You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya yi nasarar tureshi bisa gado, Momma
wacce ke gefe tsaye ta kurma mashahuri ihu sakamako yanda taga Daddy yana dambe
cirewa Jarumi masks, kururuwa take yi da dukan k'arfinta shiru nata ya tsaya ne
cak....adai-dai lokaci da Daddy ya yi nasarar yaye face masks d'in, fad'uwar
gabanta ya k'aru a dalilin fuskar da take kallo wacce tsawon rayuwarta bata ta6a
koda mafalkinta ba, kafin tayi yunk'uri tambayarshi waye shi ya akayi ya rikid'e ya
zama Jarumi?"
Shin ko Jarumi yana canza launi ne ko kuma yana da sihiri da yake canza kamanu,
idan kuwa haka ne tabbas ya cuceta me zata cewa Daddy ta tabbata koda zata mutu
tasake dawowa duniya ta cewa Daddy abokin fasik'ancinta d'an uwanshi ne Suraj Ardo
ba zai ta6a yarda ba.
Daddy yana cire masa face masks ya koma gefe yana kallonsa da idanuwanshi da sukai
jajir, yayin da numfashinsa ya shiga daukewa yana dawowa ya misalta shekarun abokin
fasik'ancin momma wanda ko d'anta Aliyu ya girmeshi nesa ba kusa ba, saidai ya zo
tsaran Meena ba ma Zee-zee ba.
"Cikin mugun tashin hankali momma ta nufi wajen duplicate d'in Jarumi, kafin ta
aika masa tambayar da ke nuk'urk'usar zuciya da kwakwalwarta kafin tayi wani
yunk'uri 'yan Median suka bankad'o k'ofa suka cika d'akin kowane su yana k'ok'arin
daukar abinda zai watsawa duniya.
"Gani haka yasa Daddy ya k'ara firgita, numfashinsa ya tsaya cak....ya sulele
k'asa ya some.
Momma tafasa ihu tayi kanshi tana jijjiga shi yayin da press sai ya k'ara cika
d'akin suke, kamar turo su ake yi yayin da wasu nan take suka watsa akan social
Median, asirin uwargida M Ardo ya tonu an kamata tana fasik'anci da d'an cikinta,
wasu maganganu ba dad'i ji.
Yanda momma taga flash d'in camera yana shawagi ta ko ina akanta, yasa tayi suman
k'arya.
Ma'aikatan hotel d'in ne suka kira ambulance aka turo Daddy da momma akan gadon
daukar marar lafiya, sai lokaci direban Daddy yaga abinda ke faruwa.
Alokaci da ake k'ok'arin fitowa da Daddy da momma duplicate d'in Jarumi ya sami
hanyar guduwa.
Kaitsaye national hospital akai nufa da su har a can....basu tsira daga Median ba
saboda biye suke da su har lokaci da aka shigarda su d'akin taimakon gaggawa.
"Bayan kowa ya kama gabansa manager hotel d'in ya tsinto kayan momma ya rufe
d'akin.
Jin kad'an da fitarshi Jarumi uncle suraj ya fito daga ma6oyarsa bathroom, ya dinga
kwasa dariya kaman wani motsatsi.
Saida ya yi mai isarsa ya nufi k'ofar fita ya ciro key daga aljihunshi ya bud'e
y k'ofa, ya lek'a ya ga babu kowa a corridor ya fito abinsa zuciyarshi fara
tass....yau burinsa na daukar fansa akan d'an uwansa M Ardo ya cika dama burinsa ya
6ata masa reputation shi da iyalinsa.
"Lokaci da barrister A ta iso k'ofar gidan Jamal tayi horn batare da mai gadi
ya bud'e gate ba, ya fito gefen goshinsa sanye da plaster ya gaidata tare da sanar
da ita mutane gidan duka suna asibiti.
"Sosai tasake shiga firgici cikin tsoro da fargaba ta ce "waye ba lafiya a
gidan?"
Mai gidan da iyalinsa jiya daddare armed robbers suka shigo mana gida kalli
goshina, dukan bindiga ne suka yi wa maigida dukan tsiya suka yi awon gaba da
bak'in da suka zo jiya gidanan.
Barrister A ta dafe saitin zuciyarta da ke hal6awa da k'arfi kana ta shiga furta
"Innalillahi wa'inna illaihim raji'um.....!
Da kyar ta iya tambayarsa wane asibiti Jamal yake, sannan an sanar da Jami'an
tsaro.
Ehh.....an sanar da su ko d'azu sun zo sun sake bincike da yi min tambayoyi shi
kuma maigidan yana Nimzamia hospital.
"Cikin mugun tashin hankali ta tashi motarta, da zumar zuwa asibitin da Jamal
yake kiran Abbata ya shigo wayarta kaman ba zata dauka ba, sai kuma tayi tunani
tana buk'atar wanda zata yi magana da shi.
Tana picking ko gaisuwarta Abba bai tsaya amsawa ba ya ce "Minal wai meke faruwa ne
a family mijinki?"
saura kad'an tasaki steering mota, muryarta tana rawa ta ce "Abba wani ya sanar
da kai wani abu ya faru ne?"
Ba wanda ya sanarda ni gashinan yana yawo a kafaffen yad'a labarai da kafaffen sada
zumunta, abin ba kyau gani.
"Abba ni bansan komai ba wallahi.
Cike da takaici Abba ya ce "mother in law d'inki mijinta M Ardo ya kamata a waster
dream hotel she's having an affair abin takaici da k'aramin yaro, kuma wani kayan
haushi Median ta shigo cikin al'amari
sai yad'awa suke yi.
Kiyi gaggawa ki had'a kayanki ki zo Yola banaso press su yi wani rubutu akanki
matsayinki na daughter in law a gidan zai iya shafar career ki.
Idan babu flight ki nisanta daga gidan ki 6oye kanki zuwa gobe ki biyo jirgin
safe.
Girgiza kai tayi har ta bud'e baki za tayi magana sai ta laura ga mirror mota da
wani black van tun daga fitowarta gidan Jamal yake biye da ita, tunaninta ya bata
watakila hanya d'aya zasu bi kuma gashi ta tare musu hanya saboda sannu-sannu take
driving, gani haka sai ta d'an k'ara gudu sai kawai mai motar ya dinga yi mata wani
mahukacin horn.
Kawai tayi decided ta gangara gefen hanya tayi parking saboda zata fi samun natsuwa
ta fahimtarda Abba ya fahimci ita ma a yanzu tana d'aya daga cikin alhalin duk
abinda ya shafe su, ya shafata ko ta gudu ko ta tsaya ba abinda zai canza hakan.
Tana gama parking sai kawai van d'in ta zo da matsiyacin gudu, tasha gaban motarta
cikin tsananin tsoro ta ce "Abba ga wata black van tasha gaban mo.....
Kafin tak'arasa wasu mutane guda biyu suka fito daga van d'in d'aya daga cikinsu ya
d'aki glass d'in motarta ya tarwatsi da sauri ta duk'e gudu kada glass d'in yayi
mata rauni a fuska, da k'arfi ya fincikota daga cikin mota ya fito da ita waje sai
ihu take, ta wayarta da tafad'i Abba yake jiyo ihunta tana neman taimako, d'ayan ya
duk'a ya dauki wayarta ta ya yi switch off d'inta tare da jefawa aljihun black
lather jacket d'in jikinsa, tana ji tana gani suka jefata cikin motar tare da saka
mata blindfold suka kuma rufe mata baki da salatif, ba ka ji komai sai gurnaninta
doguwar tafiya suka yi saida suka fita garin Abuja k'auyen madallah suka nufa sai
da suka yi tafiya mai nisa kafin su nufi wani poultry house suka yi horn mai gadi
ya bud'e musu gate, bayan su yi parking d'ayan daga cikinsu ya sa6o barrister A a
kafad'arsa suka shiga da ita wani flat.
*****---****-----*****
Jamal da ke kwance akan gadon asibiti saboda yaran, Jarumi sun yi masa shegen duka
har da rauni aka matarsa Zulaiha ta shiga shafinta na Facebook sai kawai taci karo
da sabon labari, cikin mugun tsoro ta mik'awa Jamal wayarta. sosai shima ya firgita
da ganin labarin jikinsa yana rawa ya mik'e daga kan gado ya cire rigar asibiti
Zulaiha ta taimaka masa ya saka jallabiya, hannunta ya riko had'e da daukar handbag
d'inta wacce yake da tabbacin makullin motarta yana ciki, parking space suka nufa
ya mik'a mata handbag d'inta tare da cewa Zulaiha yi sauri ki ja mota mu tafi.
Ina za muje Jamal kai da baka lafiya?"
Nace ki ja mota mu tafi banso silly questions.
Yanda ya k'arashe magana cikin tsawa yasa babu gardama ta ja mota suka fice daga
Nimzamia hospital.
***--*----***-----*---***
*LAGOS NIGERIA*

Tun safe Aliyu yake conference hall yana meeting saboda wani contract na gina
manya-manya tituna da hanyoyin ruwa da kamfaninsu na contractual & building
material company wanda kowane kamfani irin nasu yake sa ran ya samu project d'in,
daga k'arshe kamfanin su Aliyu ne ya yi nasarar samun contract d'in.
"Saboda haka cike da farin ciki Aliyu ya fito daga conference hall direbanshi
ya bud'e masa mota ya shiga, sai lokaci ya yi switch on d'in phones dinshi da zumar
ya gira rabin ransa.
Da safe kafin ya shiga meeting da suka yi waya bai sake waya da ita ba gashi yanzu
har 1:27pm, ya yi dialling digit d'inta saidai wayarta ta a kashe kafin ya yi
yunk'urin kiran d'ayan layinta call d'in k'anwarsa Zee-zee ya shigo wayarsa, ya yi
picking tare da kara wayar a kunnenshi cikin matsanancin kuka Zee-zee ta ce "Don
Allah Ya Sultan duk inda kake duk abinda kake yi ka jinginar ka zo Abj muna cikin
tashin hankali wanda ba za mu iya jure shi mu kadai ba, muna buk'atar taimakonka.
Ya lumshe idanuwanshi tare da fad'uwar gaba mai tsanani ya ce Zainab waye ya
rasu?"
Ya Sultan ba wanda ya rasu amma wallahi gara ace rasuwa ce aka yi da wannan
iftila'i da ya fad'awa zuri'armu. Yaya Daddy ne ya kama momma a hotel tare da
k'aramin yaro wanda a shekaru ba zai wuce age mate din Meena ba they're having an
affair kuma gaba d'aya duniya ta dauka bansan ya aka yi median tasan abinda yake
faruwa a hotel din ba yanzu haka sai yad'awa ake yi musanmman a social median
saboda Abba Yusuf, ya biya wasu daga gidanje rediyo da talevision da su daina
yad'awa shiyasa abin ya yi sauk'i a kaffafen yad'a labarai
ta k'arashe magana tare da rushewa da wani sabon kuka har tana shed'ewa.
Innalillahi wa'inna illaihim raji'um!
Aliyu ya shiga maimaitawa har wani duhu-duhu yake gani da yana da d'abi'ar saurin
kuka da yau ba abinda zai hana shi rushewa da kuka, cikin wani yana yi na k'onar
zuci ya ce "Zainab ki daina kuka saboda ba abinda zai canza faruwar wannan
al'amari, ba'a fata sai ma ya haifar miki da wata matsala muyi hak'uri mu kuma
doshe kunneyenmu mu dauki wannan al'amari a matsayin k'addararmu, ke ce babba ki
rarrashi k'anneki kafin na zo kinji?"
"To Yaya tafad'a tare da share hawaye.
Ina Amina in tana kusa da ke ki bata waya nayi magana da ita.
Yaya batanan tun lokaci da al'amari ya faru na shiga apartment d'inta, masu aikinta
suka ce tafita kuma har yanzu bata dawo ba, duk da muna hospital na bar ma Daniel
sak'o idan tadawo ya sanar da ita muna asibiti.
"Shikenan Zainab ki kula da Daddy kafin na zo ki kuma kira uncle Suraj ki
sanar da shi abinda ya faru, ya sameki a hospital ba za ki iya hidimar asibiti ke
kadai ba.
"Yaya na kira shi yafi a kirga wayarshi switch off.
Aliyu ya dafe goshinsa damuwarsa ta k'ara k'aruwa.
"Ba damuwa ki cigaba da zama wajen Daddy ita kuma Meena da Fateema su zauna wajen
momma kafin in iso.
To....Yaya ta k'arashe magana had'e da hanging up.
Aliyu ya kira number wani friend dinshi da ke aiki a Airport ya ji ko akwai jirgin
da zai tafi Abj da rana, cikin sa'a ya ce akwai 2:30pm zai tashi ya ce ya siya
mishi ticket gashinan zuwa a cikin Airport din ya samu ya yi sallar azhar, yana
gama sallah saida ya sake gwada kiran number barrister still tana rufe hakan ya
k'ara jefa shi a damuwa saboda yasan bata da hearing a court, da kanta ta sanar da
shi lokaci da ya kira ta da safe ta ce yau tana gida ba zata fita ba.
"Oh.....ya rabbi ka taimake ni kasa ita ma ba wani mummunan abu ne ya sameta
ba.
har ya shiga jirgi bai fasa tunani da zance zuci ba yana cikin tunane-tunane
jirginsu ya d'aga.
***----**----***----**
Jarumi uncle Suraj yana hakince akan royal chair wacce ta k'awata masa falonsa, da
ke poultry house d'inshi ya yi crossing legs dinshi jikinshi sanye da farar shadda
hannunshi na dama rik'e da pistol yaranshi suka shigo d'aya sabe da barrister A a
kafad'arsa, ya direta gaban Jarumi tare da furta "mai girma Jarumi mun cika aiki.
Da pistol d'in hannunshi ya yi masa ishara da ya ja baya, ya tsare barrister A da
shegu idanuwansa kafin ya saki wani shegiyar murmushi ta gefen baki.
Ya kalli d'aya daga cikin yaransa ya yi masa alama da ya cire mata salatif d'in
bakinta, nan take ya cika aiki tana jin an bud'e mata bakinta ta dagargaje iya
k'arfinta ta kurma ihu wayyyo........don Allah ataimake ni wasu la'ananun Allah sun
satoni wayyo Allah....ataimakeni.
"Jarumi ya mik'e daga mazauninsa ya nufi wurinta ya shiga zagayata, jikinta ya bata
akwai mutum a kusa da ita ta juya da k'arfi ta shiga ja da baya tana kuma kici-kici
kwance igiyar da suka daure mata hannaye, tuntube tayi da center table tayi baya za
ta fad'a kanshi cikin sauri Jarumi ya rik'o hannunta ya daura bakinsa dai-dai
k'ofar kunnenta ya ce "welcome to my palace sarauniyata.
"Un.....cle....sur..raj!
Tafad'a cikin rawar murya. "Yesss.....sweetheart ashe ina da matsayi a wurinki har
haka bansani ba duk da kin kasance, a cikin wannan hali kika iya sheda muryata ina
godiya rabin raina kai....oska zo maza ka kwance ma sarauniyata hannayenta, za mu
fi jin dad'in gaisawa da sauri wanda ya kira da Oska ya zo ya kwance mata hannaye.
Ita ma ciki sauri ta cire blindfold d'in idanuwanta ta yada ganinta cikin
parlor, tana kallon gumaka yaran Jarumi saboda yadda suka yi tsaye k'ame sun fi
kama da gumaka har ta gangaro kan Jarumi wanda ke tsaye gefe yana zabga murmushin
mugunta.
Wani mugun kallo ta watsa masa shi kuma ya washe mata hak'ora tare da nufar
mazuninsa na tun farko ya zauna ya yi crossing legs dinshi, ya d'aga pistol d'in
hannunshi yana sosa gefen fuskarsa a fusace barrister ta nufi wurinsa ta nuna shi
da yatsa tare da fad'in "kai.....uncle kayi hauka ne me yake damun kanka, ka ne
shin kuwa ka san hukunci kidnapping a kund'in shari'a?"
Uhm..uhm....Ya za'a yi nasani my beautiful daughter in law wannan sai ku manyan
lawyers.
Ta girgiza kanta cike da takaici take kallonshi saboda ta fahimci yana so ya raina
mata hankali, cikin fushi ta ce "to.....uban me zan maka da kasa aka yi kidnapping
d'ina zuwa nan...?"
Ta6e baki ya yi kafin ya ce ki natsu barrister muyi magana cikin mutunci da lumana.
"Harara ta zabga masa tare da fad'in babu zance natsuwa ko mutunci atsakaninmu
uncle, idan har kana so mutunci da lumana ka sa banzaye gumaka yaranka su maidani
inda suka satoni, ni kuma zan rufa maka asiri na dauke wannan al'amari a matsayin
sharrin zuciya.
"Idan kuma nak'i fa my beautiful daughter in law?
Za kayi nadama mafi muni a rayuwarka, ni kwata-kwata kaina ya daure nasa gane
menene manufarka na satoni?"
To....ta ya za'a yi ki sani baya baki bani damar da zan sanar da ke ba.
ya k'arashe magana yana murmushi abinsa.
Ya cigaba da cewa Ki nemi kujera ki zauna ki bud'e kunnenki da kyau ki saurare
manufofin da suka sa na tura gumaka yarana suka yi kidnapping d'inki, saboda haka
ki nemi wuri ki zauna tun kafin ki kaini bango nasa a zaunar da ke dole.
"Rau-rau tayi da idanuwa tare da furta amma kasan hakan bai dace ba, ko?"




Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:28 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO

_SECOND TO THE LAST PAGE_

*39*


*NATIONAL HOSPITAL ABUJA*



Daddy kwance akan gadon asibiti anyi masa fixing d'in drip a hannunshi na dama,
sai sharar bacci yake yi Zee-zee wacce ta gama waya da Aliyu ta mik'e daga kan
kujerar da ta ke zaune, ta nufi wajen gadon Daddy ta zauna kusa da shi.
"Ahankali ta rik'o hannunshi na dama cikin tsananin tausayi take kallon fuskar
mahaifin nata, yayin da bangare zuciyarta guda take ji tsanar mahaifiyarta tana
huda sasssa jikinta.
Ta lumshe idanuwanta hawaye masu zafin gaske suka zubo mata, bata damu da ta goge
su ba ta ce "Daddy sam ba kayi dace da mata tagari ba, ba ka samar mana da uwa
tagari ba.
Daddy a yau ina nadamar kasancewar 'yar da Zaituna ta haifa momma ta cucemu Daddy
ta zubar mana da daraja da k'ima a idon duniya.
Ahalin yanzu ba wanda zai auremu saboda mu kasance 'ya'ya matar da ta aikata Zina
da igiyoyin aureta. "Shikenan yanzu ba mu da damar shiga Jama'a sai an goranta
mana.
ta k'arashe magana had'e da rushewa da kuka mai tsananin gaske ta kifa kanta akan
k'irjin Daddy, tana cigaba da kukanta.
Teema ta Kalle Meena wacce idanuwanta suka yi luhu-luhu saboda tsabar kuka, ta ce "
Ya Meena na rok'e ki da ki daina kukan nan ni fa ya dace nayi ta rusa kuka ba ku
ba, saboda ko ba komai ku ta hanyar ha.....
Da sauri momma ta zabura daga bacci k'arya da take yi, ta dannawa Teema ashar tare
da fad'in "Teema wane sharri ne aljanunki suke shirin k'ula min?
Da ba zasu bar ni naji da wanda aka riga aka doura min ba.
"Meena ta taso da sauri ta nufi wajenta gabanta na fad'uwa ta ce "momma kina
nufi abinda ake yad'awa a kafaffen labarai akanki sharri ne ba gaskiya bane?"
"Kuka momma ta fashe da shi tana girgiza kanta kaman k'adangarwa "sharri ne da
gadar zare da magauta suka shirya min Meena, saboda an ga mahaifinku zai fito
takarar kujerar Governor.
"Meena ta share siriran hawaye da suka zubu mata da bayan hannu, ta ce
"to.....amma momma me ya ki ka je yi a hotel kuma ba kaya a jikinki sai wani d'an
munafukin bathrobe ne sanye ga jikinki...?
Gaba d'aya momma ta didice da ji wannan tambayar ta Meena, nan da nan tayi tunani
k'aryar da zata yanka mata sai kawai ta karkace bakinta ta ce "na fito daga gida da
zumar zan je gidan k'awata Hajiya Dijama, har na kusa isa gidan wata bak'ar mota
tasha gaban motata wasu katti majiya k'arfi nagani sun nufo motata kafin ki ce
kwabo sun fesa min wani abu ga fuska shikenan ban sake sani idan kaina yake ba sai
falkawa nayi nagani akan gadon hotel tsinane yaronan da ban san uwar da ta haife
shi kwance kusa da ni, na yunk'ura da k'arfi na nufi k'ofa ina bud'ewa sai kawai
naci karo da Daddynku a tsaye kafin nayi wani yunk'uri kare kaina sai kawai
wad'annan la'antattu 'yan jarida suka kewaye mu.
Cike da fushi Meena ta ce "tabbas....ko waye ya shirya miki wannan abu momma
sai Allah yasaka mana ya bi mana hakki 6ata mana suna.....
Mtssss......Dogon tsaki Teema ta ja tare da fad'in kaichonki.......momma wai kam
har sai yaushe za ki daina daukawa kanki zunubai?"
Shin ke bakisan hukunci k'arya bane a addinance?"
Kiji tsoron mahalincinki momma ki tuna komai dare dadd'ewa za ki mutu kuma
tilasss.....za ki riske abinda kika shuka yana jiranki a kabarinki.
Momma ki sani duniya k'ararriya ce lahira kuma a can za mu dauwama......iya
aikinka nagari shine zai ceceka, tun tashe ni nayi wayo momma banta6a gani kin yi
aiki nagari ba shin ke ba ki tsoron azabar Allah ne?"
Teema ta k'arashe magana tana mai tsare momma da firgitattu idanuwanta.
"Momma ta rushe da kuka tare da fad'in Teema me nayi ma aljannunki ne me na
tsare musu ne da akoda yaushe suke bi na da mugun alkaba'i?"
"Har Teema ta bud'e baki zai tayi magana Meena ta dakatar da ita ta hanyar rik'o
mata hannu tashi mu tafi d'akin Daddy mu bar momma tana buk'atar hutu.
Batare da Teema ta furta uffan ba ta mik'e yayin da Meena da tana janye da
hannunta, saida suka kai bakin k'ofar fita Teema ta juyo ta kalli momma cikin sa'a
idanuwan momma su na kansu, tasaki mata mushirinki murmushi had'e da karkad'a mata
babban yatsanta ta nota shi k'asa alamar you're finished.
Da sauri momma ta sadda kanta k'asa tana jin wani masifaffen zafi da turiri a
k'asan zuciyarta, ta kuma sha alwashi ko ta wane hali sai ta dauki fansar abinda
Jarumi ya yi mata.
Ba zai yu ba ita kadai sunanta ya 6aci a duniya dole su biyu ne zasu sha tsinuwa
daga bakin mutane duniya ba wai ita kadai ba.
Sannan wannan tozarci da ya yi mata iya saninta ba su shirya shi cikin tsarin
plans d'insu ba, wato nufinshi ita tun anan ya gama amfanin da ita shiyasa ya
fallasata a idon duniya, hawayen takaici suka zubu mata bata damu da ta goge su ba
saboda wuta ce take ci a zuciyarta ba kuma zata daina ruruwa ba har sai ta cimma
burinta na gani bayan Jarumi da Barrister A domin ita ce mutum ta farko da tafara
challenges d'inta.
"Idanuwanta ne suka hasko mata wayar Meena da ta bari a gefen drawer gado,
hannunta har rawa yake yi ta dauki wayar, idan Allah ya taimake ta Meena bata saka
security code a wayarta, abu na farko da tafara yi shine calling d'in number Jarumi
abin takaici wayar tashi a kashe take.
K'awarta Dijama ta lalabo ringing biyu zuwa uku tayi picking muryarta adak'ile ta
ce ''Hello.....
Hello....Dijama!
Wa ke magana...?
Cewar Dijama duk da tagane muryar momma.
Ban so tsohon iskanci Dijama atsawon zaman da nayi da ke ko sautin tusa ta kika ji
yaci ace kin sheda ta balle muryarta.
"Allah ya ba ki hak'uri Zaituna ni sai yanzu na sheda ki, da farko naji muryarki
tayi dususu shiyasa ban gane ki ba.
Zaituna wani mugun abu naga yana kara kaini gidan rediyo da gidan television ke
har ma da kafaffen sada zumunta, shin ke ce da kanki kika aikata wannan mugun aikin
ko kuma ussaina ki ce....?
Mtssss.....momma ta bata amsa da dogon tsaki tare da cewa uwata ce ta aikata ba
ussaina ta ba, look.....Dijama ban kira ki ba don tambaya da bada amsa ba na kiraki
ne don ki taimaka min ki zo ki fitarda ni daga asibiti nan, tun kafin ciwo na
gaskiya ya kamani.
Uhmm.....cewar Dijama har tana ta6e baki kina wane asibiti ne....?
"National Hospital a room 9 ki zo min da kaya nasaka saboda ni da wanda yake
tsirara duk d'aya.
"To.......shikenan gani nan zuwa ki zama ready kada gari taimako ni ma a zuba ni
a Median.
Mtsss.....momma ta ja tsaki tare da hanging up.

*FEW MINUTES AGO*

Dijama ta parker motarta a parking space d'in asibiti, ta fito cikin sauri ta nufi
cikin reception d'in asibiti ta bi corridor da zai sada ta da room d'in da momma
take kwance, ta tura k'ofa ta shiga momma tana ganinta tayi zubur ta mik'e zaune
tun kafin Dijama ta zauna ta ce "Bani kayan na saka banso yara nan su shigo su
ganki.
"A yatsine ta bud'e handbag d'inta ta ciro brown jallabiya ta mik'a mata, tasaka
jikinta har rawa yake yi ta yanne kusan rabin fuskarta da mayafin rigar.
"Har suka fice daga d'akin zuwa parking space ba su ci karo da idon sani ba.
***----***---*****----**
*MADALLAH VILLAGE*

Barrister A ta gallawa Uncle Suraj harara tare da fad'in wallahi da sannu Allah zai
toni asirinka uncle, sai ka girbi abinda ka shukka da hannunka mugu bak'in
azzalumi.
"Ko kad'an fuskar uncle bata nuna ya ji zafin kalamanta ba, sai ma wani shegen
murmushin da ya yi ya d'aga pistol d'in hannunshi ya yi pointing d'inta cikin
kakkausar murya ya ce "Za ki zauna ko sai na har6e ki ne...?
Sai da tasake zuzzuba masa harara kafin ta zauna tayi bala'in daure fuskarta ta ce
"Na zauna sai ka yi gaggawar fad'amin uban me zan maka da ka satoni mugu kawai mai
fuska biyu...?
"Numfasawa ya yi tare da gyara ya zamanshi ya ce "ina fatan kina da labari
halin da in laws dinki suke ciki....?
Dama ka satoni ne don ka sanar da ni halin da suke ciki...?
Cewar barrister tana aika masa da wani mugun kallo.
Cikin kwanciyar hankali ya ce "ah'a......ba ko d'aya.
To kayi gaggawa sanar da ni dalilinka saboda banida lokacin 6atawa tare da kai.
"Barrister kenan ki bi ni ahankali saboda duka mutanen ki suna k'ark'ashin
ikona, ba ki da zabi sai abinda na za6a miki.
"Zaro idanuwanta tayi cikin kad'uwa ta ce "me kake nufi da wannan kurman zance
naka....??
Murmusawa ya yi tare da mik'ewa tsaye ya nufo wajenta, yana mai cigaba da
murmushi da sauri ta tashi tsaye muryarta tana rawa ta ce "kar ka sake ka matso ku
sa da ni.
Dariya ya kwashe da ita tare da fad'in ki biyo ni domin ki sami amsar tambayar
da kika yi min saboda ni ma banida lokaci 6atawa wajen amsa miki tambayoyin ki.
Mtsss.....ta ja tsaki ta bi shi abaya kaman kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Upstairs ya nufa haka ta dinga bin shi har zuwa k'ofar wani d'aki da ke rufe, ya yi
using d'aya daga

1 Comments On Gidan Rina by Jidda Aliyu
avatar
hidaya-ismail

2 months ago

Reply

Allah ya Kara basira

Please Login or Register in order to submit comment