You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iyayyen nashi suka haifa.
Mahaifinshi ya mutu kusan shekaru goma kenan hakan yasa mahaifiyarsa ta koma
Nigeria a yanzu tana zaune ne a d'aya daga cikin gidaje da mahaifinshi ya bari a
Abj, shi ma yana daff....da komawa Nigeria.
Tun ya shigo yake kallon barrister A k'asa hak'uri ya yi ya mik'e ya nufi
wajenta cikin husky voice dinshi ya ce "hey......beautiful!
Barrister A ta d'ago kad'an ta kalle shi saura kirisss....ta kwalla ihu
sakamakon yanda ta tsorata tare da bud'e idanuwanta, ba don long necklace mai dauke
da cross da ke sanye da wuyan shi da tace Aliyun ta ne.
Tabbas ba ko tambaya tasan wannan twin brother Aliyu ne, saboda tsananin
kamanun su kuma kafin momma ta mutu ta sanar da cewa abokin haihuwar Aliyu bai mutu
ba ranshi ta jefar da shi.
Cikin tsadadd'en turancin shi ya ce zan iya zama.
Cakk.....barrister A ta mik'e tsaye ta shiga rarraba idanuwa ko za ta hango
Aliyu, can.....ta hango shi tafe tun kafin ya k'araso ya ga wani k'ato tare da
matar sa hakan yasa ya k'ara sauri da yake iya bayan shi yake iya hangowa.
Yana k'arasawa dai-dai Joel yana jiyowa karaf.....suka had'a idanuwa sauri
kad'an kowane su ya saki fitsari a wando, Joel ya fi Aliyu shiga firgici saboda bai
san yana da d'an uwa ba saboda iyayyen shi shi kadai suka haifa sa6ani Aliyu wanda
bai dauki dogon lokaci ba ya dawo cikin natsuwar shi, bai san lokaci da ya rungume
Joel ba.
Duk da Joel bai san alak'arsu ba sai kawai ya tsince kanshi da k'amk'ame Aliyu
d'in.
Bayan sun saki juna Aliyu yake mishi bayani ba wai haka kawai suka yi kama ba,
su Twins ne Joel ya 6ata tun yana jinjiri hatta da 6th finger irin na Aliyu Joel
yana da shi.
Shi kanshi Joel ya yarda da abin da Aliyu ya fad'a duk da ana kama a duniya
amma kamanun shi da Aliyu, dole ta kasance ta jini ce.
Babu 6ata lokaci suka nufi gidan Joel d'in inda ya kira mahaifiyarsa mrs Kenneth
domin ya ji daga bakin ta, da yake a vidoe call ya kira ta ya nuna mata Aliyu ya
kuma sanar da ita abin da ya sanar da shi.
Nan take ta fashe da kuka cikin kuka ta sanar da shi gaskiya mr Kenneth adopted
dinshi ya yi a gidan marayu kasancewar bashi haihuwa, amma ya sani har gobe tana
kallonshi a matsayin d'an su tana kuma taya shi murna gane biological parents
dinshi da ya yi.
Tsabar farin ciki da kuma suna so su yi surprising family su yasa washe gari
suka dawo Nigeria tare da Joel.
Lokaci da Umma maryama tayi arba da d'anta da ta fidda ran gani saida ta suma
aka yayyafa mata ruwa ta farfad'o, Daddy ranar kamar zai yi hauka.
*AFTER THREE MONTHS*

A cikin watani uku abubuwan farin ciki sun samu a M Ardo family, inda Joel ya kar6i
musulunci ya tashi daga Joel zuwa Abdulrazaq sai cikin da Barrister A take dauke da
shi na tsawon watani uku.
Burin Daddy ya cika iyalinshi sun kammala kuma suna cikin farin ciki.
Bayan wata biyar barrister A ta haihu ta sami baby boy, ranar suna ya ci sunan
Uncle Suraj saboda tunawa da Uncle yasa.
"suna kiran shi da Aiman rayuwar Barrister A da Aliyu gwanin ban sha'awa kullum
k'ara k'aunar Juna suke yi.



*TAMMAT BIHAMDILLAH*

_ANA NA KAWO K'ARSHEN LITTAFIN GIDAN RINA KUSKURE DA KE CIKI ALLAH YA GAFARTA MIN,
IDA NAYI DAI-DAI ALLAH YASA YA AMFANI AL'UMMAH MUSULMI_

Sai mun had'u a cigaban novel d'ina mai suna *ZAZZAFAN KISHI*
Jeeddah Aliyu




Jeeddah Aliyu

Downloaded From https://tknovels.com.ng


1 Comments On Gidan Rina by Jidda Aliyu
avatar
hidaya-ismail

2 months ago

Reply

Allah ya Kara basira

Please Login or Register in order to submit comment