You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Addini,

    Idan ya dawo gida da daddare bayan sallahr isha'i yana ɗaukan karatu gun mallam ,

    Yanzu haka Aliyu ya nada Shekara 26
babban burin mallam yaga Aliyu yayi Aure ya samu mace ta gari,
ƴar gidan mutunci ya aura,

  Naseer ya nada 23 umar kuma 19 shekarun su ɗaya da Isma'eel sai Fatima 16  sannan Auta Amina 13


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT



RAYUWAR MU

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Babu Rayuwar da Babu ƙalubale acikin ta 👌


Written by ✍️
SA'ADATU IBRAHIM FULANI
           ( Ta Batulu)


Page 5-6

Aliyu ne ya shigo gida bakin shi dauke da sallama,

Inna tana zaune a tsakar gidan ta amsa mai sallamar tana hararan Shi,

  Aliyu yayi kamar bai ganta ba yace mata sannu da aiki,

Inna tayi kamar bata jishi ba yana ganin hakan bai ƙara cema ta komai ba,

ya leƙa ɗakin Mama ya ganta a kan darduma tana jan charbi,
ya shigo ya zauna bakin shi ɗauke da sallama Fatima ta amsa,

      Tace sannu da zuwa Aliyu yace yauwa Auta ya aiki tace lafiya qalau ya kasuwa,
yace Alhamdulellahi daga nan taje ta kawo mai ruwa mai sanyi

  Aliyu ya ƙarba yace nagode,
  
Daga hakan bai ƙara cewa komai ba,
ya jingina da kujeran da yake zaune akai,

na karema ɗakin kallo yana dauke da saitin kujeru blue black da ratsin golden a tsakiya,

    Sai fridge mai ɗan girma, ɗakin yasha tayis fari ƙal yana ta ɗaukar ido,

Fatima akwai tsafta bata son kazanta,
  Kuma hakan ya samu ne da tarbiyan Mama,

Fatima ta leƙo tace ya Aliyu in kawo maka abinci yace a'a ba zanci yanzu ba,

Mama ta kalleshi bayan ta gama jan charbin,

Tace mai kaci da zaka ce ka ƙoshi Aliyu yayi shiru,

mama tace ma Fatima kawo mai abinci da ruwa,

bayan Fatima ta fita mama tace Aliyu ban san ko sai yaushe bane zan daina Maka faɗan cin abinci
,
  Aliyu ya sunkuyar da kai ƙasa yace kiya haƙuri mama,

Fatima ta shigo bakinta ɗauke da Sallama hannunta riƙe da plate tazo ta aje gaban Aliyu,
shinkafa ne da miya sai salat,

Fatima taje ta buɗe fridge ta ɗauko mai zoɓo mai sanyi a gora tazo ta aje,

  Aliyu ya sau koh ƙasa yayi bismillah yaf ara cin abincin yaci rabi yace ma Fatima ta ɗauke ya ƙoshi,

mama ta kalle Shi ta kaɗa kai bata ce komai ba,

  Fatima ta ɗauke plate ɗin ta fita mama ta kalli Aliyu tace,

Dama inna son magana dakai,
Aliyu yayi shiru Yana kallon Mama,
  Fatima ta shigo ganin kamar suna magana yasa bata zauna ba tashige ciki,

  Mama tace Aliyu koza kaje ka duba Yarinyar Alhaji Ibrahim ne idan tayi Maka sai ku dai dai ta,"?

Aliyu yace to Mama zanyi ƙoƙarin hakan in Sha allah,
ko zuwa gobe idan allah ya kaimu,

Mama tace masha allah ubangiji yayi maka albarka,

  Allah ya zaba maka mafi alkhairi,

  Aliyu ya aje mata ledar da ya shigo dashi ya tashi ya fita,

Yana fita Fatima tayi tsalle tafito dama jira take ya fita ta samu ta fito,

Fatima tace mama wallahi yaya Aliyu yayi sa'ar mata,
Amina bata da matsala gata da kunya allah yasa su dai dai ta,

Mama tace nima yarinyar tana burgeni,

Fatima tana ta murna Mama tana ta kallon ta bata ƙara ce mata komai ba,
Fatima ta janyo ledar da Aliyu ya a je ta bude kayan shayi ne a ciki

Mama tace ta dauka taje ta a je,

Bayan fitan Aliyu dakin mahaifinsu ya shiga,
ya same Shi Yana karatun ƙur'ani
   Aliyu ya zauna a ƙasa kusa da mahaifinsu wanda suke cema baffa,

Aliyu bai daɗe da zama ba mahaifin nasu ya rufe ƙur'anin ya kalle shi yace mai,
ya a kayi gadanga daman wasu lokutan haka yake cemai,

Aliyu ya gaishe da shi yace mai daman na dawo gida ne banji motsinka ba shine nace bara in duba a she kana ciki,"?

Baffa yayi murmushi yace gadanga babu wani matsala koh,?

Aliyu yayi murmushi yace ba komai baffa,

Sai baffa yayi murmushi irin nasu na manya, yace gadanga inna son ka riƙe abubuwa guda 4
Wanda ko bayan babu raina za kai alfahari da hakan,

Aliyu bai ce komai ba
baffa yaci gaba da magana yace gadanga,

Inna son kaji tsoran allah kaji tsoran zalunci ka guji addu'ar wanda aka zalunta,
kariƙe gaskiya a dukkan lamarin ka lallai Idan kariƙe waɗan nan abubuwan guda 4 zaka zauna lafiya,

Aliyu yayi murmushi yace nagode baffa allah yaƙara lafiya da nisan kwana,

in sha allah kuma zan ki yaye, baffa yayi murmushi yace ubangiji yayi muku albarka,
Kai da 6an uwanka allah yaƙara rufa muku Asiri duniya da lahira,

Aliyu ya duƙar da kan shi yace ameen baffa, 
suna cikin magana sai gashi an shigo zuruf haɗe da sallama,
ko basu duba ba sun san mai wannan halin,

inna ce ta shigo tazo ta zauna kusa da baffa ta ɗaure fuska Aliyu na ganin hakan ya mike,
yace ma baffa a tashi lafiya yafito daga dakin,


Ya shiga ɗakin su bakin shi ɗauke da sallama,
Ismael yana zaune a bakin kofa,

Yana ganin Aliyu ya daure fuska ya kau da kai,

  Aliyu yayi kamar bai gan shi ba ya shiga ɗakin Shi yana mamakin yan da kwatakwata Ismael bai da kunya yayi murmushi,

Yana tinanin irin punishment ɗin da zai bashi idan ya kama shi,
 
Yana shiga ya fito da bokiti yayi cikin gida ya na shiga ya ga Aminah a tsakar gidan yace mata,

Kije gurin Mama ta baki ruwan zafi ki kawo mun,

  Amina tazo zata karɓa tana tura baki,
tana zuwa kusa dashi ya bige bakin nata,

Ai ko K
Kamar jira take ta fara hawaye Aliyu yace mata wallahi Idan baki shanye wannan hawayen ba
sai nayi miki mugun duka,

Aliyu yace
baki da kunya Koh,"?

ni zan aikeki kina tura mun baki koh,"?
Amina tayi tsit domin ta san halin Aliyu baya son raini,
ta karbi bokitin ta shiga dakin mama bakin ta ɗauke dansallama ,

  Aliyu ya kada kai yana mamakin yanda,
Inna take lalata tarbiyan ƴaƴanta da kanta,

Kuma idan kayi musu faɗa tace ka zalunce su,

Yana tsaye sai gata tafito ita da Fatima sun shiga kitchen, yana ganin hakan yace ma Fatima tazo ta huce ta bashi guri,

Fatima tazo ta huce tana ƙunshe dariya,

Daman tana kallon su ta window har turo Amina amsar ruwa duk ta gani da abinda ya faru,

Aliyu ya maida kallon shi kan Amina dake tsaye tana kallon shi,
yace mata in zo ne in zuba ruwan da kaina,

Amina ba tace komai ba ta shiga ta ɗibo mai ruwan ta kawo mai ta aje,

Aliyu

yace mata ta ɗauka ta kai mai toilet,
 

Amina ba tace komai ba tazo ta ɗauka ta shiga parlour ɗin,
ta samu Ismael zaune a inda yake tin dazun, 

tana ganin shi ta watsa mai harara shi kuma ya hau mata dariya,
   Suna cikin hakan sai ga Aliyu ya shigo Yy kalli Ismael ya daure yuska yace mai,

  tashi ka wanke mun toilet yanzu,
ya kalli Amina yace ke kuma shigo mun da ruwan ki share mun parlour nan,

a tare Amina Da Ismael suka kalli juna kafin kowa ya kama kanshi,

Domin sun san abu kaɗan za suyi ya basu punishment din da har a kwana biyu suna jinshi,

Amina tabi bayan Aliyu da ya shiga ɗaki Ismael kuma ya dau bokiti yayi cikin gida,

Amina ta na shiga ta samu Aliyu zaune a saman katifa ya na danna waya,

tazo ta aje ruwan a bakin kofa ta fita,
ta dau tsintsiya ta fara shara ta nayi tana surutai,
ta na gamawa sai ga Ismael ya shigo da bokiti cike da ruwa,

Yana zuwa ya shige dashi toilet ya fito ya shiga dakin su ya dauko omo da wani ruwa a gora,

Ya koma bayin 10 minutes ya gama ya fito ya mai da kayan ɗkin su,

Ya shiga ɗakin Aliyu da sallama ya ga Amina a tsaye,
Ismael yace mai yaya na gama ,

Aliyu yayi kamar baiji shi ba,  Ismael ya kalli Amina ya harareta ita ma ta rama,

Aliyu ya tashi ya dau kayan wankan shi da ruwan zafin ya fita yaje parlourn su ya surka,
Daman su nada roban ruwa a cikin parlourn ya shiga wanka abin shi,

Bai jima da shiga ba sai ga Fatima ta shigo da sallama ta shiga ɗakin yayan nasu,
taga Amina da Ismael a tsaye tace musu dan allah ya Aliyu yana nan su kayi banza da ita,

Fatima tana ganin hakan ta kwashe musu da dariya tace,
Yau layi ya biyo ta kan ku,

tana cikin dariyar taji motsin bude ƙofar toilet,
ai ko tayi tsitt kamar wanda ruwa ya cinye,

Aliyu ne ya shigo da sallama suka amsa dukan su,

Duk da yaga Fatima amman yayi kamar bai ganta ba,
ya huce saman mirror ya ɗauko man shafawa yazo ya aje ya nemi guri ya zauna,
Ya dauko wayar shi yana dannawa,

Fatima ta matsa kusa da Aliyu tace Mai, ya Aliyu dan allah zanje gidan su Nusaiba na tambayi mama tace mun babu ruwanta,

Aliyu ko ɗaga kai baiyi ba ballatana tasa ran zai bata amsa,

Amina ta hau murmushi tana yima Fatima gwalo Aliyu na kallonta,
Shi koh Ismael tinda yaga hakan ya aro natsuwa ya yafa ma kanshi,

Aliyu ya kira Nasser a waya yace mai idan zai dawo gida ya tsaya ya amso mai form guda 4 Na islamiyyar ƙasan layinsu,

Fatima najin hakan ta fara tinanin zuci tace nasan wannan form din namu ne bana kowa ba,
kuma nasan su Amina da Ismael sukaja mana,

Aliyu yace ma Fatima ta fita ta bashi guri ba za taje ba kuma zaiyi maganin yawonta,

ai kafin ma ya gama rufe baki Flfitt ta fice a ɗakin daman neman hanyar guduwa takeyi,

Aliyu ya kalli Amina yace mata zamu haɗu dake,
sai nayi maganin ki,

Amina najin hakan ta fara kuka ta na bashi haƙuri,
Aliyu yace ta fita ta bashi guri zai shigo gidan ya sameta
da gudu tabar ɗakin,

Aliyu ya kalli Ismael da yayi fuskan tausayi yace mai,
ka sameni anjjma bayan sallahr la'asar,
Ismael yace to
shima yayi waje yana sauke numfashi,

Yana fita yace wallahi unguwar ma zan bari gaba ɗaya,
ba gidan ba kuma sai kayi bacci zan dawo,

   Aliyu ya gama shafa man ya samu kaya ma rasu nauyi ya sa ya koma ya kwanta ya rufe Ido,
Daga hakan bacci ya ɗauke shi,

  Sai bayan la'asar ya tashi shima kiran waya ne ya tayar dashi, 
Yana tashi ya duba lokaci yaga lokacin ya ƙure,

Ya tashi a gurguje yaje yayi alwala yazo yayi Sallah,

Koda ya idar bai tashi ba ya daukoh ƙur'ani ya fara karan tawa cike da ƙwarewa
ga muryan shi mai daɗin sauraro,

Aliyu matashine mai cike da haiba da kwarjini ,
mahaifiyar shi ba fullatana ce ta asali domin danginta duk suna ruga,
Aliyu dogo ne mara ƙiba amman ba siriri bane Yana da fadin kirji,
ga manyan idanu ga hanci har baka fuskan shi dai dai,

Masha allah duk cikin su Aliyu yafi su haske,

   Ya jima yana karatu kafin ya mike ya aje ƙur'anin ya fita ya shiga cikin gida,

Yana shiga yaji hayaniya a ɗakin Mama


Ta Batulu ✍️


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT

RAYUWAR MU


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Written by ✍️

SA'ADATU I FULANI
( Ta Batulu🥰)

Haquri mai cimma rabo 🥰
Dukanin abinda haƙuri bai baka shiba rashinsa ma bazai taɓa baka,

Page 7-8

Shima ɗakin ya shiga da sallama yana shiga,

ya ga Nasser ne tare da umar da Fatima sun sa Mama a tsakiya a nata fira,

Nasser yana ganin Aliyu yace mai bro har ka tashi,"?

Nasser yace ai na shigo na samu kana bacci,

Aliyu yayi murmushi yace eh na tashi,
Daman gajiya ce kawai,

Umar yace barka da wannan lokacin ya haydar,

Aliyu yayi murmushi ya kamo shi ya rungume yace barka dai ƙanin yayan Shi ,

Daman wani lokacin hakan suke cema juna,

Aliyu ya kalli Nasser tin kafin yayi magana Nasser yace ma umar,
jeka dau koh mun jakar da na shigo da shi,

Aliyu ya zauna kusa da Fatima da tayi shiru tinda taga shigowa warshi yace mata ya dai teemah,"?

itama haka yake cema ta wani  lokacin,

Fatima tayi murmushi bata ce komai ba,

mama tace ma Aliyu ba dole tayi shiru ba zaki yazo gurin,

Nasser yace ai shine dai dai dasu,
a gidan nan shi dai Aliyu bai ce komai ba,

sai ga umar ya shigo da sallama ya mika ma Aliyu jakan,

Nasser Ya taso ya karba ya bude ya ciro baƙin leda ya miƙa ma Aliyu, 

Umar yaje ya ciro ruwa mai sanyi ya ɗauko kofi ya jawo teburin dake gaban Nasser,

Ya ɗaura ruwan akai ya aje a gaban Aliyu Nasser yace to sarkin iyayi,
umar yayi dariya ya zauna kusa da Aliyu,

Fatima ta tashi zata shiga ciki Aliyu yace ta koma ta zauna,

Aliyu ya fito da form din nan duka yaba Nasser ɗaya yaba umar ɗaya itama fatiman ya bata ɗaya Slshima ya dau daya yace duk su cike mai,

Ya kalli Nasser yace mai Amina zaka cike mawa,
shi kuma umar yace nashi ne,

tin kafin yace ma Fatima daman ta san nata ne,

Aliyu yace ma Fatima ke kuma fa daga baki abu har kin fara rubutu baki tsaya kinji jawabi ba,"?

Fatima tayi dariya tace ai na san nawa ne shiyasa,

Aliyu baice komai ba ya mai da hankali akan form din gaban shi ya cike ma Ismael,

ita dai Mama tana zaune tana kallon su cike da sha'awar yanda suke kulawa da junan su tana musu addu'ar su ɗore a hakan,


  Bayan sun gama cikewa Aliyu ya kalli Fatima yace tinda naga kun kusa gama makaranta zaku fara zuwa islamiyya ranar monday,

zan bawa Nasser kudi ya yanko muku uniform Sai a bada ɗinki umar yace yaya har dani,"?
 

Aliyu ya kalli umar yace mai ko ka girmi karatun ne,"?

Nasser ya kwashe da dariya umar ya ɓata fuska yace mai a'a,

Aliyu yace dukan ku zaku koma babu wanda na ware a cikin ku,"

Ya kalli Mama yace baki ce komai ba,
mama tayi murmushi tace mai zance,"?

Bayan kayi komai yanda ya dace,
ubangiji yayi muku albarka,

Dukan su suka amsa da ameen,
Aliyu ya ɗauki ruwan da umar ya aje mai,
yasha ya tashi yayi ma mama sallama ya fita,

Yana fita umar yaje kusa da mama yace,

Wai da girma na za a kaini makaranta kamar wani yaro,

Nasser yace wato ita ka raina koh, "?

Naseer yace shi wanda yayi maganar ka kasa faɗa a gabanshi,

Fatima tayi dariya tace ƙyale shi ya Nasser kamar a kunnen ya Aliyu,

umar yace to munafuka sai kin dawo,

Nasser ya kallesu dukan su yace musu kun San menene,"?

suka ce mai a'a yace musu wlh bro gata yayi muku,

Nasser yace
yanzu kai umar ka gama makaranta kayi candy
wannan shekaran,

mai ya rage Maka,"?

  Umar ya hau washe baki yace saura jami'a Fatima tace ai shi mafarkin Shi kenan,

Nasser ya cigaba da cewa, amman ka san ba kai tsaye bro zai barka ka tafi jami'a ba,"?

Umar yayi shiru sai Nasser ya cigaba da cewa ni dai shawaran da zan baka,

itace karka nuna mai baka son wannan makarantar domin kuwa,

Idan kuma ka nuna mai baka so ka san abinda zai biyo baya,

Nasser

Ya kalli Fatima yace kefa,"?

Fatima tace ni wallahi banda zaɓi Nasser yace kin huta ma kanki shima ya tashi yayi ma mama sallama ya fita, 

Umar ya kalli Fatima yace mata wallahi Ismael nake tausayawa domin na san baza su kwashe ta daɗin rai ba shida ya haydar,

Fatima tayi dariya ta bashi labarin abinda ya faru ɗazun,

Shima dariyan yayi yace kice anjima akwai kallo,"?

Fatima tace ai dukan su har yanzu basu san halin ya Aliyu ba,

umar yace na tina wani mari da ya taɓa mun sai da na suma,

Fatima tayi dariya Mama ita kanta sai da ta dara,

Fatima tace ni dai karka ƙullar mun da ciki bari in ɗauko Assignment ɗina Dan allah, 

Fatima tashiga ciki ta fito da jaka tazo ta aje a gaban shi tace mai ya koya mata ne,

  Fatima tana da wani ɗabi'a guda ɗaya,
ita ko abune bata iya ba bata cewa ayi mata,

Sai dai tace a koya mata saboda gaba,

Umar ya sau koh ƙasa ya zauna itama ta zauna a kusa dashi ta bude littafin ta suka fara,

Fatima tana SS two ne going to three ita kuma Amina JSS one
Ismael kuma tare suka zana jarabawa da umar,

Duk da shi zana mai a kayi umar kuma yace yafi son ya zana da kanshi,

Nasser kuma Degree yake ɗaurawa a cikin garin Jos,

Yana karantar fannin lafiya ne sannan ya iya gyaran wayoyi,

Yana zama a shagon abokin shi idan ya dawo makaranta,

Shi kuma umar shagon ɗinki yasa Aliyu ya kai shi yana koyan ɗinkin keke na maza,

Bayan sun gama Assignment din umar ya tashi yace ma Mama bari yaje shagon su ya dawo,

Mama tace yamma yayi magariba a ke shirin kira,

umar yace mata ba zama zaiyi ba yanzu zai dawo
Mama tace mai a dawo lafiya,

Fatima ta kwashe jakanta da kuma form ɗin da suka bari a parlourn ta shiga dasu ciki,

ta zuba su a cikin jakan ta na makaranta ta shiga bayi tayi alwala tadau Qur'an ta fito parlour tazo ta zauna kusa da mama,

A saman darduma irin darduman nanne mai faɗi da taushi,

Mama ta tashi ta shiga ciki Fatima kuma ta fara karatu cike da natsuwa, 

Fatima bata da tsawo kamar ƴan uwanta sannan kuma tana da jiki ga diri masha allah,

itama tana da hanci

Daman duk ƴan dakin Mama suna da hanci,

kuma itama mama bata da tsawo kamar dai Fatima,

Amman dukan su suna kama da juna,

Bata jima da fara karatun ba aka kira sallah ta rufe Qur'anin,

ta tashi sai ga Mama ta fito daga bedroom, tazo ta hau darduman suka bi jam'i,

Bayan an idar Fatima ta kwaso littafan ta na addini tazo Mama tana mata bita,

Sun jima a hakan kafin Fatima ta mayar da littafan tazo ta fara azkar,

  Bayan ta idar ta ɗauko chasbi ta naja har aka kira sallahr Isha'i,

Bayan sun idar da sallah sukayi nafila sannan Fatima ta tashi taje kitchen,

Tana zuwa ta samu Amina zata shiga ɗauko abincin baffa,
Fatima tana ganin Amina ta bata guri ta huce,

itama ta shiga ta ɗauko abincin su ta koma ɗaki,

tana shiga umar na shigowa shida Nasser,

suka gaida Mama suka zauna Fatima ta koma kitchen ta kwaso plate da spoon takoma,

Bayan ta kai sai ta shiga bedroom tana shiga umar ya mike yana cewa daɗin abun dai muna da hannu,

Mama da take gefe tayi murmushi Nasser kuma yace to acici mala'ikun tauna,

Fatima dake fitowa tayi dariya tace wallahi kuma sunan ya dace dashi, 

umar bai tanka musu ba ya bude kular abincin,

shinkafa ne jallop na manja da wake,
ya zuba a plate ya koma ya zauna Fatima na ganin hakan ta bude fridge ta ɗauko zobo da ruwa tazo ta aje musu,

Umar yace kinyi taimako domin bana gane baƙin karatun shiyasa ban tsaya nai man ruwa ba,

Fatima ta kalli Nasser tace in zuba maka abincin,"?

Nasser yace a'a bari bro ya shigo daman tayi tinanin hakan,

indai suna gida basu cika cin abinci ba tare ba,

tazo ta ɗiba ta koma kusa da mama ta zauna ta faraci bayan tayi bismillahi

bata ci da yawa ba ta tashi ta shiga ciki sai gata da roban yaji,

umar na ganin hakan yace daman tin ɗazun nake tinanin inda zan samu yaji,

Dukan su suka mai dariya saboda tinda ya fara cin abinci baiyi magana ba,

Fatima ta ɗiba ta aje Mai roban yajin a gaban shi,

mama tace ma Fatima idan kin gama ki ɗaura mun Lipton,

Fatima tace ai muna dashi a cikin plask,

mama tace to gama ki ɗauko mun,

suna cikin hakan Aliyu yayi sallama ya shigo hannun shi riƙe da baƙar leda,

Yana zuwa ya miƙa ma Fatima

Ya gaida mama ya zauna kusa da Nasser suka gaisa,

umar kam sai da ya gama cin abinci,

Sannan yace sannu da dawowa,

Aliyu yayi murmushi yace an gaishe da acicin gidan mu,

Umar yace kuma banci da yawa ba,

Domin nasan zaka dawo mana da tsaraba,

Fatima da take shigowa ɗakin tace wallahi kaji tsoran allah ya umar duk irin abincin da kaci,"?

Umar ya kalleta yace to inna ruwanki dani,

Nasser yace haba Fatima ya zaki tona mai asiri,

Mama tayi dariya tace karku tasa mun ƴa a gaba,

Fatima ta zauna bayan ta shigo da babban plate ta juye abinda Aliyu ya shigo dashi,

Nama ne mai yawa sai ƙamshi yake tashi,

Mama tace ma Fatima ta diban ma Inna takai mata,

Fatima ta ɗau plate guda ɗaya a cikin wanda  ta kwaso domin suci abinci ta ɗibo naman aciki ta fito,

ta shiga ɗakin Inna bakin ta ɗauke da sallama ,

Inna ta amsa sallamar ta ɗauke kai Fatima tace barka da dare Inna gashi inji mama tsaraban ya Aliyu,

Inna tace to aje kice angode Fatima ta fita daga ɗakin,

tana fita Amina ta sauko da sauri tazo ta bude plate ɗin taga nama ne,
aciki Inna tace Mai kike shirin yi,"?

  Amina tasa hannu ta faraci tai banza da  Inna,

  tana cikin cin namar saiga Ismael ya shigo babu sallama baice musu Komai ba,

ya zauna kusa da Amina shima ya fara cin namar,

Ta Batulu ce🥰✍️



Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6o




💖💖RAYUWAR MU💖💖


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



Written by ✍️

SA'ADATU I FULANI 
   (Ta Batulu🥰)

Page 9-10

Inna ta kalle su tace amman baku da zuciya,

Babu wanda ya kalle ta acikin su,
bayan sun gama cin namar,

Ismael yace Amina ta zuba mai abinci,

Amina ta ɓata fuska,

Inna ta kalli Amina tace bakiji ana magana ba,"?

Amina ta tashi ta fita tana turo baki,

Ismael ya kalli Inna,

yace mata wallahi wata rana sai na karya wannan yarinyar gaba ɗaya ta raina mutane,

Inna tace ma Ismael ka dinga haƙuri dan allah koba ka ganin ita yarinya ne,"?

Inna taci gaba da cewa,

Ismael kaine babba dan allah kaja girmanka,

Amina ta shigo tana tura baki,
ta aje mai abincin gabanshi tashige Bedroom ɗin su,
 
Shima ɗakin irin na Mama ne komai da komai sai dai ya nayin kayan ɗakin,

wannan ɗakin duk yayi ƙura kamar babu masu rayuwa aciki ,

Domin Inna akwai ƙazanta kuma ta koya ma ƴarta,

Tarbiyya ana koya ne daga uwa ba daga uba ba
Domin na uba da ban naki da ban,
Duk yanda kike yi a gidan mijinki itama ƴarki haka za tayi a gidan nata mijin,
ubangiji ka datar damu, allah ka haɗamu da iyaye na gari,🙏
  

Inna ta kalli Ismael da yake cin abinci,
tace mai ya maganar makaranta, nifa nagaji da ganinka hakan,
bokon baka mayar da hankali ba islamiyyar ma hakan,
gashi kowa yana zuwa gurin sana'a amman banda kai,

Ismael yace mata nifa bana son wahala ne shiyasa,
kuma ni nagama makaranta sana'a kuma inna tinanin wanda zai dace dani ne,
Inna ki daina damun kanki a kaina,

  Yana gama fada mata hakan yayi waje Inna tace zaka dawo ka same ni,

Ɗakin Mama bayan sun gama cin abinci mama ta kalli Aliyu tace karka manta da maganar mu ta ɗazun Aliyu yace mata ban manta ba,

  Suka taɓa fira da ƴan uwan shi yana jadadda musu maganar tafiyansu islamiyya babu fashi su zauna cikin shiri,

  Yayi musu sallama ya fita yana fita Naseer shima yayi musu sallama ya fita ,

Aliyu ɗaki ya shiga yaje ya ƙara shirya wa ya fita,

Mama tace ma umar ya duba mata ɗakin baffan su idan yana nan,

Umar na fita yaga Inna tana tsaye a bayan windows din ɗakin su,

 

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment