You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta faɗa motor ta tai horn mai gadi ya buɗe get ɗin ta fice,acikin mintina ƙalilan ta isa haraban gidan kai tsaye ɓangaren MAIMUNATU tayi tana nocking ɗin ƙofar MAIMUNA can daga toilet tana watsa ruwa a gaggauce ta watsa ruwan ta fito ta ɗanji daɗin jikin ta tana fitowa ta zira dogon riganta sai pant batasa bra ba ta tako tazo falon ta buɗe ƙofar MOM wayanta na hannunta alaman kira takeyi baa ɗaga ba sai ƙwafa take.












MAIMUNATU ƙaƙalo murmushi tayi tace,"sannu da zuwa MOM ki shigo kisha ruwa",kwantar da murya MOM tayi tace ,"sannu kinji ɗauko hijjab ɗinki muje aabiti,ina ta kiran shi bai ɗagaba","tou MOMU bazaki shigoba?,"a'a kibari har mu dawo","tou MOM",juyawa tayi ta ɗauko hijjab ɗinta da ƙyar take ɗaga ƙafa tafito lokacin MOM harta shiga motor ta juya tana jiranta ƙarasawa tayi ta buɗe ƙofar ta shiga ta zauna yayinda MOM ke mata sannu,horn tayi maigadi ya buɗe get ɗin suka fice.










Aasbiti basu jima ba suka shiga wajen likita ya dubata tare da tambayoyi lab ya turata aka ƴaba jinin ta,ta dawo baa jima ba wata nurse ta shigo da result ɗin a hannunta ta miƙa ma likita,dubawa yayi kafin ya ɗago ya dube MOM fuskansa ɗauke da murmushi yace,"congratulation HAJIYA ƴarki na da cikin wata huɗu",MOM miƙewa tayi cike da farin ciki tanacewa dagaske kake DR ciki ajikin MAIMUNATU,mun gode Allah".












MAIMUNATU soro-ro tayi tana kallon MOM dake farin ciki tana kallon likita mai raina mata wayo da yace tana da ciki shekaran jiya tayi wankan tsarki an taɓa ciki da jinin al-ada tace,"MOM ƙarya yake nifa shekaran jiya nagama period MOM wani ciki,so yake kawai ya miki wasa da hankali",MOM buɗe baki tayi tana kallon MAIMUNATU tana kallon DR da yake murmushi yana kallon MAIMUNATU gyara farin glass ɗin idon shi yayi sabida ya ga tsantsan yarinta a tare da ita hala cikin farko ne bama shakka da tan tama na farko ne yace,"MY SISTER mata kala-kala ne ,akwai mace da zaran ta samu ciki period ke ɗauke mata,wata kuwa sai tayi wata shidda kafin ta dena ganin period ɗin maana duk wata zai rinƴa zuwa mata wani so ɗaya wani so uku ko huɗu ba normal yanda kikeyi da ba akwai macen da bayan ta haihu period na ɗauke mata in har tana shayar wa da zaran ta yaye maana ta cire yaron a nono jini zai dawo mata da zaran ya dawo mata kuma zata samu ciki,akwai kuma wacce take shayar wa tana period tou ke kina cikin masu jini suna da ciki,kuma nasan ba normal kike yi ba kamar da ba".










Cike da gamsuwa da maganan shi MOM tace,"hakane likita nima haka ya faru dani in ina shayar wa bana jini duk da haihuwa É—aya nayi".












MAIMUNATU kuwa ƙasa tayi da kanta tana tinanin tabbas taga yanayin period ɗinta ya canja ba kaman da ba da take sati ɗaya kuma tanajin wani sauyi a jikinta musamman nono ta da suka ciko suna mata nauyi ga ƙaiƙayi da suke mata,ga yawan cin abinci sometimes tana jin abu na ɗan motsawa a cikinta inta kwanta zataji abu na ɗaure wa a ƙasan maranta kuma ga yawan fitsari ta duk ta ɗauka infection ne shiyasa take ta haɗiyan tafarnuwa amma batajin sauƙi,amma miyasa cikin bai fitoba saide tanaji cikinta ya kumbura kullum duk tunaninta basir ne harta ce ma SALEEM ya siyo mata maganin basir cikinta komi taci kumbura yake.








MOM ko DR na mafa bayanin randa MAIMUNATU zata fara zuwa awo tana ta washe baki kamar auduga rubuta musu magunguna yayi ya miƙa mata su saya a pharmacy ansa tayi tana masa godiya suka fice,MAIMUNTU cike da mamaki wai iyace da cikin wata huɗu bata sani ba,ansan maganin tayi suka wutu gida lokacin da ta sauketa a bakin get zata fita tace," ki kulamin da kanki komi kikeso ki kirani zanzo banso ki faɗa ma SALEEM maganan cikin nan harsai ya fito keni zuciyata bai kwanta ba nafiso ki haɗo kayanki mu koma gida can inrinƙa kula dake sosai yanda ya kamata,murmushi ta sake dama zuciyarta a cunkuahe take so take tace zata bita,horn tayi mai gadi yazo ya buɗe get suka shiga parcking MOM tayi sukai fito a tare bedroom ɗinta suka nufa MOM tace ta zauna ita ta haɗa mata kaya tana zaune duk wani abunda zata amfana dashi kafin suka fito,saida MOM ta gargaɗe mai gadi da karya faɗama SALEEM tare suka fita ita ta ɗauke ta inko ya faɗa a bakin aikinsa,jiki na rawa yace inshaAllahu HAJIYA ciro kuɗi tayi masu yawa ta miƙa masa ya amsa yanata godiya da haka suka bar gidan ɗakin kusa dana MOM tasa a ka gyra mata tasa kayanta su MUNAYYA sai murna suke AUNTY su ta dawo MOM jan kunne su tayi tace," ko SALEEM yazo karsu gwada mai tana nan,MUNAYYA da tafishi wayo tace,"tou MOM,shiko MAHAFUZ da maganan ma ba wata iyata yayi ba ya gyaɗa kai.












_MAI MOM KE NUFI DA TACE KAR A GWADA MA SALEEM TA ÆŠAUKO MAIMUNA?_




MORE COMMENTS




_typing🖌️_








*MATAR BAHAUSHE*




_NA MARUBUCIYAR📖🖌️_
*SAMHA*
*ƳARMACE*
*KISHIYA CE*
*JAHAN KHATOON*
*NOOR JAHAN*
_ND NOW_
*SURUKAR ZAMANI ND MATAR BAHAUSHE*




NA *MRS BASAKKWACE*






_GMAIL'S_
*MUHAMMADKHADIJA416@GMAIL.COM*
_OR_
*MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*






SADAUKAR WA GAREKI UWAR MARAYU:-
*HAJIYA HAFSAT MANNIR ÆŠAN IYA UWAR GIDAN MATEMAKIN GWAMNAN SOKOTO (MOMYN IMAN ÆŠAN IYA).*






DEDICATED BY *MY BLOOD SIS KHADEEHATOU S DOGARAI(LIPTON GIRL☕) BAN MANTAKI BA ƘAUNAN KI A JINI NA YAKE LUV U LODI-LODI.😘*










*DEDICATED 2 ƳAR UWAN MU SAKINA GUSAU ND FATEEMAH MAINA*






*SHAFI NA TALATIN DA BIU DANA TALATIN DA UKU 32 &33*






*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI.*










MAHAFUZ da magana ba wata iyata yayi ba ya gyaÉ—a kai.










SALEEM bai farka ba sai 12:45pm kafin ya farka daga nau yayyan baccin da ya kama shi tun daran jiya da ƙyar ya tashi yai sallah asubah a ɗaki inda yai sallah anan yai baccin,tinani yake mai ya faru dashi kamar yasha ƙwaya duk a iyakan tunanin sa bai gano mai ya hadasa masa baccin nan ba gashi zaije office miƙewa yayi a gaggauce ya faɗa toilet ya watso ruwa tare da ɗauro alwala yafito ya shirya jallabiya kawai ya zirah ya feshe jikin sa da turaruka ya sa hula wayanshi ya ɗauka don yasan zaisha kira daga wajan AMMAR ganin miss call rututu yasa gaban shi ya faɗi na MOM duk yafi yawa gana MAIMINATU gana mutane da yawa MOM ya fara kira amma wayan harta gama ringing baa ɗaga ba,yakira MAIMUNTU wayar a kashe,gaban shi faɗi yayi,jin an tada sallah yasa ya zira wayan a aljihu yafito a gurguje a falo ya isketa tayi ɗaiɗaya kannan tuja-ja kauda kai yayi ya fice.










Zaune take kan nan tujaja riga daban zani daban kai ba kalabi ta dafo indomie da kaza ta zauna tana taci kamar mayuwa ciya da baisan gidan su HANEEFA akwai kuɗi ba da yace bata taɓa cin indomie ba,itako da kallon raini tabishi har don haushin shi takeji da bata sa masa maganain bacci ba da yanzun ya fice a gidan nan sai goma zai shigo mata amma in yana ɗakin karuwan can tunkafin mangariba ya shigo shiyasa ta sayo maganin bacci taje ta zuba masa a dudu milk ɗin dake cikin firich ɗin ɗakin sa lokacin yashiga toilet ta girgiza dariya ta sheƙe dashi kamar sabon taɓin hauka.










Dawo-wa yayi ua isketa inda ya barta nan ya isketa cike da takaici yace,"ina break ɗina?,ɗagowa tayi ta yatsina fuska tace ,"kaje kitchen akwai sauran wanda na dafa yana nan a tukunya na ajema",girgiza kai yayi in halin HANEEFA ne ya gama sani baabin da ta canja kuma baisan randa zata canja ba,"tace," yauwa account ɗina yayi low kuma ina da bikin ƙanwar ƙawata MARIYA inaso miyi bikin kece raini,tana maganan tana lasan yatsu,kallon ta kawai yakeyi baki sake.








Girgiza kai kawai yayi ya nufi kitchen zuciyar shi cike da tinanin second wife ɗinsa mai son shi da tattalin sa in yana ɗakin bata da lokacin kanta in ba nashi ba ko ƙwaƙƙwaran motsi yayi sai tace lafiya honey,sai yace bakomi,bata iya cin abinci sai taga ta ciyar dashi ya ƙoshi kitchen ɗin ya shiga komi a hargitse wanke-wanke tuli guda ga baƙin tukunya duk ya ɓata kulolin ta ga indomie da tace ta aje masa a buɗe har kyankyaso ya faɗa bin tukunyar yayi da kallo yana girgiza kai juyowa yayi ranshi ɓace yafito falon yana ƙwala mata kira.










"Lafiya kake ƙwala min kira kaman kana bina bashi".








"Nunata yayi da ɗan yatsa yana faɗin banson iskanci banza da rainin wayo halin ki fa ya isheni ya kaini maƙura miye bana miki a gidan nan da kike misguna min haka HANEEFA?








Miƙewa tayi ta riƙe ƙugu tana watso mai wani kallon raini tace,"SALEEM mai ka taɓa min da kake cewa kana min komi auran ka auran ƙaddara airan tauye haƙƙina da kake yi miye banda shi na mace wanda bai maka ba sakamakon da kamin dashi shine kishiya aiko baka min komi ba illa cin amana ta da kayi".








Dariya mai cike da takaici yayi kafin ya haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba yace,"kinyi kuskure HANEEFA bazaki san kin tafka babban kuskure ba sai nan gaba nayi dana sanin kallon ƙyalƙyali waje dana aure ki banyi tunanin naciki ba MATAR BAHAUSHE sai Allah komi mijinta yai mata bata gani balle ta gode masa rayuwanta a rainuwa yake bazan sakeki ba amma ki guje ranan ɗaukan mataki"yana gama faɗa baijira mizata kuma cewa ba yasa kai yabar wajen yashiga ɗakin sa key ɗin motor shi ya ɗauko yafito ya fice ,rakashi tayi da tsaki.










Kai tsaye gidan MOM ya nufa ba tare da yayi tunanin shiga ɓan garen MAIMUNATU ba,koda ya isa ita kaɗai ce a falon tana zaune tana waya tanaganin shigowan shi ta ƙara haɗe rai taci gaba da jan magana,zama yayi a gefen ta yana jira ta gama amma yaga ba ranan da zata gama takamo wancan hiran in an bar wancan.










Miƙewa yayi ya nufi dining ya zauna yasa abinci yaci har ya gama ci bata gama wayan ba dawowa yayi kusa da ita saida ta gaji don kanta kafin ta yanke wayan ba tare da ta dube shi ba ta miƙe zata bar wajen kamo hannun ta yayi ya marairaice murya yace,"kiyi haƙuri MY LOVLY MOM".








Harara ta juyo ta galla masa,dole yasa ya sake ta cikin kakkausan murya tace,"wani aiki kake da har zankira ka baza ka É—auka kafaÉ—a min uziri ka ba".








Marairai cewa yayi tare da yin ƙasa da murya yace,"MOM kiyi haƙuri bacci ya kwashe ni mai nauyi".






Cike da mamaki take kallon sa tace,"...............!












MORE COMMENTS
MORE TYPING




_typing🖌️_








*MATAR BAHAUSHE*




_NA MARUBUCIYAR📖🖌️_
*SAMHA*
*ƳARMACE*
*KISHIYA CE*
*JAHAN KHATOON*
*NOOR JAHAN*
_ND NOW_
*SURUKAR ZAMANI ND MATAR BAHAUSHE*




NA *MRS BASAKKWACE*






_GMAIL'S_
*MUHAMMADKHADIJA416@GMAIL.COM*
_OR_
*MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*






SADAUKAR WA GAREKI UWAR MARAYU:-
*HAJIYA HAFSAT MANNIR ÆŠAN IYA UWAR GIDAN MATEMAKIN GWAMNAN SOKOTO (MOMYN IMAN ÆŠAN IYA).*






DEDICATED BY *MY BLOOD SIS KHADEEHATOU S DOGARAI(LIPTON GIRL☕) BAN MANTAKI BA ƘAUNAN KI A JINI NA YAKE LUV U LODI-LODI.😘*


_TUKUYCI GA ƳAƳANA ƳAƳANA GARI ƊIYAN ALBARKA_
*ASMA'ULLAHIL HUSNAH,MUHAMMAD NASEER,MUHAMMAD ARABI,MUBARAK,MUHAMMAD ADNAAN IBRAHIMUL KHALEEL,AMEEMATOU ND UMAR FARUƘ,ALLAH YA RAYAMIN KU YA ALBARLACI RAYUWAN KU YASA ALUMMAN MUSULMAI SU ANFANA DA KU🙏*






*DEDICATED 2 SAKKWATAWA MUTANAN MU ZAMHWARAWA ƳAN UWAN MU KABAWA MAƘWAFTAR INAYINKU SOSAISOSAI DANGI YAFI KOMI DAƊI🥰*






*SHAFI NA TALATIN DA HUÆŠU DANA TALATIN DA BIYAR 34 &35*






*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI.*












Cike da mamaki take kallonsa tace,"bacci kuma?






"Eh MOM",ya faÉ—a yana gyaÉ—a kai.






Giriza kai tayi tace,"Allah tou ya kyauta".








"Ameen",ya amsa a taƙaice,shiru ya biyo baya ,ita MOM bata zauna ba shikuma yana duƙe.






"Tashi ka zauna nifita zanyi mayafi zan É—auko inje gidan HAJIYA AA'I".








"Nima MOM office zan leƙa,in rage aiyuka".








"Ameen MOM,wai inasu MUNAYYA?






Murmushi tayi tace,"suna can suna bacci".








Yace,"ok inna dawo na gansu",miƙewa yayi yamata sallama fatan alkhairi tayi masa ya fice,mamaki ya bata da bai tambayeta miyasa takira shiba,shiyasa tai shiru.








MAIMUNA kuwa MOM ri-rita-ta take kamar ƙwai komi tace tana sha'awa zata sa ayi mata,ga ƙannanta baibaye da ita hakan ba ƙaramin farin ciki yasata ba.








*WASHAGARI*
Yau ta kama MAIMUNATU keda girki SALEEM sai ɗauki yake da rawan kai zaiga hasken zuciyar shi,abinda yake damunsa tun jiya yake kiran wayanta a kashe,ko ɗan text ɗin da take masa ranan da ba girkinta ba bata masa ba,hankalin sa duk atashe yake a tunanin sa fushi tayi shiyasa ya ƙosa ya bar office,don zama sashin HANEEFA ji yake kaman yana kan ƙaya duk a takure yake mata kamar jaka ba tarairayan miji ba kwalliya,ba tsafta,abinda tasani kawai ya bata kuɗi,in ba abin biyar a side ɗinta bazata iya cirewa ba tasaya sai ya dawo kullum bani-bani,gashi bata godiya Allah komi aka bata ta raina idon rainuwa gareta kamar *(MY SAKNAH ƳAR GUSAU SHIYASA SALIM MAMUDA GUSAU YA GUDU😆🏃‍♀️)* saɓani MAIMUNATU shi komi ya kawo duk ƙan-ƙantan sa a ladabce take ansa taita gode ma bata da rainuwa ko kaɗan yanzun maigadi ma yadena zuwa siyan abinci,ita ka zuba masa,ko kuɗin cefane ya rage aje masa take in yadawo ta bashi,saida yace tadena bashi ta ringa riƙewa shine dalilin da yasa ta dena bashi canjin cefane.








*MATA MUJI TSORON ALLAH,YANZUN MATA NAWANE SUKE DA HALIN MAIMUNATU ACIKIN MU NA TABBATA ACIKIN KASHI ƊARI 100% DA WIYA ASAMU 10% ACIKIN MATA MASU RAGE CANJI CEFANE SU RINƘA BA MA MIJIN SU ,YA KAMATA MUGANE WANI ABU KUMA MUSANI,INFA KUƊIN CEFANE YA RAGE MIN ƁOYE MUNKAI GIDAN ADASHE WALLAHI BA HALAL BANE HARAM NE DAIDAI YAKE DA ƘUƊIN SATA,AMMA YANZUN ALLAH-ALLAH MUKE MAI GIDA YA BADA KUƊIN CEFANE MUGA NAWANE RIBAR MU MU HAƊA MI ZUBIN ADASHEN WATA-WATA KONA SATI-SATI,ALLAH DE YA KYAUTA ,AMMA YA KAMATA MU SANI WANNAN CANJIN FA BA NAMU BANE HANƘƘIN MIJI NE WALLAHI,IN BAI BAMI BA SAI MIN BIYASHI RANAN GOBE ƘIYAMA,ALLAH YASA MU DACE MUFI ƘARFIN ZUƘATAN MU AMEEN.*










*BARI IN ƊAN YI TSOKACI AKAN MATA MARASA GODIYA AKAN DUK ABINDA MIJIN SU YE MASU,MATA DA YAWA BAMA DA GODIYA IN MIJIN MU YA KAWO MANA ABU WATA A WULAƘANCE ZATA ANSA WATAKO INDA YA KAWO YA AJE NAN ZATA BARSHI SAIDE TASA ƳAƳA SU ƊAUKE KO ƳAR AIKI BA GODI BARE NA GODE KOMI YAYI BAKI GANI KULLUM RAYUWAR KI A RAINUWA YAKE,INKO KINA SO KI RIƘE MIJI KI JUYA SHI BA BOKA BA MALLAN NAMIJI YANASO A RINƘA TARAIRAYAN SA KOMI YAYI ARINGA YABA MASA IYA GIRKI IYA KWALLIYA TSAFTAN GIDA DA ƊAKIN KWANAN SA IN YADAWO AIKI YA GANKI ACAN ACAN KINYI KYAU KAMAR YA WANKE HANNU YATAƁA AMMA BA WAI YA DAWO YA ISKEKI KAMAR YANDA YA BARKI BA DA KAYAN BACCI,KAMAR WATA (FATEEMA ZAHRA MOM JIDDA MY SURUKAR ZAMANI KAWAI😆 ƘAZAMA CE SOSAI BATA WANKA KAMAR HAJIYA HANEEFA TA LITTAFIN MATAR BAHAUSHE,GA RASHIN KITSO),KAI BARI IN TAƘAITA NASAN KUN GAJI DA SURUTUNA,AMMA WALLAHI NASAN DA AKWAI WACCE RABONTA DA TACE MA MIJINTA I LUV U TUN TANA AMARYA😂,IN KUNASO KUJI WANENE ITA PC ME😉,ALLAH YA SA MU DACE,ALLAH YA BAMU IKON SAMUN ALJANNAR MU A ƘARƘASHIN ƘAFAR MAZAJEN MU AMEEN YA ALLAH🙏.*






*_FANS NIFA HAKA NAKE A ZAHIRI DA BAƊINI NA IYA TONON FAƊA,DAN HAKA KOWA TA ƊINKA WANDO IN NA TONO NAZO BAYANKI SAI KI SAKA ABINKI.😎_*








05:30PM dai-dai yai parking fitowa yayi niƙi-niƙi da ledoji baƙaƙe ya nufi ɓangaren MAIMUNATU tunda ya doshi ɓangaren gabansa ke faɗi innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai yake nanatawa har yakai bakin ƙofar falon sa hannu yayi ya murɗa ƙofar yayi yaji kulle,saki key yayi ya buɗe ƙofar don yasan tana kullewa sabida gudun tujaran HANEEFA sa kai yayi cikin falon duhu ya mamaye idanuwanshi kacancewar ko ina a kulle yake kuna wutan ɗakin yayi yana faɗin BABYLUV-BABYLUV,jin shiru ba ansa ba yasa ya zubar da ledojin ya nufi bedroom ɗinta donde bata taɓa masa haka ba duk a tinanin sa bata da lafiya ganin ɗakin wayam yasa ƙirjin sa ƙara yankewa ya faɗi duba toilet yayi nan ma bakowa da sauri ya fito ya nufi kitchen duk baiji ƙamshin da ɗaɗan girkinta ba nan ma wayam,dafa goshin shi yayi yana tunanin ina taje ba ta faɗa masa ba yasan bata fita ko bakin get inba izinin sa ciro wayan shi yayi a aljihu ya dai-daita na tsuwar sa ya kira number MOM ringing biyu ta ɗauka bayan sun gaisa shiru ya biyo baya na ƴan daƙiƙa,MOM ta katse shirun da yaya dai BOI,dariyan yaƙe yayi.








Kafin yace,"MOM dama zan tambayeki MAIMUNATU ta tahone in biyo in É—auketa na sauketa gidan kitso tace in angama mata zata taho gidan ki in na taso office sai in biyo mu wuce".








MOM buɗe baki tayi tana kallon MAIMUNA dake zaune ta zauna ta miƙe ƙafa tana ta gwaguyan goriba gasu MAHAFUZ na gefe suna game,mamakin SALEEM kawai take da ya iya karkacewa ya watso ƙarya wato bai ma san bata kwana gidan shi ba sabida halin ko inkula nasa,gayaran murya tayi tace,"aa aiko batazo nan ba ƙila tayi gida".










Gaban shi faÉ—i yayi dummmmmmmm jin abinda MOM tace,cewa yayi "ok", ya kashe wayan .










Fita yayi a gaggauce ya nufi inda mai gadi ya tambaye shi ko yaga fitan ta yace mi aa baigan taba bata fitaba.










Ɓangaren HANEEFA ya nufa ya tura ƙofar ya da sauƙi tayi gyara ta sa turaren wita ɗakin sai ƙamshi yake tana zaine tayi wanka taci kwalliya kamar mai shirin zuwa unguwa,ganin yanda ya shigone yasa ta ɗaugo ta wani watsa masa kallon raini.






Cikin tashin hankali yake tambayanta ina MAIMUNATU?






"MAIMUNATU tana na nata tace,"waye kuma da wannan sunan?








Harzuƙa yayi jin yana tambayanta tana tambayan shi yace,"mata-ta mana banson raini hankali".








Sheƙewa tayi da wani dariya irin na rainin wayo tace,"dama sunan ta kenan ai ban sani,wai shin ajiyarta ka bani koko nono take sha ka taɓa bani ijiyanta ko nine mai gadi je ka nemo inda take waya sani ma taje wajen samarinta ne dama can gantalalla c......!.










Saurin da katar da ita yayi ta hanyar É—aga mata hannu tare da daka mata tsawa idanuwan shi sun rine sunyi ja kamar garwashi cikin kakkausar murya yace................!












MORE COMMENTS
MORE TYPING🖌️




_typing🖌️_








*MATAR BAHAUSHE*






NA *MRS BASAKKWACE*






SADAUKAR WA GAREKI UWAR MARAYU:-
*HAJIYA HAFSAT MANNIR ÆŠAN IYA UWAR GIDAN MATEMAKIN GWAMNAN SOKOTO (MOMYN IMAN ÆŠAN IYA).*






DEDICATED BY *MY BLOOD SIS KHADEEHATOU S DOGARAI(LIPTON GIRL☕) BAN MANTAKI BA ƘAUNAN KI A JINI NA YAKE LUV U LODI-LODI.😘*












*SHAFI NA TALATIN DA SHIDDA DANA TALATIN DA BAKWAI 36&37*






*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI.*










__________📖Cikin kakkausar murya yace banson maganan banza HANEEFA,karki ƙara dangana min mata da lalatattu don sabuwa fil na buɗeta da hannuna,sam na ragowar maza bace".








"Uhm sai ka gwada ragowar maza".






Tai maganan cike da rashin kunya.






Girgiza kai kawai yayi batare da ya kuma cewa uffan ba yasa kai yabar É—akin.








Da uwar harara tabishi tana ƙwafa.






Shiko motor shi ya faɗa ya bar haraban gidan bayan mai gadi ya wangale masa get,yawo yarinƙa yi har ƙarfe ɗayan dare cikin gari yana dubedube koh zaiganta amma tayi ɓatan dabo bata ba labarinta daga ƙarshe gefen titi ya samu yai parking ya dafa kansa da yake sara masa da hannu bibbiyu yana tunanin ina mafita miyasa MAIMUNA ta masa haka ina taje ne haka,miyasa ta zaɓi guduwa ta barshi,wani sashen zuciyar shi ko cewa yayi ba guduwa tayi ba ƙila sace ta akai don ko ta gudu ba inda zata,Innalillahi'wainna ilaihi'rajiun ya furta a fili, wasu hawaye masu ɗumi suka zubo masa akan kumatu wa ƴanda bai san sanda suka zuboba,in taƙaice muku anan wajen ya kwana yanda yaga rana haka yaga dare ga kansa na sara masa kamar zai sauka ƙasa,da asubah da ƙyar ya buɗe motor yanufa wani masallaci yabi jam'i bayan an idar ya dawo ya shiga motor sa ya nufi gida a bakin get ya tsaya ya tambaye maigadi ko MAIMUNA ta dawo yace masa a'a hankalin shi ƙara tashi yayi.










Bai san sanda ya kuma ƙara barin ƙofar gidan ba tsintar kanshi kawai yayi a harabar gidan MOM baisan sanda yazo ba gaban shi tsanan ta faɗi yayi duba agogon hannun shi yayi yaga bakwai da kwata,wani sashe na zuciyar shi tace miya kawo ka gidan MOM salon ka tona ma kanka asiri,ɗayan sashen yace kashiga kawai ka sanarda ita halin da ake ciki tun wuri tunkafin dare yama,nan ya rinƙa tufka da war-wara,da ƙyar ya tattaro jarumtar sa ya buɗe gambun motor ya fito jiki asanyaye yanufi hanyar part ɗin MOM kallo ɗaya zaka masa kagane baya cikin hayyacin sa idanuwan sa sunyi zuru-zuru duk sun kumbura,nocking ɗin ƙofar falon yayi.










MOM da yanzun ne sakkowanta riƙe da hannun MAHFUZ da MUNAYYA sanye da uniform ɗin su milk nd nevy blue kowanne su goye da school bag ɗinsa,ƙarasawa tayi ta buɗe ƙofar cike da mamaki take kallon sa da sassafen nan kamar ankoro sa kallo ɗaya ta masa ta fahimci ya gane MAIMUNATU ta ɓata daga gani baiyi bacci ba cikin tashi hankali ya kwana dagani idon sa bai samu bacci ba wani tausayin shi taji ya saukar mata a cikin zuciyarta a zahiri kocewa tayi.










"Lafiya MY BOI ko MAIMUNATU ce ba lafiya naga kayi ƙozai-ƙozai ha sammako da sasaafen nan?








TafaÉ—a cike da mamaki.








Hawaye masu É—umi da maisan sanda suka sakko masa ba sanda yayi tozali dasu MUNAYYA dake kan dining sunyi tagumi.










MOM ƙara gwalo ido tayi tace.






"Kamin bayani kasani cikin ruÉ—ani waya mutu?














Rungume MOM yayi ya fashe da kuka............!








MORE COMMENT
MORE TYPING




_typing🖌️_








*MATAR BAHAUSHE*






NA *MRS BASAKKWACE*






SADAUKAR WA GAREKI UWAR MARAYU:-
*HAJIYA HAFSAT MANNIR ÆŠAN IYA UWAR GIDAN MATEMAKIN GWAMNAN SOKOTO (MOMYN IMAN ÆŠAN IYA).*






DEDICATED BY *MY BLOOD SIS KHADEEHATOU S DOGARAI(LIPTON GIRL☕) BAN MANTAKI BA ƘAUNAN KI A JINI NA YAKE LUV U LODI-LODI.😘*




*GODIYA DA JIN JINA GAREKU BASHEER SARDAUNA nd ABUBAKAR SARAKI INA GODIYA DA KULAWAR KU GARENI ALLAH YA BAR ZUMUNCI.*






*SHAFI NA TALATIN DA TAKWAS DANA TALATIN DA TARA38&39*






*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI.*










__________📖Rungumo MOM yayi yana fashewa da kuka.




MOM shafa bayan shi tasa hannun ta tanayi tana ɗan bubbuga bayan shi jan shi tayi zuwa kan kujeran falon ta zaunar dashi tare da zama gefen shi ta riƙo hannayen biyu ta sa anata tana fuskan tanshi tace.






"FaÉ—a min MY BOI miye damuwan?.








Tsura mata idanuwa yayi na mintina zuciyar shi na tsanan ta bugu kamar bazai magana ba yana nazarin wani ahankali ya buÉ—e baki yace.








"MOM MAIMUNA ta ɓata bansan inda taj.........!






Baikai da ƙarasawa ba MOM ta miƙe a hasale ta ɗauke shi da mari a fuska har guda biyu hakan yasa shi maƙale sauran maganan shi.








"Minake ji SALEEM mai kai ma ƴar mutane SALEEM dama wulaƙanta ta kukeyi kai da matar ka alƙawarin da ka ɗauka kenan ƴar amana zaka banzartar ka wofintar,tun jiya dama yanayin da kakirani nasan baka da gaskiya wallahi SALEEM tun wuri ka wuce kaje ka nemo ƴar mutane runkan raina yayi mummunan ɓaci akan ka,ko dan kaga basa da galihu ba wanda zai tuhume ka shine ka watsar musu da ƴa tou wallahi kar in ƙara ganin ƙafar ka a gidan nan matuƙar baka nemo ƴar mutane ba".






Cike da ɓacin rai take maganan,wanda azuciyarta tarin tausayin ɗan natane tama kanta alƙawari saita hukunta shi kafin yaga MAIMUNA.








"MOM ki haÆ™....!".




Cikin sanyin murya ya fara maganan jikin sa har rawa yake .










"Dakata fice min a gida,banso in ƙara ganin fuskarka matuƙar bakaje ka nemota ba".








Cikin tsawa ta dakatar dashi,tare s fara magana cike da ɓacin rai.






Zai ƙara magana mugun kallon da ta wurga masa yasa yayi shiru amma ya kasa ko motsi.








Da gudu ta juya ta faɗa bedroom ɗinta matsanan cin kuka take sosai don tunda MOM tafito ta biyo bayansu kan ta ƙarasa sakkowa taji kukan SALEEM take ya taɓa mata zuciya tsawaya tayi taji mai zaifaɗa ma MOM sanda MOM ta mareshi sai da tai saurin

Please Login or Register in order to submit comment