You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


‫ اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله‬SAW 🖤🤍
GARGAƊI: masu YouTube channels, masu yin Audion littafi, kada wacce ta ɗaura mini
littafi ba da yawu na ba, domin muddin na ci karo da haka to ko wacece/ wanene zan
ɗau mummunan mataki a kai, hukuma za ta rabani da mutum, A KIYAYE.


̶ ̶F̶r̶e̶e page
Billy Ammin Safwan, masoyiya bealkysou Allah Ubangiji ya miki albarka ya nuna mana
bikin nan da rai da lafiya, ƙanwar aunty Ummi kiyi yacce kike so da page ɗin nan.


PAID #500
Shafi
Na
Uku.


Ƙwafa Hajiya Mama tayi ta ce, "Ni ban ma san me ya kawo ki ba takwara, kin zo
dare-dare kaman mara gaskiya za ki addabi rayuwan mutane."

Jidderh na daga kwance ta ce, "Ni bansan ma me yake kawo ni gidan stohuwar nan ba,
bana iya haƙuri sai na zo, idan nazo kuma ki ta mini gori kaman ɗauke mijin zan yi
na tafi da shi, laifi nane ma da nake zuwa ma gidanki ai", ta ƙarishe zancen
muryanta na rawa, kaman mai shirin kuka dan har idanuwanta yayi ƙwalla.

Hajiya Mama haɓa ta kama ganin ikon Allah, ta ce, "Eh samun waje kare da rawa a
bakin ramin kura, mai arahan hawaye, yanzu me abin kuka anan? To Allah ya azurtaki
da Manzon sauƙi takwara, mutum sai son hawaye da kuka kaman wacce mijinta ya mutu,
wai haka za ki dinga yi wa mijin ko nice da kike ganin damana kike min wannan
taɓaran? Sai ka ce daman ni na ce ki zo."

Tura baki tayi ta ce, "Ni dai Hajiya banaso, zan tashi na koma gidanmu,
alhamdulillah muma muna da gida."

Hajiya tana ƙoƙarin miƙewa ta ce, "Na kan ga rasulu idan nayi hali na gari, yanzu
ke takwara ni kike faɗa wa kuna da gida? To naji daman nasan kuna da shi ai ba a
daji kuke kwana ba, amma a haka kika zo mini gida dan ki takura wa mijina, to kin
zo kenan ba in da za ki koma, ke da barin gidan nan ai kuma ba yau ba, abin da ya
sanya ki zuwa dare-dare, shi zai zaunar da ke ki kwana dole, dan ƙafan gwoggonki
Fatu."

Jidderh tura baki ta kuma yi, kaman mai shirin yin kuka ta ce, "Nidai ba ruwan
gwoggona."

Murmushi Hajiya Mama tayi ta ce, "To naji masu gwaggo, mu da bamu da su a raye
Allah bamu haƙuri, kuma na kowa ma zai tafi indai mutuwar yanzu ne, taso muje mu ci
tuwo dan nasan daman kwaɗayi ya kawo ki gidana."

Jidderh ƴar dariya tayi jin wai kwaɗayi ne ya kawo ta, miƙewa tayi daga kwancen da
take tana faɗin, "Eh koma menene dai na zo ne dan na ci tuwo da sakwarata."

"Sai dai sakwara kam, ni rabani da halinki, bansan abin da ya kai Sama'ila saka
miki sunana ba, dan ni ba haka halina yake ba", Hajiya Mama ta faɗa tana ƙoƙarin
ficewa a ɗakin.

Jidderh sauƙowa tayi ta naɗe wa Hajiya Mama sallaya da hijabinta, sannan ta ɗauki
wayanta ta bi bayanta a niste, suka fice a ɗakin, palour suka nufa dai-dai Baba
Alhaji na shigowa shi da wani matashin saurayi.

Stohon da suke cewa Baba Alhaji murmushi ya saki ganin jidderh, ya ce, "Ah!
Amaryata ce da daren nan."

Jidderh na murmusawa ta ce, "Nice dai angona mai ran ƙarfe, ka ƙi zuwa hatta ɗaukan
amaryan shiyasa na taho abina da naga dare tayi."

Baba Alhaji ya ce, "To Masha Allah! Amaryata ta kyauta, Allah ya miki albarka."

Amsawa da "Ameen", jidderh tayi, sannan ta ce, "Yaya Sabeer an wuni lafiya?"

Matashi mai suna ya Sabeer murmushi yayi ya ce, "Lafiya alhamdulillah stohuwa
amaryan stoho."

Jidderh kallon Hajiya Mama tayi, tare da turo baki ta ce, "Allah kuwa sakwara ki ce
musu su daina ce mini stohuwa, ƴar gangariyan budurwa da ni haka kawai a rage mini
farashi."

Hajiya Mama haɗe fiska tayi tare da kallon Ya Sabeer ta ce, "A daina faɗa wa
takwarata stohuwa, ita ba stohuwa ba kuna ganin yarinya ƴar jinjira da ita, kuna
stofar da ita."

Ya Sabeer dariya yayi tare da riƙe bakinsa, da kunnensa alaman yaji ya daina, ita
kuma jidderh murmushi tayi ta ce, "Yauwa Hajiya Mama ta."

Baba Alhaji ne ya ce, "To azo aci tuwo kubar shirmen nan, dan Hauwa'u rigimanta
ya mata yawa."

Duk akan centre carpet suka zauna, Jidderh ce tayi serving nasu, ta saka wa baba
alhaji tuwon biski da miyar zogale da ya ji kifi kasancewan yana da ciwon sugar,
Hajiya Mama kuma ta saka mata tuwon shinkafa da miyar zogale da kifin ita ma, ta
saka wa Ya Sabeer tuwon shinkafa da miyar kuɓewan da yaji man shanu ga namomi,
sannan ta saka wa kanta tuwon doya(sakwara) da miyar egusi shi ma ya ji bushashshen
nama.

Abincin suke ci wajan shiru ba ka jin ƙaran komai, sai na taunan abincin nasu,
jidderh bata wani ci sosai ba ta cire hanunta, ɗiban ruwan zafi tayi ta haɗa black
tea ta sha, gefe ta matsa tana duba wayanta hankali kwance ciki ya ɗauka.

Hajiya Mama kallon jidderh tayi tare da girgiza kai, ta ce, "Ke dai takwara Allah
ya yaye miki rashin cin abincin nan, watarana har gwanda mai sunan Alhaji da ke
kam."

Murmushi kawai jidderh tayi ba ta ce komai ba.

Ya Sabeer ya ce, "Ai Hajiya Mama dai-dai kenan, kin ga an haɗa su perfect match,
amma dai nikam ina namiji ban ci ba wa zai ci? Ni fa na nemo abincin, ai gwanda ace
mace bata ci sosai akan a ce namiji ne baya ci sosai, don ita mace hakan ma ado ne
gare ta."

"Kubar damar mini amarya da surutu, tun da ta ƙoshi to a ƙyale ta", faɗin baba
alhaji.

Jidderh murmushi tayi tare da cewa, "Yauwa mijin ka gama ci kai ma sai muyi fira",
ta faɗa tana komawa kan kujera ta zauna.

Alhaji baba ne ya mayar da dubansa kan Ya Sabeer ya ce, "Nikam yaushe ƙanwarka za
ta dawo ne? Ko ita ma ta fara ɗaukan huɗuban wancan mara jin maganan ne eyye?"

Ya Sabeer ya ce, "Baba Alhaji wannan yarinya kam me mutum ma zai ce ne, su Mom sun
jima da sakalta ta, kawai ka ƙira Dad ka tambayesa, dan nikam ban san ko tana hanya
ko bata hanya ba, ba ma magana take mini ba tana jin yanzu ta girma ta fistare."

Ƙwafa Hajiya Mama tayi kawai, amma ba ta ce komai ba, shi ma baba Alhaji bai kuma
cewa komai ba, har suka kammala cin abincin, baba larai ta zo ta gyara wajan tass.

Alhaji baba sai da ya gyara zamansa har da kishingiɗa, sannan ya ce, "Amaryata
ɗauko mini ƴar salulata (waya) a ɗaki, ki zo ki mini ƙira dan naga iyayennaku sai
an saɓa musu za su yi abin da ya kamata, su kuma kula da tarbiyyanku, idan ba ma
lalacewan zamani ba duk cikin yaran nan akwai mai yara irin yacce na haife su ne,
ni ban kasa tarbiyyansu su kusan goma sha ba, amma ni za su wasta mini kasa a ido
su kasa yi wa jikokina tarbiya, daga mai uku sai mai huɗu, ba mai yaran da suka
wuce biyar, sun ɗau rayuwan yahudawa sun ɗaura wa kan su, basu san yahudawan la'ana
ce ke bin su ba, da akwai wan da ya kai yahudu auran mata da yawa da haihuwa ne,
addu'an Annabi ne ya sa yanzu suke zama da mata ɗaya kuma yara biyu mace da namiji,
ai Annabi Dawuda yahudu ne kuma matansa sun kai ɗari, Annabi sulaiman ma yahudu ne
matansa sun bai wa ɗari baya, yanzu Allah ya rahamce mu muke auren mata har huɗu
sannan mu hayayyafa, yacce Annabi SAW zai yi alfahari da mu ranan ƙiyama, kuma sai
ga shi mun ɗauko al'adan yahudu mun iza a kawunanmu, to zan kuwa saɓawa iyayenku."

Jidderh tashuwa tayi ta tafi ɗauko wayan da sauri, dan kowa yasan Baba Alhaji bai
da mastala amma idan aka taɓo sa, ransa ya ɓaci to fa jam'i yake haɗawa, stoho mai
ran ƙarfe.

Ya Sabeer ma tuni ya miƙe ya musu sallama, yayi gaba abinsa kamun Baba Alhaji ya
haɗa da shi, a basa kasonsa, gidansu ya wuce a ƙafa kasancewan gidansu yafi kusa da
na su Baba Alhaji.

Jidderh ta ɗauko waya tana ƙoƙarin zama, sai ƙira ya shigo wayanta ita ɗin ma.




Baby ce zaune a dinning area ita da Ummiy suna cin tuwo, kuma tuwon da Ummiy ta fi
so, tuwon shinkafa da miyar kuka da man shanu.

Da Ummiy ta gaji da surutun baby, sai ta ƙwalawa Talatu mai aiki ƙira, zuwa tayi
cikin ladabi ta ɗan durƙusa ta ce, "Hajiya gani nan."

Ummiy na murmushi ta ce, "Yauwa Talatu yarinyar nan ta dameni, tun ɗazu yarinya
taƙi barina na ci tuwo, cikin kwanciyan hankali sai fitinata take, wai sam ita ce
tayi miyan ba ke ba, dan taji na ce yayi daɗi, gaskiya ne ita tayi ko kuwa fitinane
irin na baby?"

Talatu murmusawa tayi ta ce, "Hajiya ai wallahi dai ita ce tayi, dan taƙi ƙyaleni
na saka ko hannu na taya ta, ita tayi har da tuwon ma."

Ummiy na washe baki cikin jin daɗi ta ce, "Inyee ki ce mini babyn Ummiy ta girma
saura aure, amma wannan iya girkin dai kyawunsa na aurar da ita a ƙauye, dan ta
wuce auren birni da wannan girkin."

Talatu dariya ta fara yi, da yake daman sun saba raha da Ummiy, ba ruwan Ummiy da
kana mata aiki ko wani abu, bata wulaƙanta ɗan Adam sam-sam, wasa da raha duk idan
ta kama tana yi da masu aikinta, kuma ita ɗin ce ta ce su dinga shiga kitchen da
baby dan ta koya aiki, tun da ita asibiti na cinye mata lokaci, kuma kada ta ɗau
alhaƙin yarinya irin tarbiyan yaran masu kuɗi a yau, yarinya ta girma ta kai aure
amma ba abin da ta iya, komai sai mai aiki ta mata, idan tayi aure to ita kawai
kwanciya da miji ta sani, masu kuɗi ku gyara tarbiyan yaranku saboda halin rayuwa
shawara ce.
Talatu tana dariya ta ce, "Haba dai Hajiya wannan ai matar drivern jirgi ce, ba in
da aure ba ya kai mutum, amma Insha Allah ko a ƙauye Saudiyya ba za ta zauna ba."

Baby murmushi tayi ta ce, "Yauwa aunty Talatu na, faɗa wa Ummiy ko a Makka ne to a
babban birnin zan zauna in Allah ya yarda, shiyasa nake yin ki auntyna."

Ummiy ta buɗe baki za ta yi magana sai wayan baby ya fara ihun neman agaji, Ummiy
da yake wayan na kusa da ita, ɗauka tayi ta miƙawa baby tana faɗin, "Duba mana ko
ƙiran kuɗaɗe ne za su shigo Mu fara shiri, amaryan ɗan ƙauye."

Baby amsan wayan tayi tana tura baki wai bata so, ganin saƙo ne ba ƙira ba buɗewa
tayi, ai ba shiri ta waro ido akan wayan tana gani da kyau, ai miƙewa tayi ta ɗan
yi tsalle har da juyi tana faɗin, "Wayyo Allah na! Ina son ki yaya jidderh, Allah
ya bar mini ke, Allah ya mallaka miki Yaya ke kaɗai ba kishiya, Ummiy ga shi ki
gani yaya jidderh ta saka mini card."

Karɓan wayan Ummiy tayi ta duba, ganin yawan katin sai ta murmusa ta ce, "Allah ya
mata albarka ya ƙara buɗi, Allah bata miji nagari", ta faɗs tare da miƙa wa baby
wayanta.

Baby ya amsa wayan tana cewa, "Ai Insha Allah Yaya ne mijin, shi ne nagari kuma na
alkairi, kai idan yaya ya kuskura zai yi wa yaya jidderh kishiya ko yaudara, to ni
kaɗai na ishe sa tuwo da miya dan ba zan bari ba ma hakan ta faru."

Ummiy haɗe fiska tayi ta ce, "Sannu addarsa, Allah zan saɓa miki akan manyancenki
baby, shi shameekh ɗin sa'anki ne, to ki yarda ya ji abin da kike cewa, addu'an
alkairi kawai shi za ki yi ba surutu ba, kuma maza ki ƙirata yanzu ki gode mata,
bana son surutunkin nan mara kai."

Cunna baki baby tayi wai dan Ummiy ta mata faɗa, Ummiy kuwa ko kallonta ma bata yi
ba ta ci-gaba da abin da take yi, sai da Talatu ta bai wa Ummiy haƙuri Allah ya
huci zuciyanta, sannan ta bar dinning ɗin, baby kuma layin yaya jidderh ta laluɓo
tayi dialing kaman yan da Ummiy ta faɗa.






Wani haɗaɗɗen club ne a ƙasar Dubai, club ɗin da sai wane da wane ke zuwa, don
classic club ne, Shameekh ne zaune a wani table da wani matashin saurayi wan da za
su yi sa'an juna a shekaru, matashin kyakkyawa ne Masha Allah, amma fa bai kama
ƙafan Shameekh ba, duba da yacce suka mai da hankalinsu akan juna, to kasan tabbas
abu mai muhimmanci suke tattaunawa a kai, wannan matashin ne ya ce, "Man yanzu to
ya za'a ɓullowa abun?"

Shameekh ya buɗe baki zai yi magana sai haɗaɗɗiyan stadaddiyar wayansa, tayi flash
ta kawo haske da vibrating alaman ƙira ne ya shigo, fasa maganan yayi tare da saka
wayan a silent, yana gani har ƙiran ya kaste.

Wannan matashin ƙwafa yayi ya ce, "Gaskiya idan aka ce maka kana kyautawa to ƙarya
aka maka Man, kai fa ka laƙantu da wulaƙanci da iyayi kaman wani Garage gare ka ba
dick ba, haba mata masu Garage su ya kamata su yi wannan iyayin, ba gardi irinka
mai Banana ba, tun ɗazu wannan baiwar Allah sai ƙiranka take yi, amma ka ƙi ɗauka,
wai meyasa ne kake mata haka?"

Shameekh haɗe fiska yayi tare da aikawa matashin da wani kallo ya ce, "Manseer
please let's talk about what brought us here, kabar maganan wani dick wani Garage
ne ko me, kasan ba son maganan banza nake ba, dan ba shi bane a gabana."
Manseer dariya yayi ya ce, "A faɗawa kaji da agwagi mu zabbi firewa muke yi, magana
kake nema wai an ce da gauro ya iyali, kai ɗin ne baka son maganan banza? Hhhhh ko
da yake daman ai nasan ba shi ne a gabanka ba cucumbern jidderh ne a gabanka, so
please idan za ka bar wulaƙanta ƴar mutane ka bari idan ba haka ba za ka sha
mamaki."

Wani kallo Shameekh ya yiwa Manseer tare da haɗe fiska ya ce, "Yanzu idan da yara a
nan ba sai ka ja su renamu ba, ni na faɗa maka ina da issue da mace balle wani ka
ɗosana mini wani shirme."

Murmushi Manseer yayi ya ce, "Eh lallai a yanzu kam ba ka issue da mace, amma ka
guji haɗuwanka da ita, Allah ya sa ta dinga ƙarar maka da ruwan jiki za ka dawo
hanya."

"Abar wannan magana", faɗin Shameekh rai a haɗe.

Manseer ya ce, "Ai dole ka ce abar maganan tun da kasan kwanan zancen, Man nifa
idan ba ka yi ka bani waje, ka masta na shige layin masu nema ayi da ni, wannan
haɗaɗɗiyar wa zai so ta wuce sa, irin su idan ka ajiye su a gida ko ba komai ka
dinga farinciki idan ka kallesu, mace har mace ga....", wani irin kallon da
Shameekh ya yiwa Manseer, shi ya sanya shi haɗiye sauran maganan da zai yi yana
dariya, dan Shameekh ɗin ya san dole maganan banza zai faɗa.

Tsaki Shameekh ya ja rai a ɓace ya miƙe ya kama hanyan ficewa a club ɗin, dan daman
a takure yake da kallon da ƴammatan club ɗin ke masa.

Yana ficewa waje yayi wajan motansa, fiskan nan a haɗe rai a ɓace ya buɗe motan ya
shiga, yana ƙoƙarin tayar da motan sai Manseer ya fito daga club ɗin shi ma dan
dama bayansa ya biyo tun fitowansu, kallonsa ya sashi saurin tayar da motan yayi
gaba, yana driving ya ja wayansa ya duba lokaci, ganin mid-night ne yanzu a wajensu
suna fin agogon Nigeria da 4 to 6 hours, wanda hakan ke nufin yanzu bai wuce 9 zuwa
10 na dare ba.

Yana isowa gidan nasa yayi horn, mai gadi ne ya taso ya leƙa duk da dare ne amma
ya gane mai gidannasa ne, tun da daman ya sani yana iya kai ire-iren wannan lokacin
a waje, buɗe masa gate yayi ya shigo da motan, parking yayi ya fito mai gadi ya
masa sannu da dawowa, hannu kawai Shameekh ya ɗaga masa alaman ya amsa, ya shige
cikin gidansa.

Bai staya yin komai ba a palourn ya wuce ɗakinsa, yana shiga ya cire kayan jikinsa
ya rage daga shi sai white short nasa, sanin idan ya shiga toilet ɗin zai iya
jimawa, shiyasa ya fasa shigan ya koma ya zauna a kujeran da ke cikin ɗakin nasa,
wayansa ya ɗauka ya kalli misscall's da aka masa, scrolling na number's ɗin yayi,
da ya zo dai-dai layinta sai ya tsaya kaman ya ƙira kaman kar ya ƙira, sai ga wani
ƙiran ya shigo wayansa kuma new number ba suna, kasancewan ya gane numbern sai ya
ɗauka dan misscall na numbern da yawa, yana ɗauka yayi shiru bai ce komai ba, a
ɗaya ɓangaren kuma cewa aka yi, "Hello! Ya Shameekh ya kake?"

A taƙaice ya ce, "Lafiya, ƙira da daren nan lafiya? Wacece?"

Wani numfashi aka sauƙe a ɗayan bangaren wan da zai tabbatar maka da na haushi ne,
amma ba'a ce komai ba.

Shameekh kuwa jin shiru ba a ce masa komai ba, sai kawai ya kashe wayansa yana taɓe
baki, amma fa ya gane wacce ta ƙira ɗin dan true caller ya nuna sunanta ɓaro-ɓaro,
kuma daman ya gane layin da take addabansa da shi, damuwane baya so shiyasa yayi
hakan kawai, guntun staki ya ja a fili ya ce, "Ke kika sani."
Shameekh bai gama rufe baki ba wani ƙiran ya kuma shigowa, kuma da wannan numbern
ne na ɗazu, yanzu kam ransa a ɓace yayi picking, dan ba abin da Shameekh ya stana
kaman yawan ƙira kuma da number mara suna ko ɓoyayyen layi, a harzuƙe ya kara wayan
a kunnensa tare da cewa..





Jidderh ganin ƙira ya shigo wayanta fasa miƙawa Baba Alhaji wayansa tayi, cikin
zaƙuwa ta duba dan duk a tunaninta shi ne ya ƙirata, amma sai ganin layin baby tayi
wan da tayi saving da "Lil Sis", ɗauka tayi tana murmushi ta ce, "Assalamu alaikum
babyn aunty jidderh ya aka yi?"

Baby a ɗaya ɓangaren cewa tayi, "Na'am yaya jidderhta, lafiya lau naga kati nagode
sosai, Allah ya ƙara buɗi, Allah ya bar mana ke yayarmu."

San-sanyar murmushi jidderh tayi ta ce, "Ameen ya Rabbi babynmu, ki gaishe da
Ummiy ko sai da safe."

"To Yaya jidderh Insha Allah Ummiy ta ji gaisuwa", baby ta faɗa suka yi sallama
sannan jidderh ta kashe wayanta.


Jidderh ta ce, "Mijin ga wayan naka wa za'a ƙira maka?"

"Yauwa Hauwa'u dubo mini layin babanku Sulaiman."

Jidderh amsawa tayi tare da shiga numbonin wayan, ta laluɓo layin big Dad ta aika
da ƙira, yana shiga ringing ɗaya yayi aka ɗauka, ana ɗaukan ƙiran ta miƙa wa baba
alhaji wayan ta ce, "Ga shi nan an ɗauka stoho."

Amsan wayan yayi tare da karawa a kunnensa, ya amsa sallaman da big Dad ke masa a
ɗaya ɓangaren, gaisawa suka yi big Dad ya ce, "Baba ya jiki ya kuma su hajiya?"

"Duk muna lafiya sulaimanu, na ce yaushe Safiya za ta dawo?" Faɗin Baba Alhaji
fiska a haɗe.

Big Dad a ɓangarensa sai da ya ƙai-ƙaya kan sa sannan ya ce, "Ammmm baba tana
dawowa Insha Allahu."

Alhaji da faɗa ya ce, "Kai Sulaimanu ungo naka, na ce ungo naka ɗan ƙaniya, daman
na ce maka ba ta dawowa ne? Ka fa shiga hankalinka Sulaimanu, ita Safiya fa
yarinya macece kar ka ɗaure mata baya ka lalata mini jika, dan bazan yafe maka ba
muddin tarbiyan jikata ya lalace, maza-maza indai na isa da kai ka ce ta dawo goben
nan, ba zai yiwu ƴa mace da ita ta zauna a ƙasar marassa ishashshen tarbiya ba, tun
da rai na ba za ku ƙonani ba, yarana basu yi wannan abun ba to jikoki na baku isa
ku ce za ku sanya su a wata bidi'ar rayuwan ba."

Hajiya Mama rai a ɓace ta ce, "Alhaji ka bani wayan."

Baba Alhaji miƙa mata wayan yayi, big Dad na ƙoƙarin gaisheta ta ce, "Sulaimanu ka
riƙe gaisuwanka, ina fatan ka ji abin da babanku ya ce ko? To sayfiya ta dawo goben
nan kuma duka zan haɗu da ku ne mutanen banza mutanen wofi kawai."

Haƙuri big Dad yake bayarwa amma ba wan da ya saurare sa, dan baba alhaji ma karɓan
wayansa yayi ya kashe.

Jidderh cikin girmamawa ta ce, "Ayi haƙuri mijin, a dinga mana addu'a Allah ya
shiryamu, ke ma kinji Hajiya sakwaralle ta, Insha Allah ba abin da zai samu
tarbiyanmu duka."

Baba Alhaji murmushi yayi ya ce, "Allah ya sa, Allah kuma ya kare ku a duk in da
kuke, Allah ya muki albarka Hauwa'u."

Jidderh ta ce, "Ameen mijin, saura ke ma sakwaralle ki saka mana albarka indai ba
kishi kike ba", ta faɗa tana yiwa Hajiya Mama dariya.

Dan-ƙwalo Hajiya Mama ta yi wa jidderh ta ce, "Ungo naki ke da ƴan uwan naki,
Allah ya shiryaku."

Jidderh na dariya ta amsa da Ameen, ta miƙe ta nufi ɗakin Hajiya Mama tana faɗin,
"To abar mini kallon kishi sakwaralle dan yau da ni ke da miji", ta faɗa dai-dai
tana shigewa ɗakin.

Hajiya Mama girgiza kai kawai tayi ta ce, "Wannan takwara tawa sai addu'an
shiriya."

Baba Alhaji murmushi yayi ya ce, "Allah ya shirya mana su duka, amma da ace duka
yaran nan irin halin Hauwa'u gare su, ai da hankalin kowa a kwance, wannan yarinya
dai Allah ya mata albarka, Allah ya nuna mana ƙarshen watan nan lafiya, kowa ya
halarta nasan hukuncin da zan zantar, dan dole na yiwa abin tufkar hanci."

Hajiya Mama ta ce, "Ameen, Allah ya kai mu da rai da lafiya ya kuma tabbatar da
alkairi."




***
MASU DARAJA HABIBTIEES KADA KU MANTA DAI WANNAN TAFIYA TA DABAN CE, MASU SHARHI
KUNA GIGITANI ALLAH BAR ƘAMNA🤝💜, ANA FARA PAID PAGE'S INSHA ALLAH ZAN ƘARA YAWAN
PAGE KU DAI A CI-GABA DA SHARHI.


# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚, SHAAMEEKH ,
B̶̶O̶O̶K1

Officially


𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


‫ اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله‬SAW 🖤🤍


GARGAƊI: masu YouTube channels, masu yin Audion littafi, kada wacce ta ɗaura mini
littafi ba da yawu na ba, domin muddin na ci karo da haka to ko wacece/ wanene zan
ɗau mummunan mataki a kai, hukuma za ta rabani da mutum, A KIYAYE.


PAID #500
Shafi
Na
Huɗu.



Shaameekh a harzuƙe ya ɗau ƙiran, wanda da alama har yanzu ɓacin ran maganan
da Manseer ya masa bai wartsake ba, "Wai ke kam wace kalan mayya ce? Sau nawa ina
gargaɗanki da ƙira na, na hana ki ƙira na amma sam bakya ji, sannan kina ƙira na da
wani number daban, wai ke baki da aji ne? Ko baki iya kama mutuncinki irin na ƴa
mace bane?", ya ƙarishe faɗa yana mai jin, kaman ya shaƙeta ya huta.

A ɗaya ɓangaren kuwa mai ƙiran nasa fashewa tayi da kuka, cikin kuka ta tausasa
muryanta ta ce, " Haba Ya Shaameekh dan kawai ina sonka, ai kai ma kasan ba laifina
bane, dan ba nice na ɗaurawa kai na ba, kuma mai son ka ai yafi mai ƙin ka, idan
kana wulaƙanta ni kuma kai ma kada ka manta za ka haifa, idan aka yiwa taka ƴar ai
ba daɗi za ka ji ba."

A hasale Shaameekh ya ce, "Nace miki bana son ki, ki riƙe kan ki kada ki bari na
ɗau mataki a kan ki, ni ba sa'anki bane da za ki dinga faɗa mini ko wani maganan da
ya fito a bakinki."

"Wallahi kana so na Ya Shaameekh, kuma sai ka aureni, wannan karon zan koma gida,
kuma za a yi duk abinda za a yi, wallahi ina a shirye tsaf a kan ka ba wan da ba
zan iya ja da shi ba, har Mom and Dad, kuma idan ma akan wancan figaggiyar kake
mini wulaƙanci, to za ka sa na kasheta ne a banza, idan ya so daga baya nima a
kashe ni kowa ma ya rasa, dan a kanka ba wan da ba zan iya yiwa illa ba, ko waye
kaji na faɗa", ta faɗa a ɗaya ɓangaren a yanayin kaman wacce ke cacar baki da
abokiyar faɗanta.

Wani killer smile Shaameekh yayi, domin shi baya son hayaniya, amma duk yacce ya
kai da rashin son magana, wannan yarinyar sai ta ingiza sa yayi, ga shi ko yana
faɗan ma ba za ka ce faɗa bane, kawai dai maganan nasa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment