You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kowa ya ga ji da ita
ba. Hatta Mama sai da yi mini barka da zuwa cikin sakakkiyar fuska. Inna kuwa sai
kiran kananun y'ay'anta take yi tana fa'din "ku je ku yiwa Adda Yabi oyoyo."
Na fito da alawa na dinga bawa kowa a hannunsa. Tun fil'azal kyautar alawar da nake
yi musu ya sanya suka fi sakewa da ni. Dakin mama na fara shiga na gaisheta na
ajiye mata omonta zare guda. Sannan na shiga na Inna na bata nata.
Sai kuma na dawo dakinmu na baje.
Na fa'da kan gado na fashe da kuka a hankali.
Ta zauna jikinta na rawa ta ce "Duk yadda jikinkinki ya nuna kina zaune k'alau ashe
ba hakan ba ne. Daga zuwanki zaki daga mini hankali, ki shafe murnar da na ke ciki
ta ganin ki, cikin yanayi me kyau?"
Na share idon na ce "Ai ke ce "Baki taba zuwa mini ba. Kowa a gidan nan ya je amma
ban da ke. Ko har yau fishi ki
ke yi da ni Gwaggo?"
Ta ri'ke hannuna ta ce "Ba komai a zuciyata game da ke sai alheri mai yawa Yabi. To
me zan je na yi miki ne? Babanku ya je. Mama ta je, Inna ta je, yayarki tana zuwa.
To su duk kin raina k'ok'arinsu?"
Na juyar da fuska na ce "Ban raina ba Gwaggo. Amma ina so ki zo".
Ta mike ta ce "Zan zo. Amma sai kin haihu."
Na rufe fuskata domin kunya na ji irin sosai din nan.

✍️
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered,
Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan
farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon
yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.


*Oriflame products*
*Daga make up artist din Guduyo*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin
register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*

57&58.
Yini na yi cikin farin ciki. Domin Baban Marina tunda ya dawo cin abinci da azahar,
bai fita ba. Zama ya yi muke hira ni da shi domin ba k'aramin da'din ganina ya yi
ba.
Sai da aka fara kiran sallar la'asar sannan muka yi sallama ya fice.
Sai dare kuwa muka tafi kamar yadda ya yi mini al'kawari. Albarka na sha ta daga
wajen mahaifana har da Dada ma.
A k'ofar gida ina shirin d'ale wa mashin din, sai ga Baban Tsakiya. Na yi kamar ban
gan shi ba, na dauke kai. Tijjani ya mini inkiyar na gaishe shi amma na waske. Sai
shine da kansa ya ce "Tijjani wannan ba Yabi ba ce?".
Kafin ya ba shi amsa Na rusuna ka'dan na ce "Baban Tsakiya ina yini".
Ya ce "Ai har yanzu ba zaki daina kama suna da inkiya ba?" Ban ce komai ba daga
hakan. Na haye mashin d'in ko kunyarsa ban ji ba. Duk da yana kallona haka na dafa
Tijjani da zan hau din, tunda har yau ba zai shafa mini lafiya ba.
Ya kad'a kai ya ce "Tijjani Allah ya k'ara maka hakuri da juriya".
Ya kasa amsa masa, amma gaba'daya na ga ya yi wani iri.
Kafin ya ja mashin din sai ga J ya fito da alamu tare suke da mahaifin nasa.
Ya mika wa Tijjani hannu suka gaisa.
Hasken solar da gwamnati ta kafa akan layika ta haske fuskokinmu tunda muna da ita
a k'ofar gidanmu.
Karon farko da na kalle shi ban ji wani abu na so ko na burge wa ya taso mini ba.
Domin ko ranar da muka je gidansa yin barka sai da tsumin sonsa ya taso mini.
Na bu'de baki na ce Yaya J ina yini, ya Baby?"
Da wani irin yanayi ya ce "Lafiya k'alau Yabi. Ya kike, ya ruwa?"
Na amsa da Alhamdulillah".
Daga haka Tijjani ya ja mashin dinsa muka wuce.
Lafiya k'alau muka isa gidan, muka gama uzzirinmu muka kwanta. Tsawon lokaci ina
jiran na ji hannunsa a jikina shiru. Na dinga mutsu mutsu, amma bai motsa ba. Da
k'yar na samu barci ya sure ni. Da asuba ma hakan ya yi, ga shi ya riga ya sabar
mini da al'amarin dare da asuba basa wuce mu sai idan fashin sallah nake yi. Shi ma
sai mun yi abubuwan da zamu samu nutsuwa.
Na rasa yadda zan yi, domin kunya ta hana na fara kai hannuna gare shi.
Na daure dai nima na share. Muka koma barci. Ni na fara tashi, na gyara gidan, na
duba na ga akwai taliyar hausa. Nasan kuma yana sonta sosai. Sai kawai na d'ora
jolof d'in ta.
Ina shirin gamawa na ga ya fito ya yi band'aki. Can kuma ya fito da brush dinsa ya
zauna daga gefe ya yi, sannan ya mayar ya ajiye.
Maimakon ya shigo kicin ya taya ni mu k'arasa kamar yadda ya saba sai kawai na ga
ya yi falo.
Na fara jin wani iri a dalilin sauyinsa. Na dinga tunanin me ya faru. Amma na kasa
gano ko na yi masa wani abu.
Na gama, na tafasa shayi. Na ha'da komai na kai falon.
Muka fara karyawa amma babu doguwar hira yadda ya saba mini.
Muna zaune, jigum jigum yaro ya yi sallamah daga ba'kin k'ofa ya ce "Wai ana
sallama da Tijjani".
Na zabura na ce "Kai shigo". Ya shigo na kare masa kallo, gaba'daya ba zai wuce
shekaru takwas ba.
Na zare masa ido a dalilin na ji haushin gatsa sunan da ya yi. Na ce "Ba zaka ce
ana sallama da maigidan ba sai ka wani gatsa sunasa tamkar sa'an ka. Zaka iya
fa'din sunan Babanku gatsal?"
Yaron ya yi shiru yana kallona da alamu ma tsorata ya yi kada na rufe shi da duka.
Sai lokacin Bulkachuwa ya ce "Kai je ka ce "Ina zuwa".
Ya mik'e ya bar ni.
Tunda ya fita sai yamma ya dawo. Bai ce mini ga inda ya je ba, nima ban tambaya ba.
Na gabatar masa da ruwa da abinci na yi tafiyata wajen k'unshina. Domin na fara jin
haushin daddaurewar da yake yi mini haka siddan.
Haka da daddare ma ya sake matse wa bai ta'ba ni ba.
Kwanaki uku ke nan, muna haka, na fara k'osawa domin gaskiya ya riga ya yi mini
sabo a harkar, tun ina turjiya, ina raki har na zama yar hannu da al'amarin nasa.
Sannan na fahimci nima irin halittarsa ce da ni. Ina son harkar, ina jin da'din ta.
Ban sani ba ko ya fahimci hakan ne shi yasa zai fara yi mini gayya.
Sai na yun'kura zan tambaye shi dalilin sauyinsa sai na yi maza na fasa. Ina
jaddada wa zuciyata na ja ajina. Shi da yake namiji ma ya yi jarumtar runtsi idonsa
daga gare ni, sai ni mace ce zan k'osa?.
Dan haka na yi hakuri, na zuba masa ido, amma gaba'daya bana cikin nutsuwa.
Mussaman idan ya shek'a kwalliya ya baza turare sai na ji tamkar na yi tsalle na
mak'ale shi.
Sai ya fita nake samun damar na yi kukana. Ina ayyana wai ni Tijjani yake yiwa
wannan wula'kancin haka siddan dan ya fahimci na fara sonsa.
Na fara zargin akwai abin da yake yi a waje da ya sanya yake iya kawar da kansa a
kaina.
Gaba'daya na rasa sukuni. Na yi wani iri.
Ranar da muka yi kwana hudu a cikin wannan halin. Gaba'daya ya juye mini, tamkar ba
shine mai rawar jiki da tsoron ganin fishina ba. Tamkar ba shine mai kulafacina
kamar me ba.
Ranar da wuri ya shigo. Na yi wanka na sanya riga da wando silky. Wando iya guiwa
rigar ma iya tsayinta kenan wando kawai ta rufe.
Na taje gashina da yake a tsefe na mulke shi da man gashi na kwakwa da asalain man
alaiyadi. Na dauko turarena na mai maiko na oudi na murtsike hannayena da jikina
har ma da gashin. Na sake dauko turaren active woman da Tijjani ya canja mini na bi
jikina na feshe. Na saka hula marar nauyi kalar kayan barcin nawa.
Na fita na same shi yana kallon labaran NTA Bauchi.
Na zauna ya dago ya kalle ni. Domin na tabbatar kamshina ya kai masa caffa mai
yawa.
Na sassauta na ce "Wai mun b'ata ne?"
Cikin nutsuwa ya ce "Da yaushe?"
Na yi sakare ina kallonsa. Na numfasa na ce"Ai tambayar ka na yi."
Ya girgiza kai ya ce "To ke mun b'ata ne?"
Na rasa me zan ce masa ma. Na nisa na ce "Nasan bamu b'ata ba. Amma na ga ka sauya
ne".
Ya daure fuska ya ce "Tun yaushe na canja d'in?"
Na ce "Tun kwanaki hudu, tun ranar da ka kai ni gida".
Ya yi shiru tsawon lokaci kafin ya bu'de baki ya ce "Kuma sai yau kike bu'katar
sanin dalilin sauyin nawa saboda baki d'auke ni a bakin komai ba?"
Ga mamakina sai na shiga rud'u na ce "To ai kai ne zaka fa'da mini."
Ya girgiza kai ya ce "Babu damuwa ki cigaba da zaman jiran na fa'da miki".
Idona ya ciko da k'walla. Na zuba masa ido sosai na nuna kaina da yatsana na ce "Ni
kake wula'kantawa saboda kawai ka shiga ka fita kasa na saba da kai ko?.
Ai shike nan na gode".
Daga hakan na kifa kaina a hannun kujerar na fashe da kuka mai tsananin gaske.
Ya taso da azama ya zauna kusa da ni. Ya ru'ko ni na fizge tare da ce wa "Ba
ruwanka da ni, komai kake yi na barwa Allah. Ka cigaba da yi mini wula'kanci komai
lokaci ne ai, watarana ba zaka yi ba".
Ya sake tarairayo ni jikinsa yana kamo weak points dina. Jikina ya fara tsuma. Amma
na sake k'wace wa na mike, cikin muryar kuka na ce "Bana so Tijjani, ka bari na
fa'da maka".
Na fice na yi d'akina ina kuka sosai.
Sai da ya yi wanka sannan ya shigo d'akin har lokacin kuma ina dukunkune ina kuka
sosai.
Sai da ya yi shafa'i da wutiri sannan ya tarar da ni a gadon.
Bai kwanta ba. Ya zauna ya kaurara murya ya ce "Asiya tashi mu yi magana."
Na share shi, na k'i na nuna ma na ji shi.
Ya saka hannunsa biyu ya d'aga ni ya zaunar da ni.
Na sake yun'kurin koma wa na kwanta dan na nuna masa ba ni da lokacinsa, sai kawai
na ji ya bu'de murya sosai ya ce "Wallahi idan kika kwanta idan ranki sun kai dubu
ki tabbatar sai na bisu d'aya bayan d'aya na b'ata su."
Jin ya rantse sai na zauna din. Amma na tattaro dukkan fishi na yab'a a fuskata.
Ya jima yana kallon yadda nake tunbatsa.
Shima ya d'aure tasa fuskar ya ce "Ki saurare ni da kunnen basira Asiya Toro".
Jin ya fadi wannan sunan na sake hassala ainun.
Ya furzar da iskar baki ya ce "Ranar da muka je gida kin wula'kanta ni, kin tozarta
ni!
Watannin baya na fa'da miki, ba zai yiwu a gabana ki wula'kanta iyayenmu ba. Idan
kin ture girmansu na k'annen mahaifinki ne, to ki sani baki isa ki ture nasabarsu
da ni ba. Ina kuma da hak'kin ki mutunta iyayena. Dole ne, wajibi ne Asiya ki
mutunta mini dangin uwata matu'kar kina son mu zauna lafiya. Ba zai yiwu ina
aurenki kuma in zuba miki ido ki dinga yin rashin mutunci ba. Bilhiillazi wannan ne
karon k'arshe da zaki ga wani cikin iyayenmu ki k'i gaishesu, ko ki yi musu
gaisuwar je ka na yi ka".
Na fara kuka ina ce wa "To ina ruwanka ne kam. Kai baka ga irin k'iyayyar da suke
yi mini ba? Saboda baka kishina, saboda kai sun yarda gyatumarka yar'uwarsu ce
shiyasa kake ganin bekena. Duk abubuwan da suke yiwa ubanmu baku da kaico. Ai ka
sani ba sai na fa'da ba, ko auren nan nawa sun yi sanadinsa ne dan kawai suna ganin
bazan cigaba ba.
Amma da sun tabbatar zan samu nutsuwa a cikinsa a sai sun rugurguza shi. Yanzu ma
kuwa nasan akwai lokacin da zai zo da zasu rabamu tunda zuciyarsu mai k'yashi ce."
Ya buge mini baki ya ce "Kada ki kuskura ki fa'di maganar banza a kansu a gabana.
Dole fa ki mutunta su a matsayin surakanki tunda ke kin yanke nasabar da ta hada
ku".
Cikin gigita na ce "To ka sake ni, bana son yin surukuta da su. Kai ma bana sonka
Tijjani".
Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki
da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*

Jikinsa ya yi sanyi domin ya ga matsanancin fishi a tare da ni.
Ya numfasa ya ce "Na sani ai ba kya sona Asiya. Ban manta ba, amma na sakankace a
d'an zaman da muka yi, zaki iya mini kawaici da alkunya akan abin da kika san zai
musguna mini tunda kin sani sarai an jarrabe ni akan son ki. Amma yanzu na gane da
gaske ba kya sona tunda akan idona kika k'i gaida Baban Tsakiya cikin mutunci duk
da kashedin da nake yi miki da ido. Sannan kika gaida Jabir cikin falli har kina
kiransa Yaya alhalin kin kankare zumuntar da ubansa."
Na yi shiru domin kam jikina ya yi tub'us.
Ya cigaba da ce wa "Saboda shi kina sonsa, kuma yafi ni ku'di shi yasa kike ce
masa Yaya ni kuma ki gatsa Tijjani gatsal duk da na girme shi kuma ni ne mijin ki.
Asiya ba zamu tab'a daidaita wa da ke ba alhalin kin ri'ke BAK'AK'EN TA'ADODI.
Yanzu duk k'uruciyar ki ai k'iris ya rage ki yi sha bakwai. Kin san kuma hukuncin
wacce ta bu'de baki ta ce mijinta ya sake ta ba tare da gamshasshen dalili ba.
Sannan kina da ra'ayin ruk'au na k'ullaci. Hakan kuma ba siffar mace ta gari ba ce.
Kamata ya yi zuciyar mace ta zama mai taushi da sassauci ba mai tauri da tsanani
ba."
Na ji kunyar kalamansa mussaman akan J.
Na tabbatar shi ba na ce masa Yaya. Amma ban da yau ai nafi wata ban kama sunansa
ba, sai dai na yi masa magana kawai. Domin na da'de da daina fa'da a dalilin kunya
na kama ni tare da nauyin gatsa sunan nasa.
Na tura baki na juya baya. Cikin k'unk'uni na ce "To ai kai ma kana da Bak'ar
Ta'ada din, akan me tun a ranar ba zaka fa'da mini laifina ba, sai kawai ka k'ulla
ce ni, ka tsiri fishi. Ni ba Allan musuru ba, ta ina zan san kuskurena?"
Ya matso jikina ya ce "Da kina sona ai tun a lokacin zaki fahimci sauyin nawa, sai
ki shawo kaina ki ririta ni, ki mantar da ni b'acin ran da nake ciki. Amma saboda
am nothing to you ai share ni kika yi. Kika tattara kika yi wurgi da ni".
Na cuna baki na yi shiru. Ya mik'e dukkan k'afafuwan sa. Ya janyo ni ya kwantar a
kai. Ya shiga wasa da gyararren gashina. Murya a dak'ushe tabbacin yana cikin kewa
ya ce "Bana son abubuwan da kike yi a gabansu. Su din iyaye ne. Ta ko wacce fuska
sune a sama da ke.
Zan yi hakuri da komai akan sha'anin ki, amma ban da na fito na fito da iyaye, bana
so, ki bari."
Na yi shiru ban amsa ba.
Ya sassauta murya ya ce "kin yi shiru."
Na sake yin shiru still.
Ya zame ni daga jikinsa ya juya baya ya yi kwanciyarsa.
Ina ganin hakan ai kuwa na tak'ark'are na zunduma masa fallashasshen kukan da baya
so.
Ina ce wa "Tunda juninka k'ullaci ne ka mayar da ni gidanmu kawai".
Ya juyo da azama ya ce "Asiya ki cigaba da wula'kanta ni. Amma ki sani komai zaki
yi ni ba zan mayar da ke ba, domin ina son ki, ke da ba kya sona sai ki tafiyar ki,
hakan kuma ba shine k'arshe farin-ciki a gare ni ba."
Na sassauta kukana domin na ga ya hassala sosai.
Na dinga yinsa kasa kasa irin mai cin rai din nan.
Da ya gaji da jin kukan nawa ya saka hannunsa ya ja ni jikinsa ya ce "Yi shiru
Asiyata, amma ba zamu shirya ba sai kin ba ni hakuri dole".
Duk yadda na k'agu mu shirya fuska na yi da ce wa "Ai ban maka laifi ba. Sannan ba
dan komai nake ce wa Jabir Yaya ba sai dan yana ce mini Yabi ne. Amma kai sai ka
dinga ce mini Asiya Toro babu ko sha'awa ma".
Ina rufe baki ya ce "Har abada ba zan ce Yabi ba, idan ya so ba Tijjani kawai ba,
ki fa'di cikakken sunan nawa Tijjani Yusuf Bulkachuwa! Marar kunya. Shine rannan
kika yiwa yaro sababi akan ya k'ira ni da Tijjani to ke d'in kin saya ne bare ki ji
ciwon wani bai saya ba. Kuma ni ban damu sai kin saya d'in ba".
Na nisa na saki ajiyar zuciya irin wacce ake yi idan an ci kuka sosai. Na ce "Ni fa
tuni na samo maka sunan da zan fa'da maka, amma sai na haihu".
Maganar ta zo masa a bazata. Ya ru'ko ni ya ce "Kina son haihuwa ne Asiya?"
Da sauri na ce "Ina so sosai, domin duk wanda muka taso ko wacce ta haihu. Wadanda
aka yi aurenmu tare Nasiba da Ubaida dukkansu ciki ne da su, ni ce kawai ba ni da
shi".
Na fa'da da karyayyar murya.
Ya sassauta ya ce "Asiya haihuwa lokaci ne da sannu ke ma wataran zaki gan ki da
naki cikin. Tunda kin daina guduna, sannan nima ina iyakacin k'ok'ari, kawai mu
dinga addu'a".
Na ce "To. Ka ga Gwaggo ma ta ce ba zata zo gidan nan ba sai na haihu".
Ya rungume ni sosai ya ce "In sha Allah zaki haihu Asiyata. Mace kike so ko
namiji?"
Kai tsaye na ce "Ni dai na samu cikin nafi so. Ko mai na haifa ina so ba ni da
za'bi."
Ya yi dariya ya ce "Tom shike nan Allah zai bamu In sha Allah! Kawai ki kara zama
jaruma, ko sau nawa za'a yi kada ki yi musu ko ki ce kin gaji".
Na ce "Da gaske idan na yi haka zan samu cikin ko dai wayo zaka yi mini?"
Ya k'yal-k'yale da dariya ya ce "Ba wani wayo gaskiya nake fa'da miki Asiyata".
Daga hakan kuma ya shiga kissing d'ina tare da zafafan sakonni masu rikita ni. Sai
da ya tabbatar ya rura mini jiki. Sannan ya sake ni ya kwanta tare da ce wa "Au
ashe baki ba ni ha'kuri ba fa, bamu shirya ba".
A hankali na ce ", Mun shirya mana, ba har ka yi dariya ba yanzu".
Ya ce "Ai ba ki bani hakurin da na ce ki ba ni ba".
Na fara kukan shagwaba, ya juyo ya ce "To fa'da mini a kunne na ji".
Cikin kuka kuka na ce "Allah ya baka hakuri".
Ina fa'din hakan ya rungume ni yana cewa"Ameen little girl na ha'kura na huce
gaba'daya".
Daga hakan kuma ya dinga b'arin jiki a kaina, komai ha'dama ha'dama yake yinsa har
na gamsu k'arfin hali ya yi a kwanakin amma ba samu yake yi a waje ba. Domin duk
kulafacina sai da na k'osa amma shi bai k'osa din ba".
Haka muka cigaba da gurgurawa ciikin rufin asiri. Dai-dai gwargwadon k'arfinsa yana
yi mini komai.
Matsalar da ta fara damuna har cikin zuciyata rashin samun cikina gashi watanmu
goma da aure Nasiba jiya ta haihu Ubaida kuwa har an saka ranar da za'a yi mata
tiyata(c.s).
Da aka sanar mini da haihuwar yini na yi cikin sanyin jiki.
Sai kuma matsalar Rafi'a. Wata guda da kammala karatunta na digiri ta tattaro ta
dawo gida gaba'daya.
Kusan ko yaushe a k'ofata take. Idan ina k'unshi sai ta hakince a falo da sunan
kallo. Ko Tijjani ne ya dawo ba zata tashi ba, sai ma ta yi ta jansa da zancen
makaranta su yi ta hirarsu. Ko idan ta ga ya fita sai ita ma ta bi shi su fita
tare.
Ranar da na yi masa k'orafi ya balbale ni da sababin wai na raina shi, ban yarda da
shi ba.
Na kame baki na yi shiru, kuma sai da na ba shi hakuri akan hakan.
Tunda ya ja ya tsaya ba shine yake zuwa wajenta ba, ba shi yake kiranta ba, tunda
bana so ta zo mini gida to na hanata zuwa kawai.
Na rasa ta yadda zan kore ta domin dai gaskiyar magana uwarta tana mini kirki da
alheri mai yawa a matsayin ta na babba. Bayan haka ita kanta Rafi'a din kirki ne da
ita. Bai zame mata komai ba ta yi mini gyaran gida ba. Kawai ni yadda take shige wa
Tijjani ne bana so, domin na riga da nasan shi akan lutayen mata.
Wadannan matsaloli sai suke neman sauya zaman aurenmu. Domin ni a k'arancin
shekaruna dauka na yi Tijjani ne ya ki yi mini cikin kawai. Sannan yana son Rafia.
A hankali na fara janye masa, abubuwa suka fara sauya wa a tsakaninmu.
Na daina sauraronsa ko na saurare shi ma to kuwa sau daya ne shima ba cikin da'din
rai ba.
Ranar da na dawo daga sunan Nasiba kuwa. Kuka na zauna na yi masa mai d'aga hankali
k'warai da gaske. Ina yi ina ce wa "Akan me zaka matsa mini sai ka ta'ba ni bayan
bana so, na riga na gane ba cikin nan zaka yi mini ba, dan haka na gaji da
nukurkusata da kake yi babu sassauci babu kuma wani abu da zan samu."
Ya zuba mata ido yana kallon yadda take kuka bilhakki. Ya tafi tunanin shekarunta.
Watan da ya shud'e ta ciki shekaru sha bakwai.
Ke nan akwai k'uruciya mai yawa a tare da ita. Bai kamata kuma ya biye mata ba,
domin ya fahimci da dukkan zuciyarta take ganin shine bai mata ciki ba.
Ya numfasa ya saki gauron numfashi kafin ya ce "Asiya Allah ne fa mai bayarwa, kuma
ba mantawa ya yi damu ba. Kika san tanadin da yake yi mana?"
Cikin kuka na ce "Ba wani, ni kawai ciki nake so, ai ko wacce ta haihu saboda
mazansu suna sonsu, sai ni ce kawai saboda baka sona, kowa wani gani gani yake yi
mini ba'a yi mini ciki ba".
Dariya ta so subuce masa, amma ya maze ya ce "Asiya zai yi wahalar gaske a samu
wacce ake takarta irin yadda nake yi miki a cikinsu. Kin san da yawan yi ne sanadin
samun ciki da yanzu kin haihu sau uku.
Amma shi samuwar ciki ai ikon Allah ne."
Da rawar murya na ce"Ba wani kawai dai ni ce baka so na samu ba, ga Ubaida nan
yarinya da ita jibi za'a ciro mata d'a ko y'arsu, kai ma da su Nasiba ka aura ai da
tuni ka yi musu.
Ina goge idona na ce "Wallahi na baka nan da wata d'aya, idan ban samu ciki ba to
ba zan zauna ba".
Ya sake zuba mini ido cikin mamaki mai yawa. Ni kuwa ko d'ar ban ji ba.
Ya ha'diye komai ya ce "Shike nan Allah ka taimaki Tijjani ya yiwa Asiya Toro cikin
y'an-uku".
Na yi maza na ce y'an uku tashi guda? Y'an biyu ko daya ma ya isa."
Ya fara ta'ba ni, na bige hannun na ce "Ni fa yau na gaji Wallahi".
Ya ce "To shike nan Asiya Toro Allah ya kai mu gobe, tunda ciki kike so ki sani fa
babu ke babu hutu, amma na yarda ki huta yau din".


*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a
kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu,
nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*



✍️
*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki
da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*


*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA
KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA
KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
59&60.
Haka al'amuran suka ci gaba da gudana.
Aka ciro wa Ubaida kyakkawar jaririyarsu mai cike da koshin lafiya. Ita kam gida
aka tafi da ita. Tunda bata da lafiya.
Sai da aka yi sati biyu da haihuwar sannan aka yi taron suna.
Ranar sunan na ga dukkan y'anmata da muka taso har ma da k'anwata kowa da d'a ko
y'a a hannunta amma ban da ni. Na shige d'akinmu na dinga kuka. Yaya Ummi ce kawai
ta gano ni. Dan kuwa ita Gwaggo ma bata dauki hakan a matsala ba ne. Yaya Ummi ce
ta dinga ba ni hakuri tare

Please Login or Register in order to submit comment