You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng ˙ūGABATARWA

da sunan Allah me rahma me jinkai tsira da aminci su kara tabbata ga manzon tsira manzon rahma (SAW) ina farin cikin gabatarda wannan littafin tareda fatan zai amfanar da iyayenmu mata allah yasa

albarka acikinsa.

BIKIN  YAR GATA session1

"Aduk lokacinda kika hadu da namiji amatsayin mijin aure Wanda zakuyi rayuwa ta har abada ki tuna da abu guda KIMAH, wanda itace ginshikin  ya mace domin duk wani farin ciki da zaki saka namiji awannan duniyar koba Dade koba jima wataran zai iya man tawa"

"amma kimah da daraja awajen miji sune zaisa ki zama abun misali, shikuwa misali kullum nunashi akeyi ba a mantashi"

"wannan itace hudubar mahaifiyata wanda tun ina karama Na kasa mantawa da ita har izuwa yau Wanda hidimar bikina ta gama karade cikin garinmu a tunanin mahaifiyata nice kadai mace da zata zamo abin misali,"





"tun ina karama na fahimci burin mahaifiyata gaba daya akaina yake kasancewar ni kadai ta Haifa ta dora duk wani saka rai akaina yayinda tasha alwashin mayar dani mace me kimah da daraja acikin al umma sannan daga karshe na zama sarauniya awajen mijina saidai ni kaina bansan cewa na ruguza wannan burinba kafin aje ko ina na rasa duk wata garkuwa inda na rasa abu mafi muhimmanci awajen  ya mace,"

Da akwai wani yaron gidanmu amintacce daga iyayena wanda cikin nutsuwa da taka tsantsan mahaifiyata ta daukoshi daga cikin danginta ta mayar dashi dan gida domin dora masa alhakin kaini makaranta

"Amma abinda ko kadan baizo ran mahaifiyata ba shine wajen tarbiyar mace ba a bukatar namiji a tareda ita koda kuwa dan uwanta ne,"





"haka tayi wannan kuskuren yayinda ni kuma na daukeshi amatsayin yayana ashe nawa kuskuren yafi nata muni,"

Da farko yayi kokarin samun soyayyata ba tareda sanin mahaifiyataba muke soyayya wanda shine dalilinda yasa ya mayar dani tamkar matarsa mahaifina baya zama haka zalika mahaifiyata tana zuwa aiki wannan itace damar da muka samu wanda saida muka shafe shekara biyu ahaka yanzu kuma an samomin miji da zan aura wanda yakai kowacce mace tasoshi koda yake na aikata mafi girman kuskure amma nasan cewa kaddara abace mara tabbas kowanne lokaci tana iya sauyawa& & .





"Akwai hanyoyi uku da nake tattaunawa da mutane akan abinda ya shafi rayuwar aure,"

"na farko shine mutum ya kira wayata Na biyu ana iya samuna ta media wato chat,"

"Na uku kuma mutum yazo kai tsaye mu tattauna,"

"To shine wannan baiwar allah ta zabi zuwa daga nisan duniya kai tsaye ofishinmu tattaunawa dani domin dalilai biyu,"

"v'na farko shine abunda ke faruwa tsakaninta da dan uwanta wanda tana ganin dole wanda zata aura ya gane ita ba budurwa bace,"

w'abu na biyu kuma mahaifiyarta ta bukaci ta nemo duk wani ilimin zaman aure tareda koyon gyaran jiki don tanaso ta zama abun misali wajen sauran mata





tofa shine ta kare duk wani tunaninta amma ta rasa wane garine yafi ko ina iya gyara mace?

"Abu mafi muhimmanci da zaki fara sani shine bakida budurci don budurcin mace dayane ba lallai a saduwar farko ko ta biyu ya bude ba amma bazaiyu ayi shekara ana saduwa da mace kuma ta zama budurwa ba saidai tayi matsi wanda zai matseta sosai ta yanda kofar zata hade kamar na budurwa wannan kam zai yiwu saidai ba asamu ingantaccen magani tareda shawarwari ba,"

Abu na biyu shine sirri wannan sirrin ba a fadawa kowa ballantana wanda zaki aura saidai wanda zaki sayi magani wajensa ko likita idan zakiyi dinki





"wannan kuma ya zama dole don itace hanyarda za a gyara matsalar,"

"Sai kuma abu na karshe shine magani wajen neman magani kuma dole kina bukatar sirri kyan samu kisayi maganin tayanda saidai kawai kina amfani dashi ba tareda sanin mahaifiyar kiba, gabaruwa da aloebera"

Idan kika kona gabaruwa ruwan zai fito to shine zaki hada da ruwan aloebera kiyi matsi bayan sa'a daya ki wanke

Sannan kisamu kanunfari kizuba agarwashi kiyi tsuguno akayi sanna kizama me yawan matsi da miski





Wannan kuma ganyen gwaiba mai kyau zaki samu ki wankeshi saiki tafasa sosai Idan ya tafasa saiki zuba acikin wani ma zubi da zaki iya shiga sai kinyi mintuna goma saiki fita sannan kisamu gabaruwa da kimba kadai ki tafasa su sosai kinasha ruwan safe da yamma.





Wannan kuma man kwakwa ake hadawa da zuma da aloebera da man zogale a dafa ana matsi dashi

Ana iya jika kwaro da man kadanya da ruwan aloebera sai man zogale ana matsi dashi kullum zuwa kwana10





1 alobera (aloevera)

2 Karo (jirai)

3 man zaitun (olive oil) 4 kanunfari (Cloves)

ki sami alobera da Karo ki saka kanunfari ki tafasa saiki tace ki ajiye ruwan ya zama shine ruwan tsarkinki





idan kuma kinaso kiyi sha yanzu magani yanzu to ki matse ruwan alobera saiki hadashi da man zaitun kiyi matsi dashi gam gam kenan

"kina iya hada itatuwan matsi wanda muke hadawa me jego na wata daya, wannan shine ma yafi dacewa dake kisamu dan bagigita sauyar bagaruwa ko bawonta da sauyar lalle da bawon tsafau sauyar kalgo wadannan itatuwan zaki dafa kina tace ruwan kina tsarki dashi sannan kina zama aciki na tsawon mintuna goma."

Wannan shine karshen shawara daya kamata abaki dama me matsala irin taki koda yake shima kansa rasa budurci yana bukatar bayani amma kedai bakya bukatar kowanne bayani kasancewar tuntuni kin rasa naki amma idan kikabi wannan hanyar insha allahu bakida wannan matsalar.

Maganar gyaran jiki kuma a zahirin gaskiya bazai yiwu mace ta samu wayewar kai akan gyaran jiki yanda ake bukata kuma a waje dayaba dole saikin dage da bincike daga sassa daban daban domin hakan yanada matukar tasiri wajen sanin abubuwa da wani wajen da





"ba'asan dasuba amma dai tunda kinzo wajenmu zaki samu cikakken bayani,"

Awannan kasar akwai manyan garuruwa wadanda suka kware matuka wajen maganin mata harma dana maza wanda zaka samu kusan kowanne gari akwai

baiwar da allah yayi musu na gyaran jiki.





SOKOTO

haryanzu babu wani gari dayakai jihar sokoto sanin maganin mata

saboda kusan sune tushe akan maganin gyara mace wani abun mamaki basu damu da sihiriba sudai sunfi damuwa da maganin gari da ruwa zallah wadanda haryanzu babu wani gari daya kama

kafarsu ballantana yakaisu shiyasa nake





"matukar kaunar mu'amala da yan sokoto saboda nasan akwai dumbun ilimi awajensu,"

to saidai akwai wani karin abun mamakin shine sunfi kowanne gari shan wahala awajen namiji dukda wannan sanin magani da allah yabasu amma sun gaza wajen iya kissa me jan hankalin miji wannan yasa suke fuskantar babban

"kalubale awannan fannin,"





akwai tsumi Dan sokoto haka zalika zuma itama akwai yar sokoto wanda duk inda kaje awannan kasar dama kasashen ketare kanajin labarinta saidai yanayin kayan hadin ya banbanta amma dai sune

"musabbabin samuwarta,"





"sassaken baure Dana gamji sai kuma icen malmo dana zogale,"

"anasaka kanunfari da minanas sai Dan bashanana da iccen kukuki,"

wadannan icen ake dafawa atace ruwan sai a gurza kwakwa da ruwan kwakwa da Zuma shikenan ana bawa amare sunasha

safe sa yamma Na tsawon sati biyu.





itama Zuma yar sokoto ta dade da shahara koda zaku duba rubutuna Na baya akwai ta domin hadata ana bukatar

1 baure

2 marke

3 kukuki ko kuma dan bashanana





"wadannan kadai sun isa adafa atace ruwan sai azuba zuma wanda adadinsu zai zama daya (misali) idan ruwan ya cika kofi to itama zumar zata zama cikin kofi sannan anason zumar ta zama asalin zuma ta gida, mace tana iyashansa sau"

"biyu arana,"





sannan akwai wata zumar itama dai anan garin sokoto Na sameta

bawon kankana bawon cocumbar bawon kabewa yayan minannas

kanunfari

Wadannan kisan yanda zakiyi su zama

gari suyi laushi sosai saiki hada da Zuma fara me kyau yar gida shikenan





saiki gauraya sosai ki ajiye kullum da safe kafin kici komai kisha cokali3 da dare idan kinzo kwanciya kisha cokali3 wannan kowacce mace zatayi koda budurwa me shirin aure dandano awajen

mace koda mijinki miskiline zaki gane.

"bazaka taba samun gari wanda mace ke bautawa miji irin borno ba, mace ashirye take data bada rayuwarta don farin cikin"

"miji,"





magani kuwa idan akazo bangaren mallaka ai duk inda kaje saika dawo maiduguri domin kusan duk wani maganin mallaka da zaka bincika asalinsa zaka samu yanada nasaba da maiduguri koda yake wani mallaka din yana sabawa addini amma hakan be hana tururuwar al'umma zuwa wannan gariba don kawai neman hanyar zaman lafiya da

"miji,"

kayan kamshi kuwa sune tushensa don kuwa kusan babu inda zakaje baka samu turaren dakin amare irin na meduguri ba dan haka idan har mace nason kwarewa akan harkar gyara dole saita hada hannu

"da yan meduguri,"

yajin mallaka

nayi kokarin samun mallaka awannan Garin Wanda zai zama be sabawa shari'a ba shine nayi arba da wani hadin yaji

Wanda yake saka dadin abinci





"sannan da dandanonsa wannan ya dade da bayyana wannan kasar amma kasancewar kayan hadinsa ba'anan kasar ake samuba saiya bace gaba daya,"

hakika Na dade ina mamakin wannan al'amarin domin itatuwa da ganye ake hadawa amma da zaran an saka wannan yajin acikin abinci tofa duk Wanda yaci wannan abincin saiya bukaci kari to wannan dabarar matan suka gano ta yanda idan suna sakawa duk inda namiji yaje saiya dawo gida yaci abinci anan ana hakan idan miji baya damuwa dacin abincin matarsa duk yanda take kokarin

"yinsa yayi dadi,"





"tabbas wannan yakai a mallaki zuciyar miji,"

lokacinda mutum ya hada wadannan itatuwan saiya samu sauran kayan yaji kamar maggi da citta shikenan duk lokacinda kikazo dafa abinci tofa ki zuba

"kadan,"





iccene Wanda shikadai ana iya cinsa yanada dadi sosai



wata ciyawace Wanda da zaran ka kai hannunka zata kama tamkar



"kurar karfe,"

yana danye yanda kasan gam haka zai kama hannunka



"shima dai wannan shi kadai mutum Na iya cinsa,"







cikin nutsuwa mutanen borno suka samoshi a yankin Camaron Wanda saida Na shafe kusan mako guda kafin sanin sahihancin wannan yajin hakika ya inganta kasancewar itace da ganyene

babu sihiri acikin sa.

"Sai wani Karin mallaka din amma shi wannan shafawa akeyi da auduga kana abarshi ya dade sai awanke hadine na mallaka ga jawo hankalin miji izuwa saduwa saukin kai wajen soyayya zaman lafiya babu fada sannan yakan hana namiji neman mata,"





"Akwai mayika da akeso kamar man zakara da man damo to dama anaso asamu furen biyarana dana dan mannau ayi garinsu sai akwaba da zuma wannan mayikan sai ahadasu waje daya a dora akan wuta yana tafasa ana juyashi har saiya dafu,"





"tumbin giwa kenan koda me kazo anfika musamman iya kwalliya da gyaran fata da kissa wajen jawo hankalin miji wannan kam tabbas komai kwarewar mace idan tazo kano za'a koya mata, matan kano suna iya gamsarda namiji ta hanyar kalamai kadai wadanda suke"

dauke da shagwaba da kissa





"cikin shauki wanda iya wannan ya isa ya gamsarda namiji,"

"to idan kinason zama sarauniya awajen mijinki dole saikin koyi wadannan,"

"gyaran amarya daga wasu kasashen ana kawowa amare don kawai ahadasu kana ganin amarya kasan ta hadu,"

Amma akwai abunda ya kamata mu duba shine rashin jin sha awar amare yanda mace tana budurwa tanajin sha awa amma da zaran anyi aure saita zama babu ko kuma tanajin sha awa din amma

"babu jin dadin saduwa,"





"Abu biyu sunada matukar muhimmanci ajikin dan adam wajen sha'awa wato zuciya da kwakwalwa wadannan sune farkon kuma ginshikin duk wata sha'awa ajikin mutum,"

"kowacce akwai halitta na sha'awa tattare da ita kuma kowacce akwai matakin sha'awarta wanda ake cewa matakin karshe itace harija wanda itace karshe wajen sha'awa hallau koda yake babu wani sahihin bincike daya tabbatar da yanayinta amma masu hasashe suna iya bayyana yanda surarta yake,"





"zuciya itace mafi tasiri wajen sha'awa kafin ta aikawa kwakwalwa wanda ita kuma kwakwalwa itace ke sarrafa jijiyoyin sha'awa ajikin mace wanda hakan ke kashe mata jiki wannan kuma yana faruwa ne sakamakon taruwan maniyi da yakeyi izuwa kasan maman ta wanda idan har be fitoba zai iya haddasa mata ciwon mara a wannan lokacin ko kuma lokacin al'ada, wannan shine ya bayyana a ilimin kimiyya"

"sannan mafi yawa mace tana fara jin sha'awar namiji lokacinda ta fara al'ada ko makamancin haka,"



"abu uku sune kan gaba wato ciwon sanyi da matsalar aljanu sai kuma istimna,i,"







"Yana shiga jikin mace ya hana ni,imarta zuwa daga karshe ya dakatarda sha'awarta, bayaga haka ciwon zai hana miji yaji dadin mace yayinda gabanta zai bushe a koda yaushe irin wannan akwai aiki soaai wajen dagewa dashan maganin sanyi,"



"akwai Abinda ake cewa namijin dare Wanda yake aurar mace cikin mafarki zataga tana saduwa da namiji tanajin shaukin saduwar amma azahiri batajin dadin mijinta wannan yana kawo yawan fada tsakanin ma'aurata domin kwata kwata mace bazataji dadin namiji ba wata ko sha'awar bataji to hakan ba karamar illah yake a zaman takewar aure ba,"







"yawan wasa da gaba ko kuma madugo itama hanyace dake daukewa mace sha'awa,shikuma mace tana iyajin sha'awa amma ba bangaren saduwa ba zatafi so ayi wasa da ita sama da saduwa da namiji wannan shima babbar matsalace da zata kawo sabani tsakanin miji da mata,"







"Kamar yanda yazo a rubutuna na baya akwai banbanci tsakanin inzali na mace Dana namiji domin yanzu matsalarda wasu mata ke ciki shine basajin lokacinda suke inzali kamar yanda namiji ke sani kuma bisa binciken masana Abu ukune kan gaba wajen faruwan wannan matsalar,"

v' akwai ciwon sanyi Wanda yake hana mace sanin lokacinda take inzali domin maniyinta zai tsinke ya zama kamar ruwa zai rinka fitowa kadan kadan wata tanajin dadi lokacin fitarsa wata kuma kwata kwata babu abinda takeji na dadi amma mijinta zai iyajin dadin shima kafin ciwon yayi yawa saboda irin masu wannan matsalar koda maganin ni ima sukayi babu wani canji to a hankali sai





"shima mijin yadena jin dadinta kuma sauda dama abinda ke kawo wannan matsalar shine wasa da farji lokacin mace tana budurwa istim Na.i (mastrabution),"

A irin wannan halin abinda zakiyi shine kirinka tsarkida ruwan dumi da magarya aciki kuma kisamu garin hulba da gishiri kadan ki zuba a ruwan dumi kina zama shima lalle zaki iya dafa ganyen danyensa kina zuba Zuma kinasha

"sannan me irin wannan matsalar zata iya amfanida miski na matsi wato miskul dahara tana matsi dashi,"

w' na biyu akwai rashin gamsuwa da miji shima yana hana mace inzali domin wasu matan ana dadewa kafin suyi inzali





"to idan ya zama mijin bashida juriyar dadewa mace sai taji kamar zaizo amma ba dama ko kuma kankantar gaban namjji baya shiga gaban mace yanda ya kamata to babu damar tayi inzali to wannan matsalar daga wajen mijinne suna iya wasanni sosai har saita kusa yin inzalin kafin afara saduwa,"

"x' akwai rashin sha awa mace Wanda batajin sha awar namiji komai dadewa ana saduwa da ita bazatayi inzaliba irin wannan gaskiya ta dage dashan magungunan kara sha awa tareda ni ima,"

"to kodai yaya nene mace wanda bata inzali bazata taba jin dadin saduwaba koda kuwa tanajin sha'awa,"







garin albanunaj garin habbatussauda ganyen dan fadama

"wadannan ana hadasu waje daya ana hayakin jiki don kore namijin dare ajikin mace sannan akiyaye lokacin kwanciya arinka addu'a abinda yashafi addu o,i kuma sai atuntubi malaman rukiya,"

maganin kara sha'awa kina bukatar kayayyaki kamar haka

"1/argaf 2/sassaken baure 3/ruma fada 4/ganyen zogale
5/ganyen idon zakara"

"wadannan garinsu zakiyi kinasha da nono me kyau,"





"shima dai wannan tsumin ba sabo bane mun Dade muna bawa amare shawarar kafin aure asha wannan tsumin Na kwana biyar koda babu ciwon sanyi zai bude hanyar ni,ima idan kuma akwai shi yanada tasiri sosai wajen kashe cutar kurmus,"

anaso kisha Rabin litter akwana biyar ko kuma kisha litter akwana goma shima haka namiji zaisha.







sauyar zogale da 'ya'yansa da ganyen magarya da sauyar rawaya da ganyensa ayi garinsa ahada da kiswatil hindi sai atafasa da kanunfari aciki da kanwa da tafarnuwa bayan an tace sai amatsa lemon tsami da Zuma shikenan an kammala.

Idan ana so a gyara gashi za a iya hada ayaba da kwai sai a kwaba su sosai





"sannan a shafa a gashi a jira na tsawon mintuna sha biyar zuwa talatin sannan a wanke,"

ana matsa lemon tsami acikin zuma

"agauraya sai ashafa afuska bayan mintuna talatin sai awanke,"





ana iya tsoma sakar zuma acikin man zaitun da zuma da lemon tsami sai arinka shafawa ajiki awa daya kafin wanka zai

"fitarda dattin fata ya sakata tayi haske,"

GABATARWA

da sunan Allah me rahma me jinkai tsira

da aminci su kara tabbata ga manzon tsira manzon rahma (SAW) ina farin cikin gabatarda wannan littafin tareda fatan zai amfanar da iyayenmu mata allah yasa

albarka acikinsa.

BIKIN  YAR GATA session2

Wajen da farin ciki da walwala suke anan rayuwa take da muhimmanci amma wajenda zuciya take cike da bakin ciki da kunci mutuwa tafi rayuwa muhimmanci to amma na kasa mantawa da kalaman mahaifiyata tun ina karama inda take cewa idan akwai dalili daya da zaisa dan adam ya kashe kansa to zai samu dalilai goma da zasu saka ya rayu

"wannan tunanin nayi shiyasa ban kashe kainaba domin zan rayu ko domin abu biyu na farko nayi abunda mahaifiyata zata yafemun na biyu kuma na dauki fansar cin amanar da kawata tayimun,"





"kamar dai yanda ka sanar dani hanyoyin da zanbi nayi aiki da magani haka nabisu dalla dalla kuma kwalliya ta biya kudin sabulu domin duk abubuwan daka fada hakan ya kasance don kuwa babu wata alama da mijina yaji wanda zai gane wani ya taba saduwa dani haka yayita riritani ya mayar dani tamkar jaririya,"





baya yarda raina ya baci komai nakeso shi yakemun nima kuma iya kokarina ina kyautata masa ko tafiya zaiyi dani yake tafiya baya tafiya ya barni a gida yana alfahari dani dari bisa dari ina cikin rayuwar farin ciki hakanma bankai mahaifiyata ba domin duk yanda taso na zama a gidan mijina saida na zama saidai akwai kuskure guda biyu da nayi wanda shine mafi girman kuskure a rayuwata

na farko shine kawata aminiyata tasan abunda ya faru dani ina budurwa ita kadai tasan halinda nake ciki itama saboda bama boyewa junanmu ko wanne sirri

kuskure na biyu kuma na bari tasan sirrina tsakanina da mijina yanda yake kyautatamun





dama irin kulawar da nake samu duka tana sane dasu hasalima wani lokacin ita take kawomun magunguna wanda sune suka kara bani kimah awajen mijina

"to amma abinda bezo zuciyata ba shine zata iya cewa tana sonsa don kuwa irinsa kowacce mace ke burin samu,"

"Ranarda naga photon mijina awayarta ranar wannan tunanin yazo mun daga bisani kuma abinda nayi zargi zai faru sai gashi ya kasance,"

"bawai aurenta shine matsala ba matsalar anan tasan sirrina wanda idan har wannan sirrin ya bayyana to aurena yazo karshe shine dalilinda yasa banyi jayayya ba na amince cikin farin ciki amma zuciyata kullum cike take da kuna har akayi auren,"





da wannan sirrin ta raba tsakanina da mijina soyayyar da yakemun ta koma tsana da kiyayya baya shakkar cimun mutunci gori kuwa babu ranar da bazai munba

"a hankali duk abinda nayi tunanin zai faru dani saida ya tabbata daga nan ya daina kwanciya dani wai cemun yakeyi sauran wani bana iya furta komai sai hawaye ,"





daga karshe dole na fadawa mahaifiyata amma itama jin labarin abinda yasa mijina ya juyamun baya saima ta tsaneni fiye da yanda shi ya tsaneni harma tana cewar tayi asarar haifuwata sannan tayi wahalar banza wajen tarbiyya

"don haka take bawa mijina shawara ya sakeni na kama gabana,"

"haka zalika tace ban cancanta na zama  yar taba tunda na kasa zuwa gidan miji da budurcina bayan ta rabu da farin cikinta domin ta cimma burinta a kaina to acikin wannan halin na baro gaban mahaifiyata na dawo gidan kanin mahaifina daga bisani kuma mijina ya aikomun takarda ta wanda shine silar zamana karamar bazawara,"





"dukta cewar ina fuskantar kalubale iri iri amma bana wasa da addu a ayanzu kuma nasamu miji wanda yake kaunata dan haka nakeson duk wani abu da zai gamsar da namiji da wanda zaisa shi nishadi don a shirye nake nayi komai don farin cikinsa domin ta dalilinsa nakeso na gyara kuskurena,"

kawata kuma kaddara tana tareda ita kuma dukda cewa kaddara abace mara tabbas amma nasha alwashin saina tunkudo da ita waje ta zama ma baraciya





"don ita ta rabani da ahalina sannan ta jijjige tushen soyayyata awajen mijina na rasa komai ita kuma tana rayuwa cikin farin ciki,"

amma yanzu farin cikin mijin da zan aura shine burina nasan tanan zan samu kusanci da mahaifiyata.





"masana sirrin mace sun kasa bazawara mataki uku,"

v' bazawara ta farko itace wanda batada banbanci da budurwa bi ma'ana wanda aka daura aurenta

Amma har aka saketa mijinta be sadu ta itaba wannan itace wanda daga tazo aure kai tsaye zatayi aurenta kamar yanda budurwa keyi ba tareda ta bukaci kayan gayaran jiki sosai ba.

2 ta biyu kuma itace za'a saketa bata haifu ba koda kuwa tayi shekaru da yawa matukar bata taba haifuwaba to akwai saukin gyaran jiki saidai kamar abinda ya shafi gyaran nono da kugu da kuma gyaran fata ko fuska sai kazar amarya

"da abubuwa masu karawa mace ni,ima sai kuma butar matsi wadannan sune zasu dawoda mace kamar budurwa"





"ciki da waje ta yanda wanda ya aureki zaiyi tsammanin kamar budurwa ya samu,"

"ta karshe kuma itace wanda take haifuwa kafin asaketa wannan tana bukatar gyaran jiki da yawa musamman gyaran nono da matsi wadannan sune zasu fara zama kalubale wajenta kafin tayi sauran,"





"to awannan makalar zanyi magana akan bazawara wacce take mataki na biyu domin itace ma musabbabin wallafar littafin,"

GYARAN NONO

"mafi yawan mata abu uku ke fadar musu nono na farko kuma shine wahalar dashi kamar kwanciya akansa ko daurin kirji yawan kamasu da yawan tsalle,"

sai kuma shayarwa





wanda shine zai mayar da nono kanana su zama kamar babu komai ko

"kuma su zube kodai su koma kamar silifas,"

sannan akwai halitta wato yanayin halittar nono idan mace nononta bai zama me kyauba zai rinka lalacewa da wuri dole idan tanaso suna

"ganuwa saita dage da gyaransu, koda yake maganin nono akwai dace amma maganin gargajiya wanda aka hada da ganye ko"





gadali shine mafi kyau wajen dawoda nono wanda ya lalace kamar me shayarwa wanda ruwan nonon ya kare tana iya rike kunun alkama

"wanda akeyi da waken suya wato za asamu waken suya a soyashi sama sama sai a samu gyada itama a soyata sama sama shikenan sai ahada da alkama ayi garinsu ana dama kununsa ana saka madara ko nono anasha,"





"garin hadin gadali kuma shine me wahala kuma shine wanda yafi kowanne aiki don idan na amfaninki zaki hada zaifi miki sauki ki saya ahade don ana hadashi da kayan karin nono da yawa,"

"asalin gadalin nono wanda kina bula jikinsa zai fara zubar da ruwan nono sai kuma nonon kurciya danye da 'ya'yan baure shima danye zaki kirbasu ki bari su bushe kiyi garinsu, saiki hada waken suya da gyada da aya da ridi duka ki soyasu sai kiyi garinsu"





"sannan kuma ki samu alkama da farar shinkafa suma kiyi garinsu sannan kisamu garin hulba shikenan duka saiki hadasu waje daya kina zuba cokali daya acikin nono ko madara kinasha, anaso akalla kisha na sati biyu,"

wannan shine mafi girma a maganin nono duka wanda zaizo to daga bayan sane don shine kowanne kalar nono zai gyara amma sauran ba lallai

 maganin yazo daidai da kalar nonon kiba.





"shi kuma wannan yanda zakiyi ki samu ayaba (plantain) ki yanyankata ta bushe sannan ki daka garin to saiki samu aya ki wanketa kisaka,"

gyada kisaka amarkada miki saiki tace ruwan kina diban wannan garin plantain din kina zuba madara peak kinasha kamar sau biyu arana.

GYARAN FUSKA

Abu na farko da mata yakamata su gane

akan abunda ke gyara fuska babu sama da kwai da lemon tsami da ayaba





"da zuma wadannan ana sarrafasu sama da hanyoyi 50 kuma binciken ilimi ya tabbatar da haka,"

"zaki iya hadasu waje daya ki shafa a fuska bayan minti talatin (30minutes ki wanke sannan ita Zuma ita kadai ana hadawa da lemon tsami ana shafawa,"

Kwakwa Zaki samu ki gurzata saiki hada da Zuma da man zaitun saiki shafe fuskarki dashi sai bayan kaman mintuna biyar (5minutes) saiki wanke da ruwan dumi kiyi kullum kisha mamaki





Hallau dai Zaki iya hada man zaitun din da Zuma da lemon tsami ki saka sugar kadan saiki shafe fuskarki dashi bayan mintuna talatin (30minutes) ki wanke fuskarki

Shi kuma wannan ayaba Zaki markada dama kin jika garin hulba da ruwan dumi saiki saka man habba da man hulba da Zuma da madara duk ki hadasu saiki shafe fuskarki idan kinaso harma jikinki Zaki iya shafawa





"idan kuma kinason jikinki yayi laushi kada yayi tauri Ki samu ayaba mai kyau ki bare ko ki matse da hannunki ko ki markada yayi laushi sai ki zuba madara peak ki fasa kwai ki matsa lemon tsami ki gauraya sosai sai ki shafa a jikinki yayi sa a daya (1hour) sai kiyi wanka da ruwan zafi amma ba zafi sosaiba, Idan kinayin wannan har kwana uku zakiga yanda jikinki zaiyi,"





"sannan zaki iya daka ganyen magarya ki zuba cikin man zaitun ki hada da man habbatussauda sai ki dinda shafawa ajikinki bayan sa a daya (1hour) sai

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment