You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in kina sona Jewel...... "
Da sauri tace. "I loved you more wallahi kaman na kashe kaina nakeji saboda sanka inasanka sosai kuma banda lafiya ne shiyasa..."


Huci ya saki. "Koda kina sona bakimin irin yanda nake miki did yhu know what, wallahi duk numfashin da zanyi da sanki nakeyi inasanki like am crazy indai kinasona ki bani dama na turo gidanku a bani ke, I just want you to be mine forever na qosa na mallakeki, kaman na cinyeki na huta nakeji Jewel indai kikamin haka to zan tabbatar kina sona kuma ba yaudarata zakiyiba....."


Dan shiru tayi, kafin ta qaqalo murmushi dan yaji dad'i yasaki jiki tace. "Twinkle ai nima hakan nakeso na qosa kazama nawa shikenan ba damuwa niko yau nema ka turo na baka dama....."


Wani irin ihun farin ciki yayi. "Wow.....I love you more so bad my Jewel and I promise to take care of you am going to be ur best and truthful friends, u know truthful friends are always hard to find but am gonna be that truthful for you dear, am going to be ur 6ter friends, am gonna take good care of u just like a little baby...."


Shiru tayi tanajin wani iri a ranta, kafin yace. "Gobe zanyi tafiya zanje qasar India zan bud'e wani private hospital nawa acan ne like kaman se nayi kusan 2month indai na dawo zan turo anema min aurenki inaso a rananma a bani ke....."


Lumshe ido tayi. "Toh..."


"Jewel how is ur body yajikin dafatan kinji sauqi...."?
Kai ta d'aga. "Eh yanzu kam na warke..."


. "Allah sa Kaffarane..."
. "amin. " ta bashi amsa.


"Twinkle zanyi wanka..."


. "To a fito lafiya madam..."


Katse wayan yayi cikin farin ciki ya d'aga waya ya kira Atif danya bashi labarin yanda sukayi da Jewel.






Washe gari kam Aryan ya wuce India inda sunata waya kam sosai da Jewel dinshi har a jirgi.




Matar Abdul ce ✍️.
2022-10-08, 4:31 p.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
Haleema Isah (Mimi Queen)


Marubuciyar:
Rayuwa Sai dakee.
Labarina.
Barrister Shulaifat.
Son Zuciya.
Nisful hayat.
And now on _MANSURAT_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._


https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa


_____________________________________


Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_
Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance.


Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁.




Bismillahir rahmanir raheem.


35&36.




Kusan watannin Aryan biyu a India sannan ya fara mata maganan dawowa kullum se sunyi waya.


Soyayya da shaquwa me karfi ya dad'a shiga tsakanin Jewel da Twinkle.


A Yan tsakankani har anje an nemawa Farhan auren Laila kuma an basu anyi baiko, haka Nadiya da Atif suma an tsaida magana za'ayi lokaci daya da Farhan,
Itama Lubna da Noor dinta a maiduguri yake duk lokaci d'aya za'ayi.
Daddy dawowan Aryan kawai yake jira shima a matsa mishi ya fito da mata a had'a ayi gaba d'aya, amma yace Mansun shi karatu zatayi....


Yayinda yanzu mommy ta roqa aka bar mata Lubna a gunta.


*****
Yau taje gidansu Nadiya amsowa mommy saqo, wanda Nadiya ma batanan bayan momma ta bata saqon ta fito bakin titi dan taran napep ko mota.


Ta dad'e a tsaye bata samu abun hawaba kuma tanajin tsoro kada abunda ya faru da ita akan wa'innan smokers din ya qara faruwa, hakan yasa tafara qoqarin tsallaka titin kuma gashi ba glass a idanta.


Wata black motace kirar Benz ta shararo titin a guje, mamaki abun ya bashi yanda Mansu ke tsallaka titin duk da yaga alamun kaman ta ganshi amma ta juyar da kai, ita a nata a can nesa ta hango motan hakan yasa ta shiga titin.


Da gudu ya shiga seda ya kusa kanta sannan ya taka burki da karfi k'ara Mansu tayi tareda ja da baya.


Murmushi yayi ya bud'e motan ya fito yana dariya.


Tsayawa yayi ya zuba mata ido from head to toe wow gaskiya ta tsaru, amma qila makauniya ce.


Hakan yasa yace. "Meyasa kika fito ba sanda ba d'an jagora kuma kinsan bazaki iya tsallaka titi ba....? "


Murtuke fuska tayi, lallaima, cikin tsiwa tace. "Na maka kama da makauniya ce kome to Ina gani rasss...."


Murmushi yayi. "Badai rass ba dan ko yanda kikai da zaki tsallaka titin ya tabbatar min u not seeing well, meyasa kika fito batare da glasses ba...."?


Murgud'a baki tayi...."Saboda ban dauka zan tsallaka titi ba...."


Murmushi yayi domin yanda yarinyar keyi na burgeshi.... "To what if you got yourself killed bayan u know your condition in abu is far ko close baki cika gane waba seda glasses...."


. "In hakan ta faru shikenan na mutu meya shafeka ai ainice na mutu bakaiba....."


Murmushi yayi. "To in hakan ta faru ai ni kikama asara...."


Hararanshi tayi ta juya, da sauri yace. "Kizo in rage miki hanya miss makauniya...."


Murgud'a mishi baki tayi, da nufin wucewa cikin firgitarwa yace. "Ga daff nan...."


Da sauri ta dawo, dariya yasa hararanshi tayi. "Badan ina tsoron mutuwa na dawoba sedan banason wahala ne nafiso en uwana suga gawata lafiya..."


Murmushi yayi. "Hakane yanzu dai shiga mu tafi...."


Ba musu ta bud'e gaban motan shima ya shiga yafara tuqi,


Dubanta yayi. "Me sunan malaman."?


A sanyaye tace. "MANSURAT....."


"Mansurat..?? "
Ya maimaita, shiru tayi. "Okey am Aman Umar..."


Banza ta mishi ta juyar da kai, bata sake magana ba duk abinda yace, seda ya tambayeta sunan unguwansu, sannan tace. "Millinion city...."


A bakin gate din gidan yayi parking, a sanyaye ta fito. "Nagode..."


Harta juya yace. "Mansurat baki bani numban kiba..."


. "banda waya...."
Murmushi yayi. "Banyarda ba..."


. "Hummmmm. " huci tayi,


. "Indai wata rana mun qara had'uwa zan baka amma ba yauba..."
Tana fadin haka ta shige, murmushi yayi yaja motanshi ya wuce.


Labari ta bawa Aryan, cewa taje gidansu Deeyah, wani ya daukota amma bata fad'a mishi yanda akai ba.


Shiru yayi, hakan yasata cewa. "Kayi shiru Twinkle... "Jewel..."
Ya kirata cikin muryanshi data canza lokaci d'aya..


A sanyaye tace. "Uhmmm..."


. "Jewel inada kishi mai zafi ki temaka mini ki riqemin amanan kanki kinji ko....? "


. "Tohhh..." Tace.
. "Jewel gobe zan dawo Nigeria...."
Murna tayi sosai.




Aiko Washe gari tunda wuri suka je shooping suka dawo suka shiga kitchen itada Lubna suka had'awa Aryan abinci kala da kala na tarba, wanda mommy tayi mamaki sosai amma suka roqeta kada tace harda Mansu akayi, murmushi kawai tayi.




Karfe biyu jirgin su Aryan ya sauka, Farhan ne yaje airport ya d'aukeshi.


Waya Dikko yakeyi tunda ya shiga motan, seda ya sauke wayan sannan Farhan cikin zolaya yace. "Bro din Jewel ya aunty jewel take....? "


Hararanshi Aryan yayi. "Wai Farhan yaushe nafara wasa dakai haka....."


. "Afuwan Yaa Dikko to ya en matan India..."?
Mugun kallo Aryan ya mishi hakan yasa cikin dariya yace. "To nace ya auntyna jewel baka bani amsaba ba dole in tambayi en uwana indiyawa ba..."


Tsaki Dikko yaja tareda juyar da kai a ranshi yana addu'an Allah shirya Farhan.


Kafin Farhan yakuma cewa. "Yaya yaushe zakuyi aure..."?


Da kaman ze basar se kuma yace. "Ran Friday zan tura may be ma abani aurenta ranan...."


Cikin farin ciki Farhan yace. "Kenan saura 4days dan yau monday ne....kai Masha Allah..."


A haka suka karisa, Mansu ta kasa hakuri ta qosa taga Twinkle hakan yasa ta fito compound ta zauna kan resting chair ta saka glass tana karanta novel din the noisy neighbor amma hankalinta nakan gate.


Tun daga nesa take hangoshi ya kara kyau sosai da haske yayi 'bul'bul suman kanshi da sajen shi sun kwanta lufluf.


Yana karisowa ta d'auke kai ko kallanta beyiba ya shige ciki.


Farhan ne ya kariso yana dariya yace. "Amarya....."


Cikin rashin fahimta tace. "Kamanya.. "?
. "Amaryan Friday mana koba ranan kikama Twinkle dinki alqawarin aureba...."


Gaban tane ya fad'i se yanzu ta tuna da maganansu da sauri ta tashi ta shige ciki dan neman shawaran Lubna.


Aryan kam da kaman bazeci abincinba dan mommy tace Lubna tayi, danshi ba abincin ko wata qazama yake ciba amma kamshin abincin ne yaja hankalinshi yaci, aiko yasha santi Farhan har video yamai......




********
Yau Thursday, kuma gobane cikan alqawarin su DrDikko ze tura.


Waya tayiwa Nadiya akan tazo dan Allah,


Se safa da marwa takeyi ta kasa zaune ta kasa tsaye, zuwan Nadiya kawai take jira ta fad'a mata mafita dan tace tasamo solution.


Ayya da take kallon Arewa24 dubanta tayi. "Lafiyan ki kam Mansu ko akwai abinda ke damun kine...."?
. "Aa Ayya, bala nake jira na aikeshi ya siyomin abun. "
. "to kije ki duba koya dawo mana amma kinata safa da marwa..."


Da sauri tayi waje, dan dama wajen takesan zuwa duk ta 'kosa Nadiya tazo,


Aryan na tsaye a parking lot batare data lura dashiba ta nufi gate,


Ido ya bita dashi ganin tayi gate da sauri ko hijab bata saba, hakan yasa da sauri yabi bayanta dan yaga me zata aikata....


Bayan wata jeep ya tsaya, yana kallonta ta d'aga waya. "Wai kina inane ki sauri banaso Ayya tasan maganan da zamuyi ne kinga yamma nayi..."


Katse wayan tayi dan Nadiya tace ta qariso.


Da sauri taje ta bud'e kofan gate din, ta leqa waje,
Daidai lokacin Nadiya ta kariso, shigowa sukayi duk yana kallon su, tsaki Nadiya tayi. "Banza duk kinbi kin isheni kaman wani yaune zezo...."
Kaman zatai kuka tace. "Nadee ya zanyi yace anjima in munyi waya zan fad'a mishi address dinmu....."


Murmushi Nadiya tayi. "....JEWEL....DIN...TWINKLE....."


A razane Aryan ya juya yana kallon su yana goge kunninshi ko beji da kyau bane,


Duka Mansu takai mata. "Banasan iskanci Deeyah mu karisa garden muyi magana..."


Da sauri Aryan ya ciro waya ya lalubo numbanta a rud'e yake matuqa har dishi dishi yake gani.


Wayan Mansu ne yayi ringing da sauri tacewa Nadiya. "Shishshshshsh....it's Twinkle..."


Picking tayi tareda kaiwa kunninta. "Hello....Love...."


Innalillahi wa'inan ilaihir raji'un.....


Kasa magana Aryan yayi, jin yayi shiru yasata cewa. "Hello Twinkle dina say somethin......"


Kaman ance ta juya juyawan da zatayi sukayi ido hud'u dashi,
Idanunshi har sun fara zubar da kwalla,


Chakkk ta tsaya haka itama Nadiya da idanta ya sauka a kanshi, bakinshi na rawa ya d'ago yatsanshi yana nunata....
....."J....E...WE...LLL...."


Sulalewa yayi a qasa ya zube ko motsi bayayi.




Matar Abdul ce✍️.
2022-10-10, 8:41 a.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
Haleema Isah (Mimi Queen)


Marubuciyar:
Rayuwa Sai dakee.
Labarina.
Barrister Shulaifat.
Son Zuciya.
Nisful hayat.
And now on _MANSURAT_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._


https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa


_____________________________________


Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_
Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance.


Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁.




Bismillahir rahmanir raheem.


37&38.




A hankali ya fara bud'e idanunshi da yaji sun mishi nauyi harya bud'esu a saman pop din asibitin,
Juya idanunshi yayi zuwaga right hannunshi dake manne da drip, da sauri ya lumshe idanunshi,


Lokaci d'aya komai ya dawo mishi da sauri ya bud'e idanuwan,


Bud'o kofan akayi da sauri ya zuba idanunshi kan qofan dan wanda ze shigo.


Farhan ne ya shigo shida Lubna dake dauke da warmers na abinci a basket,


Lumshe ido yayi,
Mansu dake noqewa a sanyaye ta shigo
Ganin kaman Aryan yana bacci yasa duk suka samu guri suka zauna.


Dubanshi tayi ganin yanda yabi ya rame ciwan kwana biyu amma yabi ya fad'a kaman wanda yai jinyan shekara,


Duban Farhan tayi. "Ya Farhan be farka bane....."?


Da sauri ya bud'e idanunshi jin muryan da ko a mafarki baze ta'ba mantawa dashi ba,


Tana sanye da hijab a jikinta har qasa wanda baka iya ganin kayan dake jikinta, idanunta na manne da eye glass dinta me matuqar k'ara mata kyau, ido ya zuba mata ganin ya bud'e ido yana kallonta yasata sunkuyar da kai qasa tanajin nauyin had'a ido dashi dan wani kwarjini yau daya mata.


Bangaren Dikko kam, neman tsanan da yayiwa Mansu yayi gaba d'aya ya rasa, ji wani irin santa na fizgarshi so yakeyi kawai ya ganta a jikinshi.


Farhan ganin irin kallon da Aryan ya qure Mansu dashi yasa yayiwa Lubna signa.


. "Zo muje mu shigo da sauran kayan a mota...."


Tashi sukayi duk suka fice, sunkuyar da kai Mansu tayi qasa ganin irin wani kallo yau da Dikko yake mata kuma gashi sun fita sun barta.


Bud'e baki yayi cikin murya me breaking yace. "Je..wel....."


Banza ta mishi ta qara sunkuyar da kai, tana wasa da kyawawan yatsun hannunta,


A hankali yakai left hand dinshi ya zare drip din dake jikinshi, a hankali ya tashi.


A sanyaye ya sauka a hankali ya qarisa kujeran da take zaune, duqunnawa yayi ya daura hannayenshi a cinyarta yasa hannun ya d'ago kanta,


Seda gabanta ya fad'i ganin yanda idanunshi sukayi jajawur,
Kawar da kai tayi da sauri.


Cikin muryan kuka yace. "Please look in to my eyes Jewel ko zaki iya fahimtar irin san da nake miki, I love you more Mansu.....tabbas kinmin hukunci mafi tsauri a rayuwa but I will not judge you on it cos I love you fiyeda tunaninki.....kuma kema nasan kina sona ko My Jewel.? I vow to be royal to be honest and truthful with you at good and bad times bazan kuma barinki ki zubda hawaye ba please marry me Jewel......."


Wani irin murmushin izgilanci tayi ta d'ago ta sauke gaba d'aya idanuwanta cikin nashi.

Cikin nuna rashin tsoro tace.
. "Hummm I regret every bit of our relationship, I mean it I regret every single bit of it, you know what I hate you either is over between us...."


Tureshi tayi ta miqe zata fice, da sauri ya riqo hannunta......
. "I love you to the extend that I can't effort loosing u I love u then now an forever, am sorry please don't judge me for duk abubuwan da suka faru a baya I regret it, I repeat I regret it please forgive me..... "


Kuka ya fashe dashi dan ji yake kaman ana hura mishi wutan santa a cikin zuciyanshi.


Murmushi ta kumayi. "Am so done with you like hummm you are to smart actually I thought something was wrong with you cos u seems off...."


Cikin kuka yace. "I love you please marry me I promise to make you the happiest women on earth, I promise to be your friend, your brother and I promise to love you forever and am gonna be the best husband ever.
Am sorry for every hurt, I will tell the hole world that I love u inasanki sosai...."


. "bazan ta'ba sanka ba Dikko na fad'ama komai ya qare tsakaninmu the game is over and I......."


Bata qarisaba ya sulale a qasa yana juyi tuni bakinshi ya fara fidda kumfa,


K'ara tasa nan take hawaye suka fara fita a idanunta ta rasa me zatayi, daddy ne da mommy suka shigo dakin ganin halin da yake ciki yasa mommy tafita da sauri kiran Doctor....


Tambayanta daddy yake meya faru, amma ta kasa magana se kuka takeyi duk tabi ta firgita....


Tana tsaye Dr Ridwan ya shigo suka maida Aryan kan bed, sannan doctor ya mishi wani allura nan da nan kumfan ya dena fitowa ya koma kaman gawa illa numfashi da yakeyi sama da sama shize tabbatar maka yanada rai.


Juyowa doctor yayi yana tambayansu meya faru,
Dukkansu Mansu suka kalla,


Da gudu Mansu dake kuka sosai ta bud'e kofan ta fice da gudu, tana kuka fita tayi daga asibitin tana fita ta tari napep ta shiga.


Har suka kai , barnawa complex bata dena kuka ba ta bashi kudin shi ta shige gidan da gudu, Ayya na d'akinta hakan yasa ta shige d'akinta da gudu tana wani irin kuka me fitan rai.


Lubna ne da Nadiya sukazo gidan dan duk sun kirata be shigaba kuma sunje asibiti batanan,


Bayan sun gaisa Ayya tace musu. "Inaga ta dawo domin naji shigowanta d'azu ku shiga tana ciki....."


D'akin Mansu suka nufa, tana raku'be gefen gado se kuka takeyi tana ganinsu ta tashi da gudu taruga ta fad'a jikin Nadiya.


...."Na shiga uku Nadeeya Dikko na sona sosai bashida lafiya saboda ni wallahi nima inasanshi amma bazan iya rayuwa dashi ba, I want him to regret before I want him to know you can't disrespect women and go free,
Amma inasanshi sosai Nadiya please ku temakeni banasan ganinshi cikin damuwa pleasssss..... "


Ta fashe da kuka ta sulale a qasa dukkansu suka tarbota cikin tausayawa, da kyar suka samu Mansu tayi shiru daganan a hankali bacci ya d'auketa,


Gaba d'ayansu suka bita da kallon tausayi, Nadiya najin dana sani domin gani take itace ta jefa duka zuciyoyi biyun a halin da suke ciki yanzu, domin ita taba Mansu wannan shawaran.




Tun daga ranan Mansu bata sake zuwa asibiti ko gidansu Mommyba kullum tana gida.


Shikam Aryan kwananshi uku besan inda kanshi yakeba.....


A rana na hudu ya farka yana kiran sunan Mansu,
Lokacin kowa yana d'akin, daddy, mommy, Farhan, Lubna, Atif, Nadeeya harda doctor Ridwan.


Kowa ya cika da mamakin jin ya farka da sunan Mansu amma badda Farhan, Nadeeya da Lubna,
_To meke tsakaninsu kenan?.
Kowa ke tambaya a ranshi.


Doctor Ridwan ne ya dubi su daddy. "Dama nafi tunanin da abinda DrDikko yake buqata, to yanzu na tabbatar da bincikena dan haka wannan Mansun da yake kira ita yake buqata dan haka kuyi gaggawan mai abinda yakeso domin yanasanta sosai, dama sau tari wa'inda basu ta'ba soyayya ba in suka fara gushewa hankalinsu yakeyi se kuga ba abinda bazasu iyaba wadu har mutuwa sukeyi akan abinda sukeso dan basu iya so kadan ba, dan haka dan Allah ku ceci rayuwar tsayayyan namiji irin Doctor, yanzu dai ku bashi guri ya huta..."
Yana fadin haka ya fice.


Gaba d'ayansu sun cika da mamaki a sanyaye dukkansu suka fice.




Washe gari.


Mommy da Daddy da Farhan suna d'akin ya bud'e ido, kallo daya ya musu ganin ba Mansu a d'akin yasa ya maida idanshi ya lumshe lokaci d'aya hawaye suka fara zuba a idanunshi tuna abinda Mansu tace na bata sanshi.


Matsawa mommy tayi kusa dashi. cikin tausayawa tace. "Son.....meke damunka.."?


Daura kanshi yayi kan cinyarta hawaye na dad'a zuba a idanunshi, itama nan take taji hawayen sun wanke mata fuska cikin muryan kuka tace.


. "I know u're My strong brave boy,
My Son feel free fad'amin meke damunka....."


... "Mommyyyyy....."
Ya fad'a tareda d'ago kai, sumarshi ta shafa. "Na'am yarona...."


Daddy da Farhan ya kalla suma da suke tausaya mishi ganin halin da yake ciki a kan mace,


Kafin ya kuma kallon mommy yace. "Mom.....Mansu..Mansuuuuu...inasanta sosai she's my jewel mommy....amma ita ta tsaneni tace bata sona tanaso tarama duk abinda na mata, kuma ai I regret ko mommy.....? "


Cikin kuka ta d'aga kai, kaman karamin yaro yaci gaba. "Mommy na bata haquri nace ta aureni amma tace bazata aure niba, mommy nikuma idan bata aure niba mutuwa zany....... "


Rungume shi mommy tayi ta fashe da kuka, tanajin qaunar d'an nata ako ina,


Karisawa daddy yayi ya shafa kanshi yace. "Dikko na indai ka aureta zaka rayu zaka tsaya tareda da daddynka bazakayi nisa da niba...? "


Da sauri ya d'ago yana d'aga kai. "Eh daddy..."


Murmushi daddy yayi. "Na maka alqawari indai na isa da Mansu sena mallaka maka ita na har abada...."


Kuka ya fashe dashi na murna ya rungume daddy, da sauri shima Farhan ya rungume shi shima yana kuka.


Jin za'a bashi Mansu yasa ya saki jiki yaci abinci da magunguna sosai,
Duban daddy yayi. "Daddy na warke mu koma gida inga My Jewel..."


Shafa kanshi yayi. "Ka bari ka qara samun sauqi..."


. "daddy you know am a doctor zan iya kula da kaina please inaso in ganta...."


Daddy ne ya riqeshi suka fice, mommy da Farhan kuma suka tsaya d'ebo kaya.




A mota daddy yayi dialing numban Mansu, lokacin tana zaune tanacin abincin da take jinshi kaman magani.


Dauka tayi ta gaidashi, bayan ya amsa yace. "Kizo gida yanzu ina nemanki ki taho tareda da Ayya...."


Gaban tane ya fad'i amma ta daure tace. "Toh...."


Katse wayan tayi ta fad'awa Ayya saqo, basu jimaba suka shirya.


Bala driver ya d'aukeshi zuwa millinoin city.







Allah ubangiji ya jiqanki Ammyn mu Allah kai haske kabarinki Allah raya zuri'a.


Please kuyi mata addu'a matsayin uwa take a guna.




Matar Abdul ce ✍️.
2022-10-11, 10:31 p.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
Haleema Isah (Mimi Queen)


Marubuciyar:
Rayuwa Sai dakee.
Labarina.
Barrister Shulaifat.
Son Zuciya.
Nisful hayat.
And now on _MANSURAT_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._


https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa


_____________________________________


Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_
Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance.


Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁.




Bismillahir rahmanir raheem.


39&40.


Kan Mansu na qasa tunda ta zauna a kan carpet din bata d'ago kaiba gaban tane keta fad'i, Aryan na zaune a gefenta ya kafeta da idanuwa jiyakeyi kaman ya cinyeta ya huta se faman murmushi yakeyi.


Daddyne ya kira sunanta. "MANSURAT....."
D'ago kai tayi. "Na'am daddy....."


Maida kai tayi qasa tana sauraran abunda daddy zece.
. "MANSURAT kiyafe mana munsan mun miki ba daidaiba amma ganin mun isa dakene yasa muka aikata hakan...."


Qara sinnar da kai tayi tana girgiza kai tuni hawaye yafara bin kuncinta, cikin dakewa tace. "A'a daddy niba abinda zakumin na kuskure akoda yaushe ku masu iko ne dani kuma nime biyayya ce a gunku...."


. "Alhamdulillahi....."
Daddy ya furta, kafin ya dubi Ayya yace. "Ayya yau zamu fad'a musu komai yau zamu fayyace musu abinda muka b'oye musu muna jiran lokaci, to yau lokaci yayi..... "


Murmushi Ayya tayi. "Allah nagode maka daka nunamin wannan rana da raina ban mutuba za'a fad'i wannan sirrin da muke b'oyewa shekaru da dama...."


Cikin rashin fahimta Aryan yace. "Daddy wani sirrine wannan....? "


Mommy ce ta harareshi. "Yi ma mutane shiru..... "
Maida baki yayi ya tsuke, Mansu kam idanta na runtse in banda hawaye ba abinda ke sintiri bisa kuncinta, a cikin zuciyanta kam
" Innalillah wa'innan ilaihir raji'un. " kawai take maimaitawa.


Daddy ne ya nisa. "Uhmmmm. "
Kana yace. "Shekaru tara da suka wuce lokacin Mansu nada shekaru goma sha uku a duniya, muka zauna nida Ayya muka yanke hukunci dukkanmu bamuda buri daya wuce muga mun had'a Mansu da Aryan aure, sedai su sun tsani junansu hakan yasa muka yanke shawara a wannan lokacin muka nemi dangin mahaifin Mansu muka d'aura musu aure batareda sanin suba dan lokacin Mansu ko hankalin kanta bata saniba, hakan yasa muka maida Mansu gaban Ayya inda Aryan yakeyi da niyyar in suka taso tare qila su fara san junansu duk randa suka bud'e baki sukace sunasan juna semu bayyana musu wannan sirrin da babu wanda yasani daga ni se aminina Alh. Abubukar da wakilan Mansu se mommynku da Ayya,
Amma se gani mukayi tsanan kullum qaruwa yakeyi hakan yasa muka jinkirta ba tareda mun sanar dasu wannan sirrin ba mun qudurta ko za'ayi shekaru dubu d'ayanku be bud'e baki yace yanasan d'ayaba bazamu fada mukuba,
Shiyasa na haramtawa Mansu kula kowa kuma nima bana amsan duk wanda yazomin da maganan neman aurenta.


Munyi matuqar farin ciki da Dikko da kanshi ya bud'e baki yace mana yanasan Mansu kuma yayi nadaman duk abinda yayi a baya,
Princess ki gafarcemu munsan bamu kyauta mikiba amma ki fad'a mana idan bakisan Dikko se a raba auren dake da Dikko duk yaran mune bazamu tauye miki haqqinki ba a matsayin ki na yarinyar mu......"


Mansu kuka takeyi na fitan hankali dan gaba d'aya ba wanda bejin kukanta, tarasa ina zatasa kanta
. "Allahumma ajirni fi musibatin wakhlifni khairan minha, innalillah wa'innan ilaihir raji'un....."
Shine abinda take fad'a cikin ranta tana kuka, cikin kuka muryanta na cracking tace. ".... Da...ddy.....har abaaa...da....ni me biyayya ce....a gareku......bazan ta'ba bijirewa umarnin kuba akoda yaushe za'bin ku shine nawa..... "


Ba wanda beji dadin abinda ta fad'a ba, Dikko kam ya rasa ina zesa kanshi saboda murna baki har kunni, Farhan kam cike yake da tausayin Mansu haka Lubna.


Cikin jin dad'in magananta daddy yace. "Mungode sosai Mansu Allah muku albarka gaba d'ayansu yabaku zaman lafiya, zanyi magana da mommynku se asa ranan tarewan naki kinji ko.....? "


Batace komai ba taci gaba da kuka, nan daddy yayi addu'a ya rufe taro

Please Login or Register in order to submit comment