka amman babu komi kanku kukai mawa, kekuma Kausar ta nuna ta da dan yatsanta, rashin kunya ko?" Kinbishi kun fice dan rashin mutunci to bari kiji shi namiji komi yayi adone kekuwa mace fa?" Hmm! Komi daran dadewa saikin.....kul nafisa kul! "Karki sake kiyi mata baki a matsayin ki na uwa! "Kai Umar Faruq kanajina ko?" Maza dauki matar ka kutafi Allah yabada zaman lafiya! "Hawaye ne yafara bin fuskar Faruq bakin sa na rawa yace kuyi hakuri abba.....shut up!! " ka dau matar ka ku fice nace!


"Cikin tsananin bacin rai Umar Faruq ya fice kausar tasamu kanta dabinshi a baya, baisan tana binsa ba saida ya isa jikin motar sa,karki karaso nan! Yafada cike da hargowa, cak tayi tsaye tana zaro ido lokaci daya abubuwan suka fara dawo mata, hannu biyu tasa ta dafe kanta tare da kurma razanannan ihu,


"Da gudu mummy da abba suka fito saura kiris mummy ta kifa da gudu Kausar ta fada jikinta tana wani irin kuka hade da ihu, a firgice mummy ke tambayar ta meya faru?" Ina kuka kawai take tana fadin nashiga uku mummy nashiga uku! "Cikin lallashi abba ke fidin kausar natsu kiyi mana bayani meke faruwa?" Dole idan ka kalli Kausar sai ta mugun baka tausayi gaba daya ta fice daga cikin haiyyacin ta,


"Hawaye mummy tafara itama dan kukan kausar bakaramin taba bata zuciya yake ba, ganin hakan abba ya tarkata su d'uka zuwa falon sa,




" Umar Faruq kuwa tunsanda kausar tasaki ihu ya fice da motar sa cike da kunar zuciya sam ya tsane su baya bukatar ganin su ko kadan! Gudu yakeyi bisa titin shi kansa baisan inda ya nufa ba lokaci daya kuma ya fashe da kuka harda shessheka, wata babbar mota ce ta nufosa gadan gadan, duk iya kokarin sa na ya kauce mata amman ina....kiiiiiiiiiii!!!!! Cikin hukuncin Allah motar ta tsaya cak sai dai wani abin mamaki sam Umar Faruq baya motsi kansa bisa sitiyarin motar, mai babbar motar ne yayi saurin fitowa dan ya duba lafiyar sa aikuwa yana karasowa yaga halin da Umar Faruq ke ciki, tsoro ne ya mamaye zuciyar sa yana tunanin kila tsoratan dayayi ne yajawo masa hakan,






"Nafisa kina kuka tana yi yaza ayi musan meke damunta for god sake! Dan girman Allah kiyi shuru mu rarrasheta muji meke faruwa! " saboda shima umar na lura kamar baya cikin haiyyacinsa kawai dan yariga ya batan raine shiyasa nayi masa haka, y'ata kiyi shuru haka nan kiga yamin meke faruwa? " cikin wani sabon kukan kausar ta kan kame mummy tana gaya masu abinda yafaru wanda ganinsa tayi tamkar a mafarki komi ya faru,


"Cikin tsananin tashin hankali suka shiga k'wad'a salati suna mai tsananin al'ajabin faruwar hakan, abba ne ya mike cikin tsananin fusata yana safa da marwa a tsakiyar falon fuskarsa sam babu annuri ko kadan, mummy kuwa kuka ta fashe dashi tana fadin meyasa Ali yayi haka why?" Lallai kuwa wannan karan zan nuna masa yayi babban kuskure a rayuwar sa dan bazai taba samun abinda yake ma k'wak'wa ba Sam!!


"Wayar abba ce tashiga kuwwa a cikin falon, jiki a sanyaye abban ya tafi ya d'auka da kyar ya iya bude baki cikin sarkewar murya yayi sallama, tsawon minti uku ya dauka yana wayar kafin ya iya furta Kalmar ya salam da k'arfin sa, "ganinan zuwa doctor dan Allah Ku kular min dashi kafin in k'araso........




Fido sodangi🍃


Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 5:43 PM] ‪+234 813 502 2313‬: 🍃KAINE GATANA🍃




1⃣1⃣5⃣to1⃣2⃣0⃣








NA FIDDAUSI SODANGI






©TASKAR MARUBUTA📝










"Mekuma yafaru?" Mummy ce ke tambayar abba, Umar Faruq ne ba lafiya yana asibiti! "Ya salam! Tafada da k'arfi" kai Aliyu! Aliyu! Aliyu bai kyauta mana ba sam wallahi! "Nafisa tashi muje yanzu ba lokacin takale takale bane, " gaba daya suka fice harda kausar dake faman kuka ayanzu kukan nata ma karuwa yayi danjin cewar Umar Faruq ba lafiya tasani koma meye yasami umar dinta to Aliyu ne yajawo masa kuma bazata taba yafe masa ba sai Allah yayimata sakaiya! Tanajin tsanar Aliyu mai tsananin gaske a zuciyar ta,


"Suna isa asibitin adai dai lokacin da likitan ya fito daga d'akin da umar din yake ciki, "Dr Muhammad safana kenan,likitan daya kasance family doctor dinsu, kasancewar asibitin yafi kusa da inda abin yafaru shiyasa direban yakawosa nan, sai kuma Allah yasa sukayi dace da k'wararran likitan yana kusa, atake ya shaida Umar Faruq dan haka yai gaggawan sanar da abban sa, " gumin fuskar sa ya share da dan hankicin hannunsa, dasauri su abba suka nufosa suna tambayar meke damunsa?" Nan yace masu su biyo shi office dinsa yai gaba abinsa, "jiki a sanyaye suka rufa masa baya bama kamar kausar wacce ke d'aga k'afa dakyar,


"Bayan sun zazzauna ne likitan ya dubi abba tare da cire farin madubin dake idon sa, yace ku kwantar da hankalin ku alhaji, abinda muka dade muna jira ne yake kokarin faruwa insha Allah! Watau abinda ya faru shine hatsari ne yaso ya afku dashi Umar Faruq din to sai Allah ya tsare hakan bai kasance ba, to saboda tsorata da razana dayayi shine k'wak'walwarsa ta juya atake abinda yafaru a shekarun baya suke so su dawo masa to a sanadiyyar hakan ne yasashi shiga wannan halin dayake ciki, to amman insha Allahu daya farka zai dawo cikin hankalin sa abinda yafaru a dacan duk zai tunosu, idan baku manta ba dama na gaya maku cewar duk dadewar daza ayi idan Allah yaso to zakuga yadawo tamkar yanda yake saboda dama yayi losing memory dinsa ne idan ban manta ba shekara goma sha biyar kenan da abi ya faru koba haka ba?" Hakane doctor inji abba, "mummy tace to yanzu doctor kana nufin idan ya tashi zai iya gane garin su dakuma yan'uwansa da komi nasa kenan?" Mummy tayi tambayar cikin rawar murya, "eh haka nake nufi hajiya! Insha Allahu nan da awa uku zai tashi! To doctor mun gode kwarai Allah yasaka da alheri, " kausar dai sai dubansu takeyi sai kace wacce ta bace, "doctor zamu iya ganinsa kuwa?" K'warai kuwa saidai baya bukatar hayaniya!




"Zaune suke dukkan su sun zagayeshi, a lokacin agogo yana nuna mana k'arfe d'aya da rabi na dare, " kausar na lafe a jikin mummy sam takasa run tsawa gashi anyi anyi da ita tabi su Anty maijidda su koma gida sanda sukazo amman sam ta kiya, dole suka rabu da ita suka tafi, ita kanta mummy abba yace ta tafi gida amman tace gara zaman ta anan din yafiye mata kwanciyar hankali dan kota je gidan ba iya bacci zatayi ba, "wasu irin na'urori ne aka jona masa akansa sai wani haske abin keyi yana canza kala, lokaci daya abin ya dau wani irin kara gaba daya hasken ya dauke dif gadon tare da shi Umar Faruq din sai jijjiga sukeyi, dasauri abba ya rikesa,


"Doctor Muhammad nacikin office dinsa ya k'ura ma wata yar computer ido dasauri ya mike ya fice daga office din tare da nufar d'akin da Umar Faruq ke ciki tamkar zai kifa, dasauri ya zare masa abin tare da dafe masa kai yana kallonsa, wani irin ihu Umar Faruq yayi da k'arfi sai kuma yafara fadin Kalmar...innalillahi.....tare kuma da kalmar shahada...a lokaci daya kuma yake fadin babaaaaa!!!!!!!! " sai kuma ya fashe da kuka a lokaci daya ya bude idonsa, ido hudu sukayi shida kausar atake yai tsit yana kallonta irin kallon da ake kira na kurullah, saikuma ya kauda fuska yana kallon kowa na d'akin daya bayan daya, sannu Umar Faruq sannu kaji! Abba ne ke fadin hakan, kallo kawai Faruq ya bishi dashi a zuciyar sa yana maimaita sunan Umar Faruq din, to su kuma wayannan suwaye haka?" Atake ya maida dubansa a jikinsa dasauri yasaki salati yana kokarin mikewa tsaye, dasauri doctor ya dakatar dashi ta hanyar cemasa yi hakuri Umar Faruq nasan kana mamakin yanda akayi ka dawo haka ne to ka kwantar da hankalin ka zuwa gobe insha Allahu za kaji komi da yardar ubangiji,..........




Fido sodangi🍃




Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 5:43 PM] ‪+234 813 502 2313‬: 🍃KAINE GATANA🍃


1⃣2⃣0⃣to1⃣2⃣5⃣






NA FIDDAUSI SODANGI








©TASKAR MARUBUTA📝










"Gaba dayansu sun hadu a falon abba wanda dakyar Umar Faruq ya yarda ya biyosu acewar sa shi kam bai sansu ba kuma shi basunansa Umar Faruq ba suna shi "Nasir!" Dakyar dai abba ya lallabasa, "Aliyu kuwa wanda abba yai masa waya cewar yazo maza yana niman sa cikin tashin hankali ya iso gidan yana addu'a Allah yasa kausar bata tona masa asiri ba ameen, saidai shigowar sa falon abban ne ya raina kansa inda abba yadin ga kifa masa mari tare dacin kwalarsa yana fadin nizaka tozarta Ali! Irin tarbiyyar danabaka kenan Aliyu?" Kai ranan Aliyu yasha mari da zagi na fitar hankali daga karshe mummy ta karbe tayi tayi itama tamkar zata ari baki, fuskar sa duk ta kumbura da mari, kausar kuwa dadi tamkar ya kashe ta ita aganintama wannan ai yayima Ali kadan, batasan me zatayi masa a duniya ta huce ba amman tasha alwashin cewa saita rama kota halin k'ak'a!


"Umar Faruq dai sai binsu da ido yakeyi shikam wannan abu na matukar d'aure masa kai ya matsu yaji meya sameshi haka ne?" A daya bangaran na zuciyar sa kuma yana tunanin k'anwar sa da baban sa!


"Bayan komi ya lafa ne abba ya dubi Umar Faruq yace ka gafarce ni d'ana yanzu zakaji abinda yafaru,


"Shakara goma sha biyar data wuce a wata safiyar jama'a a hanyata ta zuwa k'urfi nida d'ana Aliyu muka sami hatsarin mota a hanya idan baka manta ba kaida mahaifin kane a cikin motar yana tuki kai kuma kana gaba to inajin motar ce ta k'wace masa daidai lokacin nikuma na taho da gudu to idan Allah yakawo tsautsayi babu yanda za ayi, Allah yariga ya hukunta, nasami karaya a k'afata da hannuna inda d'ana Aliyu kuma hannunsa na dama ne ya k'arye, mahaifin ka kuma Allah yayi masa rasuwa kai kuma kasami juyewar k'wak'walwa inda likita yasanar mana cewa ka mance da duk wani abu daya faru dakai a baya illa sabuwar rayuwa dazaka fuskanta, saidai akwai yuwuwar dawowar hankalin ka zuwa wasu shekaru masu yawa wanda shi kansa bazai ce gasu ba,


"To bayan ka war ware ne na d'auko nadawo dakai gida na ina rike dakai har zuwa yanzu bayan mun saka maka suna da Umar Faruq! Munyi iya binciken mu dan gano dangin ka amman wallahi sam hakan bai samu ba bamu taba jin wanda yace yasan kaba, gaba daya dai abba yafada masa komi bai boye masa ba harda abinda Ali yai masa bai rage ba!


"Nanfa Umar Faruq yashiga kuka wiwi suna lallashinsa,dakyar suka samu yai shuru inda shima yasoma basu labarin sa kamar haka,


" Mahaifiyata Allah yayi mata rasuwa a wajan haihuwar k'anwata wacce tazamemin "SANYIN IDANIYATA! "muntaso nida kanwata a hannun matar baban mu wacce takasance mace ce mai son zuciya! Sam bama jin dadin zama da ita musamman ma k'anwata wacce takasance yar shekara hud'u a lokacin, ina tsananin kaunar yar'uwata dakuma tausayinta, haka matar baban nan tawa take azabtar damu gashi baban mu bashi da tacewa akanta sai abinda tace, ahaka dai har na kammala karatun secondary school dina anan cikin garin dutsanma din inda nasamu admission a umaru Musa yar'adua university, to a lokacin da hatsarin nan ya afku muna kan hanyar mu ne nazuwa can makarantar domin infara registration, munbar matar babana a gida tare da k'anwata gashi kuma Allah yayima baba rasuwa ya fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai saurare, hakuri d'uka suke ta bashi tare dayima iyayan nasa addu'a,


" kausar wacce taji tausayinsa ya bala'in kamata atake tasoma kuka tana tuna rayuwar ta itama dayanda ta bar goggon ta itama a garin dutsanma, nan tace yaya Umar Faruq ashema garinmu daya nan yayi mamakin ashe basu abba suka haifetaba, abba ne yabashi labarin ta itama ya tausaya mata matuka sai tunanin k'anwar sa yadawo masa d'anye yana tuna ko a wani hali take yanzu a hannun wannan azzalumar matar oho! Nanda nan hankalin sa yayi garin dutsanma yanaso yaje yaga a wani hali k'anwar sa take,


"Atake ya shaida ma abba k'udirinsa tare dayi masa godiya bisa d'awainiyar dasukayi dashi har yazama wani a yau! " abba yace kayi hakuri umar ka kara warwarewa sai mutafi gaba dayanmu mudubasu ina gani hakan zaifi, nanfa umar yace shifa alanbaran bazai iya kara k'wana batare dayaga k'anwar saba gaskiya! "A dole suka shirya gaba dayansu cikin k'atuwar motar abba suka d'au hanyar dutsanma........






Fido sodangi🍃






Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 5:44 PM] ‪+234 813 502 2313‬: 🍃KAINE GATANA🍃


1⃣2⃣5⃣to1⃣3⃣0⃣








NA FIDDAUSI SODANGI






©TASKAR MARUBUTA📝








"Sunshiga cikin garin dutsanma da misalin k'arfe sha biyu da rabi na rana, nan danan hankalin kausar yai bala'in tashi zuciyar ta tahau bugawa tana tunanin haduwar ta da goggonta dan kuwa abba yace har can gidan zasu domin su sadu da dangin kausar din, " har abada kamannin garin nasu bazai taba sauya mata ba, duk da ci gaban da aka samu na karin gine gine dawasu sauye sauye, zuciyata bugawa kawai yake tamkar zai fado k'asa,


"Shi kuwa Umar Faruq wani irin farinciki ne ya lullube masa zuciya, awani bangaran kuma yana danjin faduwar gaba dan bai san a halin dazai tarar da kanwar tasaba,


"Shike zaune a gaba da abba dan haka shike nuna masa hanya, "mamaki ne yakama kausar ganin sun tsaya cak a k'ofar gidan su, ido ta zaro itakam tsoron shiga gidan nan take, towaima ya akai ya Faruq yasan gidan su?" Tambayar datakeyiwa kanta kenan, mamaki bai gama kamata ba sai da dukkansu suka sauko daga motar taga ya Faruq ya nufi k'ofar gidan yana doka sallama, hannun mummy ta matse da k'arfe cikin nata tana sauke ajiyar zuciya,


"Muryar goggo sukaji cikin fada tana fadin waye haka yake doka min sallama kamar naci masa bashi ban biya ba!" Gaban kausar ne yayi bala'in faduwa jin muryar goggo, shi kuwa Umar Faruq zuciyar sace ta tsinke yana fadin haryanzu dai tananan da bakin halinta!


"Goggo ce ta karaso tana kallonsu d'aya bayan daya,kafin ta tsada idonta akan Umar Faruq, cikin wani irin kid'ima da rawar murya take furta kalamar nasuruuu!!!!!!!!!!!! " A tsorace take ja baya tana nuna Umar Faruq, "dama kana raye baka mutuba?" To ina mallan yake?" Wayyo ni talatu naga ta kaina dama kuna raye tsawon wannan lokacin kuka yada ni?! Sai kuma tasaki kuka mai k'arfi tana ihu, "ganin zata tara masu jama'a ne Umar Faruq yace abba mu shiga daga ciki, gaba dayansu suka shiga banda kausar data saki hannun mummy ta kame a bakin k'ofa, mummy tace muje mana hawaye na bin idonta ta girgiza ma mummy kai alamar bazata ba, wata kod'add'iyar tabarma goggo ta shimfid'a masu tana fadin bisimillan ku, d'uka mazan suka zauna akai abba ne yakai dubansa kan mummy dake ta fama da kausar yace nafisa meke faruwa ne?" Abban su kausar ce taki shigowa wai ita tsoro takeyi ni narasa tsoron me takeyi haka ji yanda jikinta ke rawa fa, abba dakansa ya mike ya kamo hannun Kausar suka shigo ciki, ido goggo ta tsare kausar dashi sai dai sam bata ganeta ba kamace kawai acewar ta, kai nasiru ina Malan?" Ina kabaro shi ne?! "A hankali Umar Faruq yace Allah yayima Malan rasuwa nan dai yabata dukkan labarin da abba ya bashi, aikuwa atake goggo tasaka ihu tana fadin shikenan tashiga uku ta lalace sai kace wata arniya, aikuwa nanfa mata suka fara cika gidan ana tambayar ta ko lafiya?" Kuka take tana fadin Ashe Malan mutuwa yayi Allah yayiwa malan rasu hatsarin mota sukayi Ashe shida nasiru ga nasirun nan yanzu suka iso shida mutanannan yake fada mani, tasake sakin wani sabon kukan tana jan hanci,


"Nandai akaita jajanta mata saikace a lokacin abin ya faru, " babar rahane kawar kausar wacce suka tafi birni atare idan baku manta ba tace ohhh! Allah mai iko to kuma ina shi nasirun ya gano kausar ko ba ita bace wannan ne dannaga wannan y'ar gayuce dukda dai shima nasirun yazama d'an gayu dakyar na shaida shi?" Goggo tasake kallon kausar wacce gaba daya jikinta k'yarma yakeyi tace A'a ba ita bace kamace kawai waccan y'ar iskar ai izuwa yanzu nasan ta mutu tunda yawon karuwanci tasaka agaba! Yanzu kuwa wannan ciwo na zamani ai baya k'yale tsinannu la'anannu fasikai! Ubansu yakece aini wallahi nagode wa Allah kullum godiya nake agaresa!




"Cikin muryar kuka kausar tace wallahi nice goggo wallahi ba yawon karuwanci najeba! Tafada tana mai fashewa da kuka mai ban tausayi, ido goggo ta zaro tare da mikewa ta k'arasa inda Kausar take kafin mummy ta ankare harta shake kausar tana jibga duk kuwa data tsufa duk wahala ya mokad'ar da ita, dasauri mummy ta shiga tsakaninsu tana mai mamakin meke samun tsohuwar nan ne?"




"Izuwa yanzu k'wak'walwar Umar Faruq na niman rikicewa wai meke shirin faruwa ne haka?! Yana fata dai ba k'anwar sa bace wannan?" Mikewa tsaye yayi domin ya k'ara tabbatarwa yace goggo talatu ina k'anwata kausar take?!


"Gatanan kuwa kana gani a gabanka tashiga yawan duniya gatanan tazama bak'ar baturiya ai duk wanda yaga wannan yasan babbar yar bariki ce! " aishi Allah ba azzalumin bayinsa bane saidai Wanda ya zalinci kansa! Sakaiyace da hakkina ke bibiyarta! Ki fice kibar min gidana kada kisaka min d'aud'a a cikin gida!


"Basu ankara ba kawai ganin Umar Faruq sukayi ya yanke jiki ya fadi, gaba daya su abba suka Mike suma a rikice dan izuwa yanzu suma sun fahimci abinda ke faruwa, tofa! Ana wata gawata kenan, ..........




Fido sodangi🍃




Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)




Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Zanyi amfani dawannan damar domin in mik'a sakon ta'aziiyata ga iyalan marigayi Alhaji Ibrahim Kaduna! Da rashin d'ansu Nasir dasukayi, ubangiji Allah yajikansa yasa ya huta, Allah yayi masa rahama yasa mutuwa yazamo hutu agaresa, Ameen! Allah yakara mana hakuri da dangana Ameen!😭
[12/5, 5:44 PM] ‪+234 813 502 2313‬: 🍃KAINE GATANA🍃


1⃣3⃣0⃣to1⃣3⃣5⃣






NA FIDDAUSI SODANGI






©TASKAR MARUBUTA📝






"Basu ankara ba kawai ganin Umar Faruq sukayi ya yanke jiki ya fadi, gaba daya su abba suka mike a rikice dan uzuwa yanzu suma sun fahimci abinda ke faruwa. " innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Kalmar da abba ke furtawa kenan, a rikice Aliyu yayu kansa wanda tun zuwansu yaketawani yatsine fuska yana cin magani dakyar ya zauna akan tabarmar dama shi ala dole d'an gayu bayaso ya bata jiki, shikam badan abba ya matsa ba aida baiga abinda zaikawoshi wannan k'auye ba acewar sa kenan.


"Ruwa aka dibo masa adan kofi ya dan diba ya yaiyafa masa a fuskar sa nandanan yai ajiyar zuciya sannan ya fashe da kuka yana fadin wannan wace irin rayuwa ce ace mutum ya auri k'anwar sa ta jini baisani ba! Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Allah nagode maka dakasa kausar bata tare a gida naba Allah kaine abin godiya,


" kausar wacce ke kuka tamkar ranta zai fita ta fada jikin umar Faruq tana fadin Ashe banyi karya ba danake cewa KAINE GATANA! ashe da gaske kai gatan nawa ne! Allah nagode maka daka kara hadani da d'an uwana a karo na biyu, a hankali yake bubbuga bayanta alamar rarrashi,


"Goggo ce taja wani mugun tsaki tana fadin aikin banza aikin wofi anje angama tambadewa za a wani fake da zancan dababu gaira ba dalili! "Alhaji da hajiya dan Allah Ku tashi kubar min gidana dan ina ganin d'an mutuncinku tun wuri gara ku fice kafin rashin mutunci na yatashi! " kafin ma ta rufe baki mak'otanta dasuka cika gidan kowa ya fara ficewa d'aya bayan d'aya dan sun riga sunsan halinta tunda ta furta hakan,


"Umar Faruq zaiyi magana abba ya d'aga masa hannu alamar dakatarwa, nan sukayi ma goggo sallama suka tafi abinsu tace yadai fiye maku inga dan shegen dazai kuma dawo min gida! Kuje can ku karaci gantalinku mutanan banza da wofi kawai! " taci gaba da masifar ta tamkar suna wajan,


"Haka su abba suka tafi da mamakin halin goggo, Umar Faruq yace ai abba wannan kad'an ne daga halin ta! Mummy tace to umar wai bakuda wasu yan uwa ne kuma?" Ina nufin dangin baban ku kona maman Ku?"


"Ajiyar zuciya kawai yayi idanuwansa cike da hawaye yace mummy bamuda sauran dangin mu wayanda suka rage, dama baban mu su biyu ne shida Yayan sa, kuma a shekarar dana gama makaranta Allah yayi masa rasuwa, ita kuma maman mu dama ita d'aya iyayanta suka haifa kuma Allah yayi masu rasuwa tun tana raye, " cike da tausayawa mummy ta kara jawo Kausar a jikinta,


"Aliyu dai bazan iya cewa ga yanayinsa ba wayar sa kawai yaketa latsawa, tamkar babu shi a cikin motar, (miskili kafi kare ban haushi, Aliyu Haydar kenan,Ali Jan zaki, Ali Jan rina ba nama ba, Ali

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment