You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in yaji yunwar yacima wani bai saniba, ai yunwa ba Umaymah bace ko ke bare zaku lallaɓashi".
Dariya Ummi tayi kana kuma ta haɗe fuska tare da cewa.
"Je kiyi abinda nace ko".
To tace ganin kamar ran Ummi ya ɓaci.

Bayan ta dawo da kwanukan ne,
Suka bawa Saratu ta juye, kana ta harhaɗa wonke-wonken ta fara.

Ita kuwa Shatu cikin yin miƙa tace.
"Ummi me zan dafa mishin?".
Juyawa tayi tana haura wurin da Fridge yake tare da ce mata.
"Duk abinda kika iya kika san ba mai nauyi bane".

Kanta ta gyaɗa tare da cewa.
"To".
Cikin ranta tace.
"Bari inyi Special Arish, in yaga dama yaci in yaso ya bari, mutun sai zaɓe-zaɓe kamar mai ciki.
Dankali ta ɗan ɗebo da Nama, kwai, tumatur, kabeji, Bama, maggi, tafarnuwa man gyaɗa, komai dai dai-dai misalin yadda zata buƙata duk ta ajiyesu kusa da ita.

Fere dankalin tayi ba tare da ta daddatsashi ba. Ta wonƙeshi fes kana tasa a ƴar tukunya tare da tarfa gishiri da ruwa dai-dai misali, sannan ta tafasashi.
Kwan ta ɗauka ta fasa ta kaɗashi da kyau tare dasa yankekken al'basa da Curry da maggi da tafarnuwa ɗan kaɗan.

Ganin dankalin yayine ta juyeshi a ɗan kondo ta tsaneshi.
Tare da ɗan barinshi yasha iska, kaɗan.
Kana ta ɗaura Naman da maggi da gishiri da Curry da tafarnuwa da al'basa. bisa wata a ɗan tukunta.
Sannan ɗaura man ta ɗauki dankalin ta tsomawa cikin kwan tana soyashi, saida ta gama ta ajiyeshi gefe.
kafin nan naman kuma yayi lugub yayi laushin.
saida ruwan ya kusa ƙarewa sai ta ƙara wata al'basar da tumatur suka nuna tare sannan ta kwashesu.
Kabejin ta yayyanka ƙanana sannan ta ɗauki dafaffan kwai ta yayyanka shi da ɗan girma.
Kana tasa Maggi da al'basa da Bama ta gauraya kana
Ummi ta miƙo mata ɗan ƙaramin Foodflaks alamun ta amsa ta saka.
Kanta ta jujjuya tare da cewa.
"Bari in sa mishi a plate kawai tunda ya dawo".
Da mamaki Ummi ta kalleta tare da cewa
"Yaushe ya dawo?"
Plate ta ɗauko tare da cewa.
"Tun ɗazu".
Da sauri ta sunkuyar da kanta ganin kamar Ummi na mata kallon Mamaki da tuhuma.
Ita kuwa Ummi cikin Binta da ido tace,
Ya akayi kika san ya dawo".
Kai ta rausayar tare daci gaba da aikin kamar bataji Ummi ba.
Plate ɗin ta ajiyeta, ta zuba Arish ɗin gefe kana tasa haɗin naman gefe, ta kuma zuba na Kabejin shima gefe.
Ta shiryashi yayi kyau sosai.
Ɗaya plate ɗin ta kife kanshi.
Kana tasa spoon da Fork a cikin tray'n data ajiye plate ɗin.
Ɗan madaidaicin flaks ɗin coffee ta ajiye gefe, kana tasa cup da tea spoon a ciki.
Sannan turashi gefe.
Zuwa lokacin kuma tuni Ummi da Saratu su gama aikin sahur ɗin har Saratu ta tafi.
Sauran ta sako a wani plate ɗin tare da cewa Ummu gashi.
Amsa Ummi tayi tare da cewa.
"Ɗauki ki kai mishi to".
To tace tare da ɗaukan tray'n ta fita.

A tsaye ta sameshi cikin wani tattausan jallabiya da alamun wonka ya fito,
Sai wani irin masifeffen ƙamshi yakeyi.

Cikin nitsuwa ta wuce ta bayanshi, inda yake tsaye yana kunna Tv.

Bisa santa table ɗin glass mai garai-garai dake tsakiyar falon ta ajiye mishi.
Kana ta juya a hankali ta fita.

Kai tsaye ɗakinta ta wuce, nan ta samu Hibba tuni tayi bacci.
Wonka tayi da ruwan ɗumi tare da shafa mai kana tasa wata tattausar rigar bacci gajera iya karta guiwa.
Hibaji ta zura a jikinta kana ta haura gado ta konta tare da jawo blanket ta duƙunƙune a ciki.
Sabida ita bata son sanyi, shiyasa takesa ƙaton hijabi kana ta shiga borgo.
Badon Hibba Bama dake masifar son sanyi da kashe AC'n zatayi.


Ƙarfe ɗaya dai-dai ta tashi bacci al'wala tayi kana tai ta nafila hakama Ummi.
Sheykh Jabeer kuwa tuni ya tashi shima.
Ya kira su Jalal ma a waya ya tashesu.

Ƙarfe huɗu da rabi dai-dai ta isa falonshi da tray'n abincin sahur ɗin shi.
Ta ajiye ta juyo kenan shi kuma yana fitowa falonshi.
Tazo tsakiyar falon kenan tana tafiyarta a hankali ba zato ba tsammani taji daram-dam ƙaran bindigar da kullum da asuba sai an saketa sau biyu, ta kuma kasa sabawa dashi bare ta daina tsoronshi.
Wani irin tsalle da zabura tayi tare da ficewa a guje tana cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Bayanta yabi da kallo tare da taɓe baki kana ya nufi Dinnin area.

Washe gari da safe yau Jumma'a kuma, yaune azumi na shida.

Bayan sun fitone, Ummi ta kalleta cikin dariya dan tuno yadda ta fito falon Sheykh Jabeer a guje da asuba, tana jan Allah ya isanmata ana tsinka mata zuciya,
Cikin murmushin tace.
"Ummi dariyar me kikeyi ne?".
Cikin gimtse dariyar tace.
"A babu, yauwa tashi muje ɗazu Gimbiya Aminatu ta aiko, wai tayi kewarki kwana biyu azumi ya ɓoyeki bakije ba".
Cikin murmushin tace to muje Ummi".
Ta ƙarishe mgnar tanayin gaba Hibba na biye da ita a baya.
Cikin sauri Ummi tace.
"A haka zaki fita ba al'kyabba".
Kai ta ɗan dafe tare da cewa.
"Wayyo Allah na, Allah kuwa ni nauyi sukemin wannan tsarabe-tsaraben wuya gareshi".
Murmushi Ummi tai tare da miƙewa ta ɗauko al'kyabbar.
Tazo tasa kana suka fita.

Da Side ɗin Hajia Mama suka fara,
A falo suka samesu.
Cikin fuskar ba yabo ba fallasa Hajia Mama ta amsa gaisuwar Shatu.
Batool kuwa sai auna mata harara takeyi.
Hira suka ɗan taɓa kana suka fito.
Har sun fito Shatu ta ɗan kalli Ummi cikin sanyi tace.
"Ummi jirani anan bari inje in isar da saƙon gaisuwar Ummey na wurin Hajia Mama".
Da Mamaki Ummi tace to kana ta juya ta nufi ciki, ganin Hibba za biyota ne tace.
"A a jirani ina zuwa".
Haka suka tsaya suna jiranta.

A hankali ta turo ƙafar falon.
Da sauri Hajia Mama ta zuba mata ido fuska cike da tsana.
Batool kuwa binta da ido takeyi ganin wani irin takun isa da ƙasaitar da takeyi.
Kujerar dake fuskantar wacce Hajia Mama ke zaune a kai ta zauna.
Ƙafarta ɗaya ta ɗaura kan ɗaya.
Kana ta jingina da kujerar, cikin tsare Hajia Mama da ido tace.
"Uhummmm kin sanni sarai, kar tasan karne, duk motsinki a tsakiyar tafin hannuna kike, dan haka gwara kiyiwa kanki gada ki fita harka da rayuwar mijina! Da ƙannenshi da wanshi. In kuwa kikaƙi zakisha mamakin Shatu."
Tana faɗin haka ta miƙe, tana kallon Batool da tun randa akace Shatu tazo ta bawa Hajia Mama haƙuri da ta shigo tayi wasu kalaman ya ɗaurewa Batool kai ta kasa tantance tsakanin aya da tsakuwa, shiyasa batayi gigin yin mgn ba, sabida tuno abinda Shatu tace mata a ranar cewa.
"Mijina kike so ko, to kizo in ya amince ya kalli inda kike na daƙiƙi biyu rak zan sashi ya aureki".
Da sauri Batool ta dawo daga duniyar tunanin da take jin ƙaran rufe ƙofar da Shatu tayi.

Ido ta maida kan Hajia Mama dake gurnani kamar macijiya.


Jim kaɗan ta fito.
Cike da son gano wani abu Ummi ke binta da ido, amman ta kasa gano komai domin Shatu ta iye takunta, ta fito kamar ba itaba gaba tayi.

Kana suka nufi Side ɗin Gimbiya Aminatu.
Suna shiga ta miƙowa Shatu da Hibba hannu kusa da ita ta ajiyesu.
Bayan sun gaisane ta kallesu tare da cewa.
"Azumi ya boyeku da yake ku ragwagene".
Murmushi sukayi tare da cewa.
"Kai Gimbiya jiya nefa kawai bamu zoba".
Cikin kula Lamiɗo dake shigowa yanzu zai sabunta al'wala zai wuce masallaci yace.
"Shatu matar malam bauɗeɗɗe".
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kai.
Hibba ce tace.
"Sai na gaya mishi".
Dariya sukayi kana suka sallamesu suka tafi ganin lokacin sallan yayi.
Har sunje bakin ƙofa Gimbiya Aminatu tace.
"Yauwa Jakadiya kayan miyanku da saura ko ya ƙare?".
Cikin rusunawa tace.
"A'a da saura sosaima".
Kai ta gyaɗa kana suka tafi.
A hanyarsu ba komawane Shatu tace.
"Ummi wanne kayan miyan ne?".
Cikin sanyi tace.
"To ba kince bakya son na Hajia Mama ba, shine ita kuma Gimbiya Aminatu ta haɗo miki komai yanzu dasu muke amfani ai".
Cikin gamsuwa tace.
"To wancan ɗinfa ya akayi dashi?".
"Umaymah ta tafi dashi duka".
Hibba ta faɗa mata.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Ba matsala".

Nan suka tafi suna salla suka shiga kitchen yau harda Hibba.


Sannu-sannu dai bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'a jeba.

Yau an cika azumi goma. Gobe za'a shiga goma na wuya, an gama na marmari.


Yau kuma makara Shatu tayi.
Ganin har su Jalal sun zone yasa Ummi ta nufi ɗakinsu.
Ai kuwa kan gado ta hangosu.
Tadasu tayi kana ta fito.
Tana cewa.
"Shatu kiyi sauri kizo ki kaiwa Sheykh nashi".
Kusan a tare suka diro ƙasa.
Brush kawai sukayi suka fito.
Da ƙaton hijabin ta fito.
Tana zuwa Dinning area Ummi ta miƙa mata tray'n abincin nasa.

Amsa tayi ya juya ta nufi falonshi.

Tsaye ta sameshi gaban show glass ɗin dake gefen Fridge ɗinsa dake Dinning area,
Cup ne a hannunshi cike da madarar gongoni da molt a haɗe.
A hankali ta wuceshi kaɗan ta ajiye tray'n.
Kana ta juyo da nufin sauƙowa, taku ɗaya tayi a na biyu ta iso gabanshi kenan.
Aka saki bindigar shaidar huɗu da rabi tayi.
Wani irin zabura tayi tare da af....!



Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276, domin shiga Normal group wanda a wata ɗaya za'a, gama Part one. Ko kima kiyi min TRANSFER ɗin 1k ta asusuna na Jaiz bank, domin samun shiga Special Group wanda a sati biyu cakal za'a gama Part two da izinin ubangiji, 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853297.

Ke mai haushi kin turo ɗarinki uku, kinzo kinata haushi, nace ki turo ac no ɗinki in maida miki kuɗinki kin tsaya yimin tumasanci shiyasa nayi Black ɗinki, a rashin Sa'a na haɗa da number ki na goge. Kuma baki Turo ac na na meda miki shi ba. To Alhamdulillah a take a lokacin nayi miki sadaka da ɗarinki uku, ubangijina shine shaidata, banci kuɗinki ba, nasan zakiga PAGE ɗin sabida akwai waɗanda basu san darajar Allah da Manzonsa da iyayensuba, zasu fitar, to kiji ni Shatu na sauƙe nauyin ɗarinki uku.

By
*GARKUWAR FULANI*

Tare da cewa."Lahh Ummi kalli Hamma Jabeer kusa da Uncle Jabir Ali ɗin can".
Cikin Murmushin Ummi tace.
"La ai kuwa, Allah sarki masha Allah, tabarakallah. Allah ka ƙarawa Annabi daraja, Allah ka ƙara bamu hasken addini da imani a zuƙatanmu."
Amin Amin Hibba tace.
Tare da juyowa ta kalli Shatu da tayi kamar bata jisu ba,
Sai tea ɗinta take zuƙa a hankali.
A zahiri zakace idonta kan cup ɗin yake, amman a baɗini kan allon TV'n idonta yake, ta zubawa fuskarshi ido. Duk da bawai kai tsaye shi kaɗai ake ɗaukaba, limamin dake jansu ake ɗauka hakan yasa suma suka fito da yake yana cikin mamun limaman sahun forko.

Sosai take ƙare mishin kallo tare da tsarin shigarsa dana mutanen da yake cikinsu.
Sam bazaka iya bambance shi da suba, Especially ma Sheish Jabir Ali da yake matuƙar kama dashi.
Haka nan taji wasu irin zafafan hawaye masu ɗumi suna tsastsafo mata cikin jijiyoyin idonta.
Ta kuma kasa janye ƙwayar idanunta kanshi. Tana kallon tsarin shigarshi da kullum take ganinshi a matsayin takura.
Lumshe idonta tayi, kana ta buɗe su.
Ummi ta kalla wacce farin cikin ta ya fito fili.
Hakama Hibba. Sai murnar abun takeyi tamkar tayi tsalle ta shiga cikin TV'n,.

Ganin sun sunkuya kai ruku'uh da zasu tafi sujjada ta biyu ne, kuma an ɗaga camerar an maidata ɗaukar samane.
Yasa ta miƙe a hankali bisa santa table dake tsakiyar falon ta ajiye cup ɗin kana ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi kinji masallacin Joɗa ma sun fara sallan kuma muna zaune".
Da sauri Ummi ta miƙa tare da cewa.
"Farin cikine ya rufeni Shatu,. Muje muyi al'walan mu tafi".
Uhum tace ta juya ta nufi falonta tana mai share hawayenta da har yanzu suke zubowa, tanajin zuciyarta na amsar wani nannauyan abu a kan Sheykh, ta yarda ta gamsu cewa mutun me ibada da imani da ilimi abin sone a zuciyar kowane mutum na gari.

Bayan sunyi al'wala ne suka fito cikin manyan jihabai ƙatti har ƙasa suka nufi woje.
Ananne Shatu tai mamakin ganin yadda kusufa-kusufa matan masarautar ke fitowa, duk suka nufi hanyar zuwa masallacin ta ƙofar dasu Lamiɗo ke bi.

Suna fitowa jikin masallacin sai ga wani ƙaton rumfa na ƙara an lailayeshi da wani irin yashi fari ƙal-ƙal kana ga hasken wuta a cikinsa.
ko wacce da sallaya a hannunta tuni wasu kuma sunma shimfiɗa sallayunsu sunbi jam'i hakanan matan maƙota da sauran matan bayi da hadimai duk nan suke zuwa.
A jeru gaba ɗaya ananne ga kafaɗar matar sarki gata baiwa.
Babu matsayi ko milki bare isa ko ƙasaita.

Haka dai suka bi jam'i sai ƙarfe uku aka idar akayi addu'o'in kana akashafa aka kai sujjadar ƙarshi ta witirin.

Kana akayi taiya akayi sallama duk kowa ya nufi gidanshi.
Daga nan kuma aka kama aikin sahur.

Suna dawowa Hibba ta kuma kunna TV nan ta samu su tuni su sun idar. Wasu nata ɗawafi ne sai addu'o'in ake jerawa.
wanda sai kaji tsikar jikinka na tashi sabida yadda yake ratsa zuciya da jini.

Washe gari da bayan sallan isha'i da asham, yanzu Jalal da Jamil ne kaɗai ke zuwa dan Imran da Sulaiman ma dasu aka tafi.


Haka yasa yanzu duk suna zama a Dinning table suyi buɗa baki a tare.
Jalal ne ya ɗan kalli Ummi cikin cin Beans salad da Shatu tayi musu.

Hibba ce keta santi tana cewa.
"Alhamdulillah yanzu dai saura mana azumi tara ko takwas".
Murmushi sukayi, ita kuwa da sauri tace.
"Kai takwas nema in sha Allah".
Jamil kam tuni yake dariya tare da cewa.
"Tara ne".
da sauri ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi wai haka ne?".
Cikin dariya tace.
"A a ban saniba Hibbat."
Plate ɗin data zuba ferfesun jan nama ta jawo tare da fara ci tana lumshe ido tace.
"Takwas ɗin nema in Allah ya yarda".
Allah yasa haka Shatu tace.
Sai yanzu Jalal ya ɗan kallesu tare da cewa.
"Ashe dai duk kanwar jace".
Murmushi Ummi tayi kana sukaci gaba da cin abinci.


Yau dai ana zaton salla saura kwana biyar ko shida.

Da hantsi suna zaune dan yau sun tashi da wuri.
Aunty Juwairiyya ce tayi sallama tare da shigowa, Bayan Ummi ta amsa mata.
Gefen Hibba ta zauna tare da cewa.
"Alhamdulillah Ummi ɗinkunan mu sun dawo, yanzu KB ya kawosu ya shigo ko?".

"Eh ya shigo mana".

Juyawa tayi ta kalli Hibba tare da cewa.
"Je kice ya shigo Hibba yana nan zaki kanshi cikin baƙar mota".
To tace tare da miƙewa da sauri.

Jim kaɗan suka shigo tana gaba da jaka a hannunta yana biye da ita a baya da ƙattin jakunkuna guda biyu da wani yaro shi shima da manyan jakukkunan biyu.

A tsakiyar falon bisa carpet suka aniye jakunkunan kana, ɗaya yaron ya juya ya fita.
Shi kuwa Kabir ya zauna a ƙasa bisa carpet ɗin tare da cewa.
"Barka da hantsi Ummi".

"Barka dai Kabiru, munyi Sa'a an cika mana al'ƙawarin ko".

Murmushi yayi tare da cewa.
"Sosai ma kuwa Ummi aini telane mai amana".
Hibba ce ta ɗanyi murmushi tace.
"To ka bari a yebeka mana".
Cikin dariya ɗan matashin yace.
"A a ai duniyar yanzu kawai ka yabi kanka, dan ba lallai bane wani ya yaba maka".
Dariya sukayi duka.
Kana ya fara firfito da kayayyakin.
Ko wanne da sunan maishi a jikinshi.

In ya fito dana Ummi sai ya miƙa mata, in ya fito dana Aunty Juwairiyya da yaranta sai ya miƙa mata.

Hakama na Hibba yana fitarwa yana miƙa mata.

Shatu da yanzu ta fitone, ya kalla tare da cewa.
"Barka da safiya Sayyada Shatu".
Murmushi tayi Allah ya sani in sun ce mata Sayyada dariya suke bata wato irin ita matar Al Sheykh ko.
Cikin nitsuwa da danne dariyarta tace.
"Barka dai".
Sai kuma ta ƙara so ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi waye ne shi?".

"Telan mune". Ta bata amsa a taƙaicd.
Cike da mamaki tace.
"To ina ya sanni?".
Hibba ce ta amshi zancen da cewa.
"A hoto ya sanki, da mukaje kai ɗinkunanki hotonki kawai aka nuna mishi, ya ɗinka kuma kinga komai yayi dai-dai ko".
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Lallai kam yayi ƙoƙari".

Cikin dariya yace.
"Uhum ai na iya aikina sosai Sayyada".
Yanzu kam dariya sukayi duka.
Kana ya zaro kayanta a ƙalla kala takwas ya miƙa mata.
Amsa tayi tare da cewa.
"Sannu".
Hibba kuwa irga kayan tayi tare da cewa.
"Kb saura kala bibbiyu a namu nan gani basu".
Kanshi ya ɗan sosa tare da cewa.
"Wannan yarinya akwai son kalato laifin mutum to sai jibi zan kawosu ko kuma in bawa Su Jamil in sunje amsar kayansu".
Cikin murmushin Aunty Juwairiyya tace.
"Yauwa ka bawa su Jalal ɗin ma kawai".

To yace, kana ya miƙowa Ummi ƙatuwar jakukkuna guda uku tare da cewa.
"To Ummi ga na yaranki".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ka kyauta min Kabiru ngd matuƙa, Allah yayi al'barka".
Amin Amin yace kana ya sallamesu ya fita.


Ita kuwa Ummi Saratu ta kwaɗawa kira tana zuwa.
Ta tace.
Jeki kira duk sauran hadimai suzo duk wadannan Kabiru yazo ya gansu ranar."
Da sauri tace.
"To kana ta juya ta fita.
Ita kuwa Ummi. Inda take zaune ta nunawa Shatu.
Tare da cewa.
"Zo nan ki zauna, zasuzo, ko wacce zata gaya miki sunanta, sai ki duba sunan jikin kayan sai kibata, su duk kala ur'uku akayi musu.

Zaki basu da kuɗi dubu biyar-biyar.
Kai ta gyaɗa kana da sauri ta koma ɗalinta.
Sabida. Sai yanzu ta gano me zatayi da wannan kuɗin da ya bata kenan.
Kuɗin ta kwaso kana tazo ta zauna.

Nan suka rinƙa zuwa suna gaidata da gaya mata sunansu. Kana Hibba ta irga dubu biyar, ta ɗaura kan kala bibbiyu sun ta basu.
Ummi kuwa jakan gabanta ta buɗe tana basu takalma.
Aunty Juwairiyya kuwa jakar hijabai ta buɗe tana basu.
Suna godiya suna tafiya.
Haka sukayi tayi har kusan awa biyu kafin suka gama, duk kayan sun ƙare sai kuɗin ne ya rage.

Ganin lokacin salla yayi ne, suka tafi.

Bayan sun idar da salla ne, suka fito.
Nan a falon Shatu suka zauna.
Suna ɗan hira sabida yau aikinsu baida yawa, kuma Saratu nacan na rage musu.

A hankali wayar Ummi ta fara suwa, alamun ana kiranta.
Da sauri ta kalli Hibba tare da cewa.
"Hibba ɗauko min wayata a ɗaki".

Miƙewa tayi tare da cewa to.
Jim kaɗan ta fito da wayar da sauri ta miƙa wa Ummi wayar a kunne tare da cewa.
"Amshi Ummi kiyi mgna na amsa kiran Hamma Jabeer ne, kin sanshi baya kira biyu."
Cikin sauri da tarin jin daɗi Ummi tace.
"Assalamu alaikum".
Shi kuwa Sheykh Jabeer a can saudia yana tsaye ne a gaban dreesing mirror yana gyara igiyoyin al'kyabbar jikinshi.
Tare da saƙala wayar a kunnenshi ya matseta da kafaɗarshi.
Alamun sauri yake yana shirin tafiya haramine.

Cikin sanyi yace.
"Wa alaikissalam. Barka da gida Ummi".
Fuska a sake tace.
"Barka dai Sheykh, ya ibada?".

"Alhamdulillah Ummi, yasu Jalal".

"Suna lfy, kuma basa wasa da ibada, yanzu Jamil ya dena zuwa hirama wata ƙil kuma ya ɓata da Khadijah naji yanzu wata Maryam yake kira, Jalal ne dai yake ɗan fita shima ba sosai ba".
Gyara tsayuwarshi yayi tare da cewa.
"To Alhamdulillah, eh shi Jalal ba matsala fitanshi, nasan dashi.
Ya Hibba kuma tana azumi ko batayi?".
Cikin murmushin da kallon inda Hibba take tace.
"A a Hibba ai an girma yanzu ta rage rakinma".

Ɗan karamin mataji ya ɗauka yana kontar da sajenshi yace.
"To Ummi na gaisheku, na kira Aunty Juwairiyya kam nani jikin ya Jafar da sauƙi sosai mun gaisa da Hajia Mama, har take cemin Affan ɗina zai dawo a salla".
Da sauri tace.
"Uhum Sheykh".
Ajiye kum ɗin yayi tare da cewa.
"Na'am Ummi".
Cikin sanyi tace.
"Ga Shatu".
Shiru yayi baiyi magana ba, kuma bai katse kiranba,
jin haka yasa ta kuma cewa.
"Sheykh".

"Na'am Ummi".
Ya kuma cewa.
A hankali tace.
"Ga Shatu".
Still baiyi mgn ba, hakanne yasa a hankali ta mannawa Shatu wayar a kunne ta.
Kana ta sa hannunta ta kamo hannun Hibba suka fita babban falon.


Shi kuwa Sheykh Jabeer shiru yayi tsaye gaban dreesing mirror, yana kallon gemunshi.
A hankali yake jiyo sautin sauƙar numfashin can ƙasa-ƙasa, ɗis ɗas haka yaji ƙasan zuciyarshi na harbawa.

Ita kuwa shiru tayi tanajin sautin tasbihi da yakeyi can ƙasan-ƙasan maƙoshinsa,
Lips ɗin shi na motsawa a hankali suna fidda sautin can ƙasa.
Jin shirun yayi yawane yasa a hankali ta buɗe bakinta tare da cewa.
"Assalamu alaikum".
Sai kuma tayi shiru ta kasa kunnen dan jiran amsarshi.
Gyara zamanta tayi tare da ƙara riƙe wayar, numfashi ta sauƙe a hankali.
Hakan yasa yaji sautin iskar.
Har ta cire tsammanin zai amsa sai kuma taji muryarshi can ƙasa yana cewa.
"Wa alaikissalam. Ashe kin iya sallama?".
Ya jefo mata tambayar a gajarce.
Cikin juya ido tace.
"Ba'a koya min da wuri bane!."
Shine mgnar da tayi niyar gaya mishi, sai kuma tayi mgnar a zuci, ta danne abun.
Sabida tana son ta nemi al'farman addu'o'in a kaba, aka yayunta da suka bace, shiyasa cikin sanyi tace.
"Eh, Ummi ta koya min".
Shiru yayi kamar bai jitaba,
ita kuwa a hankali tace.
"Ina kwana".
Kanshi ya ɗan kalla a madubi tare da cewa.
"To Kifin rijiya su nan yanzu wunine".
Cikin sanyi da sassauta Muryar son isar da buƙatar ta tace.
"To ina wuni"."Alhamdulillah".
Ya bata amsa.
Miƙewa tsaye tayi ta nufi bedroom ɗinta.
Tare da cewa.

"Ya ibada?".

"Alhamdulillah". ya kuma cewa.
"Har ya kai hannunshi zai janye wayar sai kuma ya tsaya jin tana cewa.
"Uhmm, Ayyah Yah Sheykh..".
Sai kuma tayi shiru. Cikin saurin jin an kira salla murya a nitse yace.
"Uhumm Ayyah, me ɗin?".

Da sauri tace.
"Dama.. dama!!...".
Gajeren tsaki yaja tare da cewa.
"Sauri nakeyi zan tafi masallaci, kada kisa na rasa damata".
Cikin rauni da muryar dake nuna cewa tana zubda ƙwalla tace.
"Ayyah dan Allah da Manzonsa.
In kaje kayi min addu'a a harami mana".
Juyowa yayi yana kallon Haroon da Ya Hashim da suka shigo yanzu alamun kiranshi zasuyi.
Cikin wata iriyar murya a hankali yace.
"Addu'ar me zan miki?".
Murya na rawa tace.
"Allah ya dawo min dasu Yayana lfy, ya kare minsu a duk inda suke, ya baiyana sucikin gaggawa".
Cikin rashin fahimtar zancen nata yace.
"To zan miki saboda Allah da Manzonsa da kikace".
Cikin jin daɗi tace.
"Ngd matuƙa Allah ya biya maka buƙatunka."
Wani irin sassanyan numfashi ya sauƙe tare da lumshe ido a hankali yace.
"Amin ya rabbil izzati, kema kuma kiyita addu'a ki dage da ambaton Allah zai cika mana dukkan burinmu".
Yana faɗin haka ya katse kiran.

Ita kuma murmushi tayi tare da share hawayenta.
Cikin sanyi tace.
"Ya Allah ka dubemu da idon rahama".
Hibba dake shigowane tace.
"Amin Amin."

Daga nan suka fito falo suka kama sabgoginsu.

A kwana a tashi asarar mai rai.
Yau da gobe kayan Allah.
Kamar yau aka kama azumi gashi yau an kai azumi na ashirin da tara.
Wanda ake tsammanin tsalla gobe ko jibi.

Irinsu Hibba duk sunfi fatan wata ta dawo yau.

Gaba ɗaya wunin yau aiki Ummi da Shatu da Saratu suka wuni yi, wanda aikin salla ne.
Zabbin da Jalal ya kawo bisa umarnin Hammansun.
Da kuma kajin da Lamiɗo yasa aka rabawa al'ummar masarautar Joɗa.
Ko wani Side in dai akwai mace kaji goma ake kaiwa.
Da tarin kayan miya komi da komi, wanda shi cikin lambun masarautar ake cirewa.
Kajin kuma daga gidan Gidan gonar MJ aka kawo, kana zabbin da aka kawo manyan sashin Masarautar Joɗa ma daga gidan gonar MJ aka kwasosu. Haka ƙoyayen kaji.
Duk an rarraba ko ina.
kuma duk saida aka yanka su aka gyarasu aka rarrabusu, dan haka aiki kawai aka fara babu kama hannun yaro.
Hadimai da bayi sunata aiki.

Duk sauran ɗinku nan suma sun dawo.

Kasan cewar kusan a kitchen ɗin suka wuni ne, yasa Shatu ta ɗauki zabbi uku tun da azahar tayi musu gyara na musamman.
Hibba kuwa tana Side ɗin Aunty Juwairiyya anayi mata zanen lalle.

Akan sai dare za'ayiwa Shatu shiyasa taketa kimtsa aiyu kanta da wuri.
Dama sunje da sassafe an wonke musu kai an gyara musu.

Ummi kuwa tayi lallenta na gargajiya tana kwance a falo.
Hakane yasa Shatu ta kira Gimbiya Aminatu.
Cikin wasa tace.
"Gimbiya a ƙaro min mai taya aiki yau Ummi na tasa lalle, Hibba ma tana can ana zana mata, nida Sara ce kaɗai a kitchen."
Dariya Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa.
"To Sayyadar Sheykh bari Larai tazo".
Cikin jin daɗi tace.
"To Gimbiyar Lamiɗo".
Dariya sukayi duka kana sukayi sallama.

Juyowa tayi ta kalli Ummi tare da cewa.
"Tace zata turo Larai, Ummi ta iya aiki ko?".
Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.
"Sosai ma kuwa".
Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa kana ta miƙa wa Ummi wayarta tare da cewa.
"Ummi sai mun nitsu ki bani number Gimbiya Aminatu".
To tace kana ta koma kitchen ɗin.

Wanke zabbin tayi fes tare da ɗan matsa lemun tsami kaɗan a ciki.
Kana ƙara lallaɓeshi.
A tukunyar ƙirar ƙasar Cameroon ta zubasu.
Kana tasa al'basa, Curry, Maggi, kanamfari, citta, tafarnuwa kaɗan, da gishiri ɗan ƙanƙani.
Ta rufe tukunyar da zabbin uku suka cikashi.

Bisa gas ta ɗaurashi kana tasa wutan dai-dai.

Saratu kuwa sa sauran tayi a babbar tukunta tasa kayan ƙamshi da ɗanɗano.
Sannan ta ɗaura.

Dai-dai lokacin Larai ta shigo.
Bayan sun gaisa ne, ta ɗauki markaɗen waken ƙosan da zasuyi na kaiwa masallaci.

Da markaɗen tattasan da taruhu da al'basan.

Ita kuwa Shatu yau kunun basise ta dama mai kyau, ta cika kulolin.
Kana
Ta daura ruwan tea
Yana tafasa ta ɗura a flaks.

Duk wannan zabbin sunata sulaluwa suna bararraka sai wani irin masifeffen ƙamshi da yake tashi.
Har yawunsu na tsinkewa.

Fruits ta ɗebo a Fridge ta gyarasu ta shiryasu a tray biyu shiri mai kyau.
Kana ta medasu cikin ƙaramin Fridge ɗin data kashe dan sanyi

Please Login or Register in order to submit comment