You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ta yi ma ta sadaka da kayan sana'a ba kuma sai ta jibgeta sannan dole a biyata.
Ai da gudu Inna Abu kamar ba tsohuwa ba ta ƙari sa ga Kofar ɗakin da Larai ke kokarin shiga ta kakkare ta yi bake-bake a wurin fadi take.
“Larai idan kin ga kin shiga dakin nan ki tabbata fin ƙarfina kikayi domin da rai na da lafiya ta ba zan tsaya ina ji ina gani aci zalin yarinya karama Kamar Tanƙoki ba marainiyar Allah.”
Gwalo Tanƙoki dake daga dakin ta shiga yi ma Larai cike da shaƙiyanci ai kuwa hakan ne ya ƙara fusata Larai har takeji in ba samu ta yi ta murƙushe Tanƙoki ta jibga ba tabbas ba zata huce daga takaicin da ta cusa ma ta ba.
“Inna Abu ai da kin barta ma ta shigo ɗin domin ni din ai ba kanwar lasa bace ba zan tsaya ta dakeni ba sai dai mu daki juna ehe Tanƙoki fa nake.”
Tanƙoki ta faɗa tana wani yarfe hannu ita a la dole ga mai ƙarfi.
A zuciyarta kuwa tsoro ne fal musamman idan ta ɗaga ido taga sifar Larai irin jibga jibgan matan nan ne, ta san ko mari ta yi ma ta da wancan basamuden hannun nata da wuya takai labari bare kuma ace ta zaune a ruwan cikinta ai kuwa sai dai a dauki gawarta, ta raya hakan a ranta, amma ba shi ne ya hanata ƙara fusata Larai ba tana faɗin ai dama Inna Abu bata kare ba yayin da Larai take daɗa fusata kuma tayi aniyar sai ta koyama Tanƙoki hankali.
Ana cikin haka sai ga Kawu Tukur mahaifin Lawwali, wanda ganin abin da yake faruwa ne ya sa da gudu Lawwali ya ruga ya sanar da shi, dama gidajen nasu ba nisa ne tsakani ba katanga ne kawai ta raba, shi ne ya taho kuma ya ganewa idonsa daga ƙarshe dai shi ne ya biya mutanen duk ɓarnar da Tanƙoki ta yi tare da basu hakuri ita kam Larai da kyar ma ta hakura amma duk da hakan taci alwashin koyama Tanƙoki hankali domin ta raya a ranta matuƙar kere na yawo zabo na yawo to fa tabbas wata rana za'a haɗe, ma'ana dai shi ne muddin ta haɗu da Tanƙoki ko'a ina ne tabbas ba zata haƙura ba sai ta ɗauki mataki akanta.

ARFAAZ
Tun bayan haɗuwarsa da Tanƙoki…
ARFAAZ ya fara jin ƙauyen Yelwa daban, duk da kasancewar haɗu War tasu sau biyu ne amma yarinyar ta shiga ransa da wannan tsiwar nata abin har mamaki yake bashi.
Abin da bai taɓa kula da shi ba a baya cikin wannan ƙauye na Yelwa yanzu sai ya tsinci kansa yana lura da shi: ƙamshin ƙasa bayan an yayyafa ruwa… hayaniyar yara masu wasa… da kuma wata yarinya mai bala’in surutu da bata san lokacin yin shiru ba wato dai Tanƙoki tamu ta gargajiya 😭😂
Sai dai shi kansa baya son yarda da hakan.

Misalin ƙarfe tara zuwa tara da rabi na safiyar washegari.
ARFAAZ na tsaye kusa da filin da yake shirin siya, sanye cikin wata ash-colored shirt da baƙar sunglass. A hannunsa kuma waya ce yana duba emails.
Ma’aikatan da ya zo da su daga Abuja na zagaye suna aunawa da duba wajen da yake filin fili ne babba mai mashahurin girma.
“This place is perfect,” ya faɗa a taƙaice.
Daya daga cikin ma’aikatan ya ce, “Sir, akwai rijiyar ruwa a baya.”
ARFAAZ ya gyada kai kawai.
Sai dai kafin ya sake magana ya jiyo wani sauti cikin karaɗi.
“Wayyoooo! Ku tsaya!”
Ji ya yi kamar ya gane muryar ko ya san muryar already hakan ya sa ARFAAZ ya runtse ido a hankali.
“Not again…”
Ya faɗa akan labbansa.
Da gudu Tanƙoki ta ƙaraso ɗauke da wata kwando a kai. Kallonta kawai ya isa ya saka mutum dariya.
Tana sanye da doguwar riga mai zanen flowers, takalmi guda ɗaya a ƙafa ɗaya ɗayan kuma babu ma sam a ƙafar kuma bata damu ba haka take tafiyar Bama tafiya za'a ce ba sai dai gudu.
Wani ma’aikaci ya tambaya a hankali “Sir… who is she?”
ARFAAZ ya kalli sama tare da furta wa a hankali.
“Problem.”
Tanƙoki ta iso tana haki.
“Toh kai mai motar kwado! Ashe nan kake?”
Wani ma’aikacin ya kasa riƙe dariya. Musamman ganin yadda ta yi maganar tana washe baki ga fuskar nan tasha kwalliya irin na ƙauye.
ARFAAZ ya harare shi.
Nan take ya yi shiru.
Tanƙoki ta sauke kwandon kanta tana kallon mutanen.
“Kaiii… dukka wadan nan ma'aikatan ka ne?”
“Yes.”
Ya bata amsa kamar an yi masa dole.
Ta zaro ido.
“Toh kai ɗin nan kana da kuɗi sosai kenan.”
ARFAAZ bai tanka ma ta ba.
Sai ta matsa kusa da shi tana leƙen wayarsa.
“Kuma kullum cikin waya kake kamar ɗan rediyo.”
ARFAAZ ya ja wayar baya.
“Personal space.”
Ya faɗa cikin taushi ba tare da ya kalleta ba.
Tanƙoki ta ɗan ja baya.
“Eh?”
Ta tambaya cike da ƙauyanci.
Daya daga cikin ma’aikatan ya yi murmushi.
“Yana nufin ki rage matsowa kusa.”
Tanƙoki ta taɓe baki.
“Toh ai ya faɗa a Hausa mana. Kullum sai turanci kamar ana gasar BBC.”
Ma’aikatan suka fara dariya a hankali kuma a ɓoye gudun kar Boss ɗin su ARFAAZ ya ankara.
ARFAAZ ya ɗan dafe goshinsa.
A zuciyarsa ya ce: Wai me yasa duk inda yarinyar nan ta shiga sai ta juya wajen ne zuwa comedy stage?
Bayan ɗan lokaci…
Tanƙoki ta fara zagaye wajen tana kallon yanayin aikin da ma'aikatan keyi.
“Nan zaka gina gida ne?”
“Yes.”
Ya bata amsa a taƙaice ba kuma don gida zai gina a wurin ba kawai dai a amsa ma ta ne.
“Toh kai kaɗai zaka zauna a irin wannan katon wajen?” 😭
“No.”
Sai ta haɗe hannu.
“Hmmmm… tare da matarka kenan.”
ARFAAZ ya ɗago kai ya kalleta.
“What?”
Tanƙoki ta gyara tsayuwa kamar jami’in bincike.
“Kar ka min what ɗin nan. Ni dai naga alamar kana da mata.”
ARFAAZ ya sauke numfashi.
“I’m not married.”
Tanƙoki ta zaro ido sosai.
“Kaiii! Da wannan kyawun naka baka da mata?”
Ta faɗa duk da bata wani fahimci abin da ya faɗa sosai ba.
Wani worker ya juya gefe yana dariya.
ARFAAZ ya harare shi.
Sai worker ɗin ya yi kamar yana aikin auna wurin da yake.
Tanƙoki kuwa bata tsaya ba, ta ci gaba.
“Toh ko kana da budurwa?”
“No.”
“Toh me kake jira? Ranar lahira? Idan baka da aure ba kuma budurwa zaman me kake yi a duniyar” 😂
Hankali kwance fa take duk wannan surutun nata.
ARFAAZ ya kalleta na wasu daƙiƙu.
Sai kawai ya girgiza kai.
“You ask too many questions.”
Tanƙoki ta ɗaga kafaɗa.
“Toh kai kuma baka dariya ko sakin fuska, Mutum zai yi tunanin baka da emotions.”
Ta faɗa kalmar emotions ɗin da ta saba ji daga bakin Kawu Tukur.
ARFAAZ ya ɗan yi murmushi kaɗan.
Wannan karon kuwa Tanƙoki ta gani, tabbas taga murmushin da ya yi.
Da sauri ta nuna shi da yatsa.
“Naga nii! Ka sake murmushi!”
Nan take workers suka fara kallon juna cikin mamaki. Tun da suka san boss ɗinsu… Murmusawa idan ya yi ma sai an yi mi ruwa da ƙanƙara a cewarsu.
ARFAAZ ya gyara fuska nan take.
“I didn’t.”
Ya faɗa cikin basarwa.
“Kaiii har ƙarya zaka yi mana kana Babba da kai?” 😂
Tanƙoki ta faɗa tana kallonsa baki buɗe, sai ya rasa ma abin cewa gaba d'aya.
Ana cikin haka sai wata budurwa yar ƙauye kusa da Yelwa mai suna Laila ta ƙaraso.
Tun daga nesa idanunta ke kan ARFAAZ.
“Sannu Ɗan birni…” ta faɗa cikin sanyin murya tana gyara mayafinta.
ARFAAZ ya ɗan gyada kai kawai.
Tanƙoki ta ɗaga gira tana kallon su.
Laila ta matsa kusa da ARFAAZ.
“An ce kai ɗan kasuwa ne daga Abuja…”
“Yes.”
“Ina maka maraba da zuwa ƙauyenmu.”
Tanƙoki ta zaro ido jin abin da ta ce bayan kuma tasan ba'a garin take ba, sai dai kafin ta yi magana taji muryarsa a tak'aice ya amsa da:
“Thank you.”
Shiru ne ya ɗan ratsa wurin.
Laila ta kasa ƙara magana saboda yadda ARFAAZ yake haɗe fuska sai ya yi ma ta kwarjini.
Sai Tanƙoki ta ƙarasa kusa da ita.
“Ki barshi haka nan da wannan kallon kamar zaki cinye shi ga kuma surutunki da wanne zaiji?. Idan ya yi magana sosai a rana gajiya yakeyi har ciwon kai yake saka masa.”
Workers suka sake fashewa da dariya jin karyar da Tanƙoki ta zabgo.
Har ARFAAZ sai da ya juya gefe saboda kada su ga yana son yin dariya. Domin ba kaɗan ba yarinyar ta bashi dariya hakan ya sa ya murmusa.
Laila kuwa ta ji kunya sai kawai ta juya ta tafi, domin ta san halin Tanƙoki idan ba tafiya ta yi ba haka zata ci gaba da kunyatata.
Tanƙoki ta bita da kallo sannan ta ce:
“Toh gaskiya miskilancinka abin tsoro ne.”
ARFAAZ ya kalleta.
“But you’re not scared.”
Tanƙoki ta taɓe baki.
“Ni? Tsoron me? Kai ai mutum ne ba aljani ba.”
Sai ta ɗan tsaya tana kallonsa daga sama har ƙasa.
“Kodayake… idan ka haɗe rai sosai kana ɗan kama da aljani kaɗan.” 😭😂
Wannan karon kam hatta ARFAAZ ya kasa riƙewa, sai da ya saki dariya sosai.
Workers suka tsaya cak suna kallonsa kamar sun ga mu’ujiza.
Tanƙoki ma ta zaro ido.
“Subhanallah… Ashe haƙoranka suna nan, ai nayi tunanin sun zubene hakan ya sa bakason yin dariya?” 😂😂😂
ARFAAZ ya girgiza kai yana kallonta.
A zuciyarsa yana faɗin abu ɗaya ne kawai:
Wannan yarinyar zata wahalar dani da alama… ❤️


Washegari.
Yau tun safe ARFAAZ ya iso wajen aikin filinsa.
Workers na ta kai kayan aiki suna gyare-gyare, amma shi kuwa tun shigowarsa yake jin wajen ya yi masa shiru fiye da yadda ya saba.
Ya cire sunglasses ɗinsa yana kallon wajen.
Sai wani daga cikin worker ɗin mai suna Jabir ya ƙaraso kusa da shi.
“Good morning sir.”
ARFAAZ ya gyada kai.
“Morning.”
Sai shiru ya biyo baya.
ARFAAZ ya ɗan kalli gefen hanya.
Babu hayaniyar Tanƙoki. Babu na akuyarta, sai yaji gaba daya babu nishadi. Abin yana bashi mamaki musamman da ya tuna da yadda jiya da dare da ya tuna da wautarta da kuma shegen surutu irin nata kamar an kunna rediyo sai ya tsinci kansa da sakin murmushi yarinyar kamar mai shafar jinnu sam bata gajiya.

Sai ya gyara tsayuwa kamar ba komai.
“Where’s that girl?”
Ya tsinci kalaman sun fito daga bakinsa ba tare da ya shirya ma hakan ba.
Jabir ya ɗan dubesa.
“Which girl sir?”
Ya tambaya domin sai yaji ma bai gane yarinyar da yake nufi ba.
ARFAAZ ya sa hannu a aljihu. Like nothing.
“The noisy one.”
Ya faɗa yana kallon sama kamar an ce masa ta nan ne zai hangota.
Jabir ya riƙe dariyar dake son kwace masa.
“Ohh Tanƙoki?”
Ya tambaya yana kallonsa
ARFAAZ bai ce komai ba.
Ganin hakan ya sa Jabir ɗin ci gaba da faɗin.
“Tun safe ban ganta ba sir.”
ARFAAZ ya gyada kai kawai ba tare da ya sake cewa komai ba.
Amma a zuciyarsa yana jin wani irin rashin jin dadi da sam bai gane dalilin hakan ba.
Daga can wani bangare na cikin ƙauyen Yelwa kuwa Tannƙoki ce zaune ƙarƙashin bishiya tare da ƙawayenta guda biyu, Lantana da Bebi.
A gabanta wani ɗan ƙaramin littafi ne.
Lantana ta zaro ido.
“Ke Tanƙoki tun yaushe kika fara karatu ban sani ba?”
Tanƙoki ta gyara zama cikin isa tana wani shan kamshi ta ce.
“Turanci nake koyon yi.”
Kawayen nata suka haɗa baki waje ɗaya cike da mamaki.
“Meee?”
Tanƙoki ta turo baki.
“Toh meye abin mamaki a ciki naga kun wani haɗa baki bayan cewa kawai nayi turanci nakeson koyo?”
Bebi ta fashe da dariya tana faɗin.
“Ke da baki iya cewa refrigerator ba sai ki ce ‘rice agitator’ ta ya rana tsaka zakizo kice turanci kike koyo kuma mu yarda sannan kuma ai ke bakinki kin sha cewa baki ga abin koyo a Turanci ba Allah ya kyauta ki koya” 😭😂
Tanƙoki ta harare ta.
“Ni dai yau sai na iya turanci ko don miskilin can nan wallahi.”
Lantana ta ɗaga gira.
“Wayyooo… ashe har ya shiga ranki?”
Tanƙoki ta jefawa Lantana takalmi.
Tana faɗin.
“Rufe min baki!”
Sai ta maida hankali kan littafin ta fara practical abin da take koyo a fili ta ce.
“Gud monin…”
“Morning,” Lantana ta gyara mata.
“Eh shi ai hakan nake nufi.”
Ta faɗa cikin basarwa.
Sai ta ci gaba.
“How is your breathing condition and your family background?” 😭😂
Nan take ƙawayen nata biyu suka kwashe da dariya Lantana har da kwanciya tsabar dariya.
Bebi har hawaye ya fara fita daga idanunta saboda tsananin dariya.
“Ke ai sai ki iya kashe mutum da turancin nan naki wallahi Tanƙoki”
Cewar Lantana cikin dariya.
Ita kuwa Bebi sai cewa ta yi.
“Allah sarki R.I.P English.”
Sauka sake kwashewa da dariya.
Tanƙoki ta haɗe rai.
“Hmmm ai kuma sai kuyi kanku ake ji kuma ai na san miskilin Ɗan birnin can sai gane abin da nake nufi.”
Haka dai suka ci gaba zaman nasu Tanƙoki tana ta tafka shirme ita ala dole turanci take koyo kuma bata yarda su gyara ma ta ba ganin hakan ya sa suka kyale ta idan ta yi abin dariya kuwa suyita yi ta yi kamar sabbin kamu.

Da rana…
ARFAAZ na tsaye yana duba aikin da ake yi.
Can daga nesa sai ya ji karaɗin muryarta.
“Gud aftanun Mistah Arfazz!”
Ya juya a hankali.
Sai ya ga Tanƙoki na tahowa tana taku irin ta masu ji da kansu ita ala dole ga wacce ta iya turanci.
Workers suka fara murmushi tun kafin ta iso. Domin yarinyar tana basu nishad'i.
Tanƙoki ta tsaya gabansa tana gyara mayafi. Lokacin da ta ƙari so.
“How is your breathing condition?”
Ta faɗa har da wani karkace kai ita dole ta yi turanci.
ARFAAZ ya ɗan runtse ido.
“…My what?”
Ya tambaya cikin son tabbatar da abin da kunnensa suka ji masa.
Tanƙoki ta yi murmushi cikin alfahari. Sannan ta ci gaba da faɗin.
“And your family generation?” 😂😂
Wani worker ya juya baya yana dariyar da ya kasa riƙewa.
ARFAAZ ya kalli Tanƙoki na wasu seconds kafin ya girgiza kai.
“Who taught you that English?”
Ya tambaya in serious.
Tanƙoki ta washe baki.
“So kaga na iya turanci ko? Bari ma kaji wani... Nice to meet you.”
Ta faɗa tana wani kwambo.
ARFAAZ ya dafe goshinsa.
“This is not English. This is a crime.”
Nan take wajen ya kacame da dariya. Domin Wallahi dramar Tanƙoki da ARFAAZ dole ma ya baka dariya. Shi dai baya gani ya kyale ita kuma ka ɗan banzan surutu.
Tanƙoki ta taɓe baki.
“Toh ai kai kullum sai turanci. Ni ma yanzu international girl ce tun da na iya turancin.”
ARFAAZ ya ɗan yi murmushi.
“You’re impossible.”
Tanƙoki ta nuna kanta.
“Thank you very much.”
Ta faɗa tana washe baki domin duk a zatonta yabonta ya yi.
“Hei! That’s not a compliment.”
ARFAAZ ya sake faɗa kamar dole ita kuwa sai cewa ta yi.
“Toh ai ban sani ba.” 😂
Ana cikin haka wasu yara suka zo a guje.
“Tanƙoki! Tanƙoki!”
“Lafiya?”
“Akuyarki ta shiga rafi!”
Tanƙoki ta zaro ido.
“Wayyo Bebi!”
Da gudu ta ruga.
ARFAAZ ya ɗan ɗaga gira kafin ya bi bayanta da kallo.
Workers suka ci gaba da aikinsu amma shi ya tsaya ya kasa taɓuka komai musamman da ya tuna yadda ta tafi hankalinta a tashe.
Can kuma… Sai ya ji ihun Tanƙoki daga can gefen rafi da yake babu nisa sosai tsakani.
“Wayyooo!”
ARFAAZ ya juya da sauri.
Kafin kowa ya ankara ya fara tafiya da sauri zuwa wajen.
Da ya isa wajen kuwa sai ya ga Tanƙoki ta tsaya bakin rafi tana ƙoƙarin kamo akuyar amma ƙafarta na zamewa.
“Don’t move!” ARFAAZ ya faɗa da ƙarfi.
Tanƙoki ta juya.
“Ai idan ban motsa ba akuyar zata tafi, Ruwa zai tafi da ita!”
Ta faɗa kamar zata fashe da kuka.
Kafin ya sake magana sai ki suka yi.
Ƙwaf!
Ƙafarta ta zame zuwa cikin rafin.
Kai tsaye ta faɗa cikin ruwan
“Wayyooooo niii! Wayyo Inna Abu ki kawo ɗauki.”
Tanƙoki ta faɗa tana wage baki tare da zazzaro idanu waje.
Yaran wajen suka fara ihu da dariya a lokaci guda ganin yadda take yi.
ARFAAZ ya tsaya cak na second ɗaya…
Sai kuma, ba tare da tunani ba, ya cire takalmansa ya shiga ruwan domin taimaka mata.
Tanƙoki kuwa tana cikin ruwa tana ta faman masifa fadi take.
“Na shiga uku! Wallahi wannan akuya nema take ta zama ajalina daga taimaka ma ta gashi ni na faɗa ruwan wayyo niii!”
ARFAAZ ya yi ƙoƙari ya kamo hannunta.
“Hold still!”
Ya fada. Tanƙoki ta kalleshi kawai sai kuma ta ce cikin firgici:
“Kaiii! Kada kayi min turancin nan naka bayan gani a tsakiyar rafi ina hango mutuwa!” 😂😂
Ko ARFAAZ sai da murmushi ya kufce masa yayin da yake janyota zuwa gefe.
Amma a dai-dai lokacin da idanunsu suka haɗu kusa sosai…
Sai zuciyar su duka biyun ta ɗan buga a lokaci guda.
Su kansu… Basu fahimci me yasa ba, amma Tabbas Akwai wani abu da ƙaddara ta ɓoye a tsakaninsu… ❤️


Sanyin ruwan rafin ya ratsa jikinsu su duka biyun yayin da yake ɗiga kasa daga tufafinsu.
Tanƙoki na tsaye tana huci, ruwa na diga daga gashin kanta kamar wacce ruwan sama ya lakaɗawa duka.
“Na shiga uku… wallahi wannan akuya so take na ta tsine ma ta haba jama'a wannan wahala har ina” 😭😂
ARFAAZ kuwa yana tsaye a gabanta, rigarsa ta jike, amma fuskar sam babu alamar damuwa da hakan sai ma ita da yake kallo.
“Are you done talking?”
Ya faɗa a tausashe.
Tanƙoki ta zaro ido.
“Kai! Wai har yanzu ba zaka dena wannan turancin ba?”
ARFAAZ ya girgiza kai.
“You’re impossible.”
Tanƙoki ta taɓe baki.
“Na sake jin wannan kalmar fa yau sau uku ke nan.”
Shiru ya ɗan biyo baya.
Sai iska dake ta kada a hankali.
ARFAAZ ya kalleta.
Ita ma ta ɗago ido ta kalleshi.
Wannan karon… ba hayaniya. ba dariya. ba faɗa.
Kawai shiru ne sassanyar shiru ne ya ratsa tsakaninsu.
A cikin wannan ɗan kankanin lokaci, zuciyoyinsu bugawa take fiye da kima.
Zuciyar Tanƙoki ta ɗan buga. Ita kanta bata san dalili ba.
Sai ta ɗan ja baya da sauri.
“Kai… ka riga ka ji ruwa amma har yanzu fuskar ka kamar fridge.”
ARFAAZ ya ɗan yi shiru.
“…Fridge?”
Tanƙoki ta gyara tsayuwa tana goge fuska.
“Eh mana. Babu feeling.”
ARFAAZ ya ɗan lumshe ido, sannan a hankali ya ce:
“I do have feelings.”
Tanƙoki ta tsaya cak.
“Eh?”
Sai ya juya gefe kamar bai so maganar ta kwace ta fito daga bakinsa ba.
“Nothing.”
Ta faɗa a hankali.
Tanƙoki ta zaro ido.
“Kai yanzu ka yi wata magana fa naji fahh”
ARFAAZ ya juya ya fara tafiya.
“Let’s go. Before you catch cold.”
Tanƙoki ta bishi a baya tana magana:
“Ni ba zan kamu da sanyi ba! Ni yar ƙauye ce ba ‘Abuja princess’ ba!”
ARFAAZ ya ɗan yi murmushi a hankali ba tare da ya juya ba.
A hanya suna komawa yayin da Tanƙoki ta cika sa da surutu.
Yara na biye da su suna dariya fadi suke.
“Tanƙoki ta ƙauye tare ARFAAZ ɗan gayu!” 😂😂
Tanƙoki ta juya.
Tana galla musu harara kamar idanun sa fado.
ARFAAZ ya kalli sama yana girgiza kai.
“Children…”
Tanƙoki ta ce:
“Ni da wannan miskilancin naka? Wallahi ni ba zan iya ba!”
Amma a ranta… ta ɗan ji wani abu mai nauyi da ta kasa gane ma'anar sa.

A daren wannan ranar da abin ya faru.
ARFAAZ yana zaune a ɗakin da aka ba shi a gidan shugaban ƙauye.
Ya cire jacket ɗinsa, yana kallon ruwan sama da ke sauka a waje.
Amma a zuciyarsa… ba ruwan yake gani ba.
Sai fuskar Tanƙoki.
Yadda ta faɗa cikin rafi… yadda take masifa… yadda ta kira shi da “fridge”
Sai ya ɗan yi murmushi a hankali.
“Ridiculous girl…”
Ya faɗa a hankali.
Amma murmushin bai ɓace daga fuskarsa nan take ba.
A ɗayan ɓangaren kuwa...
Tanƙoki tana kwance ta lulluɓe kanta.
Amma ba barci take yi ba.
Tana tunanin wani abu:
“Me yasa na ji kamar zuciyata ta yi tsalle lokacin da muka yi kusa da juna?”
Ta tambaya kanta tana tuna abin da ya faru a d'azu, sai ta juya ta sake juyawa dayan barin.
“Amma ba tunanin wancan Miskilin nakeyi ba… ko?”
Ta yi maganar a fili ta sigar tambaya tamkar wani zai fito ya bata amsa.
Sai ta tashi da sauri.
“Wayyo ni! Tunaninsa kuma? Ni Tanƙoki? Impossible!”
Ta koma kwance tana ta saka da warwara.
CUT TO ABUJA ✈️
Wani katafaren gida ne mai cike tsaro.
ARFAAZ a Abuja side, real life ɗinsa.
Wani dattijo ne cikin suit mai na alfarma yana zaune (family pressure).
“Arfaaz… we need to talk about your future.”
Ya faɗa cikin isa da wata kaifaffiyar murya.
ARFAAZ ya ɗago kai a hankali.
“My future is fine.”
ARFAAZ ya bawa mahafin nasa amsa cikin ladabi
Sai wata kyakkyawar mace dake gefe ta ce: “Ba ka da lokacin aure, ba ka da budurwa… kawai kasuwanci ta saka gaba kawai Please ta ya Rayuwar zata yi maka dad'i uhumm Jarumina?
ARFAAZ ya yi shiru kamar mai nazarin amsar da zai basu...

*✦ TANƘOKIN ARFAAZ ✦*

When two souls collide…
the result becomes laughter,
tears,
jealousy,
and uncontrollable love.
A Hausa Novel With Full Cinematic Drama & Comedy
*_BY NAINARH KD ✍️❤️_*


*_Complete Document ya kammala ga wadanda basa son jira, zasu biya 400 ta account 7067953066, Khadija Sabi'u Opay, Shaidar biya ta 07067953066_*

CHAPTER 3

ABUJA – NIGERIA
Gidan ya kasance mai girma na gaske, da tsari na alfarma, tsaro a ko’ina ma'aikata kuma sai shawagi suke domin tabbatar da tsoron gidan.
ARFAAZ ne zaune a cikin katafaren palon, sanye yake cikin suit mai tsada, laptop a gabansa amma hankalinsa ba cikinsa yake ba.
Sai dai yana ƙoƙarin boye hakan.
A gefe kuma ga mahaifinsa, Alhaji Usman Arfaaz, mutum mai kwarjini da tsaurin ra’ayi a komai hatta ga iyalinsa.
“Arfaaz,” mahaifin nasa ya kira sa da murya mai nauyi.
“Ka daina wannan yawan tafiya ƙauyuka ba tare da dalili ba domin ban ga amfanin hakan ba.”
A hankali ARFAAZ ya ɗago kai. Kafin cikin nutsuwa da girmamawa ya Bama mahaifin nasa amsa da faɗin.
“It’s business.”
Mahaifiyarsa ta ce cikin sanyin murya: “Na lura idan aka barta wannan Business ɗin shi ne zai mantar da kai komai domin ya ɗauke maka hankali da yawa baka da wani batu sai na business.”
Shiru ne ya ɗan ratsa wurin kafin sisternsa da shigowarta palon ke nan ta ƙara da: “Kullum fa shekarunka ƙara gaba suke, Arfaaz. Ya kamata ka fara tunanin aure.”
Nan take dakin ya sake yin shiru na wani ɗan lokaci domin sun san abin da bayaso ke nan shi ne ayi masa maganar aure.
ARFAAZ ya ɗan sauke numfashi.
“I’m not ready.”
Mahaifinsa ya kalle shi sosai.
“Rayuwa bata da tabbas haka zalika lokaci ba zai taɓa jira har sai ka zama ready ba ka riƙe wannan .”
ARFAAZ bai ce komai ba.
Amma a zuciyarsa… da gaske ji yake yake bai shirya ma wani aure ba a wannan takin. Amma su kuma sun kasa fahimtarsa.
Sai ya lumshe ido na ɗan daƙiƙa.

ƘAUYEN – YELWA
Tanƙoki na tsaye a ƙofar gidansu tana cusa rigarta cikin wando saboda gudu.
Bebi da Lantana na zaune suna kallonta.
“Ke ina za ki haka?” Lantana ta tambaya.
Tanƙoki ta ɗaura mayafi ba tsari.
“Wajen akuya ta na nufa!”
Bebi ta fashe da dariya.
“Wallahi ke da akuyarki kamar matasa da soyayya kowanne da nasa hanyar da ya ɓulla!” 😂
Tanƙoki ta harare ta.
“Ke kuma kika sani”
Ta faɗa sai ta tsaya na ɗan lokaci. Kamar wacce wani tunani ya fado ma ta.
Ta girgiza kai da sauri. Tana mai ruga wa da gudu kamar wata yar tsana domin ko gajiya batayi.

ABUJA – NIGERIA
ARFAAZ yana daga cikin mota yana waya.
“Yes… finalize the documents.”
Amma idonsa yana kallon waje.
Sai ya tsaya da magana na ɗan lokaci.
Driver ya kalle shi.
“Sir?”
ARFAAZ ya dawo hayyacinsa.
“Keep driving.”
Ya furta kamar an masa dole.
Amma a zuciyarsa: Yana jin wani abu da bai saba ba. Wani yanayi dai na Shiru duk da shi ɗin ba ma'abocin surutu ba ne amma kwana biyu da ya yi a Abuja ba tare da ya sanya Tanƙoki a idonsa ba duk sai yaji wani daban ya kuma ji shi gaba daya cikin rashin natsuwa.
A hankali ya furta a saman labbansa:
“…How is she causing this much disturbance in my mind?”
Ya runtse idanunsa a hankali yana tuna kalamanta a waccan ranar da ta faɗa rafi ya taimaketa.
A lokacin da Tanƙokin ta ce: “Kai… ka riga ka ji ruwa amma har yanzu fuskar ka kamar fridge.”
Ya saki tattausan murmushi yana tuna nata dariyar da yadda take washe fararen hakoranta a duk lokacin da ta ganshi.

ARFAAZ ya sake yin ɗan murmushi shi kaɗai yana ƙara wa.
Driver dai sai kallonsa yake yi cikin mamaki har dai ya gaza jure ganin yanayin Boss ɗin nata a yau.
“Sir wani abu ne ya faru?”
ARFAAZ ya gyara fuska nan take.
“Nothing.”
ƘAUYEN – YELWA
Tanƙoki ta isa wajen aikin filin ARFAAZ.
Amma yau ma babu shi. Bata sameshi kamar dai jiya.
Sai kawai ta tsaya tana kallon wurin. Jikinta gaba daya a sanyaye.
“Yau ma babu miskilin, to wai ina ya tafi ne?…”
Ta yi ma kanta tambayar da babu mai bata amsa, sai ta taɓe baki.
Wani worker daga cikin ma'aikatan ya ƙari so inda take kamar ya san tunanin da takeyi ya ce:
“Sir ARFAAZ yana Abuja.”
Tanƙoki ta juya da sauri.
“Abuja?”
Ta tambaya da sigar mamaki sai kuma ta tsaya na ɗan lokaci.
Sai ta ce a hankali: “To amma me yake yi a can?”
Worker ɗin ya ce: “A can yake tare Family ɗinsa. Aiki ne yake kawosa nan ai”
Tanƙoki ta yi shiru. Kamar mai nazari.
A fili ta ce:
“To shi wa ya faɗa masa ana hada aiki da wani abun ai sai ya bari idan ya gama sai ya koma can Abujan nasa gaba d'aya.”
Ta faɗa tana turo baki ta kuma ci gaba da sababi na ba gaira bare dalili, shi dai ma'aikacin murmushi ma ya yi kawai sannan ya koma ya ci gaba da aikinsa.
Tanƙoki ba ta san me yasa ba… amma yau wajen ya yi mata wani iri daban saboda babu miskilinta a wurin.

ABUJA – NIGERIA
ARFAAZ yana tsaye a balcony yana kallon sararin sama.
Yayin

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment