You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faWar haka, Mama ba ta yi gaggawa ba, mu ma wata™il yau ko gobe ne, duk mai rai gawa ne shi a tafe. Sannan Allah Yana sane da yanayin gidanku Ya Wauke ta Win ya bar ki, sai mu bar hakan a matsayin wata jarabawar rayuwa"

"Allah Ya ba mu ikon cinyewa""."

"Hawaye mai zafi suka fara tunkuWo juna daga idonta, Yaya Abdul Winta ne kaWai mai mai da damuwarta tasu su biyu, sai dai wannan ™addarar da ta afka a dare Waya ta dalilin inganta rayuwarsa, sai dai tana zargin hatta shi Abdul Win ba zai iya karSarta ba, da wane idon za ta kalle shi idan ya gane tana da ciki? Ina zai saka kansa a ranar? Ta fi kowa sanin zafin kishin shi, shiyasa yake tsaye tsayin daka a kan ™ananun bu™atunta wanda ba su gagare shi ba, ko wannan"

"tafiyar da ya yi dominta ne, yana can yana bauta don ya tara kuWin aurensu, kuma ya"

"samu jarin da zai ri™e su, don su yi rayuwa mai inganci."

"Suna cikin waya ta ji muryar Baba yana ™walla mata kira, ta yi saurin cewa Abdul""Ina zuwa ka"

"ga Baba yana kira""."

"Ya ce""To ki yi masa gaisuwa, anjima zan sake kira""."

"Kafin ta fito Baba har ya bankaWo labulen yana cewa""Wai uwar me kike yi ne da kika share ni?"""

"Ta fito jiki ba ™wari tana cewa ""Gani nan Baba""."

"Ya ce""Ga Alhaji can a zaune, sai ki je ku tattauna""."

"Ta ce""To""."

"Ta bi bayan Baba, ta tarar da Alhaji Hashimu tsaye yana danna waya, ta tsaya tana kallon fuskarsa da wayar ta haska, babban mutum ne zai doshi shekara sittin, sati biyu kenan da haWuwarsu, ya kawow malamin makarantarsu sada™ar da yake kawowa duk wata, ya ganta, a ranar sai ga Malaminsu wato shuganan makarantar ya zo har gida wai an aiko shi, ya zo neman alfarma, ya faWa mata Alhajin yana sonta, kuma matansa uku, nauyi da kunyar Malam Isma'il bai hana ta faWa masa tana da wanda take so ba, don haka Malam ya samu Baba ya faWa masa, a ranar Baba faWa kamar zai ari baki, ya ce dole kuwa ta manta da kowa ta aure shi matu™ar da gaske yake, duk kuwa da kafin Abdulmalik ya bar ™asar nan sai da iyayensa suka zo suka yi magana akan bayan shekara biyu zai dawo sai a yi auren, a lokacin Baba murna ya dinga yi, saboda yana ganin Abdul zai tara arzi™i kafin shekara biyun, amma bayan zuwan Alhaji Baba har yana cewa""Wane shirmen banza ne ki zauna jiran wanda ya tafi Saudiya? Ai sai ya shekara goma bai dawo ba, idan ya dawo ma ya ce kin tsofe ya samu wata ya aura, don haka ba za a yi"

"wannan shashanci da ni ba""."

"Mama ta yi iya yinta don a bar zancen Alhaji Baba ya kafe, tijarar safe da ban ta dare da ban, har ™arar Mama ya kai wajen yayyunta tana hurewa ´arsa kunne, shi ne ta ce kawai Nuratu ta ha™ura ta aure shi, to a nan ne fa ta sanar mata zancen cikin jikinta, wanda ta same shi silar"

taimakon Abdul.

08028966015

"[11/18, 1:06 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*"

BY

SADIYA ABDULRAZA˜

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*

(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)

https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY

PAGE 3

"""Barka da fitowa"". Muryar Alhaji Hashimu ta dawo da ita nutsuwarta."

"Ta ce""Ina wuni""."

"Ya ce""Lafiya lau, sannu Nuratu ya ha™uri?"" Ta"

"ce""Da godiya""."

"Ya ce""Allah Ya yi mata rahma Ya sa aljanna makoma, sai ki yi ta ha™uri kin ji ko?"""

"Ta amsa da amin, suka yi shiru na Wan lokaci, kafin ya ce""Kin ci abinci dai ko?"" Ta yi banza da shi, ya sake cewa""Me kike son ci? Kar damuwa ta saka ki zama da yunwa, sai ya haifar miki da"

"wani ciwon, na zo miki da abinci ki daure ki ci""."

"Ya ™arasa yana mi™a mata babbar ledar da take hannunsa, ba ta karSa ba, kuma ba ta ce komai ba, sai hawaye da suke ta gudu a fuskarta. Ana haka sai ga sallamar ba™i gidan, suka wuce su a zauren bayan ta gaishe su, sarai ta gane Umma ce mahaifiyar Abdul, tare da abokiyar zamanta, sai ™anwarsa, su ma kuma sun gane ta, don da fitila a hannunsu suka shigo zauren, gabanta ya dinga faWuwa, saboda tana fargabar Abdul ya ji labarin an ganta da wani, ga shi mutanen da ba ta isa ta ce masa ™arya suke yi mata ba ne suka ganta, duk hankalinta ya yi cikin"

"gidan, ta ce masa""Zan shiga gida""."

"Ya ce""To Allah Ya ™ara afuwa, ga wannan ki karSa ki ci, da kuWi a ciki ko za ki yi wata bu™atar,"

"sannan duk abin da kike bu™ata don Allah ki sanar mini, babu abin da ba zan ba ki ba, Allah Ya"

"ji ™an Mama Ya sa ta huta""."

"Ta amsa da amin, ya ba ta ledar ta karSa ta yi cikin gidan, ta samu su Umma a tabarmar da ke tsakar gida tare da su Mama Asabe, suna mai da yadda mutuwar ta kasance. Ta du™a ta sake gaishe su, suka amsa suka yi mata gaisuwa cike da tausayawa, Mama Karime da ta ™yalla idonta a kan ledar ta ce""Kina zaune ke kaWai a Waki, sai mutuwar ta dawo miki sabuwa ai, ki"

"wuce Wakina ki kwanta, bari na aika a samo miki ko kunu ne""."

"Ta ce""To"" Ta shiga Wakin nata."

"Sai Zainabu ™anwar Abdul ta tashi ta bi bayanta, Khadija da Hannatu suna kwance a Wakin, ta zauna tana ajiye ledar, Zainabu ma ta zauna ta mi™a mata ledar da ke ™unshe a hijjabinta tana"

"cewa""Yaya Abdul ya ce na kawo miki"""

"Sai ta Wakko wayarta ta danna ta kunna mata voice, sai ga muryar Abdul Winta ta bayyana, daidai inda yake cewa""Nuratu ga sa™ona nan, jikina ya ba ni ba ki ci komai ba wunin yau, na yi nisan da zan ba ki wata kulawar da ta dace, amma ga ™anwata nan a madadina, idan a baki kike so sai"

"ta ba ki, don Allah ki ci wani abun""."

"A nan maganar ta ™are, Zainabu ta mi™a mata ledar, bayan ta ciro yougurt ta buWe ta matso ta kai"

"mata baki, Nuratu ta yi guntun murmushi ta ce""Wato Zainabu biye masa za ki yi ko?"""

"Tana dariya ta ce""To ai ni ´ar aike ce""."

"Nuratu ta karSa ta fara sha, ta sha kusan rabin jarkar, daidai sanda su Umma suke cewa Zainabu ta fito su tafi, Nuratu ta ji cikina ya fara hautsinawa, yawu ya taru a bakinta, da sauri ta fita tsakar gida ta fara kwarara amai, suna ta yi mata sannu, Zainabu tana cewa daga shan yougurt, Mama Asabe ta ce""˜ila don ta jima ba ta ci komai ba ne, sannu Nuratu kin ji"" Ta gyaWa"

"kai, ta gyara wajen ta koma Waki, su kuma suka yi musu sallama suka tafi."

"Tana shiga ta kwanta, a kan sallayar da take wajen, Mama Asabe ta shigo tana yi mata sannu, ta Wauki yogurt Win tana cewa ke ma ai ba za ki sha abu mai sanyi ba yanzu, tun da ™ila rabonki da abinci tun jiya, ta ce da Kadija""Dije tashi ki siyo mata kunu, ko ruwan bunu a wajen Mati mai"

"shayi""."

"Nuratu ta ce""Gara ruwan bunun Mama""."

"Khadija tana fita, Mama ta janyo ledar wajen Zainabu, ta ga wani yougurt Win ne, da lemuka biyu, sai shawarma guda biyu, ta janyo ta wajen Alhajin, ta fara cin karo da ´an Wari biyar biyar a dun™ule, ta faki idonta ta soke su a zani, ta duba sauran kayan, har da kayan shayi, da biredi da"

"manyan biskit ga kuma kaza da lemo babba, ta jinjina kai ta ce""Lallai ana gatale ki Nuratu""."

"Nuratu saman Wakin kawai take kallo, ta yi nisa a duniyar tunani, Mama ta ce""Wai ni kam dama"

"babanki bai raba ki da Abdul Win nan ba?"""

"Nuratu ta ce""Mama ni fa wannan Alhajin dole sai dai ya ha™ura""."

"Mama ta ce""Hmmm! Yaro man kaza, lallai kina da ™arancin hankali Nuratu""."

"Ana kawo shayin Mama ta Wakko kofi ta haWa mata mai kauri, ta sha, sannan ta ci shawarma guda Waya, ta ba su sauran, kayan shayin da biskit kuma ta Wauka ta tafi Wakinsu, Mama tana"

cewa ta kwana a nan ta ce a'a.

"Ta shiga ta zauna, kawai sai ta fara kuka, ga ta yau za ta kwana ita kaWai babu Mama, wayarta ta yi ™ara, ta duba ta ga Abdul ne, ta Waga a sanyaye, ko gaisawa ba su yi ba ya ce""Nuratu wane"

"ne wanda kuke tsaye Wazu?"""

"Ta sauke numfashi tana lumshe ido, da tunanin ta inda za ta fara yi masa bayani."

"Ya ce""Kar ki yi mini ™arya""."

"Ta ce""Wani ne, sunan shi Alhaji Hashimu, yana sona ne, ya fara zuwa sati biyu da suka wuce..."""

"Ya katse ta da faWin""Innalillahi wa inna ialaihi raji'un!"" Sai ya kashe kiran ba tare da ya ce komai"

ba.

"Ta bi wayar da kallo, ta so ya tsaya ta ™arasa, ta yadda za su fahimci juna, dama ta sani za a yi hakan, ga shi ba ta da katin kiran wata ™asar, sai ta kunna data, ta kuwa ganshi online, ta yi masa voice ta faWa masa komai tun farkon haWuwarsu, ya duba bai ba ta amsa ba, ta yi ta jira har ta gaji, ta kashe data, ta saka sakata a Wakin ta kwanta, tana jin wani abu mai kama da tsoro"

"tare da kewar mahaifiyarta, sai ta kasa baccin, sai hawaye da suka ™i tsaya mata."

"Haka ta yi bacci rabi da rabi, saboda kewar mahaifiyarta. Da asuba bayan ta idar da sallah ta kunna data, duk yawan sa™onnin da suke tururuwar shigowa na Abdul kawai ta kai hannu ta buWe, ""Ba zan fahimce ki ba Nuratu sai na kammala bincike a kanku. Fatana dai kar ki manta da al™awarinmu, ke kaWai ce macen da nake ™auna da fatan aurenta duk duniya Nuratu, kar ki butulce mini"". Abin da ya rubuto mata kenan, a maimakon ta ji daWi irin yadda ta saba a yau sai"

"zuciyarta ta yi rauni, ta fara hawaye."

"Ta koma ta kwanta tana jin yadda gidan nasu ya kaure da hayaniya, da alama har kowa ya cigaba da sana'arsa kenan, kwana Waya bayan mutuwar mahaifiyarta, kodayake idan ba su"

"cigaba da nema ba, waye zai ba su abin da za su ci?"

"Sai a lokacin ta Wan samu bacci ya Wauke ta sama-sama, Mama Karime ce ta shigo ta tashe ta, ta"

"tashi zaune tana gaishe ta, Mama ta amsa tana cewa""Sannu Nuratu, kin karya?"""

"Ta girgiza mata kai alamar a'a. Mama ta ce""Fito ki karSi koko da fanke ga shi na rage miki""."

"Ta ce""Idan da ruwan shayi dai zan karSa"". Ta tashi ta bi bayanta, tana jin yadda sanyi yake"

"ratsa ta, saboda zazzaSin da yake jikinta."

"³an'uwa da ma™ota WaiWai ana ta shigowa ana yi mata gaisuwa, daidai lokacin Abdul ya kira ta, ta faWa masa zazzaSi take yi, ya ce zai turo abokinsa ya Wauke ta su tafi asibiti, ta ce a'a ya bar shi, ya ce to zai turo Isa ya duba ta, Isa shi ma abokinsa ne, yana da chamest a ™asan layinsu, ta ce"

"kawai ya bar shi za ta sayi maganin zazzaSin, suka yi sallama, saboda ba ya son jan"

magana.

"Suna gama wayar ta tuna jiya Alhaji ya ce da kuWi a ledar nan da ya ba ta, sai ta Wakko ta dudduba, ba ta ga alamar kuWi ba, sai ta raya ko mantawa ya yi bai saka ba, ta san halin gidansu da sata, amma yanzun ba ta kawo wata ce ta Wauka ba, to idan ma Waukar aka yi, ita"

"yanzu ba ta su take yi ba, ta koma ta kwanta."

"Wajen azhar tana zaune tana cin abincin da ™anwar Mama ta kawo mata, sai ga Isa ya zo da leda har da ruwa wai zai saka mata, Baba yana ™ofar gida Isa ya gaishe su, ya shige, don haka"

"ya biyo bayansa, daidai sanda Nuratu ta fito tsakar gida."

"Baba ya ce""Kai yaro lafiya wajen wa ka zo?"""

"Ya ce""Baba aiko ni aka yi zan duba Nuratu""."

"Baba ya ce""Ikon Allah! Kai kuwa yaro wane hamsha™in ne ya aiko ka?"""

"Ya ce""Abdul ne saurayinta""."

"Baba ya ce""Ka ce dai tsohon saurayinta, to wuce ba ta bu™ata, sannan ka faWa masa kar ma ya"

"sake asarar kuWinsa a kan matar da ba ta shi ba, ni na riga na ba da ´ata ga wanda ya dace, lokaci kawai muke jira, ba don mutuwar nan ba ma, da a cikin satin nan za a tsayar da rana""."

"""Ok"" Isa ya faWa yana juyawa ya fice daga gidan. Nuratu"

"da duk ranta ya gama Saci, ta ce""Haba Baba..."""

"Ya ce""Buhun ubanki! Ba ki da lafiya shi ne ba ki faWa mini ba? Duk duniya yanzu kina da wanda"

"ya fi ni ne?"""

"Ya ja tsaki, ya ciro waya, ya yi danne-danne ya kara a kunne, can ya washe baki ya ce""Wa"

"alaikumus sallam, Alhaji ina kwana?"""

"Alhaji dake zaune tare da matarsa tana zuba masa abinci ya amsa da""Lafiya lau Baba, ya ™arin"

"ha™uri?"""

"Baba ya ce""Da godiya. Wallahi Alhaji dama mutumiyar taka ce dama babu lafiya, wallahi"

"zazzaSi jiya ba mu yi bacci ba, shi ne na ce to bari a sanar maka..."""

"Alhaji ya ce""Subhanallah! Bari yanzu zan aiko sai a Wauke ta a kai ta asibiti""."

"Daga nan sai Baba ya dinga jera godiya, har yana rusunawa kamar yana gabansa."

"Ya kalli Nuratu ya ce""Tafi ki shirya, zai aiko a kai ki asibiti yanzu, ai ke dai Allah Ya dubi"

"maraicinki da ya kawo miki wannan bawan Allah mai karamci""."

"Nuratu da ta shiga tashin hankali, ta marairaice ta ce""Baba Wan zazzaSi ne fa, ni ba sai mun je"

"asibiti ba""."

"Baba ya ce""Ai ke shashasha ce, har ki samu mau jiSantar lamarinki amma ki tsaya shashanci,"

"maza shirya""."

"Ta shiga Waki, ta zauna, sai ta fara hawaye, ta san manyan asibitocin nan da ™ir™ire-™ir™ire, tsoronta"

Waya kar a ce za a yi mata wani gwajin da zai fallasa sirrinta.

"Babu jimawa Baba ya shigo ya ce ta fito su tafi, yayarta Rahma ´ar Mama Karime tana tsakar"

"gida Baba ya ce""Ke Ramatu wuce ki raka su""."

"Har da saurinta ta sako hijjabi, suka fita, Nuratu tana jin kamar ta ce ba za ta je ba."

"Har da buWe mata murfin motar, ta shiga ya ja suka Wauki hanya. Dab da asibitin ta ga wani"

"babban chamest, ta ce""Bawan Allah kawai ka tsaya ka siya mini magani a nan, ba dole sai an je asibiti ba""."

"Ya Wan yi jim, sannan ya ce""To Hajiya ai ni umarni nake bi, sai dai na tambayi Alhajin, duk yadda"

"ya ce""."

"Ta ce""To ka faWa masa jikin da sau™i sosai, magani ma ya isa""."

"Ya faka motar, ya Wakko waya ya kira Alhaji, ya yi masa bayanin da Nuratu ta yi, Alhaji ya ce"

"kawai ya wuce su tafi asibiti, idan ma maganin ne su ba ta a can""."

"Ba ta sake cewa komai ba, har suka ™arasa asibitin. Tun kafin zu je Alhaji ya yi magana da likita, don haka kai tsaye direban ya rakata inda ya kwatanta masa, ta zauna a kujera sai raba ido take yi, hannunta yana dafe da mararta ta cikin hijjabi, gani take kamar likitan yana kallonta zai gane tana da cikin. Ya tambaye ta me yake damunta? Ta ce""ZazzaSi ne kawai kuma ya riga ma"

"ya sauka tun a hanya""."

"Ya ce""Ma sha Allah! Amma Alhaji ya ce ko abinci ba kya ci, ya ce a saka miki ruwa saboda ki"

"samu ™arfin jikinki, sannan zazzaSin ™ila malaria ce, za mu yi miki gwaji mu gani""."

"˜irjinta yana ta dukan uku-uku ta ce""Likita, ni fa ina jin ™arfin jikina, kawai ku ba ni magani ya isa""."

"Likita ya yi murmushi, don ya sabada mara lafiya mai gardama, ya ce""Ki yi ha™uri Hajiya, a yi"

"miki yadda ya dace kawai""."

"Ya tura su wani Wakin, wajen wata nurse, ita ta Wibi jininta, sannan aka saka mata ruwa ta kwanta gabanta yana ta faWuwa, tana ayyana ™ila yau ce ranar ™arshe cikin ranakun farincikinta na gidan"

duniya.

"A Sangaren likita bayan sun fita sai ga kiran Hajiya Laila, uwar gidan Alhaji, suka gaisa ta"

"ce""Doctor yarinyar da aka kawo daga wajenmu me yake damunta?"""

"Ya ce""Yanzu dai za a duba, zazzaSi ne take yi, sai rashin ™arfin jiki, an tafi saka mata ruwa""."

"Ta ce""Ok, don Allah kar ka bari ta tafi, sai ka samu adireshinta ko lambar waya, ka ajiye mini"

"account deteils Winka""."

"Ya ce""An gama Hajiya godiya nake"". Suka ajiye waya."

08028966015

"[11/20, 9:35 AM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*"

BY

SADIYA ABDULRAZA˜

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*

(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)

https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY

PAGE 4

"Sakamako yana fitowa likitan Hajiya Kubra ya fara kira, ya sanar mata yarinyar ciki ne da ita na sati tara, sai kuma malaria. Hajiyar ta yi murmushi ta ce""Idan ka tashi sanar masa ka ™ara da cewar tana Wauke da cuta mai karya garkuwar jiki"". Likita ya amsa, amma a zuciyarsa yana ta auna yiwuwar hakan, domin babban laifi ne, har a cikin aikinsu, sannan yana gudun Alhaji ya"

bincika ya gane ba haka ba ne.

"Har allurar bacci Alhaji ya sa aka yi mata, don ta samu hutu, ba ta san tsayin lokacin da ta"

"Wauka tana bacci ba, ta dai farka ne kawai ta ga Mama Karime zaune a kan sallaya, gefen"

"gadon da take kwance, gabanta ya faWi, ta tashi zaune, har an cire ™arin ruwan, Mama Karime ta"

"ce""Sannu Nuratu kin tashi?"""

"Sai ta kasa amsawa, kallonta dai take yi, tana son karantar fuskarta, don ta samu wani haske a kan zargin da take yi na fallasar sirrinta, sai dai ba ta ga komai a fuskar Mama ba, ta ce""Mama"

"ba su sallame ni ba?"""

"Ta taSe baki ta ce""Jira suke ki tashi, amma ke wannan gadon asibitin ai a yanzu sai ya fi yi miki"

"daWi fiye da gidanku""."

"Gabanta ya faWi, tana rabon ido ta ce""Mama saboda me?"""

"Ta ce""Saboda cikin jikinki, da ™yar aka fitar da babanki daga asibitin nan, don cewa ya yi sai ya"

"kashe ki, da tuni sai dai ki farka ki ji ana man Rabbuka?"""

"Bugun zuciyarta ya tsananta, tuni tsoro ya dirar mata, ba ta sake shiga tashin hankali ba sai da"

"Mama ta cigaba da faWin""Babban abun damuwar ma asirinki ya tonu, don na san zuwa yanzu maganar nan ta fantsama cikin gari, tun da a gaban Zainabu aka yi komai""."

"""Innalillahi! Me ya kawo ta?"" Ta tambaya tana sakin kuka."

"Mama ta ce""Ta je gida kai miki abinci, aka faWa mata kina asibiti, dama lokacin babanku ya ce gado aka ba ki, na ce ya kamata na bi ki, shi ne ta ce mu tafi tare, shigowarmu ke da wuya, muka samu ana kokowa da babanki. Nuratu kin ba mu mamaki, ba ki kyautawa Salamatu ba""."

Ta ™arasa a raunane.

"Ta kifa kai a cinyarta ta rushe da kuka, shikenan asirinta ya tonu, abin da take ta Soyewa yau"

"ya fito fili, tunani take yi yanzu ya za ta yi? Wane bayanin za ta yi musu su fahimce ta? Da wane idon za ta kalli Abdul? Sannan idan ta faWa masa dalilita zai yi mata uzuri kuwa?"""

"""Ina wayata?"" Ta tambayi Mama."

"Ta Wakko ta mi™a mata, ta danna ta ga ™arfe takwas da rabi na dare, ta sakko daga gadon, ta shiga banWaki ta yo alwala, ta fara jero salloli, lafin ta idar Mama ta zuba mata abinci, ta mi™a mata tana cewa""Wannan abincin duk Alhaji ne ya aiko miki, wallahi Nuratu kin yi asarar miji kamar shi, don kuwa shi ma zuwa yanzu ya samu labari, ai da mutunci ma, idan wani ne na tabbata korar kare"

"zai sa a yi mana daga asibitin""."

"Nuratu ta fara cin abincin a hankali, tana hawaye."

"Mama ta cigaba""Idan kuma Allah Ya tarfa wa garinmu nono sai ki ga duk da hakan bai janye ba,"

"tun da wasu suna sane ma suke auren karuwa, saboda huce takaici ta wani Sangaren""."

"Sosai surutun Mama ya dame ta, saboda tana ruguza mata lissafin da take yi ta tafkawa a"

"zuciyarta. Fatanta dai a ce yau a asibitin za ta kwana, indai lissafin da ta yi yanzu ya tafi daidai, to a tasha za ta kwana, washegari ta bar garin."

"˜arfe tara da ´an mintuna, sai ga direban Wazu da ya kawo su, ya shigo ya ce""Hajiya za mu tafi,"

"in ji Alhaji""."

"Nuratu ta ce""Sun sallame ni?"""

"Ya ce""E"". Ya kwashi kanukan abinci ya wuce gaba."

"Mama ta ce""Sai ki tashi mu wuce, ™iyamarki ta tsaya cak yau""."

"Wani sabon kuka ya zo mata, duk nu™u-nu™un da ta tsaya yi don Mama ta yi gaba, abun bai yiwu ba, haka ta saka ta a gaba suka shiga mota, a ciki suka tarar da Alhaji Hashimu, sai kunyar duniya ta rufe Nuratu, duk da ba son shi take yi ba, amma ba ta so a ce zai yi mata kallon"

"mara tarbiyya ba, haka motar ta yi tsit har suka ™arasa gidan."

"Baba da abokansa biyu suna zaune a ™ofar gidan, ya taso da sauri ganin motar Alhajin, sai dai"

"Nuratu tana fitowa ya gimtse fuska, yana huci."

"Wani mugun haushinta yake ji, gabaWaya ta canza masa lissafi. Suka shiga daga ciki, a zaune Alhaji ya ce su tsaya, Nuratu za ta wuce ya ce ita ma ta tsaya, ta dawo ta tsugunna kanta a"

™asa tana hawaye.

"Baba ya ce""Don Allah Alhaji ka yi ha™uri, wallahi da na san da wannan bada™alar a jikinta da ban"

"yi maka al™awari ba, Wan yau ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba!""."

"Alhaji ya ce""Na sani, kuma a yadda na samu labarin tarbiyyar Nuratu na san wannan ™addara ce, kar ku damu, ni tsakani da Allah nake son yarinyar nan, musamman yanzu da wannan ™addarar ta faru da ita, na san rayuwarta za ta iya shiga garari, saboda Baba ni na ji na gani,"

"zan aure ta na kau da ido a kan komai, da an cire cikin shikenan""."

"Baba ya fara jero godiya har da kukansa, Alhaji yana cewa ""Babu komai""."

"Sannan ya yi wa Nuratu nasiha sosai, tamkar tsakanin uba da ´arsa, har ta ji a ranta wannan mutumin ´a´ansa sun yi sa'ar uba, ba kamar ita ba, ya ™ara da ro™on Baba kan kar ya ce zai dake ta, ko wani hukunci, addu'a ita ce kaWai mafita, daga haka ya tafi, ita ma ta shiga gida, ta saka"

"sakata a Waki, duk bugun da Baba ya yi ba ta buWe masa ba."

"Ba ta taSa zaton mutumin nan zai ce zai aure ta a hakan ba, ta san auren nasa rufin asirinta ne, amma ya za ta yi da soyayyar Abdul Winta? Sai ta Wakko wayarta, ta yi masa sallama ta"

"whatsApp, yana online bai duba ba har tsawon mintuna, sai ta danna voice, sai dai ta kasa"

"cewa komai, har tsawon sakan goma, sai ta sake shi a hakan ya tafi, wannan karon da wuri ya"

"duba, bai ce mata komai ba, ta ajiye wayar ta kwanta."

"Can tsakar dare kuma ta tashi ta fara haWa kayanta a wata tsohuwar akwatin Mama, wanda ta bar mata ita, kayanta ne dama a ciki, ta saka komai ta ajiye ta tsaf, sam ba ta runtsa ba, kiran sallar farko a kunnenta, ta fito a hankali, tana jan akwati ta fice daga gidan a hankali, ta karo ™ofar, ta fara sauri don gudun wani ya biyo bayanta, tafiya mai nisa ta kai ta tasha, ta tarar da tsirarun mutane, ta zauna ta fara hawaye tana fatan Allah Ya sa a karSe ta a inda za ta je, sannan ta samu buta, ta yi alwala ta yi sallar asuba wanda har an kusa idarwa. Ta faWawa kwandasta Kaduna za ta je, aka saka ta a motar, ta yi zaune tana jira ta cika, zuciyarta tana ta dukan uku-uku. A daidai lokacin ne kuma Mama Asabe ta le™a Wakinta, ta ga ba ta nan, nan ta hau"

"cikiya a tsakar gida, kowa ya fito ana jajantawa."

********

"Misalin ™arfe goma Nura ya kira Hasana a waya, tana Wagawa ya ce""Ke maza ki buWe wannan"

"Wakin ki share shi tass! Gani nan zuwa""."

"Ta san dai Wakuna uku ne a gidan, ciki da falon da take ciki, sai kuma falle Waya, wanda take"

"saukar ba™inta, da kuma keken Winkinta a ciki, ta san shi yake nufi, amma hakan bai hana ta tambayarsa ba""Wane Wakin?"""

"Ya ce""Wannan wace irin tambaya ce? Šayan Wakin nan dai, da kike saka shirgi, ba na so na zo"

"na tarar da komai a ciki""."

"Ta ce""To saboda me? Yanzu ina zan kai keken nawa?"""

"Ya ce""Wannan kuma ya rage naki, idan za ki kai shi bola zan taya ki"". Ya kashe wayar."

"Ta zauna tana mamakin me zai saka a cikin Wakin? Ta san halinsa yanzu sai ya zo ya fara yi mata hayaniya, don haka ta tashi, ta fito da komai, ta share kamar yadda ya ce, ta janyo ™ofar ta koma Wakinta, can anjima sai

Please Login or Register in order to submit comment