You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

GATANAšŸƒ


2⃣0⃣to2⃣5⃣






NA FIDDAUSI SODANGI






Ā©TASKAR MARUBUTAšŸ“










"WASHEGARI"




"Gaba d'ayansu sun hallara bisa dinning table dan gudanar da kalacen safe, "kowannan su ka dubi fuskarsa wasai take d'auke da murmushi bai ban sha'awa sunata auna ma cikin su daddad'an girkin mummy wacce sam bata yarda yan aiki suyi mata girkin da mijinta zaici ba, acewar ta hakan ba burgewa bane mijin ta bazai iya cin kowani kwamacala ba, shi yasa a kullum take bata lokacin ta wajan shirya masa had'addun girki fiye da kala uku dan kawai ta faranta masa rai,


" Aliyu ne yai sallama yashigo fuskar nan tasa a hade kamar hadari, ya d'uka har k'asa ya gaida iyayan nasa kafin yaja d'aya daga cikin kujerun ya zauna yana wani yatsine fuska, Umar Faruq ne ya danne dariyar dake cinsa yace yaya haydar ina kwana?" Ya madam?" A subane ya dubesa a kaikaice tamkar bazai tanka ba sai kuma yace lafiya tamkar wani mai ciwon baki, kausar daketa kai loma abinta ba kakkautawa ta dubesa itama tace yaya Ali ina kwana?" Dasauri ya d'ago kansa ya kalleta sai kuma ya maida kansa wani gefe tamkar badashi tayiba, "dasauri takuma furta yaya Ali ina kwana ya madam?" Dallah malama wayace maki haka ake gaya min! Idan baki iya fadin sunan ba dole ne saikin gaishe ni!?" Asanyaye tace to Alin madam kayi hakuri ai ni bansan ya asalin sunan naka bane, wani mugun tsaki yasaki ya jawo plate ya shiga lodan abincin sa,


"Dariya Umar Faruq yasaki harda d'ukawa kasa rike da cikinsa hawaye sai zuba sukeyi amman bai fasa dariyar ba, "mummy ce ta daka mai tsawa ganin Haydar din ya mike tsaye tace kai Umar Faruq meye haka?" Me akai dakake irin wannan dariyar kamar wani zararre?" Nan danan ya hade dariyar sa amman dukda haka fuskar sa na d'auke da murmushi alamar dariyar bata isheshi ba, "kwafa Aliyu yayi kafin ya koma ya zauna,


"Mummy ta dubi Kausar fuskar ta d'auke da murmushi dan itama abin ya matukar bata dariya kawai dannewa tayi dan kar ran gadanga yafi haka baci, tace Kausar sunan shi yaya Aliyu daga yau kinji?" Baya so anace masa Ali kinji?" Kakar sa ce kawai ke gaya masa Ali itama rikici sosai sukeyi kinji ko?" Dasauri Kausar tace naji mummy insha Allah zan kiyaye, yaya Aliyu kayi hakuri bazan karaba kaji yaya Haydar?" Hararan ta kawai yayi yaci gaba dacin abincinsa,


"Abba dabai tofa ba tuntuni yace waikai Haydar ba jiyan nan naji mummyn ku nayi maka fadan cin abinci a gidan nan ba?" Yafada tare da duban sa, kafin yaci gaba dafadin kokuwa kana aza da wasa ake maka ne?" To wannan shine na k'arshe banso in k'ara ganin ka a gidan nan dasunan kazo cin abinci kanajina ko!?" Asanyaye yace naji abba amman.......amma me!?" Banaso inji komi daga gareka kawai umurni nake baka kuma dole kabi!


"Mikewa yayi batare daya ce komi ba yana k'okarin ficewa mummy tace au! Fishi kayi kenan zaka bar abincin ka fice?" Fuska a daure yace A'a na koshi ne sai anjiman ku, yafice abinsa dukkansu suka bishi da ido,


"Bayan sun gama karyawa ne abba ya tara su gaba dayansu a falonsa inda yanimi da kausar tabasu tarihinta ko Allah yasa su gane inda iyayan ta suke domin su mai data, dukda karancin shekarun kausar hakan baisa takasa basu labarin taba kamar yanda suka bukata babu abinda tarage saidai wanda bata sani ba amman dukkan abinda take iya tunowa saida ta fadi masu tas! "Nanfa hankalin su yai bala'in tashi musamman mummy wacce tuni ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai saurare, shikansa Umar Faruq tuni yanayin fuskar sa ta canza zuwa kalar tausayi, abban kuwa dayake mai dakakkiyar zuciya ne fuskar sa ba yabo ba fallasa,


"Abba ya dubi Kausar bacin takare maganar ta yace kausar ki kwantar da hankalin ki Allah ne yahada mu dake, kuma da izinin Allah zamu rike ki da gaskiya da amana tamkar mu muka haifeki, inaso ki zauna damu tsakaninki da Allah kema kuma ki dauke mu matsayin iyayanki insha Allah zakiyi alfahari damu ga yayunki nan ya nuna Umar Faruq ki rike su yan uwa ko bayan ranmu nasan zasu kula dake,


" mummy ta amshe maganar dafadin kausar ki godewa Allah daya hadamu dake domin kuwa zamu zauna dake ne tamkar yanda muke zaune da ya'yan mu kuma inaso ki kasance mai ladabi da biyayya,kinji ko Kausar?" Hawaye cike a fuskar kausar tace to mummy nagode kwarai Allah yasaka maku da alkairi yabiya maku bukatocinku na alkairi gaba dayansu suka amsa da Ameen ya rabbi.........






Fido sodangišŸƒ








Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 3:57 PM] ‪+234 813 502 2313‬: [7/12, 9:01 PM] FIDDAUSI SODANGIšŸ’…: šŸƒKAINE GATANAšŸƒ

2⃣5⃣to3⃣0⃣










NA FIDDAUSI SODANGI



Ā©TASKAR MARUBUTAšŸ“




"BAYAN WANI LOKACI"


**************************
Kwanaki sunja rayuwa tacigaba ayanzu Kausar nada shekara 16 inda take jss3 saboda promoting daaka mata,kowa na sonta,
********
Yau takama Saturday kowa na gida babu school babu work, umar faruq da kausar suna garden a field suna buga basket ball,dan yana bala'in ji da kausar kaman kanwarsa ta jini itama haka take sonsa,
Kausar na sanye cikin mini short skirt na sport wears da riganshi mai short hannu,kirjinta acike suke tam tamkar zasu yage rigar kasancewar ta mai cikar gaba," blue color, tasa blue facing cap yafito da jelar gashinta Wanda yanzu yakusa kaiwa gadon bayanta,da witsle a bakinta ta daura fararen compos sai tsalle takeyi.
Ball dinne yafita daga field, Umar Faruq yace kausar jeki dauko mana, aiko dagudu tabi kwallon, ta durkusa zata dau kwallon hartakai hannu saitaga wani kakkyawan kafa dake sanye cikin black cover ya daura akan ball din.
Atsiwace ta Mike batare data kalli fuskanba tace meye haka zaka takemana ball, tana turo wanan karamin bakin nata, tai rau rau da ido tace give me d ball,we are playing basketball, ya umar said I should bring d ball 4 him duk maganan bata kalli fuskanba,ganin anki daga ball din yasa iya karfinta ta daddage ta tura kafan amma ko gezau kafan baiyiba, sa bakinta tayi a gwuiwan kafan ta gansara cizo nan ma baiyiba, dukan kafan tafara sosai tana kuka tana cewa ya umar!" someone is trying to still our ball jin muryanta yasa Umar Faruq zuwa wurin dagudu amma ganin Wanda take duka yasa shi tsayawa cak batare daya motsaba, wata irin natsuwa tashige shi kaman ba shiba, " tsawon lokaci sannan yai karfin halin karasawa dasauri yadagata tafashe da kuka ta fizge kanta ta koma kan mutumin ta turashi, wani gigitachen mari taji a fuskanta fau tasasssss,




"Ta sandara ihu, Aliyu
yakara falla mata wani kakkyawan mari, ta fadi akasa belt din jikinshi yaciro yafara lafta mata yace bakida tarbiya abi?kin raina nagaba dake,am back zan gyaraku duka, sai alokaci ta kalli fuskanshi tagane Yaya Aliyu ne wanda tsawon shekara biyu baya k'asar shida matarsa ummi Aisha,
"Cikin kuka tace Yaya am sorry bazan karaba,plz 4give me, baimabi takantaba saida ya zaneta sosai tass sai ihu take, ya kalleta fuska adaure yace hold ur lips, idan nakarajin koda tarinkine saina saba miki, da sauri tarike bakinta tana hadeye kukan,ya maida belt dinshi. da yatsa ya nuna Umar Faruq yace zonan kaima, meye dalilinka na wasa da mace da irin shiganan?" Yayi zuru zuru da ido, bakasan kaiya kamata Ka gyarataba? Bakaga tafara girmaba, 4 god sake wot is wrong wid u?" kaida nakema kallon mai hankali kaiya kamata kai couching dinta," bakasan haryanzu yarinya bace?"batasan komiba y? Ita bakasan mace bane dakake koyamata abubuwan mazaba, 4rm today nabaka last warning ko ka gyara kona saba maka, " yace Yaya Aliyu kayi hakuri bazamu karaba. Itama kausar tasake bashi hakuri
. dukda tana inda take jikinta narawa tarike bakin nata gam hawaye nazuba, ya daka mata tsawa Mike ki wuce cikin gida maraji kawai, tamike jikinta narawa, yace cire hannun 4rm ur lips da sauri tacire tawuce cikin gida.


"Tana zuwa da gudu tafada jikin mummy dake falo tafashe da kuka sosai, mummy arude tace my kausar menene maisa kike kuka?wayatabaki? Takara shigewa jikin mummy tareda daura kanta kan hannun mummy tace mummy Yaya... Sallamar dataji yasa takama bakinta da sauri jikinta narawa, Aliyu ya Balla mata harara,yace sauka ajikin mummy,da sauri ta sauka tana hawaye tana rike lips dinta, hararanta yakarayi wuce kibamu wuri da sauri tajuya hartana kokarin faduwa tabar wurin.




"Mummy tajuyo ranta adan bace tace Aliyu maisa zaka dake ta haka?" Bakasan yarinya bace?banason nama fada agabantane dankai yayane amma karka Kara dukanta haka banso, yace mummy kiyi hakuri batada kunya ne! mummy tace yanzu gashi ai kasa tana tsoranka zaka hanamin yaa walwala, yay murmushi yadawo kusa da ita ya kwanta akan cinyanta yace mummy ai gwara tadinga tsorona. Mummy zatai magana ya shagwabe yace I missed u mum, hakanan yanzu kinfison kausar kanmu haba mum, yaufa nadawo harkin faramin fada kan ita, mum tace banason kana yawan dukanta mace ne, idan tai Abu ba daidaiba ka gyarata amma karka samata tsoranka aranta yace shikenan mum naji daganan suka cigaba da hiran da da uwa....






Fido sodangišŸƒ






Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)






[12/5, 3:56 PM] ‪+234 813 502 2313‬: [7/13, 1:53 PM] FIDDAUSI SODANGIšŸ’…: šŸƒKAINE GATANAšŸƒ

3⃣0⃣to3⃣5⃣ 3⃣5⃣to4⃣0⃣








NA FIDDAUSI SODANGI







Ā©TASKAR MARUBUTAšŸ“










"Kausar bata Kara fitowa daga dakintaba,bayan sallan isha an hadu a dining zaayi dinner amma babu kausar,


"Abba yace ina kausar?"mummy tace tana daki haydar ya tsoratamin ita takasa fitowa, Abba yace kai Umar Faruq jeka kirata,


" tana zaune kan gadonta umar faruq ya shigo da tsallenta tahau kanshi dayake kausar akwai son mugun wasa, Umar Faruq yadan zaro ido yace kinason Yaya yadaken?baya hanaki wasa dani ba?" adan taorace tace ai kai katoto ne kanada tsawo bazai dakekaba, yace injiwa? Yaya Aliyu yana decipline din kowa komi girman sa, baya daukan nonsense, yace tashi muje dinner Abba nakira, tamake kafada hawaye yazuba a idonta tace Yaya zai daken ai ko? "Umar Faruq yay murmushi yace ai sai anyi laifi yake duka yanzu dai mutafi tashi tayi tarike hanunshi gam suna kaiwa dining jikinta yafara rawa takasa zama ta tsaya, mummy tace zoki zauna my kausar ta girgiza kai tareda rike lips dinta tana kallon kasa, Abba yayi dariya yace my kausar zo kinji Haydar bazai Kara dukanki ba, dawani irin gudu tawuce inda Aliyu ke zaune ko dago kanshi baiyibama yanadai jinsu. Ta zauna kusa da Abba aka faracin abinci sai wasa take da abincin, mummy tace zaki farako wai mesa bakison cin abinci? ta tabe baki tareda buga kafa tana juya kai tace nibanaso, "Aliyu ya daure fuska yace oya eat ur food nabaki 1min kigama da plate dinan, da sauri tahauci taci Rabin plate tarike cikinta tacigaba daci, mummy tagane takoshi tace Haydar amata hakuri batada yawanci duka plate din yamata yawa murya Chan kasa yace OK. tashi tayi tafara kwashe plate din tana kaiwa kitchen tazo gaban Aliyu amma takasa daukan plate din hanunta narawa mummy da Abba suka Mike suka bar dining din, Umar Faruq ma haka, jikinta yacigaba da rawa, ya dago fararen idonshi ya kalleta yanda take hawaye tarike lips dinta gashi takasa cemishi zatadau plate din saitabashi dan tausayi.


"Yace kewai komi saikinyi kuka? Ta girgiza kai, yace hadiye hawayen ta hadiya, yace nace kiyi hold ur lips ne? Ta girgiza kai, ya daka mata tsawa will u remove ur hand 4rm ur lips my friend da sauri tacire. Yanda yaga tana harhada kafa yagane fitasari takeji kar tsoranshi yasa tasaki anan,yace dau plate din kitafi da sauri ta dauka tajuya takai kitchen tatafi dakinta tai fitsari. Bayan tagama shirin bacci ta fito ta kulle kofanta tawuce side din Umar Faruq saboda duk nyt yana bata story labari mai dadi sai 10 yarakota dakinta shima yatafi dakinshi.


"Tana shiga taga mutum akan gado ya lullube da bargo, da gudu tafada kanshi ta kwanta akan jikinshi tace yaya umar bacci kake is tym 4 my story, "Tahau birgima ajikinshi tana wakeup, duk da rigar jikinta nada kauri sosai amma yanda take goga mashi jikinta ajikinshi yasa kasala ta saukar mai,


" tunkudata yayi tafadi akasa ya Mike, daidai lokacin Umar Faruq
Ya shigo dakin yana fadin ya Haydar naje har gidan nasu amman tace ita bazata tahoba a can zata kwana, nikuma nayi tahowata,




"Kausar jabaya tafarayi a zaune tana neman hanyar guduwa, amma yariko hannunta yace waike wace irin mace ne? Namiji ne abokin wasan ki?" Yauzakici gidanku


"Waya gaya maki mace na wasa da maza?" Bakisan babu kyau ba! Sorry yaya wlh baxan sake ba.pls. idanuwansa ya kura Mata aikuwa da saurinta ta runtsa ido dan kuwa bala'in tsoron idon sa takeyi.ya Kama kunninta yaja da karfi tasaki ihu wayyo ya Aliyu pls am sorry baxan sakeba pls. Wlh idan kika kuma sai na cire wannan dan iskan bakin naki! Yasaketa aikuwa ta zura da gudu sai da takai dakinta sannan ta tsaya tana haki. Aikuwa tana kwanciya bacci ya dauketa cike DA tsoron Aliyu Haydar gadanga kusar yaki!




"Da safe suna zaune a parlour suna kallo itada mummy kanta na bisa cinyar mummy tanata zuba Mata shagwaba tana bata lbrn cartoon dinda akeyi sunata dariya.saiga Umar Faruq nan ya shigo, da gudu ta mike ta rungume shi tana fadin i miss u bro yau bangan kaba tun dazu Ina kashige? Sorry kausar naje unguwa ne , na manta ne jiya ban fada maki ba. Ta zunburo baki tasake shi ta juya masa baya tace kasayo min ice cream din?" Yace no sai anjima sai muje musayo ko? Tace A'a tare da bata fuska zatayi kuka nidai gaskiya yanzu nakeso mum ba tun dazu nake jiran Saba? Mummy tace gaskiya kuje asayo Mata.


"Tsalle takama yi tanajin dadi ahaka suka fice sanye take da riga da wando kanta ko dan kwali babu, Umar Faruq na rike da hannunta,


"Sun shiga motar zai tada kenan sai ga ya Aliyu nan yace Kai! inazaku haka!?"


Umar Faruq ne yace ice cream zamu musayo Mata. Ice cream?" Bataci abinci bane?" kobabu abinci a gidan ne?" da tsawa yake maganar da allah kufito Ku wuce Jo!!! dubeki!! Kalleki! ko dan kwali babu akanki amman wai ahaka zaku fita! Sai na karya maki kafa idan baki kiyayeni ba wallahi! da gudu ta ruga cikin gidan tabarsu nan tsaye yana cigaba da masifar sa,




"Jikin mummy tafada tasaki kukan ta mai bala'in cin rai da tsuma zuciya.a gigice mummy ke tambayan ta lfy me yafaru ina faruq din yake?" Kuka kawai takeyi itakuwa mummy hankalin ta ba karamin tashi yayi ba suna ahaka yayi sallama yashigo tsit Tayi ta hade kukan nan tamkar ba itabace take ta rusa ihu ba.


" Yace au kuka kikeyi? dasauri ta mike ta rike baki tana girgiza Kai no! Ba kuka nakeyi ba! Abinma dariya yabashi yadake yace tome kikeyi?" Mum tace wai dama Kaine kasata kuka?" Aliyu wai meyasa kakeyin haka ne wlh banajin dadin abinda kakeyi Sam tunda kadawo yarinyar nan atakure take inadalili ni kam banison haka gaskiya! To mummy menayi Mata dan kawai nace baxa a siyo ice cream ba?" Au wai hanawa kayi dama?" to wlh maxa ka tafi kasayo Mata inajiran ka yanzu kuma!


"Harara ya watsa Mata yace Bari kallo na Ana min magana kin tsareni da ido! dasauri ta runtse ido harya fice sannan ta bude.mummy Nata lallashinta.




"Towai mummy meyasa bazai koma gidan saba yake kwana mana a gida?" Ina matar tasa ne?" Nidai gaskiya mummy ki koresa yakoma gidan sa, wallahi ni nafison yaya umar, meyasa kika haifi ya Aliyu mummy bayada kirki fa! Murmushi kawai mummy tayi taka ra rungume ta, kausar takara shigewa jikinta tace mummy kuma kice masa yadaina cemin yar bak'a banaso! Banaso! Wai bak'a! Aidai bak'ina mai kyau ne ko mummy?" Murmushi mummy takuma yi tace ai kinma fishi kyau y'ata,




"Ranan monday misalin 2:30 umar faruq ya daukota daga skul yana ajeta yajuya yace Mata wani waje zashi.


" Jakanta ta goya a bayanta da gudu tashigo cikin gidan mummy nazaune a parlour tana karanta newspaper ta fada jikinta tana fadin am back mum mummy ta rungume ta tana shafa bayanta mum yaufa anbamu assignment bari kigani tasauko kasa ta zazzage littafan duka akasa tana niman book din da assignment din keciki can tace la!!! la!!!! Wlh mum sainabi zainab Muktar gidan su yanzunnan wlh ta dauke min book Dina ta mike ta nufi kofa mummy ta rukota tana fadin sorry my baby Kibari gobe idan kuka hadu a skul sai ki karba kuka ta fashe dashi tana cewa no! Mum no! Niyanzu xani! Mummy Nata lallabata dakyar dai tai hakuri kancewa gobe ta karba din.


Amman wai ita saitaje ta gayata da yaya Umar dinta saiya Zane ta gobe.mum tace to kije kicire kaya idan kikai wanka kikai sallah sai kixo kici abinci kinga sai kije Kai karar ko?" Ina ai da gudu ta fice ta nufi side dinsa, tana tafiya duwai nannan na kadawa kamar wata babbar budurwa, koda yake 16yrs aiba nan kusa bane, Uniform din riga da skirt din Iya gwaiwa sai dan hijabi Karami Iya wuya.kayan sun bala'in yimata kyau kamar ba uniform ba.daidai kwanan daza a shiga side din akwai wani lungu dan karami harzata shige sai taji kamar Ana magana kasa kasa aikuwa lungun ta nufa tana fadin waye ne awajan nan?" Ido hudu sukai da ya Aliyu yana zaune bisa kujerar roba hannunsa daya rike da waya akunninsa alamar waya yakeyi daya hannun kuwa sigari ne yake zuka (Taba) yana wani fesar da hayaki cikin kware wa. Ai kuwa da sauri takama ja baya tana kare fuskar ta da hannu alamar wai ita bata ganshiba. Yace ke!!!! Mekikazo yi anan? Jikinta na kyarma take fadin Allah ban gankaba wlh ko ganinka banyi ba.nibanma ko kallekaba Allah ya Aliyu!!!!


" Dariya ce taso kufce masa yace tocewa nayi kin kalleni?" Ta girgiza Kai yace waya koma inda kika fito! da gudu kuwa ta ruga yace keee!!!! Zonan!! Ta dawo tana jujjuya hannunta alamar ban hakuri sai kuma ta rike kunni tana motsa baki alamar pls am sorry dinnan.yace idan naji kingaya ma wani kinganni inashan wannan ya daga Mata sigarin hannun shi yace sai na yanka maki wuya na huda cikin ki!! Ido ta zaro alamar tsorata tace wlh ni banma gankaba! Yace gud kina Iya tafiya.ta gudu ta ruga ya fashe da dariya abinda baitaba ba.first time in history.......




Fido sodangišŸƒ






Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 3:57 PM] ‪+234 813 502 2313‬: šŸƒKAINE GATANAšŸƒ


4⃣0⃣to4⃣5⃣






NA FIDDAUSI SODANGI






Ā©TASKAR MARUBUTAšŸ“










"Tun daga bakin gate kausar ke jin hargowar Aliyu Haydar da alamar ransa a bace take, "dawowar ta daga islamiyya kenan, lefewa tayi a jikin k'ofar tana mai tsoron shiga, "kalaman dake fita a bakinsa yasakata natsuwa tana saurare, "A'a mummy! "Maganar Allah fa ba son zuciya ba, tayaya za ace k'atuwar budurwa kamar kausar ace tana irin wannan sangarta?" Yarinya sam bata san wani wai wannan namiji bane baligi bai kamata inayi masa kaza ba, baidace ni ina kaza ba! Haba mummy! Karfa ki manta yarinyar nan amana ce a hannunki! Na rantse da Allah wannan wasannin banzan dasuke aikatawa itada Umar Faruq haramun ne! Saboda ba muharraman sa bace! "Kai koda ma ace muharraman sace bai dace ba wallahi mace fa take! Gaskiya lamarin gidan nan akwai gyara wallahi sosai aciki dan wannan ba waye wa bace wallahi! Muji tsoron rannan da Allah zai tambaye mu, "mummy kiyi tunani ki duba maganata idan kuma ranki ya baci akan abinda na fadi to Allah ya huci zuciyar ki Amman wannan kam wallahi ba cinye wa bace!


"Waini abinda ma ke bani mamaki yarinyar nan fa tashin k'auye ce! To yaushe tayi irin wannan wayewar haka?" Acewai budurwa y'ar shekara goma sha shidda amman tana irin wannan sangarta saikace d'iyar goye?" Hmm! Allah ya kyauta, nabarki lafiya,


"Daidai k'ofar fita yaci karo da kausar wacce ke rakube gefe sai hawaye ne ke gudu bisa fuskar ta, tsayuwa yayi cak yana kare mata kallo,yaji dadin da Allah yasa tajiyewa kunnuwanta zancan sa, dan haka batare dayace mata uffan ba yai tafiyar sa,


"K'arasawa cikin falon tayi ta zube a jikin mummy tana wani irin kuka mai ban tausayi, mummy kanta shuru tayi takasa cewa komi illah bayanta datake d'an bubbugawa, sai da tayi Ku kanta iya son ranta sannan tafara magana cikin rawar murya, "hakika mummy abinda yaya ya fad'a gaskiya ne kuma nayi alkawarin cewa insha Allah zan canza halina daga yau zan gyara, ta tashi da gudu ta shige d'akinta tana mai cigaba da kukan nata,


****************************
" BAYAN SHEKARA UKU"
****************************






"Abubuwa sun faru sosai a wannan shekarun dasuka wuce ciki kuwa harda kammala karatun Kausar na secondary school,


"Kausar anzama babbar budurwa,Allah yayi mata k'ira mai daukar hankali komi na jikin kausar a cike yake,duk kayan data saka sai sun karbeta sunyi mata bala'in kyau gata dai bak'a kirin amman kuma bakin ta mai kyau ne,


"Soyayya suke itada Umar Faruq abin babu kama hannun yaro,wata irin soyayya ce mai wuyar fassarawa, suna bala'in son junansu sosai,


"Zaune suke a harabar gidan akan wasu kujerun roba suna fuskantar juna, "kausar meyasa kikeso ki ringa wahalar da zuciyata ne! Nace maki ki bari insamu abba da maganar mu amman kinki! Why?" Why?" Meyasa kike hanani mekike tsoro ne iyee! Yaya umar dan girman Allah ka rufa min asiri! Wallahi Allah ina tsoron faruwar wani abu, "A fusace ya mike tsaye yana fadin mekike tsoro meye shi abinda kikema tsoron faruwar?" Kausar kodai baso na kike ba! Idan baki sona kigaya min ki daina wahalar da zuciyata da gangan jiki na! Kifito fili ki gaya min cewar baki sona! Amman bawai kiyi tamin wasa da hankali ba ki dubenifa ni ba yaro bane yakamata ace na dade da aje iyali! Amman na tsaya inata jiranki nayi rainonki har kin girma na jure duk wani gori da ake min akancewa naki aure na toshe kunnuwa na amman sai ki zauna kina raina min hankali a banza a wofi! "Fashewa da kuka tayi tana fadin ba haka bane yaya Umar wallahi ba haka bane ina sonka ina kaunar ka bansan yanda zanyi maka bayanin irin sonda nake maka ba! Amman.....katseta yakarayi a fusace jikinsa har wani rawa yakeyi Amman me mekikeso ki gaya min kausar! Yaya Umar ina tsoron ya Aliyu......dasauri ya kuma katseta cikin rawar murya yace bangane kina tsoron Aliyu ba! Mekikeso ki gaya min iyyye!!.......... Gaba dayansu hankalin su yakoma kan gate din gidan da mai gadi ya wangale yana wani rawan jiki, motar sabuwace dal wace tashigo gaba dayan ta tint ce bak'a wulik babu yanda za ayi na waje ya ga naciki, motar tazo ta parka har a gaban su dukda cewar ba wajan parking bane wajan, "kusan minti uku sannan nacikin motar ya fito bayan ya kare masu kallo tas cikin kuluwa ya nufosu, zuciyar kausar tamkar zata tarwatse dan tsananin tsoro da gudu ta nufi cikin gida tabarsu nan tsaye kowanne zuciyar sa na bugawa tamkar zata fito waje................






Fido sodangišŸƒ




Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 3:57 PM] ‪+234 813 502 2313‬: šŸƒKAINE GATANAšŸƒ


4⃣5⃣to5⃣0⃣






NA FIDDAUSI SODANGI






Ā©TASKAR MARUBUTAšŸ“










"Wani irin mugun kallo Aliyu kewa umar wanda zuciyar sa ke tafasa yana kissima wani abu a zuciyar sa, "k'awafa Haydar din yayi sannan yai wani irin taku zuwa gaban sa ya nuna sa da d'an yatsan sa yana fadin nalura kamar kanka na rawa kwanannan ko?" To wallahi wallahi ka kiyayeni! Na rantse da Allah bakin rijiya bawajan wasan yaro bane! Kuma karka manta BABBAN GORO SAI MAGOGIN K'ARFE! "Yajuya a fusace zai bar wajan, Umar Faruq yayi saurin tsaidashi dafadin hyyy!!!! Dakata Malan!!! Ya isa har inda yake sannan yashigar da idanuwansa cikin nasa, cikin d'aure fuska yafara fadin nifa ban fahimce kaba bansan mekake nufi ba ban san manufar kaba wannan tada jijiyoyin wuyan nameye?" Yakama kafito ka fiddani cikin duhu......wani mugun tsaki Aliyu yayi yace lallai yaro wuyar ka ya giga! Tunda har kake iya kallon cikin ido

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment