You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng [11/14, 11:41 AM] Salmah Queen💍💅🏽: 👩🏻‍🎓 *Barrister Salmah* 👩🏻‍🎓


_*Written by Salmah Queen*_💍💅🏽



🇳🇬 _God bless Nigeria_🇳🇬




® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com




_*Bismillahir rah manirrahim da sunan Allah me rahma mai jin kai zan fara rubuta wannan littafin Wanda yake cike da fad'akarwa da gami da ilman tarwa Allah ubangiji ya ban ikon kammala shi ameen*_



Page 1-5



Yau take talata da misalin 9:am a garin abuja cikin eagle square hall cike yake da mutane maza da mata kowanne ka ganshi fuskar sa d'auke take cike da farin ciki,
Hall din ne yayi shiru sakamakon tahowar shugaban baristocin nigeria ya k'araso sakamakon kiran da akai masa domin yin jawabi tare da rantsar da d'aliban

Tafi jama'ar wajen suka d'auka jikake raf raf raf d'aga hannun sa yayi alamun jinjina da nuna farin cikin,
Shiru ne ya jiyar ci hall d'in fara jawabin sa yayi ,sai da ya dau lokaci yana jawabi tare da nasiha ga d'aliban

Kiran d'aliban akai domin su fito a rantsar da su

Jere suke ciki kayan su na baristoci sun ja dogon layi su hamisin da tak'was abin gwanin sha'awa hannun su d'auke su ke da award,

Bazan iya misalta irin farin cikin dake d'auke akan fuskokin su ba

Gaba d'aya naji muryoyin su sun had'a baki suna magana nan take na maida hankalina wajen su,

"Munyi alkawari zamu kasance masu gaskiya da amana a cikin ayyukan mu ba son kai ko rashin adalci"

Gaba d'aya hall din ya dau tafi jikake raf! raf!! raf!!! Haka suka cigaba da yiwa k'asa alkawarurruka sannan nan suka fara sakkowa daga kan steps din zuwa wajen 'yan uwan su cike da farin ciki kasancewar su baristoci.

Wata matashiyar budurwa nagano tafe take cikin nutsuwa har ta k'araso wajen wasu da ke zaune cikin farin ciki ta rungume su

Cikin kuka take magana "Umma yau Allah ya cikan burina nagode ma Allah" cikin jin dadi wadda aka kira da Umma da dago ta tana share mata hawaye "ba abinda zamu cewa Allah sai godiya kiyi amfani da abun da kika fad'a ki kasance mai gaskiya da amana da adalci karki kasance mai karb'ar cin hanci domin tauyewa wasu haqqin su" Umma ta fad'a cike da farin ciki
"To Umma in shaa Allah zan kiyaye"

Ido suka had'a da Abban ta hannun sa ta rike sannan ta mika masa award din karb'a yayi sannan ya had'a da hannun nata ya rike "duk abinda zan fad'a miki Umman ki ta fad'a sai dai na k'ara jaddada miki cewa kikasance mai gaskiya a cikin aikin ki koda koda kuwa aikin ya biyo ta kaina Allah yayi miki albarka ya kare ki daga mahassada" gaba d'aya muka amsa da "ameen"

"Wai waya ga wata akan kujeran barrister nida 'yar shila" ya Salim ne yai magana zumb'uro baki nai had'e da Kai masa duka caraf ya rike hannun
"tuba nake ranki shi dad'e ina taya ki murna Allah ya taya riko ya baki ikon aiki da gaskiya"
Ya fad'a tare da rissinawa "amin" nace cikin jin dadi hade da mitsinin sa a kumatu
"Irin wannan mitsini haka kamar 'Yar bare-bari kin ci bashi"

Rungumar da akai mata har sai da suka kusa zubewa k'asa "bestie yau Allah ya cika mana burin mu ko batai magana ba nasan maryam ce ko k'amshin turaren ya isa ya sanar da ni hakan.

Kuka suka fara " hmmm sufa mata haka suke komai kuka farin ciki Kuka bakin ciki Kuka ko Abu ne ya fiye burge su yanzu sayi masa kuka" ya Salim ya fad'a

Wasu dattawa ne suka k'araso wajen nan mazan sukai musabaha matan suka gaisa cikin girmamawa daman can sun San junan su har k'asa na durk'usa nagaida iyayen maryam nan suka kuma yimana nasiha gaba d'ayan mu

Nan kowa ya fara hawa mota dan komawa garin su nan muma muka hau tamu motar nida Umma muna baya sai ya Salim a matsayin driver sai kuma Abba a gefen sa nan muka hau hanyar *kano ta dabo tumbin giwa*sai kusan biyu da rabi sannan muka Iso

A gajiye muka shiga gidan nan 'yan gida suka taso cike da farin ciki aka soma murna kamar ranar suka fara ganina

Shiri sosai school of law bagwada dake kano take domin dumin gudanar da partyn da ta shiryama d'aliban nata da sukai grad a the efficient inda kowane d'alibi aka bashi damar gayyatar 'yan uwa da abokan arzik'i.........🖊



Urs Salmah queen💍💅🏽
[11/17, 11:47 AM] Salmah Queen💍💅🏽: 👩🏻‍🎓 *Barrister Salmah* 👩🏻‍🎓


_*Written by Salmah Queen*_💍💅🏽



🇳🇬 _God bless Nigeria_🇳🇬




® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.comcom



Page 6-10




_Albarka da nasara sun tabbata ga wanda yake kyautatama mahaifan sa kasance mai biyayya sai kasami cigaba a rayuwa,Ka kasance mai yiwa iyayenka biyayya domin watarana kaima mahaifi ne nashiha ce Allah ya sakawa iyayen mu da aljannna ameen_ 👌🏻




Salmah kenan tun safe k'awayen ta ke kiran ta domin shirin partyn nasu kwance take a d'akin ta shiru kamar ba kowa wayar ta dake jone jikin charge ta fara ringin bestie maryam ne ya fito kan screen d'in saura kad'an kiran ya tsinke sannan ta d'auka "wallahi kedai kin fiye Jan aji da yawa Allah da ya katse kiran bazan kuma kiran ki ba" maryam ta fad'a "haba bestie na to ai in baki kira ba ni sai na kira balle ma baza ki iya jure rashin kira na ba"

"Kira nawa nai miki baki picking ba"

"Ayya sowie ban gani bane kin San bazan k'i d'aukan kiran ki ba ynx na fito daga wanka ne pls"

"Tom naji sai shegen dad'in baki ko shima wajen k'walliayar baza ki ba"

"Ni gaskiya baza'ae min ba sai dai na rakaku"

"Kut ke kin ma isa ae wllh ko kina so ko baki so sai anyi ki zama cikin shiri yanzu zamu k'araso" kit ta kashe wayar

Kayan da muka k'arbo daga wajen tela nagama gogewa jaka na da takalmi na d'aukko naji muryan su maryam da Aysha a tsakar gida suna gaishawa da Umma

Da sauri Aysha ta shigo d'akin "to tunku sai ki taso mu tafi kin San k'awalliya da cin lokaci" maryam kuwa kayana dake gefen gado da zuba a jaka nan suka jani muka fita sai da naima umma sallama sannan muka tafi wajen make-up d'in

Sai da akai musu sannan akai min light make-up dan ko jam bakin arzik'i ba'a sa mata ba amma hakan besa ta kasa yin kyau ba duk da ba fara bace amma tana da kyaun fata nan muka sa ankon grad din nan me kwalliya ta fara d'aukan mu photo.

"Idan nayi editing pictures d'in zan turo muku"
"OK tom shikke nan"
"to sai kun dawo"

Nan suka tafi basu zame ko ina Ba sai the efficient inda tuni jama'a sun halarta kowa kagani cike da farin ciki
nan aka hau yin pictures da friends

Waje na samu na zauna daga can gefe ina iya gano Aysha da saurayin ta ita kuwa maryam ta shige cikin jama'a kamar k'amshin dahuwa lol

Waya na na ciro na fara aikin selfie gaskiya ni kai na nasan nayi kyau nan nan fara juya ido tubarkallah daman akwai shi, k'aran shigowar message naji life partner nagani fuska d'auke da murmushi na bud'e

Take annurin fuska na ya d'auke
"please my future kiyi haquri bazan sami damar zuwa ba yanxu muka shiga meeting ne kuma ba lallai mu fito da wuri ba kiyi haquri amma zan san yadda za'ae na..."

Ban k'arasa karanta wa ba na fita daga ciki kamar nai Kuka haka fuska ta tayi maryam ce ta k'araso da sauri "tun d'azu nake neman ki" shiru nai mata ban magana ba
Dan Kuka zai iya zuwa idan nayi magana
"Lafiya me ya faru haka ran ki ya b'aci"?

Mika mata phone d'in nayi nan ta karanta " mtsww wllh kina da matsala akan haka zaki Kuka kawai share kinga da ba wani babban uzirin ba abinda zai hana shi zuwa just forget taso muje ku gaisa da sweet hrt d'ina"

Hannun na tafara ja "cika ni ba inda zani ae dole kice na basar kin san naki swtyn yazo"

Hakuri ta fara bani da k'yar na tashi muka tafi

A bakin motar su muka ganshi shi da abokin sa gaisawar mutunci mukai sannan na tafi wajen 'yan gidan mu

"Kai sa'eed wannan fine gal d'in fa amma dai maryam k'awar ki ce ko uhmm gaskiya ina ciki"

"Kai ko gajiya da magana baka yi" sa'eed ya fad'a

"To ae irin wannan ba'a sanya da su"

"Ae kuwa kama fita dan wannan da kake gani amarya ce" maryam ta fad'a

Wata irin zabura yayi "haba dan Allah da gaske kike ko kuwa dai baki son bani itace" ya fad'a yana kallon abokin sa sa'eed

"Allah da gaske nake"
"Oh my gosh!"

Ita kuwa har b'acin ran ta ya tafi tuni ta shige cikin jama'a kamar ba ita ba............🖊



Urs Salmah queen💍💅🏽
[11/20, 10:05 AM] Salmah Queen💍💅🏽: 👩🏻‍🎓 *Barrister Salmah* 👩🏻‍🎓


_*Written by Salmah Queen*_💍💅🏽



🇳🇬 _God bless Nigeria_🇳🇬




® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.comcom



Page 11-15





_*Ka kasance mai yin sallah akan lokaci dan watarana itace zata tayaka kwanciyar kabari,Ka kasance mai yawan istigfari don samun kusancin ubangijinka,Ka yawaita yin hailala koda yaushe domin shine mafi soyiwar kalami a gurin Allah*_






Daga wajen taron sukai sallama da k'awayen ta nan suka taho gida ita da 'yan uwan ta,

Da sauri na fad'a toilet dan yi alwala har anyi magariba ana ta kiran sallar isha'i

Na idar da sallah ke nan ina azakar dan ban samu nayi da yamma ba waya na ya soma ringing life partner tsaki nayi sannan nayi banza da kiran wani kiran ne ya kuma shigo nan ma ban d'auka ba sai a na uku dan nagaji dajin ringin sannan na d'auka murya k'asa-k'asa sallama yayi kamar yarda ya saba a k'aaan mak'oshi na amsa

"Tun d'azu nake kira baki picking ba lafiya"? Shiru nai masa " tab yau na tab'o 'yar rigima ayi min afuwa a fito ina waje"
"Ni ni ni gaskiya" be jira na gama magana ba ya kashe wayar

Kamar nai Kuka haka na fita da hijjab d'in da nai idar da sallah a falo na tarar da su Umma "Umma Ahmad yana kira na" "karki dad'e" haka kawai ta fad'a

Yana tsaye tun daga soro nake jin k'amshin turaren Wanda yaso mantar dani laifin sa bakina na kuma zumburowa

Shi kuwa wani lafiyayyen murmushi ya saki tun kan na k'ara so ya tsugunna a k'asa "am on my kneels gimbiya ta kaina bisa wuya na, nazo a hukuntani akan laifin da na yi"

Allah sarki tausayin sa ne ya kamani amma ban nuna masa ba" to ka tashi ni ban son naga kana min irin haka"

"Sai kin hakura zan tashi"
"Allah in ba zaka ta shi ba zan koma gida" na fad'a ina k'ok'arin juyawa da sauri ya tashi

"Haba tawan d'an saki ran naki mana ko ma samu ruwan sama ya zubo" yana magana yana kallon sama har 'Yar dariya yaso ban amma na dake "ni ban son wannan ae salon sab'o ne"

"To ya gajiya ina taya ki murna Allah ya bada sa'a yayi jagora amin" muka amsa gaba d'aya

Dai dai saitin kunne na yazo ya rad'an wata magana ban San lokacin da nasaki dariya ba har da d'an rissinawa

"Ni yau banyi niyar dariya ba ka sani"
"Ya ma za'ae nazo na tafi ban saki dariya ba so kike na kasa suku ni"

Nan suka shiga ba da tsare-tsaren su daga nan yayi mata sallama ya tafi ita kuma ta shiga gida kamar ba wadda ta fito da fushi ba falon Umma ta shiga nan ita ma ta zauna tana cin abinci suna shirin su ko wane shiri suke yi ku dai ku biyo ni



4:45am na asuba alarm din wayar ta ya soma cikin bacci ta sa hannu ta kashe 5:00 am wayar ta kuma yin k'ara sai dai wannan ba alarm bane kira ne cikin bacci ta d'auka ba tare da ta duba ba "nasan baki tashi ba an yi kira kije tashi kiyi alwala haba yanzu fa na kwanta har asuban yayi" "eh ki tashi mana oya oya kinje fili kinyi rawa dole Kika sa tashi sallah maza tashi"

"Ni ba rawar da nayi to tashi ni zan tafi massalaci karki koma sai kiyi azkar" be jira amsa ba ga kashe

"Da k'yar ta tashi idon ta da k'yar take bud'e shi sabida bacci ta shiga toilet sanyi ruwan me yasa tayi da wuri ta fito amma da sai ta cigaba da bacci a toilet

Tana idar da sallah tana shirin komawa ya kira " kinyi azkar d'in ne"? "A'a sai anjima zan yi"

"Yanzu me kike jifa da bazaki ba ban son wasa fa da addini" kashewa nayi dan ya fara ta kura min
Sarai yasan taji haushi amma ya share ta koda idar bata bi ta kasan ba ta koma baccin ta,

Magana sa'adah k'anwar tace ta she ta "ke kuma mene kin ishi mutane da magana sai kin samin ciwon kai" "Umma ce tace nai miki magana ki tashi ki wanka ki fito ki breakfast" "to naji fita"
Har ta fita ta dawo
"Oh ya ilahi me kika dawo yi"?
" na manta ban gaishe ki ba good morning aunty "
Fuska na saki nace "morning ya kike ya gajiya" sai alokacin na kalli agogo 7:6 cikin sauri na kammala komai na fito a gurguje na karya dan duk inda su maryam suke suna hanya............🖊


Urs Salmah queen💍💅🏽👩🏻‍🎓 *Barrister Salmah* 👩🏻‍🎓


_*Written by Salmah Queen*_💍💅🏽



🇳🇬 _God bless Nigeria_🇳🇬




® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.comcom



Page 16-20



*Idan xakayi taimako karkayi saboda wata manufa kayi saboda Allah ladan ka yanaga Allah,idan mutum yayi maka abu Mara kyau katuna da maikyau dayayi maka saboda kowani mutum yanada hali maikyau yana mummuna,karka bari bacin rai yadinga ziyartar zuciyarka saboda duk lokacin da ranka yabaci shaidan ne acikin jinin jikinka da ruruhinka nasiha ce*👌




Na fara sharar tsakar gida ke nan naji sallamar su "har kun iso sannun ku" nan suka shiga d'akin Umma ni kuma na k'arasa sharan a d'akin na tarda su suna karyawa zama nai suna ci ina hira "ke wllh da k'yar na tashi sabida gajiya" maryam ta fad'a tana tura dankali a baki "ke dai maza ci mu tashi mu tafi kar lokaci ya kure wai umma ice dak ba wannan ce tai girkin nan ba naji yayi dad'i da yawa" aysh ta fad'a tana kallon Salmah "ke da halla can an fad'a miki ban ita girki bane ke dai ci karki k'ware"

Haka suka gama ci Abin sha'awa k'awaye kamar 'yan uwa kan su a hade "to ni dai nace Allah ya bar zumunci"

A gurguje sukai ma Umma sallama sannan suka fita Aysha ce ke Jan motar basu zame a ko ina ba sai gidan kunshi bakowa sai wasu 'yam mata su biyu

An gama yiwa d'aya nan suka zauna ana hira har aka gama yiwa 'yam matan
"To da wa xan fara" mai kunshin ta fad'a tana murmushi maryam da Aysha har suna had'a baki "da wannan" suka nuna Salmah dan itace amarya

Nan mai Kunshi ta ran gad'a masu baki da ja masha Allah sunyi kyau ba irin na Salmah domin ya hau fatar ta sosai sabida gyaran jiki da ta sha

Yinin ranar Sam basu zauna ba

A gidan d'an hausa sokkoto road dake kano da yamma gidan ya fara cika da mutane ga wajen da aka tanada dan amarya ya sha traditional ducration masu kid'an k'warya kuwa sai kid'a ake inda nago fili cike da manyan mata ana ta rawa

"Haba wai baza ku k'araso bane tuni an fara cika ko so kike ayi Abu da magariba " aunty ga munan fa muna state road kad'an ya rage mu k'araso"

Kashe wayar nai na mik'awa Aysha idona ya kawo k'wallah "haba mene haka karki b'ata kwalliyar mana" maryam ta fad'a "ni wllh duk na gaji a d'aga anki dame xan ji ko'ina na jiki na ciwo yake"

"Ke dai k'ya fad'i gaskiya kawai kice yau baki ga swt kalbin ki ba shima duk inda yake yana can yana tunanin ki" duka na kai mata dai-dai nan muka k'araso wajen kamun.

Wow masha Allah abinda naji jama'ar wajen suna fad'a da sauri na k'arasa dan ganewa idanuna kai gaskiya duk hassadar me hassada bazai samu hanyar da zai kushe ta ba dan ko ta ina ta had'u

Tsawon ta baya bukatar takalmi mai tsawo baka ce chocolate colour,ga idon nan masha Allah fari tas sai kayi tunanin yasa eyelashes siririya ce bata da jiki amma hakan be hana ganin shape d'in ta ba tubarkallah komai yaji.

Maryam da Aysha ne suka sata a tsakiya sauran kuma suka rufa musu baya nan suka rankaya har gurin zaman amarya

A nutse take tafi kamar yadda ta saba
Nan ma fara ganin hasken flash ko ta ina da k'yar aka samu aka dakatar da masu d'aukan photo akai ma amarya kamu irin na al'adar hausawa duk nakosa a gama dan wata irin gajiya ce take lullube ni idona kuwa har yaji yake

Nan aka fara watse wa kowa ya tafi cike da fari ciki,

Haka sauran rana ku kowacce da event d'in da aka shira duka ango yaje in banda kamu Wanda shi ka d'aine be je ba...........🖊



Urs Salmah queen💍💅🏽👩🏻‍🎓 *Barrister Salmah* 👩🏻‍🎓


_*Written by Salmah Queen*_💍💅🏽



🇳🇬 _God bless Nigeria_🇳🇬




® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.comcom



Page 21-25






*Haba 'yar uwa ki sani kefa uwace wata ran ke zaki bada tarbiya kuma duk irin halin da shi 'yar ki zata tashi,mene amfanin beyewa samarin zamani ana d'aukan ki ana shan minti ke kuma sabida k'awadayin abinda za'ae miki ba Wanda duka-duka bazai wuce wani abun ba mene amfanin ki bari jikin ki mai daraja ya zama kamar kasuwa kowa ne kato yazo ya kai hannu dan kawai kar aga bakya rike babbar waya bakya wanka irin na waccan, kisan shifa namiji duk abinda yayi ado kefa rayuwar gajeriya duk dadewar ki wata ran gidan miji za'a kai ki, ki rike mutuncin ki domin mutunci madara ne nasiha ce*👌🏻





Yau ta kasance ranar lahadi da musalin 11:00 jama'a suka shaida d'aurin auren Dr.Ahmad idris me k'wabo da sis da Brr.Salmah Muhd

Kowa yana San barka inda marok'a suke ta fama aikin su

K'arfe hud'u tuni gidan su amarya sun fara shirin raka amarya gidan ta nan aka kai ta gidan ta gwanin sha'awa kamar kar na fito komai a tsare yake nan mutane suka watse aka bar maryam Aysha sai aunties d'in ta nan suka hau gyaran gidan suka bi kowane sako suka sa turare kan kace me tuni gida ya d'au k'amshi nan sukai mata sallama

Dan bazan ce rakiyar ango dan wannan al'adar bata yarda da ita ba haka ango ya shigo gidan tun daga haraba k'amshi ya fara yimasa Barka da zuwa haka ya shiga cikin gidan cike da farin ciki da annashuwa

Sallama yayi sannan ya shiga d'akin a hankali ta amsa sallamar basu b'ata lokaci ba sukai alwala sannan sukai sallah raka'a biyu kamar yanda addinin mu ya tanadar

Kajin da ya siyo ya d'aukko ya zuba a plate wayyo tuni k'amshi ya maimaye d'akin sannan d'aukko fresh milk masu sanyi gaske

Tuni yawu na ya fara gudana ganin ba samu zan ba basu San ma da ni ba yasa na tashi na bar d'akin ina had'iyar yawu

To ayi bacci lafiya ango da amarya.

Anyi kwanan nan farin ciki kiran sallah asuba ne ya farkar da shi a hankali Ya tashi sai da yai wanka sannan yayi alwala bakin gadon ya zauna yana kallon fuskar ta cike da so da k'auna "Allah nagode ma daka bani mata ta gari" abinda naji ya fad'a ke nan

A hankali ya fara shafar gefen fuskar ta kamar a mafarki taji anan hura mata iska a kunne a hankali ta bud'e idon ta cike da bacci ganin sa yasa tai sauri rufe fuskarta da hannun ta

"Asuba tayi amarya ta" nai kamar banji shi ba k'ok'arin Jan bargon yake da k'arfi na rike

D'aga ta yake k'ok'arin yin "a'a ni kabarshi zan tashi da kai na" "ki bari na taimaka miki"
"Nop ka tashi ka tafi masallaci kaji zasu tayar karka rasa jam'i" *madallah da samun mace ta gari da watace Sam yau bazai sami damar tashi asubar ba bare yaje masallaci*
Da sauri ya tashi "ki kular min da kanki" ya fad'a yana fita

Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta tashi da k'yar jiki duk yayi tsami a haka ta shiga toilet nan ta tarda ruwan zafi a abun wanka shiga tai sai da ta tabbatar ko ina na jikin ta ya gasu sannan ta fito

*point of correctioga amare idan mace aka kaita gidan miji lokacin da zaki wanka karki zuba detol kamar yadda kukaji anan fad'a hakan yana da illa domin shi detol anyi shi ne domin kashe k'ayoyin cututtuka nan kuma jikin akwai k'wayoyi masu amfani in kika zuba detol tofa har su zai kashe dan haka a ruwan zafin gishiri kawai zaki zuba*

Wanka tayi sannan tai alwala a hankali ta fito duguwar riga kawai ta jira sannan ta tayar da sallah,tana cikin sallah ya shigo zama yayi yana kallonta wani irin son ta yana k'ara shigar sa

Alamun ta idar dan kunya irin tata ta hana ta ko d'aga kan ta,tsugnnawa yayi gabanta ya riko hanun ta
"barka da asuba zaujatee tunda ba zaki gaishe ni ba" a hankali ta bud'e baki tace "good morning"shima alamar motsawar bakin kawai ya gani ya gane " morning dear ya gajiya"shiru tai ba amsa "fatan ba inda yake miki ciwo ko"? nan ma shiru " oh ya salam kiyi magana mana"
Murmushi yayi Wanda har sai da tajiyo sautin sa
Kan ta Ankara tuni ya d'auke ta caraf sai kan gado.................🖊[11/23, 8:19 PM] Salmah Queen💍💅🏽: 👩🏻‍🎓 *Barrister Salmah* 👩🏻‍🎓


_*Written by Salmah Queen*_💍💅🏽



🇳🇬 _God bless Nigeria_🇳🇬




® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.comcom



Page 26-30




*ki zama mace mai aji kamun kai da nutsuwa yawan tara samari beda amfani karki bari ki zama kamar motar haya sai dai kowa ya tare ya hau nasiha ce*👌🏻






"Pls dan Allah ka yi haquri"

"Au daman kina jina kika min shiru" to bakai ne ba" sai kuma tayi shiru tuni ido ya kawo ruwa

Nan ya fara lallashin ta "ni ka k'yaleni bacci nake ji" ta fad'a a shagwabe

"Ni bazan k'yale ki ba sai kin kalle ni" ya fad'a yana k'waik'wayon ta

K'ok'arin had'a ido yake da ita amma duk yanda yaso had'a ido abun ya ci tura dan wata irin kunyar sa take ji
Haka ya haqura ya k'yale ta cikin mintuna kad'an bacci yayi awon gaba da ita abun ka ga wadda ta gaji

Shima bayan ta yaje ya rungume ta kamar wani zai sace ta haka ya rike ta cike da tunani iri iri har shima bacci yayi gaba da shi .


K'aran phone d'in shine dake kan bed side drawer ya tashe shi sai da ya nutsu sannan Ya d'auka hajiyar sa ce

"Cikin girmamawa ya gaishe ta" ta amsa da kulawa "ya Yar tawa" kallon ta yayi tana baccin ta hankali kwace gefen fuskar ta ya sha a ranshi yace sleeping beauty
"bacci take Hajiya"

"to ka gaishe ta,daman abinci driver ya kawo ya kuma tarar baku bud'e gidan ba sai kaje ka bud'e" kan yace wani abun ta kashe wayar

Nan ya tashi yaje ya bud'e sannan driver ya gaishe shi cikin girmamawa a dining ya ajiye sannan ya fad'a toilet har ya fito bata farka sai da ya gama shirin sa cikin shadda sky blue kai masha Allah ku zo kuga inda kyau yake Ahmad dogone yana da d'an kauri kadan baki ne me kyau ga sajen sa ya kwanta gefen fuskar sa abun sha'awa da ka kalle shi kaga cikakken namiji me hankali da kamala

K'amshi turaren da yake fesawa ne ya tashe

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment