You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi,daga haka ya kwanta bayan ya yi addu'o'in neman tsari. Saida SUDESS ya shafe tsawon kwana biyar kullun suna zarya Campany idan suka fita tun 10 sai dare suke dawowa,lokutta da yawa mantawa yake da yarinyar nan sai idan Salisu ya tunamai,abincima sai Salisu ne yake kaimata,gaba Waya kan SUDESS ya Wau zafi sai fama yake yi,waya ma da yan gidan su sai jefi-jefi yake samun time su gaisa. A cikin rana ta shida ne da dare bayan ya kimtsa ya nufi Wakin da Jemima take yana addu'ar Allah yasa ta faWamai unguwar su ya mayar da ita. Yana tura kofar ya jita a rufe knowking ya fara yi yana jin haushin kanshi.cikin magagin bacci ta ji kamar ana buga kofa ta buWe idonta,kofar ta tsirawa ido tana nazarin ko wanda yake kawomata abinci ne,to amma idan shi ne ai ya kawomata tun Wazu,agogo ta kalla ganin karfe goma saura yasa ta yi saurin ziro siraran kafafunta tana jin wani jiri,bakin kofar ta tsaya ba tare data buWe ba.Ji ta yi an kara bugawa,kafin ta saka fararen yatsunta ta murWa kofar bayan ta cire key Win.Ganin shi ta yi a tsaye sanye da brown jallabiya ya zuba hannuwan shi cikin aljihu ,sosai ta kuramai ido ganin ya Wan rame idon shi ya kara fitowa. Cikin yaren turanci ta ce ""Good evening""tana ja da baya ganin zai shigo cikin room Win."

A hankali ya zauna saman karamar kujerar dake passing bed ba tare daya amsa ba. Jemima ta yi tunanin bai ji ba ta kara maimaitawa kafin ta tsugunna gefen kafafun shi tana tsurama yatsun kafar shi ido.

"A hankali ya amsa cikin yaren turanci ya ce ""Ya jikin na ki"" amsawa ta yi ""Da sauki"" ""Allah ya sauwake"" ya ce yana picking call na Doctor Mujaheed ""Hello Doctor barka da dare?""."

"A Wayan bangaren Doctor Mujaheed saida ya kalli matar shi yana murmushi kafin ya ce ""Lafiya lau gauro,shugaban gaurayen Katsina da Abuja"". Sosai SUDESS ya murmusa har fararen ha™oran shi suka baiyana ,yar yalwatacciyar sumar shi ya shafa yana jin nauyin maganar kafin ya ce ""Uhmm tau sarkin surutu ina maman takwarana?""ta can Doctor Mujaheed ya ce ""Gata nan kusa da ni,takwaranka kuma ya yi bacci,ya jikin wannan yarinyar ta warke ko?"" Ya yi tambayar yana Wora kanshi bisa kafaWar Hannatu."

"""Ta ji sauki,but ina so gobe na mayar da ita gidan su,kaga bai kamata ta yi ta zama anan ba,Ni kaina bana iya kula da kaina ballanta ita,na ga ji Doctor Mujaheed,jibi zan koma gida insha Allah"" Ya kai karshen maganar yana langabar da kanshi gefe Waya alamar ya kosa da maganar."

Ita dai Jemima jefi-jefi take Wagowa ta kalle shi saboda ta kasa fahimtar wane irin yare ne yake yi.

"Daga can Doctor Mujaheed ya ce ""Ayya sorry tazuru gobe ka kawo ta nan Hindatu zata kula da ita,tun farko na yi tunanin ka mayar da ita shiyasa,kada ka damu gobe Salisu ya kawo ta before ku fita kada hakurin ka ya kare ka kwamishe yar yarinya""Ya ida maganar yana saka dariya dan yasan yanzu zai katse call Win.Haka ta kasance kuwa cike da bacin rai SUDESS ya katse kiran yana jan dogon tsaki ya furta ""That man is not easy"". Jin ya katse call Win Doctor Mujaheed ya kalli Hindatu yana kyalkyala dariya, ""Uhm Dear ka kyale SUDESS ya huta,na fahimci ka takuramai shiyasa baya san kiran ka""cewar Hindatu,""Kyale shi Wan"

"iska ne saiya rika nuna shi bai san wani felling ba danya raina mu,dan dai nasan yana da tarbiya,amma ina jiyemai kada ya fara neman mata, SUDESS fa ya fini a haife amma kinga kusan shekarar mu biyar da yin aure,saika yimai maganar aure ya rinka wani lumshe maka eyes saboda tsabar iya shege,barni da shi dole ya nemi matar aure ko zai kara samun natsuwa"" ita dai Hindatu bata kara cewa komai ba ya ci gaba yimata hirar SUDESS. A bangaren SUDESS kuwa"

Ta kasan ido ya kalleta kafin ya mike ya fice daga Wakin.

Jemima tana ganin ya fita ta mike tana taSe Wan madaidaicin bakinta ta haye bed.

"Yana komawa Wakin shi kiran AUTAH yana shigowa wayar shi,katsewa ya yi kafin ya kirata,cikin siririyar muryarta mai daWin sauraro ta ce ""Assalamu Alaikum Ya barka da dare,hope kana lafiya?""."

"Murmushi ya saki tamkar yana gabanta kafin ya amsa da ""Lafiya lau little,ya rashin jin magana?kin daina ko?""ya tambaye ta cikin hosy voice irin na mai jin kasala.Yar dariya ta yi suka Wan taSa hira kafin ya katse call Win."

"Wani iri yake jin jikinshi tamkar mai zazzaSi,magani ya sha kafin ya kwanta bayan ya turawa Salisu sako akan da safe ya zo ya kai wannan yarinyar gidan Doctor Mujaheed."

"Washe gari da wuri ya shirya ya fito palor yana Waura agogo.saman one seter ya zauna saiga Salisu ya shigo Wauke da kayan break,saida ya aje kafin ya gaishe da ogan na shi,na Jemima ya Wauka ya nufi bakin kofar Wakinta,harya kusa kaiwa daidai kofar ya ji Muryar ogan shi ya ce ""Kada ka shiga"". Da ""To"" Salisu ya amsa kafin ya yi knowking.saida ta buWe ya mika mata kafin ya sanar da ita sakon ogan na cewar ta shirya za su fita. Amsawa ta yi da ""Ok"" ta koma ciki."

"Palorn Salisu ya dawo shima ya yi break kafin ya fita. Ita ko Jemima kaWan ta ci arish Win da wainar kwai ta goge bakinta, rolling mayafinta ta gyara kafin ta saka plant shues Winta ta nufo palorn.A hankali ta tsugunna tana gaishe da shi.can kasan makoshi ya amsa kafin ya mike ta biyo shi baya.har bakin motar suka karaso ya Salisu ya buWe mai front sit ya zauna,kafin ya buWe ma Jemima ta shiga shima ya zagaya mazaunin driver bayan ya aje kayan ogan na shi ya tayar motar,mai gadi ya buWe gate suka fice daga gidan."

"Wajen government House suka nufa anan gidan Doctor Mujaheed yake,ba tare da Saga lokaci ba aka buWe masu gate suka shiga,a wurin parking suka tsaya,kafin ya kira wayar Doctor Mujaheed time Win suna break ya ga kiran abokin na shi kuma Wan'uwan shi.Šagawa ya yi jin sun karaso ya ce ""Ku shigo mana"" ya aje wayar yana cema Hindatu kinga harsun kara so."

"Fitowa SUDESS ya yi yana cema Jemima ""Zo mu je"".Sauka ta yi tana bin shi a baya kamar jela, tas ta karem halittar shi kallo ganin yadda yake da murjewar jiki kamar na mazan India."

"Suna shigowa palorn Hindatu ta taso da sauri ta rungume Jemima tana shafa kyakykyar fuskarta ta ce ""Your welcome Dear"". Ganin haka yasa itama Jemima ta saki murmushi tana gaisheta.Zaunar da ita ta yi kafin shima SUDESS ya zauna,nan take Hindatu ta fara haWamasu abinci,amma SUDESS kin ci ya yi ya ce ai sun yi break a gida.Bayan sun kara gaisawa ta kalli SUDESS ta ce ""Am gsky Yayanmu ina ka samo wanna little Win,irin wannan kyau haka kamar ita ta yi kanta""shidai SUDESS murmushi ya yi bai ce komai ba."

"Sai Doctor Mujaheed ya ce ""Uhm kin gani ba abinda nake faWa maki,sai anyimai magana ya rinka wani lumshe ido kamar wani jarumi,to wallahi wannan week Win zan je Abuja saina"

"Kunno maka wuta wurin Uncle Hasan,kuma kasan halin shi tsaf yake iya yima auren dole,kai baka tausayin kanka,sai faman zafin neman kuWi amma ka kasa samun abokiyar rayuwa""ya karashe magar with compidens."

"Danda nan SUDESS ya Sata rai ya kankantar da ido ya ce ""wallahi Mujaheed ka fita a idona,kasan me kake cewa kuwa,Ni ba yayanka ne ba""."

"""Sorry tazuru yanzu ni ne babba tunda harna a jiye iyali,sai ka yi hakuri ka Wauki kankantar,ai na fahimci baka tausayin kanka,amma idan aka yima auren dole to bamu san lokacin da zaka rike matarka ba,muma Momy ta huta da dafa maka abinci"" ya ida maganar yana yimai dariya.Ganin haka yasa SUDESS mikewa yana cewa ""Maman Boy ni na wuce saina dawo""ya fice ba tare da ya kara kallan inda Mujaheed ya ke ba.Da Allah kiyaye ta bishi tana mayar da kallanta ga Jemima da take ta faman kallansu saboda bata gane Yaren Hausa. Kama hannunta tayi suka nufi ciki tana cema Mujaheed ""Dan Allah Hubbi ka kyale bawan Allah nan,kaga ka Sata mai rai,kada ya yi fushi""."

"""Kyale shi Hubbi ai na fahimci idan ba haka aka yimai ba,to shi bai ki ya karasa rayuwar sa a haka ba,a ce mutum kusan shekara Arba'in amma yaki yin aure,anjima zan kira Uncle Hasan na haWa mai bom""."

"Ita dai Hindatu jan hannun Jemima ta yi suka wuce ciki ta kaita Wakin da zata zauna,ta nuna mata wasu abubuwan kafin ta koma kitching dan Wora girkin rana""."

"Shima Doctor Mujaheed asibitin shi ya nufa,da zummar da ya dawo zai kira Uncle Hasan su tattauna."

"A yinin ranar hakanan SUDESS ya yi shi a Company ba tare da walwala ba tun bayan maganar da Mujaheed ya faWa mai,yasan halin Uncle Hasan mutum ne mai zafi,ko last year dakyar ya samu suka hakura akan magar auren shi,yanzu kuwa yasan idan tsautsayi yasa aka tado da maganar to yasan ko shawara bazasu yi mai ba,shi kuma tsakanin shi da Allah yanzu idan aka haWa shi da wata ai an takura mai bazai iya kula da ita ba,tunda shima Momy ce take kula da shi to ina zai iya,da wannan tunanin suka ta shi kafin suka wuce gida."

"A bangaren Mus'ab kuwa sosai suke sheke ayar su shida Meema ba tare da tunanin komai ba,ya sakarmata kuWi kamar ba gobe,tunda ya yi kwana Waya a Hotel Win Dady ya kira shi akan cewar duk inda ya ke ya zo gida,saboda baya so suna kwana a wani wuri idan har ba aiki ne ya kai su ba,badan ya so ba haka ya hakura ya ke kwana a gida,da rana idan ya ta shi daga aiki saiya wuce wurin Meema."

"A ranar dai SUDESS tunda ya dawo daga aiki bai samu damar zuwa gidan Doctor Mujaheed ba,saboda a gajiye yake saida dare Mujaheed ya kira shi akan meyasa bai zo ba,anan ya sanar mai da ya ga ji,to anan ma dai saida suka yi faWan da suka saba kafin aka rabu."

"Yau kwanan Jemima biyu a gidan su Doctor Mujaheed,hankalinta kwance komai na bukata tana samu,sun siyamata sabbin kaya masu kyau da kayan kwalliya.Haka suke zama da Hindatu suyi ta labari idan Mujaheed ya fita wurin aiki.Matsalar guda Waya ce idan Hindatu ta tambaye ta ina iyayen ta ba amsa sai dai ta saka kuka,dole tasa ta kyaleta."

Ta faWama Mujaheed yadda suka yi ya ce ba matsala a bita a hankali zata sanar masu.

"A ranar da SUDESS zasu koma Abuja shida Salisu around 8 yana bacci ya ji ringing Win wayar shi,cikin magagin bacci ya janyo wayar ko duba mai kiran baiyi ba ya yi picking yana ajeta gefen pilwo."

"Muryar Mujaheed ya je ya ce ""Gaskiya ne dole kake bacci da nasari,to karka bar garin nan sai ka zo ka Wauki yarinyar nan,yanzu na kara tabbatar da bazaka iya kula da mace ba,tunda ka ki zuwa""."

"Cikin muryar bacci SUDESS ya ce ""Pls Doctor wai meya faru,kai dai baka so hankalina ya kwanta,dan Allah ka kyale ni na ji da ayyukan gabana"".ya ida maganar yana juya kanshi gefe Waya""."

"Daga can Doctor Mujaheed ya ce ""wallahi sai ka zo ka tafi da yarinyar nan,ko na kira Uncle Hasan kuma kasan abinda zai biyo baya""."

"Cikin jin haushi SUDESS ya ce ""Wait malam wai me kake cewa?wata yarinya kake nufi?""."

"""Innalillahi wa'innailaihirraju'un"" ya ji Mujaheed ya rafka salati."

"""Yanzu SUDESS ka kawo yarinya gidana yau kwana huWu,amma ka ce ka manta,gaskiya ina ga baka rasa aljanu a kanka,amma karka damu nasan maganin ka""."

"Sauke ajiyar zuciya SUDESS ya yi kafin cikin muryar wasa ya ce ""Afuwan very sorry my bro wallahi kaina ya Wau zafi,kasan bazan yima haka da gangan ba,wallahi ayyuka ne sun sha kaina,amma yanzu kasan idan na je da wannan Girls Win akwai matsala,kasan halin goggo rigima ce zata barke,ka lallaba yarinyar ta faWi unguwar su da gidan iyayenta ka mayar da ita kawai,ni ina ganin wannan ne hanya mafi sauki ko?"". Ya karasa maganar cikin muryar tausayi dan yasan halin bro Win nashi da tausayi,idan ba haka ya yi ba to ba makawa ya dawo mai da yarinyar nan,shi ko wallahi ya manta da ya kai ajiyar ta.haba ina dalilin wannan tashin hankalin a haka ake cewa ya yi aure,sanadin hawan jini ya sameshi."

"Jin ya yi shiru ya kara cewa ""Pls bro kasan kai ne dole na,ba yadda zan yi"" cewar SUDESS."

"""To kana ji kafin ka tafi Abuja ka zo mu tattauna yadda za'a yi,amma wallahi idan har ka tafi baka zo ba saina kawota Abuja,dan Nasan halinka kamar yunwar cikina""."

"Yar dariya SUDESS ya yi jin abinda Doctor Mujaheed ya ce,nan take ya Wan ji san yi a ranshi,dan shi harga Allah bazai iya tafiya da yarinyar nan ba,zata tadomai fitinar kannan mahaifan shi na sai ya yi aure."

"Daga haka suka katse kiran,harya juya yana gyara kwanciyar shi dan bacci yake ji sosai,ya kara jin karan wayar a karo na biyu.Har zai katse ya ga Nomber Uncle Hasan dammmmmmm ya ji gaban shi ya bada wani sauti dan yasan ba magana mai daWi ba ce idan yaga kiran wannan Uncle Win na shi."

"*Chakwakiya iya chakwakiya =ØÞ=ØÞ to wai ya zata kaya ne da rayuwar SUDESS*?""."

*Pls masoya kada ku manta wnn Book Win na kuWin ne*

*By*

*AUTAR AREWA*


'þ
'þ
'þ
'þ
'þ
'þ.

<Øß<Øß *SUDESS*<Øß<Øß

*Written story*

*By*

*AUTAR AREWA*

"*Paid Book ne akan farashi mai sauki ¦ 500 kacal za ki sha krt cikin kwanciyar hankali.Ta wnn Account Nomber 3125654602 Rukayya Idris first Bank, ki turo shaidar biyan ki ta wnn Nomber 08162385196,ko hoton katin MTN pls banda VTU >ØpÝ idan kinsan ba ki shirya ba karmu Satawa juna time*."

*Bismallahi Rahamir Rahim*.

*Free page* 5þã

*Pls banyi editing ba*.

"=ØÝÜ Sororo ya yi yana kallan call Win har Saida ta katse bai motsa ba,wani kiran ne"

"ya kara shigowa still dai Uncle Hasan ne,cikin sanyin jiki ya katse kiran kafin ya kira shi.Ringing Waya ana biyu Uncle Hasan ya Waga.Da sauri SUDESS ya ce ""Assalamu Alaikum Uncle barka da safiya,Ina kwana,ya iyali?""."

"A dakile Uncle Hasan ya ce ""Lafiya, ina maganar da muka yi da kai,kasan yau saura sati biyu ya rage wa'adin da ka ce a baka ya cika ko?ina fatan baka manta ba?""."

"Daman nasan karshen maganar kenan,kai wannan mutumi baya san na zauna lafiya cewar SUDESS a cikin ranshi."

"Maganar da Uncle Hasan ya Kara yi ita ta dawo da shi daga duniyar tunanin daya lula. ""Kana jina ko?"""

"""Eh Uncle ina jinka,ban manta ba insha Allah kafin time Win zan yi abinda ya kamata"" Cewar SUDESS yana kara sunne kai tamkar yana gaban shi."

"""To to hakan dai zai fi,dan wannan karin idan ka kawo mishkila to zaka ga abinda zai biyo baya"""

"Ya ji Uncle Hasan ya faWa kafin suka yi sallama ya katse kiran yana dafe goshin shi daya ji yana saramai tamkar zai faWo.A hankali ya mayar da kan shi jikin pilo yana sauke ajiyar zuciya.Agogon da ke like jikin bangon Wakin ya kalla ganin tara saura mintuna ya yi saurin ta shi ya nufi toilet yana sake-sake a ranshi na yadda zai Sullowa wannan matsalar guda biyu,dan ya fahimci wannan karin ba zasu kara yimai uziri ba."

"Karfe 10:20 daidai ya fito parlon shirye cikin blue shadda mai adon ba™in zaren ulu a gaban rigar sai bakar madaidaicyar hula daya Wora saman kanshi sai tashin kamshin turaren Uhud yake yi fuskar shi fes gwanin sha'awa .saida ya zauna saman doguwar kujera kafin ya Waura agogon shi na silver mai kyau,wayar shi ya Wauka yana niyyar kiran Salisu ganin har yanzu bai fito ba,sallamar shi ya ji daga bakin kofa haka yasa ya fasa kiran.karasowa Salisu ya yi yana gaishe da ogan na shi,amsawa ya yi yana cewa ""Pls salisu time fa yana kurewa,bana so muyi tafiyar dare fa saboda kasan hanyar sai a slow.bedroom Salisu ya wuce ya Wauko trolyn kayan ogan na shi da tarkacen system Win shi ya kai cikin mota,basu tsaya yin break ba suka fita,direct gidan Doctor Mujaheed suka nufa.cikin mintunan da basu haura sha biyar ba suka iso kofar gidan,saida suka yi horn kafin aka wangale masu gate suka kutsa hancin motar su cikin harabar gidan.Salisu yana daidaita parking SUDESS ya nufi cikin gidan,door bell ya danna cikin two minutes aka buWe mai kofar falon.Cikin natsuwa ya shiga da sallama Wauke a bakin shi a tsakiyar kujerun ya samesu saman capet suna break ya karasa bisa kujera mai cin mutum Waya ya zauna yana cewa ""washhh Allah na,na ga ji sosai,ku bani abinci na ci ina jin yunwa""."

Da sauri maman Sudess (jenior) ta tashi ta fara haWamai tea mai kauri da soyayyar doya sai yar miyar jajjage ta Wanyun kayan miya da aka soyata da kaWaWWen kwai sai kanshi ke ta shi.

"A fakaice Doctor Mujaheed ya kalli SUDESS kafin ya ce ""Wallahi bro tausayi kake bani,yanzu da kana da mata duk inda zaka je ka tafi da ita kafin ka shirya an haWama abinci mai rai da lafiya,amma yanzu duk ka zama sorry""."

"Shidai SUDESS ko kallan shi bai yi ba,kasan capet Win ya sauko ya wanke hannun shi a cikin wata faffaWar roba kafin ya yi bismalla ya fara cin soyayyar doya,a hankali yake ci yana kurSar ruwan zafin.Sai da ya Wan ci sosai,kafin ya dubi Hannatu yana cewa ""Pls maman Jenior Salisu yana wace,ku ba shi abinci""."

"Da ""To""ta amsa kafin ta fara haWama Salisu."

"Sosai Doctor Mujaheed ya saka wata uwar dariya harda rike cike saboda tsabar mugunta,dariya yake sosai yana nuna SUDESS da yake ta faman mazurai."

"Sosai SUDESS ya kule takaici ya kama shi,shi kam ya rasa me yake damun Mujaheed ga shi babba amma yana abu kamar yaro.Cikin dakiya ya ce ""Mujaheed Are You out of your sense?bansan meyasa ka raina ni ba,wallahi da nasan haka zaka yimin bazan zo ba,kuma yanzu ma bari kaga tafiya zan yi""ya idar da maganar yana kokarin tashi.Da sauri Doctor Mujaheed ya tare shi yana gimtse dariyar da take san kubcemai ya ce ""Pls bazan kara ba,amma kaima bro kai Win ne ka cika abin dariya,wallahi ka ragama kanka,sannan ka samawa kanka mafita haba,kaga yadda ka faWa kuwa?""."

"""Uhmm dole na rame mana tunda kun taso ni a gaba kaina wancan Uncle Hasan Win,dan Allah ku kyale ni kamar ni kaWai ne mutum a ciki kin familyn mu,kullun ni ne nake laifi haba,Kun takuran da yawa""cewar SUDESS idon shi na taruwa da kwalla wacce shi kanshi bai san kota mecece ba.Doctor Mujaheed ji ya yi ya ba shi tausayi,zaunar da shi ya yi kafin shima ya zauna ta gefen shi tare da riko hannun shi,daidai lokacin Hindatu ta shigo parlon ta dawo daga kaima Salisu abinci,ganin kamar akwai matsala yasa ta wuce room Win Jemima dan ganin kota shirya ne."

"Saida ta shige kafin Mujaheed ya mayar da kallan shi kan SUDESS ya ce ""Come down bro ka kasa fahimtar abinda muke nufi ne shiyasa kake ganin kamar bama sanka,kaga jiya da dare munyi magana da Momy akan wannan issue Win,but karka damu insha Allah very soon komai zai daidaita,kai dai ka ci gaba da addu'a""daga haka suka ci gaba da tattaunawa,saiga Hannatu sun fito Jemima na biye da ita a baya a hankali SUDESS ya mayar da eyes Win shi kansu yana tunanin yadda zai ce idan ya je gida da wannan yar ficiciyar yarinyar,Wannan wace irin ™addara ce?ya tambayi kanshi yana mikewa tsaye.Har bakin mota su Mujaheed suka rakasu,bayan an saka kayan Jemima a both kafin suka shiga da gudu Jemima ta fito ta rungume Hindatu tana saka kuka,itama Hindatu ji tayi wasu kwalla na zubomata saboda a ´an kwanakin nan ta saba da yarinyar bata so su rabu. SUDESS harya zauna ya ga ta fita shima ya fito,cikin takaice ya ce ""Wallahi idan kika bari aka tayar da motar nan to saida mu barki anan,zamu tsaya zaman jiran ki ne?"" Ya ida maganar a hasale yana hararar Mujaheed.Bayan motar Hindatu ta mayar da ita kafin ta rufe kambun motar bayan ta sharemata hawaye,ta zagayo gefen da SUDESS ya ke ta ce ""Sorry bro Allah ya tsare hanya,a gaishe da su AUTAH""."

can kasan makoshi ya amsa kafin suka tayar da motar suka nufi hanyar fita daga gidan.shiko Mujaheed gaba ya yi ya kyale Hindatu a tsaye tana faman Waga masu hannu har suka fice daga gate Win kafin itama ta juya cikin gidan da gudu wani kuka mai tsima rai yana kufcemata.

"*To jama'a koya zata kaya a Abuja, gadai SUDESS ya tafi da Jemima,acan kuma Uncle Hasan yana jiran dawowar shi* >ØpÝ>ØpÝ=ØÞ"

*Pls masoya kada ku manta wnn Book na kuWi ne*>ØpÝ

*By*

*AUTAR AREWA*


'þ
'þ
'þ
'þ
'þ
'þ.

<Øß<Øß *SUDESS*<Øß<Øß

*Written story*

*By*

*AUTAR AREWA*

"*Paid Book ne akan farashi mai sauki ¦ 500 za ki sha krt cikin kwanciyar hankali ta wnn Account Nomber 3125654602 Rukayya Idris first Bank.ki turo shaidar biyan ki ta wnn Nomber 08162385196,ko hoton katin MTN pls banda VTU >ØpÝ idan kinsan baki shirya ba karmu Satawa juna time*."

*Bismallahi Rahamir Rahim*.

*Free page* 6þã

"=ØÝÜ Tunda suka fita daga garin na Katsina Salisu ya kara gudun motar,dansu"

"samu isa kafin dare,haka suka yi zaman jugum ba mai cewa Wan'uwan shi komai,shi ogan nasu wato SUDESS chart yake yi a iPhone Win shi,ita kuwa Jemima baiwar Allah bacci ne yake kokarin Waukar ta saboda yadda sanyin ACn yake ratsa fatar jikinta,ga wani daddaWan kanshi mai saka kasala.Haka ta fara gyangyaWi karshe ta kwantar da kanta jikin kujerar da SUDESS ya ke,ta kifa kanta ta koma baccinta.Duk abinda take yi SUDESS yana lura da ita,ya fahimci yarinyar she is very leazy,tana da san jiki,yanzu da kusa da wani ne may be haka zata kwanta jikin shi,kodan tana ganinta yar karama?ya tambayi kanshi yana taSe bakin"

".kokarin kawar da tunanin ya yi yana tuno maganar da Uncle Hasan ya faWamai,gaba Waya kanshi ya cushe ya rasa irin tunanin da zai yi,ya zama dole ya nemo mafita kodan ya huta da korafin wannan mutanen,ga Goggo ta taso shi a gaba itama,haka ya yi ta faman sake sake a ranshi har tafiyar su tayi nisa."

"A daidai wannan lokacin kuwa a Abuja cikin babban gidan su SUDESS tsit kake jin gidan kamar ba motsin mutane sai masu aiki suna ta faman zirga-zirga daga masu shara da goge- goge sai masu ban ruwan fulawa sai Baba tsoho mai gadi wanda kana ganin shi kaga cikakken buzu irin mutanen Niger,a yanayin shekarun shi ya manyanta amma kana hango kyawun shi.Cikin gidan kuwa a part Win Momy ce zaune cikin parlon ta, ta sha ado da sarka ga zobina ta zuba a yatsunta gwanin sha'awa,da alama waya ce ta ke yi jin tana cewa ""To dan Allah Hajiya Karima ya kike so na yi,na yi iya bakin kokarina akan yaran nan amma abin ya gagara,nifa bari ki ji bazan yima Wana auren dole ba,saiya zaSi wacce yake so ehee"". Ban ji amsar da aka bata ba naga ta katse call Win tana faman jan tsaki.Cikin jin haushi ta kara cewa ""Aikin banza kun bi kun takurawa yaro,kowa yasan yarinyar ki bata da tarbiyya,dan haka bazai taSa auranta ba insha Allah koda kuwa bayan raina ne""tashi ta yi ta nufi kitching tana duba yanayin abincin da House girls Win suke dafawa na taryar SUDESS ne,musamman tasa a haWamai amma wasu abubuwan dole da kanta take yimai,saboda bayasan abincin yan'aiki a cewar shi kazanta.Suna cikin aikin Zaheeda ta shigo riga da wando ne a jikinta brown color irin masu santsin nan sai Wan karamin mayafi data Wora saman kanta,da sallama ta shiga kafin ta gaishe da Momy tana cewa ""La Momy wai da gaske yau Yaya SUDESS zai dawo?tunda asuba AUTAH ta damemu sai wani faman murna take yi dan zai dawo,ni site Win Goggo zan koma""."

"""Eh yanzu haka suna hanya insha Allah,dole bazaku so dodon ku ya dawo ba,tunda baku jin magana"".Cewar Momy tana cigaba da aikinta, ganin haka yasa itama Zaheeda ta saka hannu aka ci gaba da aikin."

"Lokacin da motar su SUDESS ta shigo garin Abuja karfe 5:00 daidai sun Wan bata lokaci a Kaduna saboda sun yi Sallah kafin suka ci abinci a wani restorent kafin suka karaso.Gaskiya shi kanshi ya ga saurin tafiyar ya yi tunanin zasu kai dare.Tunda suka doso Unguwar ya ji gaban shi ya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment