You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kuma takaici at the same time,
cikin muryan kukan take magana ma Farida

"Tun da muka taso da ke ban taba jin wai bani da dan uwa ko yar uwa ba a duniya
saboda kin cike ko wane gurbi Farida, duk abinda kika san ina so yi kike kafin in
furta, kome zan bukata aje wa kike kafin na ambata, ban san dame zan saka Miki ba
Farida, ban san me zan Miki ba in biya ki, a kullum roko na Allah ya kara miki budi
da daukaka, Allah ya jikan iyayen mu in basa raye, Allah y raya Miki zuri'a yasa
masu amfani ne, Allah kuma ya bar ni dake har karshen nunfashi na.
Yanzu dai dubi Alhaji da nake karkashin sa, hakkin neman lafiya ta ke rataye
a wuyan sa amma ya nuna lafiyar tawa bata gaban sa, ya tattara ya zuba min ido yaki
yin wani hobbasa kan neman lafiya ta bayan babu rashi balle kuntata a tare dashi
face zallar son zuciya da rashin adalci, b azan yi masa mummunan fata ba Farida
amma tabbas da sannu se hakki na ya kama Alhaji in har ya zalunce ni".

Kwalla Hajiya Farida ta shiga gogewa tana duban Falmata emotionally,

"Ni ya kamata in Miki wannan addu'ar Falmata, ke din macece me kyakkyawar zuciya,
ba ni na fara miki alkhairi ba halaccin saka alkhairi da alkhairi kawai nayi, kome
Hammad ya zama a yau kin san dalilin ki ne?, Ko wace daukaka Hammad ze samu a
rayuwar sa kin san kece jigo, ban da kuma tarin alkhairan ki gare mu tun Alhaji na
da rai, Falmata kin so ni tun ina abin ki da gudu wajen jama'a, kin kusance ni
yayinda kowa ke gudu na, kin tallafe ni lokacin da na rasa wani mataimaki, shin in
ban Saka alkhairi ba me kike so a kira ni, balle kuma ni ina miki kallon yar uwa ce
da muka fito daga cikin mahaifa daya, ko kin manta kece.........".

Da sauri Falmata ta sa hannu kan bakin Farida tana girgiza mata kai hakan yasa
Farida ta cire hannun daga bakin ta

"In har ba kya san in tuna Miki to ki bar maganar dan in ance za'a ayi tone tone to
kuwa kece kika yi sadaukarwar, ni kwatanta wa kawai nake, shi kuma Alhaji kamar
yadda kika fada Allah ze Miki sakayya tabbas hakane, a da nayi niyyar in kin tafi
can India nikuwa in shiga in fita har se na rama miki abin da aka miki sedai yanzu
tsakani na ga Allah na fasa na bar shi da Allahn kamar yadda kika fada, ina kuma
fatan ace an yi aikin nan cikin nasara".

"Allah yasa Farida, in har kuwa akayi Nasara ki rubuta ki aje se na rabu da auren
Usman domin kuwa bashi da wani amfani gare ni ta kowace fuska".

"Allah ya kai mu, nidai fatana a dace in ga kin dawo gare ni lafiya lau, wannan shi
ze samar min da kwanciyar hankali da nutsuwa".

"Allah ya yarda, in Kuma bani da rabo...".

Wani irin ƙatuwar harara da Farida ta balla mata yasa bata karasa a binda zata fada
ba ta kyalkyale da dariya tana dagewa Faridan gira cikin tsokana lamarin da yasa
suka tuna baya su ka kuma sake darawa sosai...

____________

"Yaaya na fadawa Haanah ai kar ace za'a sama min mata a bar ni in zaba da kaina".

Cikin son kwantar masa da hankali ta yadda ze amince wa kudirin ta ta shiga yi masa
bayani

"Kar ka damu kan ka Ibrahim, duk abin da za'a bukata a wajen mace Saratu na dashi,
halin ta kuwa base na ce maka komai b adan kasan daga gidan d take, fatana kawai
amincewar ka dan ba zan maka dole ba".

"Amma yaya bakya tsoron a maimaita yar gidan jiya?".

Da sauri ta shiga girgiza kai

"Insha Allah ba abinda ze faru, bana fatan in maimaita kuskuren da nayi a baya
shiyasa ma ban yi maka magana ba se da naji t bakin ita Rahinatun kuma alhamdillah
tayi na'am dan yadda take walwala ya shaida min tana farin ciki da lamarin".

Shiru Dada yayi dan daga jin yadda Hajiya Yaaya ta ambaci sunan sa Ibrahim kai
tsaye yasan ta kai makura wajen son hadin nan ta yadda komai daze fada ba zata gane
ba duk kuwa da tace wai amincewar sa take nema dan haka se ya shafawa kan sa lafiya
kawai

"Shikenan Yaaya, Allah ya sa hakan yafi alkhairi".

"Ameen, ko kai fa, insha Allah wannan karon se mun ce gwara da akayi".

Shidai be Kuma cewa komai ba har ta gama maganganun ta ya mata sallama ya fice,
sedai fa a fili yake ya amsa mata ne kawai dan ba yadda ze yi dan ya kasa boye
hakan a ransa, sanadin bacin da ran sa yayi ranar a gidan ya bar su Haanah suka
kwana abinda ba ya iyawa se an kai ruwa rana dashi, jikin Hajiya Yaaya yayi sanyi
ganin hakan se dai kuma wani bangaren zuciyar ta na fada mata ta share shi da sannu
da kan sa ze dawo yana gode mata.

To abu kamar wasa karamar magana na neman zama babba dan kuwa sati biyu kenan babu
Dada babu labarin shi, shi be zo gaishe da Yaaya ba kuma be zo dibar su Meerah ba,
a kuma tsukin lokacin har an yi maganar sa da Rahinatu an karbi komai na aure in da
saura kwana biyar a daura kasancewar ta bazawara.

Ba wanda ya kuma ganin Dada se ranar daurin aure wanda shima ya je ne dan kar ya
kunya ta mahaifiyar sa cikin jama'a, haka yabi dangin amarya Rahinatu da ke ta masa
barka da zuwa dan cewa Yaaya tayi wai yayi tafiya.

A ranar amarya ta tare inda Yaaya ta rike su Haanah wai zasu yi mata sati in da a
fakaice ta bawa Dada da amaryar sa damar sakewa ne, dan a ganin ta yaran zasu
takura su sedai bata san tayi wa amarya bukulu bane dan kuwa Dada tun da aka kai
amaryar be kuma komawa gidan ba se bayan sati shima se da Haanah ta kira shi a waya
cewar sun koma gida.

___________

Wata daya kenan da kwana biyu da fara aikin mu yau, shirin da muka yi yau na
musamman ne dan tsawon lokacin da muke ma'aikatan yau din ne zamu fara ganawa da
shugaban mu gaba daya don haka kowa ka gani cikin shiri yake tun bare da muka sami
labarin he's a non nonsense Man, he's very strict and concentrated kan aikin sa.

Moroccon gown ce a jikina light purple in color se dark purple veil da nayi using,
jaka na da takalmi duk dark purple, a rayuwa ta ina son purple dan lokacin da ina
secondary school da miss purple ake nicknaming dina.

Gaban mota na hakim ce Salees ya shiga owner's corner ya tuka mu muka bar gidan
zuwa ma'aikata, ko ina was very very neat though kullum gurin is neat but na yau is
extra + special neat, hatta flowers an yi trimming din su t a good level ta yadda
suke bad sha'awa and the silence of the environment is just so wow.

Muna fita daga mota muka rabu kowa yayi bangaren sa dan office din Salees na admin
block ne ni kuma nawa na bangaren normal offices ne, se da na gama arranging table
dina tare da kara extra scents sannan na zauna na fara aiki cikin nutsuwa.

Karfe tara daidai aka hau knocking kofa ta, still working na amsa tare da bada
izinin shigowa idanu na kafe kan screen din system, sassanyan kamshi me shiga cikin
gabban jiki suna kassara su ne ya fara kaiwa hanci na ziyara kafin kuma in ji gaba
ki daya iskan da nake shaka ya zama shi, a hankali na dago kai na na sauke kan
being din da na tabbatar shi ya kwankwasa kofa ya kuma shigo.

Kan kyakkyawar fuskar sa ma'abociyar haiba, tarin kamala da matukar kwarjini na
sauke idanuna, fatar sa wata irin kala ce me daukar hankali, ita ba fara ba haka
kuma ba za'a ce baka ba, manyan idanu ke gare sa da ya ya rage musu girma ta hanyar
lumshe su, hancin sa dogo ne zit yayinda bakin sa yake nan madaidaici da ya dace
da doguwar fuskar sa, a gaggauce na sauke idanu na daga kan fuskar sa saboda
kwarjininsa da ya dake ni hakan kuma ya bani damar ganin gangar jikin sa.

Dogo ne shi irin na sosai din nan, ba siriri bane dan a murje yake hakan yasa
tsayin nasa zanowa me fasali haka kuma abin sha'awa, sedai duk tsawon sa a tsaye
yake kyam alamun cikakken namiji haka kuma dukkan wata kirar maza ta bayyana a
tattare dashi.

Gaba daya wannan kallon a cikin sakanni nayi masa su ina mikewa da sauri dan
girmamawa, ban san waye shi ba haka kuma nayi mamakin zuwan sa wajena dan in ma
guest ne to bani ya kamata ya gani ba sedai na bar shi as ko an masa kwatance ya
kuskure ne hakan yasa na mike dan girmama shi

"Pls have a seat Sir".

Na Yi amfani da kalman sir ne dan ban san sunan a ba a ganina kuma is not polite to
call him Mr.

Cikin wnai irin taku ya shiga heading to kujerar da na nuna masa lamarin da ya
tilasta min sake kallon fuskar sa sedai wannan karon maimakon cikin idanun sa se na
sauke duba na kan kyakkyawan sajen sa da yasha gyara yake kyalli da daukan ido
shedar yana samun gyara matuka, wani irin urge nake ji na son kallon kan sa dan
ganin gashin kan sa yaya yake sedai na danne da sauri ina ambata auzubillahi minash
shaidanir rajim a raina.

Wani irin zama yayi na ban mamaki amma se n share nayi kamar ban gani ba na koma na
zauna nima kafin in a polite manner na tambaye shi

"How may I help you sir".

Shiru yayi min har seda na sake maimaita tambaya ta kan cikin wani tone me cike da
kamewa hadi da tsare gida ya yi min wata bahaguwar tambaya

"Your name?".

Kamar in ki amsa masa se kuma na dan saki murmushi bayan nayi tunanin ko so yake
yaji in ni yake nema

"Khadeejah Ma'aruf Nasidi".

Nan ma se da yayi shiru kafin kuma ya mike ya fita in da ni kuma kamar shashasha
nabi bayan shi da kallo baki sake ina tunanin wane irin mutum Allah ya hada ni
dashi yau ni kuwa?.

Kusan minti uku ina zaune baki sake ina bin kofar da ya fita da kallo kafin na iya
rufe baki na na maida hankali na kan system din sedai sa'i da lokaci na kan kalli
kofar da tun da ya fita ya rufe min ita take a kulle.

Karfe sha daya da rabi muka nufi hall gaba dayan mu inda a nan za'a yi meeting da
general head da se yau ya sami zama da mu, baki na dauke da boyayyar sallama na
shiga hall din, kujerun wajen adadin ma'aikatan dake ma'aikatar ne excluding irin
masu share share da goge goge and the rest, kujera na samu na zauna ina aje yar
ipad dina kan table din gabana.

Se da aka zzzauna kafin muka ji gyaran murya with a matured tune hakan yasa duk
muka sake shiga nutsuwar mu, for the second time wannna sassanyan kamshin ya sake
kai wa hanci na ziyara, wannan karon lumshe ido nayi ina shaka dan yadda turaren
yayi min dadi na dade ban ji bakon kamshi me dadin sa ba.

Tattausan Muryar sa yet cike da bossing ya fara magana cikin welcoming din mu kana
ya fara addressing din mu, shiru kowa yayi muna sauraren sa cike da nutsuwa, irin
yadda turancin sa ke fita fluently with Fulani ancient dole ya burge kowa, awa daya
meeting din ya dauka ya sallame su bayan ya bada damar kowa yayi introducing kan sa
hakan kuwa muka yi tare da fadar post din da yake kai.

Ko da na koma office na dade ina mamakin me ya kawo general head office dina,
hankali na be kwanta ba se da naji ashe ba office dina kadai ba ya shiga office din
duk wani sabon zuwa.

Ranakun da suka biyo baya aiki muke tukuru dan kuwa boss din mu ba shi da wasa kan
aiki, in kuna jin workaholic to shine, ina zaka aiki, daga ina kake aiki, me kake
yi aiki, me zaka yi aiki, komai aiki, ni har mamaki nake in yana da lokacin wani
abu bayan aiki, Allah ya dasa min shakkar wannan bawa ta yadda har bana san abinda
ze hada hanya ta da tashi dan kuwa kwarjinin sa ba karamin duka na yake ba.

Yau ma dan ba yadda zan yi na hada files din da dole se na kai masa na fit heading
to his office, kamar me tsoron duka haka nake sanda a corridorn har na kau gaban
office din inda aka rubuta boldly

"IBRAHIM ABDALLAH MAIDOKI".
A fili na karantawa sunan na sake maimaita wa kafin na tabe baki kana na maza na
gyara sannan na shiga knocking, kasa kasa na ji muryar sa na amsa min da

"Yessss".

Irin yadda ya fadi yessss din kamar wani wanda yayi aikin karfi ya gaji lilis, not
minding hakan na tura kofar na shiga with my little sallama a baki na, ban jira jin
ya amsa ko be amsa ba na karasa gaban table din sa na ajiye files din hannu na na
koma gefe ina jiran ya gama phone call din da na same shi yana yi dan na masa
bayani

"Dada is sorryyy, no I'll be coming back today insha Allah".

Ya fada can kasa,

"I missed you more Haanah, where's my Meerah and pretty?".

"Is okay, I'll be back today, I promise".

"I love you more dearies, byee".

Kaman dole haka na tsaya ina sauraren sa har se d ya gama wayar da yake yi wanda
tsabar yadda yake magana yayi baya yi ba se da nayi kusan minti biyar a tsaye ynaa
fadar iya wancan sentence din na sama.

"Here's the list if files you asked for sir".

Gyada min kai kawai yayi lamarin da yasa takaici ya cika min ciki, yanzu duk
tsayuwar da nayi dama gyada kai ne kawai amsa ta, lallai mutumin nan karshe ne.

Fita nayi ina tafe ina kunkuni abina har na kai office, daga nan kuma wani abu be
kuma hada mu ba.

__________

Watan mu hudu kenan da kama aiki a garin Bakwarni, matsaloli kamar sun tafi ashe
wanda suka fisu na gaba, a zaman da muka yi a nan har na manta da damuwoyi na na
saki jiki dan babu Mariya babu Hajiya Iya babu kuma su Amir an hada husuma.

Sedai tashi daya wai se ga wani sabon zance, ba'a kawo maganar ba se da muka je
Darma yin hutun sallah, cikin farin ciki nake bin ko ina da kallo da tunanin zan je
in ga Ummi na in kuma zagaya dangi, aikuwa haka nayi din dan naji dadin sallar ba
kadan ba, na gama zagaye na kana muka hau shirin komawa dan hutun mu ya kare se
kuma ga wani sabon tsari daga Hajiya Iya.

Wai ai ni a nan zan zauna Salees ya tafi da Mariya dan baze yiwu yaje ya tare da ni
ba alhalin babu abinda na aje ban da in ci in kasayar so wannan karon ni zan zauna
da yara su kuma su tafi, gaba daya am confused jin wata magana kuma, wai shikenan
ni mutanen nan ba zasu bar ni in samu kwanciyar hankali ba.

Duk yadda naso in fahimtar da matar nan taki dan rantsuwa tayi ba za'a bar Mariya
ba a gida, nima kuma a wannan karon nayi rantsuwa ba zan zauna ba dan ba abinda ze
sa na zauna nan alhalin aiki na yan can, wannan ma bame yiwuwa bane.

Haka dole Salees ya tarkata mu muka tafi mu uku, ni dashi da Mariya se kuma Amir,
Sahal da Ilham kuma aka bar su wajen Hajiya Iya saboda karatun su.

Base nace muku komai ba kan zaman dan kuwa rayuwa da Mariya kun san se hakuri
kawai, ana dai malejin rayuwa kawai, yau dadi gobe akasin haka har muka kuma shafe
wasu watanni biyun, anan ne kuma Kaddarar mu ta tsaya.

Tun zuwan su Mariya d sati Uku Amir ya fara rashin lafiya sama sama, da farko
Mariya bata dauki abin da wani mahimmanci ba ta rin ga bashi magunguna batare da
anje asibiti ba, wasa wasa ciwo ya fara karfi a jikin yaro hakan ne yasa ta sanar
da baban sa nan suka tafi asibiti, bayan series of test likitoci suka ce basu ga
komai ba amma suka ba su magani aka dawo aka cigaba da sha, maimakon sauki ya samu
se ciwo ya cigaba da gaba, gashi kuma duk asibitin da suka je se ace ba'a ga komai
ba lamarin da ya daga hankalin Mariya da Salees tun bare ganin yadda yaron ya kare
ya tsiyaye, hakan yasa suka buga waya gida suka fada aka fara yawon neman na Hausa
aka aiko kanwar Mariya ta kawo, ta bangaren Hajiya Iya itama Hannatu ta kawo sedai
duk a banza.

A lokacin ne suka fara rade radin ai nice na kama yaron tun da ban so dawowar uwar
sa nan garin ba dama ni mayya ce, hakan yasa aka koma karbo maganin maita sedai
kwana biyu da fara amfani dashi aka tashi ba yaro, YA MUTU!.

Anan ne cikakken tashin hankali domin kuwa ba su Hajiya Iya da Hajiya Ramatu ba,
wannan karon har da Salees a masu yarda ni na kashe masa da, a farkon maganar ban
famuyba sanin shi wanda ya aje ni yasan wace ni sedai awanni kadan kafin Amir ya
mutu Salees ya same ni a daki na dawo daga aiki dan duk abinda ake ban fasawa zuwa
aiki na ba dan na sawa raina akan su ba zan yi asarar means of earning dina ba, so
ranar na dawo na wuce su a falo, Mariya da Hannatu da Safiya suna ta kokarin ganin
sun durawa Amir maganin dan baya iya sha da kan sa, daga sallama ban sake ce musu
komai ba dan ko nayi magana basa amsa min, ina aje jaka ta kan gado se gashi ya
shigo a fusace yana buga min kofa, dan turus nayi ganin yadda ya shigo a fusace yan
huci kamar wanda ya hadiyi garwashi so se na dakata daga kokarin cire kayan da nake
yi na zuba masa ido dan nasan akwai Magana a bakin sa.

"Shin a zuciyar ki babu imanin da zaki ji tausayin wannan dan jaririn da be san
komai ba a duniya, me ye hadin sa da fadan ku da mahaifiyar sa balle kice zaki huce
a kan sa, shin Khadijah ko dan ni be kamata ki kyale yaron nan ba ya huta, eye".

Gaba daya na daburce na kasa accessing inda maganganun sa suka nufa, to cut the
drama short se na fada masa kawai

"Ban fahimci zancen ka ba, nayi wani abu ne? Wane yaron kuma kake magana ?'.

"Dan Allah ki daina wannan pretending din naki alhalin na san kin san kan me nake
magana, a rayuwar ki ki rasa wa zaki cutar se jina na saboda duniya babu amana, is
okay bari in fito Miki a mutum ki sakar min kurwar yaro da kika kama dan ina
bukatar ganin sa a raye, in zaki yi kwadayin ki kar ki kuma sauke idanun ki kan
yayana".

Yanayin da na shiga alokacin baze bayyanu ba dan kasa magana nayi, baki na da
zuciya ta suka yi min nauyi se idanu na da suke zubar hawaye Masu tsananin radadi
da azaba.

Ko a jikin Salees se ma wani uban tsaki da ya ja yana nuna ni da yatsa

"Bar ganin ina cewa ina son ki a kan yayana na sha fada Miki zan iya komai, tun
muna mu biyu ki saki yaron nan ya mike, na baki awa biyu zan je na dawo, wallahi in
baki sake shi na se kin hadu da mafi munin tozarci dan se na tabbatar na sanar da
duniya wace ce ke bakar muguwa, green snake under green grass, kina zaluntar mutane
da wannan innocent fuskan da kike displaying alhalin bakar kumurci ce ke, banda
kaddara me ze hada rayuwa ta da taki, wallahi i curse the day I met you".

Da kyar na iya daga kai na kalli lokaci wanda ya nuna min na ci awa daya da mintuna
cikin awanni biyun da Salees ya diba min, hannu na karkarwa na janyo waya ta daga
jaka na shiga call logs dina, akan number Ummi na tsaida idanu na kafin na danna
mata kira, bata dade tana ringing ba kuwa ta dauka da sallama cikin dattijuwar
muryar ta kamar yadda ta saba

"Ummi kizo zan mutu, zasu kashe ni Ummi dan Allah kizo, innalillahi wa inna ilaihi
rajiun".

Abinda na dinga maimaita wa kenan wanda ya tashi hankalin Ummi, ina ji tana kiran
suna na amma na kasa amsa wa hakan yasa ta kashe wayar, kifa wa nayi kan bed din
Ina sauke wani irin numfashi da duk wanda yaji yasan ba lafiya ba, kwakwalwa ta ta
daina tunani ta tushe, kaina yayi wani dummm.

Ina nan a haka Salees ya dawo, a lokacin kuwa tuni Amir ya bar duniya domin a yadda
naji kururuwar Mariya da yan uwan ta ko awa da fitar Salees ba'a yi ba lokacin,
irin yadda take fadar ta shiga uku ta lalace na kashe mata da shine ya shaida min
ya rasu, tun lokacin da naji haka na tashi na kulle kofa ta na koma na zauna ina
jiran tsammani, ganin hakan ba ze min ba ne yasa na kira Ummi na.

Kamar sun manta dani ba wanda ya kuma bi ta kaina aka shiga kokarin mika Amir gidan
sa na gaskiya, se bayan an kai shi an dawo sannan Salees yayi lokaci na, irin yadda
yake dukan kofar yana kiran suna na tare da zagi da munanan kalamai yasa gidan ya
rikice, wanda basu san abinda ke faruwa ba ma aka dinga tsegunta musu, ni kuwa
hankalin tashe ta ciki na daga kai na dubi agogo se naga ko awa uku ma ba'a yi ba
da kiran Ummi na, alhalin tafiyar awanni goma sha biyu ce daga garin Darma zuwa
Bakwarni, so se na saddakar dan nasan kafin su zo maybe sedai gawata dan yadda
Salees ke dukan kofar ya na tabbatar min se ya kashe ni abin ba magana, ga can kuma
taron mata makwabta da suka shisshigo suma suna fadin a fito da ni se sun yi
maganin na.

A firgice na mike tsaye lokacin da Salees ya sami nasarar balle kofar dakin, yadda
ya koma kamar wani mahaukacin zaki shine y sake rudar dani na fara girgiza masa kai
ganin yana nufo ni

"Na rantse da girman Allah Salees ni ba mayya bace ban kashe maka da ba, ka kawo
Kur'ani ma dafa wallahi bani na kashe shi ba".

Ina Salees da alama baya ma fahimtar me nake cewa dan wani irin shaka yayi min
kamar me shirin raba ni da duniya, take na fara kakari idanu na na juye na shiga
kokarin fisge kai na amma na kasa, a yadda nake shaƙe a hannun sa ya shiga kashe
fuska ta da maruka yana zagi ta uwa ta uba, hanci da baki na suka fashe suka dinga
jini amma bawan Allahn nan be yi imanin bari na ba, can sama sama nake jin wasu
muryoyi na fadin ya sake ni kar ya kashe ni sedai ban tantance na waye ba na sume a
hannun sa.

_____________

Ko da ta suma be fasa dukan ya ba seda kyar aka samu aka kwace ta a hannun sa ana
fadin ya bari kar ya daukar wa kan sa masifa, ruwa me sanyi Hajiya Iya da basu dade
da zuwa ba dan ma jirgi suka biyo tasa aka watsawa Khadijah dake kwance helplessly
sedai ko motsi bata yi ba, ruwa cikin bokiti ya sa aka watsa min wannan karon amma
duk a banza, a nan ne hankalin ta ya tashi dan tunanin shikenan Salees ya kashe ni
shima za'a kashe shi dan tafi kowa sanin dangin Khadijah ba zasu zuba ido ba, gashi
in maganar kudi ake yi ko alfarma da hanya ne sa ba kusa ba su din ba sa'an danta
bane.

A daidai lokacin Ummi mahaifiyar khadeejah tare da yayyen ta maza biyu Hashim da
Hashir da kuma autan su Hisham suka shigo, gaba daya hankalin Ummi a tashe yake ta
yadda bata tsaya kallon kowa ba ta shiga nema na
"Khadijah, Khadijah, ina Khadijahn take".

Se kuma aka rasa wanda ze bata amsa inda tashin hankalin Hajiya Iya ya ninku haka
ma Mariya, ga tashin hankalin rashin da ga kuma wani na miji yayi kisan kai, ja
baya Ummi tayi jin kafar ta ta taka mutum ya kai duba se kuwa idanun ta suka sauka
kan fuskar mafi soyuwar yar ta Khadijah, fuskar ta kumbura da shatin hannu haka
kuma tayi kacal kaca da jini, wani irin juwa ce ta dibi Ummi yasa tayi taga taga
zata fadi ya Hashim da shine babba kuma yafi kusa da ita ya maza ya tare ta, kwace
wa tayi daga hannun sa ta kai tsugunne ta shiga tattaba fuskar Khadijah kana ta
dube su cikin wani yanayi

"Hashim, Hashir wannan khadeejah na ce ko, Deeje ce wannan ko?".

Se lokacin suka lura dani suka kuma shiga rige rigen durkusawa waje na, cikin wani
irin kururuwa Hashir ya mike yana bin jama'ar falon da

Please Login or Register in order to submit comment