You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"rigar ta yafara kokarin sakamata hade da hijjabinta, daukanta yayi cak zuwa cikin motarsa ya shimfideta a baya kafin yaje ya rufe gidan yana fadin wallahi kausar wasa nakeyi maki kawai nayi maki haka ne dan in tsorata ki amman bawai niyyata kenan ba na rantse da Allah dan Allah kada ki mutu ki tashi haka nan please natuba wallahi bazan karaba! " da gudu yaja motar yajefata bisa titi bayan ya maida gate din yarufe, "gudu yakeyi naban mamaki Allah ne kawai yakai su asibitin dayake aiki lafiya, " nanfa ya sunkuceta dagudu yayi ciki da ita,wata nurse data hango shi tabishi a baya da gudu itama,


"Duk wani kokarin sa naganin cewa kausar ta farka amman ina abin ya faskara nanfa hankalin sa ya tashi yanimi taimakon wani abokin aikinsa likita danyazo shima yanuna tasa k'warewar,


"Kuka Aliyu keyi sosai yana rokan kada Allah yasa yarinyar nan tamutu ta wannan hanyar shikam ya shiga uku mezaice da iyayan su, d'an likitan ne yadafa kafadar sa yana mai basa hakuri kayi hakuri Dr Aliyu insha Allahu zata farfado nanda awa uku ta tsoratane dayawa shiyasata shiga wannan halin, ka kwantar da hankalin ka komi zaixo dasauki insha Allah,


" Ajiyar zuciya mai k'arfi Aliyu yasaukar tare dayima likitan godiya, murmushi kawai yayi yafice abinsa yana mamakin irin rudewar da Ali yayi lallaikam yanaji dawannan kanwa tasa acewar likitan,


"Wayar sa dake aljihun wandonsa ya zaro yafara kiran number Abba,


" Gaba dayansu zaune suke a falon harzuwa wannan lokacin suna jiran zuwan su Aliyu din, Abba yagaji da korafi harya gaji yai shuru mummy ce ke tausar zuciyarsa, Umar Faruq kuwa jiyake tamkar yabisu danshikam sam baiyarda da Aliyu ba shiyasama baiji dadi da akace ya daukota ba yaso ace shine yaje ya daukota dakansa amman dai dole yahakura dan babu yanda zaiyi,


"Wayar Abba ce tashiga niman agaji dasauri ya daukota ganin number Aliyu yanaso yaji uwar dazai gaya masa ya shanya su tamkar kayan wanki, a fusace ya daga yana sauraransa, what!!!!! Garin yaya haka ta kasance?!...........mummy ce ta katse shi a rikice tana fadin meya faru abban su?" Wai hatsari sukayi a hanyar su tazowa yanzu kausar na asibiti......






Fido sodangišŸƒ




Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 4:23 PM] ‪+234 813 502 2313‬: šŸƒKAINE GATANAšŸƒ


8⃣0⃣to8⃣5⃣










NA FIDDAUSI SODANGI






Ā©TASKAR MARUBUTAšŸ“










"A fusace Umar Faruq yamike yana fadin wallahi karya ne! Wallahi karya yakeyi! " Abba karku yarda dazancan sa karya yakeyi.....tsawa mummy ta daka masa tana fadin bakada hankali ne?" To meye abin karyan aciki zancan Aliyun ne karya kokuwa zancan Abban kune karyar kokuwa hatsarin ne karya?" Dallah wuce kakaimu Mallan inga halin da yata ke ciki........a fusace Umar Faruq yafice a zuciyar sa kuwa fadi yake na rantse da Allah saina d"aure Ali har igiya tai rara idan har abinda nake zato shi ya faru hmm!Barister Umar Faruq kenan me saurin karantar mutum, kodan yana Barister ne oho!


"Gudu yaketa shararawa kamar zai tashi sama mummy ta daka mai tsawa kai dan uwarka ni tsaya in sauka! wannan wani irin tuki kakeyi na hauka haka?" Wallahi Umar wannan bakar zuciya taka babu inda zata kaika gara kayiwa kanka fada tun wuri wallahi!


"Sassauta gudun yayi yanawani cika yana batsewa! " A haka suka isa asibitin,nurse din dazu ce taimasu jagora zuwa dakin da kausar ke ciki kasancewar ta shaida iyayan Aliyu ne, suna shiga suka iskeshi zaune akan gadon datake kai yawani kafeta da ido, dasauri mummy taka rasa tana fadin Aliyu ya jikin nata?" Dasauki mummy bataji ciwoba tsoratane kawai tayi saboda yanda taga motar na juyawa amman dai Allah ya tsare nima babu abinda yasameni, yafada yana wani sosakai,


"Abba ma yakaraso kusa da gadon ya tattaba jikin kausar tare dayimata fatan samun lfy, " Aliyu ne yacigaba dafadin ai dogon suma ne kawai tayi insha Allah nanda anjima kadan zata farka,


"Umar Faruq nadaga k'ofa yana kare masu kallo, shikam sam hankalinsa bai kwanta da zancan Aliyu ba bai kuma san meyasa ba, " kujera suka ja suka zauna dukkan su ahaka har lokacin sallar azzahar tayi gaba daya mazan suka fice danyin sallah inda mummy ma tashiga toilet ta dauro alwala wata nurse ta bata dadduma ta shimfida ta gabatar da sallan ta,


"Ta idar kenan bada dadewaba Kausar ta farka a firgice daidai lokacin dasukuma mazan suka dawo suka shigo gaba dayansu, " wayyo Allah na ya Aliyu kayi hakuri dan Allah wayyo!!!!!! Nashiga uku!!!!!!!!dasauri Aliyu ya karasa inda take yayi saurin yi mata allura ganin zata tada zaune tsaye!


"Wani irin shak'a Umar Faruq yayi masa yana fadin uban me kayimata! Mekayi mata Aliyu mekayi mata nace?!! "Sam Aliyu yakasa wani yunkuri dan yasan baida gaskiya gaba daya jikinsa yai bala'in yin sanyi, " wani wawan mari mummy takwashe Umar Faruq dashi tana fadin bakada hankali ne?" Wai yaushe ka haukace ne ni bansani ba Faruq?! Kokuwa kanaso ka gaya min cewa kai bakasan kaddara bane?! Kokuwa kanaso ka gaya min cewa da gangan Ali yayi hatsarin da ita?" Idanuwan Umar sunkada sunyi jawur sai ajiyar zuciya yakeyi alamar ran maza ya baci! "Dakyar ya iya bude baki cikin sarkewar murya yace but mummy....... Shiiiii!!!!! Ta katse shi banaso inji komi daga gareka mezaka gaya min mezakace sake shi dallah! Asanyaye ya saki wuyar rigar tasa yanayi masa wani mugun kallo, Abba ne yace tunda haka abin yazama to dukkan Ku kuzo mu koma gida shi Alin yazauna da ita ya kula da ita har ta farka, yadubi Aliyu yace bana bukatar ayi mata wata allura idan har ta farka ataho min da y'ata gida kawai kanajina ko?" Eh naji Abba, oya kumuje yayi gaba yabarsu nan, wani irin kallo Umar yayi masa kafin ya fice, "mummy ce ta dafa kafadar sa tare dafadin kayi hakuri son bansan meke damun Faruq haka ba! Bakomi mummy kowa yayi nagari ai kansa! Hakane Allah yabata lafiya Ameen,


" Bayan tafiyar su da awa daya takuma farkawa tana ihu ido kawai Aliyu yasama har ta bude idonta ta diro daga kan gadon, ido suka hada da Aliyu hadiye kukan tayi tana fadin kayi hakuri ya Aliyu dan girman Allah kada ka tabani ka rufa min asiri please! "Wani irin malolo Aliyu ya hadiye ya dubeta yace kausar ki kwantar da hankalin ki wallahi dama wasa nake maki babu abinda zan maki kawai inaso in gwada ki ne dama kinji?" Kai kurum ta daga masa amman zuciyar ta sai bugun tara tara yake, "sai data huta tashiga natsuwar ta kafin yatasata gaba zuwa gida,...........




Fido sodangišŸƒ






Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)










[12/5, 4:23 PM] ‪+234 813 502 2313‬: šŸƒKAINE GATANAšŸƒ


8⃣5⃣to9⃣0⃣






NA FIDDAUSI SODANGI










Ā©TASKAR MARUBUTAšŸ“








"BAYAN K'WANA BIYU"






"Babu irin nacin da Umar Faruq baiyiba akan Kausar tagaya masa abinda Aliyu yayi mata amman sa ta kiya,cewa take kawai wallahi babu komi towai kai ya umar mekake tunanin zaimin ne?" Hmm! Shikenan tunda bakiso ki gaya min yanzu munfara yan boye boye a tsakanin mu kenan, nima bazakidinga jin cikina ba daga yanzu! "Ahakadai aka shashantar da zancan,


"Da daddare bayan sungama cin abinci abba ya kira Aliyu yace maza yazo yana bukatar ganin sa yanzu, " ba a dau wani tsawon lokaci ba saigashi ya baiyyana, zaune suke gaba dayansu a falon abba, yaran na zaune a k'asa su mummy kuma suna bisa kujera, "abba ne yafara da kallon kausar yace y'ata wannan taron fa domin ki akayi shi, yanyinki ne suke rigima akan ki to nikuma gaskiya banason abinda za a tauye maki hakki, dan haka yanzu zamu baki zabi acikin su ki fidda duk wanda yayi maki zuciyar ki keson shi kike ganin halinsa yayi maki kuma zaki iya zama dashi batare danaji wata rigima ta taso ba! Ina fata kin fahimce ni?" Zuciyar kausar in banda bugawa babu abinda yakeyi, itakam ansakata a tsaka mai wuya!


"Kanta tadan dago tasaci kallon Aliyu shima ita din yake kallo idonshi ko kiftawa bayayi, dasauri ta kauda kai, Umar Faruq ta kalla wanda shima nasa idon akan ta yake fuskar shi na dauke da murmushi,


" mummy tace uhum munajin ki baby na! "Cikin sarkewar murya tace abba ni yaya Faruq nake so......aikuwa kafin ta rufe baki Aliyu yai wani wawan tsalle ya kai mata wani naushi a baki nanda nan jini yafara zubowa, Umar Faruq ya mak'ure sa yana fadin uban me tayi maka dazakaji mata ciwo?! " wani maka da Aliyu yai masa saigashi k'asa warwas, "Abba yace yauwa ku kashe kanku, idan d'aya ya kashe d'aya sai kuyi mana magana muna ciki, " nafisa tashi muje! "Mikewa tayi itama adan fusace tayi gaba abinta, " kuka sosai kausar keyi ganin kamar ran iyayan nata ya baci dangane da zabinta, "Umar Faruq ya mike ya nuna Aliyu da dan yatsar shi yace " fice kabar mana gida tunda tace batayi dakai ai sai aje a rungumi hakuri aci gaba kuma da maneji da........wani irin dariya Aliyu yayi yace k'arfin hali barawo da sallama! Yasake fashewa da dariya ya nuna Umar Faruq yace ni kake kora a cikin gidan nan?" Nida kai wayafi wani iko da gidan! Lalle to bari in tuna maka idan ka manta.......






Fido sodangišŸƒ




Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 4:23 PM] ‪+234 813 502 2313‬: šŸƒKAINE GATANAšŸƒ


9⃣0⃣to9⃣5⃣






NA FIDDAUSI SODANGI








Ā©TASKAR MARUBUTAšŸ“










"Kul!!! Naji maganar nan tafito daga bakin ka,bakada hankali ne?" To yanzu idan ka tuna masa a haukar ka me hakan zai haifar?" Meye amfanin yin hakan?" Bashida wani amfani! Dan haka shurun shiyafi zama alheri! Fice kabani waje mutumin banza kawai! "Abba ne keta wannan fadan danjin Aliyu zaiyi masa katobara acikin gida!


" A fusace Aliyu ya fice kai tsaye gidan sa ya nufa yasa key ya bude kofar ya shiga, "gidan shuru tamkar babu kowa a ciki, kai tsaye wajan firij ya nufa gorar ruwan swan ya dauko irin babban nan, budewa yayi yakafa kansa yaringa kwankwada bashi ya ajeba saida yaga ya shanye shi tas! Sannan ya hakura ya fada bisa kujera yana maida numfashi tamkar wanda yayi tsere,


"Yafi minti goma ahaka kafin ya mike zuwa d'akin sa wanka yayi yaji sanyi kafin yasaka kayan baccin sa, wasu magunguna ya balle ya hadiya tare da korawa da ruwa sannan ya zauna kamar minti goma yana lallatsa wayar sa kafin ya kasheta ya fice daga d'akin tare da rufo k'ofar, " kai tsaye d'akin ummi Aisha ya nufa 'kwance take bisa makeken gadonta tana bacci, wata yar guntuwar rigar bacci ce a jikinta gaba daya ya tattare yayi sama, "kyakkyawan fuskar ta ya tsurama ido na tsawon lokaci kafin ya kashe wutar d'akin, gadon ya haye tare da jawota jikinsa yafara shasshafata cikin sauri sauri, " a tsorace ta farka tana zare ido, "cikin rawar murya tace Aliyu dan Allah kayi hakuri ka yafe min bazan karaba please dan Allah! Shiiiii!!!! Ya dora dan yatsan sa bisa bakinsa,alamar taimasa shuru! " cigaba da shafata yayi yanawani shinshinarta tamkar wani mage, jin yana kokarin rabata da rigar ta yasa tai saurin rike masa hannu tana kuka, Aliyu wallahi na gaji yaufa kwata kwata abinda karinga yi kenan ko fita yau bakayi ba in banda abba daya kiraka dan Allah kayi hakuri wallahi natuba bazan kara ba....bakin sa yakai cikin nata yanai mata wani irin salo, "da karfi ta fisge kanta tana kuka tana fadin nace kayi hakuri nace kayi hakuri kaki! Indai akan maganine ai ka kwashe bashi kenan ba to mezaisa ka ringa cutata!


" Hannu yasa ya kunna wutar d'akin yana kallon cikin idonta, a fusace yafara magana ohh!!! Ashe kinsan laifin naki! To tunda kinsani inaso inji meye dalilinki nayin hakan?! "Sonane bakiyi kokuwa kaunata ne bakiyi?! Kokuwa tsabagen iskanci ne dasamun waje! Ke nake sauraro! Kuka kawai takeyi sam takasa magana, daga k'arshe jawota yayi da k'arfin tsiya nan suka shiga kokawa da karfinsa ya kece rigar ya shiga aiki babu ji babu gani, tun tana daurewa harta fara zanbada ihu tana niman kufcewa, haka yaita wahalar da ita har asuba,


" Dasafe bayan yayi wanka yayi shirin zuwa aiki ya kalleta a fusace fuska babu annuri yace "kada indawo gidan nan in taddaki tunda baki kaunar hada jini dani banga amfanin zama dake ba! " a tsorace take kallon sa har ya fice daga dakin ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya tana mai data sani, yanzu mezataje tace a gida?" Itakam tashiga uku idan mahaifin ta yasamu wannan labarin, wai ita anata haukan bataso tafara haihuwa yanzu ta tsofe Aliyu yai sabuwar Amarya ya fara yi mata wulakanci, ita kuwa a rayuwarta ta tsani kishiya ko sunanta batason ji! Yanzu meye lafiya?" Wayyo ni ummi Aisha "NAGA TA KAINA!" Aliyu meyasa zakace intafi gida bayan kasancewa "KAINE GATANA!"...........




Fido sodangišŸƒ




Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 4:23 PM] ‪+234 813 502 2313‬: šŸƒKAINE GATANAšŸƒ


9⃣5⃣to1⃣0⃣0⃣






NA FIDDAUSI SODANGI






Ā©TASKAR MARUBUTAšŸ“






"BAYAN SATI BIYU"


*******************


"Bayan dukkan wani sabani da a ka samu a k'arshe dai abba ya yanke hukun cin cewa nanda wata biyu za ayi bikin kausar da Umar Faruq kowa ya hutu, " ran Aliyu ba karamin baci yayi ba dajin wannan furucci na abba, acewarsa ai dashi kausar ta dace bada Umar ba, kuma ai badole sai tanason saba za a Iya bashi ba, shikam gaskiya ba ai niyyar bashi bane kawai!


"Mummy ce keta kwantar masa da hankali, my son dan Allah kacire damuwa a ranka kasandai wani baya auran matar wani dan haka kaidai kaci gaba da addu'a kawai,


"Kausar kuwa sun dad'a kullewa da Umar Faruq soyayya akeyi baji ba gani akoda yaushe zaka samesu tare suna tattauna yanda bikinsu zai kasance, " idan akai kaza za ayi kaza,kullum maganar kenan,Aliyu kuwa har zuwa gidan ya rage dan kuwa bayason ganin kayan takaici acewar sa, wani irin haushin su yakeji musamman ma kausar wacce yakeji tamkar ya mak'ureta dan tsananin haushinta dayakeji,
***********************




"Abba ne zaune a falo shida mummy suna dan tattaunawa akan bikin,
"Nafisa wani tunani ne nakeyi acikin zuciyata, a hankali mummy ta dubesa tare da gyara zama, tunanin mekakeyi haka abban su?"


"Inagani lokaci yayi dayakamata mu waiwayi k'auyen su yarinyar nan kausar saboda muji ko akwai wani lbr akan iyayan ta ko y'an uwanta, domin kuwa yakamata asakasu cikin lamarin auran nan koya kika gani?"


"Ajiyar zuciya tasauke mai Karfi tare da fadin tabbas kayi tunani mai kyau abban su, saidai wani hanzari ba gudu ba, mezai hana mu bari akare bikin lafiya sai mu tafi gaba dayan mu inaga su iyayan nata da yan uwanta zasufijin dadi ganin mun riketa da amana harmun aurar da ita,inaga hakan zaifi koya kagani?" Hakane nafisa, hakane, abinda yakamata kenan,Allah yayi mana jagora Ameen,
***********************




"BIKI WAN SHAGALI!"




"Biki fa ya kankama shagali kuwa babu kama hannun yaro, biki akeyi na kece raini abin sai wanda yagani, anyi party yakai kala goma sannan daga k'arshe aka gudanar da walima wanda yatara manyan malamai akayi wa Amarya da ango nasiha mai ratsa jiki wanda gaba dayansu babu wanda jikinsa bai yi sanyi ba,(Aliyu dai yace shiririta kenan saida aka gama zuk'e albarkar auran awajan party sannan za a wani fake da walima)




" Ranan d'aurin aure yakasance jama'a bayan ansauko masallaci, dubunnan jama'a suka shaida d'aurin auran Umar Faruq da kausar, "hakika wannan d'aurin aure yaga tarin mutane daga kasa kasa gari gari kasancewar abba d'an siyasa,


" Amarya tayi kyau harta gaji duk wani gyara daya kamata aimata babu wanda ba ai ba musamman mummy ta dauko masu gyaran amare tundaga Niger, sokoto, Maiduguri, dan kawai a gyara mata y'arta ciki da bai, aikuwa ba karamin gyara tasha ba dan har wani k'elli takeyi batun k'amshi kuwa ba a cewa komi domin kuwa itacema k'amshin! "Maganin mata kuwa masu inganci tasha su har tausayawa kanta takeyi domin kuwa tasan ma'anar su tunda ba k'ankanuwar yarinya takeba, hatta Umar Faruq mummy bata kyale ba shima ya shassha wayanda suka dace yasha, har mamakin mummy yakeyi sam batajin kunyar su kanta a waye yake tazama free da y'ayan nata shiyasa suma basa iya boye mata komi nasu, fruits kuwa sunshashi harsun gode Allah domin sunama kan sha dan kuwa yazame masu abincin cinsu, gaskiya mummy ta taka rawar gani!




"Da daddare anata shirye shiryan kai Amarya gidan ta,wata kanwar mummy ce ke shirya ta cikin wata lifaya tayi bala'in yin kyau tamkar a sace a ruga, wayar ta sai tsuwwa takeyi, gashi sai kira akeyi babu kakkautawa, kanwar mummy mai suna maijidda ta miko mata wayar amshi hala ma angon ne ya ishemu inma yayi hakuri ai yanzu ne za a kai masa ke! " kausar dai ta amsa tana murmushi kafin ta duba screen din wayar aikuwa shine ke kiranta, asanyaye ta d'auka tana fadin "hello!" Ki fito wajan gate yanzu ina jiran ki kiyi sauri! "Daga haka bai kuma cewa komi ba ya kashe wayar tasa, dasauri ta mike tace anty maijidda inazuwa dan Allah! Ina zaki inazuwa dai tayi ficewar ta mata dankare a falon anajiran fitowar su, dasauri sauri ta fice kamar wata tsuntsuwa dan bama kowa ya lura da ficewar taba, " hankalin tane bai kwanta ba dayanda taji muryar Faruq dinta jin muryar tayi tamkar ba tasa ba, kuma tamkar wanda yasha kuka ya koshi!


"Tana fitowa wajan gate din taga motarsa batare da tunanin komi ba ta fada kasancewar motar tint bataga kowaye ba harsai data shiga ta zauna, motar ya dannawa luck, a firgice take kallonsa ita rabonma data gansa tunkan asoma hidimar biki! Bakinta na rawa tace "yaya Aliyuu!!..........






Fido sodangišŸƒ




Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 4:25 PM] ‪+234 813 502 2313‬: šŸƒKAINE GATANAšŸƒ


1⃣0⃣0⃣to1⃣0⃣5⃣








NA FIDDAUSI SODANGI




Ā©TASKAR MARUBUTAšŸ“




Bakinta na rawa tace
yaya Aliyuu!" bai sauraretaba yaja motan dagudu wanda hatta mai gadin sai dayaji tsoro dagudu ya lek'o dan ganin meke faruwa, baici nasarar ganin komi ba illa iyaka kurar daya turnike wajan, a dan tsorace yadawo ciki yana kissima abubuwa a zuciyar sa, to koma dai meye Allah yasa lafiya acewar sa,




" Gudu Aliyu yake a titi kamar zai tashi sama,itako kausar sabo da tsabar tsoro ta kasa magana saidai jikinta dake rawa kamar ana kada mazari,idonta kuma nafidda hawaye kamar anbude famfo ta takure jikinta akujeran, tana mai rokon Allah ya rabata da sharrin Aliyu Haydar!


" Acan gida kuma anty maijidda tagaji da jiran kausar gashi mutane harsun fara kosawa, wata yayar su mummy ce tashigo tana fadin maijidda wai wani irin shiri kikema y'ar taki haka ne har yanzu kunki fitowa tamkar an shuka dusa?" Ganin maijiddar ita daya yasata fadin to ina amaryar kuma?" Murmushi anty maijidda ta kirkiro na karfin hali tace tashiga toilet yanzu zata fito, "to yakamata dai tafito haka nan ahadata da abban nasu yaimata nasiha atafi hakanan dan ga hadari nan ya hadu sosai mutane kowa naso akaita ya kama gabansa, tafice abinta tana ci gaba da sababinta,


"Hankalin Anty maijidda yakara tashi ganin ankuma k'wasar wasu mintinan batare da dawowar kausar ba, haushi da takaici yasata
fitowa daga dakin tanufi d'akin mummy kai tsaye, tasami dakin cike makil da kawayen mummyn, matsawa tayi har inda mummyn take ta sassauta murya tafada mata cewa faruq yakira kausar gashi haryanzu bata dawoba kuma tashafe sama da minti talatin,


" Aiko nan mummy tahau ta dafada meyasa zata barta tafita wannan ai rainin wayau ne! wani irin aikin banza ne zasu maidamu iyayen kawai,kai yaran yanzu suncika zumudi inyayi hkr saura minti nawa ne zaakai mishi ita?" Wata kawar mummy ce tafadi haka jin inda zancan na mummy ya nufa, maijidda dauko mun wayata gashi can akan drower inkirashi inji inda suke.


"Anty maijidda tanufi wajan da sauri zuciyar ta cike da takaicin yanda aka d'ora mata laifin fitar kausar din, mummy takira wayar faruk fiye dasau goma amman shuru babu amsa, tashiga kiran kausar din itama shuru daga k'arshe ma aka kashe wayar, hawaye ne yacika idon mummy wannan wani irin tijara ne haka!


"A bangaran Umar Faruq kuwa tun bayan d'aurin aure yake niman wayar sa bai ganta ba bai kuma san ina ya ajetaba har izuwa yanzu da abokansa suka cika farfajiyar gidan su da motoci na alfarma dan daukar amarya, gaba dayansu sun kosa daganin fitowar amaryar dankuwa har an fara yayyafi, sai a lokacin ya lura da babu motarsa ma a inda ya ajeta, bai wani damuba dan yayi tunanin kila daya daga cikin abokansa wani ya dauka tunda sha'ani akeyi kuma dama key na ajiki yabar ta dazu dan saurin yashiga ya fito," wani abokinsa mai suna faisal yace kai Faruq ka shiga ka fito da ita da kanka tunda sunki fitowa, hararar sa Umar Faruq yayi yace ai sai kazo ka jawoni! Bai karasa fadin abinda yayi niyya ba yayi shuru dan hango mummy dayayi ta taho wajansa a fusace,


"Batai wata wata ba tanazuwa ta d'aukeshi da mari har guda hudu k'warara baki yasake yana kallonta hannunsa dafe da k'uncinsa, bama shi kadai ba gaba daya abokansa dake wajan bakin nasu a bude yake suna tambayar zuciyoyinsu dameyayi zafi haka za a tsittsinkawa ango mari a irin wannan lokacin?"


"Hannu ta nuna masa tana huci, cikin sarkewar murya tafara magana daganinta kasan ranta a matukar bace yake, aidama ance tsintaccan mage bashi mage! Nizaka wulakanta ka tozarta?" Menayi maka Faruq dakake nima ka kunyatani a idon duniya?" Cikin kidima yace ban fahimce kiba mummy menayi maki?" Wani marin takuma sakar masa tana fadin au! Tambayata kakeyi?" To ina kausar?!!!! A firgice ya dubeta yace kausar? Wallahi mummy tunda safe rabon da in ganta! "Murmushin takaici tayi tace ni zaka rainama hankali Faruq ta nuna kirjinta da dan yatsanta, na rantse da Allah mummy rabona da inga kausar tun dazu da safe! " ido mummy ta zaro tana kallon sa..........




Fido sodangišŸƒ




Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 4:26 PM] ‪+234 813 502 2313‬: šŸƒKAINE GATANAšŸƒ


1⃣0⃣5⃣to1⃣1⃣0⃣








NA FIDDAUSI SODANGI






Ā©TASKAR MARUBUTAšŸ“








"ido mummy ta zaro tana kallonsa cikin rawar murya tace kausar din allura ce kenan dazata bace ko?! " wani tunani ne yazowa Umar Faruq dasauri ya juya zai tafi mummy tace wallahi umar zanci mutuncin ka idan baka turo min y'ata ba! Mummy Kausar na wajan Aliyu duk inda yake a yanzu! A fusace tace mekake nufi da wannan kalma taka?! Cikin wata irin murya tayi maganar, bai kara cewa komi ba dasauri yabar wajan, ido ta bishi dashi kafin tayi k'wafa ta wuce,


"Da sauri faisal yabi bayan Umar da mota, mai gadi ya bude masa ya fice can ya hango umar nata sauri ko ina zashi oho! Hon yayi masa dasauri Umar Faruq ya waigo yana ganin shine ya fada motar yana fadin Faisal taimaka muje barhim yi sauri dan Allah! Cikin rashin fahimta Faisal ya dubesa mezakajeyi ne a barhim yanzu?" Cikin kuluwa yace baza ka kaini bane in sauka?! Dasauri yaja suka tafi,


"Kuka takeyi sosai tana fadin nace maka bazan shaba dole ne! Wallahi ka maida ni gida Aliyu idan baso kake inyi maka abin da baka zata ba! " dubanta yakeyi da tsananin mamakin yanda sam yaga rashin tsoron sa a idonta, ni kikema tsawa kike kirada Aliyu gatse haka?! Ni tsaran kine?! Na fada na fada kazo ka maida ni gida! "A fusace ya jawota yana fadin wallahi saikin sha shi matse ta yayi da k'arfin tsiya duk iya kokarinta na ta kufce ta kasa sai mutsu mutsu take, hannuwanta ya batse a bayanta sannan yashiga dura mata yar maganin dake cikin kwalba na hannunsa, saidaya dure mata shi tas sannan ya saketa , dasauri ta mike, saikuma ta tsaya cak tana kallonsa nanda nan idanuwan ta suka canza kala, " a hankali ya taso ya iso inda take dasauri ta fada jikinsa tana maida numfashi, dago kanta yayi yana kallon cikin idonta sannan yace kausar! "Dakyar ta iya amsawa yace kina sona?" Dasauri ta daga masa kai, ko tunanin meyayi oho kawai dasauri ya tureta daga jikinsa ta tafi luuu zata fadi dasauri ya tare ta daukarta yayi cak zuwa bisa kujera ya kwantar da ita yana kallonta hawaye ne ke bin fuskar ta ita kanta batasan na meye ba, cikin murya kasa kasa tace ya Aliyu dan Allah matso kaji! Kai kawai ya girgiza mata alamar a'a kawai saita fashe da kuka tana fadin pls ya Aliyu pls......tsayuwar mota yaji daga wajan gidan can, dasauri ya karasa wajan window yana lekawa, Umar Faruq ya hango ya bude gate din da Karfi tare da shigowa kamar wani zaki haka Aliyu ya hango sa, aikuwa dawani

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment