You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri take tana huci cikin nan nata da yay kama da rubber ring na gaba na rawa, bata tsaya ko inaba ta nufi bangaren hadiza dan tunda hayakin asirinsu ya fado mata akai takejin kamar hadizan ce ke kirarta sai ta zama kamar wacce bata cikin hayyacinta gabaki daya duk dama hanklinta bai gama gushewa ba kawai dai bata san metakeyi bane kwata kwata.

Wani irin bankado kofar ramatu tayi wanda saida kirjin hadizar ya girgiza sosai sabida tsoro,amai na mugun damunta amma haka ta daure tahau lura da yanayin ramatun tare da dukan nitsuwarta.

ganin yanayinta yasa ta tabbatar da cewa tabbas tarkonsu ne ya kama bushiya wani murmushin bazatane ya kufce mata aranta tace "Dakyau" yar bura ubar mata yau zaki san kin shigo hannu na.

Mikewa tay daga kasan a daddafe snn ta bude jakarta ta dauko wani kullin magani mai laushi in form of powder snn ta nufi gaban ramatun ta watsa mata a fuska.

Ramatu na tsaye cak kamar wata kungi tanata kallon hadixa amma bata iya mata komi ba bare yin mata wata magana.

Tanaji tana ganin komi yana faruwa da ita amma ji take kmr bata cikin hanklinta sosai.

wani irin shu'umar murmushi hadizan tay snn tace hahaha,the great honourable ramatu Bukar yau sai gaki kin kawomin kanki?tana murmushi tare da sake mata wani irin kallon kaskanci tace Hmmm Toh ai Dan hakin daka raina wata rana shine zai tsole maka ido, ba kinxo ne ki ci arziki agidana snn ki kasheni ba?...hahahaha Ramatu kenan. . inkinacin kasa ki kiyaye na shuri,..kin jima kina haukatar da mata wasu kuma kina kashe su har lahira snn kibi yayansu da kika maida marayu ki kwace destinynsu me kyau da tsafinki sukuma ko su mutu ko rayuwarsu ya kare a walaknce ke kuma kiyi suna kiyi kudi ana miki ikirarin kin gagari kowa muguwa baqar azzaluma kafura..to akaina wann mugunta da zaluncin taki duk ya kare tsohuwar banza kawai yar bariki, Jibeki fa cikakkiyar kilakiya dake wai har kinsakawa miji kayan bacci zakiyi first nite a gidana ko hahahahahah
...to nidin hadiza da kike cewa karamar yarinya sa'ar yar cikinki da kika haifa nice nan zan kawo karshen terrorncinki a duniya ramatu..

Hawaye na zubowa a idanun ramatu tafara motsi da bakinta ɓbbbbb..eeee kamar zatay wata magana amma ina babu baki.

Cikin dakan mata tsawa hadiza tace "na umarce ki da ki fara tonawa kanki asiri..ki tonawa kanki asiri kowa sai yasan ke wacece azzaluma kawai kafin ki kasheni kece zaki fara mutuwa.

Wani razananniyar kukan kura mai nunnuke da amon baqin ciki mai radadi ramatun ta saki mai kuma dan uban kara wanda yasaka kusan kowani halitta agidan ya birkice aka fiffito waje da zimman jin meke faruwa.

Kamar wata zakanya haka take huci huhhhhh huhhhhh waaa waa, Aranta ji take kamar a mafarki wann abun yake faruwa da ita. Dan inba a mafarki bane toh lallai koita dakanta zata iya jadaddawa kanta cewa tay mummunan karshe inde wai hadiza maitama da tagama rainawa wayo itace zata kawo karshen ta a doron kasa.

Bayan tulin issashun mata manya data tarwatsa ma rayuwa amma sai nata ya kare a hannun karamar yarinya

Alhaj kyari dake cikin rudewa jikinsa take yahau rawa rawa na rashin sanin meke faruwa agidansa wanda shikansa baisan yaushe ya ture mai aiki ya nufo waje da sauri ya nufi sashen hadizar ba.

Ramatu tay tay ta kwaco kanta,amma ina sihirin yariga da ya shige cikin jikinta ya mata wani irin mummunn kamu sabida dama ita bawani ibada takeyi arayuwarta ba daga neman kudi sai shagalin siyasa sai kuma bibiyar malamai,kusan ahaukace tayo kan hadiza zata shakure mata wuya hadiza tay wuf tare da watso mata sauran powder akan fuskarta..


Wani irin gigitaccen kara tasaki kafin nan tayi wufff akaro na biyu ta riko hadizar kamar zata ballata tafara ihu tanata ihu da alamar dukkan mugayen abubuwan da tayin ne suke dawowa kanta tanaso ta fadesu a fili.

Sanin cewa yanxu mutane zasu iya shigowa yasa hadiza fashewa da wata tsumanmiyar launin kukan makirci tabi ta sake jikinta tana fidda numfashi mai uban ƙarfi kamar ramatun ne threatning dinta zata kasheta.

Tunda daga waje alhaji ya soma jin gurnanin ramatu mai tahowa da huci mai radadi...

Manyan Masu aikin gida sama da su biyar sune suke tafe abayansa sabida yanayin yadda hayaniyar ramatun yake fitowa.

Sauri alhaj kyari yakeyi domin yakai kansa ta bakin kofar yabi yarike gaban towel dinsa dake neman sincewa a rikice..

Har kamar zai yi tuntube abakin kofar jin muryan ramatu na fitowa ata ciki

Zan kasheki zzzzaaann kashe ki hadiza..

Sai memeta hakan ramatu takey da ihu da kuma hauka hadixa kuwa banda kukan mkirci babu abunda take saukewa.

Wayyo Allah na na shiga uku Ni mena maki da zaki kasheni. haka kawai zaki shigomun dakina kice xaki kasheni ni mena miki..

Agaggauce alhaj ya tura kofar yabi yatsaya cak kansa na mummunan sarawa ganin yadda ramatu ta damko masa matarsa hadizar kamar wacce zata hallakata.

Cikin gurnani take cewa Zan kasheki....

Hatta motsi kasa yinshi yay, Suna hade ido da Hadizar tadada fashe masa da wata iriyar makirtacce kuma rikitaccen kuka mai balain saka tausayi ta shiga mikamai hannu tana cewa ALHAJ kazo ka cece ni, wallahi kasheni zatayi alhaji kazo ka cece ni karna mutu...

Rudewar da ya ballo dashi irin wanda tunda yake arayuwarsa bai taɓa jin irinsa akan ko wacce diya mace face hadixan dan wani irin azaban tausayi tabashi yanajin sonta dabaisan yanaji ba na mamayeshi.

Kusan a rikice bakinsa na ɓari ya soma cewa hadiza hadiza ina zuwa ki tsiya ynzu zanzo na kwatoki, hadiza sai kuka takey kamar zata cire ranta, shikansa baisan sadda yayo kansu fanjam a mugun agaggauce ba nan da nan yasoma kokuwa da ramatun yana kiciniya kwato matarsa daga hannunta ganin zata hallaka mata ita.

Muryansa kamar zaiy amon wuta yake cewa waime haka ramatu kasheta zakiyi dan ubanki...ki sake mun matata... ramatuuuuuu.
Ramatuuuu..kinci kutumar ubanki kenan wai shin kasheta zakayi.

Duk hayaniyar kukan hadiza dake tashi a wajen amma saida muryansa yafi nata karfi dan bakaramin tausayi da tsorota yaji yay ba.

Kokawar dayakeyi wajeb bambare ramatu yasaka ta dada haukacewa ta fara naushin shi dan sihirin an matane dan ta nisanceshi jinshi a kusa da ita yasaka tafara jin kamar kanta na ci da wuta sosai.

Abazata wata Razanannen ihu ya kufce mata, tafara ihu ahaukace tanata cewa wallhi saina kashe matarkaaaaa, saina haukatata kamar yadda na kashe ....nan ta fara lissafo sunayen mataye da kuma sauran ire iren mutanen da ta kashesu sanadiyar zaman aure.

Kusan a kangare alhaj kyari yake kallon bakin ramatu ayayinda take tonawa kanta asiri .

Banda salati da jinjina kai babu abunda masu aiki sukeyi. Bakin Alhaj a buɗe kamar an zazzago shi tsabar mamaki gashi duk jikinshi rawa yakeyi ya kasa tsayuwa waje guda danji yay kamar ma baisan ramatunba tsabar baqar muguntar daya ji ta shimfida a dorun kasa.

Agigice yay yunkurin mahaukata ya tureta akasa snn ya kwaco hadiza daga hannunta da kyar yawani irin rumgumeta sosai.

Mikewar ramatun keda wuya ta dawo kansa da tonon asirii Alhaj ka kwaceta a hannu na, ka kwaceta a hannu na to walh kaima saina kasheka. Tafara ihu hadiza ta makalkaleshi sai kuka takeyi sosai.

Duk wani abunda Alfa ya gaya musu akan ramatu shine ramatun take fadan musu da bakinta tare da wasu abubuwan da ma basu sani ba..

Rungume da matarsa hadiza suka tsaya cak Jikinshi na rawa rawa yanata kallon ramatu tana bayanin yadda zatay dashi da rayuwarsa dana yayansa tare da hadizar gabaki daya..

Hawayen da baiyi niyyar saukesu bane suka shiga saukowa jin hadiza na kuka ajikuminshi ahankli tanace mishi.."Wayoo Allah na shiga uku...Alhaj kaga irin Abunda ka jawo min ina zaman zaman na ka kawo matar da zataso ta rabani da rayuwata..
What have i done wrong to deserve this..nasan baka kaunar farin cikina amma banyi tsammanin cewa hatta rayuwata ma batada wani muhimmnci agareka ba..

Dada rungumarta yay sosai yanata jijjigata sigar lallashi hanklinsa ya mugun tashi da tunanin ko bata cikin hayyacinta ne yanzu.

Silent hawayensa suke saukowa akanta yanamai rarrashinta witout uttering a word ya jawota sukayi waje tanata kuka har ya kaita cikin dakinsa ya ajeta akan gado jikinshi na ɓari yabi ya kwanta kusa da ita muryansa a kasa cikin magiya yana cewa honeey Sweetheart please calm down okay.
Kidena kuka hadiza kinsan banason jin kukanki i promise u i wll deal with that evil woman wallhi yanxun nan zata barmin gidana. Saki uku zan mata i swear, and for ur sake i wll have her arrested bakiji tsoron danaji data shakemin ke ba..honey am soo sorry kinji ki dena kuka..i wll do sumting about it righ now and i promise you she wont go unpurnished

Yadda yake maganan da dukkan energynshi na tausayi ya mugun bata mamaki dan har ga Allah batasan da cewa mutum kamr mijinta yasan yadda ake lallami da karya murya kasa wa mace ba...

Sassauto da kukan tay tay shiru idanunta a lumshe batacemai uffan ba..

Jin saukar sanyin lips dinsa tayi akan goshinta
snn ya mike agaggauce ya zare towel din dake jikinshi ya sako wata short ya dora farar jallabiya akai..

Wayarsa ya daauka cikin gaggawa ya kira comandant yay report nan take aka turo masa da motar polisawa wanda zasu zo su capke ramatu a tafi da ita.

Dagata can fannin ramatun kuwa suna ficewa taji kanta na juyawa muryoyin wayanda ta kashe a sanadiyar zaman aure sune suka soma dawowa mata cikin kanta sai ji take kamar suna kiranta suna ce mata taho taho.

Ayanaayin datake ta balle waje da gudu tana cewa wayyo karku kasheni gani nan na zuwa..da dan uban gudu tabar cikin gidan wasu daga cikin masu aiki duk sun dauki videon ta awayoyinsu kowa nata shan mamakin abubuwan da ta fada.

Barinta gidan bada jimawa ba polisawa suka iso akaje har dakinta tare da alhaj kyari akayi bincike sosai..

aikuwa haka aka cicciro tarkacenta na tsafi dataxo dashu gidan awani jaka. Gasunan Hilimi guda su Madubi ne babyn rubber ne, kana nan gumaka da wanda aka dauresu da wanda aka caccaka musu allurai
Da wanda ta durkusa su akan giwarsu.

Haka polisawa suka tarkata komi suka tafi dashi yawon nemanta acikin dare aka kakkama wasu daga cikin manyan kawayenta aka kaisu CID ana musu tambayoyi.

Hadiza na kwance a dakinsa akan gado tay shiru cikin sauke ajiyar zuciya da mugun jin dadin yadda komi ya kammalu mata a cikin samun nasara harma fiye da yadda tayi tsammani aranta..

Duk wani hayaniyar da akeyi awaje na bincike bai darata bare ya dameta ba,agogo ta kalla ganin ana neman karfe 9 na dare tanakan kkrin gyara kwanciyarta taji an bude kofar ahankli.

Alhajn ne ya shigo yayo kanta da sassarfa muryansa a sanyaye yahau shafata cikin shauki yana cewa ohhh my hadiza my darling my honey, hadiza ta hade ranta cikin jan aji taki ta kulashi sam, A susuce ya kuma biyota yanamai kamota jikinta yana cewa come to me,come to dady ehnnn. Kiyi haquri mana hadizata toh ganan liktarki awaje na kirata tazo tadubaki u knw i care about, matso bakinta yay ya dora mata hot kiss..ahankli ta turesa muryanta salon kukan shagwaba tace nide tsoro nakeji Alhaj babu inda zanje nasani ko hada baki kayi da amaryanka zaku kasheni

Yace subhanalla hadiza i can neva do such thing pls trust me..yanxu haka polisawa nacan na neman shegiyar, trust ur man okay? Yana maganan tadada sauke mishi hawaye, muryanta kasa kasa gwanin tausayi tace How can i trust you bayan u went behind my back and marry her..ka riga ka nunamin baka sona..
Yauma Allah ne ya temake ni dana mutu, Dan Allah nide ka sawwake min tunda basona kakeyi ba tun kafun wata tazo ta kasheni abanza.

Hankalinsa a makurar tashe yajawota jikinshi
Ya dada saukar da muryansa kasa kasa yana lallamata da dukkan zuciyarsa tsabar yadda guilty consience din auro ramatun ke cinshi a zuciya.

Ya zakina fadin haka Wallhi inasonki hadiza ta bazan iya rayuwa babu ke ba...ahankli yake shafata da hannunshi yanamai sumulmukata ajikinshi. honey pls calm down kidena zancen sakin nan kinji? Nayi ganganci da rayuwarki buy I will make it upto to u i promise..kinason na canza miki motocinki?
How about some nice jeweries..ko vacation zamuje ne a kasar new zealand?..if u want i can give u all...Honey pls forgive me kinji...

Lumshe ido kawai hadiza tayi jin wani irin sanyi na mamayar zuciyarta irin wanda tamugun jimawa bataji irinsa arayuwrta ba..
kasa daurewa tay jin wayann kalamai na rarrashi na fitowa abakin sa with corect love and emphaty abunda da wuyane kagansa yanayi ma mace arayuwarsa

Wasu irin zafafan kisses yake sauke mata awuya ayayinda yake mata wnn magiyan Jin kamr ya gama kashe mata jiki yasakashi Dagota cak ya dorata akan cinyarsa baiyi wata wata ba ya hade bakinsu waje guda.

Cikin kasa iya daurewa da wann yanayi yasaka hadixa ta sakar masa jiki tanami maida masa martani acikin wata salo dayaso gigitamai yanayi dan arikice ya kwabe mata kayan jikinta batare da ya shirya ba itama nan da nan ta cire masa nasa kayan agaggauce kamar wano mayuncin zaki yayiwuf yakama nonowarta da suka sha gyara suka tsaya cur yahau jefasu abakinsa yanamai wasa mata dashi sosai.

daga nan wata iriyar zazzafar romance ce ta gauraye a tsakaninsu wanda rabonsa dayaji hadiza tana gigitasa da zazzafar romance mai shigewa hanyar jini da kunce duk wata notinan kwakwalwa tun lokcin farkon aurensu.

Kafin kace wani abu alhaj yarude yagigice ya rikice jikinsa na rawa sai uban gurnani da sumbatunsa kakeji na tashi a dakin shaff suka mance da batun wata likita dake can waje suka lula cikin wata duniyar soyayya mai mugun tsayawa arai dan kuwa kaf grop dinsu su biyar din nan babu wacce ta iya juya hanklin namiji akan gado kamar hadixa.



Ata bangaren shema'u kuwa ba gidanta direct ta wuceba saidata biya wajen meenal talba suka tattauna wata magana akan bacewar fadila a garin lagos da meenal din tay reporting jiya awajen polisawa...

Kwana biyun sosai take cikin fushi ganin aiki baya tafiya da sauri da sauri kamar yadda in da ace fadila tana nan komi ke tafiya mata dede kuma akan lokci.

Kullum acikin zagin fadilar takeyi a idon jama'a da sunan wai saurayine ya rudeta tabar aiki taje karuwanci.

Dake mutane dayawa basu san meya saka fadilar ta dena zuwa talba group of companies ba babu wani bincike ko kyakkwan zato duk suka soma daukar karayerayen dake cikon maganganun meenal din na cewa wai fadila tabi saurayine taje yawon karuwanci abunta.

Sosai meenal ta saka maganan nan a bakin kowa har wasu na tausaya mata atunanin su ko dan ta damu da rayuwar fadilar ce.

Tunda shema'u tazo take zuga meenal akan da tashare maganan fadilar kawai tunda ma ankawo mata sabuwar sectary idan ba haka ba zata jawo fadila tay black mailing inta da wani abu na zubar da mutunci tunda yanxu kowa yasan da cewa fadilar karuwa ce.

Ba iya wann ke damun meenal na harda rashin kula raininta da mijinta khaleel yakeyi kwana biyun nan. dan kota masa bori awaya baya kulata sosai wani bin ma da kyar yake kiranta awaya dan sosai yagaji da fitinarta dan tunda yaje abuja bata kyaleshi ba complain din yau daban na gobema daban ga baqar magana da nuna masa gadarar itama tasan right dinta sam ta hanasa samun nitsuwa ata can.


Wajajen karfe 8 na dare shemau ta dawo gidanta amugun gajiye ganin babu kowa agidan yasa ta wuce room dinta da tunanin hala mijinta yana masallacine tunda ya riga ya sanar da ita cewa yau din ranarsu ce babu inda zaiceshi.

Saida ta dawo gidan snn ta soma tunaninshi aranta ganin ko ina tsaf tsaf agyare yasa batay tunanin hafsa ba.

wanka ta fada domin ta zabge gajiyar data kwaso tabi ta hada da alwala


Tana fitowa ta tazo ta shimfida sallaya akasa ta fara biyan basukan salloli dake kanta tun na azahar har ishai wanda ya dauketa minti 10 kafin ta kammalasu.

Tana idarwa ko wani mint biyu bata kara ba ta bar wajen ta koma gaban
Mirror aranta tanata tunanin inda mijinta yaje da kuma irin karyan daya dace ta masa sanin cewa dolene yaji haushin ficewar datay da ssafe batare da izininsa ba ga tulin misscalls dinsa dataki ta amsa duk dama ya umarceta akan data jira.

Hakan yasaka tunda ta zauna agaban madubin tabi ta sake ranta tafara bida jikinta ahankli tana tattala ko ina da wasu hadaddun mayukan qamshi, bayan nan ta yi kwalliya tay kyau sosai ta nemi shararar nity red colour ta zura a sexy body inta ta hau gadonta ta kwanta tanata jiransa ya dawo daga masallaci dan tasan inhar ya jima haka bai shigo gidan ba hala ya tsaya bitan karatun qur'ani ne a masallaci.......

Dagata dayan bangaren kuwa tun lokcin ana kokarin ceto rayuwar mahaifyar hafsa engrn mahmud ya kirawo hafsat din gefe ya nitsar da ita da nasiha da kuma tambayoyi.

Kasancewarsa shi namiji ne kuma me ilimi da cikakken hankli yasaka ya shawo kanta acikin dan kankanin lokci harta gaya masa yadda sukayi da shemau alkcin data gaya mata batun rashin lafiyar mahaifiyarta.

Jin yanayin mummunan fassarar da kazafin da shemaun tay ma batun rashin lafiyar mahaifyr hafsat yasaka shi kasa boye mamakinsa a fuska
Se nanata mata tambayar yakeyi yana cewa shemaun ce tace miki karya kikeyi akan batin ciwon wai zaku hada bakine ku karbe kudinta keda mamanki?

Kan hafsat na kasa tace masa eh. Sai hawaye datake saukewa ganin already ransa ya sosu Duk dama taki sam taa fayyace masa komi da komi da shemau take mata agidan na mugunta duk gudun karta kunna wata fitina atsakaninsu a tunaninta inta fassara matarsa a sigar muguwa azzaluma sam bata masa adalci ba...

Tunda sukayi maganan sai bai karace mata komi ba, yana asibitin har saida likitoci suka fito sa news na cewa jikin umman nata yayi stabilising an saka mata engine taya nunfashi.

Duk wani kudaden da ake bukata shiya biya snn ya zauna tare da hafsa izuwa wajajen karfe takwas da rabi na dare snn yace mata shi zaai dawo lagos.

Baice mata zai dawo ba yaje motarsa ya dauko kudi sabbin dubu dubu harna naira dubu hamsin ya bata ta rike ahannunta yace mata izuwa jibi zai aiko wani yazo jigawan yadubasu.

Godiya hafsa ta dinga masa ta rakosa har bakin motarsa nan ma ya mammata nasiha akan
ta kula da mahaifyatta sosai, daga nan ya wuce airpot ransa cike da mamakin shemau, yana mai saka ran cewa ixuwa karfe sha daya na dare yaci ace ya iso gida dan yana da tambayoyi da yawa aransa dayake son shemaun ta amsa masa gameda yanayin zaman hafsa a karkashinsu....
SHARE PLEASE AND SHARE UR VIEWS ON WHATS COMING NEXT!!

CHAT SURAYYAHMS VIA
08060712446
[1/25, 2:15 AM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB...*_
_(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_


#ROMANCE
#FICTION
#ADULTHOOD
#SEXADDICTS
#WOMENPOWER

BY
_SURAYYAHMS_
_08060712446_


⏯️2️⃣4️⃣


Wani irin shirune yaratsa ilahirin gidan engr mahmud wajajen karfe tara nadare deidei shema'u marafa ta bude kofarta ta sauko izuwa kasa daga ita sai nitynta kafarta sanye da wata dunlop sleeper na fenty mai azaban laushi .

qamshin daddadar turaren na mousuf sexy data fetsa shike ratsa wajen ayayinda sanyin qamshin ke bibiyrta duk inda ta aje kafafunta,..

ahankli take saukowa tanamai bin kanta cikin sanyi da tattali, ixuwa yanzu babu wani abun da yake wakana acikin fadar zuciyarta face tunanin yadda komi zai kasance atabangaren kawarta hadiza dan tasan babban cakwakiyace suka ballo a tsakaninsu da hajiya ramatu.

kowani step ta sauke kan stairs din saita ja masa kasalallen numfashi, agatsine take kallon ihahirin wajen fuskarta a dan tamke cikin shan qamshi tana saukowa tana sauke kananan tsaki.

takaici da wata boyayyar hassada dake damun cikin zuciyarta shiyake dafata ataciki dan aranta ji kawai take kamar itace tayi asalin dacewa da matsayin da hadiza take ciki aynxu, wanda da ace Allah yabata irin shi da hala shikadai ne kawai yasan irin kalar mulki da baqar makircin da zata shimfida batare da neman shawarar kowa ba.

a tunaninta hadiza ba kalar macen da tadace ta zauna akan irin wann tarin dukiya bane, she is too soft hearted, snn ta fiye nuna rauninta akan batun aurenta,a duniya babban burin hadiza baifi taga tana samun cikakken kwanciyar hankli da kulawa a zaman aurenta kamar ko wace ƴa mace ba.

Ta lura cewa Sam sam damuwar hadiza bana kudi bane ko na siyasa bare neman suna....
dankuwa da damuwarta ne samun hakan da kokadan bazata dauki lkci wajen samunsu ba dan sosai take gewaye dashi.

ynzu gani take kamar ma hadizar ɓata lkcinta takeyi datake tsallake uban kayan duniya dake shinfide a gabanta take zaman aure har wai tanajin tsananin kishi da kuma nuna damuwarta akan lamarin samun kulawar mijinta.

Da wayann tunani mai ban takaici shemau ta karaso kasa cikin hadadden fankacecen falonsu daya cinye set din kujeru manya guda uku tanajin kamar qaddarar rayuwa ne bai mata adalci ba daya jefota gidan mijinta engrn mahmud snn ya jefa hadiza a matsayin da aganinta shine kawai ya dace da ita.

Kullum taje gidan hadiza sai tay imaginig inama ace itace acikin iriyar wann narkakken daula da kuwa babu abunda zai kaita mulki babu kuma abunda zaisakata ta damu da harkan mijinta koda kuwa mata dubu zai je ya auro.

Tsaki taja abayyane da tunanin halama ruwan ciki da tsoro bazai kyalei hadizan ta gabatar da shirinsu akan ramatu kamar yadda ya kamata ba.

tay tunanin kirarta awaya taji me ake ciki amma gudun zargi yasata fasa ga boyayyar sauran burburshin damuwar datakeji aranta na hassada da rainakon irin rayuwar da Allah ya zaɓa mata take ciki ayaxu.

Isowarta falon bata tsaya a ko ina ba sai gaban wata 35 inches dinning tabl dinsu da aka kawata shi da golden chairs..

Brown colour Wamers din dake kai tahau budewa tana kallon abunda ke ciki sama sama.. ganin jollof spagtheti da sardines tay aciki har yanxu yana zuba qamshi da turiri alaman da zafinsa wanda hakan yasata sakejan wata kakkauran tsaki.

Daga kanta sama tay da wani irin daurarren fuska ta dubi hanyar dayabi kan matalakala tana shirin zata kwalawa hafsat kira ta balbaleta sai kuma ta tuna cewa hala mijinta zai iya shigowa akowani lkci karya zo kuma yagansu ahaka dan batason yagani ko yasan dalilin daya saka yawancin masu aikinsu basu jimawa taredasu suke guduwa subar masu gidan,kuma bakomi bane face tsabar iya baqin hali tareda rashin imani da tsananin muguntar da shemau take wainasu aciki.

Daga aurensu izuwa yanxu da suke neman cika shekara na uku sunyi masu aikatau sunkai arbain da takwas..

Wasu kwana uku kacal sukanji sun gaji, wasu kuma basa iyayin sati da shemau agidan axaban muguntarta yakansa su gudu, wasu kuma da Allah ya isa kawai suke rabuwa.

Koda ta duba jollof din taliyar tagani, wani irin Karkada kanta tay sigar mugunta alaman gobe zaki gamu dani in nan.

duk a tunaninta wa ita hafsat ta ajewa abincin dankuwa ta tsani ganin spagheti jollof arayuwarta takance masa abincin matsiyata ne da yan yunwa...

duk dai haka tagama bambaminta ta zauna akan chair din, can sai ta fara zubawa da kadan kadan a plate hartaci iya cinta takoshi dan kuwa hafsat din bakaramin iya girki tayi ba.

Tana tsaki tana cin abincin kafin kace wani abu hartayi tass tassss da coolern batarage komi acikinsa ba.

Bayan nan Zama tay na kusan awa guda tana daddanna remote na tv, lkncin har 9 na dare ya wuce ga wani irin gajiya da bacci dake fizgarta da karfi mijinta bai shigo ba.

10:30 nayi jin baccin ya fara figarta da karfi yasata kashe tvn tana hamma ta wuce dakinta ta kwanta, nan ma Banda juyi akan gadon babu abinda takeyi sai yan sake sake dake bijirowa kwakwlrta, duk tayi tunanin duniyan nan na inda mijinta zai shiga bata gano ba harta gaji.

minti kadan intay juyi zata daga kanta takalli agogo, har can da dare ya nutsa ganin ƙarfe goma ya wuce da mintina arbain da biyar still baidawo ba snn taji hanklinta sam bai wani kwanta da shirunsan ba, shi mutum wanda inya jima a wajene yakai irin takwas da rabi xuwa tara, amma bayan nan bai taɓa kaiwa wann lkcin awaje ba..

Wayarta ta dauka for the last time ta kuma kirar layinsa haryanzu baya shiga,da haushin hakan ta yasar da wayar gefe ta dan mirgina bada jimawa ba bacci mai nauyi yay awon gaba da ita.

Wajajen 11:45 jirgin dake dauke da engrn mahmud ya iso garin lagos dake dare ne direct ya nufi gidansa abunsa.

Koda ya shigo gidan yaji shiru bangarensa kawai ya shiga yay wanka dan ya samu

Please Login or Register in order to submit comment