You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng *✦ TANƘOKIN ARFAAZ ✦*
⚠️ COPYRIGHT & WARNING ⚠️

© 2026 NAINARH KD⁂𝒩𝓀𝒹𝓈❦♡

All Rights Reserved.

An haramta kwafi, bugawa, rabawa, canjawa ko amfani da kowane ɓangare na wannan littafi ba tare da cikakken izini daga marubuciya ba.

Duk wanda aka kama yana:
❌ Satar littafin
❌ Cire sunan marubuciya
❌ Canja wani ɓangare na littafin domin amfanin kansa

Zai fuskanci matakan da suka dace bisa doka da ƙa'idojin kare haƙƙin mallakar rubutu (Copyright Law).

📌 GARGAƊI

Wannan littafi mallakin marubuciya ne kaɗai.

A mutunta haƙƙin marubuta ta hanyar gujewa:
• Screenshot ba tare da izini ba
• Forwarding PDF da suka kasance paid ba tare da izini ba
• Copy & Paste na paid page's
• Reposting a wani shafi da sunan wani

Ku taimaka wajen tallafawa marubuta ta hanyar karanta littafi daga sahihin tushe.

Allah Ya saka da alheri.

✍️ NAINARH KD⁂𝒩𝓀𝒹𝓈❦♡

This book is dedicated to:

Every dreamer who refuses to give up despite life's challenges.

Every reader who believes that true love can blossom in the most unexpected places.

To everyone who sees a part of themselves in Tanƙoki – imperfect, loud, fearless, and full of life.

And to those who have loved sincerely, laughed wholeheartedly, and kept believing in happy endings.

May your story be as beautiful as the one you dream of.

❤️

– Nainarh KD⁂𝒩𝓀𝒹𝓈❦♡

Dear Reader,

Welcome to the world of Tanƙokin Arfaaz.

This story was written with love, laughter, emotions, and countless moments of imagination. While reading, you will encounter characters who will make you smile, laugh, cry, and perhaps remind you of people you know in real life.

Tanƙoki is not a perfect heroine. She is loud, stubborn, funny, and sometimes completely chaotic. Yet, her imperfections are what make her special.

Arfaaz, on the other hand, teaches us that love is not about finding someone perfect; it is about finding someone whose imperfections become your happiness.

Beyond the romance and comedy, this story also carries lessons about family, forgiveness, resilience, destiny, and the power of true love.

I hope this book brings you joy, comfort, and unforgettable memories.

Thank you for choosing to be part of this journey.

Happy Reading!

With Love,

✍️ NAINARH KD⁂𝒩𝓀𝒹𝓈❦♡

_Abin da sunan Labarin yake nufi shi ne; Tanƙoki dai suna ne da mutanen ƙauyen Yelwa suka saka ma Jarumar labarin saboda ta kasance mai shegen neman magana da tsiwa da kuma jan magana yayin da ARFAAZ ya kasance sunan Jarumin labarin wanda kuma Tanƙoki ta kasance shi da ita su ne Ƙaddarar junansu... TANƘOKIN ARFAAZ_


Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinƙai.

CHAPTER 1
Mota ce ƙirar Lamborghini Aventador take sharar gudu a kan hanyar zuwa ƙauyen Yelwa. Haɗu wa da tsayuwar motar da yadda take sharara gudu cikin nutsuwa ba tare da hayaniya ko tada ƙura ba kaɗai ta isa ta saka mutanen ƙauyen fitowa bakin hanya suna kallon ikon Allah.
“Wayyo ni Sahura! Amma dai wannan ai ba mota bace, jirgin ƙasa ne!” wata mata ta faɗa tana dafe ƙirji tana kuma zazzaro idanu domin ganin tsaruwar motar Ba kalar wacce suka saba gani ba ko a film ya sa take wannan sambatu ba tare da ta sani ba.
“Ya Allah ko'a mafarki ne kasa ina da rabon shiga irin wannan mota na sama damar tuƙa ta, da kuwa naji dad'ina domin kuwa saurayi zan koma d'anye jagal ah to ai dama talauci shi ne ya tsufar dani domin da saurana” wani dattijo ya faɗa hankali kwance yana kuma ware ido akan motar da tuni ta yi gaba ta bar su da santi, yayin da maganar nasa tasa mutane dariya. Yayin da wasu ya basu tausayi wasu kuma suke ganin wautarsa.

A cikin motar kuwa wani matashi ne zaune cikin shiga ta alfarma. Farar rigar polo ce a jikinsa, sanye da agogonsa mai tsada da ba kowa ne zai iya kallo sau biyu ba tare da ya gane kuɗi suke magana ba a wurin.
ARFAAZ ke nan saurayin matashin ɗan kasuwa mai ji da kansa musamman da ya kasance kyakkyawa abin so ga ko wacce mace kuma akayi katari ta ko'ina ƴan mata rububinsa suke.
Fuskar sa ɗauke da wani irin kwarjini da miskilanci. Tun daga yadda yake riƙe da steering har yadda yake magana a waya zaka fahimci ba mutum ne mai son hayaniya ba.
“Yeah… I’m already in Yelwa. Just send the land documents to my email before evening,” ya faɗa cikin sanyin murya yana ci gaba da tukin.
Ƙwayar idonsa ko motsi bata yi ba yayin da yake magana. Shi kansa nutsuwar sa tana ba mutane tsoro, yayin da yake jefar ƴan mata da suka mato akansa cikin shaukin kaunarsa.
A zuciyarsa kuwa: Wani irin dadaddan yanayi yakeji mara misaltawa daga ƙarshe dai burinsa yana dab da cika. Yana son ya sayi wani katafaren fili a ƙauyen Yelwa domin wani project da bai sanar da kowa ba. Ya dai bar ma zuciyarsa sani akan dalilinsa na son siyan filin da yin project a ƙauyen na Yelwa.
Sai dai bai san cewa zuwansa ƙauyen zai haɗa shi da wata annoba mai suna…
Tanƙoki. Ta gefe guda kuma dama hakan yana rubuce ne a kundin ƙaddararsu su duka daga shi har itan.

A dai-dai wannan lokacin ne kuma…

“Tsaya nace miki! Ke yar akuya mara mutunci, kin rantse yau ma sai kin wahalar dani koooo!”
Wata budurwa ce ta fito daga wata yar ƙaramar hanya da gudu tana bin wata yar akuya fara tas! A hannunta kuma soso ne da roba cike da ruwa.
“Na rantse yau sai na yi miki wanka ko kina so ko baki so ba!”
Ita ce dai shahararriyar yarinyar ƙauyen Yelwa da ta addabi kowa da tantiranci da rashin ji wato dai Tanƙoki tamu ta gargajiya.
Ba don an haife ta da sunan na Tanƙoki ya kasance ta amsa sunan ba, sai dai mutanen ƙauyen sun daina kiranta da sunanta na asali ne saboda bala’in surutu da jan magana irin nata da kuma rashin barin ko ta kwana.
Ga ta da shegen surutu domin idan Tanƙoki ta fara magana. To gwara rediyo domin shi ana kashewa zai yi tsitt amma ban da bakin Tanƙoki.
Sanye take da doguwar rigar atamfa da ta ɗan ɗaure saitin ƙugunta da mayafi saboda gudu, ƙafarta babu takalmi, gashin kanta kuma a ɗaure yake kuma a buɗe yana ta wani reto abin dai ba tsari, amma ita a la dole yar Gayu ce kuma ta yi kalar yadda yan indiya suke yi ne da yake kuma Allah ya azurtata da gashin abin ba'a magana shi ya sa take zuba feleƙe da firirita idan yan abin nata suka matso.
Akuya kuwa sai gudu take kamar ta san abin da ke shirin samunta.
“Ke dawo nan! Wallahi baki isa ki raina ni ba!”
Da gudu ta ruga zuwa tsakiyar hanya…
A dai-dai lokacin kuma motar ARFAAZ ta ƙaraso a guje!
“Damn it!” ARFAAZ ya faɗa yana taka birki da ƙarfi.
Ƙiiiiiiiiii!
Motar ta yi wani irin kara har kura ta tashi.
Tanƙoki kuwa saboda razana sai ta zube zaune a ƙasa, soson hannunta ya tashi sama ya faɗi kai tsaye bai yi masauki a ko'ina ba sai a kan motar ARFAAZ.
Shiru ne ya ratsa wurin yadda kasan an saka remote an dakatar da komai dake wakana a wannan daƙiƙun.
Mutanen gefen hanya suka tsaya cak.
ARFAAZ ya sauke wayar hannunsa a hankali sannan ya fito daga motar.
Salon tsayuwarsa kaɗai ta saka wasu yan mata biyu da ke gefe haɗiyar yawu a zuciyoyinsu suna ina ma ina ma.. ina ma wannan hadadde ya zama nasu.
“Subhanallah… kamar ɗan film,” ɗaya ta faɗa. Yayin da ɗayar ta ce. “Kamar su ɗaya da jaruman Korea.”
ARFAAZ ya kalli soson da ya baci jikin motarsa sannan ya maida idonsa kan Tanƙoki dake zaune tana kallonsa kamar mai shirin fashewa da kuka.
“What is wrong with you?” ya faɗa cikin turanci cike da ɓacin rai.
Tanƙoki ta lumshe ido.
“Eh?”
Ta faɗa cike da ƙauyanci.
ARFAAZ ya dafe goshinsa.
“I said, are you blind?!”
Tanƙoki ta miƙe tsaye tana kakkaɓe ƙura.
“To ni kuma nace lafiya? Kai ne zaka kashe mutane saboda iskancin mota!”
Ta faɗa cikin son nuna laifinsa ne.
ARFAAZ ya ɗan ɗaga gira.
“What?”
“Kar ka min wannan wat ɗin naku na yan birni! Ni ba turancinka nake ji ba!”
Wani saurayi dake gefe ya fara dariya.
“Ɗan gayun birni da Tanƙokin Yelwa… an haɗu!”
ARFAAZ ya kalli saurayin da wani irin kallon ya sa ya yi hanzari ya haɗiye dariyarsa.
Sai ya maida kallonsa kan Tanƙoki wacce yanzu ta ɗora hannu a ƙugu.
“Ka wani fito kamar shugaban ƙasa! Ai ko ka fi ƙarfin mota ba ka fi ƙarfin mutuwa ba!”
ARFAAZ ya yi shiru yana kallonta.
A rayuwarsa… Babu wanda ya taɓa masa magana kai tsaye irin haka, sai yau da ya haɗu da Tanƙoki.
Shi kansa ya rasa dalilin da yasa yake jin yarinyar na bashi mamaki daga haduwar farko.
Tanƙoki kuwa ta ci gaba.
“Kuma ka tsaya kana min turanci kamar ɗan BBC. Ni Hausa nake ji malam!”
Sai ta nuna motar.
“Wannan motar taka kuma kamar kwado take ƙara.”
Nan take wasu yara dake gefe suka fashe da dariya.
Fuskar ARFAAZ ta ɗan canza.
A karo na farko cikin shekaru… Yana jin kamar ya rasa abin cewa.
Sai dai kafin ya sama zarafin magana...
Nan take Akuyar nan ta dawo ta fara lasar jikin motar!
“Wayyooo! Yar akuyata Bebi!” Tanƙoki ta kwalla ihu tana bin akuyar.
ARFAAZ ya tsaya cak yana kallon yadda take gudu tana jan rigarta tana masifa.

A hankali tare da ya shirya ba…
Sai murmushi ya subuce masa karon farko cikin kwanaki masu yawa.
Amma murmushin ya ɓace nan take da ya lura mutane na kallonsa.
Ya gyara fuska ya shiga motarsa.
Sai dai kafin ya rufe ƙofar…
Sai yaji muryar Tanƙoki daga baya:
“Kai mai motar kwado! Idan zaka sake zuwa kauyenmu ka rage gudu!”
ARFAAZ ya lumshe ido yana girgiza kai.
“This village is insane…”
Bai san cewa ba… Wannan yarinyar mai suna Tanƙoki zata rikita masa rayuwa fiye da yadda yake zato ba…




Washegari da safe…
Kamar yadda yake a al'adar Ƙauye haka ma kauyen Yelwa ya tashi cikin hayaniya kala-kala ta Mutane da dabbobi musamman kaji da carar zakaru, ƙamshin kunun dawa daga gidaje. Mata na zirga-zirga domin neman abin rufawa kai asiri yayin da yara yan dagwai dagwai ke gudu babu takalmi, wasun su ma ba riga sai iya wando kawai, samari kuma suna zaune a ƙarƙashin rumfar mai shayi suna ta hirar duniya.
Amma abin da ya fi ɗaukar hankalin mutane yau shi ne, raɗe raɗin da aka wayi gari da shi na;
“An ce ɗan birnin jiya bai tafi ba fa!”
Mata da yan mata sai zumud'i suke wai had'ad'd'en ɗan Birni mai kud'i ga kyau ya kwana a garin su. Wai yana gidan shugaban ƙauyen.
“Kaiii! To yau Tanƙoki zata sake faɗa masa magana kenan!” cewar wani saurayi wanda dramar jiya tsakanin Tanƙoki da ARFAAZ ya kasance ya faru ne a gabansa.
A gidan shugaban ƙauye kuwa…
ARFAAZ ne zaune cikin wata baƙar kujera irin plastic ɗin nan yana duba wasu files a laptop ɗinsa.
Shugaban ƙauyen, Alhaji Sule Yelwa, ya gyara zama yana kallon sa cike da girmamawa.
“To ranka ya daɗe… wannan filin da kake son siya yana bayan gonakinmu ne.”
ARFAAZ ya ɗaga kai kaɗan.
“Good. I want everything settled today.”
Alhaji Sule dai bai gama fahimtar rabin turancin ba, sai dai ya gyada kai kamar ya gane 😂
“Eh… eh… hakane.”
Ya faɗa yana zazzare kwalan-kwalan idonsa, shi ala dole yaji turancin da ARFAAZ ya yi.
Daga can waje kuwa… Tanƙoki ce yau ma ta taho a guje tana bin yar akuyar ta fadi take.
“Wallahi tallahi Bebi idan kika sake cin wainar Inna Abu sai na sayar dake!”

Kafin kowa ya ankara sai ta kutsa kai cikin gidan shugaban ƙauyen rike da yar akuyar da ta sama dama ta cafke ta.
Da shigowarta ta tsaya cak.
ARFAAZ ma ya ɗago kai.
Idanunsu suka haɗu.
Tanƙoki ta taɓe baki.
“Kai mai motar kwado…” ta faɗa tana washe baki kamar wacce ta faɗa abin arziki.
ARFAAZ ya runtse ido kamar wanda kansa ke ciwo.
“You again…”
Tanƙoki ta juya wajen shugaban ƙauye.
“Barka dai Baba Sule. In tambayi matar ka ko zata bani gishiri?”
Bata jira amsar shugaban ƙauye ba kuma sai ta sake kallon ARFAAZ daga sama har ƙasa.
“Aiiii Ɗan birni, zaka kaini Abuja?”
ARFAAZ ya rufe laptop ɗinsa a hankali.
“Listen… can you please stay out of my business for once?”
Tanƙoki ta tsaya tana kallonsa.
Sai ta juya wajen shugaban ƙauye.
“Baba Sule me yace?”
Ta tambaya.
Shugaban ƙauyen ya yi gyaran murya.
“Hmm… wai yana cewa kina da kuzari kuma ki dena kallonsa saboda kina saka masa ciwon kai.”
ARFAAZ ya juya da sauri jin wannan uwar ƙarya da Babban mutum kamar shugaban ƙauye ya shatato.
“That’s not what I said!”
Ya faɗa yana kallonsu su duka.
Tanƙoki ta ɗaga gira.
“Toh ai ka ga ya fi kyau haka.”
Wani murmushi ya kusa kubucewa shugaban ƙauyen amma ya danne domin a ganin sa ya burge tun da har ya fassara turanci kuma Tanƙoki ta yarda.
Tanƙoki kuwa ta ƙarasa cikin ɗakin tana cigaba da magana kamar ba komai.
“Kuma malam ka rage wannan fuskar taka kamar wanda aka cirewa network. Tun jiya kana haɗe rai.”
ARFAAZ ya zuba mata ido kawai.
A zuciyarsa yana tambayar kansa: Yaushe rabon da wata mace tayi masa magana babu tsoro haka?
Yawancin mutane idan sun gan shi sai sun shiga taitayinsu.
Amma wannan yarinyar? Ko kaɗan bata da tsoro ko shakku a lamarinta.
Sai kawai ya miƙe tsaye.
“I need fresh air.”
Yana faɗa wucewa ta kusa da Tanƙoki da ta fito daga d'akin matar shugaban ƙauye Tanƙoki ta ja baya tana kuma buɗe hanci tana shakar kamshin turarensa.
“Kaiii Baba Sule! Wannan mutumin ma yana ƙamshi kamar sabuwar mota!”
Nan take wani yaro daga cikin yaran Baba Sule dake ƙofar ɗakin ya fashe da dariya.
ARFAAZ ya tsaya cak.
Slowly ya juya ya kalleta.
Tanƙoki ma ta haɗe hannu tana kallonsa ba tsoro.
Sai ya ce cikin sanyin murya:
“You talk too much.”
Tanƙoki ta gyara tsayuwa.
“Toh kai kuma baka magana ko kaɗan. Allah ya haɗa mana iri biyu kenan.”
Wani irin shiru ne ya ɗan ratsa wajen…
Sai shugaban ƙauye ya kwashe da dariya.
Ko ARFAAZ sai da ya saki ƙaramin murmushi kafin ya fice.
Tanƙoki ta zaro ido.
“Kaiii! Ashe miskilin nan yana iya murmushi?”
Bayan wasu mintuna…
ARFAAZ na tsaye kusa da motarsa yana waya.
“Yes, transfer the money before evening.”
Yana cikin magana kenan sai ya ji wani sauti daga bayansa ana magana cikin karad'i.
“Ke Bebi tsaya!”
Da gudu Tanƙoki ta sake biyo akuyarta.
Sai dai wannan karon…
Akuya ta wuce ta ƙarƙashin motar ARFAAZ!
Tanƙoki bata tsaya ba ta rarrafa ƙarƙashin motar tana ƙoƙarin kamo ta.
ARFAAZ ya cire wayar daga kunnensa yana kallonta cikin mamaki.
“What are you doing?!”
Jin maganarsa ya sa Tanƙoki tama manta karkashin mota ta shiga, sai da ta yi yunkurin ɗagowa ai kuwa kanta ya bugi ƙarƙashin motar.
“Wayyo Inna Abu!”
Ta faɗa tana ɓare baki
ARFAAZ ya dafe goshinsa.
“This girl is impossible…”
Tanƙoki ta fito daga ƙarƙashin motar fuska cike da ƙurar ƙasa.
Sai ta miƙe tana huci.
“Na rantse akuyar nan zata kashe ni wata rana idan ban ɗauki mataki ba.”
Sai idanunta suka sauka kan takalmin ARFAAZ mai tsada wanda ya ɗan samu ƙura.
Ta yi sauri ta share ƙurar da hannunta.
“Kayi haƙuri kada motarka ta yi kuka.”
Kuji Tanƙoki fa jama'a ban da abin ta ta ina ne mota ke kuka?
ARFAAZ ya kalleta.
A karo na farko… Sai ya yi dariya sosai har sautin dariyar ya fito fili. Domin har ga Allah idan ya ce yarinyar bata bashi dariya to kuwa ya yi ƙarya.
Tanƙoki ta tsaya cak tana kallonsa.
“Subhanallah…” ta faɗa a hankali.
ARFAAZ ya ɗan gyara murya yana komawa serious.
Kamar bashi ne ya gama dariya ba.
Tanƙoki ta nuna shi da yatsa.
“ka yi dariya! Wallahi ka yi dariya!” 😂
ARFAAZ ya buɗe motarsa da sauri.
“I have to leave.”
Ya faɗa yana kokarin shiga motar.
“Eh toh ka tafi mana mai motar kwado ce motar, taka kuma ai kayi dariya naga dariyarka”
Kafin ya shiga motar sai ta ƙara da faɗin.
“Kuma idan zaka yi murmushi ka riƙa yi mana sosai. Fuskar ka zata fi kyau!”
ARFAAZ ya tsaya na ɗan daƙiƙa…
Ba tare da ya juya ba.
Sai kawai ya shiga motar ya tafi.
Tanƙoki kuwa ta tsaya tana kallon motar har ta ɓace ma ganin idonta.
Sai ta ɗan taɓe baki.
“Miskili… amma yana da kyau fa, aradu wannan a 'yan birnin ma shi ɗin na daban ne.”
Ta yi maganar tana juyawa da sauri jin muryar Lawwali yana kwala ma ta kira.
*✦ TANƘOKIN ARFAAZ ✦*
When two souls collide…
the result becomes laughter,
tears,
jealousy,
and uncontrollable love.
A Hausa Novel With Full Cinematic Drama & Comedy

*_BY NAINARH KD ✍️❤️_*

CHAPTER 2
“Tanƙoki wai kizo Inna Abu tana nemanki.”
Ya faɗa daga nesa ba tare da ya yarda ya ƙari sa kusa da ita ba, domin ya san hali tsaf zata iya mangareshi.
“Har ankai ma ta gulma na ke nan daga fita na ni da bana abin arziki.”
Cewar Tanƙoki tana wani harara harare.
Shi dai Lawwali yana daga gefe yana raba ido bai ce komai ba.
“To ai sai kazo ka tayani neman Yar akuyata Bebi, kayi da ƙaton kanka a wurin.”
Jiki na rawa ya ƙari sa suka shiga neman yar akuya Bebi domin tuni ta yi gaba lokacin da Tanƙoki ta tsaya magana da ARFAAZ.
Da kyar suka ganta can bayan gari ta haɗe da sauran awakai ai kuwa lokacin da suka ganta sai da Tanƙoki ta haɗa ma ta da rankwashi kamar wata mutum tana masifa akan ta bata wahala.
“So kike na siyar dake kwanan nan tun da na lura wahala zaki ke bani. Kai Lawwali maza juyo bayanka ka goyamin yar akuyata Bebi domin ta gaji ba zata iya tafiya ba.”
Wani irin kwalalo ido Lawwali ya yi cikinsa na kartawa da jin abin da Tanƙoki ta faɗa gashi sanin kansa ne ba'ayi ma ta musu, hakan ya sa yana ji yana gani ba yadda ya iya, haka ya juya bayansa Tanƙoki ta saka masa yar akuyar a baya.
“Yawwa Lawwali na ɗan albarka maza tafi a hankali kar Bebi ta fado ko ma dai na saka mayafi na ne na daure ya zama ka goyata da kyau.”
Ai cikin hanzari Lawwali ya amsa da “A'a a'a Tanƙoki ba sai an daure ba.”
Tanƙoki ta yi dariya kawai suka ci gaba da tafiya, duk wanda suka haɗu da shi kallo ɗaya zai yi ma Lawwali yaji tausayinsa gefe guda kuma matuƙar ƙoƙari zai yi ba tare da dariya ta subuce masa ba, domin yadda Tanƙoki ta tilasta ma Lawwali goyon yar akuya Bebi da yadda Lawwali yake tafiya a wani shagiɗe ga kuma akuyar sai tsala ihu take amma ita kam Tanƙoki ba ruwanta hankali kwance take tafe a haka har suka haɗu da wani yaron makwaftan gidansu Tanƙoki yana tafe da ƙosai a fallasa yana talla, ai kuwa Tanƙoki ta shammaceshi ta kwace robar ƙosan, tana faɗin “da wa Allah ya haɗa ni?...”
Tuni yaron ya fara kuka faɗi yake.
“Ni ki bani robar ƙosai na na tafi.”
Rankwashi ta zuba masa tana faɗin.
“ba zan bayar ba ɗin ba kai ne ka tsokaneni ba rannan ko kayi tunanin na manta ne? ai kuwa tun da Allah ya haɗa mu yau akan ƙosan nan zan fanshe.”
Ta faɗa tana ɗibo ƙosan guda hudu tashi guda ta lunƙuma a baki, sannan ta kara ɗibowa tsabar neman magana irin nata sai Bama yar akuyarta Bebi ta yi shi kuwa yaron tuni ya fara birgima yana rokon ta bashi fallasar ƙosansa amma Tanƙoki ta yi kunnen uwar shegu da shi bata bashi ba har sai da ta ci ya isheta dan neman magana irin nata ma sai ta kira wasu almajirai ta basu ragowar ƙosan duka sadaka sannan ta kakkaɓe hannunta tana goge baki ta yi gaba Lawwali yabi bayanta goye da yar akuya Bebi.

Lokacin da suka isa anguwansu tun da daga farkon layi ganin yanayin kallon da mutanen anguwan suke bin ta da shi ya sa ta fahimci cewa lallai akwai wata a ƙasa. Ai kuwa suna shiga gidan da taron jama'a suka fara cin karo yayin da Inna Abu take tsaye tsakiyarsu tana surfa masifa ai kuwa juyawar da zatayi taga Tanƙoki da sauri ta ƙari sa gareta fad'i take.
“Sannu Tanƙoki ta yar albarka maza wanke hannu kije ga koko da kosai can na aje miki da zafinsu na san yunwa kikeji kin fita bakici komai ba, Allah dai ya suburbuda miki albarka yar nan domin yadda kike kula da wannan yar akuyar marainiyar Allah kamar yadda kema kike marainiya ba uwa ba uba, abin yana min dad'i amma su mutane da kullum basu da buri da ya wuce suyi miki sharri shi ne daga ɗan fitan nan da kika yi har wadan nan gayya gudan sun zo fadi suke wai duk ɓarna kikayi musu saboda babu Allah a zuciyarsu kwata-kwata mintina nawa ne da fitar naki gaba daya amma suke batun duk yawan nan nasu wai kece kikayi musu ɓar na.”
Turo baki Tanƙoki ta yi tana wani harara harare ta juya tanayi musu kallo ɗaya bayan ɗaya kuma duk wanda ta kalla cikinsu tana tuna irin ɓarnar da ta yi masa a safiyar nan.
Ta farkon wata mace tsaye da ɗanta wanda ta aike shi karbo niƙe ne kuma a hanyarsa ta dawowa yaci karo da Tanƙoki da take bin yar akuyarta Bebi zata kamota ai kuwa kafin ya kauce ma ta tuni tayi ciki dashi daga shi har niƙan da ya karɓo basuyi masauki a ko'ina ba sai a cikin kwatami, shi ne dalilin da ya sa mahaifiyar tasa ta kamosa suka zo domin ta ce ba zata yarda ba sai an biyata.
Yayin da na biyun kuma ya kasance wani saurayi ne, shi kuma yana zaune a teburin mai shayi an miƙa masa haɗin kauri da ya biya aka yi masa ke nan ya ɗa ga kofin shayin zai kurɓa a daidai nan akuyar Tanƙoki da ta taho a guje ba tare da ya ankara ba ta yi ciki da kofin shayin hannunsa yayin da biredin dake ɗayan hannun nasa ya yi tsalle bai dire ko'ina ba sai a cikin taɓo kuma ƙarin abin haushin a wurinsa shi ne kota kansa Tanƙoki bata bi ba ta yi gaba a ƙoƙarin ta na kamo akuyar tamkar ma batasan ɓarnar da ta yi masa ba shi ne ya ɗauko ƙafa shima yazo domin a biya shi asarar da akuyar Tanƙoki ta saka ya yi domin cewa ya yi ba zai yarda ba sai an biya shi.
Ita kuwa ta ukun yarinya ce sanye da kayan boko sai dai sun ɓaci da taɓo ita ma ta sama rabonta ne a lokacin da take kokarin tafiya makaranta ita kuma Tanƙoki tana bin yar akuyarta Bebi.
“Ku yanzu tsakaninku da Allah nan zuwa kukayi a biyaku sai kace ce muku aka yi da gangar nayi muku ɓarnar? ai kuwa naga mai biyanku nidai aradu ba ruwana tun da ba da gangar nayi ba ah to.”
Tanƙoki ta faɗa buguzum buguzum ta wuce cikin ɗaka.
“Ai wallahi ba'a isa ba yau ko da me ake taƙama sai an biyani ɓarnar da aka yi min ko kuma na kai ƙara wurin hukuma subi min hakkina ehe.”
Cewar wannan saurayi a kufule.
Yayin da a fusace Inna Abu ta ce. “In kaso kaje wurin shugaban kasa ma bayan hukuma tun da kai baka san ƙaddara ba ai cewa ta yi bada gangar ta yi ba tsautsayi ne saboda haka in ma zaku ɗauki na annabawa to in kuma ba zaku yi hakuri ba ku kuka sani...”
Kafin Inna Abu ta rufe baki sai ga sallamar Sahura uwar ɗan da Tanƙoki ta cinye wa ƙosai kuma ta yi sadaka da sauran.
“Tana ina Tanƙokin ai wallahi yau sai na cire miki duk wannan karyar fitsarar da kikeji da shi tun da har kika taɓoni saboda baki da mutunci shi ne zaki taremin ɗa ki ci ƙosan bayan kin san na siyarwa ne sannan dan rashin mutunci kuma ki yi sadaka da sauran sai kace da kudin ubanki na haɗa nayi jarin...”
Maganar matar ne ya katse sakamakon tsawar da Inna Abu ta yi ma ta tana faɗin.
“Ke Larai kalleni da kyau, kiyi duk rashin mutuncin da zakiyi saisa-saisa amma kada ki kuskura kice zaki taɓo iyayen Tanƙoki a ciki domin ba zan lamunta ba.”
Shiru duk suka yi jin yadda Inna Abu take maganar rai a ɓace yayin da maganar Tanƙoki daga ɗaki ya katse shirun da ya ratsa wurin.
“Larai Baabar Masa'udu ki iya bakinki kuma ai baki san abin da Masa'udun ya yi min ba, tsokanata ya yi kuma ni ba sa'ar wasan sa bace shi ya sa naci ƙosan dan na nuna masa ba'a min raini a zauna kalau domin komai daran daɗewa sai na dauki mataki, sannan kuma nayi sadaka da ƙosan ne saboda na lura baki son yin sadaka bayan kuma sadaka maganin masifa da bala'i ne shi ya sa nayi miki sadakar domin Ubangiji ya dubeki ya kuma buɗe miki kofofin rahamarsa.”
Tanƙoki ta ƙare maganar hankali kwance tana sakin gyatsa tare da cusa sauran ƙosan hannunta a baki.
Rai a ɓace Larai ta nufi Dakin da Tanƙokin ke ciki tana faman masifa da da kumbar bakin ai ba ita ta aike

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment