You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayar idan.... Ba ta ?arasa maganar ba ta ri?e ?ugunta ta ce "Washhh"

A Wan rikice ruma ta ce "Sannu Anty Aisha, kwanta a kan cinyata ki mi?e ?afar to".

"A'a kar na hanaki bacci baby ruma, yi kwanciyarki".

Ruma ta ce "A'a ai ba zan iya komawa ba kwanta".

A hankali Aisha ta ja jikinta ta kwanta a kan ?afafuwan rumaisa, Ruma ta ce "Bari na yi miki tsifa, kin san ni nake yi wa mama tsifa har kitso na iya" Aisha ba ta hana ruma ba, ta dinga jagwalgwala mata gashi, sai dai duk da mawuyacin halin da take ciki, ruma dariya take bata, dan sam ruma ba ta da rufi.

"Anty Aisha ina son in ga kina dariya, daWi nake ji, tun da ki ka zo wurin nan na rage damuwa duk da ina missing Win gidanmu, in sha Allah idan Allah ya ?addara muka bar nan, ko a wane gari ki ke zan zo gidanki".

Tayi murmushi ta ce "Nima haka ruma, tun da na zo wurin nan, kawai nake jin ki a raina, nake kuma sarawa jarumtarki, sai dai babu lallai na bar wurin nan a raye haka jikina yake bani"

"?aga mini cinyata tun da ba zaki daina wannan maganar ba" ruma ta faWa rai a Sace.

"Haba ruma, ni Win ki tsaya ki ji mai zan gaya miki, idan ma na mutu lokacina ne yayi kuma zan yi shahada". Ruma ta ture kan Aisha daga kan cinyarta ta tashi ta ce "Sai ki je ki yi ta shahadar ai, ba zan sake kulaki ba"

Kowa yayi bacci, sai masu gadi da su ruma ne idonsu biyu, da wani ne yake wannan surutun cikin daren nan, da yanzu ya sha tijara ?ila a haWa masa da duka ma, amma kasancewar rumaisa ce take magana ba wanda ya kulata, dan yanzu da an taSata zata hau kwarmato, idan kuma ba a isa ayu mata wani abun ba kamar tayi musu asiri.

?ayan ya kalli ruma da ta tashi zata canza wuri daga kusa da Aisha, ya ce "yau kun yi faWa da uwar taki ne?"

"To meya dameka ne, ka cigaba da gadinka mana, sa ido sana'ar banza".

"Ni ki ke cewa sa ido sana'ar banza, dan kin ga ana ?yaleki?"

"Ai wallahi ko me zan yi, baku isa ku yi mini wani abu ba, addu'a nake banka muku ta ko ina, in gaya maka, ka san wani abu kuwa?"

"Bana son ji, wuce ki nemi wurin kwanciya".

Ruma ta ?arasa wurin da suke zaune sun kunna wuta, wasu suna shaye-shaye, ta zaune a gefansu ta ce ta yi ?asa da muryarta ta ce"Ka san meya haWani da anty aisha muka yi faWa kuwa? Cewa take yi wai zata mutu ta tafi ta barni, shine ta bani haushi"

"To ina ruwana? Sauran da suka mutu meyasa baki damu ba?"

Ta Wan yi shiru sannan ta ce "Tana sona ne wallahi, nima kuma ina sonta, dan Allah ku saketa, ko ku kai ta asibiti ba ta da lafiya"

Ya ce "Wallahi na yadda addu'a ki ke yi mana, ko kuma daga can gidanku ake yi, ban da haka ba a taSa kawo Wan iskan mutum mara tsoro irin ki ba".

"A'a nifa ba 'yar iska bace, so nake ku kasheni, amma kun ?i ya zan yi, kalli yadda na koma kamar 'yar jari bola, wataran a gidamu mama sai ta yi mini wanka sau biyu a rana, amma yau ban san adadin kwanakin da na shafe ban yi wanka ba, tun ina warin har na daina".

"To ai ko ni ma sai na yi miki wankan, akwai kogi a gaba"

Aisha tana daga can nesa, amma ko ?ifta ido ba ta yi a kan ruma, dan kar wani abu ya faru, ruma tayi zaman dirshen sai zuba take, duk da ba ta san mai ruman take cewa ba, amma hirarta kawai take yi da su hankali kwance.

Ba ta sake bi ta kan Anty Aisha ba, har aka yi sallar asuba, ruma ta yi salla tayi kwanciyarta bacci.

***

"Mummy, wallahi na san in da maganin nan yake, a Wakin iman yake, kuma na sake tabattar da takawa yana nan da wannan ciwon mai kama da na aljanu, mai kuma kama da na hauka"

Mummy ta kalli Fauziyya a tsanake ta ce "Fauziyya, bana son shirme da ?arya fa".

"Haba mummy, kamar wata ?aramar yarinya, kin ga yadda ya sha?e iman a Wakinta kuwa, ya Wage mata riga baki ga ba"

Mummy ta yi murmushi ta ce "Kin tabattar kin ga in da maganin yake? Idan kin tabattar ina son gaya wa uwani ta kawo mini shi, dan da maganin wannan malamin yace zai mini aikin da zai kawo ?arshen hankali a jikin adam, kin ga ba shi ba sarauta kenan"

"Wallahi mummy na gani, sai dai akwai mukulli a drower mudubinta ne"

"Fine, kafin nan, ina son ayi raising issue na cewar yayi yin?urin yi wa iman fyaWe, wani sashin kuma ace an kama shi shi da ita, hakan zai ?ara Sata sunansa, da yi wa zuriyar binta ba?in jini a cikin masarautar nan"

Fauziyya ta Wan yi jimm sannan ta ce "Anya Mummy, decision Win nan naki bai yi tsauri ba kuwa?"

"Ban gane tsauri ba, duk wannan fafutukar ba dan ku nake yi ba, ki shiga hankalinki fa"

"Am sorry, ba zan sake ba duk hukuncin da ki ka yanke dai-dai ne"

Mummy ta yi ?wafa ta tashi ta fice.

***
Habiba ?awar ruma kullum sai ta je layinsu ruma, ta tambaya ko an ga rumaisa, dan tsoron zuwa gidan su ruma take saboda yayyen ruma, tsoro suke bata, ita a da can ma idan ba dole ba ba zuwa take yi ba, balle yanzu da suke cikin damuwa da tashin hankali.
A ?ofar gidan su ruma take tsaye tana le?e.

"Me ki ke dubawa ne?" Ta ji muryar usman.

Da sauri ta waiwaya tana kallonsa.

"Me ki ke yi a nan?" Ya maimaita.

Habiba ta ce"So nake na ji ko zan ji yo muryar ruma ta dawo"

Cikin sanyin jiki usman ya ce "Ruma ba ta dawo ba Habiba, na san kina yi mata addu'a, to ki cigaba kar ki daina dan Allah".

Hawaye ya cika idon habiba za ta yi kuka, usman ya ce "Kar ki yi kuka kin ji, maza tafi gida kar a neme ki kin ji"

Haka nan ta juya ta tafi gida.

***
Ruma kuwa sai da rana ta take, sannan ta tashi daga baccin da take yi,ta tashi zaune ta Waga kai suka yi ido huWu da Aisha, amma rumaisa ta kawar da kanta gefe ta?i kula Aisha.
Sai dai a kallo Wayan da ruma tayi mata, ta hango damuwa a fuskar aishan.

Gaishe da mutanen wurin tayi, ta koma gefe ta tattara duwatsu ta hau 'yar carafke.

"Sannu rumaisa, ke rayuwarki baki da wata damuwa, yau ba kya jin yunwar ne?" Cewar wanda suke kira da sha tara.

"To kun bani abincin ne?"

"Ga abinci nan barde ya kawo miki kina bacci"

"Nifa na gaji da buredin nan ba yau ba gobe... Au ashe waina ce yau" tayi maganar tana murmushi, yayin da mutane suke kallon tsabar samun wuri da ruma ta yi.

Ta koma gefe da nufin ta fara ci, suka yi ido huWu da Aisha ta zubo mata ido,haka nan ruma ta ji jikinta yayi sanyi, dan haka ta tashi ta je gaban Aisha ta zauna ta ce "zo mu ci"

Aisha ta?i magana, kawai ta zubawa ruma ido.

"Mu ci mana" ruma ta sake maganar tana kallon idon aisha, amma ga mamakinta taga hawaye a kwance a cikin idonta.

"To Meyasa kuma zaki yi kuka?" Ruma tayi maganar kamar ita ma ta yi kukan.

"Meyasa ki ke fushi da ni ruma? Na ji daWin kwanciyar da na yi a kan ?afafuwanki, har na ji ina son yin bacci, amma ki ka tashi ki ka barni" tayi maganar cikin damuwa.

Ita ma ruma cikin damuwar ta ce "Ba ke ce ki ke cewa zaki mutu ba, na gaya miki kuma bana so".

"To na daina, amma ki matso kusa da ni in kwanta a kan ?afarki, ko zan Wan ji daWin kwanciyar, kwana na yi ina ciwon baya da ciwon mara, ?afafuwana kamar ana sara mini su"

"To mu ci wainar, sai ki kwanta"

Ta girgiza wa ruma kai, ta karkata da ?yar ta kwanta a kan cinyar ruma, sannan ta kalli ruma ta ce "Har na ji daWi, mu daina faWa dan Allah ?awata, gurin nan yana bani tsoro, da sakani cikin damuwa ke kaWaice ?warin gwiwata, idan na ganki nake jin daWi, kuma ko ina cikin damuwar barkwancinki na sakani nishaWi".

Murmushi ruma ta yi ta ce "Ni wallahi idan ki ka ce baby ruman nan, sai na ji kamar na fara rarrafe da shan hannu, kamar wata jaririyar zanin goyo, wai da mama baby take ce mini da har a yanzu sai na din ga fitsari a wando, zan zuba taSar wallahi".

Cikin dariya Aisha ta ce "Ki gauraya da mai sunan baba ba" tare suka cigaba da dariya, kamar babu abin da yake damunsu duk su biyun. Can aisha ta ce "Wai ina Wan kunnenki, na ga kunnenki babu yari".

Ruma ta haWiye lomar wainar da ke bakinta ta ce "Ai ni ina ga sai salla salla nake saka Wan kunne, nifa kamar su Huzaifa haka nake yawona, dan da za a barni, zan iya yawo da gajeren wando a cikin unguwa, in je ayi mini askina"

Aisha ta girgiza kai ta ce "Ruma idan na biye miki, sai ki saka na fara na?uda yanzu" ta saka hannu ta ciro Wan kunnayen kunnenta, ta sakawa ruma.

Ruma ta yamutsa fuska ta ce "Ni fa bana son Wan kunne, idan suka dameni tsaf zan ciresu na watsar"

"Ruma kin san kuWin abin da na saka miki a kunnenki kuwa? Gold ne tafiyayye daga dubai, dan Allah kar ki yar".

"To ni me zan da shi?" Ruma ta tambaye ta tana shafa kunnenta.

"Bar miki na yi, ga wannan ma, ta mi?awa ruma Wan kwalin kayanta, ta ?ulle wani abu a ciki ta ce "Sar?ar Wan kunnen ce, da zobuna da kuma sar?ar ?afa".

"To su kuma me za ayi da su?" Aisha ta Wan yi shiru, daga bisani kuma ta ce? "Ajiya ce na baki, zan karSa, idan kuma ban karSa ba na bar miki"

"To ni yanzu wannan ajiyar taki, a kaina zan Waurata ko kuma ?uguna zan Waurawa, dan tsaf zan manta ya kama gabansa na kama nawa"

"Amana ce fa, ki kula da su sosai" ruma ta takurawa aisha sai da ta Wan ci wainar nan, amma kallo Waya zaka yi wa aisha ka san bata da lafiya, amma sai ?arfin hali take tana biyewa rumaisa.

A 'yan kwanakin nan kusan kullum, akwai kalar mutanen da suke zuwa wurin nan, wasu idan sun zo su Wauki manyan jakunkuna.
Yau ma wasu ne suka zo a babura kusan huWu, amma su waWan nan sanye da ba?a?en coat, suma fuskokinsu a rufe, ruma ba ta damu da su ba, ta mayar da hankalinta kan aisha, tana fatan kar ?arar baburan nan nasu ya tasheta.

Bayan mutanen sun tattauna da waWanda suka sace ruma, kai tsaye aka nuno musu in da su ruma ke zaune, suka tunkari su rumaisa.

Tsayawa ruma ta yi taga ikon Allah,wurin wa aka zo, wurinta ko kuma wurin Aisha....

Ayshercool


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR? DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

=?I? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1.? Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2.?? Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3.? Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4.? Supplements na karawa fata kyau da sheki? glowing skin*

*5.?? Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6.?? Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7.?? Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8.? Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9.? Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10.? Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11.? Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12.? Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13.? Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14.? Supplement na whitening/glowing skin*

*15.? Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*






Cigaba da tunkaro su ruma suka yi, ruma kuma ta tattara hankalinta ta ga me za ayi.
Suna zuwa suka kewaye su rumaisa, Waya daga cikin su ya sanya hannu zai Waga Aisha, amma ruma ta saka hannu ta kare, ta ce 'Wai me zaka yi mata? Matar aure ce fa yaya zaka taSa ta?".

"Ke, ni ki ke yi wa wannan maganar?" Ya kuma kai hannu zai janyo Aisha, amma ruma ta ri?e hannunsa. Jin hayaniya ya sanya Aisha motsawa a hankali ta buWe idonta, ta kalli mutanen da ke tsaye a kanta, ta yin?ura da ?yar ta tashi zaune ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un Lafiya?"

A karo na uku, mutumin ya kai hannu ya dan?i Aisha, ya fara janta, ruma kuma ta mi?e zata bi bayansa, Waya daga cikinsu ya dan?o ruma, yayi jifa da ita a gefe ya saita ta da bindiga.

Da sauri sha tara ya ce "A'a kar ka kuskura ka yi mata wani abu, akwai yarjejeniya tsakaninmu da ?ungiyar su barde, mun yi yarjejeniya a kanta, muddin wani abu ya sameta zamu ya?i juna, babu ruwanku da ita, zan ri?e muku ita, dan ba zata yarda ta bari ku yi aikinku ba".

Yayi maganar tare da ?arasawa ya dan?o ruma, aikuwa ta hau bori, tana kiran Anty Aisha, Aisha kuwa ta kasa magana, sai mi?awa ruma hannu take yi, mutumin nan kuwa babu imani sai janta yake yi.

Cikin gigita ruma ta ce "Dalla ka cikani, suwaye su me zasu yi mata?"

Sha tara ya ce "Ke a shegen shishshigin ki, zaki jawa kanki abun da ba shikenan ba" kan ruma ta kuma yin wata maganar, sha tara ya watsa wa ruma wani abu a fuska, ta silalale a wurin nan, tana gani sama-sama.

***
"Uwani ki buWe kunnenki da kyau ki ji ni, bana son a wannan karon a samu wata matsala, ki yi mini aikin nan yadda yakamata"

Baba uwani ta risuna ta ce "In Allah ya yarda ba zan bari a samu wani kuskure ba uwar Wakina".

"Yauwwa, aikin da na saka ki ki ka kasa, Fauziyya ta yi mini rabin aikin, dan haka ?arashe ne zaki yi yanzu, Fauziyya ta tabattar mini da ta gano in da maganin nan yake, yana Wakin iman, a cikin drowern mudubinta, dan haka duk yadda zaki yi, ki samo mukulli ki buWe wardrobe Win nan, ki Wauko mini, akwai wani aiki da za ayi mini, wanda lallai sai da shi".

Baba uwani ta Wan yi shiru tana nazarin yadda za ta Wau wannan kasadar.

"Ya ki ka yi shiru ko ba zaki yi ba?"

"Wace ni? Ki ?addara an gama wannan aikin uwar Wakina, zan yi da iznin Allah".

"Ai na zata ba zaki yi bane, sai kuma abu na biyu, wata jita-jita nake son ki yaWa mini a gidan nan, na san daga nan har masarauta kowa zai ji, dan duk wani mufurci ku hadimai kun iya shi. Ina son ki je ki yayata cewar, Adam ya yi shaye-shaye ya bugu ya tashi yin?urin yi wa iman fyaWe!"

Ras! Gaban baba uwani ya faWi, ta gyara zamanta ta ce "Uwar Wakina, fyaWe kuma?"

"Eh, ko baki ji ba?"

"Allah ya baki yawan rai, na ji zan kuma aiwatar"

A wula?ance "Mummy ta ce "Tashi ki je"

Jiki a sanyaye baba uwani ta tashi ta bar Wakin.

A hanyar komawa sashinsu ta haWu da baba sabuwa, sabuwa ta ?ure uwani da ido, uwani ta ce "Lafiya ki ke yi mini wannan kallon haka?"

"Lafiya lau, kawai ina tunanin ranar da dubunki ta cika ya zaki yi? Baiwar Allah can ta yarda da ke ta baki amanar kanta da ta 'ya'yanta kina ci, duk wahalar da take yi miki"

A fusace baba uwani ta ce "To ina ruwanki, bana son saka ido fa, wallahi idan ba ki yi wasa ba, sai na gaya mata ta Wau mataki a kan ta".

"Wallahi ki ka gaya mata, kan ta Wau mataki a kaina zan Wauka a kanku, dan sai na ja abun da za'a Wauremu duka, dan nima na san sirrinta tana sakani aiki, ni idan nayi mata babu laifi, dama hadimarta ce ni, ke kuwa fa? Ki dai ji tsoron Allah wallahi" ba ta jira me baba uwani za ta ce ba, ta tafi ta bar wurin.

Hajiya Jamila Wawisu sarkin ado, sukari ba ka yi farin banza ba, gugar ?arfe sha kwaramniya. Haka hadimanta suka shiga jera mata kirari, sai dai babu wanda ta kula ta cigaba da takunta Wai-Wai ta nufi sashin Ammi.

Ammi kuwa na zaune ita da Adam a Wakinta, yana zaune a gabanta ya sunkuyar da kansa, sai dai duk ya rame, cikin nutsuwa da tawakalli Ammi ke yi masa nasiha.
"Har kullum Adam ba zan gaji jadadda maka batun yin addu'a ba, addu'a na da muhimmanci a rayuwarka, tun da na haifeka a cikin jarrabawa ka ke, ko in ce muke, ka ?ara ha?uri wannan ma zamu cinyeta da yardar Allah, ka yi ha?uri ka jure, na sani akwai ciwo amma ka sani, jarrabawa alamar soyayya Allah ce ga bawansa, kullum cikin Addu'a nake maka, har abada ma?iyanka fadawanka ne, waWanda ka sani da wanda ba ka sani ba, Allah zai ije maka su in dai har kana Addu'a, ni dai fatana ka rage zafin zuciya adam, babu in da zuciya zata kai ka, ka din ga ha?uri da yanayin da duk zaka tsinci kan ka" wata hadimar Ammi ce ta nemi izini ta shiga, ta sanarwa da Ammi zuwan Mummy.

Sai da gaban Ammi ya faWi, ba ta ?aunar abin da zai haWata da Mummy, dan ba ?aramin fargaba take shiga ba, ?arfin Addu'a ne yake sanya ta iya ri?e kanta.
Jiki a sanyaye ta tashi ta fita falo, ta tarar da Mummy a zaune a falon tana yi wa iman magana, sai dai ba ta kai ga jin abin da take cewa iman Win ba ta yi shiru.

Ita kanta iman ba ?aramin tsoron Mummy take ji ba, saboda haWuwarsu babu daWi sam, ta tsaneta sosai da sosai.

Fuskar iman Ammi ta kalla, ta san akwai wani abu da Mummy ta gaya mata, da ya sanya Iman shiga ruWi, dan fuskar iman kullum idan ba murmushi ba, to tabbas shagwaSa, amma sai ta ga iman a razane.

Mummy kuwa na ganin Ammi ta faWaWa murmushin ta, ta risuna ta ce "Allah ya taimaki giwa, barka da fitowa".

Ammi ta nemi wuri ta zauna, ta ce "Barkan ki dai, kuna lafiya?"

"Eh to, mun gode Allah sai dai ba na ce lau ba, yara babu wanda yake zuwa, duk sun Wauke ?afarsu".

"Kin san yanayin makaranta, ba sa samun zama shi ne kawai".

Mummy ta yi murmushi ta ce "Haka ne, dama yara ne suka zo mini da batun rashin lafiyar takawa, na ce bari na zo na yi masa sannu, Allah ya bashi lafiya, amma gaskiya yakamata ki tashi ki nema masa magani, shi da ake sanya ran ya gaji mahaifinsa, amma ya din ga abu kamar mahaukaci, gaba Waya zance ya cika masarauta har kunnen manya".

Kalmar mahaukacin da ta kira Adam da shi, ba ?aramin dukan Ammi ya yi ba.

Amma ta maze ta ce "Ai shi lamari irin wannan, duk maganin da zaka nema, lafiya ta Allah ce, idan ka mi?a masa lamarinka kuma, sai ya kawo maka mafita, tun da shi ya halicci kowa".

Mummy ta Wan kaWa ?afa ta ce "Haka ne, akwai wasu Wabi'unki da suke burgeni, wanda har nake koyi da su, ?arfin hali da yarda da kai, bari mu gani idan yana da rabon warkewa, Allah ya bashi lafiya, na barki lafiya uwar masu jiran gado" ta mi?e tana wani irin shu'umin murmushi.

Kan iman Ammi ta mayar da idonta ta ce "Iman, me ta ce miki ne?"

Iman ta ?a?alo murmushi ta ce "Bakomai Ammi, tambayata take ya jikin Takawa" Ammi tayi shiru, dan ta san iman ?arya tayi mata, ba ta takura sai ta ji ba, saboda kar ta ji abin da zai ?ara bata haushi.

***
A hankali ruma ta buWe idonta, ta ji kanta kamar ba nata ba, yayi mata wani irin nauyi har yana nema ya rinjayeta, daga kwance nan ma jiri take yi.
Shiru ta yi tana ?o?arin tuna abin da ya faru, kan abun da aka watsa mata ya Wauketa, ta tuna yadda ta ga ana jan Aisha, da ta ja ta tsaya saboda cikinta, Waya daga cikinsu wani ya tsinketa da mari, har sai da ta dur?ushe saboda gigicewa, Waya daga cikinsu ya takata da ?afarsa, ta saki ihu daga haka ruma ba ta san meya kuma faruwa ba.
A gigice ruma ta tashi, sai dai ta cigaba da tangaWi, saboda abun bai saketa ba, Aisha ta hango a zaune jingine da bishiyar da suke kwana a ?asanta da daddare.
Ruma ta nufeta, amma ta kasa sauri, da ta yi ?o?arin yin sauri, sai ta ji tana ?o?arin faWuwa.
Tana zuwa ta tarar da Aisha a zaune, idonta Waya ya tara jini, fuskarta duk a kumbure, zaninta kuma na farin leshi, ya rine da jini, sai haki take yi.

"Anty Aisha menene? Me suka yi miki?" Ruma ta yi maganar da ?yar.

Alama ta yi wa ruma da ta ?araso kusa da ita, ruma ta ?arasa a hankali ta zauna a kusa da ita. Aisha ta mi?a hannu ta ri?o na ruma, ta Wora a kan cikinta sannan ta ce "Rumaisa, takani suka yi a cikina, kin ji babyna ba ya motsi" tayi maganar tana fashewa da kuka.
Kuka ruma ta saka ta ce "Suwaye su? Me ki ka yi musu?"

"Ban sani ba, sun ce ba dan su karSi kuWin fansa suka Waukoni ba, dan su tozarta ni ne, ki yi mini Addu'a dan Allah, Allah ya sa babyna yana raye, na fara jin jiri, na zubar da jini da yawa".

Ruma ta rasa abun yi, ta rungume Aisha suna kuka.

"Zaki iya tashi a rakaki wurin da zaki wanke jikinki?"

Barde yayi

Please Login or Register in order to submit comment