You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

barki da Wanda kike so, naga kamar Ina takuraki shiyasa na barki,


'ba haka bane, har ynxu xuciyata ta kasa tantance min xabina, idan nace bana son ka ko bana son Deen nayi ma qarya, amma fushinka akaina K.... ya katseta,


'ki auri Dr Deen....itace kalma dana fito bakin Sa'eed ta ďago tana kallonsa cike da mamaki,


'I know Kinason Dr Deen, he loves you too, na taba gayamiki ya sameni nan saboda ke, bawai ya roqeni na barmashi ke ba ya roqeni akan idan na aure ki na kula da ke da yaranki, na baki farinciki har a qarshen rayuwarki, ba abinda na fahimta a idanuwansa sai xallar soyayyarki, bai fito ya faďa a baki ba amma idanunsa sun nuna, ina sonki Iman, dole ta sanya xn haqura dake ki auri Dr Deen domin yafini buqatarki, bashida kowa bayan mahaifinsa, nikuma I have family matsalar bnda kwanciyar hankali akansu,


Tunda yake magana tayi shiru tana kallonsa ta kasa fahimtar komai a kalamansa Illa na ta auri Dr Deen, yes xata iya haqura da Sa'eed cos xuciyarta tafi rinjaya kan Deen and she accept it, ta amince xata auresa ko dan kwanciyar hankalinta dana yaranta,


'but Sa'eed...... Shishshsh ya katseta, kada kidamu dani, Allah is with me idan salima mai shiriyace Allah ya shiryata ya ganar da Ita, ban kullace kiba, idan kin amince I will be your brother na har abada kamar mun fito ciki ďaya dake....


Ta gyada kai tana murmushi mai tare da hawaye, farin cikinta a yau, ta rasa yayyunta biyu da suka rasu yau ga madadinsu, Dr Merah da Sa'eed, kyautace daga Allah Kuma ta karba da hannu biyu, ta rasa mahaifi ta sami baffa a hannu sai dai fatan miji na gari wannan shi kaďai ne burinta a Yanxu.


Tare da Sa'eed sukaje suka sami baffa da Mgnr kan ta amince da auren Deen, sosai baffa yayi farinciki kamar xai haďiye Iman haka yakeji,


Koda baffa ya gayawa Deen Mgnr bai nuna masa farinciki ba amma har a xuciyarsa yaji daďi, duk da hakan ya basar bai nemeta ba kamar baisan da Mgnr ba,




Dr Merah, Sa'eed da wani kawunta su suka karbi sadakinta, sune waliyyanta,


Sai dai ba yanxu xata tare ba sai tagama shirye shiryen ta kamar yanda Dr Deen shima yana buqatar lokaci har ya haďa kayan aurenta.


Salima na xaune a falo tare da yaranta taga mutane na shigowa gidan,


'waďannan su Waye ta faďa bayan ta tashi, ga mamakinta sai taga qatuwar Mota da kaya ana saukewa irin kayan amare ďinnan, maxa ke shigowa da kayan yayin da matan suka nufi ďayan part ďin da ke rufe, tana gani suka buďe suka shiga,


'no she can't believe it Sa'eed baxai mata haka, tor kodai haya yabada gurin, inajin haya ya bada gidan, let me confirm it,


Ta sanya hijab ďinta ta fita, cikin maxan masu sauke kaya ta nufa,


'sannu malam,
'sannu hajiya,
'wancan part ďin haya aka ďauke sa kome?
'A'a amaryar mai gidan ce gobe xa'a ďaura aure ta tare,


Batace komai ba amma jikinta har rawa yake saboda tashin hankali,


Koda taje ďakinta kasa xama tayi sai safa da marwa take, ganin ba mafita ta dauki hijab ďinta ta fice kai tsaye gidan Iman ta nufa ta Kuwa yi Sa'a ta sameta,


Ba Sallama ba komai ta faďa gidan suna haďa ido da fatyma ta soma faďa da xage xage ta inda take shiga batanan take fita ba,


Iman na xaune da adama tana yanka mata fruits, idan ke mai karatu kin tanka tor Iman ta tanka, tunda ta maida kanta ga cin fruit bata qara waiwayarta ba, dama iman ga haquri da sanyin hali.


Wannan ne yafi komai baqin ciki da haushi kana faďa ayima shiru amaidaka banxa Hakan ya qara kufular da salima ta soma ball da duk abinda ke falon,


Iman ta tashi ta dubi adama, ki shiga ki qarasa aikinki adama, idan wannan mahaukaciyar ta gama haukarta ta bata gurinnan kiyiwa securities magana a fitar min da Ita daga gidan kana a gyara falon tasa kai ta fice haďe da rufe ďakinta,


Kamar ta sanya ihu haka takeji angama cin amanarta a ganinta, qawarta xata aure mata miji wallahi bata isa ba, Gashi ta kirata mahaukaciya, kamar daga Sama sai ga Sa'eed a gidan abinda idanuwansa na gani ya tsoratashi, meya fito da salima da ixinin wa ta fito meyasa tayiwa falon kaca kaca haka, nan take ya ďauketa da wani Mari sai data ga gilmawar taurari, hancinta ya fara jini,


Basai na gayamaku irin Faďan da sukayi a ranar ba kamar xasu haďe junansu a haka ya fisgeta suka bar gidan......


Daren ranar basu kwantaba kwana sukayi bala'i haka ta xamar masa tamkar wata xararriya sai daya sanyata a ďaki ya rufeta kafin ya sami sa'ida.


Washe gari aka ďaura auren Dr Iman da Dr Deen...


Kana aka ďaura auren Sa'eed da Habbi qawar salima,


Koya xamansu xai kasance da salima, ya salima xata kasance idan ta wayi gari ta sami habbi a matsayin abokiyar xamanta, qawar dake bata shawara akan yanda xata Kula da mijinta, wani abin qarin haushi habbi budurwace bata taba aure ba.




My wattpad Phertymer*Babana da mijina*




©Fertymerh Xarah 💞




42






Har ynxu ban fahimce ka ba, idan ba Iman ka aura ba to Waye ka aura, ko kana tunanin bansan cewa yau aka ďaura aurenka da Iman ba,


'bani ke auren Iman ba, Wanda take aure daban wadda nake aure daban, idan Kina tunanin saboda haukarki naqi auren Iman tor kina tunanin banxa ne, anjima da dare matata xata tare koma wacece xaki ganta,


Hankalinta ya qara tashi numfashinta har fita yake da sauri da sauri, qaryane Iman yake aure idan ba shiba to wake aurenta?


'kagayamin Iman *Matar Waye?* idan har bakai ke aurentaba,


'wannan ne baxakiji a bakina ba, inaji kin saba xuwa gidanta ki sameta ki nuna mata rashin mutuncinki ynxu ma you are free... ya cigaba da haďa kayansa,


'kayan me kake haďawa Sa'eed, har ynxu ban fahimceka ba me kake nufi ne,


'kayana nake haďawa na maidasu inda amaryata inda xa'a kula dasu da darajasu.... Kafin tayi magana ya fice,


Kuka take tana haďa kayanta tayi yaji gida xataje, yana ganin lokacin da ta fita da kayan bai hanata ba, kai tsaye gidansu ta nufa, Ummanta na jin dalilin dawowarta ta rufeta da duka kamar xata cinyeta,


'ai Sa'eed yamin dai dai wallahi, kinci amanar tarbiyar danayi maki dan ba haka kika taso kika samu inayi da mahaifinki ba, kina gani da tsufana a ynxu nake kula da mijina, sau nawa yake kawo qararki gidannan in xaunar dake inyi faďa inyi rarrashi duk bakiji ba,


'xaman gidan kikeso kixo ki xauna muna gugar kafada dake, idan nayiwa mijina kwalliya kema kiyi masa gaki ga gidan ki xauna tunda kin xabi hakan a rayuwarki,


Kuka take sosai Kamar ranta,


Mahaifinta ma ya tsoma bakinsa,
'idan har kika bari kika kashe auren ki saboda son xuciya bani bake kuma baxaki xauna min a gida ba, tashi kije kibani guri shashasha kawai,


'na shiga uku *babana da mijina*, babana xai yafeni saboda mijin dayaci amanata, ta tashi tana kuka ta shiga motarta, wayar habbi ta Kira ko xata sami shawara a gurinta,


Tana ringing ba'a ďauka ba har ta tsinke ta qara kira sai data kusa tsinkewa kana ta ďauka,


'kina gida ne habbi?
'a'a Ina saloon,
'naso naxo ne, Sa'eed aure xai qara yau amaryarsa xata tare, ta fara kuka,


'wannan matsalarkice salima, sanda nake baki shawara bakiji ba ynxu ni banda abinda xn maki, bikin dake gabana ma ya isheni,


'bikin waye Kuma,
'au bakida labarin aurena ne?
'Hhhhhh wasa kike, har yaushe xakiyi aure baki sanardani ba gobe xn shigo kibani mafita,
'a'a basai kinxo ba ni xnma xo, ta tsinke wayar....


Da dare aka kawo amarya duk a nata tunanin Iman ce amarya musamman data ga little a sashen Sa'eed yau, tana ji sanda aka shigo da amaryar da guda sai leqe take ta window, bataga fuskarta ba,


ďakin Sa'eed ta nufa suna haďa ido ta fashe da kuka, yasan xafin kishin da takeji a xuciyarta, yana son matarsa bawai baya sonta ba halintane ya sanya yayi mata haka,


Ya taso ya rungumeta, rarrashinta yake cikin Kalamai masu sanyaya xuciya, sai abin na bashi mamaki ganin yau duk inda ya taba a jikinsa bata hanashi, babu harara babu mitar ta gaji sai ma qara narkewa da tayi a jikinsa tana qara kissing ďinsa....


Da kyar ya sami kansa kamar mai son yi masa fyade a Wannan daren, ya ďauki little dake barci ya fice da sauri......


Washe garin ranar ta kasa haqura ta isa sashen amarya, dai dai lokacin habbi ta fito da gudu Sa'eed na biye da Ita daga baya....


Duk suka ja turus ana kallon kallon... Tamkar a mafarki salima ke ganin habbi da mijin da tafi so fiye da komai a rayuwarta,


'barka da safiya anty xo ki xauna, cewar habbi tana kallonta qasa qasa...


tsananin ruďewa yasa tayi kan habbi suka fara kokawa, da kyar Sa'eed ya rabasu,


'munafuka, snatcher, azzaluma macuciya mai kwacewa mutane miji, sai da kika gama jin sirrina xaki aure min miji Wlhy baxan taba yafe maki ba, kaima baxan yafe ma ba Sa'eed ta soma kuka, basu ankaraba sai ganin kawai sukayi ta ďauki kwalbar malt dake ajiye ta jefata ga plasma t.v ,tayi ratsaratsa, duk abinda tasan mai fasuwa ne tabi tana fasawa, Sa'eed na fisgota ya ďauketa da Mari kana yajata ya fiddata gidan suka rufe...


Kamar habbi xatayi kuka haka take tsaye ganin yanda aka farfasa mata kaya, jiya jiya da kawowata,


Haquri ya soma bata anjima xaisa akawo mata duk abinda salima ta fasa, tana jin haka ta saki ranta ta rungume shi tana kissing,


Tare sukayi wanka sukayi breakfast, daďin da Sa'eed keji baya misaltuwa, bai taba samun irin Wannan kulawar ba, ta rakasa har motarsa sai da taga yabar gidan kana ta ďauki qaton icce ta nufi motar salima,


Salima na ganin tana farfasa mata mota ta window kafin ta fito tuni habbi tayi shigewarta cikin gidanta ta rufe, tabi motar da kallo Kamar xata sanya ihu dan haushi da takaici.......


*


Bayan wasu kwanaki Iman ta haďa duka ma'aikatan gidan guri ďaya, ta roqesu gafara kana ta sallamesu, irin sallamar da tayi masu baxasu taba mantawa da Ita ba saboda ta cikasu da dimbin alheri mai tarin yawa, sunyi rabuwar arxiki mai cike da shaquwa da kewar mace mai hankali da taqwa kamar Iman...


Mutum uku kawai tabari a tare da Ita, Suleiman, dijeh da adama,


Tun bayan auren su da Deen bata qara sanyashi a ido ba, sai dai taji muryarsa a falo shida su fauxie,


Parking tayi sosai duk abinda take buqata ta hadasu guri ďaya saboda rufe gidan xasuyi, ansa ranar tarewarta lokacin da Deen ya aiko kayan lefenta kamar na wata budurwa,


kaya ne masu kyau da tsada na gani a faďa, haka little da fauxie sai da yayiwa kowa set ďaya...




Sa'eed na bank ta kirashi ta sanardashi abinda habbi tayi, tsaki yayi ya tsinke Wayar hankalinsa a dagule wannan masifa dame tayi kama yasan duk laifin salima ne,




Da yadawo ya hadasu yayi masu faďa sosai akan su haďa kansu shi baxai ďauki wannan kishin tsiyar ba,


Habbi ta bashi haquri tace baxata qara ba xata xamo mai biyayya garesa, yaji daďin haka amma salima Kuwa buďar bakinta sai cewa tayi,


'maganar motata a gyaramin...


'yace xa'a gyara itama xn siya mata tata...


'idan har ka siyamata sabawa nima sai an canxamin Kai bnmason gyaran wata nakeso a canxamin,


'duk ba matsala bane salima indai xaku haďa kanku ku xauna cikin yardar juna....


Habbi ta dubesa tana kashe masa ido,
'sweet muje intayaka kayi wanka kaci abinci inyima tausa nasan a gajiye kake, ya saki murmushi yana kallonta ko baiyi magana ba kasan yaji daďi, ba gardama ya tashi yabi bayanta bai qara waiwayen salima ba haushi kamar xai kasheta,


Tunda yabita part ďinta bata qara jin duriyarsa ko motsinsa ba sai faman leqe take ta window ko xata ganshi shiru kakeji har Washe gari, tana tsaye a window taga fitowarsu, habbi na ďauke da briefcase ďinsa shi Kuma ya riqa hannunta har gurin motarsa,


Tana ganin lokacin daya Karbi briefcase ďinsa ya shiga mota habbi ta sunkuya ta sumbacesa kana ta soma yi masa bye bye shima yana yi mata har ya fice, wannan ranar harda kuka tayi, tunda take dashi ko falo bata taba rakashi ba ballantana hr gurin motarsa.




Amarya Iman sai faman shirye shiryen biki ake tasha qunshi ja abinka da farar mace qafafunta da hannuwanta sun fito sosai tayi kyau ga xoben xinari dake sanye a yatsun hannuwanta Wanda ya qara fito da kyawun lallenta,


Affiya, Dr Fulani da Dr Umayma sune abokanta suke tsaye a kanta na ganin sun shirya amarya sosai ciki da wajenta ta fito,


Fauxie itama Anyi mata tata shigar cikin gown fara, haka shima little cikin suit duk suna gurin Merah.....




Amarya kawai ake jira ta fito ango na cikin Mota yana jiranta, Sa'eed xaija motar amarya da ango xuwa gurin dinner....


Duk ya qagu ta fito cos sunyi late kamar ance ya ďago akayi Sa'a su affiya sun fito da Ita, an rufe fuskarta da wani net duk da haka baxaka rasa ganin fuskarta ba, ba qaramin kyawu tayi ba har ya kasa ďauke idanuwansa akanta, bama shiba har Sa'eed da sauri ya ďauke kansa gareta yana sauke numfashi, Iman yayi asararta ya fada ahankali,


Dr Fulani na bude motar ta shiga kana suda Affiya suka nufi nasu motocin,


Tunda ta shigo ta xauna qamshin turaren ta mai sanyin qamshi da daďin gaske ya mamaye motar, ga wani qamshin amarcin da take,


Sa'eed yaja motar a hankali jikinsa a sanyaye...


Duk qoqarinsa na ganin ya kauce mata ya kasa, he can't, yaga kyawun Iman sosai, kayan dake sanye a jikinta sun fito da shape ďinta wanda baisan Iman ďin haka take ba duk ganin da yake mata acikin hijab da labcoat ne amma yau ya ganta in her real image, no hijab, no labcoat,


Ya juya yana kallonta kanta na sunkuye, bata Kalle sa ba kuma batayi masa mgn ba sai dai xuciyarta ta kasa nutsuwa ta rasa dalilin shariyar da yake mata har wannan lokacin da ta amince na xamowa matarsa.


A hankali ya sauke kwayar Idanunsa akan hannuwanta inda yayi arba da Jan qunshinta, Dama gashi da son qunshi yana sha'awar yaga mace da lalle balle wannan da ta xama tasa mallakinsa, baisan lokacin daya ďora hannunsa akan nata ba ya haďe yatsunsu guri ďaya yana murzawa a hankali.......






Nima ina shirin xuwa dinner ne🏃🏻‍♀, nasan su Xuhura da Pherty novels ma suna can suna shirin xuwa dinner.




My wattpad Phertymerh1*Babana da mijina*




©Fertymerh Xarah 💞




43




*Dedicated dis page to Ayusha Muhd, Rash Kardam, Fido Sodangi, Ummi Ahmed, Uwani Tahir & Sumayya Dikko*




Hakan bai sa ta ďago ta dubesa ba kuma bata janye hannunta daga garesa ba,


Har suka iso ba Wanda ya tanka acikinsu, a tare suka fito motar ga mutane tsaye ana jiransu hotel ďin cike yake da jama'a samari da yan mata,


Suna fitowa aka soma watsa flowers a gefenta fauxie ce cikin irin tata gown, shikuma little yana gefensa cikin suit kamar Dr Deen, sunyi matuqar kyau sosai,


Nan da nan masu camera suka fara aikinsu, masu yi a waya suka soma, Sa'eed ma sai daukarsu yake, ga fertymerh Xarah novels ma kowa da wayarsa qoqarinsa yaga Dr Iman da Dr Deen a wayarsa, bama kamar Pherty novels dake ture ture burinsu suxo gaba su ďauki amarya, sai da Dr Deen yasa hannu ya kare fuskar iman ganin hasken camera sunyi yawa akanta😜.




Habbi kusa da Sa'eed ta xauna dama yabarta taxo, aka xaxxauna, nan aka fara gudanar da bikin cikin farin ciki da jin daďi,


Deen ya sunkuya dai dai kunneta,


'Na kasa haqura amma dole xn gayamiki kinyi kyau sosai har Ina kishin dubban maxan dake gurinnan....


Ta dubesa suna haďa ido ta saki murmushi cikin jin kunyarsa, shima murmushin yayi dai dai lokacin da mai camera ya daukesu....


Ana cikin yin dinner sai ga salima taxo gurin yanda tayi parking ma xai tabbatar ma da a fusace take,


Tana tsaye tana neman inda xataga habbi, Iman ta ganta sai ta ďauke kanta gefe kamar bata ganta ba, Dr Deen ma ya ganta sai dai baisan ko Wacece ba,


Kamar daga Sama ta hango Sa'eed da habbi suna dariya ba xato ba tsammani habbi taji duka, nan fa suka shiga kokawa dambe suke sosai,


Nan fa gurin ya qaure da ihu, lafiyayyun Mari biyu Sa'eed yayi mata amma bata damu ba ga hancinta na jini burinta kawai ta illata habbi, ganin yanda ta xama tamkar mahaukaciya a gurin kowa na soma neman inda yayi komai ta samu jifan mutane take dashi,


Dr Merah yaja Affiya saboda hankalinsa na gunta baya son komai ya sameta ko kaďan dan ma basuxo da yaran suba,


Dr Fulani taja hannu fauxie da little tayi Mota dasu, kowa ta kansa yake dan salima bata bar kowa ba har mijinta ta jimasa ciwo a hannu, bai taba tunanin haka take ba balle harta iya aikata hakan,


Iman a tunaninta duk saboda itane salima ke wannan haukan, a ruďe take ganin take xataxo ta jimata ciwo ne, sai ta qanqame Deen sosai Kamar xata shiga cikinsa, shi Kuma hankalinsa na gun su fauxie sai dayaga an sanyasu Mota kana ya maida hankalinsa ga riqon da Iman tayi masa, idanunta a lumshe sai hawaye take abu kaďan ke ruďata baisan irin xuciyarta ba, yasa wayarsa ya ďauketa pic batare da ta sani ba kana yasa hannunsa ďaya ya rungumota..


Da kyar wasu maza suka rirriqeta, Sa'eed ya ďaure ta da wata waya sai faďi yake,


'batada hankali daga gidan mahaukata ta fito, ta qara xabura


'qarya kake, kunci amanata ne Kuma baxan barku ba,


Ya ďaure bakinta da gyalen habbi, sai kuka take ya ďauketa ya nufi motarta da Ita ya sanyata ciki ya Kulle motar sai xufa yake, wannan wahalar dame tayi kama, ga hannunsa sai jini yake habbi ta riqosa tana hawaye,


'dear muje asibiti dan Allah,
Ya dubi hannun kafin ya nufi inda Deen yake tsaye da Iman,


'Dan Allah kuyi haquri d....... Deen ya katsesa,


'ba komai Sa'eed kayi sauri kaje asibiti, iman ta ďago tana kallonsa cikin tausaya shi har sai yaushe xai sami kwanciyar hankalin wannan matar? Suna haďa ido dashi ta qara fashewa da kuka ta maida kanta jikin Deen, Sa'eed kuma da sauri ya juya nan cikin motar suka barta habbi ta jasa suka nufi asibiti.....


Kowa ya watse sai gasu ci biki ynxu ake xuwa😂, Ummi Aysher, Faxyfashion, Serdia, Halimcy, Zarah dange, miss Aysher, baby Bello, Kdeey, Kwaise, Lilmeerahcute, Xuhura Ajiya, Meenah, Rabi'atu Sk, Didi Aneesa, Afrah bhai, Anty maijidda musa, Khadija Sidi, Shafa Umar, Maryam kaumi, Sally, Teemah cool, Anka, H.Melody, RAZ, Nusee, Pherty, Rukayya Umar, Hafsat rano, Zarah Bukar, Zee yabour, Faty Shuwa, Hindatu Arzika, Hamidata, ya salam🙆🏻 gasu nan dai dayawa har bn iya lissafaku am sorry please 👏🏻,


Sukaja suka yi turus ganin ana watsewa, Dr Merah tuni yabar gurin, Dr Deen da Iman ba motar shiga dama da ta Sa'eed suka xo kuma sunyi asibiti,


Suka tsaya cirko cirko suna kallon mutanen dake shiga mota suna barin gurin, suna kallon salima acikin motar, haka kawai Deen yaji ya tsaneta, ya juya yana kallon Iman dake qanqame da hannunsa,


'ita wannan wai wacece, meyasa tayi haka?


'matar Sa'eed ce, uwargidansa, tana kishina saboda Sa'eed, amma bansan dalilinta nayin haka ba,


Ya gyada kai cikin gamsuwa batare daya kalletaba, suna tsaye sai ga mota tayi parking gurin, sunsan motar Merah ce, suka buďe suka shiga har yakai affiya gida,


Acikin motar Dr Deen da Dr Merah suka cigaba da nanata mgnr kowane ransa a bace fuskokinsu kawai xaka gani ka karanci hakan, iman na baya tayi shiru tana saurarensu, ita suka fara ajiyewa gida kana suka fice kowane ba walwala a fuskarsa ita kanta bataji daďi ba she will never forget salima in her life....


Sa'eed sai da akayi masa ďinki a hannu, koda suka dawo ta galabaita sai xufa take tana kuka, shi yaja motarta habbi taja motarsa suka nufi gida, suna xuwa gida ya fito da Ita motar ya cillata gefe ďaya ta faďi, ya nunata da yatsa ransa a matuqar bace,


'kije na sake ki saki ďaya.... ta buga wani ihu a harabar gidan har yaranta suka fito,


'wallahi baka isaba, kayi kaďan ka sakeni saboda wannan yar iskar, ba inda xanje nida kai mutu ka raba, tana kuka ta nufi cikin gidanta.....


Sa'eed yaje ya bawa Iman haquri sosai, ta nuna masa ba komai, suna xaune Deen ya shigo gidan yanda ya gansu a falo su kaďai xaune sai dayaji wani kishi, fuskarsa kadaran kadahan suka gaisa da Sa'eed, Iman ta karanci yanayin fuskarsa sai taji jikinta ba daďi,


Sa'eed ya qara bawa Deen haquri duk ya damu ba daďi ace matarka ce sillar duk wata matsala dake afkuwa,


Deen ya nuna masa ba komai kana ya ajiyewa Iman wata alkyabba mai kyau da tsada sai qamshi take wadda xata sanya anjima idan anxo ďaukar amarya, baiyi mata mgn ba ya fice ta tashi tabi bayansa har gurin motarsa ya dubeta,


'kin fito kuma kinbar baqonki, Ashe bakida karamci.... xuciyarta na buga tasan mgn ya gayamata ta dubesa,


'ya xone fa kan mgnr salima, bayan wannan Sa'eed is a brother to me a ynxu,


Ya tabe bakinsa batare da yayi mgn ba yaja motarsa....


Da dare amarya tayi kyau cikin alkyabba, manyan motoci suka xo ďaukar amarya harda yan karere irinsu Pherty novels motarsu daban,


Motar Merah amarya ta shiga tare da Fulani, sauran qawaye da abokan arxiki da yan uwa suka shiga sauran motoci, kana aka ďauki hanyar gidan Dr Deen.......




My wattpad Phertymerh1
*Babana da mijina*




©Fertymerh Xarah 💞




44




Basuyi wata doguwar tafiya ba suka iso, sai da akaje da Ita sashen baffa kana suka nufi part ďinta da Ita, ita tsaruwa ya tsaru, komai na gidan Deen ya cnxa har fenti,


Nan su affiya suka xauna kusa da ita kowa da abinda yake gayamata cikin tsokana sai dariya suke, kwata kwata hankalinta baya kansu tana tuna farkon auren ta da Deedah, ta tuna baba da kansa ya rakata har ďakin mijinta a wancan lokacin, tana tuna rayuwarta da Deedah ynxu Kuma batasan ynda rayuwarta xata kasance a Wannan gidan ba, lokaci ďaya kuka ya xo mata Wanda a tunaninsu affiya saboda tsokanar da suke mata ne,


'daga mgn sai kuka amarya, kiyi haquri Kada kisa angonki ya koramu waje cewar Dr Fulani


Suka ďauki dariya harda sowa kafin su koma rarrashinta,


Bayan wani lokaci kowacce ta tashi tasan inda dare nayi mata suka barta ita kaďai a qaton falon ta sai kallon falon take ba laifi tasan ta kashe masa kuďi, kuma yayi kyau,


She is missing little, ko ina yake? tun safe rabonta dashi, tayi kewar rigimarsa,


Harta qaraci xamanta Deen bai shigo ba, ta tashi ta nufi inda take xaton ďakinta ne, taga su affiya sun shiga kafin su tafi, ta sauya kayanta xuwa na barci bayan tayi adduo'i tabi lafiyar gadon ta kwanta batare da damuwa a xuciyarta ba...,


Dr Deen Kuwa fitowarsa kenan daga theater room, yana tafe yana cire kayan aikinsa a hanxarce ya isa office ďinsa, ya ďauki kayansa hankalinsa da tunaninsa duk yana Kan amaryarsa yasan ta gaji da jiransa a ynxu, wannan ba damuwa bane tunda yayi qoqarin ceto rayuwa ne fatansa yarinyar da yayiwa aiki ta sami sauqi,


Tafiya yake yana tuqi yana tausayin wanna yarinyar, life is nothing....


Horn yayi mai gadi yaxo da gudu ya buďe gate ďin, bayan yayi parking ya fito kai tsaye inda baffansa ya nufa, ga mamakinsa yayi barci ga little a kusa dashi shima yayi barci ba komai a jikinsa sai pampers, ya ajiye kayansa gefe yaje inda kayansa suke ya sami riga marar nauyi ya Sanya masa kana ya fice, sai da yaje ďakin da aka bawa fauxie da Ita da dijeh ma sunyi barci, dijeh na qasa akan mattress fauxie Kuwa na akan

Please Login or Register in order to submit comment