You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusa, dan sofar kusa da carpet ɗin da take ajiye abincin, shi ne ma ya kara sawa taki kallon nasa.

Tazo daidai zata wuce shi ta je ta ajiye mashi abincin ne, ya daka mata ƴar tsawa na cewa ya ce mata yana da buƙatar abinci ne, ko an gaya mata ana kawo mashi abin da bai bukata bane?.

Wannan tsawa da ya yi mata ne ya yi sanadiyar mugun tsoratata da har ta saki tray ɗin abincin ya faɗi kasa komai na ciki ya tarwatse. BABBAR MAGANA.

Gaba ɗaya fruits dake a ciki sun watse, wani apple ne ya yi tsalle ya dake shi a kirjinsa kafin ya dawo ya bugi screen ɗin wayar hannunsa, da yake ba wani riƙe wayar ya yi sosai ba sai wayar ta faɗi kasa a saman carpet dake tsakiyar set ɗin.

Gaba ɗaya abincin sun zube kaza gudarta tana kwance mashi a tsakiyar ɗaki, ga shi jikin kazar duk kayan haɗi da akayi baking nata da shi. Tiles nasa fari tas sai kyalli yake yi duk ya ɓaci jaga jaga da miya.

Jikinta wani irin mugun kerma yake yi, ta kasa tsayawa akan kafafunta a in da ta durkushe a wajen domin tasan ba makawa zata hukuntu ba kaɗan ba, jiya ma da ba wani abin ta yi mashi ba ya azabtar da ita har haka, ina ga kuma yau da ta ɓata mashi ko ina na ɗaki, bayan haka kuma ta sanya apple ya dake shi a kirji sannan ya patale mashi wayar dake a hannunsa, ya ilahi ya lillahi, ita wlh ko da faɗuwar gaba da tsinkewar da zuciyarta keyi tare da bugawa ma kawai ya isa ya kasheta ba tare da wani hukunci nasa ba. Shi ne ta gudu ne ko ta tsaya? Idan ta gudu ma ina zata je a duniyar nan ta tsirawa hukuncinsa? Ya ilahi ya lalliahi!..

A zafafe ya ɗago kansa ya.................


Alhadulillah Alhadulillah Alhadulillah, Allah na gode maka da ka bani iko da dama na kammala book 2 na wannan littafin, kuskuren dake a ciki Allah ka ya fe mana, gyaran dake a ciki kuma Allah kasa mu yi amsani da shi, Allah ka ba mu dace wa, nan na kawo karshen book 2 sai mun haɗu a book 3 idan Allah ya kai mu nan ba da jimawa ba dan jin yadda zata kaya. Keep praying for me My people's, one love 💗 💘

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment