You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa hijjab ɗin dake kusa da ita Aliyu ya ce
"Ya shigo,

Sani ya shigo ya tsaya daga bakin ƙofa ya duƙa ya gaida Aliyu sannan ya gaida Amina ya tashi ya fita.

Amina ta tashi ta shiga kitchen ɗauke ma Sani Abinci tana tashi Aliyu ya bi bayan ta.

Ta shiga kitchen ta ɗauko kulan da take zuba mai abinci.

Ta haɗa mai tea a cup ɗin shi tazo fitowa taci karo da Aliyu tsaye a bakin ƙofa yana kallon ta,

Amina ta ɓata fuska ta ce
" Abban Shukrah zan wuce.

Aliyu bai ce komai ba ya bata hanya tazo wuce wa ya riƙo ta ya ce"
Haba madam laifin me nayi ake share ni Amina ta ɓata fuska Aliyu ya ce"
Na tina abin da ya faru ya karɓi kayan hannunta ya fita dashi.
Ya samu Sani yana shara ya bashi abincin ya ce"
Idan ya gama aikin shi yaje ya dawo bai jira Amsar Sani ba ya koma ciki.

Yana shiga parlour yaga Amina zaune a saman kujera ya je ya zauna kusa da ita yana cewa tazo suje ya nuna mata wani abu,

Amina tayi shiru taƙi magana

Aliyu bai ƙara cewa komai ba ya ɗauke ta yana dariya ya nufi bedroom ɗin su,

Bari mu leƙa gidan Baffa mu dawo

Ta Batulu 🥰 ✍️


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT



💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖



*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Written by ✍️
Sa'adatu I Fulani
   (Ta Batulu 🥰)

Page 17-18

Ismael ne zaune a ƙofar ɗakin Inna suna fira da ita, Rabi'a kuma tana wanke wanke a ƙofar ɗakin mama

Amina ce ta shigo idonta jajir fuska ta kumbura babu sallama bata ce musu komai ba ta shiga ɗakin Inna Ismael ya ce zanga lokacin da yarinyar nan za tai hankali wallahi ana girma ana ƙara hankali amman ke ƙara hau kacewa kikeyi,

Inna ta kalli Ismael ta ce  "dan Allah ka rufa mun baki ban san dogon zance ko baka ga yanda ta shigo a furgice bane Ismael yaci gaba da cewa Allah yasa ba wani haukan tayi ma mijin ba ya kileta,

Inna tai banza dashi ta tashi ta shiga ɗakin ta samu Amina kwance a saman kujera tana kuka Inna ta kamo Amina ta ce "dan Allah ki natsu ki faɗa mun abinda yake faruwa,

Amina tayi banza da Inna taci gaba da kukan ta Inna tayi tayi ta faɗa mata abinda yake faruwa amman taƙi magana,

Inna ta tashi ta fita kai tsaye ɗakin Baffa ta shiga ko sallama ba tayi ba ta bankaɗe ƙofar ta faɗa,

Baffa yana zaune a saman darduma yana jan carbih Inna ta shigo ta fara bashi labarin abinda ke faruwa har tayi ta gama Baffa bai ɗaga kai ya kalleta ba,

Inna tasa mai kuka ta na cewa saboda ita ba yarinyar so bane shiyasa yayi banza da ita amman da Fatima ne da tini ya fusata yayi waje.

Inna taci gaba da magana tana cemai wallahi yaji tsoron Allah ya daina nuna bam bamci a kan iyalan shi har tayi ta gama bai kalleta ba Inna tasa kai ta fita,

Bayan fitan ta Baffa ya tashi yaje ya tsaya a bakin ƙofa ya hango Rabi'a tana kwashe wanke wanke Ismael kuma yana zaune a inda yake tin ɗazun bai motsa ba,

Baffa ya kira Rabi'a ya ce "ta kira mishi Mama sannan ta kira mishi Amina a ɗakin Inna,
Baffa ya kalli Ismael ya ce "zoka kira mun gadanga ko Nasser a waya
Ismael ya tashi yabi bayan Baffa da ya shiga ɗaki,

Baffa ya bashi ƙaramar wayar da Aliyu ya siya mai ya ce  maza kira mun su kabani wayar,
Ismael ya kira Aliyu ta shiga tana ringing bai ɗauka ba sai ya kira Nasser ringing ɗaya Nasser ya ɗauka Baffa ya karɓi wayar bai tsaya amsa gaisuwar da Nasser yake ba ya ce  kazo gida ka sameni yanzu,

Nasser ya ce gayi nan zuwa Baffa yaba Ismael wayar Ismael ya amsa ya kashe wayar Mama tayi sallama ta shiga ɗakin.
Baffa ya samu guri ya zauna Mama ta zauna kusa dashi
Baffa ya kalli Ismael ya ce "ka gaya ma tsohuwarka ita nake jira.

Ismael ya fita yana ƙunshe dariya ɗakin Inna ya shiga ya same su zaune ta tasa Amina a gaba tana kallo ita kuma Amina ta nata kuka,

Ismael ya kalli Inna ya ce  "Baffa yana jiranku keda wannan mara kunyar yana faɗin hakan yayi waje da sauri,

Inna tace daka sani ka tsaya kaga a binda zanyi maka ƙaramun mara kunya kawai
Inna ta hau lalaɓa Amina akan ta tashi suje kiran da Baffa yake musu.

Daman tin ɗazun take lalaɓa ta amman taki motsawa suna cikin hakan Nasser yayi sallama ya shigo ya tsaya bakin ƙofa.

Inna ta amsa sallamar ya duƙa har ƙasa ya gaishe ta Inna ta amsa ta tambaye shi iyali ya ce
Alhamdulellahi Nasser ya kalli Amina ya ce
waye sa'an wasanki a gidan nan da zaki shanya mutane zaman jiranki Amina ta duƙar da kai ƙasa.

Inna tai karaf ta ce  "bacci ne ya ɗauke ta yanzu ta tashi Nasser bai kara magana ba ya fita Amina ta tashi tana tura baki tabi bayan shi Inna tabi ta a baya.

Amina tayi sallama ta shiga ɗakin ta gaishe da Baffa ta gaida Mama ta samu guri ta zauna Baffa ya kalli Amina ya ce "lafiya kika zo kina kuka kuma kinƙi magana Amina ta duƙar da kai tana hawaye ta ce

"Daman shi ya ce in zo gida sai ya nemeni Baffa ya kalli Nasser ya ce "kira mun mijinta muji gaskiyar zance,

Nasser ya miƙama Amina wayarshi ya ce "tasa mai number shi Amina taƙi karɓan wayar Baffa ya daka mata tsawa ya ce idan tai wasa yanzu nan zata ji a jikinta,

Hannu yana rawa ta karɓi wayar tasa number Nasser ya karɓa ya baɗe kiran gaba ɗaya sannan ya kira ringing ɗaya a ka ɗauka haɗe da sallama,

Suka gaisa da Nasser tin kafin Naseer yayi magana ya riga shi

Ya ce "Amina ta zo gida Nasser yayi banza dashi ya cigaba da cewa.

Wallahi Amina bata da mutunci ga rashin kunya ga rainuwa idan yayi mata abu sannan kuma ta raina mahaifiyar shi bai isa yasa ta ko ya hanata ba.

Duk abinda yayi mata bai iya ba ga hangen rayuwar wasu.
Ga faɗar baƙar magana hatta mahaifiyar shi gaya mata ta keyi dan Allah su barta a gida ta kwana biyu ko zata sanja hali amman shi gaskiya ya gaji da ita.

Nasser zaiyi magana Baffa ya hana sai da suka gama jin abinda ya faɗa sannan Baffa ya karɓi wayar ya ce " idan babu damuwa yana son ganinshi ko zuwa anjima Sager ya ce " in sha Allah zaiyi ƙoƙirin zuwa.

Bayan sun gama magana ya kalli Inna da ke tsaye a bakin ƙofa ya ce "ta shigo ya kalli Nasser da Amina tin kafin yayi magana suka fita.

Baffa ya kalli Inna ya ce " hanakalin ki ya kwanta kin ɓata mun tarbiyan yarinya Inna ta ce "tayaya daga faɗan magana zai hau kai ya zauna babu bincike ita yarinyar mana a tambayeta aji ta bakin ta.

Baffa ya kalli Inna ya ce "duk abinda ya faɗa bakiji ba Baffa ya cigaba da cewa wallahi kinji na rantse duk abinda ya faɗa ta aikata shi.
Baffa ya cigaba da cewa cikin yarana nasan halin kowa nasan abinda in a kace sun aikata zan yarda amman saboda ƙin gaskiya irin naki kince sharri a kai mata.

Inna ta fara hawaye Baffa ya ce "ta adana hawayenta domin lokacin zuban su baiyi ba ya ƙara da cewa ta fitan mishi a ɗaki zai zo ya sameta Inna ta fita tana kuka.

Mama ta kalli Baffa za tayi magana ya da katar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu ganin hakan Mama tayi shiru tana kallon shi.

Baffa ya ce " tasa Rabi'a ta kawo mishi tea idan ta fita.


Mama ta najin hakan ta miƙe tana cewa dan Allah yayi haƙuri kar yasa wannan damuwar a zuciyar shi tinda baida isashen lafiya.

Bayan fitan Mama daga ɗakin Baffa ɗakinta ta nufa ta samu Rabi'a tana guga Mama ta ce " ta haɗa ma Baffa Lipton ta kai mishi bata jira amsar da Rabi'a ke bata ba ta shige bedroom domin ta kwanta.

Rabi'a ta kashe socket ta fita kitchen ta shiga ta haɗa kamar yanda ta san yana so ta shiga ɗakin bayan tayi sallama ta samu Baffa zaune a inda Mama ta barshi.

Rabi'a ta duƙa tayi mishi sannu da jiki ta miƙa mishi tean Baffa ya karɓa yana samata albarka.

Rabi'a tana son Baffa saboda duk idan suka haɗu sai ya sa mata albarka ko gaishe shi taje yi da safe zaita mata addu'o'i.

Rabi'a ta koma ɗaki ta cigaba da aikin ta.

Bari mu koma gidan Aliyu

Ta Batulu ✍️



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment