You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai dai kawai nace kar ka sake ka koya ma k'anwa ta rashin kunya irin taka"
Dariya gaba d'aya parlon suka k'washe da ita

Gaisawa mukai da ita cike da kulawa kinga ni yanzu unguwa zani amma in shaa Allah zan zo na yini mu sha hira na baki labarin k'uruciyar mijin na ki" tafita tana dariya

Nan ta fita muka cigaba da hira sama-sama da su Hajiyan

"Ai kullum ya zo sai munce yaushe zai kawo ki sai yace be komawa gida da wuri sai da yaji mun ce zamu zo shine yau ya kawo ki yara ma suna son zuwa yace a barki ki huta sa zo" Aunty sa ce ta fad'a
"wllh nima in son zuwa sai yace wai na bari a kwana biyu ma zo"

"To yanzu dai magana ta k'are tunda na kawo ki, af kinga na manta" hermper d'in ya d'aukko "Hajiya ga girkin amarya"
"Hajiya aunty ce ta k'arba kai masha Allah harda wahala" bud'ewa ta shiga yi "kinga kamar tason Alhaji yace ai masa chickenpepper" Nan kowa ya d'auka har kusan magrib ana tare ana hira, nan suka tashi suka bar mu da su Jasmin da Hamida

"Allah aunty in mun gama exam zamu zo mu taya ki kwana" Jasmin ta fad'a "kai amma da naji dad'i kuwa dan gidan shiru wata ran har tsoro nake ji" "aunty.." Da sauri na katse ta pls dan Allah kudaina cemin Aunty kunga duk age mate d'ina ne ni har kunyar amsawa nake" "tab ai gwanda ma ki koyi amsawa dan duk family d'in nan haka ake cewa matan yayye koda ka girme su" Hamida ta fad'a "OK naji amma ku dinga ce min Sister salma ba sai kunce Aunty ba" "tom shikke nan Aunty au Sis Hajiya Aunty tace kije daga nan sai kiyi sallah " tom nace tare da shi har d'akin suka raka ni, "to wai ku duk inda take kuna biye da ita ko hira kun k'i bari muyi ku fita ku bani waje" ta Kore su Haba Aunty muma ba sai ayi hiran da mu ba" Hamida k'yale ta su gana ai barin ta zaiyi ta kwana" jasmine ce ta fad'a tana kok'arin fita "lallai da yake kowa sha-sha-sha ne irin ku ba sai ya bar ta ta kwana Kinga shiga toilet kiyi alwala ki fito kiyi sallah"

"Hajiya Aunty ina Amaryar tamu yanzu ake cewa ta zo shine na shigo mu gaisa" "ai kuwa baza ka ganta ba tunda baka iya zuwa can ba"

"Haba zani mana kin San kullum cikin hidima muke da yau zani ni da friends d'ina sai kuma naji tazo"
"Daman lawyer ka karanta da sai yafi dacewa da ka iya shirya zance" Jasmin ta fad'a wallih ya mukky ka daina abinda kake yi"

Dariya suka yi Jan kunnen ta yayi ya fita "bari naje wajen amaryar ta ta nunan pictures din ta kamin naje har gida mu gaisa"

"Mukky Mukky na kuma maimaitawa a raina..............๐Ÿ–‹







Urs Salmah queen๐Ÿ’๐Ÿ’…๐Ÿฝ
[2/18, 2:11 PM] Salmah Queen๐Ÿ’…๐Ÿฝ๐Ÿ’: ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿปโ€๐ŸŽ“๐Ÿ‘ฉ๐Ÿปโ€๐ŸŽ“ *Barrister Salmah*๐Ÿ‘ฉ๐Ÿปโ€๐ŸŽ“๐Ÿ‘ฉ๐Ÿปโ€๐ŸŽ“



*Story and written*
*By*
*Salmah Queen*๐Ÿ’๐Ÿ’…๐Ÿฝ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ _God bless Nigeria_๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ


ยฎ *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ษฏษ› ษ–ฦกล‹ลง สลณลžลง ษ›ล‹ลงษ›ล™ลงฤ…ฤฑล‹ ล‹ษ– ษ›ษ–ลณฤ†ฤ…ลงษ›, แƒชลณลง ษฏษ› ฤ…ูณลžฦก ลงฦกลณฤ†ษง ษ– ษงษ›ฤ…ล™ลง ฦกส„ ล™ษ›ฤ…ษ–ษ›ล™ลž_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https:/bio/www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com






Page 61-65




*A gaskiya ina jin dad'i masoya ma da irin k'aunar da kuke nuna min naji dadi ina alfahari da ku nagode masu kira na da masu yimin magana ta WhatsApp ne ko Facebook haka ma Wanda suke turo min da sak'on test messages ina godiya Allah ya bar zumunci nagode*๐Ÿ˜๐Ÿ˜

just follow me on Instagram @aleeyusalmah





*M* ukky! Mukky!! na kuma maimaita a raina nayi nisa cikin duniyar tunani muryar Hajiya Aunty ta katse ni "in kin idar taso muje wajen Alhaji ku gaisa" "tom" nace tare da tashi zaman mayafi na na kuma gyarawa muka fita tana gaba ina biye da ita

" Allah ya Mukky Aunty Salmah me kyau ce ka gatan kuwa" pictures d'in bikin ta fara k'oka'arin nuna masa "kalli ka gani har tafi kyau a fili"

Daman k'irjin sa ya buga ta maza yayi ya b'oye razanar sa ya k'are mata kallo lallai Wannan kamar Wannan Mara kunyar ko da yake ba lallai ta zama ita ba naga Wannan ba tai kalar rashin kunya ba duk cikin ransa yake fad'a ita kuwa Jasmine bata lura da tunanin da yake ba sai surutu take zuba masa

"Ke ni karbi wayar ki, kin tsaida ni kin cika ni da magana sauri nake zamu unguwa k'yacewa Hamida na zo ina sauri ne amma zan dawo" "Tom amma nasan baza ka dawo ba kawai ka fad'a ne" nan ya fice yana tuntun-tuni

Cikin girmama muka gaisa da Alhajin su Ahmad kai amma Wannan gidan anyi mutanen kirki muna zaune Ahmad ya shigo nan yayi mana nasiha gaba d'aya muka fito
D'akin Hajiyan sa muka tafi nan itama tai mana nasiha a haka su Jasmin da Hamida suka shigo "Sis zo muje d'akin mu muyi tamu hiran"

"To aku uwar magana tafiya zamu yi weekend k'wa zo kuyi hirar ki shirya nan da 5munites ki samen a mota" yayi ma Hajiya sallama ya fita

"Yawwa to zo muje d'akin mu kiyi kwalliya" Hamida ta kama hannu na kallon Hajiya nayi "to tashi kuje amma kar ku Dade tunda jiran ki yake yi"

D'akin muka je kallon d'akin nayi amma yayi kyau irin na 'Yammatan zamani masu ji da aji da gayu komai a tsare gaban dressing mirror suka kai ni zama nayi ina kallon kayan k'walliya kamar gidan make-up

"Sis bari nayi miki kin San ina zuwa wajen training make-up ita kuma Hamida wajen training din cake take zuwa"
"A'a nagode ban son make-up da yawa" "ai nima kad'an zan miki" "ki bari in kin zo k'ya yimin" nan na kashe maganar powder kawai na sa sai lipstick amma duk da haka nayi kyau ta mudubi muka had'a ido da su dariya mukayi gaba d'aya dan sun kwantan a raina na,number d'ina suka karb'a sannan muka fito, a kofa muka ga Aunty tana k'ok'arin shigowa "yawwa muje" ta fad'a har mota suka rakani ledoji naga Afnan tasa a gidan baya suka rufe motar har muka bar gate d'in suna tsaye suna d'aga mana hannu.

Shi kuwa Mukky be zame ko ina ba sai gidan su Jibson "ah abokina yanaga ka shigo kamar Wanda aka koro"?
" ai dole ka ganni haka me kama da Wannan yarinyar nagani" "wacce fa" Mubaraq ya watso masa tambayr "ni wallahi har ban son ma na tunata wadda mukai fad'a" "OK wadda ta mare ka zaka ce" Jibson ya fad'a wata uwar harara ya watsa masa "nifa ban son iskancin nan ban fad'a dan kai min rashin mutuncin ba" "oh sorry my friend a ina ka ganta"?
" a wayar Jasmin wai ita ce matar Ahmad " "ah haba dai kana da pictures din mu gani" ya fad'a yana matsawa kusa da shi "a'a sai dai na duba IG din Jasmin d'in" "kai abokina ni wallahi ma d'auka ka manta haba sai kace ba namiji ba kawaika share" mubaraq ya furta Wannan maganar "hmm dan dai ba kai aka Mara ba ne ni nunan muga ko ita ce Kasan har yanzu ina gano sanda ta filla ma mari jikake tasss!" jibson ya fad'a da tare da tuntsirewa da dariya ba Mukky ba har Mubaraq sun ji haushi "to wakilin shaid'an daman duk abinda Mukky yake kai ke zuga shi" Mubaraq ya fad'a "to wai shin ma in ita ce me zakai mata ma Abu sama da shekaru da yin sa" Mubaraq ya tambaye shi murmushin takaici yayi tare da cije lebe kamar a lkcn akai masa "daukar fansa zan yi sai ta San ta mari namiji wallahi" "wallahi Mukky kabi a hankali kar ka biyewa Wannan wawan" Mubaraq ya fad'a tare da gyara kwanciyar sa "yawwa ka ganta" nuna masa yayi da sauri jibson ya k'arb'a "wow so cute irin matar da ake so" nan ya fara zance ya manta akan me suke magana "kaga Mayan mata ba yayi abinda ya dace ya tsaya kallon matar aure" Mubaraq ya fusge wayar kallon ta yayi "ba lallai ta zamo ita ba ai an kwana biyu kawai ka basar" ya mik'a masa wayar "kai baka San zafin abin ba" to ai daman duk tsun-tsun da yaja ruwa shi ruwa ke doka da bakai musu ba da bata mare ka ba,wai da ita ka Mara kila Zane ka zata yi"wata dariya suka kwashe ta ita Mukky kuwa kamar yayi kuka nan ya fita yana cin alwashin sai ya rama ya bawa abokan sa mamaki.cikin hanzari Mubaraq ya tashi ya bishi tsaya ni mana ka tafi kabarni wajen Wannan d'an iskan" da gudu jibson ya bisu "to ai nima k'afar ku k'afata duk inda zaku sai na biku my guys ina ji da ku"

A mota kuwa hira yake mata amma sam hankalin ta baya kan sa yana wayar ta da take chatting da su Jasmin ko waccen su hira take mata tama rasa wadda zata saurara dan hiran tayi dad'i fusge wayar yayi "haba dan Allah ka ban wayana mana" mtsww yayi tsaki wace irin hira kike haka har mun zo ina miki magana baki Sani ba" kalla tayi sun ma shiga gidan dariya tayi "ni da su Jasmin ne sisters d'in ka sun min ina ma a gidan nan suke" "to ai sai ki dawo da su, muje ni na gaji" kwanciya tayi ta lumshe ido darling ni na fika gajiya ko tafiya k'iwar yi nake yi " fitowa yayi ya zagayo inda take "oya fito" yi tayi kamar bata ji shi ba ai kuwa batai aune ba sai ji tayi ya d'auke ta kamar baby dariya ta soma "ka ajiye ni mana" ai baki son tafiyar shine na hutar da ke" cakulkuli ta soma yimasa dariya ya fara abin abin sha'awa ai kuwa be dire ta ko ina ba sai kan gado nan suka zube gaba d'aya suna dariya.................๐Ÿ–‹






Urs Salmah queen๐Ÿ’๐Ÿ’…๐Ÿฝ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿปโ€๐ŸŽ“๐Ÿ‘ฉ๐Ÿปโ€๐ŸŽ“ *Barrister Salmah*๐Ÿ‘ฉ๐Ÿปโ€๐ŸŽ“๐Ÿ‘ฉ๐Ÿปโ€๐ŸŽ“



*Story and written by*
_*Salmah Queen*_๐Ÿ’๐Ÿ’…๐Ÿฝ




๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ *God bless Nigeria* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ




ยฎ *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ษฏษ› ษ–ฦกล‹ลง สลณลžลง ษ›ล‹ลงษ›ล™ลงฤ…ฤฑล‹ ล‹ษ– ษ›ษ–ลณฤ†ฤ…ลงษ›, แƒชลณลง ษฏษ› ฤ…ูณลžฦก ลงฦกลณฤ†ษง ษ– ษงษ›ฤ…ล™ลง ฦกส„ ล™ษ›ฤ…ษ–ษ›ล™ลž_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com




*follow me on Instagram* @aleeyusalmah



Page 66-70



*fans kuyi haquri na rashin typing na kwana biyu da ban ba kusan jiki da jin yana bukatar Hutu nagode da kulawar ku ina tare da ku a duk inda kuke*๐Ÿ˜๐Ÿ˜



Previous page:- A mota kuwa chatting suke ta yi da su Jasmin ta rasa wadda zatai ma reply dan kowaccen su magana take mata har suka iso bata sani ba kallon ta yayi gaba daya hankalin ta yana kan wayar gun tun tsaki yayi ya fusge wayar "haba malama wannan wane irin chat ne haka har mun iso baki sani ba" wllh ni da su Hamida ne sisters d'in ka sun min wllh dama anan gidan suke" "to ae Sai I dawo da su, muje ni na gaji" kwanciya tayi Kamar bata ji shi ba "darling na fika gajiya ni kiwar tafiyar ma nake yi"
Zagayowa yayi saitin kofar "oya fito" yi tai Kamar bata ji shi ba ae kan tayi wani Abu ya d'auke ta kamar wata baby dariya take "ka ajiye ni mana" "ae baki son tafiyar shine na hutar da ke" cakul-kuli ta fara yi masa nan suka fara dariya be ajiye ta ba sai akan gado.....






D'agowa yayi yana kallon ta ita ma kallon sa take yi "dia ni na rasa wane irin so nake miki kullum k'aruwa yake yi pls mene sirrin"?

" kawo kunnen ka kaji" da sauri ya mika kunne ae kuwa tana gani ta kama kamar zatayi magana sai kawai ta cije kunne wata k'ara ya saki ai kuwa da gudu tayi toilet tana dariya

Bin bayan ta yayi "ai bashi kika ci sai na rama nan ya fara zuba mata ruwa tana ramawa abun sha'awa
Haka Salmah da Ahmad suke gudanar da rayuwar su cikin jin dad'in

Sai da ta cika two months a gidan sannan ya kai ta gidan su ta wuni kamar baza ta dawo ba dan idan ya fita gidan fad'i yake mata

Sai da yamma sannan Abban ta ya dawo shi da ya Muhd

Cikin farin cikin ta gaishe shi " Abban wllh I miss you so much " "to my salmaty yaza'ai haka rayuwar aure take, sanda aka kawo Umman ki har kuka take in zan fita" gaba d'aya suka sa dariya banda umma da tayi kicin-kicin "to kije ki shirya kamin me gidan naki ya zo" "tom Abba"

Tana fita yazaro wata paper daga brief case d'in sa umma ya mik'awa "tame ce Alhaji" "to ki karanta mana "

Tun daga yanayin da umma ta shiga kana gani kasan tana cikin farin ciki "kai Alhamdulillah masha Allah naji dad'i"

"D'azu ina office Alhaji Hassan yace yana son gani na ina zuwa ya mik'o min, Yanzu in zasu tafi sai ma bata kinga system d'in da d'an uwan ta ya saya mata"da sauri umma ta d'auka ta kamfanin apple farin ciki wajen umma bazai k'watan tu ba

Suna zaune Salmah ta shigo "Abba ga Ahmad ya zo zamu tafi" " to ce masa ya shigo" a ladaf ce ya gaida su nan Abba ya bashi takardar "to ga wannan opper d'in Salmah ce ta samu aiki a federal high Court" ai Salmah wani irin tsalle da ihu tasaki "wayyo Allah na Allah nagode ma" rugume Abba tayi tana murna shi kuwa yana ta murmushi irin nasu na manya "to Abba angode Allah ya k'ara girma da lafiya"


sai da umma tayi mata tsawa sannan ta nutsu suka tafi suna ta murna


"Darling ina taya ki murna Allah yataya rik'o amin sweet heart wllh na rasa wane irin farin ciki zan yi"


"In mun koma gida sai ki sallah ki godewa Allah"


"Cikin nasara Salmah ta fara zuwa aiki a sabuwar motar ta da Ahmad ya siya mata, Salmah ke nan buri ya cika

Suna ganin cases iri-iri abun tana ganin sa kamar ba wuya Ashe abun bana wasa bane

Kullum tana cikin bincike amma in ta dawo gida a jiye komai take ta kula da mijin ta................๐Ÿ–Š






Urs Salmah queen๐Ÿ’๐Ÿ’…๐Ÿฝ

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment