You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gefen 'kofar, wato a lamar da mutum a 'kofar.

Dama sun san da zuwan sa kuma dama babu wanda ya ke zuwa musu gida, Sede Lubna wato 'kawar Basmar in da itama yan zu haka tayi aure. Atare suka taso hannu su cikin na juna kai da kagan su kasan suna cikin farin ciki, ita ce ta bud'i 'kofar, dede lokacin da shikuma idon sa na kan gofar damin ganinn wan da ze bud'e.

Shuru sukayi dikkan su su ukun kowa da abin da yake sa'kaw a zuciyar sa,
Babu wan da yayi maga Se kawai Basma tace.. Abar bar ka dazuwa, be am sa mata ba ya bita da kallo se kawai tace.. "Abdul ga Amar, Amar ga Amdul kuma mijina uban yara na, tana fad'awa jikin sa.

Amar beyi mgn ba har yan zu, Kuma yaji hau shin abin da tace, Abdul ne ya ce.. "Amar bar ka da zuwa yana miga masa hannu. Be am saba shima ya bi'ka masa hannu ya ce.. Zamu iya shiga ciki? Kanlon juna sukayi Tsakaninn Abdul da basma Sannann suka bashi han ya yashige.

Abdul ne ya nuna masa d'akin sa sannan ya ce masa dik abin da yake bu'kata ya sanar da shi in yaso a saka masa a d'akin.

*BAYAN A WA 10, WATO LOKACIN CIN ABIN CIN DARE*

Zau ne suke a gaban Dayneng tebur domin cin abin cin dare, Amar ya ce.. Ina son a had'amin kofi? "Basma ta ce.. Ai ga kayan had'a kofi d'in nann ka had'a da kan ka, kafin yayi mgn kuma ta ce.. amma bari in had'a maka, cikin sauri Amar ya ce.. "Dama de kin had'awa megidan ki tukunna ko? kafin suyi mgn ya 'kara cewa ai shima kafin yayi aure gworo ne. Basma ta ce.. "Kai ma base kayi auren matar ka tadin ga had'a maka kofi shayi da kuma dik wani abu da ka bu'kata. "Kenann ke bazaki had'a min ba ya tam bayeta yana kallon Abdul wanda jin su kawai ya keyi yana mur mushi!!.

Suna cikin cin abin cin Amar yaga wani gula daban an iji ye shi a gefe ya ce.. To shi kuma wannann kulan da ba a bud'e shi ba kufa?

Basma ta ce.. Aa wannann wani had'i ne na daban wan da nake yiwa mijina domin yana te makawa lafiyar sa, saboda haka babu ruwan ka da wannann kai de kaci abin cin ka.

Amar ya kalli Abdul ya ce ..kai kuma irin wannann abin cin kakeso Abdul ya ce.. "Eh kasan yana gara lfy , Amar ya ce.. Ai to naga ba wani abin cin kirki bane shi yasa, Kasan cewar kular irin wacce dik abin da ya ke cikin ta zaka iya gani ne. Amar ya ce.. Kin tina lokacin da kike bani abin ci a baki kamar wata ma hai fiya ta? Ya tam bayi Basma, lokaci d'aya dikka ninn su suka tsaya da cikin abin cin suna kallon kallo. Ganinn yan da suka tsaya da cin abin cin yasa Amar ya ce..

A can na kenufi, Ai a cen gidan itace ta ke kawo bin abin ci kullum in ban ciba seta din ga bani a baki har se na ce na goshi. Yana fad'a yana cin abin cin sa han kalin sa 'kawnce.. Yaci gaba da cewa nasan Basma ta iya gir ki sosai, Amma abin da ta kemin wani lokaci fita takeyi da kan ta tasiyomin abin cin a waj. "Amar ya isa haka cikin tsawa ta yi maga nar. Amma ina mar ya cigaba da cewa..

Ai gaskiya ta iya had'e-had'e sosai, kuma a cikin soyayya take ga batar min da komai, Shin mema kike yawan gaya min ma a wan cen lokacin? Yana tam bayar ta lokacin da ya kai lomar abin ci bakin sa, bata ce komai ba , ya ce.. Yau wa na tina abin cin masoya, nayi ti naninn zan cigaba da cin irin wannann abin cin a gurin ta har tsawon rayuwa ta, Saboda Amar na kasan ce na Basma ne.

Lokaci d'aya Abdul ya tsaya da cin abin cin sa Amma kan sa yana 'kasa zuciyar sa wani irin suya take yi, Amar ya ce.. Yanaga dik kunyi shiru? Ko sabo da nafadin abin da yafaru a soyayrmu?

Abdul ya d'ago kan sa ya kalli Amar ya kalli Basma sannann ya ce.."ya naga kin de na cin abin cin? kici mana, yana kawar da tam bayar da Amar yayi musu, Basma tace.. Zan iya barin komai domin ka miji n. Kafin ta 'karasa Amar "ya tsuro da tarin 'kar ya hakan ne yasa bata 'karasa ba, ganinn haka yasa Abdul ya ce.. Tom alhamdu lillha nina goshi zan je in 'kawn ta, ita ma Basma tashi tayi ta nufi bayan sa domin 'kawn ciyar, har sun fara hawa sama Amar ya ce..

Gaskiya bazan iya 'kawna ni d'aya ba domin tsoro na keji. Shi ru sukayi suna kallon juna Sun rasa abin cewa se Basma ta ce.. "Amar wannann gidan nabu bamu da Aljanu babu abin da ze tsorata ka kaje ka 'kaan ta kawai. Amar yace.. Aa ni ban iya 'kawna ni d'ayaba kuma in naje d'aki zan iya shan kayan chaskewa saboda haka kawai, Wani yazo mu 'kaana tare, yana fad'a yana tashi tsaye, Se a lokacin Abdul yayi mgn yace.....✍️📝




**HAHA 🤣🤣🤣KAI JA MA A, GASKIYA CAKAWKIYA TAFARA , DAGA INI 'DAYA HAR YA ISHE SU, TO WAI ABDUL* **ZE JE SU KAWNA NE? KODE BASMA CE ZATA JE😉. KU KASAN CE DA S* ~REZA~ ✍️



HAGIQA ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️

The end of fart 9️⃣
To be continue..✍️


Please comment and Sher 🙏🥰


*By S REZA*
[12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: CAKWAKIYAR SOYAYYA 💔
Story and writers..✍️
S REZ.





بسم الله الرحمن الرحيم...

*08100785178*📞


ASLM


Ina maibawa masoya chakwakiyar soyayya hakuri bisa rashi jina da kukayi kwanan biyu✌️hakan yafaru ne sakomakon wayata da akadauke🤦🏽‍♂️ amma yanzu alhdul nayi wata nakuma dawo muku ashirye tsaf domin faran tamuku rai💞

GA SABON NUMBER NA.08100785178 S REZA``_

Gamasu bukatar cigabansa sai sumin mgn na sakasu cikin group din chakwakiyar soyayya 👌

*SADAUKARWA GA MASOYAN CAKWAKIYAR SOYAYYA* ❤



Page 1⃣1⃣


Da wani irin sauri ya fito daga cikin motar ko magana bai tsaya yiwa Amar ba ya nufi gurin motar,
Ganin ya kasa samun damar d'aure mata bakin ne yasa yake son ya d'auke ta gaba d'aya amma ina taki nustuwa D'aga kansa da zai yi sai ya ga ankusa zuwa gurin da su ke,
gashi kuma be cimma ai kin saba, yana ganin ya kusa ya fisge jakar hannun ta ya ruga aguje.

Ganin haka yasa Abdul bebi ta kan Basma ba ya bi bayan sa gudu su keyi amma ya kasa kamo shi Amar ne ya iso gurin da take ya tashe ta yana tambayar ta dama de lafiya?

Basma tace "Lafiya
babu komai fa pls muje kar yayi wa Abdul wani abu."

haka kuwa akayi tashi tayi su ka nufi gurin da Abdul d'in suka ruga da gudu.

Gudu ya keyi kamar gudun mutuwa domin kuwa yasan in har ya sake a ka kama shi to shikenan tashi ta k'are Yana cikin gudun ne agarin juyawa ya kalli me bin nasa yayi tinti'be take kuwa ya zube a gurin Yana fad'uwa Abdul yana karaso wa gurin domin kuwa babu tazara a tsakanin su.

Kafin Abdul ya karaso gurin sa Yazaro wata siririyar wuka

yace "Wallahi kana k'ara sowa sena yanka ka kar ka matso." yana nu nawa Abdul wukar Dede lokacin da Amar da Basma su ka k'araso gurin tare

Amar ya ce "Abdul rabu dashi dan Allah kana ganin fa wuka ce a hannun sa kar yayi maka illa."

Abdul ko kallon Amar beyi ba seda ya d'au kewa Wannan 'bara won hankali tukun se ji kayi ya kufce wu'kar a hannun sa, kafin ya ankare ya zab ga masa wani irin mari guda 3, yari 'komasa kwalar riga ya na zuba masa naushi. Tsabar wahala har besan lokacin da yasa ki jakar ba ya 'kwasa a guje, har Abdul yayi niyar sake bin sa amma "Basma tayi saurin tare shi tare da cewa pls Abdul dan Allah ka barshi haka, cikin kuka ta keyin maganar.

Amar ya zo kusa dashi cikin fad'a yake masa maga Haba Abdul baka ga abin da yake hannun sa bane wu'ka cefa, yan zu da ya yan keka fa akan wata jaka jakar ban za zaka je ka salwantar da rayuwar ka.

Abdul yace.."Wan'nan ba ban zan jaka bace , Wan'nan jakar abar tinawa ce agareni domin kuwa ita ce kyautar farko da na fara yiwa Basma. Ya mi'ka mata jakar. "Da gudu tazo ta rungume shi cikin kukan farin cikin tana cewa ina son ka Abdul ina alfaharida kai miji na.

Amar kuwa iya haushi yaji hau shi ganin yan da suke cikin farin ciki hakan yasa ya koma gefe har suka gama shirmen su acewar sa fa wai shirme su keyi. Ahaka suka dawo gurin moto cin su, Amma Abdul yaso yaji ko wani ne ya turo Wan'nan yaron, Abdul da basma su ka shiga motar basma, Shikuma Amar ya shiga motar Abdul, a haka su ka 'karaso gida.

Amar da Abdul suka nufi d'akin su, Ita ma ta nufi d'akin na ta. Yau asabar kuma yau kwanan Amar 5 da zuwa gidan. Suna zau ne shida Abdul a parlorn gidan suna hira, Basma ce d'au ke da tiran Kayan marmari, ta aje musu zata juya tata fi kenan Amar yace.. Basma ya a kayi ne? "bakomai" taba shi amsa a ta 'kaice.

Basma tace "yauwa Abdul dama ina son in sanar da kai gobe Zainab da mijin ta zasu zo akan magar da mu kayi da su ranar kuma sun ce yan zu da gaske suke akan rabuwa za suyi na tambaye su akan me suka ce wai se sun zo tukun na zamu ji kuma dama Lubna ma tace "zata zo tare da mijin ta." Abdul yace.. Wai da ma basu ha'kura da Wan'nan maganar ba har yanzu? Tom shi kenan Allah ya kawo su lafiya, Amin tace, tana niyar barin gurin se taji muryar Amar yana cewa..

Yauwa Abdul dan Allah in tam baye ka mana? Abdul ya ce "ina jin ka

Amar ya ce Shin kafin Basma da 'yan mata nawa ka ta6a yin Soyayya?

Abdul domin yaji meze ce yace "masa ina ganin za su kai uku ko hud'u, ya bashi amsa.

Amar yayi murmishi ya ce.."Haka d'in yana nufin Basma ce ta biyar, duk sau ran hud'un ba kasa mu damar auran suba, hakan yana nufin da ka auri wata daga cikin su da baka auri Basma ba ko? Kaga kenan kai kasamu za6i ni kuma bani da za6i, yaci gaba da maganar sa cikin nitsuwa da tau sayin abin da zai furta, ita kuwa basma har idanun ta sun fara cikowa da hawaye.

"Ni ban ta6a samun irin wan'nan damar ba, ita kad'ai na ta6a soyayya da ita, kuma da ita kad'ai naso nayi rayuwa ta, nayi burin ace tare zamuyi rayuwar auran mu tare, kuma sabo da Soyayya ta ta gaskiya ce, yana kawo wa nan hawaye suka wan ke masa ido yana kallon Basma wacce tini hawayan ta suka da d'e da yin ambaliya a fuskar ta.

Basma ce tayi juriyar iya ce wa "Amar ya kamata ka gane kana wuce 'ka'ida fa. Kafin ta 'karasa Andul yace "Basma kibar shi yayi maganar sa, jin haka yasa tayi shiru shi kuma Amar ya ci gaba da magana kamar haka.

Ya kalli Abdul yace.. "Shin lokacin da kaje neman auran Basma ka ta6a tambayar da ko tana da wanda ta keso? To da ace ka tambaya to tabbas zata sanar da kai ni take so nine a zuciyar ta, Ka ga kai dama ka ta6a yin soyayya kaga kenan da a ce ka tam baye ta da kaga kai zaka samu wata se kayi auran ka, to nikuma fa bani da kowa."

Kafin ya 'karasa Basma tace..Amar ya ka mata kasan irin maganar da zaka din ga furtawa Wan'nan abin da kake gaya an yishi ne tin a baya sabo da haka duk sun wuce.

Amar yace.. Haka ne ko? Wato sabo da ni yaro ne ku kuma man yane ko? Cikin kuka ya ke yin Wan'nan maganar. Yanzun ina son in muku wata tambaya? "Muna jin ka kayi tambayar ka, in ji Abdul wan da tin da Amar ya fara maga kallon sa ya keyi dik jikin sa ya mutu kuma har ga Allah dik abin da Amar d'in yake fad'a gaskiya ne.

Amar yace.."Wata yarinya anyi tunanin bata cikin farin ciki ita da mijin ta, Se ya tafi domin tabbatar da haka in kai ne ya za kace? Shin zaka fad'i kuna da wata ha la'kane tsa kanin ku kokuma baza ka fad'a ba?

Yaci gaba da cewa.. Idan yarinya tana soyayya da wani kuma taje ta auri wani daban shin shi wan cen meza a cemasa? Kaga kenan zan iya cewa kana da mummu nan hala'ka da wacce nake so rabin rayu wata, "ya ishe ka Amar baka da hankali ne angaya maka hakuri tsuro ne? Cikin ihu ta yi masa maga san'nan ta shigq d'akin ta tana kuka. Shima Abdul d'in hawa yen ya keyi ya tashi ya bita d'akin.

Amar kuka ya keyi kamar wanda a ka dake shi, afili yake furta, walhi ina sonki kuma Allah se nasa shi da kan sa ya sake ki, kuma na aureki, dan ke akayi ni nima kuma dan ke aka yini, a haka shima ya tashi ya nufi nasa d'akin.

*_________ALHAJI SANI*
Zaune suke shida uwar gidan sa wato Zainab hankalin sa a mu tu'kar tashi, kallon Ali yayi wan da shima hankalin nasa a tashe yake yace.. "An ya kuwa Ali bamuyi rashin tunani ba? "Ali yace abin da za'a yi kawai shine mushir ya zuwan baza ta dumin mu tabbatar" Alhaji sani ya ce.. "Gaskiya ina son yarin yata san'nan kuma bazan yarda ni da kai na in selaka ta a tsaka me wuya ba, walhi abin da ya faru da 'yar gidan mlm bala bana son ya faru a kan yarinya ta, gaskiya kashir ya mana tafi ya *ABUJA* gobe kuma bana so ta sani domin muje mu tabbatar da abin da muke tunanin, a haka suka tayar da maganar.

*TOFA MENE NE ZE KAWO ALHAJI SANI GIDAN BASMA? SHIN MASU KARATU DAMA DE BAKU MAN TADA 'YAR GIDAN MLM BALA BA WAN CE RANAR DA SUKA 'DAUKO AMAR A MOTAR SU HAR SUKA GA, WANI SAU RAYI WAI SHI DOLI SEYA AURETA, SHIN ME YA FARU DA ITA? ,HAR ALLAJI SANI YAKE TSORAN KAR YA FARU DA 'YAR SA, SHIN KUN SANE DA CEWA BESAN AMAR YANA GIDAN SU BASMA A ZAU NEBA?* KUKA SAN CE DA S REZA




*WASHE GARI* Da wuri basma ta tashi ta fara tar yar ba'kin su da abinci kala-kala, Seda ta kusa kammala girkin ne Lubna ta 'kirata ta sanar da ita cewa baza su samu da mar zuwa ba pls dan Allah tayi ha'kuri, amma zasu zo wata rana, bata ji d'iba haka taci gaba da 'kara girkin.

Mesalin 9 nasa fe kasan cewar yau lahad'i ranar hutu ce yasa Amar da Abdul babu wan da ya farka ita kuma se had'a musu abin ci take yi, tana cikin haka ne taji ana matsa 'kararrawar alamar mutum tayi mamakin jin haka domin kuwa tasan basu da wani b'ako, tin da lubna ta sanar mata sun fasa zuwa.

Tana bud'ewa ido ta zaro waje cikin mamaki had'e da far gaba da kuma tsoro duk a lokaci d'aya, Daddy ne shida Ali , da gudu tazo ta fad'a jin sa tana dariya, tace "daddy welcome san'nan ta gai sar sa Ali tana basu han yar shiga cikin parlour, tace.." Daddy me yasa zaku zo amma baka sanar da niba" "muna son muyi muku zuwan ba zata ne kuma gashi munyi muku ya me gidan naki?"

Dede lokacin da Amar ya tashi da wata shegiyar yunwa, ya man tama daga shi se rigar barci iya guiwa da wani gajeran wandan rigar, yabfito se wata mi'ka ya keyi yana hamma. Dede Daddy ya na tambayar ta cewa ya naji baki tambaye ni little b... Ai be 'karasa ba sukayi ido biyu da Amar wan da ya ke saukowa, shima sud'in yake kallo cikim mamaki da firgici, Daddy ne yayi 'karfin halin tambayar ta cewa shin Wan'nan meya keyi a gidan nan? Cikin kame kame Basma ta ce.. amm amm dama dama whi dad dad.......✍️📝




End of part 1️⃣1️⃣
To be continued..

Please comment and Shere🙏

This is my new number 08100785178. S REZA

By S REZA
[12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: *CAKWAKIYAR SOYAYYA*

*Story and writing..✍️ *S REZA*


©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم...


*Cakwakiyar* *Soyayya*🥰💔♥️

*PAGE* 1️⃣0️⃣


........ ABDUL yace" badamuwa bari inje sai mu kwana da shi ai ba damuwa, Kafin tayi magana ya sau'ko daga saman ya nufi d'akin da suka sau'kar da Amar d'in. Basma cikin mamaki tabisu da kallo har suka shige, bata iya cewa ko mai ba itama ta shige nasu d'akin.

A cikin d'akin madai kafin suyi barci abubuwan ban haushi ya ke tayi masa, irun su 'kurnanin barci da kuma d'aura masa 'kafa, kuma duk abin da ya keyi Abdul d'in yana jinsa amma ya nuna masa barci ya keyi. Shi kuwa Amar duk abinda ya keyi da saninsa ya keyi wai shi hakan kishi ya keyi.

*WASHE GARI* bayan sun kammala breakfast ne, wanda shi ma gurin breakfast d'in saida akayi abinda a kasaba. Abdul ne ya fara tashi ya ce" Basma ni zan tafi office. "Ok nima dama na gama shiryawa zan huce school bari se mutafi tare, kasan cewar dama tana cigaba da karatun ta` Har sun fara tafiya suka ji Amar ya ce"

Nikuma me Zanyi to?Sai ka kula mana da gida ko kuma kuyi wasa da teger, Tana nuna masa gurin da d'an 'karamin karan da suke kiransa da tegar. Shima kallon karan yayi yace "Dama kina nufin kun kirani gidan ku domin in yi wasa da tegar ne ko kuma in yi gadin gidan ku? Kafin suyi magana ya ci gaba da cewa to a cikin ku ina so in bi wani, Kallon junan su sukayi San nan Abdul yace " tom ba damuwa tashi mu tafi.

Suna cikin tafiya a motar ba wanda yake yiwa d'an uwansa magana, sai cann wani lokaci Abdul ya kalliAmar yace" Ka saka belet d'in ka, Amar ya ce "ok sannan ya ce yanzu a ina zamu ci abincin rana tunda ita matar gidan ta tafi school? Abdul be kalli in da yake ba yace"sai lokacin cin abincin yayi, Amar ya ce" Duk yanda kace ai haka za a'yi.

Basma waya ta d'au ka takira 'kawarta domin gaskiya lamarin Amar ya fara bata tsoro. Lubna Daidai lokacin tana duba wani mara lafa wanda ciwon ha'kori yake damun sa, dama ita 'ban garan data karanta kenan. 'Daga wayar tayi had'e da sallama, Bayan ta gama jin duk abinda Basma tace mata, san nan taja wani gajeran num fashi!! tace"

"Gaskiya wannan abinda ki kayi baki daidai ba ya za a yi ka kawo shi gidan ki tare da mijin ki wai ke hakan kina son ki temaka wa rayuwarsa? wai ma ina tinanin ki da hankalinki sukaje ne? lokacin da kika yanke wan nan d'anyan hukuncin? Gashi kince jiya yazo kuma daga kwana daya kacel kince yafara baki tsoro, to ina ga yakai sati daya ko biyu?

Basma ta ce"Ni zan iya fuskantar duk wata matsala a rayuwa in dai Amar zai koma cikin Rayuwarsa ta da, kuma nasan in sha Allah zai koma d'in. Lubna ta ce "kina ganin Amar zai iya dawowa cikin Hankalinsa nan kusa ?kinsan fa Amar yana son ki bazai yarda Bata bari ta'karasa ba Ta ce "sai anjima ta kashe wayar ta, Taja wani tsakii san nan ta ce" Dama nasan halinki shi yasa ma lokacin da zan kira shi ban nemi shawararki ba saboda nasan zaki iya 'bata min lamari.

Idan mun shiga office duk wanda ya tambaye ka kace masa kai aboki na ne, Abdul ne ya ke gayawa Amar haka lokacin da suke shigowa cikin camfanin. Amar ya yace"Idan kuma na gi fad'a fa Nace musu ni ne tsohon Saurayin matar ka Lubna fa? Yaba shi amma ata'kaice, ganin yanda ransa ya 6aci ne yasa shi saurin waskewa, ya ce" Ina nufin in na fad'a hakan baza kaji dad'i ba, Abdul bai masa magana ba ya huce suka ci gaba da tafiya ganin sun shigo ciki, kuma gashi ma'aikata sai gai she shi sukeyi.

office ya shiga, ya tarar ta ai'ki a gabansa sosai hakan ne yasa ya d'au lokaci yana ai ki. Amar kuwa ma'aikatan kamfanin gaba d'aya ya tara yana basu labarin cin amanar da Budurwarsa ta yi masa, Daidai lokacin da Abdul ya fito daga office d'insa ne yaga abin mamaki! wato Amar ya tara duk ma'aikatan yana basu labari ,su kuma sai dariya sukeyi suna washe baki. abin bai gama baki mamaki ba saida yaji abinda Amar d'in ya ke cewa,

Bama ai so d'aya ko sau biyu ba ai sau da yawa, wani daga cikin ma'aikatan yace" Kenan ta kasan ce har class d'in ku ta ke zuwa a school d'in ku? Kai amma gaskiya yarinyar kirkice, Wata mace daga ciki ita ma ta ce " kuma yanzu tana cikin farin ciki kuwa? Amar yace Ban sani ba amma nasan bata cikin farin ciki, wani ya 'kara cewa"

To me yasa bata kira ka ta sanar da kai ba se kawai ta auri wani? gaskiya bata kyu ta maka ba, Wan nan mace ta 'kara cewa "Gaskiya kam bata kyuta ba ai yakatama ace lokacin da a ka saka ranar ta kira ka ta sanar da kai in yaso se kusan abin yi,amma kuma taje ta auri wani gaskiya batayi ba, ta 'karasa maganar tana wani ya tsine fuska.

Amar yace" Ba damuwa fa yanzu haka ma yarinyar tana nan a *ABUJA* ita da mijin ta, amma fa wan nan ba komai bane bafa kawai dai ina baku labarin yaudarar da tamin ne. Duk abin da yafaru a kunnensa domin yaji komai Amma ya nuna masa baiji me yace ba.

Daya ke Abdul yana da sau'kin kai yasa ko lokacin da ya 'karaso gurin su babu wanda ya ji tsoran kar ya same su a haka, 'Daya daga cikin ma'aikatan ne yace" Gaskiya yalla'bai wan nan abokin naka ya had'u kaji labarin soyayya da ya ke bamu yanda kasan a cikin film wallahi gaski labarin abin tau sayi,

Abdul ya ce"Labarin soyayya kuma soyayar wa? Ya tambaye su, Wani ne ya ce "Yalla'bai labarin soyayar abokin sane ya ke bamu, Abdul ya ce" Tom tashi mutafi yana kallon Amar d'in Kafin Amar d'in yayi magana wan nan macen tace"Yalla'bai gashi kuma labarin ya fara dad'i kuma zaku tafi yaushe zaku dawo da shi domin ya 'karasa mana? "Cikin jin haushi yace kowa ya tashi ya koma bakin aikin sa ban san shirme!!... Haka kowa ya tashi yana ganin yanda Ran ogan nasu ya 6aci lokaci d'aya.

Bayan sun fito Ne suka biya ta wani kamfani wanda shima na Abdul ne, sai wajen biyar suka iso gida' suna shiga gida Abdul ya ce" Duk ranar litinin bama cin abincin dare a gida muna zuwa restaurant ne muci a can kashirya mutafi zamu same ta a can din.

Bayan sun iso ne kamar yanda yace kuwa a cen suka sameta tana jiran su, bayan sun zaun

Please Login or Register in order to submit comment