You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da babu muhallin sa, kau da kai a abinda yake zahiri ko da an cuta
maka, danne bukatar kai saboda ta abokin rayuwar ka, ji ka nuna baka ji ba, ka gani
ka nuna baka gani ba haka kuma a taba ka ka nuna baka san an yi ba ta hanyar
yafiya.
Base kin ce min komai ba ba kuma se kin fada min halin da kike ciki ba, kukan ki ya
bayyana min komai, sai dai ina so in tuna miki da abin d kika manta, ni baban ki
ne, dan Adam kuma ajizi, da ni dake Allah muke bautawa gaba ki daya haka kuma wajen
sa muke neman taimako, kama ta yayi da damuwa tayi miki yawa ki tashi ki dauro
alwala ki fuskanci qibla ki kai kukan ki wajen me duka cikin kaskan da kai, yi masa
kirari da kuma tsarkake shi, ina me tabbatar miki da wallahi in kika yi hakan zaki
sami saukin kome ke damun ki, damuwar ki zata yaye, ruhin ke ze aminta haka kuma
zaki sami nutsuwar zuciya.
Ba kamar ni ba da in kika fada min sai dai in miki kalamai wanda bayan haka ba
abinda zan miki in Kuma ba so kike in zama uban kawai me shiga sha'anin rayuwar
auren yar sa ba.
Yanzu maza ki tashi kiyi kamar yadda na fada miki kinji, insha Allah nima zan taya
ki, a kullum cikin addu'a ta kike uwatah ke da sauran yan uwan ki amma zan kara da
izinin Ubangijin mu, ina fatan Allah ya yaye miki kome ke damun ki, ya aminta da
ruhin ki ya kawo miki sauki da salama a rayuwar ki, zan kira ki da safe, Allah ya
bamu alkhairi".

Kit Abba ya kashe wayar sa da ya gama min wannan bayanin, be saurare ni ba, bance
masa komai ba game da halin da nake ciki amma ga mamaki na wallahi se na ji kaso
fiye da hamsin cikin kuncin da nake ci ya kau, lallai na gaida iyayen mu, ya
Allah kasa iyayen mu su cika da imani ka saka musu da mafificiyar aljanna, Amin.

Batun yanzu ba ina sha'awar rayuwar Abban mu da Ummin mu, so da yawa ina fadar in
da ace kowane miji kamar Abban mu yake da ba'a samu gurbacewar rayuwar aure ba, da
ba'a sami yawaitar matsalolin aure ba, da ba'a samu yawaitar zawarawa ba haka da
mata basu ji tsoron aure ba, in Kuma na dube shi ta fuskar uba se in ga lallai babu
ya'yan da suka kai mu yin dacen uba nagari, se in dun ga tausayin wanda Abba be
kasance mahaifi gare su ba har in dinga ganin lallai sun yi rashi babba.

Alwala nayi na shimfida tsaftatacciyar pray mat dina dake nan kamar sabuwa saboda
samun gyara na sa wadataccen hijab dina na kabbarta sallah, a cikin kowace sujjada
kuka nake yi gaban Ubangiji ina rokon sa sauƙin rayuwa, farin cikin rayuwa, haka
kuma yayewar bakin ciki tare da cikawa da imani, irin kukan da nayi ba zan ce ga
sanda nayi shi ba dan tun da na dora goshi na a kasa naji bani da wani sauran karfi
ko kwarin zuciya.

Cikin ikon Allah na yi raka'a goma wato sallama biyar sannan na daga hannu na
cigaba da addu'a, ina shafawa na dau Kur'anin da na aje gaban sallaya ta na budo
Suratul mu'umin na soma karatu cikin kyautatacciyar kira'a murya can kasa dan gudun
takurawa abokan rayuwa ta a gidan, sai da nayi surori uku bayan ta sannan na rufe
tare da sake wasu addu'o'in na kuma shafawa, abin babu karya ba kuma yaudara tun
kafin na kai ga idar da sallar naji zuciya ta wasai tamkar ban taba sanin wani abu
wai shi damuwa ba, farin ciki da walwala suka cika rai na tamkar wadda akayi wa
bushara da kujerar hajji.

Agogo na kalla wanda ya nuna karfe biyu da rabi na dare na tashi na cire hijab din
da na sa na rataye shi tare da maida daurin dan kwali na na nufi gado na na kwanta
hannu na rike da calbi ina ja cikin kirari wa madaukakin sarki, cikin rahmar Allah
se gashi na samu salamammen bacci me cike da jin dadi kamar kar na farka dan se da
nayi da gaske na iya tashi asuba ba kamar ragowar ranaku da ake kiran farko a kunne
na ba saboda damuwar da kan hanani bacci, lallai Allah buwayi ne garara misali haka
kuma duk wanda ya bar Allah tabbas yayi hannun riga da nutsuwar fili har ma da ta
boye.
Ba fa wai na manta da abinda Salees ya min bane, ba kuma na manta da kara ta da ya
kai wadda zamu je yau bane kawai dai damuwar hakan Allah ya cire min daga rai na.

Ban yi gigin yin breakfast ba dan ban manta layin d ya shata min ba na cewar in har
ban kwana dakin sa ba to bani da girki gaba daya, ma'ana har dafa abinci, a can
baya da yasa dokar na damu amma a yau se naji ni hakan ma yayi min dan gashi na
samu damar bajewa a gado ina baccin safe kasancewar asabar babu aiki.

Se after 10 na tashi nayi wanka da shower gels dina da ragowar turarukan wanka masu
kamshi da gyaran fata wanda a kullum yanayin yadda nake kula da jikina yake bawa
wanda suka san ainihin shekaru na mamaki, dan da yawa mutane basa yarda na kai
shekaru na, so da yawa se kiga ana bani shekara Ashirin da biyar da shida koma da
hudu, nidai in irin haka ta faru sai dai nayi dariya kawai, amma fa bana mamaki dan
ko ke kika kalle ni ba zaki ce nayi talatin har da biyu ba wanda sune shekaru na na
gaskiya da gaskiya .

Doguwar riga na sa kirar Morocco, kafin kace me na zama wata bakar balarabiya
saboda yadda rigar ta min ainihin kyau ta bi dirarren jiki na ta zauna Kamar yar
asalin ƙasar, kai har ma nafi dan su ba su da cikakken diri irin nawa.

Karamin fridge dina na bude tare da zubawa kayan snacks din ciki ido sannan a
hankali na debi samosa uku tare da drink na maida murfin na rufe, a tsanake naci
abina na kora lemo na kara da ruwa me dan sanyi, take naji ciki na y dauka masha
Allah na koma tare da zama kan doguwar cushion din dakin ina bibiyar chats din
kawaye na cikin group din mu me suna *UWAR GIDA*.

Knocking din da aka min yasa na dan saurara daga karanta wani post da nake yi kana
na tashi na tafi na bude bayan na kuma jin wani, Sahal ne me bin Ilham, tsakanin su
shekara daya ne dan yanzu sha biyu yake yayinda ita take sha uku

"Daddy yace ki fito".

Yace tare da barin wajen da sauri, jinjina kai nayi tare da komawa daki ina fadin

"Wata matsalar ta dawo" a raina dan zan iya cewa Sahal har yafi Ilham dan shi kan
kamar uwar sa ta bashi zuciyar ta ne, bakin hali a cikin yaron abin se addu'a
shiyasa tun farko ban sake masa ba bare ya raina ni ko da dai b wai girmama ni yake
ba duk tsare gida na, tun hutu ya tafi gidan iyayen Mariya kuma ko da aka koma
makaranta be dawo ba ta can yake tafiya se yau da aka dawo dashi.

Sai da na koma gaban madubi na sake gyara zaman mayafi na na kara turare kadan me
sanyin kanshin da baya tashi sannan na dau waya ta da karamar purse dina na fita,
basa falon hakan yasa na fita compound bayan na rufe kofar falon.

A tsaye na hango Salees jikin motar sa wadda ina fitowa ya bude ya shiga, takawa na
shiga yi zuwa wajen su sedai kafin na karasa ya ja motar sa yana yi wa maigadi horn
ya bude gate tsayawa nayi kallon ikon Allah se kuma na bar shi as tun d ta kusa
dani zai wuce maybe ze tsaya in shiga,

"Motar ya cika, ki biyo bayan mu a naki tun da kina dashi".

Sakatoto nayi ina bin shi da kallo kafin kuma na kau da mamaki da sauri dan wannan
kadan ne daga halin shi, shi in har kuna fada to fa ba zaki kuma jin dadin sa ba,
duk yadda ze bata wa mace rai to se yayi so tuna haka se kawai na saki murmushi me
kyau na gyada kai na alamun toh na juya zuwa wajen mota ta.

Farin ciki na daya , kamar yadda yace ina da motar, mota kuma ba karama ba domin
suna gogayya da tasa a wajen kudi, bangaren tashe kuwa har ma tawa ta zarta tasa,
ina tsananin so da kaunar motar domin kuwa Abban mu da hannun sa ya bani kyautar
motar lokacin da Mariya ta haifi Amir wata shida da suka wuce.

Cikin tuki na na natsuwa na fitar da motar daga gidan tare da hawa titi na nufi
babban gida kamar yadda suke kiran family house din su inda nan ne iyayen Salees
suke.

Gefe da tasa motar na aje parka tawa sai dai ban fito ba sai da na gama addu'o'i na
na samun rinjaye kan makiyi dan kusan zance makiyan nawa ne mutanen da zan hadu
dasu.

Bakin babban falon Hajiya Iya nayi sallama tare da daga labulen na shiga bayan na
sabule takalman kafa ta, a duk cikin mutane takwas dake zaune a falon ba'a sami ko
daya da ya iya amsa min sallamar da nayi ba wanda hakan ba bakon abu bane a waje
na, gefen one sitter na samu na zauna kana na shiga gaida Hajiya da ta nuna kamar
bata san da shigowa ta ba tana yi wa Amir dake hannun ta wasa, seda na maimaita
gaisuwar sannan ta amsa min a watse.

Daga Lafiya lau din bata kuma cemin komai ba nima kuma naja baki na nayi shiru, sai
da ta gama da shalelen ta sannan ta mikawa Hannatu kanwar Salees dake zaune a wajen
Amir kana ta fuskanto mu gaba daya.

"Uhm, kace mene?".

Dan muskutawa Salees yayi ya fara rattabo zance kamar me karanta labari

"Hajiya karar khadeejah na kawo miki, ban san meke yawo a ranta ba, ban san wake
zuga ta amma gaba daya ta birkice, gaba daya ta canja halaye da dabi'un ta ta kwaso
mugayen akidu da ra'ayi ta ɗorawa kan ta.
Babu damar naman Amir tayi wani abu yanzun nan se ta hayyako ta fara fadin
maganganu marasa kan gado, kwata kwata bata neman zaman lafiya kamar yadda ita
Mariya ke son su rayu cikin salama, a kullum burin ta ta kuntata min ta bata min
rai.
Duk ma kuma ba wannan ne babbar damuwar ba, kin ga yaran nan wallahi khadeejah
yadda ta tsane su bana jin ko makiyin ta ta tsana haka, daga ni uban su har ita
mahaifiyar su bamu san me mukai mata ba da take neman saukewa kan su.
Shekaranjiya iIlham d zazzaɓi ta kwana me zafi saboda yadda ta fasa mata baki ga
kuma kunnen ta da ta murde saboda wai tayi mata rashin kunya wanda zan iya rantsewa
baby ba zata yi haka ba sedai yarinta, wai kuma daga uwar ta ce ta dinga sassauta
hukunci shikenan ta dau fushi da ita da yaran har tana tafiya wajen aiki ta bar
baby bata je makaranta ba saboda tana tutiya da tinkahon baban ta ne ya sai mata
mota, Hajiya Iya fa abubuwan da zan iya fada miki kenan kuma akwai wasu bayan su
sai dai in zan zauna lissafa miki wallahi zamu wuni ba mu gama ba, shiyasa na kawo
ta gaban ki ta fadi meye matsalar ta da ni, Mariya ko yayana"..............
Ouummey ✍️
.




Ouummey 05 {4/30/2023 }

😭 *RASHIN HAIHUWA*😭

_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕

Wattpad @ouummey



*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya
jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye
jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya
hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan
mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su
ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace
uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.

____________________________________________________________________________


_Free Chapter Five_

Har ya gama zuba surutun sa ina zaune kamar yadda nake tun farko sedai tsoron Allah
ya dade da cika zuciya ta jin wai yau a kaina ne Salees yake rattabo wadannan
Laifuka da matsaloli, lallai rayuwa juyi juyi ce wai kwado ya fada ruwan zafi.

"Uhmmm yanzu duk wannan abubuwan ita hamshakiyar ke yi amma ka zauna kana kunsar
bakin ciki, lallai sannu khadeejah autar mata".

Sake kasa da kai nayi ina jin tune din da Hajiya Iya ke magana dashi kafin ta ja
dogon tsaki

"Ke dago nan ki kalle ni bana son munafurci, ana magana kina sunkuyar da kai kamar
wata mumina bayan kasurgumar muguwa ce ke, dago nace ki kalle ni".

A sanyaye na dago na zuba ido na cikin na Hajiya Iya

"Yanzu ke dan kin kasance butulu wadda bata san alkhairi ba har ya'yan Salees abin
ki ne a wajen ki bayan dimbin halaccin da yayi miki a rayuwa?, Da zaki fidda hannu
ki daki yarinya karama irin haka saboda baki san zafi da ciwon haihuwa ba, anyi
magana ke ga Sarkin an iya bakin rai kin dauki fushi da su".

Se kuma ta juya kan Salees

"Ai duk kai ne shashasha shi yasa har mace ta raina ka, ban da raini kana kallon ta
tana iskanci ka zuba ido baka yi maganin ta ba, ko da yake ai ta gama da kai yanzu
ma da sauki tun da kana iya ganin laifin ta".

"Saurare ni nan kiji, in kin gama da Salisu to ni na fi karfin ki, shima kuma gashi
nan Allah ya fara karya alkadarin ki ta hanyar matar kwarai da ya samu, na san ba
komai ke damun ki ba face bakin ciki da hasssada tare da asararren kishi, ke a
rashin tunanin ki se mu bar Salisu ya zauna da ke kadai bayan ba haihuwa kike ba,
kullum yayi ta cika miki ciki da abinci kina juye wa a masai babu fus balle as, to
ta Allah ba ta ki ba, jinin Salisu ne gasu nan kina gani, karewar bakin ciki ki
hadiyi zuciya ki mutu ni da wallahi farin ciki zan yi dan zaman ki gidan dana dan
kawai babu yadda zan yi ne amma ba so nake ba.

Batun yara kuma daga yau na shata layi tsakanin ku, ko da wasa kika Kuma kai hannun
ki kan jikoki na wallahi a bakin auren ki dan se Salisu ya sake ki ko na tsine masa
albarka, uwar su kuma in dan kin ga me hakuri ce kike cuta mata to Allah yana
kallon ki kuma baze bar ki ba".
"Kai kuma in zaka dauki mataki akan juyar matar ka ka dauka in kuma zaka cigaba da
zama tana raina ka kai ka sani".

Hakuri Salees ya shiga bawa Hajiya Iya ganin har dashi cikin fadan sedai ni tun
daga gaishe ta ko tari ban yi ba balle wani ban hakuri, na bata hakuri akan me, me
nayi mata, bayan duk cin zarafin da aka min kuma na bada hakuri, tabdi.

Aikuwa rashin bada hakuri na ya sake tunzura Hajiya ta cigaba da bala'i da fade
faden maganganu na cin mutunci d zarafi a kaina har muka mike zamu tafi

"Allah ya bamu alkhairi Hajiya".

Na mata sallama batare da na bada hakurin ba, Hannatu tayi tsagal ta zage ni
yarinyar da yanzu take shekara sha takwas, fadin shekarun da na bata ma bata baki
ne

"Juyar banza da wofi mara amfani kawai, ciki ba komai se kashi, mtsww Allah dai ya
raba yayan mu da kayan bakin ciki".

Na jita sarai kuma zagin ya ci min rai dan na tsani raini a rayuwa ta shiyasa duk
runtsi bana yarda na wulakanta ko cin mutuncin na gaba da ni.

Ashe shima Salees zagin ya masa zafi dan har na dan yi gaba se ji nayi ya fisgo ni
baya kofar dakin hajiyar ya hade rai tamau yana yiwa Hannatu mugun kallo

"Dan ubanki matata sa'ar ki ce?".

Ya tambaye ta a kausashe lamarin da ya matukar daurewa Hajiya Iya kai dan su a
ganin su ai yanzu Salees ya daina so na dama suna cewa soyayyar sihiri ce, to tun d
yanzu ya karye ai zasu taka ni yadda suke so

"Kar ka kuma zagar min ya in ba haka ba ranka ya ɓaci".

"Amma Hajiya kin san dai hakan ba daidai bane, ban da iskanci karamar yarinya kamar
Hannatu ta kalli khadeejah ta zage ta, Hannatu da bata fi kanwa ta kusan shida ba
wajen khadeejah, to wallahi tun wuri ki shiga hankalin ki in ba haka ba se na kusa
karya ki, mahaukaciya mara hankali kawai".

Ya fada yana karasa directing maganar kan Hannatu, nidai ina samu na zame hannu na
daga cikin nasa se kawai na yi gaba abina na fice dan wallahi ko kadan shigan min
da yayi be burge ni ba.

Na riga su isa gida dan haka na shige daki na kulle tare da yin lamo kan gado na,
in ka ganni zaka yi zaton wata marainiya ce d babu uwa kuma babu uba haka babu
sauran gata, kulle ido na nayi ina sauke numfashi ina fadawa kai na rayuwa ce haka
kuma Allah yaso gani na, jarrabawa tace da ban isa na tsallake ba har na samu na ji
sanyi a raina kafin na shiga toilet dan yin wanka.

★★★★★

"Yanzu haka zaki zauna kullum kina kuka akan matsala daya, na baki shawara tuntun
tuni Falmata amma kin share, kin gwammace ki yi ta asarar hawayen ki a banza ko, to
ai shikenan".

Babbar mace da a kalla zata kai shekaru hamsin da biyu zuwa da biyar ta fada tana
kallon kawar ta dake zaune ta zuba tagumi hawaye na bin fuskar ta kamar an bude
famfo.
Ganin bata ce komai ba yasa matar jan tsaki tana duban Falmata

"Bata akan ki kadai abin ya tsaya ba, yanzu haka ina fada miki da zan shigo na hadu
da wancan fitsararren dan Adam, wallahi yaron nan akan ido na yayi min tsaki har da
tsartar da yau sannan ya shige bangaren su, shin haka zaki zauna ke a raine wanda
ya alakantu dake ma ana masa kallon banza shara wofi mara amfani Falmata, shin ba
zaki yi komai domin kwato abin da ya kasance naki ba tun farko? Ko kuwa zuba ido
zakiyi har se rayuwa a gidan nan ta gagare ki, ki dubi karamin yaro Haisam irin
motar da yake hawa ki kuma dubi taki wadda kike jin jiki da ita tuntuni, ya kamata
ki farka daga barci da kike yi ki amso what is rightly yours, Ina baki shawara ne
matsayin yar uwa aminiya wadda bata san ganin ki cikin komai face farin ciki".

"Ban damu da nawa ze kashewa yayansa ba Farida, ban kuma damu da kyautatawar sa
gare su ba, damuwa ta yadda kome na bukaci Alh yayi min se ya kawo uzuri, ba kuma
ze yi abin nan ba ko da zuwa da shekaru nawa ne, a cewar sa kullum nauyi kara
karuwa yake a kan sa saidai yana mantawa cikin nauyin nasa akwai ni, ina da hakki a
kan sa wanda a yanzu ya sauke wa kan sa, da ni da babu duk daya ne a wajen sa, se
ya shigo ya ishe ni da dadin baki, kin san matsalar da nake fama dashi na ciwon
ciki, naje naga likita akan shi sedai ya bukaci naje babban asibiti, to ko da naje
sun ce se an min aiki, yanzu halin da ake na fadawa Alh dan ya shirya min tafiya
zuwa India ayi min aikin a can amma yace be da kudi se gashi dazun nan a gabana
yayi wa yar lelen sa alkawarin sabuwar mota zuwa gobe, ban face ya bini ba, ban
kuma ce ya biya min tare da wani da zai kula da ni ba, iya ni kadai nace amma yace
babu se gashi be rasa na canja wa yar sa motar hawa ba, innalillahi wa inna ilaihi
rajiun".

Hajiya Falmata ta fada tana sake rushewa da kuka, hatta da Hajiya Farida hawaye
take yi na tausayin kawar ta, aminiyar ta kuma yar uwar ta

"Mata sune matsalar mata yan uwan su Falmata, na rantse miki da girman Allah duk
abinda Alh yake miki da sanin Hauwa kuma tsarin ta ne, tun asali matar nan bata son
ki kin sani ta ya zata so miki kwanciyar hankali, kai hasbunallahu wa niimal
wakeel".

"Farida ina ganin zan hakura da auren Alh kawai dan be da wani amfani a waje na,
gara kawai in san single nake da ciwon zuciyar da Alh ke kokarin ganin ya kakaba
min karfi da yaji".

"Ba zaki bar mata gidan ki ba, ba zaki bar mata mijin ki ba, wallahi ba zaki je ko
ina ba, kenan ma kin yi biyu babu, baki ga tsuntsu baki ga tarko inaaa, sam
wallahi".

"Gwara in tafi da in zauna Ina kun sar bakin ciki".

"Kece kin cika sanyin rai, tuntuni na kawo miki shawarar yadda zamu yi maganin ta
amma kin xayan wasu tunane tunane, ke yar uwa ta ce kuma kawata, wallahi ba zan
taba yin abinda zan cutar dake d sani na ba, ki bani dama mu nuna wa Hauwa ita
karamar kwaruwa ce, ita yanzu ta soma bariki lokacin da mu kuma muka riga muka
maida ita gida".

Shiru Falmata tayi kafin ta saki ajiyar zuciya a hankali

"Ba tsoron Hauwa nake ba Farida, saidai ina tsoron Ubangiji na, ban haifa ba, ban
ji dadi ba a gidan aure na sannan kuma na lalata kiyama ta Falmata?, Anya in nayi
hakan ban cuci kaina ba?".

Da sauri Farida ta shiga girgiza kai,

"Ba zaki lalata kiyamar ki ba, ramuwar gayya zaki yi wadda tafi gayya zafi, daga
lokacin da kika rama zaki ji sanyi a ranki daga nan kuma se mu tuba, amma ai kafin
nan itama taji ko da rabin yadda kika ji ne".

"Bazan iya ba Farida, ba zan iya lalata dan kowa ba, ba zan iya sanya mahaifiya
kuka ba, ba zan iya fuskantar Ubangiji da laifin shirka ba, na hakura Farida, na
barwa Allah shine ze min sakayya kan Alh da Hauwa amma ba zan iya kauce hanya
saboda ita ba".

"Banza tursasaki ba Falmata, ban kawo wannan shawarar dan batar dake ba sai dan
sama miki salama amma tun da baki yarda ba ba za'a yi komai ba, sai dai kiyi hakuri
domin zan janye jiki daga gidan ki dan ba zan iya zuwa ina ganin ki kullum kina
ramewa da karewa a tsaye saboda bakin cikin wasu ba bayan kina da yadda zakiyi,
zuciya ta ba zata iya hakurin ganin ki cikin matsala ba alhalin kece yar uwa mafi
kusanci da ni, kiyi hakuri ba wai na janye gaba daya bane sai dai yawan zuwa zan
rage, sai an jima zan kira ki in na koma gida".

Da haka Hajiya Farida ta dauki jakar ta bayan ta yafa gyalen ta ta fara daga falon,
babban compound ne da ya lashe motoci kusan sha biyar wanda daga nan zaka san gidan
ba karamin girma gare shi ba, gate ta nufa tana tafe kama zatai bindiga saboda
haushi da takaicin yar uwar ta, sanyin ta yayi wa, zuciyar ta ta fiye kyau da yawa
haka hakurin ta ya wuce ka'ida.

Ta dade da sanin da ita ke rayuwa a gidan matsayin kishiyar Hauwa to wallahi da
tuni labari ya dade da suyawa dan ba zata dauki ko rabin rabin abinda yar uwar ta
ta dauka ba, da ita ce da tuni ta takawa Hauwa birki dan ai rashin Haihuwa ai ba
hauka bane da zata dinga wani iskanci, kai da ita ce da ta nunawa Hauwa itama
Shegiya ce dan wallahi yadda take mata iskanci kan haihuwa ita kuma se ta lalata
rayuwar yaran ta ga karshen tutiya da tinkaho, abinda take so Falmata ta goya mata
baya suyi kenan amma tsarkin zuciyar ta ya hana ta hango me ita take ganowa.

Tana zuwa gidan ta tayi parking tare da shiga falon ta me bala'in kyau, abu na
farko da ta fara yi bayan zama shine kiran Falmata taji yaya take, Allah shaida ne
tana matukar san Falmata, ta dauke ta yar uwar da suka fito kamar ciki daya ne
shiyasa duk abinda ke faruwa a rayuwar falmatan yake matukar damun ta.

Hankalin ta be kwanta ba se da taji lafiyar ta kalau kafin tayi shiru cikin zurfin
tunani se kuma ta gyada kai cikin yarda da shawarar da ta yanke.

Tana nan zaune yan matan yaranta biyu suka shigo daga islamiyya, hassana d
hussaina.

Har kasa suka gaishe ta tare da mata sannu da zuwa ta amsa kana suka wuce dakin su
suka canjo kaya

"Yaya jikin momyn?"

Hassana ta tanbaya a kagauce, sanin yadda hassana ke bala'in son Falmata yasa
Farida boye mata halin da take ciki

"Ta sami sauki sai dai zamuje India a sake duba ta, yanzu dai kuje ku dora girki
sannan ki kira yayanku

Please Login or Register in order to submit comment