You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauti da kara Fadi take"Don Allah kayi hakuri..Don Darajan iyayenka kayi hakuri..!
Wlh kadan ya rage bai Bugama wani mai adaidaita ba saboda yadda Ihun ya shiga kansa ransa yakai kololuwar baci in ya zauna acikin motan nan zai iya ma yarinyar nan Lahani yasa baisan sadda ya Gangara gefen kwalta ba ya faka Motar a fusace ya Bude bangaransa ya fita Amina kuwa ta zata ita ya tsaya ya Daka yasa ta koma ta Lafe jikin kofa tana Rufe bakinta Cikin kuka sai taga ya fita ya Rufe kofar da karfi kamar zai ballah.

Bayan Motar ya koma ya Dafe kansa cikin wani yanayi yake maimaita Hasbunallahi wani'imal wakeel..!
Bai saurara ba sai da yaji ya Dawo Cikin natsuwarsa ya zai yi da wannan Fitinanniyar yarinyar da ke neman chajamai kai..?
Wlh bazai iya zama da yarinyar nan ba Tun aTarihin rayuwarsa bai taba Daga Sautinsa irin na yau ba bai taba Fada irin na yau ba ko Sakina ta batamai rai baya Biyemata yana da Hakuri da kawaici sai ta Dade tana abunta bai Dago ya kalleta ba shi in ya tashi nashi Lokaci Daya zai yi shikenan kuma ya huce ballatana Sarood da bata da Hayaniya banda ma dan matsalan da suka samu da zasu taho Bikin nan.
Karamin Tsaki yaja kawai afili yana kokarin samo ma kansa mafita Visar sa zai yi kokari ta fito Cikin Satin nan ya kara gaba kafin yarinyar nan ta kai shi bango yayi mata Dukan mutuwa Tunda ya Lura Baba mallam ya gama batata sannan su jafar ba Hukunci suke mata ba wani Burauban nata Harda iskanci da rashin natsuwa.
Ya lura ba yarinta bane Tsabar iskanci ne da samun wuri banda haka kamar ita tasan ta iya waya da Saurayi a boye har suna haduwa..?ai shi sanda Mallam ke fadamai yana ta fadin yarinta ke damunta jinsa kawai yake wannan abun ya wuce yaro yayi sa tana Sane da duk abunda ta aikata shine Hajiya ke son ya kwasheta ya kaita Madina wlh ya tabbata watarana sai ta jawo silar abunda zai sa a Dauresa in ma bata yi sanadiyar barowarsa kasar ba gabadaya bama.

Yana cikin wannan Tunanin wayarsa Dake gaban aljihun rigarsa ta Dauki kara,Daukota yayi ganin mai kirasa yasa ya saki ajiyar rai da salama da sauri ya Daga kiran yana Fadin"Ka kira alokacin Dayace Aliyu..!
Ko sallama bai tsaya yayimai ba Tsabar Tashin hankali
Aliyu dake zaune afalon gidansa ya gyara zama yana fadin"Shehi ango..Angon Sixty.. Tsabar Rudewar ne yasa yau Shehi ya manta da sallama..?

Ya fada cikin shakiyancinsa Umar ya Saki karamin Tsaki kafin yace"Salamu alaikum..Na sha"afa ne Aliyu kaina ya Fara ciwo wlh..!
Aliyu yajisa cikin wani yanayi yasa yace"Meya faru ne..?
Baka koma gidan bane ko baka je gidan Mallam din bane..?
Daman sunyi mgana Kafin ya fita Daga gida
Cikin Kar ya Sauti yace"Na je gidan mallam..Bakasan wani abu ba..yarinyar nan fa suka hado da ita Aliyu..!
Aliyu yace"Wata yarinya..?
Danmallam ya Dafe kansa kafin yace"Kazamar yarinyar nan mana..!
Aliyu yace"Nifa ban gane wata yarinya ba Sakina wai kake mgana..?
Yafada cikin Danne Dariyansa Umar ransa ya baci cikin Haushi yace"Sakinar ce kazama Aliyu..?
Amina fa nake maka mgana da nace maka Hajiya ta matsa sai ta tare yau din nan abu kamar za"a gudu..Ko kuma ana jirana Aliyu..!
Aliyu ya saki yar dariya kafin yace"Au to..Kaine ka fadi sunan yarinya kaki kana ta fadamin kazama ni to ya zan yi na ganeta..?
Wai yanzu kana nufin kuna tare..?To tana ina..?
Yafada daidai sanda Aliya matarsa ta shigo Falon ganin yadda yake zaune yana waya ne yasa jikinta ya bata da Umar yake mgana Hararansa take ta kasan ido domin itama tashin Datayi Da Sakina taje Daki sukayi mgana Wlh tafi sakina Jin kishi da wannan auran Rainin da Umar yayi haba in ba Raini ba wannan kazamar yarinyar ta ina zata iya hada miji da ita komawa baya ne wlh,Ta fadama Sakina kada ta Sake ta bari ta shigar mata Dakin miji sai ta zata sun zama Daya da ita kenan sai dai ta nemi Dakin kwana Tun da Sakinar ta fadamata Labarin Tarewar ranta yake bace Har Aliyun taji Shima Haushinsa take ji tunda ya shigo take fadin rai yana ganin haka shima ya shareta bai bi ta kanta ba.
Ganin yadda ta zubamai ido ne Umar na fadin"Wlh Aliyu yau kadai dana Dauko yarinyar nan har na fara gajiya..Can u just imaging kuka take min amota har tana wayyo Allanta har barazanar kaita gidam mari nayi taki yin shuru kafadamin ya zanyi..Wlh kaina har ya fara ciwo na rasa ya zanyi..?

Yafada lokaci Daya yana Dafe kansa dayake Saramai Tun dazu Aliyu, Aliya yaga tana kallonsa yasa ya mike yana Fadin"Shehi me yayi zafi..?
Kai da zakayi lallashi sai ka Bige da zuwa gidan mari..!
Yafada yana Dariya Lokaci Daya yana Ficewa daga Falon zuwa bedroom dinsa yana jinta tana raka sa da fadin"Girma dai ya fadi wlh..!
Shi yasan kan mganar domin tun da yadawo take sakin tsaki Lokaci bayan Lokaci sai tace an dai ji kunyar Wlh mutum ya rasa wazai aura sai yar Cikinsa ko batayi mgana ba yasan da Umar take so take ya tankata shima yau gidan nasu ya koma yakin Biyafara banda mata ma mata ne ina Ruwanki da batun gidan wata kai abun na bashi mamaki..!
Sai da ya shiga Dakinsa ya kulle sannan yace"Ina jinka..na baro Falo ne..kasan nima yau gidana irin gidanka ne..Aliya na taya Sakina kishin ka yo musu amarya da karamar yarinya wai kama raina su..!
Ya karishe fada yana yar Dariya Umar ya saki hanci kafin yace"Bangane tana taya ta Kishi ba..!?
Nan Aliyu ya labartamai abunda ya faru Danmallam ya shafa gemunsa yana Fadin"Meyasa mata suke da karamin Tunani ne..?,Ita Aliya Daman haka take..!To yau in kai in zaka kara aure ya kenan..?
Inaga baka ba kara aure Aliyu..!
Aliyu yace"Wane ita..?Har ta isa wlh tallahi sai dai in banga wacce nake so ba..Ina da sha"awar kara aure Shehi in kaga ban yi ba to hakan na cikin Abunda Allah ya Tsaramin ne..!
Umar yace"Lalle akwai yaki..Aliya zata cin na ma gidanka wuta..!
Yafada yana yar dariya Aliyu yace"In ta fasa..Ni fa ba irinka bane da zan zauna anamin iskanci ban ci ubam Mutum ba..Wlh ban kai ka Hakuri ba Umar..Ina da kawaici ammh ba kowani Lokaci ba yanzun ma Daka ga na kyaleta Lokaci na bata in ta bari na tankamata sai ta raina kanta ni ba Sakaran Namiji bane ka sani..!
Umar na yar dariya yace"Allah dai ya kyauta..!
Aliyu ya amsa da Ameen kafin yace"Wai ina ka barta ne..?
Umar yace"Tana cikin mota..Kaina ya fara ciwo wlh kukanta zai sakamin Dagaaawar jini Aliyu..!
Agogon Wayarsa Aliyu ya Duba kafin ya maida wayar kunnensa yana Fadin"Shehi Dare fa yayi..Pass 9 goma ta kusa..ka lallabata tayi hakuri kasan Rabuwa da gida..kuma kada ka manta aure yakin mata..Sannan ita ga yadda abubuwa suka zo shehi Dole tayi kuka..Gata yarinya ce karama Kasan kaima sai ka kara Hakurinka sannan Hajiya da Mallam sun zama gatanga gareta Dolene ko baka so kayi Hakuri da ita na dan Lokaci ne nan da wani Lokacin in ka fara cin amarci kana jin Dadinta zaka bani Labari mutumina..!
Danmmalan ya saki Tsaki kafin yace"Ammh dai Aliyu kai mutumin banza ne.. ko..?
Bai jira amsar sa ba ya katse kiran yana Fadin"Ko kunya Bai ji..Yana mganar wannan abun da wannan yarinyar..!
Tsaki yayi kasa kasa kafin ya maida wayarsa aljihu sai da ya bata Lokaci kafin ya Dawo Motar budewa yayi ya lekata ganinta nan kasan kujeran ta Dunkule yasa ya shigo Motar karan Rufe motar ne ya Dawo da ita cikin Tunanin data Fada na gata chan agidan kangararru an sakamata mari.
Tana ganinsa ta zabura tana Kokarin kara sakamai kuka wani banzan kallo yayi mata kafin yace"Ki bari naji ihim dinki ki gani..Wlh na rantse yau sai kin kwana gidan mari karyan iskanci kike da rashin kunya chan akwai Uban ninki a tacewa..!
Bakinta ta kama tana Hawaye Tsawa ya Daka mata kafin yace"Tashi ki hau Kujera..!
Da Sauri jikinta na Rawa ta koma ta zauna tana Danne Bakinta ko kara kallonta bai yi ba ya Tada Motar suka fara tafiya Amina ko Tsoron za"a kaita gidan mari ga kuma tsoron zata je wani gidan inda ba Hamida ba Hanne Ta tsorata dashi duk muguntar su ya Jafar tana ganin ya Darasu tunda su basu taba cewa zasu kaita gidan mari ba,Shiyasa duk son kukanta ta bame Bakinta gam sai da na zucci a haka suka iso gidan Danmallam Dake kofar arewa.
Yana hon megadi yazo ya Budemai get din gidan ya sulala da Motarsa parking space sai da ya gama Daidaita motar kana ya kashe ta ya Fito har Lokacin Amina na zaune ta kasa Motsi sai da ya fita yana gaisawa da Buzun megadinsa yaga bata fito ba kai ya girgiza Booth ya Bude ya Fito da Kayanta ya ijiyesu nan Kofar Falon kafin ya isa wajen motar ya Bude mata Murfin yana fadin"Sai nace ki fito sannan zaki fito ko me kike nufi..?
Dasauri ta fito tana faman sharan kwallah ko kallonta bai yi ba yayi gaba ya barta nan tsaye yana kallonta bai ce mata komai ba ita kuma Tsoro take ji kada tayi wani abu yace zai kaita gidan mari duk da bata taba zuwa ba,Ai Baba mallam na kai ziyara Lokaci bayan Lokaci yana zuwa tare da Aba ko su ya shamsu har jawad an sha zuwa dashi tana jin labarin yadda ake gana musu azaba abakinsu ina zata yi wani abu wannam mara Imanin ya mikata chan kafin Su Baba mallam su ji labari su je su karbota ta kusa mutuwa..!
Shi kuma yana ganinta Tsaye yayi kamar bai ganta ba Yasan in ya bar mata kayan bazata iya Dauka ba yasa ya Fara Dauka yana shigar mata dasu Cikin Falon gidan
Yazo Daukan na karshe ne ya Dago yana kallonta cikin Haushinta yace'"Shima sai nazo na kama hannunki na shigar dake gidan sannan zaki shiga..?
Jin haka yasa tayi saurin wucewa gaba shi kuma yabi bayanta.
Tana shigowa Falon suka hada ido da Sakina data fito daga Dakinta Cikin kwalliyarta Less ta saka riga da Sikat sun kamata ta shaba kwalliya kamar wacce zata je gasan kyau na Duniya bakinta Cingam ne tana Taunawa kas kas kafarta cikin wani takalmi mai Dubu kallon kallon suka tsaya yi da Amina cikin kyama da wani Tsana take kallonta ita kuma Amina sai ta kasa gaba ballatana baya saboda ganin Sakina shima daya shigo ya ganta sai yayi kamar bai ganta ba Tun bayan tafiyar Anty mgana bata Kara Hadasu ba Dakinta ta shige shima ya shiga nasa har ya je amsa kiran Mallam bai sata a ido ba jidalin Dake kansa sun ishesa inda zata gane da ta barsa ma yaji da abunda ke Damunsa..!
Ta gefen Amina ya raba ya wuce ko barayin Sakina bai kallah ba Dakinsa ya Nufa zai Bude yaji a kulle Cikin mamaki ya juyo yana kallon Sakina kafin yayi mgana ta wucesa zuwa kan Daya daga cikin kujerun falon ta Zauna ta Dora kafa Daya kan Daya Tana cigaba da Taunan cingam tana kas kas..!
Ransa ya baci ganin Amina Tsaye awajen yasa ya sausauta Cikin sanyinsa yace"Waya kulle Dakin nan Sakina..?
Ina key din..?
Sakina ta kallesa Cikin wani Bakinciki yau ita ce ke shakan Numfashi da wannan yarinya a matsayin Mijinsu Daya gaskiya Umar ya gama Cutar da ita.
Kai ta kauda batayi mgana ba ya kara Sausauta Murya yana fadin"bada ke nake mgana ba Sakina..?
Sakina ta wani kallesa a karkace kafin ta Hura bakinta ta saki kwan cingam din Dake Binta ta wani Rausayar Dakai Cikin Wani yanayi tace"Makullin na hannuna..Ni kuma na kulle Dakin..!
Bai ji mamaki daman yasan ita zata kulle ba kowa ba cikin son kara nazarinta yace"Saboda me yasa kika Kulle Dakin bayan na Fadamiki Hajiya tace yarinyar nan ta zauna aciki..!
Sakina ranta daman yana bace ne ga Kishi kawai sai ta mike tana fadin"Wlh Umar baka isa ka Tozartani ba..Ni zaka wulakanta bayan auran wannan yarinyar da kayi ban ce komai ba..Shine saboda a kara Kuntatamin sai ace Dakin mijina zata zauna..? To wlh bazata sabu ba...Ko Mijin bazan raba da wannan kuchakar yarinyar ba ballatana Dakin miji..Bazai taba yuyu ba..!
Tafada tana bayyana bacin ranta Hannu kawai ya kama a kirji yana kallonta Amina ma ita take kallo ita aranta ma Dadi taji Allah yasa taki Bude Dakin ya maidata gida.
Cikin Kaushinsa yace"To yanzu ya kike son ayi sakina..?
Kai Tsaye tace"kai ka sani..!
Daga haka ta koma ta zauna tana Jijjiga kafa Lokaci Daya tana Hararan Amina Dake ta sharan kwallah.
Bai ce komai ba ya kalli Amina yana nuna mata hanyar Dakin Sakina Lokaci daya yace"Zo ki wuce..!

Kamar tayi mgana sai kuma ta fasa ganin yana mata wani kallo Sakina da mamakinsa ya cikata na ganin Dakin daya nuna ma Amina Dakinta ne.
Sai dai batayi mgana ba sai da taga Aminar ta nufi bedroom dinta sannan ta Mike kamar kububuwa sai gata gaban Amina ta tare gabanta Cikin Zare mata ido tace"Kan uba..Badai Dakina ba..Allah ya Tsareni wannan kazamar ta shigarmin Daki..!
Sai Amina ta Tsaya ta kasa gaba ballatana baya Umar yana Tsaye inda yake yana kallon Sakina da Idanuwansa da suke kokarin bayyana yanayin dayake ciki.
Kokarin Daidaita kansa yake yi yasa bai yi mgana ba Sai da yaga Sakina ta Hankada Amina sai da ta kusa kaiwa kasa tayi Saurin Dafa Kujeran Dinning
Sakinar kuma ta jawo kofarta ta Rufe da makulli tana fadin"Yau ni Sakina naga Rainin hankali..Dakin nawa zaka saka Kishiyata..?Allah ya tsareni ma da ta zama kishiyata Har Abada..!
Take fada tana jijjigan Jikinta Danmallan yayi tsai yana kallon wani waje bai yi mgana ba.
Babu makullin daki ko daya a hannunsa na Gidan duka yana hannun sakina Sauran kuma suna gida wajen Hajiya,sannan akwai wajen Jafar,Shi bai taba Hausan makullayen gidan sa su zauna awajensa ba.
Bayason su yi wani abu gaban wannan yarinyar girmansa ya Zube shiyasa ya dinga maimaita sunan Allah har ya samu ransa yadan sauka Cikin Sanyinsa ya juya yana kallon Sakina kafin ya mika mata hannu yana Fadin'"Naji bazata zauna adakina ba..da Dakin ki ba.Bani key din Dakin Sarood sai ta zauna aciki..!
Shekeke take kallonsa sai dai taji shakkansa Lokacin daya kara sakarmata wani Kallo yana fadin"Ko shima bazaki bani ba..?
Jin haka yasa ta nufi kofar Dakin ta saka makulli ta Bude kada ta basa ya Bude Dakinsa tunda duka suna Hade ne waje daya gwara Dakin Sarood din ita kam banda nata Dakin kuma shima ban da nashi.
Tana gama Bude Dakin ta koma gefe tana kallonsa bai kara ko kallon inda take ba ya kalli Amina Dake dannen kukanta yace"Shiga..!
Ba musu ta shige shi kuma ya Dauki ghana dinta guda Biyu yabi bayanta Tana Tsaye Tsakiyar Dakin ko zama ta kasa yi bai ko kalleta ba ya ijiyemata kayanta nan ya fice tana bin Dakin da kallo ya sake shigowa ya ijiye mata Dayan ghana din ya Sake fita wannan karon har yana bame mata Kofar ta bisa da kallon ganin ya Ficen ne yasa ta sulale nan kasan Cafet din Dake Dakin ta hada kanta da Bango ta fashe da kuka,kukan da ko Rasuwar yaya batayisa ba kukan kewa da rasa wani abu a Rayuwa ta yaya zata fara zama in da ba hanne ba Hamida ba mamanmu.!
Tuna haka yasa ta kara sakin wani kukan ta dora kanta jikin gadon ta cigaba da Rera kukanta,Bata ma ji shigowarsa ba sai karan bude kofa taji tana Bude ido ta gansa ya shige wani kofa Dake Dakin ya kullo,sai tayi tsit tana ware idonta da sukayi zuru zuru da kuka duk ta wani yarkace ko motsi bata karayi ba ita azatonta uwar Daka ya shiga shiyasa ta kasa motsi sai chan taga ya fito Fuskarsa na Digan ruwa alamun alwala yayi ko barayinta bai kara kallah ba ya sake Ficewa ya bame mata kofar yana Fita ta Dora hannu akanta ta fashe da kuka tana fadin"Na shiga uku ni Amina..!
Sai kuka harda Birgima a kasa kamar wata yar yarinya ita kadai bamai lallashinta.
Tanayi tana rufe bakinta kada ya jiyota ya shigo,yadda take kukan sai ka Tsausayamata kuka ne Dake fitowa Daga kasan ranta.

Sakina tana tsaye tana jijjiga jikinta ya fito nan saman cafet din falon ya Daidai gabas ya tada sallah Shafa"i da wuturi yayi sannan ya zauna yana Tasbihi da hannayensa ko barayin Sakina bai sake kalla ba har ya gama yayi addu"a ya shafa Rigarsa ya Cire ya rataye ta nan saman kujera daga shi sai dogon wando ya samu Filon filon kujerun ya jera saman kujera 3siter ya kwanta Kansa na kallon Rufin Falon hannayensa kuma ya Saka ya Dunkule su waje daya ya Dora su saman Filo kansa na kai.
Wayarsa daya ciro cikin aljihun rigarsa ya ijiyeta nan saman center Table din Dake falon,Sakina sai Binsa take da kallo ta kasa mgana sai alokacin kuma jikinta yayi sanyi mganganun Anty suna dawo mata da tace kadatayi wani abun da ran Umar zai baci tabi komai a sannu ammh ita Kishi ya Rufe mata ido da kuma mgaganun Aliya dazu da sukayi mgana ita ta kara tunzurata.
Takowa ta farayi cikin Falon Cikin Sanyin jiki a gabansa ta Tsaya tana kallonsa kafin ta sauke numfashi tace"Bari na bude maka Dakin ka..!
Baice mata komai ba ta koma ta Bude Dakin sannan ta Dawo gabansa tana Fadin"tashi ka shiga ciki Habibi..!
Mikewa yayi ta Dauka zai shiga Cikin ne sai taga ya isa ma kunni wutar Falon ya kashe duhu ya gauraye wajen gabadaya ido ta zaro tana Fadin"Habibi...!
Ko kallonta bai yi ba ya koma ya kwanta Har da Juya mata baya Sakina taji ta Muzanta Sai ta Duka gaban inda yake kwance tana saka hannu ta riko hannunsa tana fadin"Habibi..Dom...!

"In kika kara tabani Sakina wlh tallahi zan sharara miki mari..Zaki ga Oder side of me da baki taba gani ba..!

Ya katseta Cikin Tsawa Daidai Lokacin daya juyo yana kallonta Cikin hasken Dake shigowa ta windows din Falon Baya Sakina taja tana zaro ido kafin tace"Ni zaka mara Habibi..?
Ni kace zaka mara saboda ka kawo wannan kazamar yarinyar nace bazata shiga Dakin ka ba..?
Wani matsiyacin kallo yake binta dashi bayaso yayi wani abu Saboda Amina na gidan yasa ya koma ya kwanta ai sai Sakina ta saka kuka ta Durkushe a wajen tana Fadin"Shikenan..Nagode yanzu har ka fara wulakantani saboda wannan yarinyar Habibi..?
Saboda na hana ta shiga Dakin ka kakemin ihu haka..?
Yar Cikin ka ce fa karamar yarinya da bata isheka komai ba..!

"Karamar yarinyar da kike mgana akanta yanzu Daya kike da ita a wajena Sakina..Dani da mutanen da sukasan abunda suke yi..!

Ya katseta a fusace,Sakina ta ji kukanta ya Tsaya Cikin mamaki tace"Daya fa take dani kace Umar..?
Saboda ma ya tabbatar mata yasa ya Mike Zaune yana fadin"Eh..Kamar yadda kike matata haka take matata..Kamar yadda igiya uku ta hau kanki..Nawa itama suna kanta Sakina..Saboda haka dake da ita Daya kuke awajena..!
Galala tayi tana Binsa da kallo Kafin tatashi Fuuu ta je ta kunna wuta Haske ya bayyana kafin ta Dawo gabansa tana kallonsa cikin karaji tace"Maimata abunda ka fada..Dazu baka kallon idona yanzu kuma idona na cikin naka nake so ka maimata Umar..!
Karamin Tsaki yaja ya koma ya kwanta yana Fadin"Sai ki sani na maimaita din..!
Sakina idonta ya rufe ta mike tana Fadin"Har gaban abada bazan zama Daya da wannan kazamar yarinyar ba..Wacece ita..?Yaushe take..?
Wlh ita bata isa in yi zaman kishi da ita ba in nayi da Sarood ita bata kai wannan matsiyan ba..Amina ba Sa"an auranka bace Umar ba sa"an zaman kishina bace..!

Kamar ya Rufe ta da Duka haka yake ji kai Tsaye ya mike zaune yana kallonta yace"Wacece ita kike tambaya Sakina..?
Kinsan wacece ita ai..in ma kin manta bari na tuna miki..Ita diyar BABA SA"IDU ce kuma Diyar YAYA ce..Sannan Unarnin HAJIYA DA MALLAN NE..Ta riga ta Hada mutane masu Daraja atare dani..Ko ba aure Tsakanina da ita ni me rike Amina ne acikin gidan nan Sakina ballatana da aure Tsakanina da ita in kina Tunanin Zata bar gidan nan to kidaina kamar yadda zaki zauna itama haka zata zauna..Kuma da kike mganar Ita ba sa'an aurena bace..Daman sai sa"an auranka zaka aura..?
Wlh in da ana bin chanchanta har Abada Dake sakina baki CHANCHANTA dani ba..!

Yafada yana nuna ta da yatsa cikin fushi ido ta zaro mgana take son yi ya hanata Cikin Kaushinsa yace"Ba shawara nake nbaki ba..ba kuma Umarni ba.ki natsu ki zauna lafiya da yarinyar nan domin zamanta Daram acikin gidanan in kika ki natsuwa ke kika sani ni dai tafiya zan yi..in kin kama girmanki ta girmamaki in baki kama ba ta fiki iskanci sai ku goga wata dai bata isa ta kori wata ba..!

Sakina taji jikinta yayi sanyi me kalaman Umar suke nufi..!?
Gabanta ya fadi kada kishinta ya Bullo mata wani sabon aiki Dakyar ta Hadiye miyau tana Sharan kwallah tace"To don Allah in ka tashi tafiya ka tafi dani Habibi..wlh bazan iya zama da yarinyar nan anan gidan ba..!

Umar ya kalleta daga sama har kasa kafin ya koma ya kwanta yana Fadin"Sakina na yi rantsuwan bazaki koma ba yanzu
Ki tashi ki bani waje bana son yawan mgana kaina ya riga ya fara ciwo..Kada zamanki agabana yasa na rasa Cont????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  rol dina..!
Batayi musu ba ta mike Cikin kaushinsa yace"Ki kashe min hasken da kika kunna min..!

Ta juyo tana kallonsa kafin tace"Bazaka ko..!
Kallon da ya bita dashi ne yasa tayi Saurin yin gaba Hasken ta kashemai ta Fada Dakinta gabanta na Fadi Gabadaya mganar Umar na ita ma bata Chachanta dashi ba ya Tsorata ta In ta Kira Anty ta Fadamata tasan sai taci Zagi Allah yasa ba abunda suka Binne bane yake son ya bayyana ba..
Da sun shiga uku kuwa..!
Mafarin komai in ya lalace ai sun gama yawo..!







*28 September 2022*
*Janafty*

*TFZB2002*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*

Karfe hudu na asuba ya farka kamar yadda ya saba,Kwata kwata bai ji dadin barcin ba akan kujera sannan zuciyarsa tana cunkushe ne ya dade bai samu barci ba kuma kasala ya rufeshi ya kasa tashi yayi ko nafila ne.
Sai da asuban ya shiga dakin nasa yayi wanka ya dauro alwala Jallabiya mai ruwan madara ya saka da Hula ya Dau cashabahansa ya fice zuwa masallaci ko ta kan Sakina bai bi ba ballatana wata Amina.
Sai shidda saura ya shigo gidan,yana shigowa tsakiyar falon suka ci karo da Sakina ta fito daga dakinta yarkace yarkace da ita idanuwanta sun kumbura sannan kanta ba dankwali kanta ba kitso gashinta ya baje kansa tana sanye da rigar barci mai taushi iyakarta gwiwanta ayanayin yadda yaganta sai da ya kara kallonta ganin yanayinta.
Kamar zai mata mgana sai kuma ya fasa ya dauke kansa zai shiga Dakinsa Da hanzari ta daga kafa zata bisa jin takunta yasa ya Dakata bai juyo ba taji muryansa yana fadin"Ina zaki..?

Cak ta tsaya jikinta yayi sanyi kanta ta maida kasa kafin tace"Da..Dama zan gaisheka ne Habibi..!
Shuru yayi mata bai yi mgana ba taga yana shirin shigewa ya barta yasa tayi saurin cewa"Ina kwana Habibi..!
Kamar bazai tankata ba sai kuma ya amsata kamar baya so da Lafiya Lokaci daya ya shige dakin nasa ya banko mata kofa saman fuskarta baya taja Hannunta Dafe da kirji tana fadin
"Na shiga uku ni Sakina..!

Kasa tsayuwa tayi kamar mahaukaciya haka ta kwashi gudu zuwa Dakinta saman gadonta ta koma ta Zauna gabanta na fadi meta aikata kenan .?Jiya ko barci batayi ba in ta tuna Kalaman Umar zuwa gareta.
Taso ta kira Anty tun jiyan sai ta kasa Tasab Halin Anty in taji abunda ta aikaata sai ta Zageta saboda haushi Saboda sai da ta tausheta akan kada tayi wani abu sai ta tambayeta yanzu in ta Kirata ta fadamata abunda ya faru ta tabbata sai Anty ta mata fada sosai.
Sai dai bata da wata mafita Anty zata kira ta fadamata abunda ke faruwa ko zata samamata mafita.
Wajen shidda da rabi ta dokama Anty Amarya kira tun da taga kiran tasan ba Lafiya cikin Tashin hankali ta Daga kiran tana fadin"Sakina kada ki fadamin kin kara aikata sakarcin naki ..?
Sakina tafara Fiki Fiki da ido tana fadin"Anty...!
"Don ubanki ki fadamin abunda ya faru..!
Sakina cikin sanyi ta fara fadamata Duk abunda ya faru jiya har zuwa yau Anty Amarya ta mike Har hijabin jikinta datayi sallar asuba na neman Hardeta ta fadi ta Dafe jikin gadonta

Please Login or Register in order to submit comment