You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faɗin "Iron lafiya? Me ya faru kuma na ga kun tsaya kuna sunkuyar da kan ku ƙasa?".

Cikin girmamawa Iron ya ce "Sir all my though zaka bamu punishment ne, zaka tsane mu dan mun ki karɓar addinin da ka kawo mana, a tunani na zaka sanya a...." Bai kai karshen maganar ba Aseef ya ɗaura ya tsaya ɗaya a saman ɗan ƙaramin bakinsa yana faɗin

"Shiiiiiiiiiii ya isa haka, me yasa zan wahalar da ku? Addinin musulunci addini ne mai sauƙi, addini ne wadda bai hana kowa ya yi addininsa ba, bai takurawa kowa ba, hasalima addinin musulunci ne kawai ya bawa kowa dama ya yi abin da yake son yi dan gane da addininsa matuƙar ba zai ci zarafin wata addini ba ko kuma abin da suke amfani da shi wajen yin addininsu, ni ba zan ki ku ba, ba kuma zan baku wahala ba, domin na san shiriya ta Allah ne, kuma addinina mai sauƙi ne tare da kamala, addinina ya bani dama na kyautatawa makwabcina ko da kuwa kafuri ne, so banga dalilin da zai sa na ki ƙu dan kun ƙi addini na ba, yanzu dai ku kawo mani abin da na ce maku, kada ku damu ina kaunar ku kamar koda yaushe".

Hawaye Iron ya fara yi yana faɗin ya yarda zai karɓi musulcin saboda Allah kuma saboda kyawun addinin, farinciki a wajen Michael da Musharraf ba'a magana, a tare suka basu kalmar shahada suka karɓa suna masu yaƙini mai kyau da kuma yi wa addinin kyakkyawar za to.

Suna tsaka da wannan farinciki uncle Herry ya faɗo cikin kitchen ɗin a ruɗe yana faɗin "Michael where are you? Naje ɗakin ka baka nan, na zo zan wuce na hangoka a nan, what are you doing here?".

Hankali kwance Aseef ya ce "Uncle what is happening? Na ganka a ruɗe" "Michael since yesterday Tyson (TGA) bai dawo ba, mun kira number sa a kashe".

Jinjina kai Aseef ya yi yana faɗin "Okey uncle go into your room zan kira Lion a kan hakan".

To uncle Herry ya amsa da shi tare da ficewa daga ɗakin, hankalinsa a tashe kwata-kwata bai ma lura da wayan da suke a cikin kitchen ɗin ba ya fita kawai.

aikin gabansa kawai Aseef ya cigaba da yi yana ƙoƙarin ɗaura ruwa a pot, dan Robert ya kunna mashi gas ɗin.

Ganin hakan ya sa Musharraf ya ce mashi ya je ya kira Lion ɗin mana, girgiza kai ya yi yana faɗin "I can't go anywhere uncle, kyalesu ina da tabbacin koma a ina yake Lion ya sani, Allah yasa ma shine yasa aka ɗauke shi zuwa headquarter aba shi jikinsa da wahala da kyau".

NI KUMA NA HAƊA KAYANA TARE DA AJIYE ALKALAMI NA SAI ALLAH YA KAI MU GOBE!!.
[11/28, 5:42 PM] Princess Teema Marubuciya Star Lady: 💖💖TRIPLETS💖💖




E 71-72


Ganin hakan ya sa Musharraf ya ce mashi ya je ya kira Lion ɗin mana, girgiza kai ya yi yana faɗin "I can't go anywhere uncle, kyalesu ina da tabbacin koma a ina yake Lion ya sani, Allah yasa ma shine yasa aka ɗauke shi zuwa headquarter aba shi jikinsa da wahala da kyau".

Shiru Musharraf ya yi suka cigaba da aikin da suke yi, su Iron sun tsaya suna kallon ikon Allah, har yanzu mamaki bai sake suba, yau ɗaya daga cikin TRIPLETS ne a Kitchen, kai abin ya yi mugun basu mamaki wadda ba za su taɓa mancewa ba.

Aseef ne ya ce masu su zo su haɗu su yi aiki a tare mana, tunda yanzu sun zama friends, har suna haɗa baki wajen maimaita sunan friends, ɗaga masu kai kawai ya yi alamar e friends, da sauri suka matso suka sanya hannu su ka fara aiki a tare.

Kasa jurewa Aseef ya yi, baya son warin abubuwan da Musharraf ke zubawa a girkin, ji yake yi tamkar zai yi amai, bai taba zama a wajen da ake yin girki ba, ga shi kuma baya son Musharraf ya fahimci cewa yana kyamar abincinsa, da kyar yake jan numfashi, har wani canza launi idanuwansa suka yi saboda bakar wahalar da yake sha ta sanadiyar rashin jan numfashi da yake samu.

Cikin dakiya ya ce "Uncle who teach you how to cook?".

Musharraf yana ƙoƙarin juya kayan miyar dake soyuwa ya ce "Na yi makaranta ai, a school na koyi duk wayan nan abubuwa".

Kasa sake yin magana ya yi saboda wani irin amai da ya zo mashi, da sauri ya nufi waje har yana yaɗawa da gudu, kai tsaye bedroom nasa ya nufa, yana shiga ya wuce toilet, amai ya fara shararawa kamar ba gobe, yana yi yana dafe cikinsa saboda yadda take murɗa mashi ba kaɗan ba, nan take zufa ta fara tsastsafo mashi daga gefe da gefen fuskarsa.

Shi kuma Musharraf bai ma lura da lokacin da ya fita ba, sai juyawa kawai ya yi yaga baya nan, bai kawo komai a ransa ba, sai ya ci-gaba da aikinsa kawai.

Sosai ya yi aman nan har sai da ya sami sauƙi sannan ya sakarwa kansa shower dan ya yi wanka kila ya ɗan sami sassaucin abin da yake ji a cikin zuciyarsa da kuma jikinsa baki ɗaya.

Bayan ya yi wankar ne ya fito ya shirya cikin wando three quarter baki da yar riga mara nauyi, mayukansa ya shafa tare da perfume nasa sannan ya nufo waje.

Yana fita ya wuce ya sanar da sojijin dake gyara masu bedroom nasu akan suje su wanke mashi toilet nasa tare da gyara bedroom ɗin, cikin girmamawa suka amsa da okey sir, sannan ya wuce izuwa ɗakin daddy, yana son komawa kitchen ɗin amma ya kasa dan saboda ba zai iya sake jin wannan wari na su kayan miya da sauransu ba.

Kwance ya isko daddy har lokacin hira suke yi da Areef, daddy ya yi ya yi akan su yi video call amma Areef ya ki yarda saboda yasa cewa idan daddy ya ganshi hankalinsa ba ƙaramin tashi zai yi ba, zai iya ja ma ciwonsa ta tashi, ga shi kuma basu kusa.

Saman bed ɗin ya haye tare da kwanto da kansa saman cinyar daddyn yana kallon Tv, a hankali daddy ya fara shafa kyakkyawar brown hair sa tare da gangarawa har izuwa bayansa, sai faman lumshe idanu yake yi tamkar mai jin barci, a ɓangaren daddy kuwa yana matukar jin kaunar ƴaƴan nasa kamar ransa.

Sun kwashi 1 hour bayan shigowa Aseef ɗin kenan suna waya da Areef, daga karshe suka yi sallama daddy ya miƙawa Aseef wayar, karɓa ya yi tare da gyara kwanciyarsa a jikin daddyn nasa ya kara wayar a kunne suka fara hira da Areef ɗin.

Suma sun jima suna hira kafin ya ce anjima zai kira shi yanzu zai je ya ci abinci ne, da haka suka yi sallama ya miƙe daga kwanciyar da ya yi yana faɗin "My daddy am coming".

Yana ƙoƙarin sauƙa daga gadon daddy ya riƙoshi tare da manna mashi kiss a goshi yana faɗin "I really love you my son" kayatatcen murmushi ya saki kafin shima ya yi wa daddy kiss a kumatu sannan ya diro kasa daga saman gadon ya fito waje.

Kai tsaye palon kasa ya nufa, wani irin fitinannen kamshi air freshener ne ke tashi a palon, da alama Musharraf ya kammala girkin da yake yi kenan, domin dama haka dokar gidansu yake, idan an kammala girki sojijin nan za su tattare ko'ina sannan su feshe ko'ina da turaren da ya dace da shi, su mai da komai mazauninsa, na wankewa su wanke na gogewa su goge, shiyasa a koda yaushe komai na gidansu yake kasan cewa tamkar ba'a taɓa taɓa su ba, kai ka ce sabbine daga ledarsu aka fito dasu saboda tsabar gyara da kula da suke samu.

Ba kowa a palon da alama Musharraf ya wuce part nasu dan dama bai cika zama a palonba, saboda takurawar da Tga yake yi mashi.

Juyawa ya yi izuwa part nasu, da sallama ɗauke a bakinsa ya shigo cikin palon nasu.

Saman table ya hango Musharraf yana zaune yana cin abinci, ya yi wanka ya canza kaya, ba ƙaramin kyau ya yi ba abinsa.

Karisawa saman table ɗin ya yi ya zauna yana faɗin "Uncle sorry na barka kai kaɗai ko?" Murmushin ya yi kafin ya ce "My Aseef don't worry".

Hannu ya kai ya karɓi spoon dake a hannun Musharraf ɗin tare da ɗibar abincin ya kai bakinsa, wani irin yanayi ya ji tare da danasanin kwatantawan da ya yi, ba tare da ya tauna abincin ba ya haɗiye tare da ajiye spoon ɗin ya yi maza ya ɗauki glass cup dake cike da ruwa dake a gaban Musharraf ɗin.

A zafafe ya kafa cup ɗin a bakinsa yana shan ruwan, sai sorry Musharraf yake ce mashi, to kawai yake amsawa da shi, jiki ba kwari ya miƙe ya nufi saman sofa ya kwanta yana faɗin "Uncle get ready fa on Monday zaka tafi Nigeria wajen JAMES".

A zafafe Musharraf ya ɗago yana kallon shi. "Aseef an gane James ne?" Jinjina mashi kai ya yi alamar e an gane shi, ajiye spoon dake a hannunsa ya yi tare da miƙewa ya sauƙa daga saman table ɗin ya tsunguna ya yi wa Allah sujudur shukur, dan nuna godiya da farincikinsa ga Allah subhanahu wata'ala.

Bayan ya ɗago sosai ya yi wa Areef addu'a tare da fatan Allah ya tsare shi a duk in da yake, sai amsawa da Amin amin Aseef yake yi.

Bayan ya kammala ya koma saman table ya cigaba da cin abincinsa yana ayyanawa a ransa ya zama mashi dole idan ya je Nigeria ya koma wajen ƴan uwansa, idan ba haka ba zai shiga matsala babba.

While shi kuma Aseef kewa kawai yake yi wa tunani, zasu barshi shi kaɗai bawan Allah. Bari mu koma Nigeria dan jin wani hali suke a ciki

GIDAN LION💖

Ya jima yana tunanin yadda zaayi ya iya kashe mahaifiyarsa da kansa, da abaya lokacin da yake kristar ne, to da sab zai iya kasheta, amma yanzu ya san mahimmancin iyaye, addinin musulunci ya gaya mashi waye iyaye, sanadiyar hakan nema har ya fara tunani a ransa zai iya yafewa mummy ɗin tasu, amma yanzu kuma ta yi laifin da idan ya tabbata hakan ne, da gangan ta aikata hakan, ba kuskure ko wani abu makamancin haka bane, to dole ne akasheta kamar yadda za'a kashe kowa dake a cikin kungiyar, babban matsalar shine yau ita ce rana ta farko da ya fara shiga damuwa dan yayi tunanin zai kashe wata, abin yasa shi ya ji kwata-kwata bashi da wata kuzari, amma kuma abin mamakin duk da wannan laifi da Josephine ta aikata, ta fi daddy samun waje a zuciyar Triplets, why basa son daddy? Daurewa kawai suke yi suke bashi kulawa kamar yadda addinin musulunci ya koyar da su, amma ba wai dan suna jin kaunarsa a cikin zuciyoyinsu ba.

Kyawawan fararen kafafunsa ya fara zurowa kasa kafin ya muƙe zaune yana kallon ɗakin, har lokacin idanunsa ba su koma daidai ba, sun yi jawur da su, tunani yake yi me yasa komai zai faru sai dai ya faru da Areef ko Aseef? Me yasa shi basu tunkararsa da ire-iren hakan? To menene banbancinsa da su Areef ɗin? Bayan kuma tare suka zo duniya, ɗan gara Aseef ma ace gaba ɗaya rayuwarsa ya yi tane tamkar ba mutunba, saboda ciwonsa, amma Areef fa? Abaya tare suke yin komai, lokacin da suke zuwa school tare suke komai, kaya iri ɗaya, karatu tare suke yi, abin da ya karanta shi Areef ya karanta, karatun addini tare suka yi, bincike akan addinan gaba ɗaya har suka fitar da na gaskiya a tare ne, to me yasa shi duk ka irin wannan abin ake tsoron tunkararsa da shi?.

Ya jima a hakan kafin ya miƙe ya nufi toilet dan ya yi wanka da ruwa mai zafi sosai ko zai sami kwarin jikinsa.

Bayan ya yi wanka ya fito sake shiri ya yi cikin pajama sky blue a wannan karon kam ya ɗaure gashin kansa ya bar wannan guntu na gaban goshin kawai.

Yana kammala shiri ya fito ya nufi kasa wajen Areef, kwance ya isko shi yana latsa wayar tasa.

Gefensa saman bed ɗin ya zauna tare da ɗan janye lallausan bargon da ya rufe jikinsa zuwa wuyarsa da shi, zubawa kirjinsa wajen ciwon nan nasa wayan nan dara-dara blue eyes ɗin nasa ya yi, shima Areef ɗin zuba mashi Ash eyes nasa na ƴan mintoci ya yi kafin ya ce "What is wrong with my blood?".

Kallon gefen ido Lion ya mashi kasa kasa a nutse ya ce "Au zaka gwada mani aiki ne?" Ƴar murmushi Areef ya yi kafin ya ce "Ni na isa in gwada maka aiki ne? Kawai dai naga kana cikin damuwa ne yasa na tambaya, amma ai ba batun na gwada maka aiki, ban kai nan ba".

Shiru Lion ya yi mashi na ƴan mintoci kafin gently ya ce "What is G.M.A?" Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya fara magana.

"G.M.A lokacin da na fara cin karo da ɗaya daga cikin members na kungiyar, a lokacin na kashe shi, yadda kuma akayi na gane, wani aiki naje to bayan na gashe waƴan da zan kashe zan bar wajen kenan sai a ka harbo mani bullet ɗin nesa, da alama suna kallona daga nesa, Allah ya tsare bullet ɗin bata same ni ba sai ta sami mutumin ɗin a kafa, ya faɗi kasa yana kuka, da sauri na karisa wajen sa, a maimaƙon naga jini na zuba daga wajen da aka harbe shi, sai naga wani farin ruwa ne yake zuba, abin ya ɗaure mani kai, sake harbin bullet da akayi ne yasa na ƙira hukumarmu akan su harbi koma waye ke mana harbin nesan nan, haka kuwa akayi suka harbesa, kasan CIA ko bata je waje ba muddin ɗaya daga cikin ma'aikatan ta za su je waje to tabbas kamar suna wajen ne, suna iya ganin komai. Bayan sun harbi mutumin nan ni kuma na fara binciken sauri akan waddake a gabana, daga karshe dai na ɗaukesa muka je cikin daji na yi bincike akan ya akayi farin ruwa yake fita a jikinsa a maimakon jini, a nan ne na gane cewa member ne daga cikin G.M.A abin ya ɗaure mani kai, ban ɓata lokaci ba waje kashe shi a wajen na tafi na bar gawar, daga nan sai na fara bincike akan suwaye su, a ina kuma suke? Me suke aikatawa? A nan ne na gane kungiya ce ta shan jini wadda ke a cikin New York, sai dai har yanzu na kasa gane a ina ɗaya taka maimai kungiyar take".

Shiru ya ɗan yi yana mai da numfashi. Jinjina kai Lion ya yi tare da ɗaukar wata ƴar karamar na'ura ya dasawa Areef ɗin a kirjinsa daidai wajen ciwon nasa, ƴar kara Areef ɗin ya yi saboda azaba.

Miƙe wa Lion ɗin ya yi ya fara haɗa abubuwan da zai buƙata, da yake Lion in dai fagen aikin likitoci ne to ba baya ba, ya kware sosai kamar babban likita, domin zance ma kusan ya karanci aikin sosai, kuma ya mai da hankali sosai wajen koyan abubuwa da dama daga wajen daddy, hakan yasa ya iya abubuwa da dama dan gane da kula da lafiyar jikinsu.

Komawa ɗakinsa ya yi ya ɗauko laptop nasa ya dawo, connecting na wannan na'uran ya yi da laptop nasa, nan take ya fara bincike akan lafiyar Areef ɗin da kuma abubuwa dake a jikinsa, a zafafe yake aikin, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan a ƙage yake da ya kammala aikin.

Good 1 hour ya ɗauka yana wannan binciken nasa kafin nan ya tattare komai ya kashe laptop ɗin nasa.

Wayarsa ya ɗauko ya kira Dr Tyrion bugu ɗaya Dr ya ɗauka, ba tare da ɓata lokacin ba ya sanar da Dr yana son da shi da wasu likitoci uku su dira a cikin Nigerian daga nan zuwa gobe da yamma, dan aikin da za'ayi wa Areef ba shi da time da zai iya yin wannan aiki, akwai abubuwa sosai a gabansa, kuma zai fi son ma dama manyan likitoci su yi mashi wannan aikin don shi ya fi bawa aikin sojan shi mahimmanci.

Bayan ya gama waya ne ya dubi Areef dake bin shi da kallo a nutse ya ce "Yanzu dai ka bar CIA har abada, kuma kasani sai na baka hukunci mai tsanani na laifin sayar da rayuwar ka da kayi, kana tunanin rayuwar taka ce kai kaɗai? Baka san cewa muma muna da hakki a kan ka bane? Iyayenka fa? Duk baka yi tunani akan wannan ba, good ka kyauta daka bani bakar wahala, ban taɓa aiki mai wahala ba irin aikinka, good 2 weeks na ɗauka ko barci bana samu bare kuma cin abinci all because of you, babban abin haushin ma sai ina bincinken ina kake sai na sake cin karo da wata ɓarna da kayi, dole na dakata nayi settle komai, kayi abubuwan dana kashe wutar bansan adadi ba, Allah dole na hukuntaka saboda gobe, ko da sunan wasa kada ka sake yi mana irin wannan gangamin, baka tunanin wani hali Aseef zai shiga? Bawan Allah da bai san komai ba sai kaunar mu, baya magana ɗaya biyu ba tare da ya kira mu a ciki ba, duk baka tuna haka ba kenan!".

Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya fice daga cikin ɗakin. Shiru Areef ya yi yana tunani, shi da kansa ya san ya yi babban kuskure, yasan cewa idan wani abin ya same shi to ba makawa daddy mutuwa zai yi, bayan daddy kuma Aseef, Aseef shine mutun na biyu da zuciyarsa zata iya bugawa idan ya ji wani abin ya same ni, gara Lion yana iya jurewa, amma shima sai ya ji ajikinsa ba kaɗan ba, babu wani ɗan adam da ya isa ya ce tun da rayuwarsa ne zai yi abin da ya ga dama da ita, hakan ba zai yi wu ba, saboda akwai haƙoƙin mutane da dama a tattare da wannan rai ɗin naka, na farko Ubangijin mu, Allah ya bamu wannan rayuwa ne domin mu bauta mashi ba dan mu sai data ga wani ko wata ba, bayan nan akwai iyayenka, suna da hakki akan wannan rai ɗin naka, sannan ƴan uwanka, to kada ya zama kana tunanin cewa ai ranka ne kana da damar yin abin da kake so da shi, a'a ba haka bane!!.

Yau sosai Areef ya yi nadama ba kaɗan ba, har hawaye sai da ya zubar, kuma a shirya yake da ya karɓi duk wani hukuncin da Lion zai yi mashi, domin yasan ya aika babbar kuskure mai girma, da ya mutu ta wannan hanya da bashi da amsoshin da zai bawa Aseef da daddy a ranar gobe kirayama dan dai yasan mawuyacin abune su biyun nan su rayu bayan mutuwarsa, sannan ba shi da amsar da zai bawa Ubangijin sa.

A ɓangaren su Jehan kuwa, barcine ya yi awon gaba da su dukkansu tun lokacin bayan da suka gama rikici da wannan Alhajin.

Barcin awa biyu suka yi Jehan ta farka, nan ta sami Aisha idabunta biyu itama ta farka tana zaune ta buga uban tagumi.

"Aisha me yake faru na ganki kin yi shiru haka?" Ta tambaya tana kare mata kallo.

Nisawa Aisha ta yi kafin ta matso ta ruƙe hannayen Jehan ɗin cike da damuwa tab a ranta ta ce "Jehan zan gaya maki ainahin abubuwan da suke faruwa a cikin gidan nan wadda ba kowa ya san da hakan ba, da farko abin da yasa ban gaya maki ba dan ina tunanin kema kamar mu ce, kema hakura zaki yi ki bada jikinki domin bamu da wata mafuta, wannan gidan da kike gani ba gidan arziki bane, wlh Allah wannan gidan bala'i ne Jehan, na san idan suka san cewa nasan wannan sirrin za su iya kashe ni ko dai su jefar da ni, kai da wuya ma su jefar da ni nasan kashe ni za su yi, Jehan sanadiyar cetar Maryam da kika yi tasa na samu karfin gwiwa na cewa sanadiyyar ki zamu iya barin gidan nan har mu kai kara ga hukuna cewa ga abin da ake yi a cikin gidan nan..."

Dakatar da ita jehan ta yi da cewa "Kin san hanyar fita daga gidan nan ne?" Girgiza kai ta yi tana faɗin "Kamar yadda aka kawo ki da tsakar dare, haka ake kawo kowa da tsakar dare, sannan babu wani alhajin da ya isa ya fita da ke da rana sai da daddare, bugu da kari magana ta gaskiya babu wanda idan ya shigo gidan nan yake sha'awar fitarta, shiyasa hajiya bata damuwa take bari a fita da ƴan matan, dan tasa ta asirce su ba zancen fita, amma na sha mamaki tun da na ga kin ceci Maryam nasan dole akwai nasara a tattare da ke, wlh asiri suke yi wa mutun ya zauna a cikin gidan nan, ina da tabbacin hakan ne, ka zauna kayi ta bada jikinka, lokacin dana fara yin hakan, da aka kawoni ina sabuwa, duk time dana kwanta da wani, zan kwanta ne cike da annashuwa da farinciki, idan mun gama abin da zamu yi kuma nadama tare da dana sani ne zai biyo bayan abin a tattare da ni".

Shiru Jehan ta zuba mata idanu tana jiran ta ji me yake faruwa. "Jehan kamar yadda kika sani ne ana fita da yarinya, Alhazawan nan suna zuwa da ita su kwana da ita a hotel da sauransu, amma fa ki sani ba kowani Alhaji bane yake zuwa ya kwanta da yarinya dan biyar bukatar kansa, a'a akwai masu zuwa su kwanta da yariya dan bokansu matsafansu sun basu wani abin su zaubawa mace a cikin cikinta dan samun kuɗi ko nasara ko dai wani biyan buƙatunsu, kuma duk wannan hajiya ta sani, domin kafin ya fita da yarinya sai ya bawa hajiya makudan kuɗaɗe ya gaya mata ga irin aikin da zai yi da yarinyar, da yake ba ƴaƴan ta bane, sai ki ga ta yarda ta karɓi kuɗin ta bada yariyar, ki sani fa wannan abin da suke zubawa mace a cikin cikinta wlh idan ya yi wuta in suka dawo da yarinya ta kara kwana biyu sai gawa, akwai kawata da muke wannan ɗakin kafin ku zo sunanta Zuwaira, yarinyar nan so silent, bata da hayaniya, to ranar da wani aljaji ya tafi da ita da daddare, bai dawo da ita ba sai washegari da daddare, lokacin da ta dawo nan wlh sai kin matsa mata kwallah, a nan ne take bani labarin abin da yake faruwa, domin ta ji duk yadda Hajiya ta yi da wannan alhajin, ta ji yadda suka yi da hajiyar daɗi, kuma ita ma ta gani da idanunta, lokacin da ya gama amfani da ita, ta ga wani bakin abu a cikin gabanta kamar garin lepton, abin ya so ya yi kama da kasa haka, tun daga lokacin ta fara jin ciwon ciki, shi kuma alhajin ya ɗauki kuɗi makudai ya bata sannan ya ce ta je ta yi wanka, haka ta je ta yi wanka ta wanke gabanta ta zo ta kwanta, da yamma ya sake dawowa ya yi amfani da ita ya sake zuba mata wannan abin, ga shi na safe da ya zuba mata ma sai ciwo cikinta yake yi mata, haka ba imani ya sake mafani da ita ya zuba mata, wlh yarinyar nan in takaice maki bata yi kwana biyu da dawowa ba ta rasu, hajiyar daɗi ta sa aka fita da gawarta ban san ina suka kai ba, cos a yanzu ba kowa yake yin zinar ba ma tsakani da Allah, wasu musamman ma manyan mutanen nan, wlh wani abin suke sanyawa mutun a jiki dan samun wani abu da suke nema, wani kuma su lalata mashi hanji ya ruɓe ya mutu, wani abin kuma idan suka saka maka ka haukace daga nan a rasa gane kanka, to yanzu dai ya kamata masu yin zinarma su kula dan yanzu ba zina kamar na da ake yi ba, kinga a ɗakin bayan mun nan, yarinya ƴar shekara goma sha huɗu wani alhaji ya ɗauke ta, yarinyar nan ya tafi da ita, wlh jehan virgin ce yarinyar nan, bata san komai ba, ga ƙananun shekaru, dan rashin imani ya je ya yi amfani da ita ta gaba da kuma ta baya, kuma ya zuba mata wani abin ta bayanta, wlh karki

Please Login or Register in order to submit comment