You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng Ouummey 01 {4/28/2023 }

😭 *RASHIN HAIHUWA*?

_(Ƙaddarar wasu matan)_

Na
💝💖* Ouummey* 💞💕

Wattpad @ouummey


Godiya
Da sunan Allah me Rahma me jin kai, dukkan Godiya ta tabbata ga Allah SWT Ubangijin
talikai, me kowa me komai da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi me suna a sama
cikin koshin lafiya, ina addu'ar Allah ya bani ikon gama shi kamar yadda na faro ya
sa mu amfana da duk wani darisin cikin sa, kuskuren cikin sa kuma Allah ya yafe
min.

*Jan hankali*.
This book is a total work of fiction, suna, gari kasa ko wani abu daga cikin
labarin in aka yi rashin Sa'a yayi daidai da naki to fa arashi ne, ban rubuta
wannan littafi dan cin mutunci ko wulakanta wani ba face dan ganin yada ce in fito
da virtues din matan da rashin haihuwa yasa ake yi wa kallon kaskantattu,
wulakantattu ko marasa amfani, a guji yanke wani abu ko juya min labarin ta kowace
siga dan tabbatar da zaman lafiya, kamar yadda na faɗa wannan labarin ƙirƙirarre ne
bisa fasaha da baiwar da Allah ya bani tare da yin duba ga rayuwar mu da abubuwan
dake faruwa cikin wasu gidajen auren.

*Dedication*
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya
jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye
jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya
hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan
mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su
ba sai dan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace
uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.

______________________________________
______________________________________

_Free Chapter One_


Tun daga kasa har sama nake karewa kaina kallo ta cikin tafkeken madubin da ke
girke a dakin baccin nawa, babu ta inda na hango wata makusa ko kasawa a tattare da
ni, hakan be wadatar da ni ba sai da na sake ɗagowa na sake sako duban tun daga kan
yalwataccen gashin kai na bakikirin dake kwance kan kafadu na, a hankali na sauke
duba na kan matashiyar fuska ta dake cike da tashen kuruciya, ba wai na budurtaka
ba a'a na shekarun tashe ga iri na da muke kan wannan mataki, zagayayyar fuskar ta
ɗauke take da wadatattun idanun da Allah ya ƙawata ta dasu, farare tas masu haske
da matukar daukar hankali, ban tsawaita ba na sauko kan dogon karan hanci na da ya
dada wa fuskar kyau bayan idon, hanci na ba siriri bane zut ɗin nan yana da dan
fadi kadan da yasa ya zauna das kan fuskar, kyakkyawan ƙaramin baki na me ɗauke da
madaidaitan lips da basu cika karanta ba haka kuma ba manya bane, a hankali kuma na
lumshe idona na buɗe tare da sakin kyakkyawan murmushin da ya bayyana jerarrun
haƙora na da basu kasance farare ba sedai milk ne masu kyau da suke samun kula a ko
yaushe.
Cikin wani irin yanayi na girgiza kai na wani abu na tsirga min cikin raina na
sunkuyar dashi kafin cikin karfin halin da na saba yi na bude na cigaba da
surveying jikina, a kan cikakken wuya na idanuna suka sauka wanda ke dauke da wasu
layi haka ko guru guru zance, cikar kirjina dake fisgar hankali na maida kaina
farin ciki na ratsa ni, shafaffen ciki na da bashi da alamar ɗagawa balle in aje
tumbin da wasu daga cikin sa'anni na ke korafi dashi suke kuma sha'awar lafewar
cikin nawa sai dai gare ni hakan shine ciwo mafi girma ga rayuwa ta dan babban
burin na a wannan duniyar be wuce in farka in ga cikina ya tasa kamar kowace mace
da Allah ya albarkace ta da arzikin haihuwa ba.

Da kyar na haɗiye wani mugun miyau ina janye duba na daga wajen na maida kan
faffaɗa kuma cikakken kugu na wanda shine abu mafi daukar hankali a jikina gaba
ɗaya, nikaina yana daya daga cikin halitta na da nake alfahari dashi dan shine
kadai abu ɗaya da ya rage min da ya riƙe ni a gidan aure na ya kuma sa nake da yar
ragowar kima a idanun mijina wato surar da Allah ya min, ban tsawaita ba na karasa
kan kafafuna dake wadace da jan lalle wanda bana rabo shi, lallen ya zauna daras
kamar a kai a aka ƙirƙire shi, yadda ya haska farar fata ta kuwa abin ba'a ce wa
komai.

Babbar ajiyar zuciya na sauke dana gama karewa kai na kallo kafin cikin sanyin jiki
na dauki kwalbar turaren da tuntuni shi ne zan shafa amma na tsaya kallon kaina
kamar bakuwar kan nawa, zazzagwa nayi a hannu na na shiga shafe lallausar fata ta
dashi lungu da saƙo sannan na aje, wata na kuma ɗauka itama na murza a hannun na
shige shafe wasu wurare masu mahimmanci a jikina, ina yi ina yan tunane tunanen da
suka zame min jiki a duk lokuta irin wannan.

Ringing din wayata dake aje kan bedside drawer yasa na dawo hankali na sosai na
shiga shiri da sauri dan nasan ba kowa ke kiran ba se oga, na dade da sanin ya
tsani jira musamman daga gare ni kamar yadda yake faɗa min times without number sai
too ifdai nikuma ya riga ya zame min jiki musamman a kwana kin nan.

Kayan bacci na ciro masu kyau, laushi hadi da daukar hankali na zura ina tattare
gashi na waje ɗaya na kama shi cikin ribbon, duk da na shafa wasu turaren kafin sa
kaya ba hakan ya hanani sake fesa wasu ba wanda suka sa take dakin ya cika da
sassanyan kanshi na me ratsa zuciya wanda nake amfani dashi kadai lokacin da zan je
ga oga.

Waya ta na ɗauka na kashe batare da duba komai ba dan bani da lokacin hakan me ni
na can na jira na kuma san tuni ya cika yayi fam se nayi rarrashi.

Seda na sawa kofa ta key dan gudun matsala da jan magana sannan na wuce upstairs
inda nan ne turakar me gidan take, seda nayi Knocking tare da dan dakatawa sannan
na tura ƙofar a hankali ina me yin sallama cikin daga murya dan ankarar da na cikin
dakin cewa gani nan fa tafe.

Nasan zaku yi mamakin wai na tsaya knocking ni da dakin mijina da addini ya bawa
damar shiga wajen sa duk sanda naso haka kuma ganin sa cikin kowane yanayi halak ne
gare ni, to ba komai yasa nayi hakan ba face gujewa haduwa da ɓacin rai, a irin
wannan yanayin na kan ci karo da mabanbanta takaicin da kan hanani bacci wasu
lokutan yayinda wasu lokutan kuwa nake hana zuciya ta damuwa ko da kuwa taso yin
hakan.

Ajiyar zuciya nayi hango shi zaune ken bed Yana danna waya, cikin tafiya ta me
daukar hankali da kuma karin wasu salo dan sace zuciyar oga na kai gefen mirror ɗin
sa na aje yar jakar kayan hannu na sannan na karasa gare sa wanda tun shigowa ta da
yayi min kallo ɗaya be sake yi ba.

Cikin jikin sa na shige ina manne masa kamar wata cingum na sanyaya murya dan nasan
nayi laifi haka kuma na shagwaɓe fuska cikin fatan samun lagon sa
"Am sorry zuma naaa, na tsaya shirya maka kaina ne ta yadda zaka mori daren ka cike
da annashuwa da farin ciki, ayi min afuwar dadewar da nayi plsss".

Na karasa ina kai hannuna cikin ƙirjin sa ina masa waiwayi cikin salon da nasan
baze iya jurewa ba, kamar yadda na sani kuwa lumshe idon sa yayi tare da rike
hannun da ke yawo jikin nasa kana ya bude su ya zuba kan fuska ta

"Kullum se kince ayi miki hakuri kuma ba haka ze Hana gobe ma ki sake ba, na kasa
gane meye matsalar ki Khadijah, ke ba da ba ba jikan da zaki fake da kula da shi ba
amma ko mariya dake goyo ba zata faɗa miki kawo uzuri ba, Allah ya sani kin fara
kaini bango dan na fara gajiya da uzurorin ki marasa kan gado da bakya rasa na
bayar wa kullum".

Daga jikin nasa da nake kwance na lumshe ido zuciya ta na motsawa, ba se Salees ya
tuna min da cewa ban taɓa haihuwa ba, ba se Salees ya tunatar da ni bani da tsuntsu
bani ga tarko ba dan hakan abu ne da bana taɓa mantawa ko da kuwa acikin mafarki
ne.

Sanin shiru na wata matsalar ze jawo yasa na daure rashin daɗi na na bar shi iya
cikin raina yayinda a zahiri na ɗago na sumbaci bakin sa ina tabbatar masa insha
Allah ba zan kara ba wanda hakan yayi tasiri gare shi dama kuma be fiya riko ba,
cikin zakuwa da natsuwa ya shiga birkita nutsuwa ta da salon sa masu tafiya da ruhi
na suke kuma karamin kaunar sa a ko da yaushe inda nima tuni na biye masa muka fada
cikin wata duniya me wuyar bayyanuwa, seda duk muka sami nutsuwar da ta dace kafin
muka shiga wanka dan yin shirin kwanciya.

Ko a cikin toilet din ma be bar ni haka ba dan se da yayi neman maganar sa san rai
kafin muka wanko jiki muka fito, cikin sanyin jikin gajiyar da ya tara min na maida
kayana tare da hayewa kan gado na lafe ina sauke numfashi yayin da gefe ɗaya nake
mamakin rashin faruwar lamarin da ya zame mana jiki cikin watanni ɗaya zuwa biyu da
suka wuce.

Ban kai ƙarshen mamakin ba sautin kukan yaro ya fara ratsa kunne na, tun ina jiyo
wa kasa kasa har ya fara ƙarfi alamun ana nufo dakin ne, cike da takaici na tsurawa
kofar dakin ido cikin jiran faruwar sabon mu, dukan kofar aka shiga yi kamar a
filin yaki wai kuma hakan da sunan knocking ne fa ake yi, daga kwancen da nake ban
motsa ba naga tashin sa daga kokarin kwanciyar da yake yi kusa da ni ya bude dakin
yana ɗan haɗe rai.

"Ka gan shi nan yaki yin shiru, nayi nayi wallahi se kuka yake har na rasa yadda
zan masa, ni yadda yake yi ne ma yafi bani tsoro kalli kaga se wani miƙewa yake
kamar ze shide".

Ai oga se ya nemi haɗe ran da ya ɗan yi ya rasa ya kai hannu cike da hanzari ya
karbi dan ya shiga riritawa, kamar abin shiri yaro maimakon yayi bacci ko yayi
shiru ba se ma karawa kukan sa karfi da yayi hakan kuma ya sake dugunzuma hankalin
uban duk yabi ya tashi dan Allah ya zuba mishi so da kawa zucin yaya, ko dan ya
dade kafin ya same su ne?.

Iya shaka na shaka domin dai a yau na gaza yiwa mariya da Salees uzuri, ba dan
komai ba sedan saboda ba yau hakan ya fara faruwa ba, abin kamar ya zame mata sabon
da take jin dadin sa ni kuma ya zama sabon da ke taɓa zuciya ta da sani cikin ɓacin
rai.

"Amma dai kasan wannan shiga hakki ne ko, yaya muna kwance kawai zaka bude wa wata
daki hakan kuma duk be yi ba se an hana ni bacci, shin shima hutun nawa ya zama
abin bakin ciki da hassada ne ko kuwa me?.
Wani kallon Salees ya shiga yi min me kama da na mamaki ko kuwa na zallar takaici
ne, kafin kuma yayi magana tayi caraf ta riga shi

"Kiyi haƙuri Khadijah, Amir ne ban san me ke damun sa ba kwana biyu, ko kuwa har ya
gane uban sa ne oho, kinga har mun kwanta amma yaron yace be san zance ba kuka har
na rasa yadda zanyi dashi shi yasa na kawo masa ko ze yi shiru dan mama tace yawan
barin yaro yana kuka ba lallashi na jawo masa matsalar ƙwaƙwalwa da kuma ciwon
zuciya".

"Kinga dan Allah dakata ba dake nayi magana ba ki bari shi da nake dashi ya amsa
min, zuma naaa da kai fa nake magana".

A irin fusacen da Salees ya kalle ni abin seda ya girgiza ni dan kallo ne me shaida
Allah ya soki bana kusa da ke

"A sani na dai ke ba kurma bace kin ji me tace ko?".

A yadda nakai geji nima hakuri na ya kare dan haka na bashi tawa amsar da
fusatacciyar murya kamar yadda ya min

"Shine nace ina buƙatar sanin me kake nufi da ni ne dan wallahi sedai ko ta fita da
yaron daga dakin nan ko ni na fita dan ba za'a dinga hanani bacci ana samun ciwo a
banza ba".

"Aikuwa sedai ke ki fita dan da dai dakin uban sa ne cikin gidan uban sa, kinga
kuwa maganar a fitar dashi ma ai bata taso ba".

Kuriii na masa da ido ina kallon sa yadda ya fadi abinda ya faɗa hankali kwance,
ban san me yasa murmushi ya zabi wanzuwa a fuska ta ba a lokacin duk kuwa da
tsananin ɓacin da rai na yayi

"Amma dai kasan nima ina da gidan uba ba daga sama na fado ba ko Salees, so ba daga
daki ba ko gidan kace in fice ma yanzu se in tafi ai".

"Mtsww, Ni dai ban ce ki fita daga gida ba sedai in Kuma ke kika so, daki dai nace
ki fita dan yaro na ba inda zeje, ke ban da ma rashin imani kina kallon irin kukan
da yaron yake yi ko tausayin sa ba kiji ba balle mahaifiyar sa da duk hankalin ta
ke tashe se wani soki burutsu kike yi, ko da yake ai baki san ya rainon da yake ba
tun da baki taɓa yi ba dole ki ga kamar karya ne".

A wannan gaɓar kam tuni idanu na suka tara ruwan bakin ciki, ɓacin rai da kuma wani
irin rauni dake tasowa tun daga can karkashin zuciya ta, ban kuma cewa komai ba na
sauko daga gadon tare da ƙarasawa inda na aje jakata na ɗauka ina nufar hanyar fita
daga dakin dauke da alwashi me girma cikin raina.

Kan bed na faɗa ina sakin kukan da nayi dauriyar riƙewa, wani irin kuka me fitar da
sauti sosai jikina na rawa, kallo ɗaya me imani da tausayi ze min yaji zuciyar sa
ta motsa, Allah ya sani na dade da gajiya da zaman auren Salees, ba dan na daina
son sa saba, ba dan bana son cigaba da rayuwa dashi ba, sai dan in aka cigaba da
tafiya a haka lallai zuciya ta na gab da bugawa, in Kuma haka be faru ba na tabbata
jinina se yayi yawan da saukowar sa se Allah, yanzu haka ina mamakin yadda ko
yaushe nayi gwajin bp nake samun negative result dan a irin damuwar da nake ciki
hawan jini shine cuta mafi kankanta da ɓacin ran gidan Salees ka iya haifar
min...................!.

_*Ba zan gaji da fada muku ba haka ba zan gaji da tabbatar muku da ba gazawa ce ta
sa Allah ya kaddare ku da rashin haihuwa ba face jarraba irin tasa da yake yi dan
gwada karfin imanin duk wanda yace yayi imani, da zafi, da ciwo, da damuwa, da
rauni amma in akaa daure tabbas rabon me girma ne kamar yadda Allah da kan sa yace
yana kunyar matan da basu taɓa haihuwa ba, Allah ya bada masu albarka inda rabo, in
Kuma babu Allah ya azurta ku da dauriya da karfin iya jure wannan ƙaddara*_.

Comment, share and follow.

Ouummey ✍🏻.




Ouummey 02 {4/28/2023 }

😭 *RASHIN HAIHUWA*😭

_(Ƙaddarar wasu matan)_

Na
💝💖* Ouummey* 💞💕

Wattpad @ouummey




*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya
jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye
jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya
hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan
mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su
ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace
uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.

____________________________________________________________________________

_Free Chapter two_



Haka na kwana cike da kunci da ɓacin rai, kwata kwata dama ban sa ran Salees ya
biyo ni wani rarrashi ba dan nasan ba yi zeyi ba, so da yawa na kan yi mamaki yadda
tashi ɗaya rayuwar aure na ta juye daga happy married life cike da so da kauna zuwa
wani yanayi da ba zan iya faɗa ba.

Sai dai ba abin mamaki bane in akayi duba da irin nakasun da mutane ke gani tattare
da ni, ba wai tawayar halitta ba, bana hali ba face na wani arziki da Allah ke bawa
bayin sa da yaso ba dan kuma dan ya tsane mu mu da be bawa ba, a'a sai dai dan ya
jarraba karfin imanin mu, wanda in ba ya shiga cikin lamarin ire ire na ba cin
wannan jarrabawar tana yin wuya domin abun ba sauki, lamarin babu dadi sam haka
yanayin me matukar taɓa zuciya ne.

Da safe ko da na tashi ban fasa yin abin kari ba sanin nike da girki, sharp sharp
na hada breakfast tare da zubewa kan table kana na ɗora na Ilham da zata tafi dashi
school sannan na koma ɗaki dan shirya wa zuwa wajen aiki, a hanzarce nake komai dan
na makara saboda rashin samun bacci da wuri sanadin ɓacin ran Salees da mariya.

Sai da na tabbatar da zaman gyalen jiki na sannan na fesa turare kasa ƙasa wanda
ba'a jin ƙamshin sa se an matse min waje sosai sannan na fito, kan table na tadda
su zaune cikin farin ciki suna hira abin su, da ka gan su kaga wasu ma'aurata da
rayuwa kewa dadi sabanin ni da rayuwar aure na ke cike da bakin ciki, ɓacin rai
tare da takaicin da namiji iri iri.

Kau da damuwa ta nayi na shanye ta cikin ciki na na karasa tare da jan kujera na
zauna

"Good morning zuma na, fatan ka tashi cikin koshin lafiya".

Na faɗa ina kissing lips din sa kana goshin sa sannan na juya ga mariya

"Barka da safiya maman Ilham, fatan kun tashi lafiya".

Duk da naga sanda yanayin ta ya canja lokacin da na sumbaci Salees amma tuni ta
ture tare da maye gurbin matsewar fuskar ta da wadataccen murmushi tana amsa min
har da yar dariyar ta

"Lafiya lau Auntyn yara, fatan kema haka".

"Alhamdulillah kam".

"Ehm nace dan Allah kiyi haƙuri da abinda ya faru jiya, sha'ani na yara ne me sa
mutum ya rude amma ba da wata manufa nake kawo Amir ba, kin san al'amarin raino in
ba wanda ya taɓa yi ko yake cikin yi wani abin ba yarda zaka yi in an fada ba, ni
kaina da Umma ke faɗa min akwai yara masu kukan dare ban yarda ba seda na haihu,
amma karki damu kema soon zaki fahimta in Kika haifa".

Duk wannan surutun da take yi ni tuni nayi nisa da zuba abincin da zan karya dan
Ina zama na zubawa Salees, ban ɗago ba duk da naji me tace ban kuma yi mamakin
maganar da ta fa min a wayance ba dan indai ita ce nasan zata yi fiye da haka dan
tuni na dade da gane da kuma fahimtar inda ta dosa.

Wahalallen murmushi na kakaro na ɗorawa fuska ta na ɗago ina duban ta

"Haba ai ba wani abu bane maman Ilham karki damu".

Haka muka fara cin abinci tana ta zungurin Salees da hirar Amir da ta Ilham shi
kuma ya biye mata dan a bayyane yake yana mugun son ƴaƴan sa tare da kulawa da duk
abinda ya shafe su, gane hakan ne kuma yasa mariya ta samu damar kuntata min kamar
yadda ta dauri niyyar yi tun haihuwar Ilham zuwa yanzu kan Amir.

Tissue nasa na goge baki na ina miƙewa daidai fitowar Ilham daga dakin mamanta goye
da skul bag ɗin ta na tafiya makaranta, tun da yarinyar ta fito na kalle ta na kau
da kai batare da na sake duban ta ba duk kuwa da yadda nake son yin hakan.

Allah ya sani ina matuƙar kaunar Ilham saboda yadda ta dauko kamaninn Salees kamar
yayi kaki, yanayin ta na surutu da sakewa yasa take da farin jinin jama'a ciki kuwa
har da ni sedai dole nake koyar dannewa tun wani incident da ya taɓa faruwa.

"Good morning Daddy, good morning Mommy".

Ilham ta gaida iyayen ta batare da ni ta kalle ni ba, ban damu da hakan ba na sake
daidaita zaman mayafi na tare da ɗaukan handbag dina na kalli Salees

"Ni na tafi se na dawo".
"No ki tsaya ki sauke baby a school yau ba zan fita da wuri ba".

Ya katse ni da sauri daga nufar falo da nayi, dole na ja na tsaya cike da damuwa
dan na makara na kuma san se na kara wata a kan wadda nayi saboda sanin halin Ilham
wanda uwar ta ta gama poisoning mind din ta a Kai na

"Yi sauri kiyi breakfast ku tafi baby, yau Aunty ce zata kaiki".

"To Daddy".

Tace tare da zama ta shiga tsakuran abincin gaban ta kamar ba zata ci ba, ni kam
daga tsayen da nake mamakin Salees ne ya cika min rai ganin yadda be damu da rashin
gaishe ni da Ilham tayi ba, na jijjiga kai kawai tare da kallon wristwatch dina me
tsada dake daure kan tsintsiyar hannu na kana na maida kan Ilham da se lokacin take
yin spoon na uku a abincin.

"Eat fast pls Baby, am already late".

Ba wanda ya tanka min cikin su ukun haka kuma ba ta fasa cin abincin yadda ta ga
dama ba, nikam tuni raina ya ɓaci dan nasan da hujja take yi dan ta bata min lokaci
saboda i overheard them once tana fada wa uwar bata san tafiya dani saboda ni nake
kai ta wataran kamar dai irin yau in baze fita da wuri ba, budar bakin uwar ta bata
shawarar dinga bata lokaci in tare zamu tafi, a cewar ta har na gaji na tafiya ta
kafin ta gama shininnikin ta.

"Ina ganin zan wuce fa Abban Ilham dan na makara tuni gashi kuma naga ita bata gama
ba".

Ban jira amincewar sa ba bare umarnin tafiya na shiga takawa zuwa waje dan da kyar
ma na lallashi kaina na yi maganar dan kar yaga laifi na sedai ashe ban tsira ba

"Wai meke damun ki ne a kwanakin nan Khadijah, ina fa lure dake duk sanda nace ki
sauke baby a school se kin kawo uzuri, makara, ba zaki fita da wuri ba and many
more, me kike nufi ne?".

Seda na lumshe ido jin wata sabuwar fitinar kuma da sanyin safiya kafin silently na
juyo Ina tausar Kai na

"Babu abinda nake nufi fa Abban Amir, kalli agogo it's already past eight kasan
Kuma ka'idan aikina thirty minutes past seven ne na makara".

"Ba matsala, zaki iya tafiya zan kai ta da kaina Allah yasa uban ta na da motar".

Ɗan jim nayi kamar na tafi sai dai zuciyar neman zaman lafiya ta rinjayi me tunzura
ni se kawai na koma cikin falon na zauna tare da rufe ido, daga haka nake jiyo
maganar Mariya murya kwance cike da tsantsar kissa da yaudara

"Haba baban yara, me ye na fusata haka, ai kaga tana da uzuri me ƙarfi, ko rannan
ma ta tafi ta bar baby ne saboda tana da meeting, se kana mata hakuri fa, kasan
bata saba da hidimar yara ba".

Abin dariya wai Salees se ya dubi mariya

"Abin da Khadijah ke min a gidan nan ya fara isa ta, amma ba komai ta cigaba".

Se kawai fuuu yayi sama,
"Dan Allah Auntyn yara ki dinga kiyaye abinda ze sa Abban Amir ya dinga miki faɗa
haka, wallahi bana jin dadi".

Ban iya cewa komai ba saboda kullutun da ya tare min makogaro, da na buɗe baki
nasan ba me daɗi zan fadawa Mariya ba wanda da nayi hakan nasan wani tashin
hankalin ze Kuma zama so se kawai na zabi yin shiru, ina jin ta tashi ta bi mijin
ta sama ta bar ni nan zaune na kasa motsi cike da ɓacin ran da ta jagoranci zama
silar sa, seda siririyar muryar Ilham yet cike da rashin kunya ta ratsa kunne na

"Ni kin ga Malama in baki shirya tafiya ba ki bari in faɗawa uba na ya kai ni, atoh
tun da ina da iyayen da suka haife ni su ba juya bane".

Wal

Please Login or Register in order to submit comment