You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

prince? Ina tunanin wannan aikin dashi ya dace ba wani ba?"ya faɗa yana karkarwa sbd yadda yaji kansa ya fara juyawa hakan kuma shine alamun nasarar aikin.

Rubuce² Boka yay saman allon tsafinsa kana ya dubi Mai martaba yace "aƙwai matsala babba,bana da ikon yiwa Lil prnce aiki a yanzu saiya gama mallakar ƴan mata guda ashirin kamar yadda yake a tsari,dan aljanin dake shanyen jinin matan shine mai akula da prince kuma bai idda shan jinin ba kamar yadda ya buƙata,babban abuma shine kaine a kan karagar mulki bashi ba,so dole wannan aikin naka ne,amma yana da sharaɗi"ya ƙare maganar yana ɗauko wata gawar mahauniya wacce aka jiƙa jikin jini kana ya cilla cikin wuta.


Jinjina kai Mai martaba yay tare da gyaran murya hakan ya tabbatarwa da Boka Mai martaba Khalid ya amshi ƙudurinsa kamar yadda yake buƙata,saida ya kammala komai na aikin sannan yace "Sharaɗin ba'a faɗarsa, kawai dai ka kiyaye da wannan yarinyar da zaka samo"ya faɗa yana shigewa cikin wani kurmin ɗaki mai duhun gaske,Mai martaba yaywa alama da hannu akan ya shigo,miƙewa yay tare da fara tafiya,yana shiga suka rufe ƙofa,wajan 3mins na jiyo surutansu sama² da kuma ihu²😱komai suke aikatawa uhuu,saida suka kammala abinda suke kana suka fito fuskar Mai martaba cike da farin ciki da alama dai aƙwai abinda akai masa wanda shima yake buƙatarsa,cikin nutsuwa ya sanya kayansa ya koma Sarkinsa sak komai na kamala ya fito,idan kaga Sarki Khalid ba zaka taɓa cewa zai aikata wani abu na saɓon Ubangiji ba,bai fiye fitowa a asalin colour ɗinsa ba,yana ɓoye mummunan habit ɗinsa sannan ya bayyana good habit ɗinsa,wannan halin duk cikin iya takune dan haka da wahala ka fahimci yana aikata mummunan abu,sai wanda suke good tym dashi.


N.S Quest Place
Shine Hotel ɗin da suka sauka cikinsa,Hotel ne mai ƙyan gske kuma da tsari sosai manyan masu kuɗi suke sauka cikinsa,room 123 shine na Mai martaba,124 kuma na Lil prince sauran rooms ɗin na amintattun Sarki da suka taho tare,daman alrdy pilto yay tafiyarsa sai gari ya hawaye zai dawo.


Yana zaune a kishin giɗe yana kallon new a B.B.C Lil prince ya turo ƙofar ɗakin hotel ɗin ya shigo,zama kusa da mahaifin nasa yay cikin girmamawa yace "Allah ya ƙara maka yawan rai da ƙwana ya mahaifina,wata buƙata gareni idan an bani damar faɗa?"


Gyara zama Mai martaba yay tare da maida hankalinsa kan Lil prince yana fatan ace ba wata babbar matsala bace take damun yaron nasa,cikin tausassiyar murya Mai martaba yace"Haba magaji matsalanku ai tamu ce,faɗi ina jinka"murmushin jin daɗi Lil prince yay yace " Allah ya taimaki Sarki ina buƙatar kuɗi masu yawa sbd nayiwa friend ɗina ƙyautar motar as her birthday gift,Papa wallahi Heroine naji dani sosai kuma naga tana mutuwar son mota Bugatti shine nakeso nai mata gift da ita"


Girgiza kai Mai martaba yay cike da farin ciki yace "ba wani abu za kaga alert anjima shikenan?"ya tambaya cike da ƙaunar ɗan nasa mafi soyowa cikin ransa da zuciyarsa,dariya Lil prince yay tare da hugging mahaifin nasa yace "Thank you soo much Papa heroine na gdy ƙwarai"bayansa ya ɗan bubbuga yace "it ok,Magaji meye tunaninka ga wannan hotel ɗin?"shuru Prince yay dan baiyi wani tunani ba,"i don't think anything kawai dai yay ƙyau sunsan aikinsu"nisawa Mai martaba yay yace "ni ina da ra'ayin gina irinsa a garin Bilhas"ɗan waro idanu Lil prince yay tare da faɗin "but ina zaa samu babban fili cikin jama'a haka?"wani shu'umin murmushi Mai martaba yay yace "muke da gari fa,zanwa Governor magana akan babban filin da wani malami ke buƙata zai gina makarantar ismaliya so gwamma ni na amfana dashi tunda harka ake ta kuɗi"jinjina kai Prince yay yace "amma makarantar fa ya...'✋🏼ɗaga masa hannun da Mai martaba yay ya sashi yin shuru dan haka yay masa Goodnight ya fice a ɗakin shime shirin ƙwanciya yay domin yana buƙatar magana da shugaban sujoji yana buƙatar a bashi mai kula da lafiyarsa data Prince da wannan tunanin ya ƙwanta bacci.





*** ***
Ƙwance take saman makeken italian bed ɗinta sai juyi take tym to tym tana murza ƙaramin ring ɗin hannunta,wanda har yanzu bata san yaya akai ring ɗin yazo hannunta ba,wata ranane ta ƙwanta bacci tai mafalkin wani haɗaɗɗan guy mai ƙyan gaske,saimun kanta tayi ta zuba masa gajiyayyun idanunta masu kaifi,cike da ƙaunarsa ta nufi wajansa kafin ta ƙarasa wani baƙin mutum ya shiga tsakiyarsu tare da nufota tana jaa baya,kafin yakai ga inda take taji wata azaba a ƙaramin yatsanta sai kuma wani haske ya bayyana,wanda yay sanadiyar guduwar mutumin cikin farin ciki ta hangi wanda idanunta ke fatan gani ya ware mata hannayensa alamar tazu garesa da gudu ta isa garesa kafin ta ƙarasa an buga mata wani abu a kanta,cikin firgici ta farka daga nannauyen baccin daya ɗauketa,tun daga wannan ranar taga wannan ring ɗin hannunta wanda kullum cikin sheƙi yake tana sonsa kamar ranta shiyasa bata rabuwa da murzasa.


Yauma tunda ta farka take yawan faɗuwar gaba,lumshe sleepyn eyes ɗinta tayi wanda koda yaushe suke a rufe cikin nauyi da kasalan daya sameta ta ware jajayen laɓɓanta masu kauri tace"ya rabbi what wrog with me,i have a test by 10:30 kuma still ina gida"ta faɗin hakan tana taune cute lips ɗinta mai sheƙi,miƙewa tayi tare da ɗaukan teddy ɗinta ta rungome tana jin wani abu mai kama da kewa na ratsa zuciyarta,cikin zuciyarta tace"i luv you my hrt dream where are you?"ta faɗi lkcn da take tura yatsanta cikin ƙaramin bakinta ta shiga tsotsa kamar yarinyar,ta daɗe zaune kafin ta sunbaci teddy tace "my bby boo"tana faɗin hakan ta miƙe tare da shigewa cikin toilet ɗin dake cikin bedroom ɗinta,sosai toilet ɗin ya tsaru komai anyi masa ado da pech colour kamar yadda fenti bedroom ɗin ɗakin yake pech,a ɗan gurguje ta sakarwa kanta shower tana wanka tana rera waƙar cikin film Sam teri kasam domin shine fovarite movie ɗinta,soyayyar film ɗin ita tafi ƙayatar da ita,bayan ta kammala wanka ta zubawa kanta idanu ta cikin mirrow'n dake manne a toilet ɗin.



Turo baki tayi gaba tare da mamulan lips ɗinta cikin ranta tace "i hate this stupid brest ɗin,banso takura garesa"sosai take ƙyaƙƙyawa fara tas da ita,babu abunda yafi ɗaukan hankali a jikinta kamar fresh skin ɗinta,kana kallonta zaka san ita ɗin ruwa biyu ce,musamman yadda eyes ball ɗinta suke blue kamar wata baturiya,tana da dugun hanci wanda yay dai² ƙaramin bakinta,ga gashin idanunta zara² wanda suke ƙwance luff,gashin girarta kam kamar zasu haɗe sbd yawansu,baƙi siɗik suke sunyi ƙwance luff,sai gefen fuskarta wanda yake ɗauke da saje kamar namiji,ɗan ya tsuna face tayi hakan ya bawa beauty points ɗinta damar lumawa,cikin sauri ta tattare tulin gashin kanta bayan ta gama busar tashi ta ɗaure waje guda,daga wajan toilet ɗin taji ana faɗin.

"ZARINA! ZARINA!"

Tana ji ta kasa amsawa sbd sam magana bata dameta ba hasalima wahala take bata,saida taji kiran yay yawa sannan tace "I'm here Mom" jin amon muryarta a toilet yasa Mom faɗin "ok be past my luv"tana faɗin hakan ta fice a ɗakin domin ƙarasa shirya break fast.

a ɗan gurguje Zarina ta gama shiryawa cikin duguwar riga ta Abaya mai ɗauke da milk colour haɗi da maroon ɗin stone,beby lipstic ta shafa saman lips ɗinta kana ta ɗauki school bag ɗinta ta rataya,harta tafi ta dawo ta ɗauki teddy ɗinta ta rungome,sosai ta ƙarewa ɗakin ƙallo kamar me nazari sai kuma ta saki murmushi tace "i will come back soon"tana faɗin hakan ta fice ta nufi babban parlour'nsu.


Tana isa ta rumgome Mom tare da bata kiss a kumatu tace "mrng Mom"shafa kanta Mom tayi tace "mrng too my luv"

"ok bye Mom i luv you"da sauri Mom tace "No! No! Zarina come back u forged ur break fast,da sauri Zarina ta dawo ta sanya yam balls a bakinta kana ta kurɓi coffee taiwa Mom bye tare da rungometa sosai cikin sanyi tace "zanyi kewanki Mamana i luv you"cikin sanyi Mom tace "i luv too my luv Allah yay maki albarka take care" ta faɗi hakan tana yi mata kiss a tsakiyar forehead ɗinta,da sauri Zarina ta fice a parlour'n ta nufi hanyar fita daga cikin gidan,tana zuwan compund na gidan ta shiga cikin WCSV drever yaja suka fice daga gidan.






Sosai dreve'n ke gudu ganin sunyi late yana tsaka da gudu tayar motar tayi faci,tsaki yaja tare da faɗin"kaji tsiyar ƙarfan nasara"Zarina dake bayan mota tana danna syetem ɗinta tace "go and cheak nayi late da yawa bro"jinjina kai yay tare da faɗin "afuwa hajia ƙarama bari na ƙarasa wajan bakanike na ari taya saimun sauya amma wannan iskar cikinta ta sace"murmushi tayi masa tace"no problms amma na fara aiki as lawyer ta kanka zan soma"dariya yay mata yace "aga farceni Hajia ƙarama" leƙa fuskarsa tayi tace "Allah yasa mudace"ɗan waro idanu yay tare da faɗin "Hajia mudace dai aike kin riga da kin dace saidai fatan cikawa da imani,Allah yasa mudace idan mundace mu dafe"ya faɗa yana fita a motar ganin idanta biye masa zai cikata da magana yasa tayi shuru taci gaba da bincikenta a cikin System ɗinta.


Wajan sama da 10 minutes taja ɗan ƙaramin tsaki tare da ɗaga kanta,murmushi ta saki ganin wasu yara na ƙoƙarin tsallaka titi sun kasa,hakan yasa ta ɗauko teddynta tare da ɗiban chocolate masu yawa,ta buɗe motar ta isa ga yaran,tana ƙarasawa tace "hi friends can i help you?"gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin “YES ANTY” hannayensu ta riƙe cikin tsutuwa ta tsallakar dasu makeken titin kana ta raba masu chocolate sannan ta juya ta nufin tsallaka titi,watan baƙar mota ƙirar Ferrari tayi parking gabanta,saurin ja baya tayi tare da sanya yatsanta cikin baki,ana haka ta hangi drever ɗinta,cikin sauri ta fara ɗaga masa hannu tare da buɗe baki zata kira sunansa taji anyi sama da ita tare da nufar mota da ita baki ta buɗe zata saki ihu akai saurin danna mata handkerchief a baki.


_*Dan hasken Annabi da kur'ani idan kin karanta kiyi share ɗinsa zuwa wani grp ɗin kana kiyi comments dan darajar Allah👏🏻🙌🏻*_



Share
Comments
Vote
THE NEW EMIR

_Wattpad *Nimcyluv*_

*_@Telegram_*
https://t.me/joinchat/U6Qw0BuhKkqh5GZ8RadieQ




7-8




Jikinta ne ya saki bayan sun sanya mata handkerchief a baki wanda yake ɗauke da powder mai gusar da hankali,gaba ɗaya idanun Zarina ya lumshe jikinta saki yaza mana bata san inda hankalinta yake ba,sabida ƙarfin powder da akai using da ita a kan handkerchief ɗin,cikin motar ya turata tare da shimfiɗeta a side ɗin baya,shi kuma ya koma side ɗin gaba,ɗan juyawa yay tare da zuba masa idanunsa yana kallon yadda ta rungome teddy tare da tura yatsanta cikin baki,murmushin gefen baki yay domin nan take wani abu ya caki zuciyarsa,juyawa ya kalli drever yace "let's go" da gudu drever yaja motar suka bar kan titin.




Ihu Dreve'n Zarina ya saka domin kan idanunsa suka sanyata mota,tsoran ransa yake shiyasa bai ƙarasa ba,domin babban titi ne mutane basu fiya zama wajan ba,cikin kuka ya faɗa mota tare da janta da gudu ya mara masu baya,yana dreving yana kuka tare da faɗin "Hajai ƙarama ubangiji ya kareki daga sharrin mutannan,Yarinya mai halin manya kenan😭idan na rasaki ina zan samu mai bani na kashewa😂"


Sosai dreve'n Zarina ke gudu tsakiyar makeken titin amma kafin wani abu tuni motar ƴan kidnapped ɗin sunyi masa nisa,haka yayta bulayi babusu babu labarinsu,sabida tsoron abinda zai faɗawa Hajia Sultanerh yasa ya kasa zuwa gida sai gefen titi daya nema ya zauna yaci gaba da rusar kukansa.



Basu tsaya ko'ina ba sai filitin tashi da saukar jirki dake garin Kogi,suna isa jet ɗinsu na sauka,gaba ɗaya suka shiga ciki babu wasting time pilto ya tada jet suka lula saman gaji mare.


Fargaba gaba ɗaya ya cika Mom ganin lkcn da Zarina ke dawowa harya gota,cikin tsoron data sami kanta ta danna number wayarta,tana ji tana ringing but amma babu picking cikin muryar kuka Mom ta shiga faɗin "why Zarina am so scared pls come back"da sauri kuma ta danna number wayar drever'n cikin sa'a ya shiga ana picking tace "where is my luv,where is she!?"ta ƙare maganar cikin ɗaga murya tamkar yana gabanta,shuru tayi tana sauraran abinda yake faɗa kafin ta ƙwala ƙara tace "What Zarina missing but how, no you're lie duk inda yarinyata take kayi gaggawar dawo mani da ita kai shashan inane mtwss" tana faɗin hakan ta juya a guje ta nufi sashin uwar mijinta a babban parlour tana zuwa ta faɗa jikinta tare da sakin kuka,sosai Mamu ta shiga tashin hankali ganin surukarta cikin wannan halin,a tsorace tace "kee! Lafiyanki mene haka kamar wacce akace Abdallah ya mutu"ta ƙara magana tana kallon Sultanerh.



Ƙara ƙanƙame Mamu Sultanerh tayi cikin kuka ta shiga faɗin "Na shiga uku Mamu innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ta faɗin hakan tana ƙara rushewa da kuka,hakan yasa Mamu ƙara ruɗewa cikin wani sabon tashin hankali tace "Waini zaki maida shasha kizu kina kuka kuma kimin shuru oyya tashi ban waje idan baki faɗin abinda yake faru"girgiza kai Sultanerh tayi kana ta sassauta Kukanta tace "Zarina missing Mamu"ta faɗa cikin wani sabon kukan,da mamaki Mamu ke kallon Sultanerh kafin tace "sorry! I did get u kamarya Zarina missing kamar wata ƴar tsana?"nan Sultanerh ta ƙwashe komai ta faɗawa Mamu har abinda ta cewa Drever'n,Salati Mamu ta fara dayin addu'ar duk dayazu bakinta kana tace "Kin faɗawa Abdallah da kuma brothers ɗinta?"girgiza kai Sultanerh tayi tace "bansan tayaya ne zanyiwa swrth baya ni ba,ina tsori domin nasan soyayyar dakewa Zarina kamar ransa,Sufyan da Taufik bansan sanar dasu sbd kinsan yanayin aikinsu na sojoji da wahala yake gashi wannan karan kona kirasu waya ban samunsu ina tsoro zan jira harsu dawo"shuru gaba ɗaya sukai domin babu wani mai sauran kuzari cikinsu,can Mamu ta nisa tace "ko za'a ɓoyewa kowa banda Abdallah domin shine mahaifinta so kowanne tashin hankali zai shiga dole ya sani,ɗaukan wayana a ɗaki"miƙewa Sultana tayi tare da ɗauko wayan ta dawo babu ɓata lokaci ta dannawa Abdallah kira.




_Masarautar Bilhas_
A hankali ta shiga buɗe manyan idanunta wanda sukai mata nauyin gaske tana mamakin irin baccin daya ɗauketa,bakinta ɗauke da addu'ar tashi daga bacci kana taja idanunta ta ƙare kullesu,teddynta ta rungome sosai tare daci gaba dashan yatsanta ƙamar wacce ake feeding,cikin abinda bai huce 3mins ya farayi mata gizu kamar yadda ya saba yi mata cikin baccinta,amma a wannan karan tana mamakin yadda komai nasa yake bayyana abu ɗayane takeson gani hakan kuma ya kasa faruwa,a duk lokacin dataso ganin fuskarta sai kanta ya fara ciwo tare juya mata,ɗan ya mutsa fuska tayi cikin ranta tace "where are you haiding ne?"ta faɗa tana turo bakinta,sosai yake bata haushin ɓoye fuskarsa da yake mata,cikin nasarar da suka samu Zarina ta manta komai tama manta cewa satota sukai,ta manta Mom,Abbanta,Sufyan,Tufik,abu ɗaya take iya tuna ta kuma fahimta shine “Heart dream”

Turo ƙofar ɗakin da akaine yasa tayi saurin ware idanunta tare da zubawa ƙofar ɗakin idanun,saurin miƙewa tayi tare da zama waje guda ta ƙanƙame jikinta ta zubawa mutumin idanu,murmushi yay mata kana ya ƙarasu cikin ɗakin cikin so da ƙaunar ganinta yace "baby harkin farka?"kasa tankashi tayi domin haka kurum taci ta kasa yarda dashi,cije lips yay kana ya zauna kusanta yace "ohh baby badai harni kika manta ba,so how was ur night beby kin daɗe kina bacci harna gaji zarya"nanma shuru tayi masa ta ƙara ƙanƙame teddynta a jikinta ta shiga mutsa bakinta alamar tana son faɗin wani abu,ganin yadda bakinta ke motsi gashi gaba ɗaya sun jiƙe da saliva wanda ya ƙara hadda fidda asalin ƙyan lips ɗinta,yasa shi saurin lashe gefen bakinsa yana jin wani iri a ransa,cikin wata muryar yaudara yace "ohhya bebyna say something pls"hawaye ne suka wanke mata fuska cikin siririyar muryarta wacce bata fita sosai tace "who are u?"ɗan ware idanu yay alamar mamaki yace "Ohh bebyna ta manta lover ɗinta whatever dai i'm ur husband to be😱"kallonsa tayi da jiƙaƙƙen hawayenta tace "sure?"
“yeah” shine amsar daya bata cike da murnar nasarar daya samu,ɗan murmushi tayi wanda ya bayyana haƙorin makkanta cikin muryar nutsuwa tace "Thank God,amma da naji tsoro sai nake ganinka kamar mugu irin kumurcin majinnan"ɗan ɓata fuska yay baice bata komai ba yakai hannu zai riƙe hannunta tayi saurin jaa baya,cije laɓɓansa yay yace "ok bbyna take a shower and za kiga komai kamar a mafalki so ki ɗauki hakan matsayin sabuwar rayuwa zaa kawo maki white clothe ki sanya as from today shine kayanki daga nan banson wata tambaga kin gane"yana faɗin hakan ya fice a ɗakin.


Baki ta taɓe ita wani tsoransa ta keji haka nan,amma taji daɗi cikin ranta tunda yace shine zai zama mijinta tasan kuma miji never ya cuci matansa,miƙewa tayi tare shige wani ƙofa data gani gefenta ganin toilte ne yasa ta faɗa ta shiga sakarwa kanta shower tana gamawa ta maida kayan jikinta kana ta ɗaura alwala,sosai tai mamakin ganin dare ya ƙarayi cikin sauri ta gabatar da sallah sannan ta zauna zaman lazimi,tana iddar wasu Hadimai mata suka shigo kayan suka ajjiye mata sannan suka ajjiye mata kayan motsa baki danginsu fruit,wata Hadima ce tayi dariya tace "kice mun ƙaro wannan mai kalan aljanun ina aka sameta?" cewar ɗaga daga cikinsu kenan,Zaituna ce tace "kee! Saurara banson rashin ɗa'a meye haɗinki da ita?"Kuyanga Furare ta amshe maganar wajan faɗin "Babu fa,nidai ƴan matan duk abinda zaki ki ɗauke idanunki akan Lil prince domin shiɗin nawa ne ni ɗaya"Zaitunce ta maka mata harara tace "ke prince ya maida kuma iska na wahalan damai kayan kaba banda hauka irina Furera waya gaya maki tsarin mulkin Masarautar Bilhas jinin sarauta na kula baiwa,kima daina mafarkin samum prince domin yay maki nisa sosai"ta ƙare maganar tana kallan Zarina wacce taci gaba da laziminta cikin ranta idanunta rufe ba tare data kallesu ba,amma sosai maganganunsu ke damunta sbd bata sama da hayaniya ba sam.
Zaitun ce ta ƙarasu wajanta tace "ƙanwata sannunki kinji mune masu alhakin kula dake daga nan zuwa sati biyi ki koma ɓangarenmu baki ɗaya,amma kiyi hqr da rayuwa ki karɓeta a yadda tazu maki,amma mene sunanki?"sai lokacin Zarina ta ware jajayen idanunta da suka sauya kala lokaci guda sbd tsaɓar tension ɗin data shiga,sosai take kallon Zaitun kafin ta ware laɓɓa tace "heart dream"tana faɗin hakan taja idanunta ta rufe ta shiga tauna laɓɓanta,girgiza kai kawai Zaitun tayi tare da faɗin "Allah yasa mudace"hannu tasa ta dafe kanta dake sara mata tayi sosai take son tuna inda taji kalman ta,
“Allah yasa mudace”amma ta gagara tuna komai,cusa kanta tayi tsakiyan cinyoyinta ta shiga rera kuka kamar ranta zai fita a haka wani sabon bacci ya ɗauketa yatsanta cikin baki.



Washe gari
Fada
Zaune Mai martaba yake kan karagar mulkinsa yana amsar bayanai daga wajan talakawa da kuma abinda ke faruwa a gari,wani dagacin baƙin da suka halarci Fadar wani ya numfasa yace "Allah ya ƙara girma yaja ƙwana muna da ƙorafi bisa babban filin da gwamna yay mana alƙawari bayarwa domin a gina makarantar islamiya yanzu kuma mun samu saƙo akan cewa ya fasa bada wannan babban filin,mu'alummu muna cikin tashin hankali bama da kuɗin saka yaranmu a manyan makarantu kuma muma munaso rayuwan yaranmu su inganta kamar t sauran yaran,wannan filin da za'a bamu jahadine kuma taimakon musulunci za'ai Allah yaja da zamanin sarkin sarakuna mai adalci a duba mana wannan lamarin"yakai ƙarshen maganar idanunsa na fidda ƙwaila.


Mai martaba ya jinjina kai tare da bada umarnin rubuta bayanai cikin peper,haka ya dingajin abubuwan da talakawa ke buƙata kana ya sallami kowa,Mai martaba ya kalli Tiraki sannan ya bashi umarnin yaje ya ƙona peper cikin girmama Tiraki yaje ya aiwatar da abinda Mai martaba ya umarcesa dashi,Ɗan aikena ya shigo da sauri tare da zubewa gaban Mai martaba ya soma kirari kafin yace "Ran sarki ya daɗe baƙwan U.S ya sauka yana airport yanzu haka" cikin farin cikin jin mai tsaronsa yazu ya bada umarnin aje a taho dashi,kana zaman Fada ya watse Mai martaba ya shiga tirakarsa.



Kilishi ta sami Jakadiya tace tana so ayi mata iso wajan Mai martaba,wajan 5 minutes Jakadiya ta dawo tare da zubewa gaban Kilishi tace "Allah ya taimaki uwar ɗakina saidai a tara nan gaba"cikin ɓacin rai Kilishi ta kalli Jakadiya tace "wai wannan wanne irin abune baka da ikon ganin mijinka a lkcn da kaga dama sai wanine zai baka dama?"Jinjina kai Jakadiya tayi tace "sai hqr haka tsarin Sarautar yake dole sai Fulanin Sura ta bada dama"rai ɓaci Kilishi tace "miƙomin Bakilawan can amma ni bazan iya lukutar masifa ba mata sai shegen iyayi kamar wani tafi"Kirara Jakadiya ta shigayi mata tare da zugata kana ta miƙa mata Bakilawan tayi waje.




A hankali wata babbar mota ƙirar Bugatti tayi parking tsakiyar masarautar,cikin sauri Drever'n ya fito tare da dawowa side ɗin baya ya buɗe ƙofa kana ya ƙame ƙam kamar wani dogari,wanda yake a zaune a bayan motar a hankali a ajjiye news peper ɗin hannunsa,gajiyayun fitinannun idanunsa yaja ya lumshe tare da taune jajayen laɓɓansa masu taushi,wani zazzafan numfashi ya fesar ta hancinsa kana ya shiga murza ring ɗin hannunta wanda ya kejin soyayyarsa kamar ransa,ƙyaƙƙyawane ajin farko Allah ya bashi murɗaɗɗan jiki kana ganinsa zakasan tabbas shiɗin soldier shi,hannunsa yasa ya shafi sajen fuskarsa kana yay ɗan gyara murya kaɗan wanda ya jawo hankalin drever'n cikin sauri ya amshi news peper ɗin tare da wayoyinsa,cikin isa da taƙama haɗi da izza ya zura da ƙyawawan ƙafafunsa waje ya ɗauki some minutes kafin ya fito da dukkan jikinsa,Sarki ya tabbata ga ubangijin daya tsara wannan halittar ni kaina na alƙalamina ya kusa faɗuwa,sanyen yake da farar t.shirt mai ƙaramin hannun hakan ya haddasa bayyanar murɗaɗɗiyar arms ɗinsa,sai dugun wandonsa na kakin sojoji yayinda ya ɗaura rigar uniform ɗinsa a waist ɗinsa,tsaiwarsa ya gyara tare zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa,cije lips yay wanda hakan ya zama kamar habit ɗinsa,cikin wata zazzaƙar murya mai daɗi da taushi yace "Masarautar bilhas"


*_sorry yau banyi edited bai idan anga errows sunyi yawa afuwa, zan ɗan rage yawan typing naga bakusan yin comments bansan mai yasa😂😂😂✋🏼tafiyar fa yanzu aka soma Dan darajar Allah da manzonsa ayi share kuma ayi comments🙌🏻_*




THE NEW EMIR IS NOT FREE IS FOR SALE


Abubuwan da suke cikinsa yasa bazan iyayi free ba,ba wai dan baku kai na baku a ƙyauta ba,fatan zaku fahimci Sarauta akan farashi mai sauƙi Akwai specail grp,Normal grp,Vip grp wanda kakeso shi zaka shiga,zuwa gobe za kuji kuɗin littafin afuwa bazan iya free page masu yawa ba iya 10 zan tsaya ina maku sahihiyar ƙauna😍😍😍A shirya sosai domin koda kuɗinka saida rabonka,bana jin za kuyi asarar kuɗinku🙌🏻🙌🏻.

08119237616



Sarauta👸🏼
https://www.wattpad.com/1030172141?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=nimcyluv&wp_originator=Blh6Mu3EzrBkjD4BiWmzf285dWVj5YiUUuBRoGy01hS0mERC1mUR9vQkUMO9RwMgwf%2BfgZeJiVJp6zbfgWZ%2F90cbe36PUMEkY6AcUViUZ4e77jBD8fgISavzW8Z1lXeE



THE NEW EMIR

_Wattpad *Nimcyluv*_

Dan Allah wanda ba suyi following nawa a wattpad ba,su daure su shiga suyi domin hakan shine ƙauna da kuma ɗaga darajar littafina😍Alkairin Allah ya kai maku masoya Nimcy ina sonku bilhaƙƙi.


*_@telegram_*
https://t.me/joinchat/U6Qw0BuhKkqh5GZ8RadieQ




9-10




Narkakkun idanunsa ya zubawa cikin Masarautar yana yaba ƙyanta da kuma tsarinta,komai na masarautar abin birgewa ne,sai ƙyalli da sheƙi take faɗin kuɗin da aka kashe wajan tsara masarautar ɓata baki ne,taɓe baki yay tare da juya fararan ƙwayar idanunsa,Wani Bafade ne ya ƙarasu wajan da sauri yana zuwa ya samu kansa da zubawa Captain kirari kamar wani sabon Sarki kana yace "Mai martaba yace akai ka masaukinka anjima yana nemanka fada"cewar ɗan aiken,shuru wajan ya ɗauka domin Saifudeen ko inda ɗan aiken yake bai kallah ba bare ya saka ran zai tankasa,jinjina kai Bafaden yay yana girmama girman izzar mutumin ko Lil prince baya wannan jan ajin,cikin gajiyawa da kallon da mutane suke masa ya ƙara gyara tsaiwarsa tare da lumshe lulu eyes ɗinsa masu firgitar da ƴar mace ta faɗa tafkin ƙaunarsa,ya ware laɓɓansa cikin muryar mai amo da sauti yace "I need to rest" ya faɗi hakan yana ware manyan idanunsa a kan ɗan aiken,sosai haiba da ƙwarjin Saifudeen suka zuciyar ɗan aiken cikin rawar jikin yace "mai martaba ya bada uwarnin kaika masauki saika biyoni"ya faɗa yana yin gaba,shima Saifudeen baya ya mara masa tare da yiwa drever'nsa wanda kuma ya kasance bodyguard ɗinsa nuni daya biyosa,motar ya faɗa kana ya dinga binsu a baya a hankali har suka isa wani ƙaramin ɓangare a cikin gidan sarautar wanda ya kasance yana kusa ɗakunan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment