You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasa. Watoh Hajjiya Salma
Kuma itama haihuwanta d'aya da mahaifin nasa... Saida mah mahaifiyarsa hajjiya Rahma ta haifesa bayan wasu shekaru uwar gidan hajjiya Rukayyat ta haihu..
Dan har tacire rai da haihuwan..
Shine take haifan Salim Wanda yanxu shima ya girma yake kula da supermarket d'in ADAMSIN...

Wannan abu yana b'ata ma Hajjiya Rukayyat rai... Yanda ADAMSY yake juya nera.
Hannunsa me albarka ne
Dan duk abinda yasa agaba zaiyi kasuwanci akansa tosaiya samu albarka...
Gashi doctor.. Ga kasuwanci.. Gashi duk fad'in garin KADUNA bawanda baisan ADAMSY ba
Kowa fatan alkairi yake masa.
Saboda kyautatawarsa ga al'uma
Ga qaninsa Salim d'in yana San d'an uwan nasa ADAMSY... dan baya nuna masa komai
Shiyake masa komai na rayuwa..
Dake shi Salim d'in kasuwanci ya karanta. Shiyasa ADAMSY ya barsa a supermarket d'in nasa...

Burin hajjiya Rukayyat ADAMSY ya mutu. Salim ya zama kamarsa.. Su gaje dukiyarsa..
Wannan dalilin yasa dataji zaije ya d'auko yaran marayu tayi tsalle ta dira tace bata amince ya ibi yaran marayu ya rainesu ba
Ganin hakan yasa mahaifinsa shima yace bai yarda ya d'aukosu ba.

Koda ADAMSY ya kalli mahaifiyarsa a lokacin nunamai tayi dole yabi umarninsu
Dan yasan bata da y'anci agidan
Kuma mahaifinsa yana da zafi.. Idan ya yanke hukunci akan abinda hajjiya Rukayyat tayanke shikenan ya zauna..
Wannan rayuwar da mahaifiyarsa takeyi agidan tana baqanta ran ADAMSY
Saidai ba yanda zaiyi. Amman zuciyarsa cike take da tsanar uwar gidan Dadyn nasa hajjiya Rukayyat

Sannan hajjiya Rukayyat bata san ADAMSY ya haihu dan bokanta yace mata duk randa ADAMSY ya haihu toh aranar duk wani asirce asircen da takema mahaifin nasa aranar zai fara warwarewa...
Ita kuma irin nata salan qaddarar asirce asircen nata kenan


Wannan shine labarin TAUDHAT da dangantakar dake tsakaninta da NUFAISAT. Da kuma d'an rayuwar ADAMSY dana d'auki muku....


**********
Ba abinda Maman TAUDHAT ta iya cema TAUDHAT d'in sai tashi da tayi tabar mata falan...
Aiko wani matsiyacin tsaki TAUDHAT d'in taja wai adole ranta ya b'aci. (Allah ka shirya mana zuri'a Amiin)

Toilet ta shiga tayi wanka da fad'awa bed nata. tana tsaka yanda zatayi taja hankalin NUFAISAT suje wajen saban bokan nata
Duk ta k'osa tazama Matar ADAMSY
Itama yadinga damawa da ita cikin soyayyarsa


ADAMSY ko yana kaiwa gidansu duk da cewar dare ne Amman hakan bai hana ma'aikatan gidan rugowa da gudu suka zube agabansa suna masu kwasar gaisuwa ba..
Suna San ADAMSY kasancewar yana kyautata musu da basu kulawa...
Da Murmushi yake amsa gaisuwarsu ahaka har ya shige falan Dadynsa
Dake yau hajjiya Rukayyat ce da Dadyn nasa tare ya gansu suna hira..
Dan haka yana gama gaishesu saiya nemi daya tashi yaje shashin mahaifiyarsa....
Da sauri Dadyn nasa yace dashi... "Dakata ADAM.. Dama ina San magana dakai
Cikin ladabi ADAMSY ya koma ya zauna yana cewa.. "Ina jinka Dady
Jan numfashi Dadyn nasa yayi da cewa.. "Dama ina San.. ka ƙara Aure ne....
Cikin sauri da rikicewa tsakanin ADAMSY da hajjiya Rukayyat suka had'a baki wajen cewa.. "Aure😳.. Suna masu kallansa
Da wani hali Dadyn ya maida kallansa ga hajjiya Rukayyat yace.. "Eh Aure..
Aure nakesan ya qara ko za'a samu rabo daga matar dazai Aura..
Yanxu fa shekarun auransa kusan Bakwai..
Ina San yara da yawa Rukayyat.. kinfi kowa sanin hakan
Daga shi sai d'an uwansa Salim nake dasu..
Hakan yasa nake kwad'ayin samun jikoki
Gaskiya ina san ganin jikokina nan kusa
Da wani hali hajjiya Rukayyat tace... "Amman Alhaji ai ADAM baiyi dad'ewar daza'ace ya ƙara Aure dan rashin haihuwa ba..
Murmushi Dadyn nasa yayi da cewa... "Haba Rukayyat. Kiyi aiki da hankali mana. Yaran nan ya haure shekaru talatin.. Idan bai haihu yanxu ba. Saiya tsufa kikesan ya haihu..
Gaskiya Ina San naga y'ay'ansa yanxu.. Nagansu kan cinyata suna jamun gemuna.... Ya ƙarashe furucin da Murmushi😀
Aiko nan take ta murtuƙe fuska.. Ta nuna ƙarara bataji dad'in furucinsa ba..
Dan haka da ɓacin rai tace.. "Toni gaskiya ban amince ADAM ya ƙara Aure yanxu ba..
Dan haka aƙaramai wasu shekaru Idan anji shuru abarsa ya ƙara Auran
Shuru Dadyn nasa yayi.. Can yace. "Toh shikenan an qara masa lokacin. Allah ya dubesa ya basa nan kusa..
Da Murmushi tace.. "Amiin Amiin..😀

Shiko ADAMSY shuru yayi yana jinsu..
Da farko yaji fad'uwan gaba dayaji furucin mahaifin nasa nasan ya ƙara Auran
Dan ko'a mafarki baiji aransa yana San qara Aure ba..
Saidai kuma yaji mamaki sosai yanda hajjiya Rukayyat ta nuna damuwarta akan batasan ya ƙara Auran
Hakan yasa kwakwalwarsa tashiga tunani dan tagano dalilinta..
Yadai fahimci koma menene dalilin nata bame kyau bane
Ya gane da daɗewa ba sanshi take da haihuwa ba
Toh me take nufi da hakan..
Shuru yayi na wani d'an lokaci... Danya raasa gane manufarta..

Dan haka Ahankali ya kalli Dadyn nasa yace mai... "Nasan kana San yara Dady.. Kuma dama nima ina San gaya maka Inasan ƙara Aure....
Kawai jira nake mugama dai dai tawa da Ita yarinyar nazo maka da batun...
Ai da sauri Dadyn nasa ya tashi daga shigingiɗan da yake cikin farin ciki da murna yace... "Masha Allah.. Allah abin godiya.
Gaskiya naji dad'in hakan
Ku dai dai ta Inasan ganin yaranka ADAM.. Allah yasa nagansu da raina
Da Murmushi ADAMSY ya kama hannun Dadyn nasa yace... "Insha Allah Dady zaka gansu kana raye.. Har suxo kan cinyarka suja maka gemu..😀
Dariya sosai Dadyn nasa yayi yana shimai albarka....

Afusace hajjiya Rukayyat ta gallama ADAMSY harara tace... "Ka kalleni ADAM. Kasan bana magana biyu anan gidan.
Dan haka bazaka ƙara Aure yanxu ba..
Sai nan da wasu shekaru..
Har yaushe kayi Auran dazakace zaka ƙara.
In banda zalama irin taku ta yaran zamani meye matarsa NUFAISAT bata had'aba
Yarinya me hankali da nutsuwa ga ladabi da biyayya
Kai yanxu baza kaji kunyar idanta Idan taji zaka ƙara Aure ba!!!

Yanxu ADAMSY ya ƙara tabbatarwa tana da manufa me qarfi kan bata San ya ƙara Aure

Dan haka da Murmushi cikin sanyin murya yace da Ita... "Momy ina San ƙara Aure ne badan matsalar haihuwa ba.
Saidan karna fad'a ga halaka.
Azahirin gaskiya ina da ra'ayin yin mata hud'u..
Wannan shine dalilin dayasa zan ƙara Aure badan NUFAISAT tarageni da komai ba
Dake mun fahimci juna da Ita na gaya mata dalilina nasan na ƙara Aure
Kuma tafahimta har ta'amince dana nema mata abokiyar zaman tagari...
Ki kwantar da hankalinki momyna.. Insha Allah mata bazu wahalar miki dani ba... Dan nasan matsalarki kenan.... Ya ƙarashe furucin da tashi yana mah Dadynsa sallma da Murmushi akan fuskarsa yake cemai daga gun Amminsa zai wucce gida basai yadawo ba
Fatan alkairi mahaifin nasa yayi masa shiko ya ficce da sauri dan bayasan hajjiya Rukayyat d'in tace mai wani abu...

Aiko yana ficcewa itama taficce zuwa shashinta dan kiran aminiyarta Susan yanda zasuyi😂

Shiko Dady da kallo yabita... Kana ya tab'e irin zakiji dashi d'innan...
[29/04 12:05 pm] 🔳◾◼▪💙: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018.

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 05☆


Shiko ADAMSY can a bed yaga Ammeen nasa tana qoqarin kwantawa..
Aiko da Murmushi ta kallesa tace... "Yanxu nake tunaninka d'an albarka...
Fad'i nake araina kodai yau bazan ganka bane nayi baccina
Zama yayi kan kujerar dake kusa da bed d'inta yana cewa.. "Wane ni da qin zuwa ganin iyayena.
Koda ace NUFAISAT shed'aniyace. Bata isa hidimarta tasani mantawa da iyayena ba.
Ina sanki Ammeena..
Zanyi komai gareki dan kiji dad'i
Jan numfashi tayi dajin daddad'an kalamansa. Kana ta zauna gefan gadan nata tana me qara cigaba da kallansa tace.. "Abu d'aya yanxu zai qara faranta raina agunka ADAM.. Shine naga y'ay'anka..
Duk da cewar ina qaunar NUFAISAT.. Bazan so ka had'ata da wata mace ba. Danta tara duk abinda yadace asamesa agun Y'a mace..
Saidai zuciyata na gayamin.. Kodai zaka qara Aure ne..
Wallahi ADAM ba abinda nake buri ayanxu kamar naga y'ay'anka..

"Ammee kenan.. Insha Allah zakiga y'ay'ana. Yanxu ma maganar da muka gama kenan da Dady
Yana San na qara Aure amman kamar momyn Salim bata San na qara Auran
Saidai na tabbatar mata da cewar zan qara dan ina da burin Auran mace hud'u

Murmushi Ammeen tasa tayi da cewa. "Masha Allah.. Saika gaggauta neman wacce zata dace dakai... Dan Idan ka d'auki lokaci ba makawa zatayi wani abu akai.. Tunda kaga kamar bata so ka qara..
"Insha Allah kuwa Ammee

Sun d'an jima suna shirarrakinsu irin na d'a da uwa..
Sai daga bisani ya numfasa yace.. "Yanxu ni zan tafi.. Naga dare nayi.. Ko akwai wani abinda kike buqata.
"aa nidai gareni babu komai..
Saidai gobe baqin da zaka gana dasu da safe suna da yawa..
Murmushi yayi da tashi yana cewa.. "Ba damuwa. Allah ya qara shige mana gaba..
"Amiin. Tace dashi tana me Murmushi
Shima da Murmushin ya fitta daga d'akin..

Direct wajen shiyan kayan sanyi ya nufa.. Inda ya siyama Matar tashi ice-cream. Dasu mittifai da sauransu.. Kana ya nufi gida


Tun daga farfajiyar gidan yake jiyo ƙamshin turaran da Matar tasa tasaka a falan nata..
Murmushi yayi da girgiza kai. Yana tuna tsafta da kwalliya irin na Matar tasa..
Da cikakken nishad'i ya shiga falan yana cewa.. "Inafa jin daɗin turaran nan...
Ahankali tafitoh daga wani d'an sak'o tana Murmushi tace... "Har sai yaushe zaka dena wannan furucin da zaran kajiyo wannan ƙamshin..
Da wani salo. Da wani yanayi yake qare mata kallo tun daga sama har qasa..
Tayi mai kyau irin sosai ɗinnan👌🏻
Danji yayi kamar ya saceta ya gudu..
Wani mini siket ne tasaka da wata riga wacce tatsaya mata a dai-dai na fulaninta..
Nan wajen kawai ta iya sitircewa a jikinta..
Haka kazanika shi mini ɗinma ba wai ya saukan mata bane.. dan Idan tayi kyakkyawan juyi zaka iya gano gabanta nan kusa basai kasha wahala ba..
Yafa kwaɗaitu fa sosai da yanayin.. Dan taga yanda yayi saurin haɗiyan yawo..
Shi dai yana San matarsa. Dan yana samun farin ciki daga gareta....
Rungumarta yayi yana kissing ɗinta tako ta ina yana cewa.. "Kinyi kyau sosai matata...
Ina sanki..
Ina ƙaunarki
Ina fatan kasancewa dake har ƙarshen RAYUWANA...

Tafi kowa sanin mijinta...
Bai iya ganinta ya barta haka kawai ba
Saidai Idan da baqi yayi musu alkunya
Ji take aranta tafi kowa Sanshi da ƙaunarsa

Taƙyer takwaci kanta tana cewa.. "Nakasa banbancewa
Shin awane yanayi kafisan kaganni..
Na saka ƙananun kayane ko nasaka kayanmu na hausawa..
Idanshi ya kaɗa yayi jah yace da ita.. "Me kika gani..
"Gani nayi a kowane yanayi kaganni rikicewa kakeyi..
Murmushi yayi da cewa.. "My luv bazaki gane qaunar da nake miki bane..
Yanxu dai muje ki bani nasamu nutsuwa.. Amman dan Allah ki barni nayi yanda nakeso..
Hararar wasa tasakar mai da cewa.. "Yaushe zaka dena wannan futunar taka...
Cikin sauri ya katseta da cewa.. "Randa namiki Kishiya ranar zan dena damunki da yawa...
Aiko nan take ta zumɓuro baki tace... "Zanfa babbakaku daga kai har kishiyar..
Dariya yayi sosai yana kallanta da bata amsa.. "Toh Idan kuma ya kasance Y'ar uwarki ce fah
"Wake nan..😳 Wai kana nufin TAUDHAT...
ɗaga mata kai yayi yana kunshe muguwar dariyar dataxo masa..

Aiko turmuƙe fuska tayi kamar zatayi kuka tace... "Dan Allah kabari... Kaima kasan abune bame yuhuwa ba..
Nasan ko'a mafarki TAUDHAT baza tataɓa zama kishiyata ba..
"Ko..... Ya katseta da faɗin hakan yana me cigaba da cewa... Amman kinsan da cewa TAUDHAT tana matuƙar sona..
Jan numfashi NUFAISAT tayi da cewa. "Na lura yau sokake ka zautar dani da zolaya...
Kaga zomuje na shayar dakai dannaga a kwaɗaice kake dasu... Ta ƙarashe furucin nata tana me karɓar ledar dake hannunsa da kama hannun nasa tajashi bedroom ɗinsa

Buɗe mata kayan sanyin yayi su ice-cream ɗin tasha San ranta...
Kana ya fara sarrafata yanda yakeso...
Sanda ya tabbatar yasamu nutsuwa da kwanciyar hankali kana ya maƙaleta yana juya na fulaninta cikin bakinsa yana jin daɗi..
Sanda ya ɗauki lokaci ahakan kana ya bar matasu ya rungumeta yana ce da ita... "My luv. Ina samun dukkanin wani farin ciki daga gareki
Sannan a iya sanina ba ma'Auratan da suka kaimu fahimtar juna..
Dan kina san abinda ni nake so
Haka kaza nika nima Ina san abinda ke kike so.
Duk da cewar nasan kishiya da zafi take..
Ina baki haƙuri wajen gaya miki dazanyi cewar ina San zan ƙara Aure.....
Sosai yaji bugawar da girjinta tayi.... Sakamakwan dama a ƙirjinsan take..
ƙokari tayi dan ta raba kanta da ƙirjinsa Amman saiya ƙara ƙamƙameta..

Shuru na wani ɗan lokaci... Zuwa can ya fara jin zubar hawayenta a ƙirjin nasa
Cikin wata siririyar muryar tace dashi... "Me zaisa ka ƙara Aure...
"Zan ƙara Aure ne saboda ina San na faranta ran iyayena
Ko Allah zaisa nasamu rabo...
Bayan hakan ina addu'a akan Allah yasa wacce zan Auran ta iya girki...
Dan ina San mace wacce ta'iya. Nasha gaya miki batun yau ba.
Sannan bawai zanyi Auran bane danna musguna miki
Zanyine kawai dan farin cikin iyayena da kuma kwad'ayin samun wacce ta iya girki... Danna San zamammu da TAUDHAT na wani ɗan lokaci ne.
Kasancewar Dole tazama matar wani.
Idan hakan ta kasance yazanyi... Ya faɗi hakan yana me kallan fuskarta daci gaba da cewa.... Nayi nayi dake akan ki daure ki d'an iya. Amman kinqi
Toh ya zanyi dake my luv....

Kuka take sosai. Dan baqamin shiga tashin hankali tayi ba
Tasani.. Mijin nata me magana ɗaya ne.. Kuma duk abinda zai gaya maka gaskiya ne
Tasan tsakaninta dashi ba batun wani ƙunbiya ƙunbiya
Duk abinda yace mata zaiyi zaiyi ne kawai
Wannan yasa tafara jin tausayin kanta
Dan tasan zamani ya lalace... Batasan wazai kawo mata ba
Tasan yana dasan yara.
Shin idan yasamu daga wajen kishiyar tata wane baƙin ciki zata kwasa....
Cikin kuka tace dashi.. "Yanxu awane matsayi zaka barni...
"Wallahi bazan taɓa canja miki matsayin da kike dashi a cikin zuciyata ba...
NUFAISAT umarni nake baki akan bana San naga wani tashin hakanlinki akan Auran nan
Sannan bana San naga kin canja daga abubuwan da kike min
Hakan zai iya tunzura zuciyata
Dan kinsan baki isa dakatar dani daga ƙin aikata hakan ba
Kinfi kowa sanin magana ɗaya nake dake. Wacce ta kasance bata wasa ba.
Ina San ki saka aranki abokiyar zaman ki zata iya zuwa miki a kowane lokaci
Daga ƙarshe ina Sanki. Kuma bana tunanin zanso wata Y'a mace KAMAR yanda nake sanki..
Jan numfashi tayi cikin cigaba da kukan nata tace dashi... "Zanbi umarninka Ya mijina.. Dan abinda ya kawoni kenan gidanka...
Saidai yanxu ina buƙatar kaɗaici
Dan Allah kabarni naje bedroom nawa na kwana..
Murmushi kawai yayi da saketa ta sauka daga gadan da suturce kanta har takai ƙofa yace da Ita "dakata
Tashi yayi shima da sitirce gabansa yaxo gabanta da kama fuskarta yace... Dawai ina San ki tayani wankan ne kamar yanda kika saba.. Ya fad'i hakan yana me janye hannunsa
Share hawayenta tayi dayi mishi Murmushin yaqe tace... "Toh muje..
ɗaukarta yayi kamar wata baby ya nufi toilet d'in da Ita KAMAR yanda yasaba mata
Akan idansa tayi wankan tsarkin. shima yayi..
Sannan sukabi da wankan sosu da sabulu

Kamar yanda tasaba temaka masa. Hakan tayi..
Bayan sun fitoh ne dukkaninsu jikinsu d'auke da tawul. Ya kalleta yace.. "Da'ace kamar yanda kike bani kulawar nan Idan mun kusanci juna wajen yin wanka. Da'ace hakan kike bani kulawa Idan kina tare da TAUDHAT dana qara sanki da qaunarki....
Dan sosai nake jin takaicin yanda baki San kulawa dani Idan kina tare da TAUDHAT..
Abin na d'auremin kai Idan kina bani kulawa bayan idanta
Kawai dai magana d'aya anan itace.. ina San kulawa akowane lokaci koma kina tare da waye..
Murmushin k'arfin hani tamai da cewa... "Ayanxu zan kula sosai ya Mijina..
Kama fuskarta yayi ya fara aika mata da wani make✔.. Kiss. Wanda yake tafiya cikin wani salo
Sanda yay mata San ransa kana ya barta yana mece mata.. "Zanso ki sami kaɗaicin da kika nemi alfarma akansa..
Murmushin dai taƙara sakar masa da cewa... "Nagode...
Tana fad'in hakan taficce daga d'akin
_yau rana d'aya kacal.. Kin raba shinfid'a dani NUFAISAT.._
Ya fad'i hakan aransa
Kana ya zauna yana tunanin maraicin dazaiyi yau
Dan yasaba da d'umin jikinta yayin baccinsa...
Shuru yayi... Zuwa can ya canja kaya da shinfid'a dadduma ya fara aikin bada lafula. Yana gaisar da ubangijinsa

Itako Sanda ta tabbatar da cewar ta kulle ƙofar bedroom natan.. Sannan ta zube a gadanta tarushe da wani uban kuka wiwi..
Ta sani... Mijinta na matuƙar santa.. Kuma ayanda take kyautatama iyayansa baici ace su mata haka ba.😭
Har shekara nawa tayi da Auran da zasuce ya qara Aure dan kawai bata haihu ba..
Abayyane take cewa.. "Wai meyasa mutune suke haka ne
Meyasa Ammee zakimin hakan
Me yasa. Meya Dady zakamin haka..
Shin bakusan Kishiya da zafi da ciwo take ba..
Ji nake kamar nayi hauka..

Ba qaramin kuka taci ba.
Candai daga bisani dataga kanta na Sara mata alamar zata cutar da kanta.. Sai kawai tatashi tayo alwala tahau lafula.. Tana rokwan Allah akan ya biya mata buqatarta na yasa Auran karya zama tashin hankali agareta
Allah yasa yinshi shine farin ciki agareta
Allah yasa hakan ya zama alkairi agareta
Allah yayaye mata baqin cikin duniya dana lahira.
Allah ya BATA DAMAR B'OYE KISHINTA agun amaryar da shi kansa uban tafiyar...
Haka tadinga addu'a kamar bazata dena ba..
Sannan kuma tadawo tafara karanta Qur'ani
Sanda taji idanta na rufewa sannan ta kwanta
Aiko bacci me nauyin gaske ne yayi awan gaba da ita...

Shiko Sam bai iya wani baccin kirki ba
Dan tunda yake da NUFAISAT wani abu bai tab'a shiga tsaninsa da Ita sun raba shinfid'a ba
Wannan dalilin yasaka ya kasa baccin kirki..
[29/04 12:05 pm] 🔳◾◼▪💙: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story
April.. 2018.

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 06☆

Asuba nayi kamar yanda tasaba... Watoh bayan kammala sallar asubarta.. Tana shiga toilet d'insa da nata ta wankesu
Bayan ta fitto tayi shara da saita saka turara nan zakaji ko ina ya d'auki ƙamshi
Kana tayi wanka sai tatarama ogan nata nasa ruwan wankan
Kasancewar baya dawowa daga masallaci har sai gari yayi haske...
Hakan yake bata damar kammala way'annan ayyukan saidai kawai ya dawo ya ganta fes Ita da dakunanta...
Toh yau abin yaxo da wani saban salo..
Kasancewar tatashi da wani yanayi ba kamar yanda tasaba tashi ba
Saidai tagodema Allah daya amshi addu'arta... Dan bata tashi da muguwar damuwar nan da mata ke tashi da Ita lokacin da mazajensu suka gaya masu zasu qara Aure ba...

Hakanne mah. Ya bata damar tagama komai kamar yanda tasaba..

Yanxu haka tana tsaye a kitchen d'inta ne..
Lokacin bakwai dai-dai.. Alokacin kuma take sakaran dawowar Mijin nata daga Masallacin
Dama shine yake dafa musu Lipton da soya musu kwai da sauransu..😂
Shine yau take San gwadawa.. Taga zaiyi dad'in da yake musu..
Saka ruwa tayi da d'an jefa citta dasu kanunfari ta cika ruwan..
Nan tatsaya har ya tafasa ta juye a fulas.. Sannan ta fasa kwai guda shidda tasaka magi dunƙule shima guda shidda...
Sannan takad'a ta soya..
D'aukar wayarta tayi takira yayarta Zainab akan tagaya mata yanda ake had'a farfesun kaza...
Da iya adadin magin da zata sakama kaza d'aya
Dariya Zainab tayi mata
Da cewa.. "Ina y'an aikinki suke.. Larai da Aseeya.. Kikara larai tayi miki mana...
Kamar NUFAISAT zatayi kuka tace da Ita.. "Kisan bana sakasu aikin daya shafi shashina. saidai imbanda lafiya..
Aikin su shine kawai su dafa nasu daba ma'aikatan gidan..

Bama wannan ba. Shi Wanda zanyi dominsa baci zaiyi ba..
Ko kin manta yanda nasha wiya wajen cusa masa San cin girkin TAUDHAT
Kinsan Daga na Ammeensa saina nata Yanxu kawai yakeci
Jan numfashi Zainab tayi da cewa.. "Toh meyasa yau kikesan kiyi masa da kanki..
Bayan nasan shine yake had'a muku breakfast..
"Ki bari kawai y'ar uwa.. Ina San ganinki pls idan kin tashi daga office yau
Ina san gaya miki wani abu..
"Ok.. Zainab tace da ita.. Sannan tagaya mata yanda zatayi..
Cikin iko na Allah ko sai tayi dai-dai da yanda tagaya matan...
Dan duk gidansu Zainab ce kawai tayo momynsu wajen iya girki..


Shidai ADAMCY daya dawo yayi mamakin ganin NUFAISAT a kitchen.. Bama wannan ba. Mamakinsa yafi tsayawa akan yanda yake jiyo ƙamshin farfesun kaza..
Yasani wannan aikinsa ne na safe 😂
Murmushi kawai yayi da girgiza kai yayi part d'insa yana dad'a jin mamakinta..
Dan yafi kowa sanin koda wasa NUFAISAT bata shiga kitchen dasunan wai tashiga dan yin girki..
Wato Kishiya ba abinda bata saka mata...
Haka yata surutansa a ZUCIYA.. Har yayi wanka da saka kayansa ya feshe jikinsa da turaransa me maƙalewa azuciya..
Kana ya nufi wani shashi na gidan nasa Wanda yake basa damar ganawa da baƙinsa..

Watoh tunda yau ta kasance asabar.. Baya zuwa asibiti ranar asabar da Lahadi
Kawai yana zuwa kasuwancinsa ne.. Amman kafin nan yana ganawa da talakawa way'anda basu dashi wajen temaka musu daga ƙarfe takwas da rabi zuwa ƙarfe goma..
Toh da zaran ya gama dasu d'inne yake dawowa ga matarsa yaci breakfast d'in daya had'a musu. Kana ya nufi wajen kasuwancin nasa...
Toh yau ƙarfe takwas ya nufi shashin dayake ganawa dasu...
Kasan cewar yau Matar gidan tatashi da himma😀 ta canjesa wajen girka musu abin da zasuci.
_Hmmm yau zaici girkin NUFAISAT_ ya fad'i hakan aransa..

Itako bayan tagama jitayi jikinta ya dauki ƙamshin girkin.. Hakan yasa taqara shaqa wanka tayi shigarmu irinta hausawa. Inda tasaka wata doguwar rigar atamfa... Kasancewar kalan ja da bak'i ne saiya haskata... Ba abinda zai baka sha'awa sai d'aurin data kafa... NUFAISAT nada kyau naban mamaki.. Macece so sweet.. Abin San kowane namiji.. Matsalarta biyuce inji ADAMCY.. shine bata masa shagwaɓa yanda zatana tsuma zuciyarsa.. Kasancewarsa d'an luv.. Sannan bata iya girki ba..
Waƴannan sune matsalar agun ADAMCY..

Falo tadawo duk ƙamshi ya rufeta.. Anan ta zauna ta d'auki wani littafin sister Rahma Nalele me suna *YA FARU AKAN KAINA* daniyar San karantawa..
Saidai kash.. Bai cancanta amatsayinta na

Please Login or Register in order to submit comment