You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bana son na yi miki dole, ko kiyi mini alfarma, dan kina jin kunyata ko ta ?anwata, ni wannan abubuwan duk ban san kan su ba, ban taSa gwadawa ba ma.
Amma na ji ina son na aureki, zaki iya auren talaka kamata?"

'Na ji ina son na aureki, baya sona kenan, ko tausayina kawai yake ji' ta tambayi kanta.

"Ba kya son talaka ko?'

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"Talk"

"A'a yaya umar" tayi maganar muryarta na rawa.

Umar ya Wan tsura mata ido ya ce "Ba takura miki nake ba, tambayarki kawai na yi, idan ba zaki aurena ba, ba wani abu, ban san meyasa nake baki tsoro ba, rumaisa ma da muke faWa, ba ta ji ne, but am good person ko?"

Ta ce "Yes you are".

"Zan tafi, duk hukuncin da ki ka yanke ki gaya mini, ba wani abu"

Ledar hannunsa ya ajiye mata, ya tashi yayi tafiyarsa, ta daWe a wurin tana tunani, daga baya ta yanke, ko baya son ta, ko iya tausayin nata yake ji, zata iya aurensa, tun da shi ba?in tabonta, bai hana shi cewa zai aureta ba.

Ammi bata matsa mata a kan sanin lallai waye ba, sai dai rumaisa ta din ga cewa ?amshin turaren mai sunan baba take ji.
Turaruka ne masu kyau, guda uku da dabino lubiya manyan kwali guda uku.

Har aka yi sallar magariba, ta kira shi ta sanar ta yi masa ya yaje gida, jikinta a sanyaye yake, ya ce mata yaje lafiya, daga nan ba wata magana suka yi sallama.

Suna zaune a falon, suna kallo, suna taSa hira, laila ta kora rumaisa ta je tayi karatu, dan jarrabawa suke yi a makaranta, ammi ta fara tambayar iman, wai waye ba?onta ya kuma suka yi da shi?.

Sai dai kan iman ta kai ga yin magana, Mahmud ya shigo tare da yin Sallama.

Masu gadi suka shigo da ruwa carton biyar, lemo carton biyar, ya ?arasa gaban iman, ya bata envelope ya ce "Gashi nan in ji umar, ya ce a baki, ba yawa ki rage wani abun, na bikin saukar ki"

Kallon Mahmud take, dan ba ta fuskanci wani umar Win yake nufi ba.

Ganin kallon da take yi masa ya sanya ya ce "Wanda ya zo wurinki Wazu" sai ta sunkuyar da kai tana jjya envelope Win.

Laila ta ce "Iman, sai Soye-Soye ki ke yi, yakamata ayi mana ?arin haske a kan wannan da yayi wuf da zuciyar taki" tayi maganar cikin wasa.

Mahmud ya kalli Ammi ya ce "Allah ya baki yawan rai, ko zan iya magana da ke?"

Jiki na rawa ammi ta ce "Ni, eh mana Mahmud mai ze hana".

"Daddy ba Allah ya baki yawan rai ba, Ammi zan iya magana da ke dan Allah?" Rumaisa ta faWa lokacin da ta fito, yake neman izinin magana da ammi.

Bai ce komai ba ya Wan murmusa, ruma ta ce "Waye ya kawo mana lemo?"

Ammi ta sake mayar da hankalinta kan Mahmud ta ce "ko ciki zamu shiga ne?"

Ya ce "To"

Sashinta ya bita, tana gaba yana baya, zuciyarsa na yi masa wani irin Waci, yaushe rabonsa da taka wurin nan, har ya manta, yau gashi a dalilin rumaisa, yana ta kokowar farkawa da nannauyan baccin da yake tsawon shekaru.

A Sangaren ammi ma haka ne, dan fes take tuna lokacin da aka ?wace mata shi, ta ?arfin tsiya.

A bedroom Win ta suka tsaya, ta ?arasa ta saka hannunta, tana sake kaWe masa makeken gadonta, da yake a Wame da bedsheet fes da shi ta ce "Bismillah zo ka zauna"

Ya nemi wuri ya zauna a ?asan carfet, ya ce "ki zauna, ni nan ya isa"

"To nima bari na zauna a nan Win, ai ba wani abu" ta zauna a ?asa kusa da shi.

Ya kalli fuskar Ammi, da ta rasa in da zata saka kanta dan daWi, farincikin ta ya kasa Suya, sai ?o?arin mayar da hawaye take yi.

Ya kawar da kai kamar bai ga komai ba ya ce "Dama na ji abubuwan da suke ta faruwa ne, da abun da wambai ya ce game da iman. Dama abokina ne yake son iman, kuma shi talaka ne, bai tara dukiya ba, amma Wan mutunci ne, kuma na yadda da kirkinsa, sanin kowaye iman Win zata gaya miki, ya ce a tambayeku, zaku bashi ita, amma nan da watanni uku yayi masa kaWan ya shirya, ku bashi kamar wata biyar, idan sun dai-daita, zai turo".

Ammi ta ce "In dai bashi da wata matsala, kuma ya san wacece ita, ba zai wula?anta mini ita ba, ba damuwa, zan iya Waukar Wawainiyar komai ni nayi masa".

"Abu ne mawuyaci ya yarda da haka, amma na san zai yi iya ?o?arin sa a kan kula da ita."

"Dama ni haka nake fata, Alhamdilillah, Allah ya yi maka albarka kaima, da nuna kulawa a kan abun da ya dameni. Na ji ka kammala karatun ka, Allah yayi muku albarka. Ya albarkaci abun da ka karanta, Allah ya sa ka koma bakin aikinka lafiya, Allah ya haWa mana kanku gaba Waya ?a?an galadima".

"Amin ammi na gode" ta ji ya tashi ya nufi hanyar fita, daf da zai fita ya jiyo sheshshe?ar ammi, amma ina bai juya ba, ya fita shima yana zubar hawaye.

Ganin ya fito yana kuka, har rige-rigen shiga wurin ammi suka yi.

Ruma ta ce "Ammi, me yayi miki me ya ce miki? ?ata miki rai yayi?"

Laila ma tambayoyin ta shiga jero mata, amma ta ri?e hannun ruma ta ce "Bayan tsawon shekaru, da fidda ran Wa na zai sake kallona a matsayin uwa, ya kirani da ammi rumaisa, Wa na ya kusa dawowa gareni, duk ?o?arin ki ne rumaisa na gode"

Rumaisa kasa ri?e hawayenta tayi, ta fara sharewa ammi nata ta ce "Haba ammi, idan kina kuka mu idan mun yi wa zai rarrashemu. You are a good mother, you deserve to smile. Idan ana maganar jajurtattun iyaye a duniya, da mama da ke, bani da na biyun ku ammi"

Ammi ta rungume rumaisa tana ta kwarara mata addu'a, da ita da iyayenta.

"Tabbas duk wanda zai ce sirikata ba ta ji, to bashi da gaskiya ne, ina alfahari da ke ?a ta".

Laila ta ce "To, ammi abun har da wariyar launin fata? Kan dai ki samu sirikar taki, mu ki ka fara sani".

Nusaiba ta ce "Muna zaune ta yi mana wayo, ta ?wace mana ammi ba".

Bisa kasada umar yayi proposing Win Iman, ba dan yana da abun da zai aurenta ba, sai dan son da yake mata da tausayinta da yake ji.

Laila tana zaune suna hira da ammi, laila ta ce mata tana son zuwa gombe, idan zasu tafi suje tare da rumaisa da Iman, ammi ta amince da hakan.
Ta Wan numfasa ta ce "Laila ko iman ta gaya miki wani abu game da ba?onta ne? Haryanzu ba ta ce mini komai ba, waye daga ina yake da sauransu, Mahmud ya ce mini abokinsa ne, ta yarda ta amince tana son sa"

Laila ta ce "Ahh ammi, ba yayan rumaisa ba ne, ni dai alamu sun nuna tana son shi, lokacin da ta kwanta a asibiti na ganshi, yana nan mai kama da ruma sosai"

Ammi ta Wan waro ido ta ce "Mai sunan baba wai?"

"Eh ina ga shi ne"

Ammi ta ce "Ikon Allah, abu kamar wasa, dama tsorata tan da yake yi na soyayya ne. Na yaba da tarbiyar gidansu rumaisa, mahaifiyarsu jajirtacciyar uwa ce, amma ina jinjina lamarin nan, anya iman za ta iya da shi, kamar boss haka yake, ba fara'a baya son mutane, mamansa na yawan faWar zafin ransa".

Laila ta ce "Ammi ki yi musu addu'a kawai, ke ba ga Wanki nan ya samu dai-dai da shi ba, duk nasa zafin kan kalli yadda rumaisa ke sola shi yadda take so, tun da ya iya cewa yana son ta, ai a wuce wurin "

Ammi ta ce "Haka ne, Allah ya sa kar a samu matsala daga baya, bari na ji ta bakin Iman Win, sai mu ga abun da yakamata ayi".

Laila ta ce "To shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ya sa daga haka a samu ?arshen wannan matsalar.

Ammi ta amsa da Amin.

Takawa na tsaye a valcony, hannunsa Waya ri?e da kofin tea, Waya kuma da takardar zanen da rumaisa ta saka masa a kayansa, sai dai kurman zane tayi, ba tare da bayanin komai ba, kuma da alama sa?o ne mai muhimmanci take son isar masa a zanen.

Kusan kullum sai ya kalli zanen nan, kuma kamar yadda ta ce kar ya tambaye ta, yasan da zarar ya matsa, ba lallai ta yi bayani.

Babban abun da ya fi Waukar hankalinsa, shi ne SMOKE, da ta rubuta da manyan ba?a?e, sai daji da ta zana da dogayen bishiyu, sai aisha dur?ushe a gefen bishiya ta ri?e ciki.

"Mimi what's the meaning of this?" Yayu maganar yana shafa zanen, hawayen sa na Wiga a kan zanen.

***
Litattafai ne a gaban Iman, tana karatu, Ammi tayi sallama, Iman ta amsa.

"Sarki littafi, ina fatan kin gama karSo komai, da za ayi amfani da shi na bikin saukar?".

"Eh ammina, everything is ready"

Ammi ta mi?a mata leda ta ce "Sidi ya kawo, ya ce a baki in ji umar"

Iman ta karSa ta duba, keyholders ne, da jotter yayi mata na sauka.

"Auta haryanzu baki ce mini komai a kan yadda ake ciki ba, kin amince da mai sunan baban, kina ganin babu matsala?"

Iman ta Wago da sauri, ba ta zaci ammi ta san waye ba.

"Ko da baki gaya mini, na gane waye, amma iman kina ganin babu matsala? Zaki iya zama da shi?"

Iman ta jinjina kai ta ce "Ammi yana da kirki"

Ammi ta yi murmushi ta ce "So hana ganin laifi, amma ya san halin da ake ciki, ya amince da hakan?"

"Eh ya sani".

"To Alhamdilillah, Allah ya tabbatar mana da alkhairi" ammi ta tashi ta fita.

Iman ta bi Ammi da kallo har ta fice.

Mai sunan baba yana zaune a gaban mama, yana cin abinci, duk suna tare da su Aliyu, Abubakar yana kwance a gefen mama yana danna waya.

"Babana" mama ta kira sunansa.

A hankali ya Waga kai ya kalli mama.

"Ashe neman aure ka ke ban sani ba?"

Gaba Waya suka Waga kai suna kallon mai sunan baba.

"Mun yi waya da hajiya, ta ce sun baka dama ka fito, sai dai ban san zancen ba sai Wazu da ta kirani a waya".

Ayshercool.


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR? DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

=?I? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1.? Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2.?? Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3.? Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4.? Supplements na karawa fata kyau da sheki? glowing skin*

*5.?? Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6.?? Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7.?? Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8.? Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9.? Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10.? Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11.? Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12.? Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13.? Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14.? Supplement na whitening/glowing skin*

*15.? Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*


Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please =?O?


*TALLA! TALLA!! TALLA!!!
*?AN?ANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ?UDURAR ALLAH*

Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab a kusantar wata mace ba? Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta  Tabbas Jaheed jininka don gwajin k wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba a yi gwajin ba.

Shiru na tsawon lokaci d akin ya d auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab a rik ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.? Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K UDIRAR ALLAH& .

(*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaWantar da ku, da WaWan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA Win sa ya kasance daidai da na yaron da bai taSa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ?uruciya har girmansa, bai taSa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ?udurar Allah. Masu bu?ata kai tsaye za su iya tuntuSar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)



Shiru yayi ya cigaba da kai lomar abinci bakinsa, suka tsare shi da ido suna jiran yayi magana.

Yaya Abubakar ya tashi zaune ya ce "Malam magana fa ake yi maka"

Mirsisi ya?i magana, ya cigaba da cin abinci, Aliyu dama ya daWe da gano yayan na su, ya afka kogin soyayya, magana ce kawai bai yi ba.

Sai dai ya gama cin abincin, sannan ya ce "Mama, ba Soye miki nayi ba, komai ya zo mini a bazata ne. Hasalima tausayinta da na ji ne, ya sanya na ji zan iya aurenta, amma kin san ni dai ban taSa kula ?ar kowa ba".

Aliyu ya ce "Wai wa ce ne?". Harar da yayi masa ya sanya shi yin shiru.

Mama ta ce "To, wai an ce turakin kano yana son ganinka, zai gana da kai, a kan maganar, kuma suna bu?atar ka fito ne"

Mai sunan baba ya Wan yi shiru sannan ya ce "Mama bani da abun aurenta yanzu, kin san komai a kanta, dan ina wurin lokacin da rumaisa ke baki labarinta.
An fasa aurenta da wani, kuma a yadda take gaya mini, shi ne karo na huWu, duk saboda waccan matsala, dalilin haka kuma, an ce wa mari?iyarta idan ba ta aurar da ita nan da watanni uku ba, ta mayar da ita in da ta tsinto ta. Magana ake ta shekaru goma sha tara da ri?onta, wurin wa za ta kai ta. Ban san ya aka yi na ji ina son na aureta ba".

Aliyu shi tausayi ma ya bashi, har yanzu bai gama yadda soyayya ce tayi masa kamun kazar kuku ba.

Mama ta ce "Na yadda da maganarka babana, kuma na goyi bayanka, dan shi Wa na kowa ne, yadda hajiya binta ke ri?e da rumaisa kamar ba sirikarta ba, kaWai ya isa na goyi bayanka. Kuma Allah ya sani tun kan haka ina ?aunar yarinyar nan sosai. Amma abun da nake tunani, kaga an saka bikin Abubakar, muna ta fama, gashi ka tsayar da gininka ana nasa, yanzu meye abun yi watanni uku sun yi kaWan".

Abubakar ya ce "Ba dan halinsa ba, kuma tun da ban isa ya gaya mini abun da yake ciki ba, saboda halin da yarinyar take ciki, da kuma duba da muma muna da ?anwa, muna fatan albarkacin wannan jihadi da zai yi, Allah ya kula mana da ita, a duk in da take, da kuma la'akari da yadda mutum ya faWa soyayya, da har ta kai shi ga yanke hukunci, ba tare da shawara ba, ni yayansa wato hassan Win sa, zan yi magana da su baffa, a Waga bikina a fara nasa, tun da abun gasa ne, nayi sai yayi. Sai su tare a nawa gidan, ni na ?arasa nasa".

Mai sunan baba ya galla masa harara.

Abdallah ya ce "Auren mai sunan baba, zama bai kama mu ba, dole mu yin?ura abu namu maganin a kwaSe mu".

Yasir ya yi murmushi ya ce "Ni zan sai akwatin kayan lefe, guda shida in sha Allah"

Huzaifa ya ce "Ji banza, an gaya maka akwatin lefen ma, jagwal za a saya, kamar kayan jagwal Win da kake na wayoyi da computer, da hacking in ji rumaisa".

"Bana son rashin mutunci, kai ka san abun da nake da shi ne? Kwanan nan daga china zan fara yin order wayoyi, kai ka sani ai, jari nake tarawa, amma ni


zan sai akwatunan lefe, kai uwar me ka ajiye da zaman basir Win Winki, banda shegiyar ?arya da saSa al?awari".

Mama ta ce "To zakaru, ai kun ci kun ?oshi, dole ku yi mini faWa".

Umar ya ce "Duk na ji ta bakin ku, na kuma gode sosai, amma babu wanda zai rabu da wani abun sa saboda ni, kai habu ba za a Waga bikinka ba in sha Allah, ina fatan nima wannan Win ba zai gagara ba, zan ?ara ?o?ari".

Abubakar ya ce "Wai dan an haife mu lokaci Waya ni sa'anka ne? Bana magana biyu kai ka sani, gidan nan ya zama naka, dama kaine ?arfin ginin, ni ba gaggawa nake yi ba, ita ma haka in sha Allah ita da iyayenta za su fahimce ni".

Mai sunan baba zai sake magana mama ta ce "Ka riga ka Waukki aiki babana, idan ba hakan aka yi ba, ni ban ga mafita ba, garbatina Wan albarka, Ubangiji Allah ya ?ara haWa mini kanku, ya kau da abun ?i a tsakanin ku, a duk lokacin da abu ya tasowa Wayanku, na ga kun haWa kanku, ba ?aramin daWi nake ji ba".

Usman da tun da ake maganar bai ce komai ba sai yanzu ya ce "Mama duk jajircewarki ce ta kawo haka, Allah dai ya ?ara miki lafiya da nisan kwana".

Suka amsa da Amin, Abdallah ya ce "Mai sunan baba, idan abu ya taso maka, bamu yi maka ba, wa zamu yi wa? Sadaukarwar da kake yi domin farincikinmu ai tana da yawa, komai ka samu mu, kai ne wa, kuma kai ne uba, kowa ya kwaso matsalar sa, mai sunan baba, dan haka muna bayanka a kowane ?adami Allah ya iya maka yayi ri?o da hannunka".

Karar da ?an uwan nasa suka nuna masa, ba ?aramin daWi tayi masa ba, har sai da hakan ya sanya shi murmushi, kuma ya kasa Soye farin cikinsa.

***
Ko da labari ya iske dangin mahaifinsu Umar, sun yi murna, tare da tsokanar mai sunan baba, dama zai iya yin budurwa yayi soyayya.
Wan mahaifinsu ya ce zasu yi ?o?ari, amma abubakar ma ba za a Waga aurensa ba.
Sai dai yayan mahaifinsu ya jinjina lamarin auro ?ar gidan sarauta yana talaka.

Tare da shi da umar, da yaya Abubakar da ?anin mahaifinsu, sai mijin iya baffa musa da ya zo daga, suka je gidan turaki bisa jagorancin Mahmud kamar yadda ya bu?ata.

Sai dai sun ga karramawa, da mutuntawa da basu taSa tunani ba, turaki ya ?ara jaddadawa mai sunan baba matsayin iman, mai sunan baba ya ce ya amince.
Turaki ya tambayi ?an uwan mahaifinsa, a kan idan sun amince su ma, suka ce ai shi ne zai zauna da ita, kuma tun da ya ce ya ji ya gani, suma sun amince ai Wa na kowa ne, a tarbiyyar da umar yake da ita, sun san ba zai kawo abun da zai cutar da shi ba.
Baffa Musa wa ga mahaifinsu ya ce "Sai dai mu ma wani hanzari ba gudu ba, yaron nan maraya ne, bashi da ?arfi saka biki nan da watanni uku yayi kusa da yawa, ga Wan uwansa nasa bikin muke hari, muna fatan a ?ara mana ya zama watanni shida, gaba Waya ya mayar da hankali ne a kan auren Wan uwansa bamu zaci nasan zai zo haka ba".

Turaki ya ce "Babu laifi, kar ku damu. Ubangiji Allah ya yi mana jagora, kuma a hakan nan ma kawai, na yaba da tagwayen sosai, ba dan ance shi ma Wan uwan aure zai yi ba, ai da sai na bashi ?a ta, ai duk wani wanda ya fito daga tsatson ?a ta rumaisa, duk abun da yake so, in dai ina da shi zan yi masa.
Allah ya sanya musu albarka, ya nuna mana lokacin lafiya".

Baffa musa ya ce "Amin, ranka ya daWe tun da har an samu daidaito, ina ga ba sai mun ja lokaci ba kawo kuWin aure, ga kuWi mun taho da su"

Gaba Waya suka kalleshi, su dai sun san ba su yi haka da shi ba.

Ya karkace ya ciro kuWi, dubu Wari da hamsin, ya ajiye a gaban turaki.

Turaki ya ce "Masha Allah, Allah ya sanya albarka, to ba dan ba a shirya ba, ai da sai a Waura, mu bashi gidan zama, a wuce wurin ko malam umar?".

Mai sunan baba ya risuna ya ce "Ranka ya daWe ni yakamata na yi ?o?arin samar da mahalli".

Yayi murmushi ya ce "Babu laifi, Allah ya nuna mana"


Ko da suka taho hanya, Mahmud har gida ya kai su mai sunan baba, a gida suka sanar da mama ai an bayar da kuWin auren ma, mama ta ce daga zuwa tambaya an biya kuWin aure? Ta ce to sai a nemo kuWin malam musa a bashi abun sa, amma ya hau mama da faWa, a kan dan yayi wa ?a?an Wan uwansa abu, dan me za ta ce a biya shi.

Turaki ma wayar ammi ya kira, ya sanar mata su mai sunan baba sun bayar da kuWin auren iman, dubu Wari da hamsin, sun sanya watanni shida dai-dai.

Ammi ta yi mamaki, dan ita bata ta;a zaton abun a haka ba, ta ce to ba a basu komai na tukici ba, sun kawo kuWin aure.

Turaki ya ce su aika musu daga baya,

Please Login or Register in order to submit comment