You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba kuma bance sai kamin hakan dole ba amma a matsayina na mahaifinka inaga hakan ne dede. Koba dan komi ba kayi dan Allah dan ka ceto rayuwar marainyar nan daga halaka dan muddin kuka barta a hannun wayann bakusan wani irin mummunan rayuwa zata fada aciki nan gaba ba.

ATake Engr ya cire hularsa yahau fifita jin wata zazzafar zufa na karyo masa, gabaki daya yaji zuciyarsa da kwaklsa ta cirke sai yaji yakasa furta wata kalma sai kame kame dayakeyi shikadansa aransa batare da yasan me zaice ba.

Dada kwantar da murya Mahaifinsan yay yanamai cewa karka damu mahmuda nasan kai ɗa ne mai hankli da biyayya dankace min bazaka yi ba ai ba wani abu bane dama shawara kawai nake baka akan abunda zai ficce ka har Agaban ubangiji..babu wani soyayyar da zan nuna maka a duniya face in bida kai ta hanyar da zai kaika ga samun kyakkwan karshe.

Zuciyar engr na bugawa cikin neman dedetu makansa yace "Hakane Abu..hakan ma yay, In sha Allah koda umarni kabani zanbi bare kuma shawara me kyau kabani namaka alkwari in sha Allah hakan za'ayi nagode Allah ya kara girma yasa agama ibada lafiya.

Murmushi mahaifin nasa yay snn yace Allah yay maka albarka mahmuda
...Allah ya tsare bayanka da gabanka snn yasaka wann aure da zakayi ya zamu alheri gareka duniya da lahira.

Muryansa ararrabe Yace Ameen Abu... amma inason amin alfarma nayi dan nazari akai kadan sabida...bai barsa ya kammala zancen ba yana dan murmushi yace dakata mana malam ai duk munyi lissafin wann Mungama magana da ni da mahaifyarka,munsan baka shirya ba dan haka ne ma tacemin koda an daura auren bazata tare agidanka ynxu ba harsai ta gama mata yan shirye shiryenta by then ma an dan samu fahintar juna kaga inka shirya kaita gidanka willingly sai ka zo ka dauketa ku tare acan. Tare da sauke ajiyar zcya yace toh masha Allah hakan yay dama abunda nake so ince kenan.

Mahaifin nasa yace Toh inda akwai wani Abu dai zaka iya gaya mata ai alfarma muke nema awajenka mahmuda duk wani abunda kake so in sha Allah zamu duba.

Yace a'a Abu karka damu in sha Allah zanyi duk abunda kukace din.

Albarka ya dinga sakamai kafin nan ya katse kirar.

Daga nn Komawa yay ya jingina kansa ajikin motarsa ahankli yake furta lahawla wala kuwwata illa billah... hasbiyallah wa neemal wakeel...dan kwata kwata baisan meyakeji aransa ba sabida baiyi tsammnin hukuncin da iyayensa zasu yanke akansa ba kenan.

Wani bangaren zuciyarsa yana ma abun kallon saukakka wani bngaren kuma tunamasa da rikicin shemau yakeyi dan yasan abune me wuyar dauka awajenta barinma ace mata yar aikin suce, dan yasan bakaramin wutar balai bane zai huru agidansa wanda hala zai iya jawowa ya rasa matarsa dayake matukar kauna.

And He does not want to hurt shemau in anyway sabida yana sonta aransa bana wasa ba sedei ata wani fannin kuma bazai taba iya butulcewa ko ya saɓawa umarnin iyayensa ba har abada dan haka ya samo masa kamar dolene ma ya amshi batun auren nan.

atake yaji kansa ya cirke abun na neman tay masa nauyi, zuciyarsa na neman toshewa da tunanin wata mafita...

sake sake yakei aransa har saida abokinsa aliyu ya dan taɓa kafadunsa kafin nan yadan dawo hayyacinshi wanda kallo daya yay masa ya gane cewa ba lafiya.

Yace abokina Meyafaru ko baba ne kuma ba lafiya?

Cikin lumshe ido da budewa engr yace lfyarsa kalau yana saudi arabiya ma.. yace ma zai kiraka anjima....ynxu de wata magana mukayi dashi da take son dagamin hankli.

Alhj Aliyu Yace sirri ne ko zan iya ji?

Yace no bawani abun sirri bane aliyu...kawai cewa yay wai na amince a auramin yarinyar dan mubata daman rayuwa. Nikuma Na amsa mishi na amince amma kai abun na min nauyi a zuciyata gaskiya..i just dnt feel like its a right decision for me now
..wallh akwai matsala a
Aliyu...yadda baba ya kawo zancen rike yarinyar nan tamkar yabani Amanarta ne, amma kuma matata ta gida fa bazata taɓa fahimtar haka ba karshe ma tafara zargina tunda kaga aiki yarinyar take mana.

Alhj aliyu yy murmushi mai sanyi yace haba mahmud wallh ure overthinking it, i knw yin aure gatsau nada wuyar dauka, amma wann ai ba wani abun tashin hankli bane, inde akan fitinar mace ne duk zaizo ya wuce amma farinciki da albakan iyayenka akanka is priceless mahmud, ni ynzu da ace mahaifina na raye i wont mind doing anything for him wallh ko a bola aka tsinceta yacemin na aura zan aura badon komi ba saidan sabida nasan duk duniya sune zasu cigaba da tsayamin alkcin da bani da komi sann sukadai ne kawai zan saɓa musu inyi babban asara tunda aljannata akarkashin kafafunsu yake bana matata ba.

Think about it aynxu ahaka inda ace wani abu zai same arzikinka macen dakake ikirarin kanaso itace zata fara azabtar dakai wata ma rabuwa dakai zatay atake
Dan haka a shawarce ni banga wani abu aciki ba
Just calm down and think about yadda abun zai kasance.

Engr Yace haka ne amma Aliyu still dis is not easy as u said. I mean taya zan fara gayama shemau cewa nayi aure just like that ....i think is not fair kuma inajin nauyin ince ma baba a daga auren
Zuwa wani lkci..aiko Addini baice in zakama mace kishiya ka mata a sigar da zai daga mata hankli ba.

Aliyu yace hmm zaku tare da yarinyar ne ynxu?

Yace a'a....bana tunanin hakan just yet sabida za a sakata a makaranta a can Abuja..im talking about the future, kasan dei dolene shema'u tasan nayi aure wata rana sabida dolene inzo na hadasu susan juna.

Aliyu yace toh dont tell her just yet mana tunda bayanzu zaku tare ba
..ka dai tsaya kayita tunanin hanyoyi mafi sauki da zaka fito mata maybe hala kasamu wata yar maslaha da zata billo maka acikin wayann lokutan.

Engr Yace toh nasan hakan zaiyu, tunda mama ne tace zata riketa for the main time amma ina tsoron wani abu yaje south wallh dan shemau bata da sauki ko kadan

Murmushi Aliyu yy yace tunda ba da niyyar cutar da ita kayi ba nothing will go south.. kawai kayi Adalci snn ka kula da yarinyar koba dan komi ba bakasan albarkan dake tattare da ita ba.

Suna cikin wann hirar aka zo aka kirawosu lokcin hajy badiatu tay iya bakin kkrinta wajen lallama hafsa dan ta aure danta
Sede da kyar da wahala hafsat din ta amince badan komi ba saidan mummunan tsoron shemau datakeji aranta sedei jin hajy tace mata agidanta na Abuja zata zauna yasaka taji dan dama dama amma ko kadan aranta bason auren takeyi ba kawai dan bata da yadda ta iyane.

Koda aka baje magana Kawunanan nata sun sha baqar mamaki jin cewa baqin nasu sunce zasu amshi auren hansatu atake.

Sede aransu gani suke kamar auren bogine ake nema dan wani dan birni ne zai aure yar kauyen tukuf irin nasu wanda batay ilimi ba kuma ma marainiya??

Hakan yasaka basu wani dau abun da muhinnnci sosai ba.

Daga lkcin da aka binne mahaifiyar hansatun izuwa karfe biyar na yamman ranan aka kammala komi dan uwan mahaifin engr dake zama a kano shi yazo har kauyen ya wakilce auren dake tsakanin jigawa da kanon baki da hanci ne.

Duk wata al'ada ta aure anyi, Nan aka kawo dubu Dari biyar sadakin hafsa aka basu, Nan ma sukay kutunkutun suka hana hafsa ganin sadakinta sukace ai sadakin nasu ne tunda sune ubanninta.

Da yamma lis aka daura auren akofar me garin kauyen, ana kammalawa basu wani ɓata lkcinsu ba suka bar garin inda har suka fita a kauyen suka nufi gidan alhj aliyu asalin cikin garin jigawa hafsatu bata dena kukan rudani da baqin cikin yadda rayuwarta ya juya mata a lkci guda ba.

Anan sukayi magrib da ishai matar alhj Aliyun ta musu tarban mutunci da mutuntawa sosai, matar tasa mai suna murjanatu cikakkiyar bahaushiyar kano ce yar babban gida datasan darajar dan adam dan ko kadan bata raina yanayin dataga hafsa ba. Koda ta bawa hjy badiatu masauki bata zauna ba,nan da nan ta jawo hafsa suka wuce ciki tamata jagora tay wanka da sabulai masu qamshi ta fidda dauda kyanta ya dada fitowa sarari, hafsa ba fara bace snn bazaka kasaata a layin bakake ba amma wani irin narkakken natural beauty take dashi wanda fuskrta sam baya bukatr wani kwalliya.

Idanuwanta yan dedei ne farare sol gata da shatin saje baki dake nuna alaman yawan suma da Allah ya albarkaceta dashi, girarta ma acike yake tam snn tana da doguwar hanci mai kmr pencil da dan karamin bakinta pink colour me shatin baki kamar an zana mata da gazal, bazaka kuma ce da ita mai kiba ko tsiriya ba dake tana da diri na lafiyayyar budurwa mai fitinannen kyau mai kuma ban sha'awa kana kallonta kaga zubin bafulatanar jeji futuk.

sabuwar abaya mai kyau matar aliyu ta bata da inner wears new pant da bra ta saka ajikinta duk dama sam taki sakewa da su bare taci abinci.

Aliyu da matarsa Sunyi sunyi akan su kwana musu agidan amma haka engr yace sam, shidai yayi musu alkwari cewa zai kawo musu ita ziyara inkomi ya lafa musu in the future.

Suna zaune suna dan hira hafsa na tare da hjy badiatu ata ciki dan haryanxu jimamin mahafyarta takeyi.

Nan da nan Engr yay booking musu jirgin karfe 8:30pm na dare amma basu samu ba sai aka maida musu shi 9.30pm wanda ya saka suka dada samun hutu kadan.


Dagata fannin victoria kuwa tun kafin dare yay nisa ta isa sabuwar estate din mijinta ya kama ma dan uwanta nile.

Tun tana parking motarta a haraba ta dinga kallon wajen tana mamaki ganin yadda aka sankamawa gidan security camera ta ko ta ina.

Bata kawo komi aranta ba harta sauka ta karaso gaban apartmnt din nile tay knckng abakin door din after few min wani saurayi yazo ya bude mata kofar ta shigo ciki

Cike da girmamawa gayen yace mata "Gud evening sister vicky..Ta kallesa da fuskar rashin sani atakaice snn tace 'evening young man am here to see nile and who are you?...

Tun bai bude baki ba saiga nile din yana saukowa daga matakala
As usual looking breathtaking sassnyar murmushinsa mai ratsa zuciya bisa kan fuskarsa yana kallonta direct da sanyayyun ruwan idanunsa. Atake ta daga kai itama tana kallonsa sabida yanada wani irin fitinannen kyaune na fitar hankli.

sanye yake da armless shirt baki da 3qtr shot na kamfanin puma wani irin fresh kafarsa yay acikin lallausar roam about sleepers din da ya zura akafafunsa na kamfanin fenty.

Har ya karaso kasa gabanta bata dauke idanunta akansa ba har saida taji saukar lallausar labbansa agefen kuncinta yanamai cewa hey sis,.. hannunsa ta kama izuwa nata tanacewa Hi Darling "Whats up..ahnkli tace and who is this? Yace ohhh..Gefen abokin nasa ya dawo yana murmushi snn yace this is my friend lucio..kin tunashi tare muka fara scndry schl back in the days,
sumtimes muna canada tare.. He is my gee, even mum and dad knws him very well.

Yana maganan vicky ta kure gayen da idanu sai can kafin nan ta tunasa tafara dago fuskarsa na yaranta tace ohh okay lucio wilson.. The model guy right?

Lucio yana murmushi yace yes sister vicky its me.

Tace lu willy???

Dariya suka fashe dashi jin ta ambacesa da sunansa na yaranta.

Lallai an girma da ahanya naganka ma ai bazan gane ka ba, well is
Nice seeing again lucio

Yace thanks sister vicky. well, am on my out zanje na karbo mana abinci me kikeso kici sai na taho miki dashi.

Tace nothing dear ba jimawa zanyi ba, yanzu zan koma gida.

yace okay bye then daga nan ya fice yabasu waje

Nan Ta juyo kan nile tanata kallonsa kafin nan ta nemi waje ta xauna akan lallausar sofar dake falon, nan shima yazo ya zauna kusa da ita yay shiru.

Tace Ehen kacemun nazo wajenka cikin gaggawa sann nazo kuma kamin shiru..i even tot it was emergency hanklina duk ya fara tashi kawai sainazo naganka looking all fresh and good bama abunda ke damunka a duniyan nan face ka dagamin hankli.

Yace nooo sister vicky ba haka Bane. Dagaske akwai abunda yasaka nake nemekin kuma yana da muhimmnci.

Tace okay am all ears.
Gayamin da sauri tun kafin abokinka ya dawo dan inada aiki sosai a schl gobe.

Dan shiru yay kafin nan Yace sister vicky dama maganan akansa ne....

Tace okay.

Ahnkli Yy gyaran murya Yace Bance mijinki baiyi kkri ba amma This house and evrything is too boring for me so i tot inna kawo lucio yana taya ni zama it will be fun...

Cikin katsesa tace nile wait..is dat why u call me?

Yace yes amma ki tsaya kiji mana...

Tace kafadamin gaskiya ka kawosane ya tayaka zama as bodygurd ko ya zame maka houseboy dan nafa san halinka sarai nile bazaka iya yin komi makanka ba tsabar lalaci and maybe dats why u needed him...right?

Karamin Dariya yay snn yace nooo sister haba im not that cliche..yes just for security reasons sabida duk neibors dina yan matane yan runs kuma banason cringy situations kinsan yadda karuwan garin nan suke behaving kamar mayu Shiyasa bana son ina zama anan nikadaine

Snn...kiyi imagining ace wann katotonn gidan nikadai ne aciki sumting can happen to me kuma am surely gonna be depressed.

Tace so what do u want me to do??? Kasan bazan hanaka zama da abokinka ba musmmn ma dayanzu naganeshi sosai ko

Yace yeah nasan bazaki hanani ba. Kai tsaye yace Amma ai mijinki Yazo dazu da abokinsa wani ana ce mishi henry, sis i dont like the way he talked me about my friend asking me to kick him out sabida bai yarda dashi ba. Kinga tun farko abunda yasaka nace miki banason na zauna a karkashin kowa kenan.
Ke kanki kinsan bana zama a inda za'a yi controlling rayuwana bcos i am not a child i can take care of my self

Dan haka nakeso pls ki gaya ma mijinki inhar lucio zai bar gidan nan gobe to i will be leaving along with him Cos I can't stay under his control am really sorry sister vicky!!!

Yanayin tune din ya mata maganan cikin nitsuwa da kamala da kuma saukakkiyar harshe kamar abun bai wani darashi ba shiya kashe mata jikinta sosai.

Atake ta fahimce sa ta kuma gane inda ya dosa dan tasan nile baison nuna bacin ransa a fili amma muddin ya kawo karar mutum to ba mamaki ya kuresa ne

Cikin sauke ajiyar zuciya tace oooh god nile, am soo sorry about that amma ka tambayesa dalilin daya saka yace baison lucio ya zauna dakai kode yana da wani hali ne da bakasani ba.

Nile yace i dont think he knws him datbm much agabana fa ya masa wasu tambayoyi harda wanda bai kamata ba.
And Der was noting on lucio.. Lucio yana da business dinsa na boutique baya harka da mutanen banza.

Nikuma Kawai ce min yay bazai amince na dinga kawo abokan banza gidan nan ba,.. like the what the fuck..i m not his child..kuma ke kanki kinsan bana tara abokan banza akan me zaice bazan zauna da namiji dan uwana ba?

Tace calm down nile..
Its okay..naji naka side d amma kayi hakuri naje gida naji ta bakin femi maybe ders sumting dabaison ya gaya maka
Idan naji both side of the story zan yanke hukunci.

Cikin kyabe baki yace what ever.. kema kunsan sabida ke nake zama anan..if not da tun lkcin daya cima lucio mutunci dana mika masa keys din gidansa na bar nan wajen... lucio ne dai dabaida zuciya yace nayi hakuri nide bazan zauna a cimin mutunci haka ba

AYanayin damuwa Vicky tace its okay nile ya isa haka ..ai nace mka zan duba kan maganan. Pls
Kaje ka kawomun wani abu me sanyi nasha.

bai mata musu ba ya tashi ya wuce gaban wine celler ya hado mata negroni drink ya kawo mata gabanta snn ya zuba mata ice cubes aciki ta amsa ta sha.

Shirune ya ratsa wajen dan Maganganun daya gaya matan ne yaketa yawo acikin kwakwalrta gabaki daya sai taji ranta ya lalace da abunda femin yay, sai sake sake take aranta tana sakawa tana kuma warwarewa yanayinta atake ya sauya gaba daya har bata lura da irin Kallon da nile yake mata ba.

Cikin katse mata tunanin ya dube kayan dake jikinta daya kenan fari kall snn yace "mmmm sis u look like a fairy today.

Scoofing tay bazata snn tace "uff young man,..
stop admiring my beauty kaje kanemi budurwa
...mai tsoron mata kawai!

Dariya yay mai sanyi snn yace da gaske nake kayan ya miki kyau, mmm all white is for angels right..amma ahaka kike zuwa lecturing din looking like a hot cake?

Rolling idanunta tay tace mai "of course no..daga gidan kawata hadiza nake we had a mini girls date..

Cikin kyabe baki yace wow aiku manyan matane kunajin dadin rayuwa, but you knw what acikin kawayenkin nan akwai wacce take balain burgeni.

Da mamaki a fuskarta
Tace and who is dat.

wayarsa ya ciro a aljihu yay strolling IG snn ya mika mata ta ga hoton halisa ne agaban screen din.. yace this woman, ranar naji dadi da kika zo min da ita.

Tace mmmm so are you now crushing on my halsy?

Da sauri Yace no...kawai de i love how strong she is ne..i mean...she is a matured and emotionally strong person, i think she will be my role model. Dan bakowace mace ba ce zata zamo so calm and bold kamarta,msmn ayadda ake baza magananta a social media kowani lungu ana kirkiran karya akanta dan aurenta ya wargaje .im sure da wata ne haka ya faru da ita da hala ma ta kashe kanta aynzu..

Tay dariya tace yes oo amma ai haka halsy take, she is bold and strong kam da wuya kaga wani abu na baqin ciki ya kaita kan gwiwarta..dan koda abun ya faru da ita ma she didnt really react awfully mune muketa kuka.., kawai de kasan abune mai wuya ka cire abun aranka but she is fine now.

Yace okay send my regard to her when ever u see her and tell her am her biggest fan.

Tana dariya tace okay ooo Inkanaso wata rana zan jawota muzo mu sake wuni maka anan tunda tana burgeka sosai.

Yace no kibari sainayi budurwa tukuna bana son kizo ki zanca maganan ya dawo wani
abu nikam baturiya nake so na aura ba yar nigeria ba.

Tace iyyeee wama zai baka yar nigeria See you...

Awasa suka kare hirar batare da ya kyaleta tagane cewa ya jawo zancen halisan bane kawai dan suyi raha ya kuma cireta a tunanin dayaga ta tsoma kanta acki, dan yasan dolene zata daga hanklinta akan maganan daya gaya mata ynxu akan mijinta

Suna cikin raharsu sai ga nan lucio ya dawo da kwalayen pizza da kuma hadadden suya a kumshe a leda yana wani irin qamshin yajin tafarnuwa me dadi da tarkacen drinks da cokolote daya kawo ma vicky ta karbi chokolate din tana masa godiya.

Tun basu fara cin abincin ba tace musu ta gaji zata wuce gida.

Ahaka suka bar abincin suka rakata har bakin motar ta snn suka dawo ciki suka cigaba dacin abincinsu acikin kwanciyar hankali.


Daga bangaren shemau kuwa tunda aka barsu su biyun take famar bugan cikin hadiza domin ta gaya mata abunda ake ciki. Sabida yarda da kuma amana yasaka Hadiza bata boye mata komi ba tace mata yanxu hankalin alhaj ya dawo kanta infact hutun dayace zataje ma tare dashi zasuje su shakata a new zealand sai bayn sati biyu zasu dawo.

Sosai shema'u tay mata murna abaki amma har cikin zuciyarta baqirin yake da tunanin inama ace itace acikin wann yanayin.

Da wann boyayyar baqin cikin aranta ta dawo gidanta tazo ta samu mijinta bai dawo ba, tsaki taja bata ko nemesa ba dan haushinsa tafara ji tana ganin kamar shine ya jawo mata rashin sa'ar datayi aida can be aureta ba hala itama da irin mijn hadizar itama zata aura.
SHARE TO UR GROUPS DAN ALLAH...MY HAND NO GO REACH EVERY WHERE.

SURAYYAHMS 08060712446
CHAT ONLY NO CALLS...
[2/8, 10:49 PM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB...*_
_(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_


#ROMANCE
#FICTION
#ADULTHOOD
#SEXADDICTS
#WOMENPOWER

BY
_SURAYYAHMS_
_08060712446_
*Only chat oo, i no dey Available for calls on this number.*


⏯️2️⃣9️⃣

Tun ƙarfe goma na dare shema'u ta shiga wanka amma bata fito daga bayinba sai can wajajen 11:30pm na dare dan tunda ta lume acikin hadadden rose berry jacuzzi warm bath dinta ta lumshe idanunta Babu abunda takeyi face mafarkin kanta acikin irin rayuwar datakeso wanda shine kawarta hadizan ta samu anata rayuwar.

Memakon dadewar datayi a ruwan wankan ya saukar mata niima ajikinta sai kuma ta fito tanamai jin wani irin sabuwar kasala da haushin kanta gabaki daya.

Hadiza maitama is living her dream right in front of her eyes and all she feels is miserable right now..

Gabaki daya ta rasa menene guda daya takeji aranta da kuma kwakwalwarta dan ya mugun cunkushewa har bata san ta ina xata billo ma tunanin lamarin rayuwarta ba.


Bacci ma kasa zuwa mata yay sai juyi kawai take daga dungu zuwa dungu na gadonta aranta tanata kasafi da lissafin yadda itama zata kai kanta izuwa wann babban matsayi da hadiza take ciki..

Wani irin maqudan bakin ciki ne ta tsaya mata a makworo tanata hadiye yawu da kyar idanun ta duk sunyi sanyi acikin radadin damuwa da yake cinta aranta bana wasa

Tay juyi nan tay juyi can sai can ta tsaya cak awaje guda tare da sauke ajyar zuciya ta lunshe idonta gam snn tace ma kanta.."..Enough is enough! All hurts.. witout a solution, solves nothing. Dan haka dole ne ta fixge kanta acikin wann raunataccen yanayin domin ta samu sauki da kuma mafita
Tana kammala ayyana hakan aranta ahankli ta bude idanun nata tare da dada jan lallausar bargonta izuwa jikinta.

tunani dayawa sunzo kanta sede raba hadiza da nata mijin baizo mata acikin lissafin neman mafitarta ba, sabida gani take kamar aurenta da mahmud ne makasudin baqin cikinta shine ma ya jawo mata komi datakeji aynxu.

Lisssafin duniyan nan tay aciki harda shawarar data yanke na neman wani hamshakin mijin mai narkakken kudi dede da mijin hadiza ko wanda ma yafishi, wanda inhar ta sameshi toh tabbas bagudu ba ja da baya zata kashe aurenta da mahmud tabishi babu wani bata lkci.

Wann mafitar shiyafi ƙarfi aranta duba da ta yarda sosai da ƙirar da Allah ya xuba mata na kyakywan mace wayayyya ta ajin farko dan haka ta tsayar da zuciyanta akan wann shawarar har bacci yazo ya dauketa tunanin ta inda zata fara zura kafa domin cika sabuwar burinta takeyi.


Ata dayan bangaren kuwa Tun karfe takwas da minti talatin engr suka bar gidan Alhaj Aliyu suka isa dutse intl airpot domin catching flight dinsu. Tara da rabi dede jirginsun ya tashi izuwa garin lagos. daga seat din hajya badiatu aai na hafsat wanda Tunda suka kamo hanyan lagos ajirgi bacci kawai takeyi Sabida maganin zazzabi da aka bata tasha dazu hadi da yunwa daya gama kashe mata jiki.

Mahmud kuwa babu abunda yake ayyanawa aransa face matarsa shema'u daya bari agida.

Daga zarar ya kalle hafsat sai yaji tausayin matarsan dik ya dabaibaye masa zuciya har kwayar idanuwansa na nunawa a fili.

Dan Har yanxu Gani yake kamar bai kyautawa matrsa shema'u dayay auren nan bada sanninta ba,a ta daya bangaren kuwa shikansa yasan tausayin hafsat din bazai kyalesa ya yanke mata wani tsatsauran hukunci ba. Har ynzu bai san a wani matsayi zai riƙeta aransa matsayin auren amana suke koko na qaddara????..?

Dan Babu tantama ko shakku yasan matsayin hafsa dana matarsa shemau bazai taɓa zamowa abu daya aransa ba dan baijin kamar zaiso wata ƴa mace a duniya kamr yadda yake kaunar matarsa shemau.


Yanayin daya kasance aciki kenan har suka shafi iya awannin da xai kawo su garin lagos sun iso dede ana neman wajajen 12 na dare saura. Lkcin jikin hajiyar sa duk yay tsami dakyar take tafiya sabida gajiyar hayaniya da dawainiya da mutanen kauyen hafsa da suka wuni yi tun safe, ga nan hafsat dinma bakanta dan a daddafe ta farka da jiri jiri tabi ta tsaya cak abayansu bata ko motsi.

hajy na karasowa kasa ta kalle engr ganin baima kalle inda hafsat din take ba bare ya san me take ciki.

Ahankli ta dubesa kamr tasan meyake ciki na rudani aransa da muryan lallami mai taushi tace "haba mahmud, da wuri ya juyo ya kalleta, suna hade ido tay masa nuni da baya inda hafsa din ke atsaye. Sihirtaccen

Please Login or Register in order to submit comment