You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi miki rashin mutunci na nuna miki 'yar
zamani ce ni.
"Dole ta kama hanya ta koma flat d'inta amma da kudurin sai ta binciko matsayin
Maryama agidan.
****----*****----****
Daddare suna zaune a downstairs falo kowane su yana aikin gabanshi, yayin da Aliyu
yake kallon basketball da ake haskawa a allon television.
Barrister A kuma tana sarrafa laptop can ta d'ago tana murmushi ta ce "Yalla6ai ina
fatan ba ka manta ba ranar Monday zan fara zuwa office....?
Shima d'agowa ya yi yana yatsine fuska, ya ce "uhm....ke nan murna kike yi za ki
fara cud'anya cikin wasu maza, gaskiya Amina ba zan 6oye miki ba ina da tsananin
kishi sai kin kula ta yadda za ki dinga mu'amala da abokan aikinki, banaso yawan
cud'anya da maza ki kiyayye banso mu fara samu matsala ta dalilin aikinki.
Ya karashe magana yana wani k'ara daure fuska.
"Murmushi tayi mai sautin gaske ta ce "Yalla6ai kenan har yanzu kana da saura sani
wacece Barrister Amina Abdallah Barkid'o, shiyasa har kake wannan tunani akaina
anyway zan kiyayye kaman yanda ka fad'a.
"Haka ya kamata ki fad'a ba wai ki ce ina da sauran sani akani ba.
Murmushi kawai tayi ta cigaba da abinda take yi, lokaci kwanciyarsu bacci ya yi yau
ma a dak'inshi suka kwana saida ya, ya motsata son ranshi sai dai bai yi mata komai
ba sannan suka yi bacci.
Washe gari kasancewar Juma'a ce k'aramin lokaci ne yasa ta tashi da wuri ta had'a
mishi breakfast kaman yanda ta saba, bayan ya kammala ta raka shi sai dai yau iya
k'ofar fita main parlour ta tsaya, ya bata goodbye kiss sannan ya nufi flat d'in
momma koda ya shiga bedroom d'inta tana wanka, sai kawai ya wuce na Daddy cikin
tsananin damuwa ya tararda Daddy, sosai Aliyu ya tsorata da gani mahaifin nashi
cikin wannan yana yin.
"Jikinshi ya yi matuk'ar sanyi ya nemi kusa da Daddy ta yadda zai fuskance shi
da kyau ya zauna.
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:18 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*



*30*


Saida ya k'arewa Daddy kallo kafin ya ce "Don Allah ka daure ka gayamin abinda ke
damunka, bana jin dad'i ko k'adan idan naganka cikin dumuwa.
"Ajiyar zuciya Daddy ya sauke ya shafi gemunshi cikin rauni murya ya ce Sultan
ni kaina ba zan iya fad'ar takamame abinda ke damuna ba, saidai inaji kaman narasa
wani gurbi a jikina.
"Aliyu ya yi shiru yana nazarin maganganu Daddy, kafin ya nisa ya ce "Daddy na
fahimce ba kaso ka sanarda ni damuwarka, amma koma menene ka rage tunani kada ya
shafi lafiyarka.
Shikenan my boy zan yi amfani da shawararka sai abu na gaba ina tunani lokaci ya yi
da zan fita da Maryama abroad a duba lafiyarta, ko Allah zai sa adace ni sai nake
mamaki meyasa duk tsawon lokaci da Maryama ta dauka cikin rashin lafiya na kasa
bata kulawa yadda ya dace.
Sultan ina zargin kaina da rashin yi ma rayuwar Maryama adalci, musanmman idan na
tuna da irin hallaci da ta yi min.
Rashin lafiyar Maryama tana d'aya daga cikin abinda ke adabar ruhi da gangar
jikina, a duk kwana duniya sai nayi yunk'uri shiga flat d'inta na dubata sai naji
na kasa.
"my boy ka sakani a addu'a Allah ya yaye min wannan matsala, inajin tsoro na mutu
a wannan yana yin tabbas ubangijina zai tuhume ni akan rashin adalci da na
shinfid'a a gidana.
Tsawon shekara 28 da nayi watsi da rayuwar Maryama ban kuma sake waiwayarta ba,
abin takaici mu kwana mu tashi a gida d'aya.
"Lokaci ya yi da zan gyara abinda na 6ata banaso na mutu da hakki Maryama.
Ya karashe magana hawaye na zuba daga kwarmin idanuwanshi.
Naunayyar ajiyar zuciya Aliyu ya sauke ya gyara zamanshi ya rik'o hannun Daddy na
dama ya had'e da nashi, ya sanyayya muryarshi ya ce "Daddy ka daina blaming kanka
is not your fault musanmman idan akayi la'akari da yana yin aikinka wasu abubuwa ba
za ka iya gudanarda su da kanka ba, in fact Daddy naga momma tana kula da ita
sosai.
Ajiyar zuciya Daddy ya yi ya ce "please.....Sultan idan ina magana ta arziki ka
daina sako min mommanka, wallahi ko sunanta banaso ji.
Cike da mamaki Aliyu yake kallon mahaifin nashi kafin ya nisa ya ce "Daddy kun sami
matsala ne da ita...?
Ba ko d'aya kawai dai banaso zancenta mu ajiye shi a gefe, muyi wani.
Shikenan Daddy wane country kake tunani a fita da ita sai na nemo muku visa....?
Nayi magana da Dr Williams ya ce akaita Indian saboda suna da kwararun likitoci
kwakwalwa.
Ba matsala Daddy yaushe kake so tafiyar...?
Nan da two weeks shima a dalilin inaso naje Lagos, da na dawo sai muyi tafiyar.
Ba damuwa ka barmin komai a hannuna.
Cewar Aliyu yana mai mik'ewa tsaye ni zan wuce Daddy daga nan suleja zan wuce na
kwana biyu banje gidan gona ba, jiya ma Abbas ya kirani yana gayamin abincin kifi
ya k'are.
Allah ya tsare ya kai ka lafiya.
"Amin Daddy ka kula da kanka banda yawan tunani.
Murmushi kawai Daddy ya yi yana jin k'aunar d'an nashi na yawo a sassan jikinshi.
Abinda Daddy baisani ba tun daga lokaci da suka fara magana momma tana la6e, duk
firar da ta wakana atsakaninshi da Aliyu akan kunnenta saida taji motsin fitowar
Aliyu ta ruga da gudu ta 6oye cikin curtain saida yafita sannan tafito daga
ma6oyarta.
***----*****-----****
Barrister A tana dawowa daga raka Aliyu ta tattara plates d'in da suka yi amfani ta
shiga kitchen ta wanke, tana kammalawa ta zari Hijabinta tafito compound adaidai
baranda da tasaba tsayuwa tayi tsaye tana kallon shige da fice na mutanan gidan can
ta hango Sa'eed yana ba flowers ruwa, wani gajere tunani tayi ta nufi wajenshi yana
ganinta ya runsuna ya gaidata ta amsa tana d'an siriri murmushi "Sa'eed idan ka
kammala aikinka ka sameni a garden I have some important matter to discuss with
you.
Duk da ya tsorata da jin farucinta bai bari fuskarshi ta nuna hakan ba, sai cewa
ya yi okay ma'am.
Ta juya ta nufi garden ta zauna tana jiran zuwanshi bata jima da zama ba sai gashi
ya zo, kujerar da ke facing d'inta ta nuna mishi please have a seat!
Ya zauna yana d'ari-dari ka saki jikinki Sa'eed tambayar da zan maka tana da
matukar muhinmmanci.
To ma'am Allah yasa ina da amsar tambayar naki.
"Amin!
Tafad'a had'e da yin shiru na wani d'an lokaci ta nisa had'e da cewa Sa'eed I trust
you completely shine dalilin da yasa na kira ka anan.
Sa'eed!
Yes ma'am!
me kasani akan mahaukaciyar da ke cikin gidanan....?
Wacece ita menene matsayinta anan gidan?
Shiru ya yi na few seconds saboda haka barrister A bata katse mishi shiru nashi ba,
sai ma tayi amfani da shiru nashi tana karantar yana yinshi.
"Asanyayye Sa'eed ya d'ago saida ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce "ma'am
gaskiya ba komai nasani akanta ba zan ba ki labari iya abinda nasani, saboda ban
wuce ten years da fara aiki a gidanan ba wani abu yafaru akan idanuwana wani kuma
nasamu labari daga bakin wasu ma'aikata da suka rigani zuwa gidan
"Kaman yanda nasamu labari Hajiya Maryama ita ce uwargidan Alhaji M Ardo, tsawon
shekaru 28 kenan da ta had'u da wannan lalura, doka ce agidanan ba'a bari ma'aikaci
ko d'aya ya kusancin koda baranda flat d'inta ne, duk yawan mutane da ke gidanan
idan kika cire Hajiya Zaituna ba wanda ke shiga wurinta.
Ni kaina ina mamaki wane zunubi ta aikata da yasa mijinta ya wofitar da ita har
haka.
"Abinda zai ba ki mamaki ma'am tsawon shekaru goma da nayi agidanan banta6a gani
wani ko wata daga danginta ko na mijinta da suna ya zo ganinta ba.
"Barrister A ta sauke zazzafar ajiyar zuciya ta talla6e kumatunta da hannayenta,
ta ce "Sa'eed anaka hasashe me ya kawo wannan rashin kulawa da Maryama take
fuskanta daga bangare biyu mijinta da danginta...?"
Meyasa kuma iya Momma ce kadai ke shiga flat d'inta...?
"Sa'eed ya nisa had'e da juyawa ya kalle hagu da damarshi saida ya tabbatar da ba
wani ido, sannan ya ce ma'am maybe yana da alak'a da labarin da maigadi Daniel ya
ta6a bani.
"Wane irin labari....?
Cewar barrister A cikin k'osawa.
A yanda Daniel ya labarta min ya ce Hajiya Zaituna asiri tayi ma Alhaji M Ardo
shiyasa baya kulawa da Maryama kuma yana zargin ita ce silar haukacewa Maryama,
saboda akwai wata rana da nurse d'in da take kula da Maryama ta zo dubata ya yi
la6e ta window ya ga lokaci da nurse d'in take yi ma Maryama wata allura wacce ba
ko shakka batada nasaba da ciwonta, ya ce lokaci da aka yi mata allurar yana kallon
yadda ta dinga gurnani tamkar ranta zai fita, daga bisani tayi bacci ma'am duk
yadda kike tunani wannan murd'ade al'amari ya wuce da saninki gidanan tamkar gidan
Rina ne komai nashi ya sha bamban da sauran gidaje.
"Shiru barrister A tayi kanta ya dau zafi ba k'aramin rud'ani ta shiga ba ta
sauke ajiyar zuciya yafi a kirga da kyar ta k'irk'iro murmushin dole ta ce "Sa'eed
nasan za ka yi mamaki yadda nake maka wad'annan tambayoyi na yarda da kai Sa'eed
shiyasa na za6e ka don ka warware min wannan al'amari, idan har da gaske momma ce
silar haukar Maryama ni kuma na dau alk'awali sai nayi silar dawowa da ita cikin
hankalinta, kuma sai na daidaita tsakaninta da Daddy wannan alk'awalina ne.
"Nima ina goyon bayanki hundred percent ma'am idan kina buk'atar wani taimako
daga gareni ashirye nake da na taimaka.
"Nagode Sa'eed indan buk'atar hakan ta taso zan nemi ka kuma wannan ya zama
sirri atsakaninmu.
"Karki damu ma'am insha Allah ba wanda zai ji wannan sirri daga gareni.
Cewar Sa'eed yana mai kallon fuskar barrister A.
Shikenan Sa'eed za ka iya tafiya.
Nima nagode ma'am ya karashe magana had'e da mik'ewa tsaye ta bishi da kallo har ya
6acewa ganinta sannan tayi ajiyar zuciya, ko ta wane hali dole ta nemi Baaba laraba
tasamu wasu information daga gareta.
"Mik'ewa tayi ta koma flat d'inta da zumar daga baya zata nemi Baaba laraba.
A bangaren momma kuma tana gani ficewa Aliyu ta koma bedroom d'inta ta kira Jarumi
a waya ta bashi labari abinda ke faruwa, sosai ya harzuk'a har tana jiyo hucinshi
kaman zai kama da wuta.
Ranshi a 6ace matuka ya ce "Abinda nakeso da ke Zaituna ki bi kowace irin hanya
ce ki hanawa barrister A shiga flat d'in Maryama, shigarta wurin zai iya 6ata mana
plans da sauri shi kuma M Ardo ki barni da shi ni nasan ta yanda zan bullo mishi.
Bai tsaya jin ta bakinta ba ya yi hanging up.
***"""***"""****
Around 9:20pm Aliyu ya shigo gida Saidai fuskarshi ahad'e ba fara'a ko k'adan ba
kaman yadda ya fita da safe ba.
Tana mishi sannu da zuwa ko inda take bai kalle ba, balle ya amsa mata ya ra6a ta
gefenta ya haura sama, ta bishi da kallo baki sake tayi shiru tana tunani laifi me
tayi mishi da zai mata haka, iya saninta har suka rabu batasan ta mishi wani laifi
ba ko bayan tafiyarshi ya kirata a waya kuma ko awayan lafiya qalau suka rabu.
"Maybe ko awaje ne aka 6ata mishi rai to ni miye laifina da laifin wani zai
shafe ni..?
Tafad'a a k'asan zuciyarta har tayi niyyar ta share shi sai kuma tafasa, ta haura
steps tanufi bedroom d'inshi ta murd'a handle had'e da sallama ya amsa mata
adak'ile shima ya amsa ne saboda sani darajar sallama da ba zai amsa mata ba, ko
inda take bai son kallo don haka ya juya mata baya yana cire kayan jikinshi da
sauri ta nufi bathroom ta dauko mishi bathrobe ta mik'a mishi mtsss....ya ja mata
tsaki had'e da ra6ata ya shiga bathroom sai kuma ya lek'o da kanshi sounding very
angry ya ce "kada ki kuskura na fito na sameki a d'akina daga haka ya rufe k'ofa,
ya barta tsaye turuss...tana kallon k'ofar bathroom jin saukar ruwa yafara wanka
yasa tafice for the first time da taji tausayin kanta ya lullu6eta da ta tuna da
irin zazzafar soyayyar da take mishi bata ankara ba taji saukar hawaye akan
kumatunta, da saurinta ta sauka k'asa ta shiga kitchen ta jingina bayanta a kitchen
cabinet tasa kuka mai cin rai she is totally confused, me tayi ma Aliyu zai mata
wannan wulak'anci.
Da ada ne zata iya daurewa a yanzu kam ba za iya ba, saboda yariga ya saba mata da
kulawarshi da soyayyarshi, idan ya ce zai juya mata baya ba ko shakka zata iya
susucewa ko kuma tayi 'yar k'aramar hauka.
"Ta kasa jurewa ta share hawayenta tafito ta zauna a dining table, tana jira ya
fito cin abinci tafi 10 minutes a zaune amma ba Aliyu babu labarinshi, tana gani
haka tagano nufinshi ko abincin nata ba zai ci ba.
Zata iya jure komai daga gareshi amma ba zata iya jure ya kwana da yunwa ba ta
tashi da sauri tanufi upstairs.



Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:18 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*



*31*


Ahankali ta murd'a handle k'ofar ya bud'e ta danna kai, ta hango shi zaune akan
resting chair ya lankwashe k'afarshi d'aya akan chair d'in, yayin da d'ayan k'afar
take k'asa ya saka laptop atsakiya yana operating bud'e k'ofar da tayi yasa ya
d'ago afusace ya ce "whats the hell are you doing in my room...?
Banace banaso ganinki ba me ya dawo da ke...?
"Tuni idanuwanta suka ciciko da hawaye she can't take its anymore ji take kaman
ta d'ora hannu bisa kai ta dinga ihu, cikin rawar murya mai dauke da alama so yi
kuka ta ce "Yalla6ai I'm sorry...ni bansan laifi da nayi ma, ba don Allah daure ka
fad'amin laifi da nayi maka na rok'eka gafara.
"Ke dallah rufemin baki I can't wasting my precious time akanki don haka kifita
ki bani wuri.
Kuka ta fashe da shi tana fad'i "Ba zan fita ba koda za ka kasheni Yalla6ai haba
don Allah meyasa za ka dinga treating dina haka..?
Cikin muryar fushi ya ce "Duk wannan kuka da kike yi na munafuci ne you really
disappointed me Amina, me nayi miki da za ki za6a ki wulak'anta min mahaifiya...?
"Kukanta ya tsaya cak...tasaki baki da hancinta tana kallonshi wato tanan momma
ta 6ullo.
Ba shakka kuwa tayi nasara amma zata tabbatar ta rusa nasararta ta.
Da sauri ta durk'usa daf...da shi ta rik'o soft hand d'inshi ta matse anata
tana massage palm dinshi ahankali, hawaye na kai da kawo akan kumatunta ta tausassa
muryarta, ta ce "Kada Allah ya kawo min wannan bak'ar rana arayuwata da zan
wulak'anta koda 'yar aiki mahaifiyarka ce Yalla6ai balle mahaifiyarka.
Idan har ni Amina zan iya wulak'anta mahaifiyarka to ashe kuwa zan iya wulak'anta
tawa mahaifiya.
"Tun daga lokaci da tafara magana jikin Aliyu ya yi sanyi, shiru ya yi yana
tuno wacece momma tun yana cikin zani goyenshi zai iya bada labarin halayyata, yafi
kowa sani makircin mahaifiyarshi musanmman da ya tuna bataso aurenshi da Barrister
A saboda haka zata iya bin kowace irin hanya don ta kawo 6araka atsakaninsu.
"Cikin sanyi murya ya ce "Mekika je yi flat d'in Maryama...?
Ba komai Yalla6ai kawai naga anbar flat d'in da dirty shine nasa housemaid su
tsaftace, ni kaina bansan hakan zai jayomin laifi awurin momma ba.
To amma ni ba haka momma ta gayamin ba.
"Zaro idanuwa tayi tare da fad'i na shiga uku me ta ce da kai Yalla6ai...?
"Murmushi ya yi had'e da d'ago ha6arta yana kallon cikin idanuwanta, ya ce manta
kawai banaso maimata zance, ni kaina banaso ki sake zuwa flat d'in wannan matar
she's very dangerous zata iya cutar min da ke ba zan manta ba lokaci da ina
k'aramin yaro na ta6a shiga flat d'inta kinsan me ya faru...?"
Cike da zumud'in son jin labarin ta girgiza kanta.
A wannan lokaci rufeta kawai ake yi a d'akin kwanata, tsautsayi yasa ni shiga
wurinta tana arba da ni ta k'ank'ameni a jikinta kaman zata mayarda ni cikinta, ga
wani irin gunji kuka da take yi da kyar aka cireni daga jikinta, tun daga lokaci
momma ta hanani shiga wurinta da yake nima na tsorata matuk'a shiyasa har zuwa yau
da nake ba ki labari k'afana bai sake shiga wurinta ba.
"Tagwaye ajiyar zuciya ta sauke ta rangwad'ar da kanta tana kallonshi ta ce
"gaskiya Yalla6ai matar nan tana da ban tausayi ya kamata ku taimaka mata, tsawon
shekara 28 tana rufe ba fa kwana 28 bane shekaru ne masu yawan gaske don kawai
Allah yasa tana da saura kwanaki a duniya da tuni an shafe babinta a duniya.
Ta6e baki ya yi yana fad'i a kwananan Daddy zai fita da ita Indian, insha Allah
zata sami lafiya.
"Yauwa Yalla6aina tashi mu je kaci abinci.
Mik'ewa ya yi yana murmushi suka sauko downstairs hannayensu sark'e da juna, suka
nufi dining area d'aya daga cikin kujerun dining table taja mishi ya zauna ta dauki
plate tayi mishi serving, sannan taja kujerar da ke facing d'inshi ta zauna tare da
serving kanta, ahankali suke cin abincinsu ba ka ji komai sai k'arar spoons suna
kammala cin abinci suka koma falo, tana zaune akan three sitter yayin da ya yi
pillow da cinyoyinta sai fira suke abinsu kaman ba d'azu ya gama fushi da ita ba.
*****"""****"""****
*AFTER ONE WEEK [BAYAN SATI D'AYA*]



Tuni barrister A tafara aiki da Greatest Nigerian lawyer firm.
Team ne na kwararu lawyers the whole nigeria ake ji da su. kasancewarta kwarariya
ta kuma san makamar aikinta yasa cikin k'ank'alin lokaci sunanta ya yi fice.
"A hankali take tafiya tafito daga wuse zone magistrate court hannunta na dama
rik'e da jakkar laptop d'inta, ta nufi parking space ta shiga motarta tayi reverse
tafice daga harabar kotun, direct gida ta wuce tana gama parking tafito har ta nufi
hanyar flat d'inta sai kuma tafasa ta nufi hanyar na Maryama, tasha magiya kafin
Baaba laraba ta bud'e mata k'ofa bayan ta shigo saida tafara lek'awa d'akin
Maryama, taga halin da take ciki sannan ta dawo falo wurin Baaba. falon ya dauki
shiru na wani d'an lokaci kafin Barrister A ta kawo k'arshen shiru ta hanyar cewa
Baaba ki yi hak'uri da ta k'urawa da nake miki wanda kusan kullum idan zan fita
office ko na dawo sai na biyo flat d'inan ina miki magiya ki budemin k'ofa ga alama
yau dai kin gaji da naci nawa, shiyasa kika bud'emin batare da korafi ba.
"Ajiyar zuciya Baaba tayi kafin ta ce ki yi hak'uri 'yar nan banida za6i da ya
wuce na hanaki zuwa sasshe nan, yau dinma na yanke shawara na bude miki ki shigo
saboda akan idanuwana Zaituna ta fita, yanzu ma ina shawartarki da ki yi gaggawa
tambayata abinda kike so sani akan rayuwar Maryama ni kuma ashirye nake da na ba ki
amsa.
"Murmushi barrister A tayi tare da gyara zamanta, ta ce "Baaba menene alak'arki
da maryama...?
Tsawon wane lokaci kika dauka tare da ita...?
Me kuma kika sani dangane da ciwonta....?
"Saida Baaba ta gyara daurin d'an kwalinta kafin ta ce "Alak'ata da maryama ta
samo asali tun shekara 32 da suka wuce abaya, na kasance 'yar aiki a wurin maryama.
Mijina ya mutu ya barni da marayu 'ya'ya har guda 4 mahaifina ya mutu mahaifiyata
kuma makauniya ce sai tayo bara muke samu abinda mu ka ci saboda ba wani dangi da
zai iya tallafawa rayuwarmu, saboda suma suna fama ne da nasu talauci.
"Asalina ni 'yar suru local government ce take cikin jahar kebbi, tsananin
talauci ne ya kawo ni aikatau a garin Abuja wanda anan Allah ya had'ani da Maryama
had'uwata da ita shine silar da rayuwarmu ta canza ni da zuri'ata, idan nace zan
tsaya gayamiki irin dibin alkhairi maryama agareni wannan makirar mata zata dawo ta
tararda ke anan.
"Haka ne Baaba sai ki hanzarta ni kaina banaso ta dawo ta tararda ni.
"Baaba tayi gyaran murya tare da cewa ciwon Maryama ya samu asaline alokaci da take
dauke da juna biyu har na watani 6 sai kawai muka waye gari da ita a haukace,
alokaci Alhaji ya nema mata magani daga bayane ya daina kulawa da ita kaman dai
yadda muka waye gari da ita ahaukace, haka muka waye gari ba wanda ke tada koda
zancenta ne.
"Tsananin tausayin rayuwar Maryama da d'inbin alkhairi da tayi min abaya yasa na
za6e na sadaukar da rayuwata agareta, shiyasa duk tsawon wad'annan shekaru nake
zaune da ita duk da a wasu lokuta Zaituna tana min barazana, ina da yak'ini tabarni
na zauna da maryama ne saboda tasan ba wanda zai iya zama da ita sama da ni.
wannan shine kad'an daga cikin abinda nasani akan rayuwar maryama.
Baaba a labarinki kin ce Maryama tana da juna biyu shin ta haife shi idan kuma ta
haifeshi ina abinda ta haifa...?
"Maryama ta haifi cikin jikinta 'ya mace sai dai bata zo da rai ba kaman yadda
nasamu labari daga bakin Zaituna.
"Kina nufi lokaci da ta haihu ba ki tare da ita ne...?
Kwarai bana tare da ita saboda na tafi suru sakamakon rasuwar da mahaifiyata tayi.
"Numfashin Barrister A ta sauke kafin ta ce "Allah yajik'anta ya gafarta mata.
Amin!
Cewar Baaba.
"Barrister A ta Kalle Baaba ta ce "ki kwantarda hankalinki Baaba insha Allah
maryama tayi kusan samu lafiya, a cikin kwanaki nan Daddy zai fita da ita k'asar
waje.
"Murmushin takaici Baaba tayi had'e da cewa idan har k'asar waje za'a fita da
ita to kuwa har abada ba zata samu lafiya ba. "Subhanalillah....!
Baaba meyasa kika fad'i haka?"
Saboda ciwonta bana asibiti bane balle har a fita da ita k'asar waje.
gyara zamanta barrister A tayi ta tattaro gaba d'aya natsuwarta, ta k'ure Baaba
da idanuwa, kafin ta ce "Ban fahimce ki ba Baaba warware min zare da abawa.
"Ciwon Maryama baida alak'a da asibiti saboda asiri ne aka yi mata, asibiti Kuma
basuda magani warware asiri.
"Wani shegen sweating ya zubuwa barrister a fuskarta, da sauri ta ciro
handkerchief tayi wiping muryata na rawa ta ce "asiri kuma Baaba...?
To waye ya yi mata asiri har ta haukace..?
Tabbas asiri aka yi mata 'yar nan kuma ba kowa bane face Hajiya Zaituna, kuma
lokaci zuwa lokaci tana sabunta asiri tare da saka wata likita marar imani irinta
tana mata allura, duk lokaci da akayi mata allura sai ta dauki kwanaki masu yawan
gaske kafin ta bar ihu had'e da gurnani, in tak'aita miki haukan sabo yake dawowa
dal....
"Sosai barrister A ta tsorata ta kuma sha jinin jikinta tabbas momma ta cika
cikkakiyar marar imani, la'ananniyar mushirika.
"Da kyar Barrister ta bude baki ta ce Baaba nayi miki alk'awali koda zan rasa
numfashina, sai na cuto maryama daga hannun wannan makirar mata wannan alk'awalina
ne.
Daga haka ta dauki jakkar laptop d'inta ta fice Baaba ta bi bayanta da kallo,
sosai yarinyar ta bata mamaki ta yaya zata ceto maryama wannan shine abinda ya
daure mata kai.
Cike da mamakin da ya kasa sakinta ta mik'e ta rufo k'ofa.
"Barrister A ko baranda flat d'inta bata kai ba, motar momma ta shigo gidan da
sauri ta k'arasa isa flat d'in nata, batare da 6ata lokaci ba ta tura k'ofa ta
shiga saboda tunda tafara zuwa aiki Aliyu ya nemo mata 'yan aiki har guda biyu.
"Tana shigowa main parlour Salama ta fito daga kitchen ta kar6i jakkar hannunta,
tana fad'in "sannu da zuwa aunty!
"Yauwa...salama ina Bintu ta shiga ne?
Gani aunty!
Cewar Bintu tana fitowa daga kitchen d'in.
"Ina fatan ba wani matsala ko?
Babu aunty.
Shikenan bari na watsa ruwa kafin na fito d'aya daga cikinku ta ciro Fish a
freezer zan yi girki.
To aunty suka had'a baki salama ta bi bayanta rik'e da jakkarta suna zuwa k'ofar
bedroom d'inta ta kar6i jakkar, saboda bata yarda da 'yan aikin nata su shiga mata
d'akin baccinta ko na Aliyu ba.
ko falon sama bata bari su shiga iyakarsu, falon k'asa sai kuma kitchen.
Agurguje tayi wanka tafito ta zura blouson gown mai supghetti hands, tasaka winter
hat akanta tana sauka downstairs kaitsaye ta wuce kitchen da taimakon 'yan aikinta
ta kammala had'add'un girkinta, ta shirya table lokaci har an fara kiran sallar
magarib.
"Wanka tayo had'e da alwala bayan ta gama sallah bata tashi

1 Comments On Gidan Rina by Jidda Aliyu
avatar
hidaya-ismail

2 months ago

Reply

Allah ya Kara basira

Please Login or Register in order to submit comment