You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na zaratan maza ne amma a
niste yake yi, cewa yayi, "Idan kika gwada aikata wannan kuskuren to lallai za ki
yi danasani a rayuwanki na da baki zo duniyar ba ma, nothing concern me with our
blood relationship, dan zan ɗau mummunan mataki a kan ki ne ko da kuwa zai raba kan
family ne i don't care, duk randa tayi ko da ciwon kai ne, kuma ke kika zama sanadi
to za ki sha mamaki, stupid girl marar aji kawai, ba ta in da za ki haɗa kan ki da
precious diamond mace mai aji da sanin ya kamata, kina ballagaza wawiya", yana gama
faɗa ya kashe wayansa yana huci, ga ɓacin ran Manseer ga wan da ta ƙara masa, a ce
ayi mace a duniya bata san inda ke mata ciwo ba, dole ne sai ka so wanda baya son
ka.

Tsaki ya kuma ja ya ce, "Mutane sai ka ce dabbobi mai zan yi da ke? useless girl
kina zaune cikin ƴan iska kina abin da ranki yake so, bazan auri sauran wasu ba no
matter how."

Sai da ya ɗan saita zuciyarsa da yake ji a ɓace, sannan yayi dialing layinta,
ringing ɗaya yana shiga ta ɗauka kaman wacce ke jira daman, cikin zazzaƙar
sassanyar muryanta mai daɗin sauroro ga sanyi ta ce, "Assalamu'alaikum wa
rahmatullahi wa barkatuhu abun ƙaunan Jidderh."

Jin muryanta kaɗai ya saka shi samun wani ni'imtaccen nistuwa, idan ana neman mace
tagari jin daɗin duniya to jidderh ta wuce in da ake nema ma, shiyasa maganan
Manseer yayi mugun ɓata masa rai, dan nunawa yake kaman bai wani damu ba, amma a
can ƙasan zuciyarsa yan da yake jin ta daban ne, duk cikin ƙannensa babu ya ita,
dan ita ɗin kyauta ce daga Allah, ga duk wan da ke tare da ita.

Lumshe ido yayi yana busar da iska mai zafi a bakin sa, amma bai ce mata komai ba,
sallaman ma a zuciya ya amsa, ita ma jidderh a nata ɓangaren lumshe idon tayi,
tana jin ta cikin wani irin yanayi, Allah ne kaɗai yasan irin ƙaunar da take wa
wannan bawan nasa, ji take rashinsa zai iya kawo ƙarshen rayuwanta, tana masa son
da bata yi wa kanta ko kwatansa, juyi tayi tare da ƙanƙame pillow a jikinta tana
jin fitar ko wani sauti na numfashinsa a cikin wayan, kaman a fiskanta yake sauƙe
numfashin, wani irin yanayin ƙaunarsa take ƙara stunduma, kuma shirunsa daɗi ya
mata bai dameta ba, dan tasan daman ba lallai ya amsa mata ba muddin ta faɗi hakan.

A hankali ta raba laɓɓanta da junansu ta fitar da sautin, "Yayana abun ƙaunata
fatan ka wuni lafiya cikin aminci? Ya gida? ya aiki?"

"Alhamdulillahi", haka kawai Shaameekh ya faɗa a taƙaice.

"Masha Allah! Yayana abun ƙaunata ina matuƙar kewanka", faɗin jidderh cikin
shagwaɓa kaman ƴar jinjiran kule.

Shaameekh da shi kaɗai yasan abin da yake ji, da kuma yanayin da yake shiga
musamman idan tayi wannan shagwaɓan nata, ajiyan zuciya kawai ya sauƙe yayi shiru
bai ce komai ba, amma dai yasan yanayinsa a yanzu ya koma dai-dai, ya ma mance da
ɓacin ran da yake ciki.

"Yayana yaushe za ka dawo? ka ga su Hajiya Mama sun fara surutu."

"Soon Insha Allah", yanzun ma a taƙaice ya faɗa hakan.

"To Allah ya sa, Allah ya dawo mini da kai lafiya, ya tsare mini kai, Allah ya
hana ko wacce mace kallonka."

"Ameen nagode da addu'a", ya faɗa yana mai shafa sajensa.

"Bakomai Mijin Jidderh in Allah ya yarda."

"Ki kwanta dare nayi, ki gaishe da kowa da kowa, gudnyt."

Jidderh a ɓangarenta shagwaɓe fiska tayi kaman tana gabansa, amma ba yacce ta iya
dole ta ce, "Allah ya tashe mu lafiya."

"Ameen take care byee."

"Byeee Yayana kuma mijin jidderh", ta faɗa tana sakin murmushi.

Shaameekh ma murmushin gefen baki yayi wan da ya matuƙar fito da kyawunsa, sannan
ya kashe wayan, ba ɓata lokaci kuma ya miƙe ya shige toilet, sai da ya staya ya
wanke toilet nasa tsaff da shi kaman ka zuba abinci ka ci a ciki, sannan ya fara
wankansa.


Jidderh kuwa bayan ya kashe wayansa, rungume wayan tayi a ƙirjinta stam (kaman
Shaameekh ɗin ta samu), tana sakin murmushi mai sanyaya zuciya, duk da ba hakan ta
so ba ƙanin miji ya fi mijin kyau, bata so ya kashe yanzu ba dan jin muryansa bai
ishe ta ba, a hankali ta ce, "Yayana ina ƙaunarka, Allah barmun kai, Allah ya
kulamun da kai a ko ina kake, Allah ɗaura ka a kan maƙiyanka."

Tashuwa jidderh tayi ta kashe wutan ɗakin, sannan ta koma ta kwanta da niyan
bacci, sai dai dirin neman agaji wayanta ya shigo wayanta, tura baki tayi kaman mai
ƙiran na kallonta, dan tasan babu mai ƙiranta yanzu idan ba maye Safwan uban ƴan
naci ba, har kaman ba za ta ɗauka ba, sai ta fasa ta ɗauka tare da yin sallama, shi
kuma ya amsa a nasa ɓangaren, tare da cewa, "Babe ya kike ya daren?"

"Alhamdulillahi!" Ta faɗa a taƙaice.

"Gud haka nake so, babe nasan yacce naji muryan kinnan bacci kike ji so, nima
daman muryanki kawai nake buƙatan ji dan na samu yin bacci, so take care ko."

"Nagode Allah ya tashe mu lafiya", jidderh ta faɗa bakin nan a ture.

"U are welcome babe I love you soo much byee", yana faɗa ya kashe wayansa.

Jidderh harara ta bankawa wayan sannan ta ce, "Ka taimaki kan ka da ka kashe", tana
faɗa ta ja blanket ta rufu sai bacci kuma, safiyar alkhairy jidderh.


A gidan big Dad kuwa, Hajiya Kubra matar big Dad wacce suke ƙira da Mom, zaune take
a gefen Alhaji Sulaiman(Big Dad), da ke waya da su baba alhaji ta haɗa rai, duk
abinda suke cewa tana ji, bayan Alhaji ya gama wayanne ya juyo tare da kallonta ya
ce, "Hajiya ya aka yi?"

"Hmmn! wani irin yaya aka yi kake tambaya na, wai nikam du-du-du yarinyar nan a
nawa take? kuma fa nasan tana dawowa ita ma soon."

Big Dad murmushi yayi ya ce, "Kar ki damu kan ki da maganan su baba alhaji,
soyayyan da yake yiwa jikokin nasa ne ya ja haka, kar ya dame ki dan Baba na son
jikokinsa fiye da tunani, mu dai mu mata addu'an Allah ya dawo da ita lafiya shi ne
kawai, duk wannan ba wani abun dogon magana bane."

"Uhmn! Ameen to Daddyn Soffy."

Shikkenan big Dad da Mom suka ci-gaba da hiransu kaman ba komai.




Shameekh bayan ya gama wankan ne ya fito ɗaure da farin towel nasa, ɗaure a
ƙugunsa jikinsa duk ruwa, wannan lema-leman ruwan sai ya tafi da gashin jikinsa
hakan ya ƙara masa kyau.

Ba tare da ya kunce towel ɗin ba balle saka kayan bacci, haka ya wuce direct kan
gado ya faɗa ya kwanta haka, yayi addu'a ba jimawa bacci yayi gaba da shi mai daɗin
gaske.

Ƙarfe huɗu 4am na dare na bugawa Shaameekh ya tashi, sai lokacin ya cire towel ɗin,
ya sanya armless da 3quater ya saka duka baƙaƙe, ficewa yayi a ɗakin da tafiyansa
ta burgewa, wani hanya ya ɗauka daga palourn wan da ya sada shi da, haɗaɗɗen wajan
mosta jikinsa.

Tun ƙarfe huɗu yana abu guda sai zufa yake haɗawa, kaman wan da ya yiwa sarki
ƙarya, shi ne bai sarara ba sai da lokacin sallah yayi.

Yana fitowa a wajan ya ɗau goran ruwa a fridge ya kwankwaɗa tass, sannan ya wuce
haɗaɗɗen ɗakinsa ya watsa ruwa sama sama bai staya ɓata lokaci ba, yayi alwala ya
fito, jallabiyansa ya saka fari mai kyau ya ɗau keyn motansa ya fice a gidan.

Masallaci ya je yayi sallah, ko da aka idar bai baro masallacin da wuri ba, dan sai
da yayi lazuminsa da azkar nasa, sannan ya juyo gida, nan ma bai yi komai ba ya
zauna karatun Alqur'ani, shi ne bai rufe Qur'anin ba sai da ƙarfe bakwai tayi, yana
rufewa ya jero addu'oensa ya shafa, sannan ya cire jallabiyan ya bi lafiyan gadonsa
ya kwanta.



Ɓangaren jidderh ma da asussuba ta farka wajan ƙarfe biyar, da addu'an bacci da
kuma salati ta fara buɗe bakinta, sannan ta miƙe ta wara idanuwanta a hankali, miƙa
tayi ta sauƙo daga makwancin nata, ta wuce banɗaki, sai da ta wasta ruwa sannan
tayi alwala ta fito, raka'atainil fijir tayi ta zauna yin istigfari har sai da aka
shiga salla, sannan ta miƙe ta bi masallaci, ana idarwa ta taɓa karatun Alkur'ani,
sannan ta miƙe ta mayar da komai mazauninsa, a cikin kayakinta da ke ɗakin Hajiya
Mama ta sanya riga da wando ta yadi mara nauyi, sannan ta fice a ɗakin ta nufi
kitchen, dan taya su baabaa Larai aiki, kasancewan ita ba mai son jiki bane, sannan
tana son ta iya ko wanne irin girki ko dan ta burge masoyinta.




INDIA

Misalin ƙarfe shida na safe a agogon ƙasar India, yanayin garin yayi kyau da daɗi
kaman hadari-hadari, wata rantsaststiyar haɗaɗɗiyar mota ce tayi parking, a harabar
wani arnen hotel da ke babban birnin Delhi.

Wata matashiyar budurwa ce ta buɗe ƙofan motan ta sauƙo, fiska ba yabo ba fallasa
tana tauna chewing-gum, sanye take da dogon wando wan da ya kama jikinta sosai, ya
ɗameta har kana hango shatin inners nata, dan dai kawai ba mai jiki sosai ba ce, da
sam-sam ba za ta ganu ba, sai dai dogo ne har ƙasa da rigansa, wan da bai gama
rufe ko cibiyanta ba, ga ƴar ficilan jakanta fashion na ratayawa, kan ta cike da
attach (wig), tana taunan chewing-gum nata ta ce, "Guy's see you letter", ta
ƙarisa faɗa tana ɗaga musu hannu har suka ja motansu suka yi gaba.

Sannu a hankali take taku irin na cikakkun wayayyun matasan ƴan duniya, a haka ta
yi cikin hotel ɗin, lifter ta shiga ya kai ta har floor da ɗakin da ta kama yake,
tana shiga ta fara cire gashin dokin da ke kan ta(wig) (Ranƙwal kenan fan's, an ce
da wata wai acici ƙwalloji, kan ta ba gashi kaman an ci giginya da wuƙa🫣).

tana cire wig ɗin ta koma kan kayan jikinta, sai da ta kwaɓe kayanta tass tayi
stirara haihuwan uwarta, sannan ta nufi toilet a haka, ta shige ba addu'a balle
salati, bata wani jima a toilet ɗin ba bayan mintuna ta fito ɗaure da guntun towel,
ba sallah bare salati ta baje a kan gadonta sai bacci.

Wannan matashiya kwance take tana sharar baccinta hankali kwance, ba batun
tashuwa tayi sallah ko wani abu sai gwarti take yi, kukan neman agaji da wayanta ke
yi, shi ya zama silar tashuwanta daga daddaɗan baccin da take kwasa.

Tana buɗe idanuwanta ta jawo wayan ba salati balle salallami, tana kallon numbern
da aka ƙira ta da shi ta ja guntun staki, tare da ɗaukan ƙiran ta sanya a hands-
free, ta na tura baki ta ce, "Hello!"

Muryan wata dattijuwan mata ce ta amsa a ɗaya ɓangaren ta ce, "daughter ya kike?"

"Ina lafiya Mom, please bacci nake yi kuma kunsan ba so nake ina bacci ana tashi na
ba, ki bari zuwa anjima idan na tashi sai ki ƙira ni", budurwan tayi magana cike da
gadara, kaman wacce ki yi wa ƴar cikinta magana ba uwarta ba.

"Sorry lovely daughter, zan ƙira anjiman amma dai yanzu daman zan tambayeki ne
yaushe za ki shigo ne?"

Tana tura baki ta ce, "Mom zan shigo zuwa gobe, i my self am very eager to be at
home, akwai abin da nake son yi, a serious mission Mom."

"No daughter, kiyi haƙuri ki taimaka ki dawo yau kin ji."

Sai da yastine fiska sannan ta ce, "Anyway shikkenan dai Mom zan duba na gani, amma
gaskiya sai na gama baccina, kuma zan dawo ne dan abin da nake so nayi."

"Tun da za ki dawo ai shikkenan daughter, ba komai huta abinki Allah ya miki
albarka ya dawo da ke lafiya, Allah kuma ya baki sa'a."

Ba tare da ta amsawa Mom ɗin ta ba ko kuwa ta mata sallama, ba ko ɗaya ta kashe
wayanta kitt, ta ajiye sa tare da jan tsaki ta ce, "Mutane sai takura, ni gaskiya
ba don ina da mission na da zai kai ni gida ba, da ba zan koma ba dan nasan aikin
masifaffen stohon nan ne, da ya ƙi mutuwa ya addabi rayuwan mutane kaman muna
oldest day's, mtswww to be in a family such like my family is a biggest problem,
family ga girma ga girman maganganun", ta ƙarishe mitanta tare da komar da kan ta
kam pillow, ta ci-gaba daga in da ta dasa aya a baccin, domin bai ishe ta ba jiya
kwanan club suka yi da freind's nata (Allah ya kyauta Allah shirya mu.)






Washegari Ummiy bayan ta yi sallahn asuba ta yi azkar nata da komai, bacci ta koma
sai zuwa ƙarfe tara ta tashi, da mamaki take kallon agogon da ke maƙale a bangon
ɗakin nata, bacci tayi har haka ana neman ƙarfe goma, amma baby bata shigo ta tashe
ta ba kam me kenan, hakan na nufin bata tafi makaranta ba tana can tana bacci,
girgiza kai kawai Ummiy tayi, tare da ƙiran sunan Allah tana mai miƙewa staye,
fitowa tayi ta nufi ɗakin da yake mallakin baby.

Tana isa ta buɗe ƙofan dakin tare da yin sallama, ai kuwa hangota tayi ta baje abin
ta tayi ɗaɗɗaya akan madedecin gadonta, girgiza kai tayi ta ce, "Wai ke kam
lafiyanki ƙalau kuwa da maganan bacci? Kina kwance har ƙarfe tara baki shirya kin
tafi makaranta ba, baby zan haɗa ki da yayanki ya saɓa miki fa."


Downloaded From https://tknovels.com.ng


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment