You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shinfiɗa a shekara guda kacal.
      A ɓangare. su Alhaji Yaro glass sunyi zaman meeting akan cikin nan, inda kai tsaye suka ƙalubalanci Aunty Hannah data ɓoye musu hakan. Ta nuna batasan Raudha nada ciki ba itama, amma hakan bashike nuna batai murnaba. Dan ita tanada manufa akan cikin koba komai zasu kasance da wani kaso na dukiyar Taura family musamman idan aka dace Raudha ta haifo namiji.
    Wannan magana tata ta banƙanta ran su Alhaji Yaro glass, harya faraji a ransa Aunty Hannah bazatai dogon zangoba zai kawar da ita. Dan ya tabbatar shi ɗinma zata iya yin kalar tunanin da take furtawa akan dukiyar Taura family akansa kenan. Duk da kuwa Samha ce kawai a tsakaninsu har yanzun.
     To komadai miye, mudai ƴan kallone ai.🤣

Kwanaki biyu da yin wannan biki na cikar masu mulki shekara ɗaya akan madafun iko Malam Dauda ya koma hutawa da shatara ta arziƙi. Dan kuwa kujerar makka har uku, tare da kuɗi masu yawa da galleliyar mota da alƙawarin buɗe masa manyan shaguna a hutawa da kuɗi zasu dinga shigo masa akoda yaushe. Wannan farin ciki ya sashi danne son Asabe daya san har Abada bazai iya dainawaba.
        A randa M. Dauda yabar Bingo a ranar hoton wani video ya karaɗe yanar gizo da duk mai wayar da take iya buɗe data zai gani. Video ne daya kasance na Aynah a cikin club ana aikata masha'a da ita. Sai kuma wani shima a cikin ɗaki kusan su biyar duk mata. Abinda zai baka mamaki na club ɗin babu face mask kamar yanda Ramadhan ya sani.
      Aminu ya saki wannan video ne bayan ya saka dukan abokansa sunyi amfani da Aynah a wannan dare wasuma harta baya (Wa'iyazubillah😭) yayi hakane a dalilin kawo mata ƴammatansa da yay gidan ta nuna itafa ta gaji ya sallameta hakanan kokuma ta tona masa asiri ga iyayensa da yake yaudarar nuna musu shi ɗin mutumin kirkine. Shiko ya tabbatar mata kafin tayi hakan shi zai fara tona nata a sirin wa duniya sai yaga nata da nashi wannene zaifi gawurta da kayatarwa. Tayi kuka ta roƙesa iyakar roƙo amma yay kunnen uwar shegu da ita sai da ya saki.
      A lokacin da wannan video ya riski su Addah Asmah data haukata kanta a neman asirin hallaka Ramadhan da wulƙanta rayuwarsa data Gimbiya Su'adah har ƙasar China ta yanke jiki ta faɗi. Kwannta biyu kenan da dawowarta NAYA, wata kawarta ta rakata China wajen wani gagarumin masanin tsafi. Sun dawo zuciyarta cike da jin ɗunbin nasara saboda abinda matsafin ya haɗo musu, ta tabbatar idan har tai amfani da su Gimbiya Su'adah da zuri'arta sun zama labari kenan. Sai gashi a yau da take shirin zuwa Taura house da fuskar yaudarar roƙon gafarar gimbiya Su'adah danta aiwatar da aikinta wannan mummunan labari ya  baje ƙasar NAYA dama duniya tunda abune na media ako ina zaka iya ganinsa.
     A firgice ma'aikatan gidan nasu da kanwar Aynah suka rufu a kanta sai dai babu alamar numfashi tattare da ita. Dole Zulfah tai kiran asibitin da suke ganin likita dan ta nema no na daddyn su ma bata samuba kasancewar shi bayama kasar.
     

          Hatta da gimbiya Su'adah da ayanzu babu wanda ta tsana a duniya sama da ƴar uwar tata abin ya firgitata, balle kuma Fulani da itama ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a sume dalilin tanada hawan jini.
     Raudha ma ta gani kafin Ramadhan, amma ta kasa nuna masa sai zama datai taita kuka dan abun ya ɗaga hankalinta. Musulma ɗiyar muslmai gaba da baya itace a wannan halin duniya ke gani babu ko kunyar mahaliccinmu. Kaicon wata wayewar, kaicon wata dukiyar, kaicon wata damar dan da wata BAƘAR INUWA ce da ita gara rana ma.
      Koda Ramadhan ɗin shima ya gani baiji abin saboba tunda a gabansa aka aikata, sai dai abinda ya bashi mamaki fitar videon bayan shekaru. Hakan na nufin dan kinyi barna ko kayi ka binneta da tunanin ta wuce mutane bazasu ganiba watarana UBANGIJI idan yaso sai ya tonota ta hanyar da kai bakai tunani ko tsammani ba. Sannan ya jiraka a madakata kazo ya hukuntaka dai-dai da laifinka dan shi bai kasance azzalumin sarki ba...........✍


*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*



*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*


*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_



Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*


*KATIN MTN*👇👇

09166221261
__________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*



Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F


*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77



*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________


*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*


Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


*_Typing📲_*







*_Episode 74_*


..........Faɗuwar Addah Asmah ta jawo mata shanyewar ɓarin jiki, yayinda lokacin da Aminu ya kawo Aynah har gida da takardar saki uku bayan dukan daya lakaɗa mata ya sake ruɗar da jikin na Adda Asmah har sai da takai Zulfah ta kira gimbiya Su'adah tana kuka akan tazo ta taimakesu Mom ɗinsu zata mutu.
     Jini ba wasa bane, dan duk yanda gimbiya Su'adah taso ignoring al'amari ya gagara gareta, har hawaye tayi itama ganin video na Aynah hawan jininta ya nema tashi. Tanda halayen banza ta wani fanin, amma tanada zuciya mai ƙyau kuma. Dama can zugar Addah Asmah ɗin ce da fulani ke sake kangarar da ita wani lokacin. Haka ta shirya Safina na roƙonta kartaje dan ALLAH Mardiyya tace danmi? Ita rayuwa ai ba'a maida sharri da sharri. Koba komai ai ALLAH ya nunama Adda Asmah ita ba komai bace ba, sannan duk makircinta a karƙashin hukuncin ƙaddara da jarabawa yake. Idan Maah taje gareta a yanzu Ai sake tabbatar mata zakaran da ALLAH ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi ne. Sannan babu hanun daya isa canja ƙaddarar ALLAH sai dai kai wahalarka ka ƙare a wahale wanda kakeyi dominsa yana ƙara zama sama da kai.
     Da wannan zantuka na Mardiyya suka ɗunguma gidan Addah Asmah, inda suka isketa ita kwance Aynah kwance cikin jini na dukan da taci hanun Aminu. Da taimakonsu aka wuce da su asibiti, a kuma daren mai-martaba da fulani suka iso suma. Sunji daɗin ganin Su'adah da yaranta a wajen, suka shiga sanya musu albarka. A daren shima Daddyn Aynah ya iso, bai kumayi zaman ɓata lokaci ba akai shirin fita da su waje dan jikunan nasu su duka yayi tsamari sosai.
      Da Fulani suka tafi, gimbiya Su'adah tai kememe tace babu inda zataje hakama ƴaƴanta. Babu wanda yaga laifinta anan, dan ansan an cutar da ita...

___________________________

         Wannan hatsaniya na cigaba da yaɗuwa cikin Raudha na ƙara girma. Komai nata ya canja, idan kaganta sai kace ba ita bace. Auren su Fatisa hanata zuwa hutawa Ramadhan yayi, iyakarta nan Bingo sabon gidan Mummynsu da yake anan akai yinin biki kamar yanda Alhaji Sageer Dogarai ya roƙa. Anyi yinin biki laraba Raudah ma a kwance ta yini da zazzaɓi, amma dan jaraba tana a gidan ɓoye. Da dare Alhaji Sageer Dogarai da kansa ya maidata government house duk da kuwa anzo daukarta, kuma dama tana tare da guards nata. Ba kowa yasan Raudha na gidan ba ƴan biki, sai da zata wuce gida. Aiko abin ya bama kowa mamaki kodan yanda Aunty Hannah tazo ita tana baza mulki kaikace itace matar shugaban ƙasar ma. Washe gari Alhamis ƴan biki suka ɗunguma Hutawa, inda akai musu tarba ta mutunci dan yanzu M. Dauda Alhmdllhi, duk da dai ginin shagunansa ko muce super market bai gama kammaluwa ba har yanzun. Amm kuɗaɗen daya samu ba ƙaramin barje guminsa yake ba. Kujerar makka kuwa ya rike sirrin a ransa shi da Inna da Baba Nafi zasu.
      Ranar Juma'a aka daura auren su Fatisa da mazajensu. Auren daya bada mamaki kasancewar shugaban ƙasa Ramadhan ya halarta tare da wasu gwamnoni da ministers. Hakama Alhaji Hameed Taura da Alhaji Basheer Hameed Taura. Ga Alhaji Sageer Dogarai da tasa tawagar dan a cewarsa su Fatisa shima ƴaƴansa ne. Saboda Asabe ta riƙe masa nasa da amana, duk da kalubalen data ɗan fuskanta ga yaran a farkon auren, sai dai halin kirki data dinga nuna musu da nuna rashin damuwa da abinda suke matan ita da Yasmin sai suma suka risina suka bata haƙuri ta haɗa ta rungume ta zame musu uwa.

     Sam Raudha bata san Ramadhan zaije ɗaurin auren ba sai gani tai alabarai da aka nuna dalilin zuwansa wajen. Jitai fushin da take da shi ya kwaranye. Dan tunda yace bazatajeba take haushi da shi, ta kama matsar kwalla Basma na lallaahinta. Koda ya dawo gidan bayan la'asar kasancewar a helicopter yaje ya dawo saita rungumesa tana kuka da jera masa tagwayen godiya.
     Murmushi yay kawai ya kama hanunta suka shige ɗakinsa. Ya zauna akan sofa tare da ɗoraya bisa cinyarsa duk da ƙaton cikinta bai damu ba.
       Sai da ya ɗan sumbaci lips nata yake faɗin, “Partner yanzu kin lalace wlhy, komai kuka komai fushi kamar ba Ustazah ɗina mai haƙuri da juriya ba. Anya kuwa ranar shiga labour room ba akwai aiki gagarumi a gabana ba?”.
         Kwanciya tai jikinsa tana murmushi da hawaye. “ALLAH Noorullah dan baka san wahalar bane. Cikin nan ya isheni ji nake kamar na cire na huta”.
     Murmushi yayi mai kayatarwa, ya ɗaura hanunsa a saman cikin nata yana shafawa. “Kiyi haƙuri jarumata saura ƙiris insha ALLAHU. Kedai kawai mu cigaba da addu'a ALLAH ya saukeki lafiya ok”.
     Kanta ta ɗaga masa da sumbatar kumatunsa. Kafin tace, “Shine ka tafi Hutawa ɗaurin aure koma ka sanar min”.
       “Hhh haba ƙawata, ina sanar miki rigima zaki sakamin da shagwaɓa, ni banjeba ke bakije ba”.
     “To amma tunda kasan zaka basai kaje dani ba da an ɗaura auren sai mu dawo tare”.
          “Ke ɗin ce zaki yarda muje mu dawo a ƙanƙanin lokacin nan. Yi haƙuri ai dakin haihu insha ALLAH zakije ki kai musu baby su gani. Kimma san ya mukai da Anne?”.
      “A'a”.
Ta faɗa tana girgiza masa kai.
      “Wai Taura house zaki koma da zama har ki haihu yaro yay ƙwari. Cikin farin ciki ta miƙe zaune sosai a jikinsa. “Kai amma naji daɗi ALLAH, koba ko....”
    Baima bari ta ƙarasa ba ya mangare mata kai yana hararta. “Oh kinmaji daɗi kenan. To ai a take nace mata ban yardaba sai dai ita ta dawo nan”.
     Baki ta tura masa gaba. “ALLAH wannan buƙulune kawai zakamin”.
   Dariya ya ƙyalƙyale da shi mai kayatarwa. “Naji gara hakan, nida aka shirya yima buƙulun barina gaurofa. Muna nan tare ki haihu muyi rainon babynmu kamar yanda mukai na cikin”.
       “Uhmm kaji wai mukayi, nadaiyi abina”.
    Gira ya ɗage sama, yana mai kai bakinsa saitin kunenta. “To amma wake ƙarama babyn ƙarfi bani ba”.
    Kansa ta ture da sauri tana ƙoƙarin tashi ya hanata. Haka ya cigaba da tsokanarta yana kunnata tana masa shagwaɓa. Daga ƙarshe suka koma gado sannan sukai wanka tare kamar yanda suka sabarma kansu a yanzu musamman irin wannan wankan na lada.
           Kamar koda yaushe langyare masa tai, dan ba karamin jigata take ba a duk sanda hakan ta faru, sai takai ya mata tausa da lallaɓata tayi barci ake rabuwa lafiya. Yanzun ma bayan tayi barcin fita yay zuwa dinig yayi lunch dan yunwa yakeji sosai.

    

*____________________________*

        A kwana a tashi babu wuya wajen UBANGIJI. Raudha ta cigaba da rainon cikinta cikin kulawar ALLAH da Ramadhan, duk da nauyin Al'umma dake a kansa yana iyakar ƙoƙarinsa gareta itama. Ga gimbiya Su'adah kadaran kadahan tsakaninsu, ba gallazawa babu nuna damuwa. Dan ko Taura House taje zata gaisheta ta amsa ba kamar da ba sai dai iyakar gaisuwarce. Bazata kulataba bazata kuma hantareta ba. Hakama tsakaninta da Aunty Hannah, takan leƙo gidan lokaci-lokaci su gaisa, wani lokacin da mutanenta ƴan siyasa, wani lokacin ita kaɗai sai guards nata. Sau uku tana zuwa gidan Mummynta Asabe. Hakama gidan su Bilkisu dake nan Bingo duk taje. Su Fatisa ne dai har yanzu bata leƙaba saboda ba'anan Bingo suke ba.
      A haka cikinta ya shiga watan haihuwa raki da shagwaɓa ya ƙaru, dole kuma Aunty Zuhrah ɗiyar Yafendo ta dawo nan government House da zama dan Anne dai taƙi hakan duk da kuwa Ramadhan jikane. Tunda watan ya shiga kwanakin haihuwa ta daina zuwa makaranta, sai ta dai su Basma suzo su mata bayanin abinda akayi. Randa takejinta da lafiya ta fahimta, saɓanin hakan tace su barta karatunma baza'ayiba. Sukan mata dariya da tausayinta. Dan hatta uban gayyar idan ta birkice masa da rikici dariyarsa yake kwasa kafin ya koma lallashinta a shirya da ƙyar.
        Tun dai ana saka ran haihuwar har kwanakin da aka bata a sibiti suka gota, koda Ramadhan ya nuna damuwarsa Dr Hauwa tace karya damu ana samun irin hakan ai ba komai bane. Adai cigaba da mata addu'ar sauka lafiya ..........✍


*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*



*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*


*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_



Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*


*KATIN MTN*👇👇

09166221261
__________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*



Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F


*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77



*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________


*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*


Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
     

*_Typing📲_*







*_Episode 75_*


...........Alhmdllhi a wani dare na juma'a da yay dai-dai da cikarta watanni goma cif ta farka da gigitacciyar naƙuda. Rikicewa Ramadhan yayi, da ƙyar ya iya control ɗin kansa ya saka jallabiya sannan ya fito kiran Aunty Zuhrah. Da taimakonta suka ɗauki Raudha zuwa clinic ɗin gidan, yayinda tuni su Basma sun sanar ma Anne. Babu bata lokaci a daren Anne da Dr Hauwa suka nufo gidan, inda suka samu har wata Dr ta shiga da ita ɗakin haihuwar. Babu ɓata lokaci Momyn Jafar ta rufa musu baya itama, aiko ta tarar Dr Ingoze na niyyar halaka yaro dama uwar. wata irin muguwar bangaza takai mata tare da sauke mata tagwayen maruka, daga haka ta hankaɗota waje ta koma kan Raudha.
    Kowa yayi mamakin yanda aka hankaɗo Dr Ingoze waje. Gashi Dr Hauwa tace security su rike mata ita har saita fito. Hakan kuwa akai zuciyar su Anne fal wasuwasi. Dama shi Ramadhan suna kawota ya koma ciki kamar yanda Aunty Zuhrah ta bashi umarni. Maimakon zama sai yay alwala ya fara nafilfili da nemawa matarsa sauƙin naƙuda da fatan sauka lafiya.
     Tabbas Dr ingoze tama Raudha lahani, sai dai cikin amincin ALLAH an samu damar ciro jaririn ta hanyar theatre kamar yanda Dr Hauwa ta yanke shawara. Dan ƙarfin Raudha ya nema karewa saboda yanda Dr ingoze ta dinga danna kan yaron yana ƙoƙarin fitowa kafin zuwa Momyn Jafar.
      Sai gabanin asuba suka fito, anci nasarar ciro santalelen yaro gashi ƙato alamar uwarsa taci ta ƙoshi. Sai dai babu damar ganin Raudha har sai ta samu isashen hutu kamar yanda Dr Hauwa tace. Atake murna ta gauraye gidan na gwamnati, kowa kuma nama Raudha fatan samun lafiya. Lokacin da jariri yaje hanun uban gayya Ramadhan hawaye yaji sun cika masa ido. Ya sumbacesa tare da rungume abinsa yana maijin kaunarsa na ratsashi. Wannan shine karo na biyu da ALLAH yay masa ƙyautar da kuɗi basa badata, hakama mulki da ɗaukaka. Ya bukaci ganin Raudha duk da Dr Hauwa taso dakatar dashi ya bata haƙuri, dole aka ƙyalesa ya shiga shi kaɗai ya dubata. Tausayinta ya kamashi, ya dinga jera mata tagwayen kiss's da addu'oi.

     Zuwa wayewar gari labari ya karaɗe lungu da sako na ƙasar NAYA akan shugaban ƙasa ya samu ƙaruwa. Ga hoton Baby nata yawo saboda su Basma da sukaita turawa ƴan uwa da abokan arziki. Sai yazam kowa ƙoƙarin ɗorawa yake a shafinsa, wasu idan sun gani suma sai su ɗauka daga haka ya karaɗe wayoyin mutane. Yaro yasha addu'oi yayinda ƴammata da yawa suka koka dajin kishin inama daga jikinsu ya fita. Sultana dake ƙasar America kam harda kwanciya ciwo dan har yanzu ciwon son Ramadhan na zagaye da ita. Kawai dai babu yanda zatai ne tunda ya faɗa mata iya gaskiyarsa shi baya ra'ayinta tayi haƙuri ta samu mai sonta..
     Karo na farko, lokaci kuma na farko da Gimbiya Su'adah ta kira waya tasa aka haɗata da Raudha data farka a washe gari da rana. Yajiki tai mata da fatan samun lafiya. Ita dai Raudha abun ma har hawaye ya sakata. Ramadhan dake gefenta yasa hannu yana share mata fuskarsa ɗauke da murmushi.
     Ɗansa dake hanunsa yanata barci ya kalla. Ya shafi lips yaron jajaye yana faɗin, “Ba kuka zakiyi ba Partner. ALLAH zaki godemawa a wannan gabar, ni shaida ne Maah ta jima dayin nadamar abinda tai miki, ta shanye a cikintane kawai saboda nauyin tunkararki. A yanzu kam koda abinda ke faruwa da Lubnah a gidan miji ya isa sake tsoratata”.
     Da mamaki Raudha ta dubesa. “Aunty Lubnah kuma?”.
     Kai ya jinjina mata batare da ya kalletaba ya cigaba da wasa da sumar yaron. “Eh Lubnah. Tun satin da aka kai Lubnah gidan aure bata sake farin ciki ba. Kuskure kaɗan miji zai lakaɗa mata duka tare da ƙanensa. Ke hatta da uwar mijinma ba ƙyaleta taiba itama dukan nata take. Duk da dukiya irin ta gidan su Mansur ƙiri-ƙiri suka sallami kaso ɗaya bisa biyun ƴan aikinsu aikin ya koma kan Lubnah. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fita hayyacinta saboda azaba. Ameenatu, tun sanda Lubnah ta kawo Mansur garemu matsayin miji na nuna ƙin amincewata, saboda na jima dajin labarin mahaifiyarsa bata zama da sutukai. Hakama kanensa basu da isashen tarbiya. Amma sai Maah taƙi saurarena saboda Lubnah tace tana son sa akace ai nima wadda nake aure bata dace dani amma suka amsa. Dan haka Lubnah zata auresa ko ina so ko banaso. To ga sakamakonan sun gani, dan yanzu a dalilin dukan da surukar mijinne tai mata tai ɓarin cikin jikinta, maimakon Mansur ɗin yaji tausayinta sai ya maidota gida da takardar saki har uku wai yana zarginta da tarayya da drivernsu kiji sharri. Koda nai bincike uwarsace duk ta tsara hakan kamar yanda take koran matan ƴaƴan itama tai sanadin da za'a korota”.
        Sosai abun ya taɓa zuciyar Raudha duk da zaluncin da su Lubnah suka dinga mata a baya. Ta jingina kanta da kafaɗar Ramadhan tana kallon babynsu hawaye na zubo mata. Shima rungumita yay da hanunsa cikin son kore mata damuwarta yace,
        “Ustazah dawa yaron nan ke kama?”.
      “Dani mana”
Ta bashi amsa tana share hawaye. Ƙeyarta ya ɗan tallara kaɗan. “Son kanki yayi yawa madam. Kowa yaga Abdull-Hameed Ramadhan Taura yasan gida ya ɗakko, mufa jininmu ƙarfine da shi yarinya”.
     Murmushi tayi mai ƙayatarwa da cewa, “Uhm nidai basan cika baki. Dama da Pa kace yana kama ko Bappi sai na yarda”.
     Dariya yay yana mai sumbatar kumatunta. Hakama babyn ya sumbaci goshinsa. “Bakice komai akan sunan dana kirashi da shi ba”.
    Murmushi tayi mai kyatarwa da shafa kumatunsa. “Saboda shine ra'ayina shiyyasa nima”.
      “Woow sweetheart inajin daɗi idan muka kasance bisa tarayyar abu guda”.
     “Noorullah! Idan duk yarana zasu kasance da sunan Bappi ko Pa ko Anne ko Maah ko kai bazan taɓa baƙinciki ba. Fatana dai ALLAH ya bani ikon sauke nauyinka dake kaina ka kuma zamemin miji har a gidan aljanna. ALLAH ya raya Abdull-Hameed Ramadhan Taura ya albarkaci rayuwarsa. Yasa yay gadon ƙyawawan halayen Bappin da Pa da kai kanka”.
      “AMin ya rabbi sweetheart. ALLAH yay miki albarka ya ƙara miki lafiya. Yasa nan da wata shekarar mu sake dawowa labour room.....”
      Da sauri ta rufe masa baki ƙwalla na ciko mata ido. “Wannan ai fatan tsiyane”.
     Dariya ya kyaƙyale da ita yana ture hanunta. Miye na wani fatan tsiya anan ai nasan zaki iya Mrs Taura.
    Haka suka kasance cikin nishaɗi har saida Aunty Zuhrah tazo ta korashi ɗakinsa sannan.

         ★Sai da Raudha ta warke sosai aka fara shirye-shiryen taron suna, amma kowa dai yasan sunan yaron Abdul-Hameed anma Bappi takwara. Ramadhan yaso ayi suna a Taura house Bappi ya hana yace ayi a government house kawai. Badan yaso ba dole hakan aka shirya. Taron sunane daya haɗa manyan mutanen ƙasar NAYA lungu da saƙo, inda amaryar jego da baby sukaci ƙyau har suka gaji. Shi kansa angon jegon yayi tsaf dashi kamar yana shirin yin sabon aure. Anci ansha an kumayi bishasha, inda yaro ya samu ƙyaututtuka masu ban mamaki wasuma dan riya sukai badan ALLAH ba. Dan kawai wane yayi kar ace su basuyiba.. Hatta M. Dauda ba'a barsa a bayaba ya haɗo kayansa na jego harda saitin robobin wanka da saƙe saƙin wanka na icce da ƙatuwar garwarsa ya kawo. Wannan abu yasa su Aunty Hannah takaici duk da ba'a wajen taron ya bayarba. Sai dai ita Raudha farin ciki tai ita da Ramadhan.
     

Please Login or Register in order to submit comment