You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng ÿþ"[11/16, 6:31 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*"

BY

SADIYA ABDULRAZA˜

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATOIN*

PAGE 1

"""Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ihu jama'a, a kawo Wauki!"".Hayaniya da ihun mutanen gidansu ya ta tashe ta daga baccin safenta mai Wan karen daWi, ta ja dogon tsaki tana jan ya™unannen bargonta don ta rufe fuskarta, wai ko za ta samu damar rage tasirin hayaniyar, gidansu gidan yawa ne, mai cike da hargitsi, sun saba da hayagaga mara dalili, sai dai ta yanzu ta fara zargin da dalilin, duba da yadda yara da manya suke ihun babu ™a™™aunatawa, ""Yekuwa jama'a!"

"Salamatu ta faWa a rijiya, ku kawo mana Wauki!."" Maganar Mama Karime ta daskarar da duk wata na'ura ta jikinta ta dakata da aiki na wucin gadi, a hankali ta juyo da kanta ta yi wa idanunta matsuguni a gefen shimfiWar Mamanta, da fatan Allah Ya sa ba ita Salamatun ake nufi ba, duk da ta san babu wata a gidan mai irin sunata, nan ta ga wayam babu kowa a kai, ta tashi a firgice daidai sanda Nusaiba ta bankaWo Wakin da take tana haki tana cewa""Ke Nuratu, tashi"

"babarku ta faWa a rijiya!""."

"Da wani irin hanzari ta fice a guje har sai da ta yi fatali da Nusaiban da ta kawo mita rahoto, ma™ota har sun fara shigowa ana ta salati, ta yi tsalle da nufin faWawa rijiyar don ta ceci Mama, ganin an tsaya kame-kamen yadda za a yi, kamar ba su Wauki ran nata a bakin komai ba, Baba ban da salati ba ya yun™urin taSuka komai, aka cafe ta ana ba ta ha™uri, ta Sarke da kuka tana kiran sunanta cikin fitar hayyaci, ""Maaamaa!"" Tsayin mintuna kafin Malam Haruna ya zo, wanda masani ne sosai a kan harkar ha™an rijiya, su biyu suka shiga, aka samu nasarar ciro ta, aka shimfiWa tabarma aka zube ta aka shiga ba ta taimakon gaggawa, sai dai ta ™i numfasawa, Baba ya ™arasa ya kasa kunnensa a saitin zuciyarsa, sai ya Wago ya Wora hannu a ka yana cewa""˜alu inna lillahi wa inna ilaihir raji'un, Salamatu ta tafi, ta tafi ta bar mu, an yi mana mutuwa ni da"

"Nuratu!"". Nuratu ta yi kanta a guje, tana jijjigata haWe da gunjin kuka, amma ko motsi ba ta yi ba."

"GabaWaya gidan aka hau salati, wasu suna cewa ba ta mutu ba, a tafi asibiti, Baba ya hau faWa yana cewa""To wane asibiti ana zaune ™alau? Ni ™aramin yaro ne da ban san mutuwa ba? Na binne uwata na binne ubana, na binne matata, na binne ´a´ana huWu sannan a ce ban san"

"mutuwa ba, aradu Salame ko ba ta mutu ba na tabbata ba za ta tashi ba sai ta ™arasa""."

"Nan aka yi masa ca, ana nuna masa muhimmancin zuwa asibitin, abin takaici Baba sai ya zaro"

"aljihun rigarsa duka biyun yana kaWewa yake cewa""To wai da shekaruna zan kai ta asibiti? Ga"

"shi dai ko ™arfanfana babu a aljihuna""."

"Ta sake fashewa da sabon kuka, nan wani ma™ocinsu ya sunkuci Mama ya fice da ita, sannan Baba da sauran mutane suka mara masa baya, haka ita ma ta bi su ko Wankwali babu a kanta, sai ™anwarta ce ta cire hijjabin jikinta ta saka mata, ta bi su titi a guje, ta tari adaidaita sahu ta shiga, ya bi bayan nasu, a tare suka shiga asibitin ko ta kan kuWin mai adaidaitan ba ta bi ba,"

shi ma bai tambaya ba ganin halin da take ciki.

"Bayan jira na Wan lokaci aka tabbatar musu da rasuwar Mama Salamatu, Nuratu ta zauna a ™asa dirshan tana gurshe™en kuka, ana ta ba ta baki, don Mama Karime ma ta ™araso asibitin, nan aka ja lissafin kuWin asibiti da na Waukar gawa, wanda Baba ya ce ba shi da shi, sai"

"karo-karo aka yi aka Wauki gawar zuwa gida, sai ta shiga Waki ta zauna ta zama kamar"

"mutum-mutumi sai hawaye da ta kasa dakatar da su, da ™yar ´an'uwan Mama suka ja ta zuwa kan gawar bayan an gama yi mata sutura, suka ce ta yi mata addu'a, kuka ta fashe da shi, da ™yar ta iya buWe baki cikin in'ina ta ce""Ma...Mama, Allah Ya yi miki rahma, Allah, Allah Ya sa can ya fi nan"". Sai ta rushe da kuka, wata zuciyar tana raya mata Mama ba ta farinciki da addu'ar nan tata, saboda ta mutu tana tsananin fushi da ita, da ™yar aka ja ta a ka mayar gefe, tana kallo"

"aka fice da gawar, zuciyarta na tururi tana yi wa mahaifiyarta kallon ™arshe."

"˜ullin wainar siyarwar da Mama take yi, na yau sai ya zama na sadakar mutuwarta, Nuratu ta tuna jiya da daddare sanda take haWawa, ko markaWe da kanta ta kai, saboda tana fushi da ita,"

dama haka take yi idan ta yi mata laifi ba ta yarda ta taya ta aiki.

"Zuwa azhar ´an'uwa sun cika gida, har an gama kuka an shiga hada-hadar rabon abinci, wanda Alhaji Hashimu ne ya kawo, ´an gidansu har da masu faWa a kan abinci, yayin da Nuratu kuma yawun bakinta ma ya yi mata Waci. Mutuwa ta yi mata yankan ™auna, Mama ta tafi ta bar ta a gaSar da take ™ishi da yunwar kasancewa da ita, a lokacin da ta fi bu™atar taimakonta da samun kusanci da ita, ta rasu tana fushi da ita, ba ta tsaya ta fahimci uzurinta ba, ba ta yarda da hujjojinta ba, idan aka ce ba™in cikin abin da ta aikata ne ya yi silar mutuwarta ba za ta yi musu ba, domin kuwa tun shekaran jiya da ta sanar da ita ™addarar da ta faWa mata take cikin tashin hankali da Wimauta, tana yin komai ne da ™arfin hali, sannan a yadda Mama Karime ta ba da labarin yadda ta faWa rijiyar ta san ba ta cikin hayyacinta ne, sannan Mama da asuba take fara suyar waina, amma a yau Win har gari ya waye ™ullin yana Waki ba ta fara ba, ita kuma sai wani shegen bacci ne mai daWi yau ya Wauke ta, cikin bargon da take kwance zazzaSi yana nu™ur™usarta, ta kai hannu ta dafa mararta tana tunanin yadda zan yi idan abun Soye ya fito fili, da wane ido za ta kalli duniya idan ta fahimci da ciki a jikinta na watanni biyu? Mahaifiyarta ma ba ta fahimce ta ba ballantana kuma duniya? Sai ta saki siririn kuka, don zuwa lokacin muryarta ta"

dashe sosai.

"³an'uwan Mama da suke Wakin sun yi iya yin su ta ci abinci ta ™i, can bayan la'asar mata duk ana zazzaune, wasu suna shirin Wora tuwon dare, sai ga Baba ya shigo, fuskar nan a dagule ya"

"kalli Inna Asabe yayar Mama ya ce""Asabe yaya na ga ana shirin kunna wuta?"""

"Ta ce""E abincin dare za a Wora""."

"Ya ce""Au! Wato kenan ku banza ta faWi, kowa ya samu wajen fakewa ya ci abinci ko? Šan abincin sadakar da aka kawo mini don rage raWaWi tun da ba fita nema zan yi ba, a zage ni a gari a ce ban zauna karSar gaisuwa ba, shi ne za ku saka abincin a gaba ku cinye, ku bar mu da"

"tagumi ni da ´ar marainiyar Allah?"""

"Sai ya zo tsakiyar gidan ya Waga murya ya ce""Kowa ya buWe kunnenaa da kyau ya ji ni! Daga yau an rufe zaman makoki, kowace mace ta shuri takalminta ta tafi gidanta, gaisuwa ce an yi na"

"gode, amma kar wacce ta sake zuwa gidana daga yau!""."

"Mama Lami wacce ita ma matar Baba ce, ta taso tana cewa ""Haba Malam..."""

"Ya Waga mata hannu yana faWin""Kin ga Lami ki kiyaye ni, ni na gama magana!""."

Sannan ya shiga Wakin mai rasuwa inda aka ajiye kayan abincin ya dinga Wibowa yana kai wa

"Wakinsa, ya rufe da mukulli ya fice, nan mata aka dinga ™ananun maganganu, aka fara silalewa"

Waya bayan Waya.

"Inna Asabe ta shigo Wakin tana cewa""Kaico! Amma wallahi wannan Iro an yi mara mutunci,"

"yanzu ban da zub da mutunci a gidan mutuwar ma sai ya nuna halinsa? A kan abinci zai hana zaman makoki?"""

"Mama Suwaiba ta ce""To ke za ki dinga ci da mutane idan kin ce su daina zuwa? Babu wanda"

"bai san halin Iro ba, don haka wannan ba wani abun damuwa ba ne, ni kin ga tafiyata""."

"Ta kalli Nuratu ta ce""Nuratu ki yi ha™uri ki bar kuka haka, Allah Ya yi mata rahma Ya zama"

"gatanki"". Sai ta gyaWa mata kai alamar ta ji."

"Haka duk aka yoye aka tafi ana yi da Baba, Wakin ya rage ita kaWai, ta tuna jiya iyanzu tana kallon"

"Mama zaune a cikin Wakin, fuskarta cike da damuwa, sai ta fashe da kuka tana cewa""Allah Ya yi miki rahma Mama, amma kin bar baya da ™ura""."

"Kiran sallar magriba ce ta fito da ita daga Wakin, har jiri take yi saboda yunwa, ta tarar da Baba ya fito daga banWaki, yana gyara tazuge, ya ce""Yawwa ke Nuratu, Wazu Alhaji Hashimu ya zo,"

"duk shi ya kawo kayan abincin nan ma, ya ce anjima zai zo ya yi miki gaisuwa""."

"""To"" Kawai ta ce, ta Wauki buta ta fara alwala, tana tunanin da wane yaren za ta faWawa Baba tana"

Wauke da ciki a jikinta ya gane abin da take nufi?

*******

"Kamar kullum tana idar da sallar asuba, ta fito tsakar gida, ta fara kiciniyar kunna wutar gawayi, shayi ta fara dafawa sannan ta Wora farar taliya, ta zauna tana ta fifita wutar ta ji kukan Aiman ™aramin Wanta Wan wata biyar ya farka, tsakanin kukan da ™walla kiran da mijinta ya yi mata ba ta ma tantance wanda ya riga wani ba""Ke Hasana! Hasana"". Ta tafi da sauri, ta shiga Wakin"

"tana raira ´ar wa™arta""Aiman ya tashi, manya sun tashi""."

"""Ke dalla can kwashe shi ki fice mini!"" Cewar mijin nata, ko a jikinta don inda sabo ta saba da halinsa na masifa, gabaWaya shi kullum a zabure yake ba shi da lokacin nishaWi tare da ita sai dai idan yana tare da yaransa ko kuma wayarsa, yaran da sai sun zama mutane yake fara son su, amma yaro indai ba ya tafiya ba ya magana to ba mutum ba ne a wajensa, ko kallo nai ishe shi ba, da safen nan idan tana can tana girki Aiman ya tashi, ta sha zuwa ta tarar ya dawo da"

"shi falo, sauro suna ta cizonsa, idan kuma ta yi magana ya ™ure ta da zagi a gaban ´a´anta."

"Haka ta goya yaron, ta tashi sauran yaran Salim da Amir ta shiga yi musu shirin makaranta, sanda ta kammala komai bakwai da rabi har ta yi, don sai ta dafa musu indomi wacce za su tafi da ita makaranta baya sun ci taliya a gida, sai lokacin Nura ya fito cikin shirinsa na fita, ya buga uban wanka ya sha wani yadi daga gani ma yau ya fara saka shi, ya kafa hula, kamar mutumin kirki, irin wankan da ya sace zuciyarta ya yaudare ta da daWin bakin sama mata rayuwar soyayya mai cike da farinciki, sai ga shi ya kawo ta ba™in gidansa mai cike da ™unci ya kulle, ba ta da wani amfani a idonsa sai na bautarsa shi da ´a´ansa, suka karya a tare, ya Wauki mukullin babur"

"Winsa ya haWa kan yaran za su fita, ta ce""Me za a dafa anjima? Babu kayan miya a gidan""."

"Ko kallonta bai yi ba, ballantana ta samu amsa, wannan yana Waya daga cikin halinsa wanda ta"

"saba da shi, suka fice tana tunawa yaran addu'ar fita daga gida."

"Da rana ta dafa shinkafa da wake, sauran yajin nata ma kaWan ne, ga shi ba ta da ko sisi ballantana ta ™ara barkonon, ™arfe Waya yake Wakko yaran daga makaranta, sai ya ci abinci ya koma kasuwarsa, wacce babu nisa da gidan nasu, dab da yaran za su dawo ™awarta Ramla ta zo, ta ce"

"daga kasuwa take shi ne ta biyo, ta zubo mata abinci, suna ta fira cikin nishaWi."

"Tana jin ™arar babur Winsa gabanta ya faWi, don ba ta son ya shigo gidan tana da ba™i, don kar ya yi"

"mata faWa a gabansu har a san halin da take ciki, don ma dai ya san Ramla."

"Ya shigo da sallama, suka amsa, Hasana ta yi masa sannu, ya amsa idonsa a kan Ramla, wacce take kicikinar mayar da hijjabinta, ya kalli abincin da yake gabanta ya kalli Hasana ya"

"ce""Ke wai Hasana wace irin mace ce mai taurin kai?"""

"Sai ta sha jinin jikinta ta sunkuyar da kai ™walla har ta kawo idonta, ya ce""Sau nawa zan faWa miki"

"ki daina dafa mai da yaji a cikin gidan nan? Ta ya zan dinga yin cefane mai kyau kina nunawa duniya gidana babu rufin asiri? Nama ya ™are ba za ki sanar da ni ba?"""

"Ita dai ta yi shiru cike da takaici, don rabon da ta ga nama tun na babbar sallah."

"Ya kalli Ramla ya ce""Wannan ™awar taki don Allah ki dinga yi mata faWa, wai idan kana da shi ba"

"ka ci ba me za ka yi?"""

"Ta Wan yi murmushi ta ce""Gaskiya kam ba ta kyautawa""."

"Ya ce""Tsakani da Allah fa! A ce za ka yi ba™uwa ka dafa garau-garau, alhalin ba babu ba ce, Ina"

"zuwa""."

Sai ya fice.

"Hasana ta sauke ajiyar zuciya, suka cigaba da taSa fira, kafin ta tashi za ta tafi, ta rako ta tsakar gida, sai ga shi ya dawo da ledoji a hannunsa, ya ce""A'a Ramla kike ko wa? Ba dai tafiya za ki"

"yi ba""."

"Ta ce""Tafiya zan yi baban Salim""."

"Sai ya mi™a mata ledojin ya ce""Ga wannan balangu ne da lemo, wallahi mai kaji bai fara gasawa"

"ba, ba zai yiwu a zo gidana a ci garau-garau ba, alhalin Allah Ya hore mini""."

"Hasana ta san Ramla da kwaWayi, ai kuwa babu musu ta karSa har tana rusunawa, ta yi masa"

godiya.

"Ya ce""Maman Salim bari na koma kasuwa, yau ba na jin yunwar ma""."

"Ba™inciki ya hana ta cewa komai, ta rufe ™ofar gidan, ta koma ta zauna tana jin zafi a zuciyarta, zuwa yanzu ta fara zargin Nura aljanun son mata gare shi, babu damar ta yi ba™uwa ya ™yalla ido ya ganta sai ya ruWe ya yi ta kaiwa da kawowa, yana siyayyar ™arya wacce ita ba ya yi mata, ™awayenta sun sha faWa mata mijinta ya bi su gidansu yana son su daga haWuwa a gidanta, wasu ma matan aure ne, sai dai idan ya bi su hanya su faWa masa ba, shiyasa yanzu sam ba ta son ma ta yi ba™uwa mace indai ba ´ar'uwarta ta kusa ba ce, group Winta na makaranta duk ta fita"

saboda yadda ake yi mata habaici a fakaice kowa ya san mijinta na mamajo ne.

08028966015

"[11/17, 9:28 AM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*"

BY

SADIYA ABDULRAZA˜

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*

(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)

Follow this link to join my WhatsApp group:

https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY

PAGE 2

"Nura ya jima kafin ya dawo, sai da ta shiryar yara suka tafi islamiyya, sai ga shi ya shigo yana haWe rai, Hasana da zuciyarta take a zafafe bayan ya zauna ta kalle shi ta ce""Baban Salim"

"yanzu haka daga gidan su Ramla kake ko?"""

"Sai kuwa ya haWe gira ya fara zabure-zaburen borin kunya yana cewa""Ko kuma uwarta ba! Wai"

"ke Hasana me kika mayar da ni ne? Yanzu rainin naki na lura kullum gaba yake yi ba baya ba!""."

"Hasana ta ce""Ai na fi kowa sanin halinka shiyasa na faWa, idan ba haka ba meye na siya mata"

"balangu, bayan rabon mu da nama a gidan nan tun watandar sallah?"""

"Ya fara jinjina kai, ya ce""Laifina ne, wallahi laifiina ne, saboda na fitar da ke kunyar ™awarki ko?"""

"Ta ce""Ka fitar da kanka dai, ko kuma na ce ka shigar da kanka, don na tabbata ko ba daga"

"gidansu kake ba, to za ka je""."

"Ya ce""Ai ke ba ki da hankali, bai kamata ma na biye miki ba""."

"Ya juya zai fita, ta ce""Ka tsaya na kawo maka abincinka""."

"A fusace ya ce""Ba zan ci ba"". Ya fice yana ta mita da borin kunya."

"Ba ta wani damuwa ba, saboda Nura ya sabarwa da zuciyarta irin wannan ™uncin, ta ci abinci ta yi wanka ta Wauku wayarta, tana kunna data ta ga Ramla online, ta Waga mata hannu, ta ce""Ya"

"kika je gida?"""

"Ramla ta ce""Lafiya ™alau, na gode fa sosai, kin gan ni nan ina cin balanguna hankali kwance""."

"Hasana ta tura mata stikar dariya. Sannan ta ce""Yau kin samu Wan rakiya ko?"""

"Ramla ta ce""Mijinki yana da kirki wallahi, kin ga har gida ya kawo ni fa, ku dai Allah Ya taimake ku, mu ga mu a gida ba karatun ba, ba auren ba, aure mai daWi wai har faWa ake miki don nama"

"ya ™are ba ki sanar ba"" Ta haWa maganar da emojim dariya da mamaki."

"Hasana ta ce""Hmm! Ke dai Allah Ya ba ki na gari, auren wuri ba shi ne kwanciyar hankali ba,"

"dace a gidan auren ko da an samu jinkiri shi ne""."

"Ramla ta ce""Hakane"" Sai ta kashe datar, dama ta so ta san Nura ya kai ta har gidansu ne ko a hanya ya ajiye ta, tun da ta ji ya kai ta tana da tabbacin zai koma, sai dai za ta zubawa Ramla ido ta ga za ta kawo mata labari ko za ta karSi mijin nata, tun da har ga shi tana yabonsa, sannan ta ™osa da zaman gidan dama, da wannan tunanin ta kai yammaci, sai dab da magriba ta tashi ta dafa farar taliya, don har yanzu bai aiko mata kayan miyan ba. Ana idar da sallah ya shigo, ya ce ta kai masa ruwan wanka, bayan ya gama ya zo falo ya zauna,yana ta faman danna waya, ta kawo masa taliyar, ya buWe ya yi tsaki, ya fara ci, duk rabin hankalinsa a kan waya yake, haka kawai ta zargi da Ramla yake chart, ta Wauki tata wayar ta kunna data, sai ta ga Ramla ba ta online, ta sauke ajiyar zuciya, amma har lokacin tana fargaba, ta rasa ya za ta yi ya daina janyo mata abun kunya irin haka, ana fara sallar isha'i ya tashi zai fice, yana cewa"

"Salim""Sai na dawo""."

"Salim ya ce""Daddy ina za ka tafi? Don Allah ka zauna yau kar ka fita""."

"Ya yi dariya yana Waga Amir sama ya ce""Ai dole na fita, idan na zauna a gidan me zan yi Salim?"

"Zuwa zan yi na gyara wasu abubuwa""."

"Salim kuwa da surutu ya ce""Wani abu?"""

"Ya ce""Kai yaro ne Salim, ina zuwa kar ka yi bacci ka ji?"""

"Ya gyaWa masa kai, Nura ya fice yana kiran waya, idan ya yi irin wannan fitar sai ya kai sha biyu"

"har ™arfe Waya, kullum sai ta yi bacci yake dawowa."

"Zuwa takwas da rabi yaran sun yi bacci, ta yi musu shimfiWa a falo, ta yi musu addu'a, sannan ta"

"rufe falon ta shige Waki, ™ofar gidan dama kodayaushe a rufe take, sai dai idan ya dawo ya saka mukulli ya buWe, dayake tana da nauyin bacci ba kullum ba take jin dawowar tasa ba."

"Ta sauke Aiman daga bayanta ta kwantar, ta yi masa addu'a, sannan ita ma ta yi, babu jimawa"

"bacci ya Wauke ta, haka take yi kafin ™arfe tara ta yi bacci, saboda babu Wan fira."

"Yayin da Hasana ta saki baki take sharara bacci, shi kuwa Nura yana fita masallaci ya tafi sallar isha'i, bayan an idar ya hau babur Winsa ya tafi gidan su wata Hafsa, wacce ya karSi lambarta tun shekaran jiya da ta zo shagonsa siyan kayan kwalliya, tun a ranar ya so zuwa, amma yana da wasu al™awuran, sai yau layi ya zo kanta, Ramla ma ya je ganin gidansu ne kawai amma sai zuwa jibi zai koma. Fira sosai suka yi da Hafsa, wacce bai Soye mata yana da mata da ´a´a uku ba, sai dai ya faWa mata sam bai yi dacen mace ba, Hafsa ta ce""Ikon Allah, amma dai auren wuri"

"ka yi, wallahi ban yi zaton kana da aure ba""."

"Ya yi wani murmushin ™asaita ya ce""Wallahi da aurena, kawai dai tsabar tsafta ne da kula da"

"kai, sannan kin san idan mutum yana cin guminsa yadda ya kamata ya ci mai kyau ya sha mai kyau, dole za a gan shi tsaf""."

"Hafsa ta ce""Hakane"" Don ita ta tsani kishiya, ba za ta iya auren mai mata ba, ta yi soyayya da masu mata wajen su uku, duk mamma™o gare su, ba sa Sarin kuWi saboda hidimar gidansu ma ta"

"ishe su, sai dai shi wannan ta ji yana zancen yana cin mai kyau."

"Nura ya ce""Wallahi Hafsa a hakan ma da kika ganni don ma dai ina da matsala ne a gidana, ban yi dace da mace ba, kin san ita rayuwa idan ka yi dacen mace ta gari wacce ta haWa komai"

"kamar dai ke Win nan, to fa har wata ™iba kake yi""."

"Hafsa ta ce""Kuna samun matsala da ita kenan""."

"Ya ce""Idan kin ji matsala Waya kenan, matsaloli ne da yarinyar nan birjik wallahi, kin ga dai irin kayan kwalliyar da nake siyarwa, amma wallahi sai na yi wata ban ga hoda a fuskarta ba, kuma duk order da na yi sai na dara kai mata ta zaSi kaya kafin na kasa a kasuwa, Winki duk wata sai na yi mata ita da yara, amma indai kin ga ta saka sabon kaya to fita za ta yi, nama a firji sai dai wani ya tarar da wani, amma idan ta kwaSa girkin kare ma ba zai ci ba, gaskiya mata kuna da"

"matsala, yawanci ku ne kuke saka mazanku ™ara aure""."

"Hafsa ta ce""Wasu matan dai, amma ni yaushe zan samu mijin da zai yi mini komai na ™i faranta"

"masa?"""

"Ya ce""To Allah Ya sa kakata ce ta yanke sa™a""."

"Ta ce""Hmm! Idan da gaske kake ba""."

"Ya ce""Kamar ya?"""

"Ta ce""To ai na ga haka kuke masu matar nan, yawancinku kuna zuwa wajen zance ne don ku rage dare ba don aure ba, sai an ce ku fito sai ka ga wani matarsa ta fi ™arfinsa, wani kuma gidan nasa ma da ™yar ake cin abinci sau uku a rana, ba shi da halin ™ara auren, ni fa shiyasa ban"

"fiya sauraron mai mata ba""."

"Nura ya yi wata dariya ya ce""Baby Hafsa kenan, kin sanfa akwai maza, akwai muna maza, wallahi ni kam namiji ne a gidana, na fi ™arfin gidana, sannan idan da yunwa a gidana a jikina za"

"ki gani""."

"Hafsa ta ce""A jikin matarka dai, ko tana da matsalar gyara jikinta na san tana cin abinci ta ci ko"

"ba daWi""."

"Ya ce""To ni dai ki gwada ni ki gani, na tabbata ba za ki yi nadamar Sata lokacinki ba""."

"Ta ce""Zan yi bincike dai""."

"Haka suka dinga fira, yana ta kushe Hasana, da ™arairayi, don rabon davya Wauki hoda ya ba ta kyauta har ta manta, ita yanzu sam babu kwalliyar ma a gabanta tun da ko ta yi ba ya ganin ™o™arinta ballantana ya yaba, sai dai idan ta yi wanka ta shafa hodar da man leSe, don kanta ba dai"

don miji ba.

"Sai ™arfe goma ya bar wajen Hafsa, ya zarce majalisarsu ta bakin titi, ana ta fita sai sha biyu ya koma gida, ya buWe ya shiga, ya saka sakata, ya tura ™ofar falon ya shiga, yana haska yaransa, ya gyara musu kwanciya, don Waya ya Worawa Waya ™afa, sannan ya shiga Wakin, ya canza kaya ya hau gadon, ya haska Hasana da take ta sharar bacci, Aiman a kusa da ita, ya taSe baki ya kwanta, a yanzu ba shi da burin da ya wuce ya ™ara aure, yana bu™atar ´ar sawalwala wacce dare yana yi zai ji yana Wokin dawowa gida su sha soyayya, babu ciki babu goyo babu yaran da za a"

jira su yi bacci.

*******

"˜arfe takwas da rabi wayar Nuratu ta fara ™ara, ta duba ta ga lambar ce daga Saudiya, ta san Abdul ne mai kira, don yana aron wayar mutane ya kira ta idan ba ta hau online ba, saboda ba kasafai yake saka kati ba, Abdulmalik mutum Waya da take gani a matsayin sanyin idaniyarta bayan mahaifiyarta, ta san bai ji rasuwar da wuri ba shiyasa bai kira ta ba, ta Wauki wayar da"

"sallama, ya amsa, sannan ya Wora da faWin""Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!""."

"Nan ta ji wani sabon rauni ya taso a zuciyarta, ta fara kuka, ya ce""Ashe Mama lokaci ya yi"" Sai"

ta kasa magana.

"Ya ce""Ki yi ha™uri Nuratu, duk mai rai mamaci ne dama, Allah da Ya Wauke ta ya fi mu son ta..."""

"Cikin kuka ta ce""Yaya Abdul ina bu™atar Mama a rayuwata, ina bu™atar uwa, yanzu da wa zan"

"zauna a wannan bahagon gidan namu mai cike da takaici kala-kala?"""

"Ya girgiza kai kamar tana ganinsa ya ce""A'a kar ki sake

Please Login or Register in order to submit comment