You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta san tabbas tana jin wani abu akan ARFAAZ, amma ta hana kanta aminta da hakan.
Hatta Inna Abu sai da ta fahimci yadda gaba daya take duk ba kuzari kamar ba Tanƙoki ba duk ta yi shiru da ita ba tsokanar tsiwa ba komai, domin koda Inna Abu ta aike ta siyo koko haka ta dawo salin alin ba tare da an biyo bayanta da sunan kawo ƙarar ta ba sai hakan ya yi ma Inna Abu wani iri ta kasa samun sukuni sai da ta tambaye ta ko dai wani abin ke damunta amma sai ta ce babu komai.

A ɓangaren ARFAAZ kuwa yau ma kamar kullum yana tsaye yana duba aikin filinsa.
Jabir ya zo.
“Sir, everything is ready for inspection.”
ARFAAZ ya gyada kai.
“Good.”
Sai ya yi shiru.
Jabir ya kalle shi.
“Sir… you’ve been coming here every day.”
ARFAAZ ya amsa a taƙaice: “It’s my project.”
Cikin suɓutar baki Jabir ya ce: “…Or something else?”
ARFAAZ ya kalle shi da sanyi sai kuma a dake ya ce.
“Work.”
Amma idonsa ya kallon wani wurin daban.
Kamar yana jiran wani ya bayyana.

“Wayyo Allah! Akuya tah!”
Kowa na wurin ya juya da sauri jin muryar mutuniyar
Tanƙoki na tahowa tana bin akuyarta kamar kullum 😂
ARFAAZ ya riga ya gane muryarta tun kafin ma ya juya.
“…Of course.”
Sai ya juya.
Idanunsu suka haɗu.
Shiru.
Tanƙoki ta tsaya.
“Kai kuma yau ma anan?”
ARFAAZ: “Yes.”
Tanƙoki: “Baka koma l Abuja ba?”
ARFAAZ: “I told you. This is business.”
Tanƙoki ta taɓe baki.
“Business ɗinka ya fi yawan zuwa nan.”
ARFAAZ ya ɗan yi murmushi kaɗan.
“…Maybe.”
Tanƙoki ta zaro ido.
“Kai yanzu har ‘maybe’?”
ARFAAZ ya kalleta sosai.
“You notice everything I do.”
Tanƙoki ta yi saurin juya kai.
“Ni? Ni ban kula ba!”
Ta faɗa fuskarta na blushing again.
ARFAAZ ya matsa kaɗan kusa.
“You were avoiding me yesterday.”
Tanƙoki ta zaro ido.
“Ni? A’a!”
ARFAAZ ya sake faɗin: “You were.”
Shiru.
Tanƙoki ta ce: “Ni fa ba damuwa nayi da kai ba.”
ARFAAZ ya kalleta sosai. Dariya na son kwace masa.
“…Then why do you look at me first every time I arrive?”
Silence mai nauyi ya ratsa tsakaninsu.
Tanƙoki ta ji zuciyarta ta tsaya na ɗan daƙiƙa.
Ta juya kai da sauri.
“Ni zan tafi”
ARFAAZ ya kira sunanta for the first time: “Tanƙoki.”
Ta tsaya.
Ba tare da ta juya ba.

ARFAAZ ya ce a hankali:
“You confuse me.”
Tanƙoki ta juya da sauri.
“Ni ban ma ji mai kace ba.”
ARFAAZ ya matsa gaba ɗaya.
“Okay.”
Idanunsu suka haɗu sosai.
ARFAAZ ya furta a hankali: “I don’t understand why I look for you every day.”
Tanƙoki ta yi shiru.
ARFAAZ ya ci gaba a hankali:
“And I don’t understand why I don’t feel normal when you’re not around.”
Shiru ya sake ratsa tsakaninsu.
Kamar duniya ta tsaya.
Tanƙoki ta ji numfashinta ya canza.
Ta ja baya kaɗan.
“Ka… ka daina min turancin banaso.”
Kamar wacce zatayi kuka ta yi maganar domin ji ta yi maganar nasa duk da da turanci ya yi kuma bata wani fahimta ba amma sun saka taji wani iri.
ARFAAZ ya kalleta.
“Why?”
Tanƙoki ta ɓata fuska: “Kullum sai kayi turanci ne wai sai kace dole?.”
ARFAAZ: “…Turancin ne baki so nayi?”
“E”
Ta bashi amsa da sauri.
“Okay zan gwada denawa amma fa ban
“Kar ka damu zan koya maka”
Ta faɗa tana rugawa da gudu tabi yar akuyarta suka bar Wurin.

ARFAAZ ya tsaya yana kallon ta tana tafiya.
A hankali ya ce:
“…Wai me yarinyar nan take nufi dani ne sai muna magana kuma ta tafi.”
Sai kuma ya basar ya ci gaba da abin da yake yi.

***
BAYAN WATANNI BIYU.
Tun safe workers suka lura yau boss ɗinsu ba kamar kullum yake ba.
ARFAAZ yana tsaye kusa da motarsa, waya a hannunsa, amma hankalinsa baya wajen aikin.
Jabir ya matsa kusa.
“Sir, za mu fara aikin bayan wajen?”
ARFAAZ bai amsa nan take ba.
Idonsa yana kallon hanyar da ta saba fitowa…
Amma babu Tanƙoki.
Jabir ya sake magana ganin kamar bai ji shi ba: “Sir?”
ARFAAZ ya dawo hayyacinsa.
“…Yes. Go ahead.”
Sai ya sake kallon hanyar.
Still nothing.
A hankali ya tambaya:
“Did anyone see Tanƙoki today?”
Jabir ya ɗan ɓoye murmushi.
“A’a sir.”
ARFAAZ ya gyada kai kawai.

“Why am I bothered?”

Ya faɗa a fili cikin son basarwa.

A ta ɗayan ɓangaren kuwa...
Tanƙoki ce zaune tana ƙoƙarin gyara gashin kanta ga ƙaton mudubi a gabanta.
Lantana ta zaro ido.
“Ke Tanƙoki… tun yaushe kika fara gyara gashi haka ban sani ba? Ni dai a iya sanina ko wanke gashin nan baki yi daga shekara sai shekara”
Tanƙoki ta harare ta.
“Tohm yau kuma nayi ra'ayin gyarawa sai aka yi ya.”
Ta faɗa tana wani farrr da ido.
Bebi ta fashe da dariya.
“Ko saboda miskilin can ne?”
Tanƙoki ta yi saurin juyawa.
“Wayyo Allah! Ku daina haɗa ni da shi mana shi fa ɗan birni ne ni kuma yar ƙauye!”
Ta faɗa iya gaskiyar ta.
Amma fuskarta ta ɗan yi ja.
Sai ta ɗauki mayafi da sauri.
“Ni kam na tafi zan je kasuwa.”
Lantana ta ce: “Kasuwar wajen aikin ARFAAZ ko?”
Tanƙoki ta jefawa Lantana kumb tana murmushi.


A can filin aiki kuwa.
ARFAAZ na duba papers ne a daidai lokacin kuma ya ji karaɗin muryarta.
“Gud morni.”
Nan take ya ɗago kai.
Tanƙoki ce tsaye gabansa, amma yau… ta ɗan gyara kanta sosai. Duk da dama can baya ganinta da kazanta Sai dai rashin kula amma yau ya ganta fess, Sai faman washe baki takeyi.
ARFAAZ ya tsaya kallonta na seconds kaɗan.
Tanƙoki ta ruɗe.
“Me kake kallo?”
ARFAAZ ya ɗan gyara murya.
“…Nothing.”
Amma idonsa ya sake komawa kanta.
A zuciyarsa ya furta:
“She looks… beautiful.”
Tanƙoki ta ce da sauri:
“Nayi turanci fa.”
Tana nufin Gud morni ɗin da ta ce.
ARFAAZ ya amsa ma ta da: “Ai naji.”
Tanƙoki ta sake washe baki. Tare da ƙara faɗin.
“Gud morni.”
ARFAAZ ya ɗan yi murmushi.
“It’s ‘good morning.’”
Tanƙoki ta turo baki: “Ai shi ɗin na fada haka nace, Morni.”
ARFAAZ ya ce: “No. Morning ake cewa.”
Tanƙoki ta sake kokarin jaraba faɗa daidai: “To 'Morni' hakan ya yi ko?.”
ARFAAZ still bai gaji ba ya sake gyara ma ta da: “Morning.”
Tanƙoki ita ma ta sake maimaitawa wannan karon sai ta faɗa daidai. “Morning.”
ARFAAZ ya ɗan ɗaga gira yana ɗan murmushi.
“Better.”
Tanƙoki ta yi wani ƙaramin tsalle.
“Kaiii! Ashe yanzu ni international girl ce tun da na iya turanci!” 😭😂
Workers suka fara dariya. Domin ita Tanƙoki kullum da irin salon nishadin da take basu.
Har ARFAAZ sai da murmushi ya bayyana sosai a saman fuskarsa har ya fara blushing ba tare da ya ankara ba.

“Kwana biyu baki zo ba.”
Ya sama kansa da faɗa.
“Ba Inna Abu ba ce ta hanani ta ce kwana biyu ina wasa da makaranta shi ne ta haɗa ni da Kawu Tukur shi kuma yake tasani a gaba kullum sai mun je makarantar a tare shi ya sa baka ganina”
“Good, kwara ki nutsu kiyi karatu muddin kina so ki iya turanci ta yadda zaki zama international girl da kyau.”
Tanƙoki ta washe baki: “Da gaske.”
Ya jinjina ma ta kai.
Bayan wani lokaci...
Tanƙoki ce ke ƙoƙarin ɗaukar wani kwando mai nauyi kamar an saka.
ARFAAZ da ya lura ya yi saurin faɗin.
“Leave it.”
Tanƙoki ta ce: “A’a zan iya ɗauka fa.”
Ta ɗaga kwandon cikin ƙarfin hali ai kuwa sai ta ɗan zame 😭
Nan take ARFAAZ ya ƙari sa cikin zafin nama ya kamo ta kafin ta kai zuwa ƙasa.
Shiru mai sanyi ya ratsa tsakaninsu yayin da kwandon ya faɗi ƙasa.
Amma babu wanda ya kula. Saboda sun yi nisa a wata duniyar.
Hannun ARFAAZ na riƙe da nata.
Tanƙoki ta ɗago idanunta a hankali.
Zuciyarta na bugawa da sauri.
ARFAAZ kuwa yana kallonta kamar ya manta komai na rayuwa, kamar ya manta da komai dake wakana a wurin baya ji baya gani sai ita kad'ai ita kawai.
Workers daga nesa duk suka zuba na mujiya suna kallon ikon Allah .
Tanƙoki ta yi ƙoƙarin magana…
Amma ta kasa first time ke nan da hakan ya kasance da ita.
ARFAAZ ya matso kaɗan.
A hankali… cikin murya mai sanyi ya ce:
“You need to stop doing this to me…”
Tanƙoki ta kasa motsi.
“Eh…?”
ARFAAZ ya lumshe ido kaɗan.
“…Every time you’re around, I forget how to think.”
Shiru....
Tanƙoki ta ji kamar zuciyarta zata fito tsabar yanayin da ta shiga.
Sai ta yi saurin ja baya.
“N-ni… ni ban yi komai ba!”
Ta ɗauki mayafinta da ya fadi da sauri.
“Ni zan tafi!”
Ta ruga da gudu ta bar wajen tana waigowa ta kalleshi.

ARFAAZ ya tsaya yana kallon ta tana gudu.
Sai Jabir ya matsa kusa da shi a hankali.
“…Sir.”
ARFAAZ ya amsa: “What?”
Jabir ya cw: “You’re smiling again.”
ARFAAZ ya tsaya cak.
Sai ya gyara fuska da sauri.
“I’m not.”
Ya faɗa yana wani shan kunu shi ala dole kar aga damarsa.


Tun bayan abin da ya faru jiya…
Tanƙoki ta kasa zama normal
Tana cikin wanke wanke kwanuka, sai ta tuna kalamansa da suka zauna daram a ranta:
“Every time you’re around, I forget how to think…”
Nan take ta jefar da cokali cikin ruwa.
“Wayyo Allah!”
Ta faɗa da ƙarfi kamar wacce kunama ta harba.
Bebi da Lantana suka juya suna kallonta.
Lantana ta ce: “Ke lafiya kuwa?”
Tanƙoki ta yi saurin gyara zama.
“Eh”
Ta faɗa a taƙaice.
Bebi ta ɗaga gira.
“Toh me yasa fuskar ki ja haka?”
Tanƙoki ta ce: “Zafi ne.”
Lantana ta fashe da dariya.
“Ko soyayya ba?”
Tanƙoki ta tashi tsaye da sauri.
“Ni na tafi zan je rafi!”
Da gudu ta fice ba tare da ta ƙari sa wanke wanken ba, Inna Abu da ta fito daga ɗaki tana kwala ma ta kira amma ina tuni ta yi nisa.

Daga can ɓangaren kuwa...
ARFAAZ yana tsaye yana magana da workers.
Amma hankalinsa baya a wurin tattaunawar da suke yi sam.
Saboda yau… Tun safe bai ga Tanƙoki ba.
Jabir da ya lura.
“Sir… you’ve checked that road like ten times.”
Ya faɗa ganin Hanyar da ARFAAZ ɗin yake ta kalla.
ARFAAZ ya ɗan juya kai.
“I’m waiting for supplies.”
Jabir ya ɓoye murmushi.
“Supplies mai suna Tanƙoki ko?”
ARFAAZ ya kalle shi da serious face.
Jabir ya yi saurin faɗin: “…I’ll go back to work sir.”

Tanƙoki kuwa tana zaune bakin ruwa tana jefa duwatsu.
“Ni me yasa ma wai na gudu ne jiya?”
Ta dafe kumatunta da duka tafukan hannunta.
“Kuma me yasa zuciyata ta yi haka?”
Sai ta kwaikwayi ARFAAZ da muryarsa.
“I forget how to think.”
Ta rufe ido da sauri.
“Wayyo ni!”
Ta faɗa a birkice.
Sai ta ji wata murya daga baya:
“You’re talking to yourself now?”
Nan take ta razana.
Ta juya da sauri.
ARFAAZ ta gani.
Tsaye yake da hannayensa cikin aljihu.
Tanƙoki ta zaro ido.
“Kaiii! Yaushe kazo nan?”
ARFAAZ ya matso a hankali.
“You didn't come shi ya sa nazo da kaina .”
Tanƙoki ta juya kai. Ba tare da ta ce Komai ba.
ARFAAZ ya sake faɗin: “You avoided me all morning.”
Tanƙoki ta yi saurin faɗin: “Ni? Da yaushe”
ARFAAZ ya ɗan yi murmushi.
“You’re doing it again.”
Tanƙoki ta ruɗe.
“Menene?”
“Running.”
Shiru.
ARFAAZ ya zauna kusa da ita.
Wannan karon babu faɗa.
Babu tsiwa duka a tare da ita. She's just Normal.
Sukayi shiru su duka yayin da iska mai sanyi ke kadawa sai kuma da bugun zuciyoyinsu.
Tanƙoki ta ce a hankali:
“Kai… me yasa kake yawan kallona ne haka?”
ARFAAZ ya kalleta kai tsaye.
“Kawai ina jin daɗin hakan ne nayi ta kallonki.”
Tanƙoki ta kasa magana.
Sai ta yi saurin ɗaukar dutse tana jefawa cikin ruwa.
“Ni dai banaso.”
ARFAAZ ya furta: “Why.”
Tanƙoki ta ɗan saki dariya kaɗan. Ba tare da ta ce komai ba.
ARFAAZ ya tsaya yana kallon murmushinta.
A hankali ya ce:
“…I like it when you laugh.”
Tanƙoki ta tsaya cak.
Yayin da zuciyarta ke sparkling dan dadi.

A dai-dai wannan lokacin…
Wayar ARFAAZ ta fara ringing.
Ya duba screen.
“Mother.”
Sunan da ya bayyana.
Ya ɗan ɗaga gira kafin ya ɗaga wayar.
“Yes?”
Muryar mahaifiyarsa ta fito:
“Arfaaz You need to come… Hafsat and her family are coming tonight.”
ARFAAZ ya yi shiru.
Tanƙoki ta lura fuskarsa ta canza.
“Me ya faru?”
Ta tambaya cikin kulawa.
ARFAAZ bai amsa mata ba.
Mahaifiyarsa ta ci gaba:
“We need to discuss the engagement.”

Idanun ARFAAZ suka ɗan canza.
Tanƙoki kuwa tana kallonsa cikin rashin fahimta.
A hankali ta tambaya:
“…Engagement?”
Tabbas duk da ba jin turanci take ba amma tana gane wani abin ciki har da ma'anar kalmar Engagement.
ARFAAZ ya rufe ido na ɗan daƙiƙa ba tare da ya iya furta komai ba.


Washegari.
Tun daga jiya har zuwa yau Tanƙoki ta kasa nutsuwa. Ba kalmar dake amsakuwwa a kunnenta fa ce:
“Engagement…”
Kalmar ce kawai ke yawo a kanta.
Ta zauna ƙofar ɗaki tana hura iskar bakinta kamar wacce ta ci abu mai yaci.
Sai yar akuyarta, Bebi, ta zo tana cizon gefen mayafinta.
Tanƙoki ta ture ta.
“Ki barni! ba mood ɗin shirmenki nake ba.”
Bebi ta sake buɗe baki: “Meeeeh.” 🐐
Tanƙoki ta harare ta.
“Eh toh ai ke baki san ciwon zuciya ba ko? To zuciyata ciwo take min”
Ta faɗa tana wani dafe kirji tana farfar da ido kamar gaske.
Sai Lantana ta shigo gidan da sallama.
“Ashe kina nan kina ta fira ne da yar akuyarki. Ni kuma ina can ina nemaki”
Tanƙoki ta turo baki.
“Ni dai wallahi ban son maganar engagement nan.”
Ta faɗa cikin subutar baki.
Lantana ta ɗaga gira.
“Uhmmm… Har yanzu dai batun Engagement ɗin bai kare ba, wai ko dai kina son bawan Allah'n nan ne shi ya sa duk kika damu daga jin ance za'a masa Engagement ”
Tanƙoki ta yi saurin tashi.
“Ni ban damu ba!”
Sai Bebi ta ciji rigarta ta ja.
“Wayyooo! Wannan akuya zata cire min kaya wallahi!” Lantana dai ta yi dariya kawai domin dramar Tanƙoki da akuyarta yana bata nishadi ita kanta.



A ɓangaren ARFAAZ kuwa yana tsaye yana waya cikin ɓacin rai.
“I said I’m not discussing marriage right now.”
Mahaifinsa daga waya ya ce:
“You cannot avoid responsibility forever.”
ARFAAZ ya dafe goshinsa.
“I’ll call later.”
Ya kashe wayar da ɗan ƙarfi.
Sai dai kafin ya juya wani sauti ya karade kunnensa.
“Meeeeeh!”
Kafin ya ankara yaji wani abu ya bugi ƙafarsa.
Ya sauke idonsa akan Bebi yar akuyar Tanƙoki.
Akuya ta tsaya tana kallonsa kamar ta san shi.
ARFAAZ ya ɗan matsa baya.
“…Why is this goat always around me?”
Sai Jabir ya fara dariya.
“Sir tana son turarenka ne ƙila.”
ARFAAZ: “…Excuse me?”
A dai-dai lokacin Tanƙoki ta ƙaraso da gudu tana kwala ma akuyar kira.
“BEBI!!”
Akuya kuwa ta ruga kai tsaye zuwa cikin motar ARFAAZ.
Tanƙoki ta bi bayanta da gudu.
ARFAAZ ya zaro: “No no no!”
Amma ina lokaci ya kure.
Bebi ta yi tsalle ta shiga cikin motar ta buɗe baki tana tauna wani paper.
ARFAAZ ya zaro ido.
“My documents!”
Tanƙoki ta tsaya cak. Ta ma kasa hana akuyar abin da take yi.
“…Uh oh.”

ARFAAZ ya buɗe motar da sauri.
Bebi na ciki tana tauna papers kamar ta sama ciyawa.
ARFAAZ ya furta a ɗan fusace: “Get that goat out!”
Tanƙoki ta ce: “Bebi fito! Wallahi zan zane ki faj!”
Ta yi maganar kamar tana yi da mutum ba dabba ba.
Akuya ta ɓare baki: “Meeeeh.”
Sai ta ƙara tauna paper ɗin.
Jabir ya juya gefe yana dariya sosai.
Har workers suka fara taruwa suna Bama idonsu abinci.
ARFAAZ ya shiga motar gaba daya yana ƙoƙarin kwace paper ɗin.
Bebi ta gudu zuwa seat ɗin baya.
ARFAAZ ya bita.
Tanƙoki ma ta shiga motar.
“Kamo ta daga can!”
Ta faɗa.
ARFAAZ ya ce: “She just ate an important contract!”
Tanƙoki ta ce: “Toh ai baka bata breakfast bane shi ya sa!”
ARFAAZ ya tsaya cak yana kallonta cike da bacin rai.
“…What?!”
Ya fada a ɗan kufule.
Tanƙoki ta ce: “Ai yunwa take ji shi ya sa.”
Sai Bebi ta yi tsalle daga seat ta taka chest ɗin ARFAAZ tana kokarin ficewa daga motar.

First time ever…
ARFAAZ ya yi wani wawan jumping ɗin da bai ma san ya yi ba saboda akuya.
Workers kuwa suka fashe da dariya.
Har Jabir ya durƙusa ƙasa yana rike ciki tsabar dariya.
Tanƙoki kuwa ta riƙe ciki ita na tana dariya.
“Wallahi Bebi kin kashe billionaire Arfaaz.” 😂😂😂
ARFAAZ a kufule ya ce: “This is not funny!”
Amma ko shi kansa yana son ya yi dariyar amma ya maze.

Daga ƙarshe suka kamo Bebi da kyar.
Tanƙoki na riƙe da ita tana huci.
“Ki daina cin dukiyar mutane mana!”
Sai ta ɗago ta kalli ARFAAZ.
Yana tsaye yana gyara shirt ɗinsa cikin haushi.
Amma idanunsa na kanta.
Sai ya girgiza kai.
“You and this goat are a disaster.”
Tanƙoki ta washe baki.
“Amma kana sonmu ko?.”
Shiru ya yi kawai yana kallonta ya ka rasa abin da ya kamata ya ce tsabar takaici.
ARFAAZ ya tsaya cak.
Tanƙoki ma ta gane abin da ta faɗa. Ta yi kato ɓara.
“Kaiii ni ba haka nake nufi ba”
ARFAAZ ya matsa kusa kaɗan.
“…Maybe I do.” ya faɗa cikin raɗa.
Tanƙoki jin kalmar nasa ta yi tamkar al'mara ta yi tsaye tana kallonsa.

Sai Bebi ta ciji gefen rigar ARFAAZ.
ARFAAZ ya ɗan ja baya yana furta: “…Again?!”
Tanƙoki ta fashe da dariya sosai.
Wannan karon kuwa…
Har ARFAAZ ya kasa riƙe dariyarsa ya yi.

Da yamma…
Tanƙoki ita da Lantana tana tafiya gida tare da yar akuyarta Bebi a gefenta.
Amma murmushi yaƙi barin fuskarta.
Sai Lantana ta ce:
“Ke dai kin fada soyayya.”
Tanƙoki ta harare ta.
“Ni da wa?”
Kafin Lantana ta yi magana sai Bebi ta ɓare baki: “Meeeeh.”
Lantana ta fashe da dariya.
“Har akuyarki ta sani!”
Tanƙoki ta ji kunya ta ruga gida a guje.
Amma a zuciyarta…
Kalmar ARFAAZ ce kawai ke yawo kwnayarta:
“Maybe I do…” ❤️🔥



BAYAN WANI LOKACI.
Rayuwa ta ci gaba gudana abubuwa da yawa na ta faru wa tsakanin Tanƙokin da ARFAAZ a halin yanzu ma tuni mutanen ƙauyen Yelwa suka haɗa sunanta da na Arfaaz suna kiran ta da TANƘOKIN ARFAAZ tun bata amsawa har ta fara shi kuma idan yara su ganshi sai dai kaji sun ce ga angon Tanƙoki nan ga angon Tanƙoki nan, duk wannan budirin da ake yi Inna Abu tana sane da komai kawai ta zubama abin ido ne domin taga iya gudun ruwansu.
Yau tun safe....
Tanƙoki ta yanke shawara guda ɗaya wadda kuma kuma ta barwa zuciyarta sani akan shi.
Ta yafa mayafi ta fita ta wata hanya dabam domin kada ta haɗu da ARFAAZ.
Sai dai…
Da take tafiyar...
“Meeeeeh!”
Bebi ta ruga wani hanyar daban.
“Wayyo dawo nan!”
Tanƙoki ta bi bayanta da gudu…
Kai tsaye ta faɗa gaban motar ARFAAZ.
ARFAAZ yana tsaye jingine da motarsa, coffee a hannunsa.
Ya ɗaga gira yana kallonta ya ce.
“…Da kina ƙoƙarin gudu ne daga gareni?”
Tanƙoki ta yi saurin gyara tsayuwa.
“Ni? A’a.”
ARFAAZ ya ce: “I know that you almost died avoiding me.”
Tanƙoki ta ce: “Ni ai akuyata nake bi.”
Sai Bebi ta je ta fara lasar takalmin ARFAAZ '.
ARFAAZ ya sauke idonsa kanta.
“…Why does this goat behave like a criminal?”
Ya faɗa yana ɗan ja baya.
Tanƙoki ta washe baki.
“Ai tana sonka ne shi ya sa.”
ARFAAZ ya ce: “Your goat has expensive taste.”
Tanƙoki ta kasa riƙe dariya.
Sai ta tuna kalmar ta kwanaki da ta yi ma rikon hadda a kanta. “Maybe I do.”
Nan take ta haɗe rai. Tare da furta.
“Ni zan tafi.”
ARFAAZ ya tsaya yana kallonta.
“…You’ve been avoiding me since yesterday.”
Tanƙoki ta zaro ido.
ARFAAZ ya ci gaba: “Kin dena magana gaba daya baki yarda fira mai shawo yana shiga tsakaninmu”
Shiru ya ratsa tsakaninsu.
Sai ya ƙara:
“…It’s strange.”
Tanƙoki ta haɗe hannu.
“Toh ai baka son magana da mutane ne shi ya sa.”
ARFAAZ ya matso kaɗan.
“Amma ai ban ce bana son yi dake ba.”

Tanƙoki ta ji numfashinta ya tsaya.
Sai ta juya da sauri ta ruga da gudu.
ARFAAZ ya tsaya yana dariya a hankali. Yana kuma bin ta da kallo yana ɗan girgiza kai

Da rana…
ARFAAZ ne yake meeting da wasu mutane da suka taho daga Abuja.
Everything serious.
Documents. Phones. Business talk.
Sai ɗaya daga cikinsu ya ce:
“Mr. Arfaaz, we need full concentration.”
ARFAAZ ya amsa da: “Of course.”
A dai-dai lokacin.
“Meeeeeh!” kukan yar akuya Bebi ya karade wurin.

Kowa ya juya. Suna kallon akuyar cike da mamakin ganin yadda Akuyar ta shigo cikin meeting ɗin kamar wata shareholder.
Jabir ya rufe baki yana dariya.
ARFAAZ ya runtse ido. Yana furta:
“…No.”
A hankali.
Amma ina lokaci ya ƙure.
Bebi ta nufi expensive shoe ɗin wani daga cikin baƙin Abuja.
Ta kai baki ta fara taunawa.
Mutumin ya kasa komai sai faɗin
“HEY! HEY STOP IT!”
Da yake yi.
Ai kuwa an kace kwabo Meeting ya watse.
Sai ga Tanƙoki ta shigo a guje.
“BEBI!!”
Akuya ta gudu ƙarƙashin table.
Mutanen Abuja suka sake razana.
Tanƙoki ta rarrafa ƙarƙashin table tana kamo akuya.
“Zo nan mara tarbiyya!”
Sai kanta ya bugi table garin ya ɗago.
“Wayyooo!” 😭😂
Workers suka fara riƙe ciki dan dariya.
ARFAAZ kuwa… ya dafe goshinsa.
“This village will destroy me.”
Sai Bebi ta fito da gudu ta faɗa jikin ARFAAZ kafin ma ya rufe baki.
Coffee ɗinsa kuwa ya zube.
Mutanen Abuja ba baka sai idanu da suka zuba suna kallon ikon Allah.
Tanƙoki ta tsaya cak.
“…Uh oh.”
Silence.
Sai ARFAAZ ya kalli shirt ɗinsa.
Ya ɗago kai ya kalleta.
Tanƙoki ta fara ja baya.
“Ni… ni zan tafi.”
Ta faɗa cike da tsoro tana ja da baya.
ARFAAZ ya tsaya seconds kaɗan…
Sai kawai ya fashe da dariya.
Duk wajen ya yi shiru.
Mutanen Abuja suka kalli juna cikin mamaki.
Domin clearly… ba su taɓa ganin ARFAAZ yana dariya haka ba.
Tanƙoki ma ta zaro ido.
“Kaiii! Ashe zaka iya dariya har haka?” 😂
ARFAAZ ya girgiza kai yana kallonta.
“You’re a disaster.”
Tanƙoki ta ɗora hannu a ƙugu ta ce.
“Amma kana surviving ba.” 😭😂❤️

Da dare…
Tanƙoki tana tafe a hanyar komawa gida amma tare suke da Arfaaz da acewarsa wai gidan shugaban ƙauye zai je bayan kuma ba nan ne hanyar ba.
Murmushi yaƙi barin fuskarta.
Sai wayar ARFAAZ ta fara ringing.
Tana kusa dashi ne.
ARFAAZ ya ɗaga wayar.
Muryar wata yarinya mai sanyi ta fito:
“Arfaaz… I miss you.”
Tanƙoki ta tsaya cak.
Zuciyarta na bugawa da karfi
ARFAAZ ya yi shiru na seconds, kafin a hankali ya furta: “…Hafsat.”
Tanƙoki ta sauke idonta a hankali.
Murmushinta ya ɓace nan take.
Sai ta ji wani iri zuciyarta ta yi ma ta ba daɗi.
Amma saboda ita ɗin Tanƙoki ce…
Sai ta haɗe rai.
“Hmph.”
Ta juya da sauri.
“Ni me ya shafe ni ma!”
Ta faɗa a fili tana tafiyarta abin ta.
Amma fa fuskar nan a d'aure ta mau.
*✦ TANƘOKIN ARFAAZ ✦*
When two souls collide…
the result becomes laughter,
tears,
jealousy,
and uncontrollable love.
A Hausa Novel With Full Cinematic Drama & Comedy
*_BY NAINARH KD ✍️❤️_*

CHAPTER 5
Tun bayan wayar jiya da Arfaaz ya yi a gabanta.
Tanƙoki ta tashi da wani irin haɗewar rai jin kanta take cikin wani kalar yanayi na daban. Hakan ya sa take jin kanta a fusace take, yanzu ma tana share tsakar gida ne, amma yadda take sharar da ƙarfi kamar zata cire ƙasar gaba ɗaya.
“Mtswww!”
Taja tsaki mara dalili.
Lantana ta zaro ido.
“Ke lafiya?”
Tanƙoki ta amsa ma ta a taƙaice: “Eh mana!”
Sai ta ci gaba sharar da ƙarfi.
Bebi akuya ta matsa kusa da ita.
Tanƙoki ta harare ta. Kamar ita ta kar zomon.
“Ke ma ki bani waje kafin nayi ciki dake! Duk ku maza halin ku ɗaya ne!”
Lantana mai zatayi idan ba dariya ba.
Akuya kuwa ta ɓare baki ta ce: “Meeeeh?” kamar mai son gane abin da Tanƙokin ta ce.
Lantana har da riƙe ciki tsabar da dariya.
“Wato har akuyar ma yau haushinta ake ji, to ai ba ita ta kar zomon ba.”
Tanƙoki ta haɗe hannu.
“Ni dai wallahi bana son mutanen da suke waya da yan mata da dare haba sai kace marasa gaskiya.m...”
Sai kuma ta tsaya cak.
Lantana ta ɗaga gira.
“Uhmmm… ke dai ki faɗa gaskiya kawai Malama nasan abin da ya sa kike duk wannan ba komai ba ne fa ce kishi.”
Tanƙoki ta zaro ido.
“Niii! Kishi?! Allah suturu bukwui inji kishiyar mai doro”
Sai ta juya da sauri.
“Ni maza ma basa damuna.”
A dai-dai lokacin akuya ta sake.
“Meeeeeh!”
Tana kama gefen mayafin Tanƙokin sannan ta ruga ta gudu 😭😂
“Wayyooo! Dawo min da mayafi!”
Ta faɗa tana bin akuyar da gudu.



A can filin aiki kuwa ARFAAZ yana tsaye yana kallon workers yadda suke aikin bisa tsari yana kuma nuna musu abin da ya dace domin gini ya yi nisa suna ma dab da kammalawa.
Amma hankalinsa… yana kan wani abu dabam.
Jabir ya matsa kusa.
“Sir… you seem quiet today.”
ARFAAZ ya gyada kai kawai.
Sai ya tambaya casually:
“Did Tanƙoki come here?”
Jabir ya ɓoye murmushi.
“A’a sir.”
ARFAAZ ya ɗan lumshe ido.
“…Strange.”
A zuciyarsa ya ce:
“Why didn’t she come?”

Tanƙoki kuwa tana biye da Bebi har suka iso kusa da filin ARFAAZ.
Akuya ta ruga kai tsaye wajen motar ARFAAZ.
“Keee! Bebi dawo nan!”
Sai ta tsaya da ganin ARFAAZ.
Shiru ya ɗan ratsa.
ARFAAZ ya kalleta.
Tanƙoki ta juya kai da sauri.
“Ni ba wajen ka nazo ba.”
ARFAAZ ya ce yana ɗan murmushi: “…I didn’t ask.”
Tanƙoki ta haɗe rai.
“Toh ai na faɗa maka ne saboda ka sani.”
ARFAAZ ya lura da yanayinta.
“…Fushi kike ne?.”
Tanƙoki ta bashi amsa da sauri: “Ni? Akan me zan yi fushi?.”
ARFAAZ ya ce: “You’ve said that every time you’re upset.”
Tanƙoki ta turo baki.
“Ni me ya shafe ni idan kana waya da Hafsat ko Half Fried ko duk wanda take ma oho ni ina ruwa na!”
Workers suka zuba musu idanu kawai suna kallon drama dariya na cin su.
ARFAAZ ya ɗan ɗaga gira.
“…Half fried?”
Tanƙoki ta ce: “Eh! Sunan ma kamar indomie.”
Jabir ya juya baya yana dariya sosai domin ya kasa riƙe wa shi ya sa ya saki abarsa.
Ma'aikatan kuwa wasunsu har da riƙe ciki tsabar dariya. Domin sun lura Tanƙoki dai ta zurma da yawa ba tare da ta sani ba gata kuma da wauta tana ta tona kanta.
ARFAAZ kuwa… ya kasa riƙe murmushinsa.
Sai ya matsa kusa da ita.
“You were jealous, haka kike da kishi ashe, amazing.”
Tanƙoki ta zaro ido.
“Ni?!”
Sai Bebi ta zo ta tsaya tsakaninsu.
“Meeeeh.” 🐐
Tanƙoki ta nuna akuyar.
“Ga ita ma ta ce ƙarya kake!”
ARFAAZ ya girgiza kai yana dariya a hankali. Tsagwaran wauta irin na Tanƙoki yana bashi nishadi ba kaɗan ba.

ARFAAZ ya ɗan rage murya.
“Hafsat is just someone my family chose.”
Tanƙoki ta yi shiru. Ba ta ce komai ba duk da bawai ta gama fahimtar kalaman nasa ba ne.
ARFAAZ ya ci gaba: “There’s nothing between us, saboda haka ki kwantar da hankalinki babu komai a tsakaninmu.”
Tanƙoki ta ɗan ɗago kai.
“…Da gaske?”
Sai kuma ta yi saurin ɓoye fuska jin suɓutar baki da ta yi.
“Ni ba tambaya nake ba!”
ARFAAZ ya ɗan yi murmushi.
“But you wanted to know. Kina son ki sani naga hakan a

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment