You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tana ganin umar ya ganta sai ta hau borin kunya tana ta zagin shi
, Umar baice mata komai ba ya huce,

    Mama tana jinsu tai shiru tana ma Inna fatan shirya,

Umar ya shigo da sallama yace ma Fatima baffa yace ta kai mai Lipton,

mama tace ma Fatima ta kai mai wanda ta zuba mata idan ta dawo sai ta zuba mata wani,

  Umar yace bari in zuba miki ita kuma Fatima ta dauki na baffa ta fita,

Fatima tai sallama ɗakin baffa ya amsa yace mata ta shigo,

tana shiga sai ga Inna ta shigo babu ko sallama Fatima tai kamar bata ganta ba,
Fatima ta matsa gaban baffa tace mai barka da dare ta aje kofin ta tashi ta fita,

Inna ta kalli baffa tace mai wannan zalunci ne ba adalci ba, kuma allah yana gani wallahi sai yayi mun sakayya,

baffa bai ce mata komai ba har ta gama maganar ta,
sai ma tashi da yayi ya shiga daga ciki hannun shi ɗauke da kofin da fatima ta kawo,

  Inna tayi kwafa tace wallahi zaka dawo ka same ni,
   

Fatima tashiga ɗakin su bakinta ɗauke da sallama ta samu umar suna fira da Mama,
itama ta zauna suka cigaba da firan da ita,

tara da rabi baffa ya shigo ya zauna suka ɗan taɓa fira kafin yayi musu sai da safe,

Yana fita umar  yayi musu sallama ya tafi ɗakin su,

Mama tayi alwala ta hau darduma Fatima tayi alwala ta kwanta,

Agurguje anyi auran Amina da Aliyu baffa ya basu gidan zama amman ba unguwa ɗaya suke ba,

  Umar ya tafi jami'a Fatima juma ansa mata rana da saurayin da baffa ya zaɓan mata,

  Duk da Aliyu baya gidan suna zuwa islamiyyar da ya sa su,
ita, kuma Amina rashin kunya ya ƙaru tinda mai tsawatar wan yabar gidan,

Ismael kuma baffa ya kaishi garin zaria karatu bayan ansha fama da Inna,

  Yanzu gidan daga Fatima sai Amina sai Nasser sannan umar,

  Fatima tayi candy  baffa yace idan taje ɗakin mijinta taci gaba a can yanzu Amina ka ɗai ke zuwa boko itama ba kullum ba,

Gidan Aliyu zama suke cike da Farin ciki da jin daɗi Amina tana girmama shi,

suna son junansu sosai, gashi allah ya fara dafa mai,

mai gidan shi ya bashi shago ya zuba mai kaya,

yace ya mayar mai da kuɗin kayan,
ya riƙe ribar shima ya kula da kanshi tinda yanzu ya aje iyali,

Bayan shekara uku anyi auren Nasser da budurwan Shi maryam har ma ta nada ƙaramin ciki,
Nasser ya gama makaranta ya kama sana'ar saida wayoyi a shagon da Aliyu ya buɗe mai,

Shima baffa ya bashi gida kusa da Aliyu daman gidan ya siyane domin su zauna aciki

Idan sun tashi aure,

Fatima tayi aure da mijinta Abubakar yana saida motoci suna zaman lafiya da mijinta,

Domin Fatima halin mahaifiyarta ne da ita,

Abubakar yana sonta sosai kuma yana kulawa da ita yanda ya dace,

Umar yana cigaba da karatu  Ismael kuma yana Zaria,

Mama ta ɗauko Yar kanwarta mai suna Rabi'a tana taya ta zama,

Amina kuma anata tara samari a kofar gida tin baffa na fada,

Inna tana kareta ya gaji ya sama ta ido,

Acewar Inna gwanda ta zaɓa ta darje ta samo wanda yafi na Fatima kuɗi,

Gidan Aliyu suna rayuwa cike da farin ciki ƴar su ɗaya mai sunan mama suna cemata Shukrah,

Yarinya mai kama da babanta sakk,

Duk da itama uwan ba baya ba gurin kyau,

Amman idan kaga shukrah kana ganinta kasan waye Aliyu ne babanta,

Shekarun shukrah 2 a duniya Fatima tana son shukrah sosai, haka shima baffa yana sonta,
itace jika na farko a gurin baffa kuma ta fito daga gurin ɗa mafi soyuwa a zuciyar shi,

Ta Batulu 🥰 ce✍️


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT


💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖



*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Written by ✍️
Sa'adatu I Fulani
   (Ta Batulu🥰)


Page 11-12

Bayan wani lokaci abubuwa da yawa sun faru,
Dawowar Ismael gida auren Amina umar ya kammala karatu ya samu aikin banki,

Fatima ta haihu na miji sunansa Aliyu suna kiransa da Sajjad,

matan Nasser ma ta haihu na mace sunan yarinyar Khadija,

Yaran Aliyu biyu bayan shukrah sun ƙara samun Sa'adatu suna ce mata Darraini,

Tsufa ya ƙara kama baffa sosai domin yanzu yaran suke riƙe da gidan,

Amina tayi aure bayan ta gama ruwan ido ta zaɓo wani mai suna sager,
suna zaune a cikin garin Jos yana sana'ar sai da takalma,

Shima Naseer kudi sun fara zama,

Matan Aliyu da matan Nasser kan su a haɗe yake,

Duk da ka san cewar ba gida ɗaya suke zaune ba,

Amman suna zaman lafiya babu mai jin ƙan su,

Aliyu ya gina gidan shi mai kyau sun tare plat biyu,
Sai nasa plat ɗin daban, kowani plat two bedroom ne kowanne da toilet a ciki sai kitchen a parlourn,

Gidan yasha tayis ga famfo harda gate,

Yanzu haka shagunan Aliyu biyu ɗaya a garin su ɗayan kuma a Jos,

Yana ta tinanin ya ɗaura Ismael a shago ɗaya tinda duk cikin su kowa yana da abin yi amman banda shi,

Saboda shi yaƙi karatu ko yanzu da ya dawo gida babu abinda yake yi face zaman majalissa,

Aliyu ya tara ƴan uwan shi ya fada musu abinda ke cikin zuciyar shi game da Ismael,

Naseer ya ce shi a nashi shawaran ya fara jaraba shi ya bashi jari ko treda ya buɗe mai ya ga kamun kan shi kar yaje ya ɗaura shi a kan dukiyar shi a samu matsala,"

Shima umar haka ya ce,"

Aliyu ya ce musu zai je gida anjima gurin baffa,

Daga haka ya sallame su kowa ya kama gabansa,

Da daddare Aliyu ya shirya tsaff zai je gida sai Amina tace mai,
ita ma zata je domin ta kwana biyu bata je ta gaida baffa ba,

Aliyu yace mata tai sauri ta shirya yana jiranta,"

Amina tace to bata jima sosai ba ta fito hannunta riƙe da Darraini ɗayan kuma leda ne mai ɗan girma tana tafe shukrah ƴar shekara 8 na binta a baya,

Tsakanin Shukrah da kuma Darraini shekara 4

Aliyu ya ɗau shukrah ya fita ya ce ta same shi a waje,
Daman lokacin auren Amina ya sai mashin,"

Amina tana fitowa ta hau mashin ɗin shukrah na gaban mashin Darraini na tsakiyya suka tafi,

Bayan sun isa gida ya aje mashin ɗin ya riƙe shukrah suka shiga cikin gidan bakin su ɗauke da sallama,

babu kowa a tsakar gidan sai Ismael shima yana ganin su ya fara zare ido kana ganin shi kaga mara gaskiya,

Aliyu yayi kamar bai ganshi ba shukrah ta ƙwace hannunta ta shige ɗakin baffa tana kiran sunan shi,

Amina kuma ta nufi ɗakin mama hannunta riƙe da Darraini,"

Aliyu ya kalli Ismael yace mai ka keyi a nan,"?

Ismael yayi ƙasa da kai yace mai babu komai,"

Aliyu ya kalle shi yace mai kaji rani ina neman ka tinda kai baka zumunci da kowa,"

Ismael yace to

Aliyu ya huce ɗakin baffa yayi sallama ya shiga ya samu shukrah ta haye mai jiki tana ta surutu,

Aliyu yana mamakin yanda shukrah take sakewa da baffa take mai surutu,

Shukrah bata da yawan magana duk da ka san cewar Aliyu muskili ne,

Amman shukrah tafi shi,
domin ita ko magana kayi mata idan bai mata ba ko kallon ka baza tayi ba,

Amman idan kaji zancen ta tazo gurin baffa ne idan kaji dariyar ta mai yawa tana tare da baffa ne,

Aliyu ya kalli baffa yana zaune yana jan charbi duk ya tsufa domin wani lokacin ko fita ba yayi,"

Aliyu ya gaishe shi ya mai ya jiki baffa yace jiki Alhamdulellahi,"

Aliya yace ma baffa daman wata magana ne ke tafe dani baffa ya gyara zama yace Inajin ka,"

Aliyu ya faɗa mai shawaran da suka yanke da ƴan uwan shi,"

baffa yayi farin ciki sosai yayi murna daman abin yana damun baffa zaman shi hakan babu sana'a tinda shi yaƙi yin karatun gaba ɗaya,

Sauƙin ta ɗaya ma daya kai shi zaria babu laifi yayi karatun domin har sauka yayi,"

Baffa yasa musu albarka dukan su sannan ya ƙara mai da nasiha kamar yanda ya saba,"

Baffa yana yawan gaya ma Aliyu yaji tsoran allah ya kula da hakkin iyalin shi karya zalunce su,
domin suɗin amana ne a gurin shi kuma za a tambaye shi yanda ya tafiyar da wannan amanar da aka bashi,"

Aliyu yayi ƙasa da kai yace in sha allah zan kiyaye na gode baffa allah yaƙara nisan kwana,
baffa ya ce mai yaje ya gaisa da mutanan gidan yazo su tafi gida kar dare yayi musu a hanya,

Aliyu ya fita daga ɗakin baffa jiki a sanyaye"

Saboda har yanxu ya kasa saba wa da wannan nasihar na baffa,

Gani yake kamar wasiyya yake barin mai,

Aliyu ɗakin Inna ya shiga bayan yayi sallama an amsa ya shiga ya zauna a ƙasa ya gaishe ta,"

Ita fa har yanxu Inna bata sanja halin ta ba domin duk cikin yaran baffa tafi kishi da Aliyu,

Inna ta amsa tana washe baki tace Inna rigimammiyar take haka take cema shukrah,

Saboda Inna shukrah bata son zuwa gidan,

Domin jinin su bai haɗu ba,

Bayan sun gama gaisawa ya tashi ya fita Inna ta bishi da harara,

Aliyu yayi sallama ɗakin mama ya shiga ya same ta a zaune Amina tana shafa mata man zafi a ƙafafun ta"

Amina tana ganin ya shigo tace bari taje ta gaida baffa,"

mama tayi murmushi tace daga nan kya tawo da sarkin rigima,

Amina tana murmushi tafita,

Ɗakin baffa ta shiga bayan tayi sallama yanda Aliyu ya barsu shida shukrah itama haka ta same su,

Amina ta duƙa har ƙasa ta gaida baffa tayi mishi sannu da jiki baffa yace jiki ai ya warware,"

Baffa ya kalli Amina yace mata daman ina nemanki,"

Amina tayi ƙasa da kai tace to baffa allah yasa ba ƙarana shukrah ta kawo ba,"

Baffa ya ce a'a
Wani amana nake son baki,"

Amina tai shiru tana sauraron baffa,"

  Baffa yayi ƙasa da kai yace Amina dan allah ina son ko bayan raina kiyi mun alƙawarin zaki zauna da Aliyu,"

Amina tayi tsit kanta a ƙasa baffa yaci gaba da magana yace Amina akwai tarin ƙalubale a gabanki,"

baffa yace kinga Aliyu duk cikin ƴaƴana yana da wata ɗabi'a wanda ba kowa ya san da ita ba,
amman nasan ke kinsan da wannan ɗabi'ar tashi,"

Baffa yace Amina ki rage bacci domin akwai aiki mai tarin yawa a gabanki,

Sannan kuma ki kula da yaranki duk rintsi karki bari tarbiyan yaranki ya lalace,

Baffa ya shiga daga ciki sai gashi ya fito hannun shi riƙe da wani babban gora yazo ya zauna inda ya tashi,
 
Yace ma Amina tazo ta karɓa,"

Amina taje ta karba jikinta yana ta rawa,

Baffa yace mata rubutu ne a ciki ina so kiba yaranki su sha kema kisha sannan shima Aliyu kiba shi yasha,"

Amina tayi godiya ta tashi taje ta ɗau shukrah da ta fara bacci a jikin shi tayi mai sai da safe tata shi zata fita,"

baffa ya kirata,

Amina ta dawo ta zauna baffa yace mata ki ƙara hakuri akan wanda kike dashi,"

Sannan kuma ki ƙara riƙe sirrinki da kyau duk abinda zaki gani ki ya haƙuri komai zai huce,
Amina ta kasa magana baffa yace mata zaki iya tafiya,"

Bayan fitan Amina baffa yayi murmushi yace tabbas ubangiji baya zalunci kuma baya barin azzalumi,


Ta Batulu 🥰 ce ✍️


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT


💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖



*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Written by ✍️
Sa'adatu I Fulani
  (Ta Batulu🥰)

Page 13-14

Bayan Amina ta fito daga ɗakin baffa sai ta ɓoye jarkan da ya bata a cikin hijjab ta nufi ɗakin Inna,

Ta yi sallama ta shiga ɗakin ta samu Inna zaune a kan kujera suna fira da Ismael,

  Amina ta samu guri ta zauna ta gaishe da Inna Ismael ya gaishe ta Amina ta ce," Ba zan amsa ba saboda tun da ka dawo ban ganka a gidana ba,

Ismael ya ce," In Sha Allah zan zo gobe idan Allah ya kaimu Amina tayi murmushi ta ce,"

Allah ya kawo ka lafiya

Inna ta kalli shukrah dake kafaɗar Amina tana barci  tace rigimamiyar tayi bacci,

Amina ta ce," eh ta yi barci a ɗakin baffa

Idon Inna yana kan hannun Amina tana son ganin a binda ke ɓoye a hannunta domin ta san daga ɗakin baffa ta shigo,

Amina tayi kamar bata ganta ba hassalima da taga kallon yana yawa ta tashi tayi ma Inna sai da safe  ta fita,

Ɗakin mama Amina ta shiga ta samu Aliyu da umar suna zaune suna fira,

Aliyu yana ganin Amina ya ce," daman ke nake jira mu wuce,

Umar yace Aunty na ni ka dai barka da dare Amina tayi dariya ta ce," Allah ya shirya mana kai
umar yayi dariya,

Aliyu ya ce," karki biye ma wannan sarkin surutun kinga dare yayi ga shukrah ma tayi barci zo mu wuce gida,

Mama ta fito daga bedroom hannunta riƙe da leda taba Amina taba takwaran ta,

Amina ta duƙa har ƙasa ta karɓa  tana godiya Aliyu ya karɓi shukrah,

Umar kuma ya ɗau Darraini itama tayi barci suka fita,

Suna fita su kaci karo da Inna a bakin window tana tsaye,

Dukan su sun ganta amman sai suka nuna kamar basu ganta ba domin idan da sabo sun saba da halinta
har Amina tasan halin Inna,

Bayan sun fita Aliyu ya kalli Umar ya ce," Ismael ya same ni a gida gobe idan Allah ya kaimu,
sannan ya karbi shukrah Amina ta karɓi Darraini suka tafi,

Bayan sun isa gida Amina ta kwantar da shukrah a ɗaya ɗakin inda suke kwana ita da ƙanwarta,
taje tai wanka tazo tasa kayan bacci  ta tsaya tana ma shukrah addu'a,

Aliyu kuma ya kai Darraini ɗakin su ya kwantar da ita shima yaje yayi wanka yazo yasa kayan bacci yayi addu'a ya kwanta,

Amina ta shiga ɗakin bakinta ɗauke da sallama ta samu Aliyu har yayi bacci ta zuba mai ido tana kallon shi,

tana ta nazarin maganar baffa tabbas akwai abinda yake shirin faruwa,

Ita da kanta tasan Aliyu yana da ɗaukan zuga,
kuma wani lokacin yana da yawan ɗaukar maganar mutane koda kuwa ba gaskiya suka fada mai ba sannan akwai shi da yarda da abinda yaran shi suka faɗa mai,

Amina ta daɗe a zaune tana ta tunanin maganar baffa tabbas ta san gidan su Aliyu akwai abinda ke faruwa,

A ƙarshe dai ta yanke shawaran zata tsananta  addu'a koma mene ne yazo mata da sauƙi,

Darraini ta tashi tana kuka Amina ta ɗauke ta ta kaita toilet tasa ta tayi fitsari,

tazo tasa mata pampas ta haɗa mata tea ta bata tasha sannan ta kaita ɗakin su ta samu  kaya marasu nauyi tasa mata ta kwantar da ita a gefen shukrah,

Har ta fita ta dawo ta ɗau shukrah ta kaita toilet ta sata tayi fitsari itama ta sanja mata kaya ta kwantar da ita ta ƙara musu addu'o'i ta jamusu kofar ta fita,

Kitchen ta shiga ta haɗo Lipton ta fito ta zauna a parlour tana sha tana tinani parlourn yasha saitin kujeru pink da fari ga ƙaton kafet a tsakiya shima pink da fari,

Lokacin da zasu tare Aliyu ya sanja mata kayan ɗaki komai na parlourn pink da fari ne, kayan kallo ga ƙaton fridge show glass masha Allah komai yaji a parlourn,

Gaba ɗaya jikin Amina  yayi sanyi gashi baffa yace ta ƙara riƙe sirrinta,

Babu wanda zata iya shawara dashi bata da ƙanwa ko ɗaya kuma mahaifiyarta ta  rasu tin bayan haihuwar shukrah bada jimawa ba,

Sunan Darraini sunan mahaifiyar ta ne shiyasa suke kiranta da suna Darraini Saadatul Darraini,

Amina takai wajen ɗaya da wani abu a zaune, kafin ta tashi ta shiga ɗaki tayi alwala ta shimfiɗa darduma ta fara sallah,
Bayan ta idar ta ɗauki Qur'ani bata tashi a gurin ba sai da aka kira assalatu,

Amina ta tashi ta shiga kitchen tana shiga suka kawo huta ta jona buta domin ya ta fasa mata ruwan zafi ta ɗau plas ɗin ruwan zafi ta fita,

Ɗaki ta shiga ta aje plas ɗin ta shiga toilet ta ɗauko bokiti ta juye ruwan plas ɗin ta shiga wanka bata jima sosai ba ta fito tazo ta zauna a gaban mirror tana shafa lotion,

Tayi simple make-up ta samu doguwar riga tasa ta fesa turare tayi ɗaurin ɗankwali mai kyau,

Ta tashi taje gaban gado tana tashin Aliyu tace mai lokacin sallah yayi Aliyu ya kafa mata ido ya kasa magana,

Aliyu ya ce ma Amina zokiji wata magana
Amina tayi dariya tayi hanyar barin ɗakin tana ce mai zai rasa jam'i fa ya tashi,

Tafita ɗakin ta leƙa ɗakin su shukrah taga sunata barci taja musu ƙofar ta fita kitchen ta shiga taga  ruwan da ta ɗaura yana ta tausa,

Ta koma ɗaki  ta samu Aliyu har yayi alwala zai fita massalaci tace mishi a dawo lafiya ta ɗau plas ɗin ta koma kitchen ta  juye ruwan ta ƙara jona wani ruwan ta fita ta koma ɗaki daman bata ɗauke darduman da tayi sallah a kai ba tana shiga aka tayar da sallah ,

Daga masallacin

Zuwa gidan su babu nisa gida uku ya raba bayan Amina ta idar da sallah tayi addu'o'i sama sama tayi azkar ɗin safe, bayan ta idar ta fita ta koma kitchen tana zuwa ta samu ruwan ya tausa,

Ta kashe jikin socket ɗin ta fita ta koma ɗaki ta shiga toilet ta ɗauko bokiti ta koma kitchen ta juye duka ruwan a ciki ta ƙara jona wani ruwan ta ɗau bokitin ta fita,

Ɗakin su shukrah ta shiga ta kamo shukrah ta shiga da ita toilet ta wanke mata baki tayi mata wanka tasa ta tayi alwala ta ɗaura mata ɗaya daga cikin towel ɗin dake rataye a toilet ɗin,

Amina ta fito shukrah na biye da ita a baya shukrah ta zauna saman ƙaramin kujeran dake gaban mirror Amina ta buɗe man shafawa taba shukrah,

Sannan ta ɗauki Darraini ta shiga da ita toilet,

Ta cire mata pampas ɗin jikinta tayi mata wanka ta wanke mata baki ta samu ƙaramin towel wanda bai kai na shukrah girma ba ta ɗaura mata
ta kamo hannunta suka fito,

Amina tana fitowa ta samu shukrah tasa uniform ɗin school tana sallah da  hijjab ɗinta har ƙasa,

Amina ta aje Darraini ta fita ta koma kitchen tana zuwa taga ruwan ya tausa ya kashe kanshi, taje toilet ta ɗauko bokiti ta juye ruwan zafin ta fita dashi,

Ɗakin yaran ta leƙa ta samu shukrah tana shafama Darraini man shafawa, ganin hakan sai Amina ta tafi ɗakin ta,

Tana shiga ta samu Aliyu yana zaune a saman darduma yana karatu,

Amina ta shiga bayan tayi sallama toilet ta nufa ta shiga bakinta ɗauke da addu'a,

Ta shiga toilet ɗin ta ƙara ɗaurayewa saboda lokacin da za tayi wanka sai da ta wanke ta ɗauko wani ruwa a gora ta yayyafa ta ɗauko bokitin da ruwan zafin yake ciki ta shiga dashi toilet ɗin ta janyo ƙofar ta fito,

Tana fitowa ta samu Aliyu zaune yana kallon ƙofar toilet ɗin,

Amina taje kusa dashi ta duƙa ta gaishe shi Aliyu yasa hannu ya jawota jikin shi, yace mata sannu da ƙoƙari matar aljanna

Amina tace baka amsa gaisuwata ba,"

Aliyu ya ce nayi kewarki ne da yawa Amina za tai magana taji sallamar shukrah a bakin ƙofa
Aliyu ya amsa sallamar,

Ta Batulu 🥰 ✍️



Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT


💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖



*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Written by ✍️
Sa'adatu I Fulani
   (Ta Batulu 🥰)

Page 15-16

Amina ta tashi a jikin Aliyu sannan ya basu izinin shigowa ɗakin.

Shukrah ta shigo hannunta riƙe da Darraini ita ma sanye da uniform ɗin school Aliyu ya kalli Amina ya ce.

"Madam kin manta yau monday baki bamu breakfast ba"
Amina ta ce ruwan wankan shi yana toilet
Shukrah ta duƙa har ƙasa ta gaida Aliyu sannan ta gaida Amina
Darraini itama tayi yanda shukrah tayi,

Amina ta ce Shukrah ta zo suje kitchen.

Darraini ta zauna ta jira su

Aliyu ya ce." A'a karki
ƙona mun yarinya.

Amina tayi dariya ta kamo Shukrah suka fita
Aliyu kuma ya aje Darraini a saman gado ya shiga toilet.

Amina tasa Shukrah ta gyara mata kayan miya.

Ita kuma ta haɗa tea a ƙaramin cup ta fita ta koma ɗaki ta samu Aliyu yana wanka. Ta ɗau Darraini da ta fara bacci ta fara bata shayin saboda ita bazata iya jiran a gama breakfast ba.

Bayan ta gama bata shayin ta kwantar da ita ta fita ta koma kitchen
Ta samu Shukrah har ta niƙa mata kayan miyan a greater.

Amina ta kunna gas saboda sun kashe wuta ta kwaso kayan ƙamshi ta zuba a tukunya tasa sugar tasa ruwa ta ɗaura a wuta.


Shukrah ta fita daga kitchen ta yi sallama ta shiga ɗakin Amina.
Bayan shukrah ta fita daga kitchen
Amina ta cigaba da aikin ta.
Bayan  ta sauke ruwan shayin ta  ɗauko wani flas ɗin ta juye wannan ruwan zafin a ciki.

Ta ɗaura tukunya a wuta ta zuba mai ta soya kayan miya tayi sanwa tasa spices ta rufe tukunyar.

Sannan ta koma parlour ta hau gyarawa ka san cewar babu datti sosai yasa ba a ɗau dogon lokaci ba ta gama gyarawa.
Tasa turare ta koma kitchen ta samu ruwan ya tausa.

Ta kwaso indomie ta zuba ta rufe tukunyar ta kwaso albasa tana yan kawa bayan ta gama yan kawa ta zuba a ciki ta rufe tayi ƙasa da wutan ta fita.

Dakin yara ta shiga ta gyara tasa turare ta kwaso musu jakan makaranta ta ɗauko darduman da suke shimfiɗawa idan zasu ci abinci ta rufe ɗakin ta fito.

Parlour tazo ta aje kayan hannunta ta kira Shukrah tazo ta fara kwaso cups a kitchen.
Ita kuma ta shimfiɗa darduman ta shiga ɗaki ta samu Aliyu zaune Darraini tana jikin shi yana mata wasa Amina ta ce
"Abban Shukrah komai yayi ready Aliyu ya ɗauko  Darraini ya fito Amina kuma ta ɗau flas ɗin data aje ta fita.

Amina kitchen ta shiga ta aje flas ɗin ta sauke girkin ta ɗauko kulan Darraini na makaranta ta zuba mata indomie sauran ta juye a plate guda biyu.

Shukrah ta shigo kitchen din Amina ta bata kayan tea tace taje ta aje gata nan zuwa
  Amina ta fita da plates ɗin data zuba indomie,

Ta samu Aliyu zaune a saman darduman da suke cin abinci yana haɗa ma Shukrah tea
Amina ta aje plate ɗin ta ɗau cup tana haɗa ma Aliyu nashi.
Shukrah abinci bai dame ta ba domin ko school bata zuwa da abinci sai dai drinks da biscuits,

Bayan sun gama breakfast Aliyu ya tafi kai su shukrah school Amina kuma ta ƙara gyara gurin tayi wanke wanke.

Ta shiga toilet ɗin yara ta wanke ta fita ta koma ɗakinta,

Ta zauna zaman make-up tayi kyau sosai ta samu kaya riga da wando tasa Amina akwai diri ga idanu dara dara masha Allah,

Bayan ta gama ta ƙara gyara bedroom ɗin har toilet sai da ta ƙara gyarawa ta ɗau rigan da Aliyu ya cire ta haɗa da nata ta fita.

Ɗakin su  Shukrah ta shiga tasa musu turare ta shiga toilet ta ɗauko bokiti ta kwaso kayan da suka cire ta haɗa da na hannunta ta fita dasu,

Ta za gaya ta baya inda igiyar shanya yake ta aje wankin ta fita ta koma toilet ɗin ɗakin su Shukrah ta ɗauko sabulun wanki da omo ta fito,

Ta zo ta fara wankin bata dade ba ta gama saboda kayan babu datti a jiki ta shanya ta wanke bokitan da tai wanki ta koma ciki,

Taje ta aje su a inda ta ɗauko su ta ɗau wayarta ta koma parlour ta zauna.

Tana chart sai ga sallamar Aliyu kallo ɗaƴa tayi mai ta ɗauke idon ta bayan ta amsa sallamar,

Aliyu da sauri ya ƙariko ya zauna kusa da ita ya ce
" Haba madam irin wannan kwalliyar haka.

Kin manta yau monday ina da ayyuka da yawa Amina ta juya ido ta ce.
Allah ya kiyaye hanya ranka ya ɗaɗe mijin Amina
Aliyu ya ce
"Ai yau babu inda zani madam,
Amina tayi dariya ta ce
" dan Allah rufa mun asiri Aliyu ya ce"
Daman shekarun Darraini 4 tana buƙatar ƙani,
Amina ta ce" ai ni na gama haihuwa yanzu domin Darraini itace auta na Aliyu ya ce
" Zakiga auta.

Suna cikin hakan sai ga sallamar almajirin su mai suna Sani.
Amina ta

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment