You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dukanta yake
tana ihu, duk yawan matan gida da gayya 'ya'yansu ba wanda yakawo mata dauki.
"Da Rudda ya gaji da dukanta sai kawai ya shak'e mata wuya sai kakarin mutuwa
take, gani zai kasheta abanza yasa tashiga lallu6e abinda za ta kwace kanta da shi,
cikin sa'a ta ci karo da wuk'a daure a k'ugunsa cikin zafin nama ta zaro ta cikin
kube, ba tare da dogon tunani ba ta da6a masa a ciki.
"Yafad'i k'asa yana kugi gani yadda jini ke malala yasa ta buga ihu tafice da
gudu tanufi dakuna kishiyoyinta, tana neman taimakonsu.
"Gani halin da mijinsu yake ciki suka fara ihu yayin da 'ya'yansu suka rufe
Zaituna da dukan mutuwa.
"Allah ya taimaketa ta kwace daga hannunsu ta 6alla da gudu bala'i ta yanki
daji, ba ta ko bi takan bakwani yaronta ba wannan shine sanadin zuwanta Nigeria da
farko Lagos tafara yadda zango ana ta hadu da k'awarta Dijama suna aikin wanke-
wanke wurin wata bayarba mai siyarda abinci.
"Gani yadda Zaituna take da kyau da diri yasa maza suka fara nemanta da lalata,
da farko ta k'i amincewa saida Dijama tai mata huduba sannan ta amince.
"Sannu-sannu idanunsu yana bud'ewa suna k'ara wayewa, da tafiya tai nisa sai
suka koma gidan karuwai suka kama d'aki.
"Cikin lokaci k'alilan Zaituna ta zama k'ursugumar karuwa.
Shekaru sun tafi customers suka fara yi musu wuya, sai suka yi kaura zuwa garin
kaduna anan ta hadu da Alhaji sambo ya nuna yana sonta da aure nan take ta amince.
"Dijama ta nemo wani malami ya zama waliyin Zaituna aka daure musu aure ta
tare gidan mijinta Alhaji sambo, anata gajere tunani tun da tafi uwargida Alhaji
kyau nesa ba kusa ba dole ita ce mowar gida.
Da yake Uwargidan Alhaji Sambo ita ma ba kanwa lasa bace, ta tsare gaba ta
tsare baya shi kanshi Alhaji tsoronta yake saboda bata bar shi a banza ba.
"Zama yak'i dad'i tsakani Zaituna da kishiyarta, ita da kanta tanemi Alhaji
Sambo yasaketa saida suka kai ruwa rana kafin ya amince yasaketa d'in.
Bayan ta kashe aureta da Alhaji Sambo ta ji ba za ta iya komawa, k'azamar
sana'arta ta karuwanci ba ta ja jari da kud'in da take tarawa a asusunta na banki.
Ta shiga safarar tufafi na mata da na zama daga Dubai, gani haka yasa k'awarta
Dijama ta watsarda karuwanci ta aure wani Alhaji Yusuf da ke zaune a garin Abuja,
wannan shine dalilin Zaituna na sake kaura zuwa babban birnin tarayya Abuja tanemi
gida a unguwar Garki ta kama hayya.
"Yayin da mijin Dijama ya bata jari mai kauri ta zuba a kasuwancin Zaituna, cikin
d'an lokaci kad'an suka bud'e manya shaguna har guda biyu.
Lokaci ya mik'a sosai har Dijama ta kai ga haihuwa, wannan ne ya sakawa Zaituna
tunanin sake yin aure kwatsan Allah ya had'ata da Suraj Ardo, da farko ya nuna zai
aure ta ko ya akayi auren ya juye kan d'an uwanshi Muhammad, Alhaji Muhammad Ardo
aminine awurin mijin Dijama.
"Batare da dogon bincike ba ido rufe da zugar Suraj Alhaji Muhammad ya aure
Zaituna, irin aurenan na bariki.
Da yake uwargidansa Maryam mace ce mai hak'uri gaske da kauda kai sai zaman nasu ya
yi dad'i.
"Wata Zaituna biyu a gidan tasami ciki, ashe ita ma Maryam tana da shi 6oyewa ne
kawai ta yi batare da tafad'awa kowa ba.
'Sa6ani Zaituna da gaba d'aya dangin mijinta ba wanda baisan tana da ciki ba,
farin ciki awurin Alhaji Muhammad ba kama hannun yaro.
"Cikin maryam yana da wata hudu ya bayyana saboda tsananin girmansa, sai lokaci
Muhammad yasan tana da ciki ranar kamar zai yi hauka saboda murna da farin ciki.
"Gaba d'aya kulawarsa da tattalinsa suka koma kan Maryam, hakan ba k'aramin
bak'antawa Zaituna ya yi ba.
"Cikin Maryam na da watani shidda ta had'u da lalura ta6in hankali, duk wani
asibiti na masu ta6in hankali, Muhammad yakaita abin yaci turo dama ciwo ke shiga
farat d'aya sauki kuma ya na zuwa ahankali.

"Rayuwar Maryam gwanin ban tausayi ga ciki ga hauka, ko yaushe k'ok'arin take
ta gudu, ba yadda dangin Muhammad ba su yi da shi ba akan yakai Maryam Mental
asylum amma yak'i amincewar da shawararsu.
Aganinshi Maryam bata chanchanci hakan daga gareshi ba, ya tabbata da shine ya
had'u da lalura irinta ta ba za ta gujeshi ba.
Za ta zauna da shi har k'arshen rayuwarta saboda haka ya za6i zai cigaba da zama
da ita har zuwa lokaci da Allah zai bata lafiya.
''Gani halin da Maryam ta tsince kanta aciki yasa Zaituna ta yi laushi, tagano
rayuwar d'an adam ba'a baki komai take ba.
Tadawo tana bata kulawa ta musanmman duk da kowace daga cikinsu cikinta ya
tsufa, wani ikon Allah rana d'aya suka haihu Zaituna ta haihu da safe d'a namiji
kyakyawan gaske.
"Yayin da dare na zagayowa Maryam ta haifi 'ya mace saidai bata zo da rai ba, ranar
Muhammad har kuka sai da ya yi ranar sunna d'a Zaituna ya zagayo aka saka masa
Aliyu.
Daga lokaci haihuwa ta budewa Zaituna ta haifi Zainab, shekarar Zainab biyu
kachal ta haifi Amina sai auta Fatima.
"Fatima tana fama da lalura ta shafar jinni tun tana yarinya take fama da ciwon
wanda har zuwa yanzu ana nema mata magani duk tsawon wannan lokaci Zaituna ba ta
waiwayin K'asarsu Nijar ba.
******------*****-----

Family Alhaji Usman Barkido family ne mai girman gaske, wanda girmansa yasa duk
wanda yake cikin garin Adamawa yasan da wannan family kasancewarsu jinin sarauta.
"Alhaji Usman Barkido yana da 'ya'ya da tarin jikoki, saidai duk yawan
'ya'yanshi bai yarda sun yi aure ba daga daga tsatso shi ba, don haka tun daga kan
'ya'yanshi mata har zuwa maza aure had'i yake musu.
"Wannan al'ada ta shi hatta jikokinshi ba su tsira ba, namiji ko mace da kai
isa aure zai nemo maka partner kuma, kuma cikin amincewa Allah sai ka ga sun zauna
lafiya.
"Barrister Amina Abdallah Barkido tana d'aya daga cikin jikokinsh 'ya ce ga
d'ansa Abdallah Barkido.
Abdallah Barkido mutum ne mai tsautsura ra'ayi mafad'aci gaske mutum ne mai zafin
rai, matarshi ta aure d'aya Hindu shi da Hindu anyi musu aure had'i batare da su na
son juna ba.
"Abdallah baya son Hindu ko kad'an duk da kasancewarta kyakyawa aji farko,
kuma 'yar uwarshi ta jini hakan bai sa ya so ta ba.
"Hindu mace ce mai hak'uri gaske duk wulak'anci da Abdallah yake mata shanyewa
take, bata kai k'ararsa ba Allah yabata cikinta na fari ta haifi Amina wacce suna
mahaifiyar Abdallah ta ci shiyasa suke kiranta da Minal.
"Zuwan Minal duniya ya chanza Abdallah har yafara nunawa Hindu k'auna.
Abdallah yana matuk'ar son Minal bai had'ata da komai ba, lokaci da tana yarinya
idan tana rashin lafiya har kuka yake yi.
Muddin kanaso ka ga 6acin ransa kata6a Minal.
"Shekarar Minal biyu a duniya Hindu tasake haihuwa 'yan biyu duka maza,
Khalil da Khalid sai Ahmad sai kuma auta Rahma wacce bata wuce 9yrs ba.
"Minal lawyer ce mai zaman kanta sau biyu Barkido yana za6a mata miji tana
rejected, tare da goyon bayan mahaifinta Abdallah wanda yasha al'washi ba zai ta6a
bari ayiwa 'yarshi auren dole ba.
"Wata rana Alhaji Muhammad Ardo yakawo ziyara a yola, ya je gaida Barkido
kasancewar Barkido abokin margayi Aliyu Ardo ne.
Anan yake tambayarshi Aliyu yaranshi nawa, sai ya ce har yanzu bai yi aure ba,
sosai Barkido yarufe Muhammad da fad'a daga k'arshe ya ce ya turoshi ya zo ya ga
Amina su dai-daita.
*wannan kenan*
[7/26, 11:38 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAN KANA SO SAI KA TUNTUBEN WANNAN NUMBER*
0813943903

*GIDAN RINA*

*Haske writers association*


Na Jeeddah Aliyu



*4*



*CIGABAN LABARI*
Barrister Amina tana tafiya tana tunanin maganganun da Barrister Zarah, ta gaya
mata wanda suka zama sanadin rage mata damuwa.
"Agajiye ta iso gida a parlour ta tararda mahaifiyarta Hindu wacce suke kira da
Ummi suna zaune da Rahma, da ke kallon cartoons.

Da sallama dauke da bakinta tashigo.

Sannu da zuwa Ya Minal.
Rahma tafad'a tana mai mik'ewa tsaye ta kar6i handbag din Minal
Yauwa Rahma kallo ake yi?"
Eh! Cewar Rahma tana mai nufar dak'in Minal takai mata bag d'in.
"Washhh! Barrister A tafad'a had'e da zama akan hannun kujerar da Ummi ta ke
zaune.
"Sannu da gida ummi?"

''Yauwa Minal sannu da zuwa ya aiki da fatar anyi nasara?"

Alhamdulillah!
cikin yarda ubangiji mu yi winning case d'in.
masha Allah!
Ummi tafad'a cike da farin ciki nasara 'yarta ta.
Mik'ewa ta yi had'e da furta Ummi bara na watsa ruwa ko na d'an ji k'arfin
jikina.
Toh! Afito lafiya
ummi tafad'a da murmushi akan fuskarta.
Da isar ta d'akinta ta cire kayan jikinta ta daura towel, ta fad'a bathroom ta
sakewa kanta shower bata dauki dogon lokaci ba tafito, ta zauna gaban mirror ta
shiga shafe lallausar fatar jikinta da lotion mai k'amshi gaske.
"Ta gyara fuskarta ta hanyar simple makeup, ta bud'e closet tafito da gown na
atamfar Holland tasaka had'e da fesa Arabia perfume ta jikinta dauki k'amshi.
"Rahma ta turo k'ofa dauke da sallama.
Ya akayi ne auta?"
Ummi ta ce in gaya miki in kin kammalla abinda ki ke tana son ganinki.
"Ta kalli k'anwarta ta anatse ta ce ki ce da ita gani nan zuwa.
Toh!
Rahma tafad'a tana ficewa daga d'akin.
Barrister A ta cigaba da daura d'an kwalinta tana kammalawa tafice rik'e da
wayoyinta.
Tana isa parlour ta tararda ummi tana waya, ta samu wuri ta zauna, tana karantar
yanayinta koda wata damuwa sai taga sa6anin haka, sai ma fara'a takeyi.
"Ummi ta k'are wayar ta juyo ta kalli Barrister A fara'a tak'ara yalwanta akan
fuskarta, ta ce dama zan yi miki magana akan mutane da za su zo neman aurenki.
"Ummi ta yi shiru na wasu 'yan dak'ik'u kafin ta ce shine naga yadace mu yi
magana.
Toh.....ummi ina saurarenki.
Cewar Barrister A tana mai gyara zamanta.
Yayin da Ummi ta cigaba da cewa Minal lokaci yana tafiya a kullum k'ara girma ki
ke, shekaru ki suna tafiya ak'allan yanzu kina da shekara 25 a duniya zuwa wannan
lokaci ya kamata ace kina d'akin mijinki.
"Amma a dalilin taurin kanki da na mahaifiki gashi har yanzu kina gida, Minal
ki yi wa kanki fad'a kada ki biyewa mahaifinki da ke cewa ba zai miki auren dole
ba.
"Daga ni har shi aure zumunta akanyi mana gashinan muna zaune har aka haifeku.
Don haka ina gargad'inki a wannan karon ki amince da za6in da Barkido ya yi miki na
tabbata ba zai miki za6en tumu dare ba.
"Sassanyar ajiyar zuciya Barrister A ta yi jikinta ya yi sanyi magangganun Ummi
suka ratsa ta tabbas zance Ummi gaskiya ne shekarunta sun tafi, ita kanta tana yi
so aure saidai sam batason aurenan na Zumunta saidai a wannan karon tana jin za ta
amince da za6in Barkido, kasancewar za6i nasa ba daga family su bane.
''Minal kin yi shiru ba ki ce komai ba.
Ummi ta katse mata zance zuci.
murmushi ta yi ta rik'o hannun Ummi cikin nata ta ce Ummi please ki daina sanya
damuwa akaina shi aure lokaci ne da shi, auren zumunci ne banaso Ummi amma tun da
wannan ba daga Barkido family ya ke ba na amince zan aure shi.
"Alhamdullih!
Ummi tafad'a very excited ta rungumo Barrister A zuwa jikinta daga bisani ta ce in
Abbanki ya dawo ya tambaye ki, kin amince da Za6in Barkido ki fad'a masa kin amince
za ki aure shi kinji My dear?''
Dariya Barrister A ta yi had'e da cewa kai Ummi.
Shafa fuskarta Ummi ta yi tana tayata dariyar, ta ce kinsan halin botsarare
mahaifinki sai da haka akanki da kowa zai iya 6atawa banaso a dalilinki yasamu
sa6ani da mahaifinshi, musanmman da yanzu Barkido ya tsofa abu kad'an zai iya mayar
da shi babba.
"Karki damu Ummi wallahi na amince da ko ma waye d'ari bisa d'ari.
Allah....ya yi miki albarka yasa biyayyar da ki ke mana ta zame miki alkhairi.
"Amin!
Ummi.
Daga haka su ka cigaba da fira duk dai akan zance auren nata ne.
***----***----*****
Alhaji Muhammad Ardo ya na isowa garin Yola direct Ardo Family house ya wuce, anan
ya had'u da 'yan uwanshi suka dunguma zuwa gidan Barkido nemawa d'ansu Aliyu auren
Barrister Amina wanda nan take Barkido ya tsayar da lokaci nan da watani biyu masu
zuwa.
"Sosai Alhaji Muhammad Ardo ya ji dad'i yadda Barkido ya karrama Su da kuma
lokaci da ya sanya na bikin.
Duk zance da ake alokaci Alhaji Abdallah kallonsu kawai yake, saboda ya sha
al'awashi muddin Barrister A ta ce bataso Aliyu yasan hanyoyin da dama da zai da bi
ya hana auren.

*8:37pm*

Alhaji Abdallah yana zaune a parlounshi, ya aika Ummi ta kira shi mishi Barrister
A.
Da sallama ta shigo dauke da bakinta.
"Alhaji Abdallah ya amsa mata yana murmushi.
Barka da hutawa Abba.
"Yauwa Minal.
Ta nemi bisa carpet kusa da k'afafunshi ta zauna
Cikin sanyi murya Alhaji Abdallah ya fara magana, Minal na kira ki ne domin na ba
ki damar da za mu tattauna akan zance aurenki.
Ya d'an numfasa daga bisani ya cigaba da cewa har ga Allah Minal naso ki fito da
wanda ki ke so za6in ranki, duk nasan zan sha matuk'ar wahala kafin Barkido ya
amince.
"Amma hakan ya gagara daga gareki duk lokaci da na zo miki da zance, sai ki ce
ba ki samu wanda ki ke so ba.
Ba komai yasa nake miki gudun aure zumunta sai irin zaman da mu ka yi da
mahaifiyarki, mun sha bak'ar wahala da hak'uri ni da mahaifiyarki ba kad'an kafin
mu fara k'aunar junanmu.
"Banaso ki fuskanci irin wannan rayuwar agidan aurenki.
shiyasa koda yaushe addu'a nake Allah ya kawo miki miji wanda ba daga zuri'ar
Barkido ba.
Sai gashi Allah ya kar6i addu'a ta, Barkido da kanshi yai miki za6i ba daga
zuri'arshi ba.
"Tun daga lokaci da ya gayamin mijin da ya za6a miki farin ciki ya lullu6e
ni, saboda nasan wanene Aliyu ba shi wata matsala ko kad'an yana da halaye masu
kyau wanda kowane uba nagari yakewa 'yarshi fatan samunshi amatsayin mijin aure.
"Yayin da Alhaji Abdallah ya cigaba da cewa, duk da Barkido ya gama zartarda
hukunci har ya kuma sanya lokaci bikinki nan da watani biyu masu zuwa kamar dai
yadda ya fad'a tun kafin zuwansu.
"Saboda haka banaso ki tashi hankalinki, nayi magana da mahaifin yaron, ya ce
next week zai zo ku gane ki kwatarda hankalinki idan bai miki ba, nasan ta hanyar
da zan biyowa Barkido ya hak'ura batare da rayuka sun 6aci ba

"Murmushi ta yi cike da jin kunya ta, sadda kai k'asa tana wasa da babban yatsar
k'afarta.
Jin Shiru ta ya yi yawa yasa Abba ya d'ago ya kalleta,
shima ya yi murmushi ba ki ce komai ba Minal?"
Idan kuma ba ki da abin cewa za ki iya tafiya.
cikin sanyi murya ta ce Abba ya yi min duk ban ganshi ba, dama ni auren zumunci ne
banaso.
"Good girl.....Allah shi yi miki albarka
Amin...Abba.
Tafad'a had'e da mik'ewa tsaye sai da safe Abba zan je na kwanta bacci nake ji.
Allah ya kai mu
cewar Abba.
"Kitchen tafara shiga ta had'a coffee ta wuce da shi zuwa d'akinta.
Gefen gado ta zauna ta yi crossing legs d'inta, ahankali take sipping coffee
d'inta.
Yayin da wani gefen na zuciyarta ke nuna ma ta, tayi kuskure na saurin amincewa da
mutume da ko sunanshi sai yanzu ta ji.
Tana gama shanye coffee ta wuce bathroom ta wanke bakinta, ta dauko laptop d'inta
ta duba wani civil case da za ta yi presenting gobe.
Doguwar hamma ta yi had'e da shafa fuskarta hakan yasa ta rufe laptop d'in ta yi
addu'a kwanciya bacci, ta kashe wuta ta kwanta, ta rufe rabin jikinta da blanket.
****----****----***
*WASHE GARI*
*Abuja 11:08am*

Aliyu yafito daga apartment d'inshi jikinshi sanye da white suit, kamar yadda ya
saba shigarshi ta farare kaya, wannan yana d'aya daga cikin d'abi'unshi gaba d'aya
tufafinshi farara ne.
Baya ta6a saka wani colour kaya idan ba white ba Hannunshi rik'e da brief case
cikin yana yin tafiyarshi ta k'asaita ya fito compound, da gudu direbanshi isah ya
zo ya kar6i brief case d'in.
shi kuma ya nufi apartment d'in momma zaune ya tararda ita har k'asa ya durku'sa ya
gaidata, wannan yana d'aya daga cikin kyawawan d'abi'un Aliyu yana girmama
iyayyenshi sosai.
"Momma ta amsa tana fara'a saida ta dube bakin k'ofa ta ga ba kowa, ta gyara
zamanta Sultan tun jiya mahaifinka ya dawo daga Yola.
"Uhm! Nasani momma naga lokaci da ya dawo ina tsaye a balcony.
Momma ta d'an yatsina fuska sannan ta ce, ya ce an tsayarda lokaci bikinka watani
biyu masu zuwa.
tak'arasa magana cikin murmushin yak'e.
"Ta6e baki ya yi had'e da mik'ewa tsaye momma ni zan wuce office.
Afakace ta galla masa harara, ina magana ka mik'e tsaye kuma ba ka ce da ni komai
ba.
"Me Zan ce momma?
Auu.....ba ka da abin cewa?"
D'an bazawari murmushi ya yi momma sauri nake in nadawo za mu yi magana anatse,
saidai gaskiya idan har Daddy ya nace akan lalle sai nayi aure to ya barni na nemo
wacce nakeso da kaina.
in fact ban shirya yin aure a wannan shekara ba, balle nan da wata biyu ban so
Daddy ya yi sauri yanke lokaci biki ba
ahali ni da nake aure ban amince ba.
Rausayar da kai momma ta yi ta ce yanzu kan aikin ga ma ya rika ya gama, ni kaina
ban zace zai yanke iri wannan hukunci ba.
Amma ba komai ni ma nasan ta hanyar da zan bulluwa al'amarin.
"Kamar ya momma?"
Ya fad'a da alamar mamaki shinfid'e akan fuskarshi.
wayacewa ta yi ta hanya cewa je ki kawai kada na 6ata maka lokaci kamar yadda ka ce
in ka dawo za mu k'arasa
magana.
"Batare da yasake magana ba ya juya ya nufi sitting room d'in Daddy.

Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:42 PM] Jiddah Aliyu: *GIDAN RINA*

Na Jeeddah Aliyu

Free page

*Haske writers association*

*5*

Yana had'a ido da Daddy yafara murmushi yana sosa k'eya alamar rashin gaskiya,
dariya Daddy ya yi ya ce lale marhaban da bak'on Scotland barka da zuwa Gadanga
k'usar yak'i.
"Dariya ce ta subucewa Aliyu ya rufe bakinshi da tafin hannu, Kallonshi Daddy
yake yana girgiza kai "Good morning Daddy Aliyu yafada yana shafar gemunshi,
Morning Sultan idonka kenan sometimes da sultan Daddy yake kiranshi kasancewar
sunan mahaifinshi da yake da, murmushi ya yi yace Daddy am sorry.
"Ba komai sultan...Daddy ya fad'a but zo ka zauna mu yi magana ta fahimta.
zaunawa ya yi kusa Daddy kafin Daddy ya yi magana saida ya rik'o hannunshi d'aya,
Sultan dangane da zance aurenka ni da iyayyen yarinyar mu yi fixing din Date nan da
watani biyu masu zuwa, saboda muna so ku same isasshe lokaci da za ku fahimce
junanku.
"This time around idan ka sake ka ruguza aurenan Sultan I won't forgive you....don
haka make sure ka shirya this weekend ka je Yola ku gana da yarinyar.
Ka ji ko?"
Daddy ya tambayeshi, yana kallon yadda ya 6ata fuska tamkar zai yi kuka ga wani
uban gume da yake ta faman shawagi akan face d'inshi, da kyar ya hadiye wasu yawu
sakamako bakinshi da ya bushe ya ce Daddy please.....idan har ya zama dole sai nayi
aure ina neman alfarma ka ba ni dama na nemo wacce nakeso, Saboda ba lalle bane
kanemo min kalar mace da nakeso ba...
Shut up....my friend!
Daddy ya daka mishi tsawa wallahi sultan ka shiga taitayinka da ni, muddin ka ga
ba'a yi aurenan ba k'addara hakan amatsayin bana numfashi tashi maza ka 6ace min da
gani, shassha banza da wofi.
K'asa da murya Aliyu ya yi ya ce Daddy am so sorry karka yi fushi da ni
please.....duk abinda ka ke so zan yi saboda ba zan iya jure fushinka ba.
"Dauke fuska Daddy ya yi da barin kallonshi, hakan yakara rud'a Aliyu ya durkusa
agabanshi, Daddy nace na amince muddin zan sanyaka farin ciki koda mayya ce zan
aureta.
Sai lokaci Daddy ya saki fuskarshi ya ce that's my boy.....saidai ba mayya ba ce
jikar Barkido ce sunanta Barrister Amina 'yar manyan mutane ce shiyasa banaso asame
matsala, daga bangare na.
''Zaro idanu Aliyu ya yi hade da Squeezing face.....Daddy kana nufi yarinya
lawyer ce?"
Kwarai kuwa independent lawyer ce[lauya mai zaman kanta]
Whatever! Daddy ni ko lawyer government ce I don't care kawai dai kasan I hate
liar's kuma mostly lawyers mak'aryata ne, hararrashi Daddy ya yi had'e da furta
banaso shirme Gadanga don kawai tana lawyer shi zai sa ta zama mak'aryyarci?"
"Turo baki ya yi a sangarce ya ce ni dai Daddy I don't love her.
mak'e kafad'a Daddy ya yi irin I don't care dinan, kafin ya ce kai dai karka yi
gaggawa ka jira har ka ganta ido da ido.
Mik'ewa Aliyu ya yi Sai na dawo Daddy ina da meeting around 12 o'clock.
asauka lafiya....Daddy ya fada da murmurshi akan fuskarshi.
Ficewa ya yi yana fitowa isah direba ya jawo mota ya bud'e mishi back sit ya kame a
owners corner, isah ya ja motar cikin kwarewa da tuk'i ya fice daga gidan.
****--*****-----****
Sai around 2:20pm Aliyu ya fito daga conference hall, kaitsaye office d'inshi ya
wuce ya ajiye laptop dinshi da wasu files akan desk ya wuce ya bathroom ya dauro
alwala, yana fitowa P.A shi Kamal na shigowa rik'e da white coat d'in Aliyu yanufi
wata hanger da ke ajiye a cikin office d'in ya sarkafe rigar.
"Aliyu yana fitowa daga bathroom da
sauri kamal ya shinfid'a mishi praymat
Batare da Aliyu ya kalle shi ba ya ce Kamal ka yi min order food a chicken republic
restaurant, yunwa nake ji cikina sai k'ugin yake.
"An gama Boss!
Har kamal ya juya ya sake cewa ba ka ji ba kamal.
Chak...kamal ya tsaya.
"please help me call Jamal tell him I wants to seen him urgently.
Yes boss!
Cewar kamal yana mai ficewa daga office din.
Aliyu yana gama sallah ya koma kan resting chair ya kwanta, ba abinda yake tunawa
sai babban k'alubali da yake tunk'aro shi, duk duniya ba abinda ya tsana irin aure
duk yadda ka ke da shi idan ka yi invited nashi daurin aure ba ya zuwa, ko a family
su ake aure sai ya k'irk'iro tafiya don kada ya je sosai abin yake ciwa Daddy tuwo
a kwarya.
"Mtsss....ya ja d'an siriri tsaki ya dafe goshinshi duk lokaci da ya tuna Daddy
ya ce dole sai ya je Yola wurin yarinyanan, sai ya ji fad'uwar gaba wanda ya rasa
na menene babban tashin hankalinshi bai san yadda zai ga yarinyar ba, ko yaya take
bashi da mafita dole ya aureta don ya farantawa mahaifinshi rai.
"Turo k'ofar da aka yi ya katse mishi tunani da sallama kamal yak'araso, kusa da
Aliyu ya ajiye ledar hannunshi.
"Boss na kira maigida Jamal ya ce zai zo nan ba da jimawa ba.
Okay.....ba damuwa za ka iya tafiya.
Ficewa kamal ya yi yayin da Aliyu ya dauki takeaway guda yafara ci kasancewar yana
jin yunwa yasa yaci fiyye da rabin abincin.
"Abinci yake ci amma zuciyarshi cike da zance zuci, turo k'ofar da aka yi ya
katse mishi zance zuci da ya ke yi, sallamar Jamal ta bugi dodon kunnenshi, ya dubi
k'ofar yana mai amsawa Jamal ya shigo ya zauna kusa da Aliyu yana mai mik'a masa
hannnu suka yi musabaha.
"Ya garin JB kwana biyu ka 6oye?"
Aliyu ya fad'a yana kallon fuskar Jamal.
Alhmdllh....kwana biyu nan am too busy tun lokaci da Abba ya yi rashin lafiya
abubuwa su ka min yawa.
"Sauke numfashi Aliyu ya yi kafin ya ce gaskiya iyayyenmu suna bukatar hutu
musanmman yanzu da k'arfi kullum k'ara ragewa yake, gara kai JB kana da siblings
maza su na taimaka maka a business d'inku sa6ani ni da bani da kowa
"Ta6e baki Jamal ya yi kafin ya ce kadai ayi sha'ani kawai amma lamarin 'yan
uwan nawa sai addu'a daga mai shaye-shaye sai manemi mata, shiyasa kullum jini Abba
k'ara hawa yake.
Girgiza kai Aliyu ya yi ya ce Allah ya kyauta ya shige mana gaba.
Amin summa Amin!
cewar Jamal yana mai daukar robar ruwan Faro ya bude, ya kafa baki ya sha daga
bisani ya ajiye.
Ya dube Aliyu ya ce king ya zance da mu ka yi a waya yanan ko ka watse shi?"
Yak'arasa magana yana dariya.
Uhm! Bari kawai JB wannan karo zance ba zai watsu ba.
Yanzu haka neman da nake maka zance nakeso, mu tattauna

1 Comments On Gidan Rina by Jidda Aliyu
avatar
hidaya-ismail

2 months ago

Reply

Allah ya Kara basira

Please Login or Register in order to submit comment