You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kukan shagwaɓa ita bata yardaba. Shiko yayta dariya da tsokanarta. Sukanyi waya da Bilkisu kullum, tana kuma cigaba da sake ɗorata akan abubuwa na musamman har gashi yanzu Raudha ta ɗauka sabbin ma'aikata. Mai mata kwalliya da kula da duk wani ado da zatayi musamman idan hakan ta kama akan wata fita ta musamman duk da har yanzu Ramadhan bai taɓa yarda yaje da ita wani taro ba. Sai mai mata gyaran jiki itama. Ramadhan bai hanaba tunda ya san duk abinda zai ƙaru da sune shima ai, to shinema mai ƙaruwar tun school dai kawai Raudha ke zuwa, sannan koda yaushe komanta a rufe.

         Zuwa yanzu cikin Raudha ya shiga watanni na huɗu, ya fito mata ɗan duk da bawani ƙato can ba, wanda ma baida fahimta zai ɗauka tumbi ta fara ajiyewa saboda ƙibar da tayi. A kuma lokacinne gimbiya Su'adah ta dawo NAYA dan likitan riketa yay ta huta sosai acan.
      Ita da shi sukaje mata sannu da zuwa a wani dare cikin fitar sirri. Har yanzu bazamuce Gimbiya Su'adah na ra'ayin Raudha ba. Sai dai akwai sassauci matuƙa a yanayin data amsheta. Harda tambayarta tana lafiya kuwa wannan ƙiba tata lokaci guda haka?. Ita dai Raudha komai batace ba sai ɗan murmushi kanta a kasa. Hakama Ramadhan bai saka musu bakiba dan a ganinsa bai kamata yacema Maah ɗin Raudha nada ciki ba taga rashin kunyarsa a fili. Sai bilkisu ce ta sanar mata Raudha nada ciki ai. Duk da gimbiya Su'adah ta danne yanayin data shiga na farin ciki ƴaƴanta sai da suka fahimta har shi Ramadhan ɗin da Pa, sai dai babu wanda yace mata komai akan hakan.
      Raudha taji daɗin haɗuwa da Bilkisu da itama mijinta ya kawota duba Maah ɗin. Dan tanata son zuwa ma taga gidajen amaren laulayi ya hanata, Ramadhan kuma yace bazatajeba sai taji ƙarfi sosai. Makaranta ma yana barintane dan kar tai asarar abubuwa.
     Sosai Anne ta bata dabarun rainon ciki da shawarwari, tare da mata addu'ar fatan sauka lafiya. Basu baro gidan ba sai kusan ɗaya na dare.........✍

         

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*



*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*


*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_



Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*


*KATIN MTN*👇👇

09166221261
__________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*



Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F


*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77



*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________


*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*


Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

*_Typing📲_*







*_Episode 72_*


.........Rayuwa ta cigaba da shuɗawa gwamnatin Ramadhan nata sakin manya-manyan projects naban mamaki. Ko'ina ka zaga a cikin ƙasa sai sambarka akeyi. Domin ƴan matsalolin dake shigowa tarin ƙoƙarin ayyukan da ake shimfiɗawa suna dannesu ƙwarai da gaske. Hatta da ƴan bani na iya abokan hammaya bakunansu sun mutu dan babu abin faɗa kuma, sai dai duk da haka sukan ɗanyi takale-takalensu a gidajen redio dana talabijin.
     Suna dire zance masoyan Ramadhan ke basu amsa dai-dai da su, amsar da su kansu basu da bakin sake maida murtani, dan kuwa dai kowa shaidane ga Ramadhan tun bai cika shekara akan gadon mulki ba manya-manyan ayyukansa sun fito fili ma duniya. Ga tausayin talaka. Ayyukan yi ga matasa da matan aure harma da ƴan mata. Ɓangaren lafiya da wutar lantarki da ruwa duk Alhmdllhi. Duk da ba komai ne ya wadaci kowaba hundred percent anci kaso mafi yawa na gyara. Makarantu tsaye ake akan albashin ma'aikata da cire kowane irin bara gurbi da zai iya dakusar da ilimin ta hanyar alfarma ko cin hanci da rashawa. Babban abin birgewa a matsayinka na ma'aikaci idan an cireka a gurbin da baka cancantaba za'a kaika wani gurbinne daya dace dakai bawai korarka za'ai ba a aiki balle kaje ka kama wata sabgar mara ƙyau kuma.
         A koda yaushe idan tunanin abu yazo masa yakan tunkari Raudha da shawara kafin ya fitar da shi ga abokan mulkinsa. Kasancewarta ta tashi ƴar talakawa, cikin takalawa da talauci yana taka rawar gani matuƙa wajen zaƙulo masa abubuwa masu muhimmanci na halin ƙunci da talakawa ke ciki a ƙasar. Idan kuma har yay bincike hakan yake samu. Wannan abu na ƙara saka masa ƙaunar matarsa mai yawa a zuciya, ko saɓani suka samu ta ɓata masa rai yakan rangwanta mata idan ya kalli hidimarta garesa....

        Duk fa wannan ƙoƙari na Ramadhan yana a idanun su forma president da god fathers nasu. Sai dai sunyi likimo ne na nuna goyon bayansu gareshi ɗari bisa ɗari har ya cika shekara biyun da suka ɗiba masa tun farkon fari. A cewarsu daga nanne wasan zai fara kuma. Tunaninsu ya ƙara tsaiwa ne akan abinda ya faru game da zubama Raudha maganin zubar da ciki da sanadinsa har yanzu kuku ke a hanun security na gidan gwamnati. Sunbi duk wata hanya daya kamata susan wani abu game da case ɗin amma an rufesa ruf sun gagara jin komai. Hakan yasa zukatansu ke basu akwai wani abu aƙasa da umarnin Ramadhan kuma aka cigaba da ɓoye kuku tabbas. Domin a bincike ɗaya da suka samu kansa suka tabbatar da hakan. Akwai yaransu cikin masu kula da cctv room na gidan, kuma sune suka sakasu lalata camara ta cikin kitchen da koda aka bibiya ba'a samu komai ba, sannan falon sama da bedrooms na shugaban ƙasa da first lady ke ciki babu cctv saboda sirrinsu ne, a ganinsu tunda har babu waɗannan hujjojin bai kamata ace ancigaba da riƙe kuku ba amma sai gashi har yanzu babu labarinsa.
     Waɗan nan dalilan suka sakasu tattara komai suka ajiye gefe acewarsu ya cika 2years ɗin da suka ɗiba masa tunda idan yasan wata ai baisan wata ba. Yana shaƙar poison a ac, yana sha a drinks wannan kaɗai ya ishesu. Kashe Bappi kuwa sun gama shirinsu tsaf akan hakan rana kawai suke jira.
         Itama Aunty Hannah wannan shine dalilinta na rage zuwa wajen Raudha ɗin, sai dai tana nan tana shimfiɗa mulkin da ko first lady ɗin batayinsa, wandama bai sani ba ya ga yanda ake bata tsaro idan zata fita saika ɗauka first lady ce, ga matan ƴan siyasa da masu mukaman gwamnati tun ta tattare ta saka a aljihu tanayin yanda taso dasu.
     Duk abinda take Hajiya Fanta naji kuma tana gani, sai dai ta bata lokacine acewarta ta gama nata kafin itama ta kammala nata shirin. Rashin sanin alwashin na hajiya Fanta kesa forma First lady Hajiya Bushira hamada da Aunty Hannah kejin duniyar da damar duka tasu ce a yanzu. Shiyyasa suke sake baje kolinsu yanda suke so.

To bara mu cigaba da binsu muga yaya wasan zai kaya🚶🏻😮😖.

*_TAURA HOUSE_*

            “Nifa nata ƙoƙarin naga na danne amma yaƙi dannuwa, hakan ya tabbatarmin zuciyata akan gaskiyarta take ba wasa baneba”.
       Pa dake kallon abokin nasa Alhaji Sageer Dogarai mai maganar yay ƴar dariya.
      “Alhaji Sageer yau kuma labaran almara ka koma kokuwa zaka fara tsara littatafai ne na marubuta, danni dai banko fahimci inda zancen naka ya kama hanyar zuwa ba balle dosa”.
     Dariya Alhaji Sageer yayi, tare da ƙurbar ruwan dake gabansu yana gyara zama. “Ko ɗaya Taura. Yanzu zan fiddo maka ainahin zancen dan na fahimci kai hausarma neman ƙwace maka take a harshe saboda yawon bin kasashe kamar ɗan sama jannati”.
    Dariya sosai sukayi a tare. Kafin su tsagaita Alhaji Sageer ya cigaba da faɗin.
      “Idan baka mantaba, a ranar ɗaurin auren yaran nan sanda muke shirin fita da kai bayan nazo na gaida Bappi, mun gamu da tawagar matar vice president”.
    “Ƙwarai anyi haka”.
“Yauwa Alhmdllh, matar da muka ɗan bigi juna har wayata ta faɗi itace tushen zancena. Sai dai zuciyata na cike da ruɗanin matar aure ce kokuwa?”.
       Ɗan shiru Pa yayi na nazari, sai kuma yaja numfashi da tunano ko wacece hakan ta faru. “Dogarai tabbas ban sanka da neman mata ba ko wani abu makamancin hakan tun bayan rasuwar matarka kuma komai bai sauya ba, to amma bazance zuciyata bazatai hasashen wani abu game da hakan ba. Dan a yanda na sanka bazakaima matar nan irin son da nake tunain zai dace da ita ba”.
        “Taura har yanzu ban canja ba, ina a yanda ka sanni wlhy. Ka ture batun yanda ka sanni akan son auren wayayyar mace mai zurfin ilimin boko, idan rawa ta canja dolene kiɗa ya canja shima a wasu lokutan. Ba wayewarta ko ilimnta na kallaba. Yanda naga kuna nuna jin kunyar juna kamar wasu surukai ne yaja hankalina sosai gareta, gata cikin shigar mutunci da kamala saɓanin sauran wanda ke tare da matar vice president. Wlhy har cikin raina sonta ya shigeni lokaci guda batare dana shirya hakan ba.”
        A karan farko Pa yay murmushi, dan yasan wanene Alhaji Sageer Dogarai. Abokinsa ne tunna kuruciya koma muce amini. Shekarar matarsa huɗu kenan da rasuwa yaransu biyu. Tunda ta rasu kuma bai sake aure ba duk da matan nakai masa tallar kansu tare da cece kucen jama'a da dangi akan ƙin sake auren nasa tunda bawai ya wuce hakan bane. Pa ya ɗan ɗage kafaɗa. “Bazance ban yarda da kai ba. Sai dai zance inhar kasan ba hakan bane a ranka dan ALLAH karka aikata abinda zai zubar da kimarmu. Domin kuwa ita wannan mata da kake magana surukatace. Mahaifiyace ga matar Ramadhan kuma a yanzu haka bata da aure dan sun rabu da mahaifin matar Ramadhan ɗin tuni. Yaranta huɗu, ta aurar da ɗaya akwai uku gabanta, sai dai tana shirin aurar da biyu yanzu haka ma”.
       “Alhmdllhi. Alhmdllhi”. Alhaji Sageer Dogarai ya faɗa yana kai goshinsa ƙasa domin yin sujudar shukur. Wannan ya sake tabbatar ma da Pa da gaske ne fa.

        ★Kamar da wasa ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai babu ɓata lokaci Pa ya tunkari Anne da Bappi da maganar. Sunji daɗi sun kumayi farin ciki, dan haka Bappi yace yabar komai a hanunsa.
     A ɓangaren Bappi ma bai tsaya jan al'amarin ba ya tunkari su Hajiyar Birni da shi, sai dai kamar yanda yay hasashe Asabe ta nuna bijirewa su Hajiyar Birni sukai mata can. Murmushi kawai Bappi yayi, tare da basu shawarar su barta tayi tunani, amma ta bama Alhaji Sageer Dogarai ɗin damar zuwa gareta tukunna sai ta yanke hukunci. Ta aminta da hakan, babu kuma ɓata lokaci Alhaji Sageer yazo gareta washe gari.
        Mutum ne kamilalle kuma mai tarin nutsuwa. Ba wani tsufa yayba dan shekarun nasa bazasu gaza dai-dai da Pa ba, ga iya magana dan a ƙankanin lokaci ya siye zuciyar Asabe har taji ta gamsu da shi. Sai dai bata amsa masa ba sai da ta garashi sosai. Shiko bai gajiya da binta ba har sai da ya samu amincewarta. Hajiyar birni kam ai likafa taci gaba burikanta nata tabbata bayan wahalar da taci a rayuwa da garari akansu. Wani lokacin bawa nayin gaggawa ne akan abinda baida masinaiyar UBANGIJI ya tanadesa cikin ƙaddararsa. Sai son zuciya ta sakashi tsayawa wajen nemansa koda ta hanyar data saɓama shari'a ne. Sai kaga yazo ya samu abin kuma daga baya.
      Alhaji Sageer ya matsa shifa ayi aurenau kafin nasu Fatisa. Itako ta dage akan a'a sai anyi nasu Fatisa. Bai haƙura ba ya cigaba da jajircewa har hajiyar birni ta tabbatar masa yanda yakeso haka za'ai. Sam Asabe bataso hakanba. Sai dai bata ƙaunar yima mahaifiyarta jayya ko kaɗan, sannan Aunty Halima na ɗorata akan shawarar ƙwarai na gara tai auren ko bikin ƴaƴan nata ya ƙara mutunci a idon mazajensu da al'ummar da zasu halarci bikin. Tasan gaskiya Aunty Halima ta faɗa mata, dan haka ta tara yaranta ta sanar musu Raudha kuma aka faɗa mata ta waya. Kamar yanda su Fatisa suka nuna kishin Abbansu a fili haka ma Raudha. Dan kuka ta dinga rusawa akan ita bata yarda Mummyn nasu ta sake aure ba.
       Shi dai Ramadhan ma da yaji tushen kuka. tagumi ma kawai yay yana kallonta. Sai da tayi mai isarta sannan yay magana.
       “Oh ni Ramadhana naga takaina. Ni karma a haifamin yara masu kukannan fa? Yanzu ke Partner dan ALLAH ba abin farin ciki bane Mummy tai aure? Kinada ilimin addini fa, kin kuma san babu sauran aure tsakaninta da Abba taya zata cigaba da zama kuma a haka bayan har yanzu shekarunta basuyi nisan da hakan zai kasance ba”.
      Baki ta tura gaba da juya masa baya zata kwanta ribda ciki ya riƙota. “K rufamin asiri, da wannan cikin zakiyi wannan kwanciyar?, ga Abba ya samu mai tayasa kishi ni ki halakamin nawa.”
     Dama ba kwanciyar zatai ba. Dan yay magana tai hakan, ta sake tura baki da buge hanunsa dake riƙe da cikinta daya sake fitowa sosai yanzu kowama zai iya shaida akwaishi.
        “Ni dai yi haƙuri karki cinyeni da baki, yarana suzo suga an gama gwaguyeni”.
      Filo ta ɗauka ta shiga kai masa duka yana karewa da dariya, sai kuma ta mike daga gadon ta sauka tana daddaga kafa. Saurin riƙota yay ya zaunar a cinyarsa. Zata ɓare masa da kuka ya ɗaura lips nashi kan nata daga haka labarin ya canja.
      Bai bartaba sai da ya tabbatar dukkan damuwarta ta gudu sannan suka shiga toilet suka tsarkake kansu tare. Bayan sun fitoma nasiha ya dunga mata har sai da ta fahimcesa ta sakama auren albarka. Suka kuma kira Asabe tare suka gaisheta da nuna mata goyen bayansu dan yanzu dama Ramadhan kanyi waya da Asabe da M. Dauda lokaci-lokaci. Hakanne ya ɗan ƙara sakama Asaben nutsuwar zaman Raudhan tare da shi.............✍


*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*



*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*


*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_



Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*


*KATIN MTN*👇👇

09166221261
__________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*



Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F


*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77



*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________


*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*


Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


*_Typing📲_*







*_Episode 73_*


..........A wata juma'a datai dai-dai da saura kwanki huɗu cikar shekarr Ramadhan guda a mulki aka ɗaura auren Alhaji Sageer Dogarai da amaryarsa Asabe. Aure ne daya tara ɗunbin al'umma musamman daya kasance juma'a ne mutane duk sun halarci masallaci. Aure ne daya saka wasu farin ciki wasu saɓaninsa musamman aunty Hannah da tun farkota nuna adawawta akai, sai dai kuma babu abinda ta isa ta hana daga hukuncin ALLAH.
      Ƴar walima kawai akai amarya ta tare ɗakinta cikin aminci da mutuntawa. A kuma daren Ranar M. Dauda da abokinsa suka iso Bingo a haukace a dalilin M. Gambon ya samo labarin a shanun ƴan talla. Inda ALLAH ya taƙaita al'amarin ya kira Bappi ta waya kafin su tunkari ko'ina. Hakan yasa Bappi saurin taka masa birki yasa Malam Adamu zuwa ya ɗakkosu. Babu wanda yasan da zuwansu Taura House sai Anne da Bappi. Aka basu masauki mai ƙyau da abinci kafin safiya. Da farko M. Dauda ya nuna shifa ba wannan ya kawosa ba Bappi dai ya sake lallashinsa.

     Washe gari da suka zauna akan batun fir ya nuna shifa sai Alhaji Sageer Dogarai ya sakar masa matarsa inhar ana buƙatar zaman lafiya a NAYA. Iya nasiha yaƙi har sai da Bappi ya bama Ramadhan Umarnin sakawa a kawo masa Raudha gidan. Tana makaranta M. Adamu yaje ya ɗakkota. Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake dan batasan mike faruwa ba. Gashi babu damar kiran Ramadhan ta damesa tasan yana office. Sai da suka iso taci karo da Abbansu ta sauke ajiyar zuciya. Yay sakalo yana kallonta da cikinta daya fito ɗas duk da ma hijjab ne a jikinta har ƙasa. Sai dai a yanda tai zaman sai da cikin ya fito.
       “Oh ALLAH sarki Raudha ashe wannan irin arziki ALLAH yaymin naketa shirme ma? Dama ciki ne da ke?”.
     Ina ƙasa Raudha ta shige dan kunya, Bappi yay murmushi mai faɗi da gyaran murya. “To kaga kariga ka fara zama babban mutum tunda ga jika kana shirin amsa duk da nasan bashi bane na farko. Ya kamata wasu abubuwan a ajiyesu hakanan kodan wasu dalilai Malam Dawood. Shi aure raine da shi, sannan ƙaddarace ta ALLAH. Ya riga ya ƙaddaro zaka zauna da mahaifiyar yaran nan na wani lokaci ku rabu, idan kuma da rabon sake zama sai kaga ta sake baro can ta dawo gareka ai”.
     Hawaye malam Dauda ya share dan harga ALLAH yana son Asabe, so irin wanda bai tabama wata mace ba. Dan ko auren nan daya kara na budurwa dal a leda bai maye masa gurbin rashin Asabe ba a ransa. Nasiha sosai Raudha da Bappi sukai masa, sai dai M. Gambo nata zungurinsa akan karya yarda wai. Tsaf Bappi ya fahimci M. Gambo, ya kuma gane shine matsalar M. Dauda. Dan haka a ranar ya saka aka maidashi Hutawa bayan ya haɗashi da shatara ta arziki.
      Sosai M. Gambo yaji zafin hakan, dan acewarsa ƙiri-ƙiri an nuna banbanci tsakaninsa da M. Dauda. hakan ya sashi ƙudirin abubuwan mugun abu da yawa cikin rai game da M. Dauda. Acewarsa in bai samu Asabe ba ai akwai hanyoyin ramuwa da yawa.
  
      Kwanan malam Dauda biyar a Bingo, dan har gidan gwamnati aka kaisa ya kaso kwarkwatar ido wannan karon. Bappi kuma ya riƙesa akan ya zauna har sai anyi bikin cika shekara guda na Ramadhan a mulki. Hakan ya masa daɗi sosai, ya kuma sakashi farin ciki. Su Fatisa ma har nan Taura house sukazo gaida shi, har kuma zuwa yanzu bayan su Anne babu wanda yasan da zamansa a gidan.

*_GOVERNMENT HOUSE_*

          Sosai aka shirya bikin cika shekara ɗayan nan har abun ya ɗan so bama mutane mamaki, dan lamarin tamkar wani arashi. An shirya ɗakin da taron zai gudana cikin tsarin ado na tutar ƙasar NAYA. Duk da gwamnoni suma zasuyi nasu a jihohinsu hakan bai hanasu halarta ba. Hakama sarakunan gargajiya da abokan kasuwancin Ramadhan.
        Su Alhaji yaro glass da muƙarrabansa harma da god fathers nasu kam sun halarci taron. Sai tarin manyan ƴan jam'iyya na kowace jiha. Kamar ko yaushe First Lady da mijinta shugaban ƙasar NAYA *_Ramadhan B. Hameed Taura_* suka iso wajen taron cikin shiga ta kamala ana take musu baya. Sanye take da hijjab har ƙasa fari ƙal mai hannu, sai kaɗan daga ƙasa ake iya ganin ƙasan doguwar rigarta mai kalar tutar ƙasar NAYA. Daɗin daɗawa akwai facemask a fuskarta tare da siririn farin glass iya hannayenta kawai ake iya gani da tsadajjen agogonta. Hakama shugaban ƙasa Ramadhan sanye yake cikin ɗanyar shadda fara ƙal daketa maiƙo da haska idanun mai kallo. Ta gaurayu da ɗinki na musamman daya ƙawatata ya kuma tabbatar fitar tutar ƙasar NAYA. Hakama hularsa zannah tayi matuƙar murzuwa. A kallo guda zaka tabbatar da tarin kwanciyar hankali da farin ciki tattare da shi. Yana riƙe da hanun matarsa har akai masa rakkiya wajen zamansa sannan mutane da suka miƙe dominsa na girmamawa suka koma suka zauna.
      Kamar yarda shari'a ta tanadar malamai sun gudanar da addu'oi kafin a fara gudanar da abinda ya tara mutane a wajen. Inda bayanin shugaban ƙasa yay matuƙar birge mutane da ƙara darajarsa a idanusu. Lokacin da aka buƙaci cewar first lady.
       Wata hamshaƙiyar mace ta miƙewa da takarda a hanunta ta tabbatar musu ga saƙon first lady ita  wakiliyarta zata isar bisa umarnin shugaban ƙasa amma matsayin miji ba shugaba ba basai tace wani abuba.
      Hakan ya bama wasu mamaki, ya birge wasu. Wasu kuwa sun gumtsi gulma da sauya zancen a muhali na daban. Oho hakan bai damu Ramadhan ba, shidai burinsa tsare mutuncin iyalinsa da kuma kishinta da yakeyi. Bayanan da aka gudanar matsayin na first lady ma sun kayatar kuma sun birge mutane daban-daban. Daga haka taro ya cigaba da guna. Anci ansha anyi hani'an first lady da shugaban kasa babu wanda yasha ko ruwa a wajen.
       Sai da ana gab da tashi a taron ne Raudha ta hango Abbanta tare da Alhaji Hameed Taura cikin shiga ta kamala tamkar bashi ba, dan kayan daya saka sun masa ƙyau matuƙa duk da jikin ya nuna ba'a saba sakawa ba. Taji daɗin yanda ya kame kansa a wajen har aka tashi lafiya.
    
     Duk yanda Raudha ke ɓoyen cikinta a hijjab hakan bai hana wasu ganewaba, tuni kuma yan jarida suka hau yaɗa cewar shugaban ƙasa gab yake da zama angon karni kuma Baba dan firt lady na ɗauke da ciki. A fanin ƴan adawa kuma sun gama baza zance first Lady dai turancine bata iyaba shiyyasa Ramadhan ya hanata magana a wajen aka samo kwararriya aka fake da kishi.
     Maganar tayi nisa sosai, sai dai cikin Raudha yaso danneta tare da manyan ayyukan da aka zano shugaban ƙasa Ramadhan ya

Please Login or Register in order to submit comment