You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nauyi. Duk da kular ba irin ƙatuwar nan bace ba kuwa. Addu'a take ALLAH yasa ta samu baba driver harta ƙaraso. Aiko ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ganinsa zaune shi kaɗai a kujera yana latsa waya. Daga can gefe maigadi na alwala. Sai Sanda na barci a barandar ɗakinsu ya juya baya. Kai tsaye wajen Malam Buba ta nufa. Duk da yanda take jin bugun zuciyarta na ƙaruwa, hakan ya zame mata jiki a duk lokacin data kusanceshi. Tunma yana damunta har ya daina. Ƙasa takai duƙe tana ajiye kular da gaishe shi. Idanunsa a kanta ya amsa, itama sai ta ɗan ɗago ta kalleshi. Cikin raɗa ta furta, “Baba mutumin kwanaki yazo nemana da bana nan ko?”.
Sosai gaban Malam Buba ya faɗi, a ransa yace (A ina tasan hakan?) a zahiri kuwa sai ya fara inda-inda.
“Baba ka faɗa min dan akwai matsala ne. Wani munafiki ya ɗauki hotonka kai da shi kuna a mota ya kawo ma Dada......”
Kaɗan ya rage zuciyar Malam Buba ya fito ta baki. Ba arziƙi yaji fitsari na neman zubo masa. Ita kanta Nimrah taga firgitarsa a zahiri. Amma sai fahimtarta tasha banban da halin da yake ciki. Ta cigaba da faɗin, “Wlhy kuwa Baba nima hankalina ya tashi. Shiyyasa tun ɗazun nake son fitowa na amshi wayar Sanda na kira shi.”
Ai malam Buba bai ma san ya furta, “I...ina da lambarshi U...u..w...a. amshi maza kirashi. Idan kuma ni na kira shi to”.
“Baba ka tabbatar wadda zaka sameshi ce yanzu?”..
“In sha ALLAHU”.
“To Baba dan ALLAH kayi da sauri kawai ka kirashi kai. Dan Dada ya fita da hotunan, kuma ban san mi zaiyi akai ba”.
Kansa ya jinjina mata yana haɗiye yawun dake neman sarƙe masa numfashi. Ita kuma tabar wajen...

★Nimran na shigowa falon Abees daya fito a bedroom ɗin Mammah ya tareta da faɗin, “Aunty Mammah tace kizo”.
Kanta ta jinjina masa, sai kuma ta ce, “Muje to”.
“Aunty zanje wajen Mamy ne, ta aikoni na kawoma Mammah abu”.
Anan ma kan nata kawai ta jinjina masa. Ya wuce ita kuma ta shige bedroom ɗin Mammah. Afeef dake zaune a falon yana binta da kallon harara ya taɓe baki. Sai kuma ya saki murmurshi a fili ya furta, “Shegiya ƴar iska. Na kusa maganin ki ai. Sai na tona muku asiri a gidan nan. Dama na faɗa miki, idan na tashi ramawa sai na miki mai zafin da har ki mutu bazaki manta da ni ba.”
Daga haka ya miƙe ya haura staircase.

Nimrah kam ta samu Mammah na waya. Dan haka ta nema waje ta zauna tana jiranta. Sai da ta kammala sannan ta sake miƙewa ta koma kusa da Mammah ɗin. Mammah ta riƙota tana kwantar da kanta a kafaɗarta. Sai da ta shafa fuskarta cikin damuwa ta ce, “Autana duk kin rame min a ido. Inaga ɗurar abinci zan fara miki gaskiya”.
Murmurshi Nimrah tayi, ta kama hannun Mammah ta sumbata. Cikin shagwaɓa ta ce, “Mammah idan kikai min ɗura zan zama ƙatuwa ALLAH. Ni kuma bama son ƙiba no da Buddy.”
“Uhm-uhm yaran zamani sai a barku. Yanzu miye abin gudu a ƙiba kuma?”.
“Mammah ALLAH ƙiba ciwo ce. Mutanenmu ne kawai ke ganin sai kayi ƙiba wai kake jin daɗin rayuwa. Amma ƙiba ai ba abin so bace.”
Mammah tai dariya kawai da sake shafa kumatunta. Sai kuma cikin kulawa da iya sarrafa zuciyar yaro ta ce, “Tun juya nake son mu zauna ki bani labari, amma iyayenki sun zagayeki. Bani labarin miya faru da kika fita ranar?”.
Daga Ruƙayya har Nimrah basu san ɓoyema Mammah damuwa ko magana ba. Ko Dagger yaci galaba a kan Nimrah ne saboda barazanar kashe Ruƙayya da yay mata. A yanzu ma akwai dalilan da bazata iya sanarma Mammah komai da komai ba. Amma akwai abinda bazata iya ɓoye mata ba. Sannan tana son sanin wanene akai mata aure da shi, idan taji a bakin Mammah kuma zatafi gane abinda ake nufi.
Received at 12:31 PMDan haka ta gyara zama ta fara bama Mammah labari tiryan-tiryan. Har batun fashewar bomb bata ɓoye komai ba. Tadai yanke labarin daga inda su Leo suka fiddata a gidan da aka fara kaita, duk abinda ya faru a gaba bata faɗa ba. Ta share hawayen da suka zubo mata, cikin rawar murya ta ce, “Mammah sunce an min aure, kuma assignment ne naje na bincika waye mijin da kaina.”
Sosai ƙirjin Mammah ke duka, amma sai ta danne tana murmurshi da kamo Nimrah ta sake rungumewa a jikinta tana share mata hawaye.
“To shine kuma abin kuka Autar Mammanta. Ai aure alkairi ne, sannan Rahama ne. Ɗan gata kuma akemawa da ƙarancin shekaru. Ke da Ruƙayya kuma ƴan gatan Mammah da iyayenku ne. Tabbas basuyi ƙarya ba ke matar aure ce. Kuma kina da shekara bakwai aka ɗaura......”
“Mammah saboda mi?”.
“Saboda ke ƴar gata ce Nimrah. Duk da dai akwai ainahin abinda ya faru a lokacin, amma bazan faɗa miki ba sai kin ƙara girma”.
“Mammah waye mijin?”........✍️
Received at 12:31 PM
2 people reacted
[16/02, 10:59 pm] null: KIƊA A RUWA 3

19

........Sosai Mammah tai murmurshi mai yalwa da hango ƙuruciyar Nimrah a fili. Sai kuma ta shafa kanta. “Miyasa kike son ji tun yanzu? Kiyi haƙuri zaki sanshi. In sha ALLAHU kuma zakiyi farin ciki.”
Kai Nimrah ta jinjina kawai tana sauke ajiyar zuciya. Sai dai taso tasan wanene mijin, amma bazata iya jayayya da Mammah ba. Zata cigaba da haƙuri, da juriya har lokacin da Mammah tace ɗin yayi. Mammah data fahimci halin da take ciki, sai ta ƙara gyara zama ta shiga lallashinta da nasiha mai tsada da daraja. Ta yanda a hankali komai ke shigar Nimrah tamkar ruwan allura a jijiyoyin jiki. Daga ƙarshe Mammah ta fara bata labarin tarihin rayuwarta. Ai gaba ɗaya sai Nimrah ta shagala, sai dai daga lokacin da tazo gaɓar rasuwar Baba Abdul-rasheed da ciwon Mama Yakura zuwa rasuwarta duk Nimrah ta rikice da kukan tashin hankali, ita kanta Mammah hawaye take, tama kasa ci-gaba. Sai da sukai kuka sosai sannan Mammah ta ƙarasa mata har ƙarshe lokacin da suka dawo garin nan da zama.
Nimrah ta share hawaye, idanunta jajur ta furta, “Mammah kun sha wahala ke da Dada. Amma miyasa tun sanda aka rufeshi na farko baki hanashi aikin soja ba?”.
Fuskar Mammah da murmushi ta shafa kan Nimrah. “Nimrah kowanne bawa da irin ƙaddararsa, kowa kuma da irin rayuwar da UBANGIJI ya tsara masa. Dadan ku na son aikin soja, kuma na gamsu da jajircewarsa akan ƴan uwansa marasa ƙarfi irinmu da yake ƙoƙarin bama kariya. Hanashi ba itace masalaha ba addu'a ce komai”.
“Hakane Mammah. Nima yau naji ina son nayi aikin soja”.
Yanzu kam sosai Mammah tai dariya da faɗin, “Soja fa Auta?”.
“Eh Mammah, ina son na zama kamar Dada da Daddy”.
“To bazance a'a ba, muyi addu'a ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi”.
“In sha ALLAHU zanyi. Amma Mammah a ina shi ƙauyukan Bankaura ɗin da akaima kisan gilla ɗin suke? Ina son zuwa garin”.
Yanzu kam shiru Mammah tai tana kallonta. Ta bata labarin komai daya shafi su da al'amarin Muhammad, har abinda ya faru a ƙyauyukan Bankaura daya zama sanadin rufe Dada na shekaru 8. Amma bata gaya mata komai daya shafeta ba balle tasan ita ƴar wannan yanki ce, tayi hakan ne kuma dan tafi son Muhammad ya sanar mata komai da kansa.....
“Kinji Mammah”.
Nimrah ta katse mata tunani. Ajiyar zuciya Mammah ta sauke. Cikin jinjina mata kai ta ce, “Saboda mi kike son zuwa?”.
Nimrah tai murmushi tana haɗiye abinda ke ranta. Cikin nuna rashin damuwa ta ce, “Mammah haka nan kawai. Dan wani ma tunani nake yi...”
“Na mi?”.
“Zan fara rubutu a kansu. Mammah bayan aikin soja yanzu na ƙara jin ina son zama MARUBUCIYA”.......


×××××××××××

“Wlhy Daddy da gaske nake maka. Har video ma na musu jiya. Ai tun randa ya shiga ɗakinsu da daddare na fara saka musu ido. Sai naga ita ɗayar bata shiga ɗakinsa da daddare kamar yanda wannan shegiyar keyi. Aiko jiya dubunsu ta cika......”
“Kaga katse kiran nan ka tura min video ɗin”.
Babu musu Afeef ya katse kiran, yana wata ƴar dariyar ƙeta ya tura videon da jiya yay ma Dada da Nimrah batare da sun sani ba. Sai da ya kammala ya juyo yana kallon Hanoon datai tagumi...
“Afeef wai baka jin tsoro, mutum nan daga ganinsa wlhy ba imani zai yi ba. Itafa shaidar zina ance sai ka gani da idonka...”
“Ke ai dama wawuya ce, dan kina son shi shiyyasa ma kike kamar baki yarda da abinda na nuna miki ba. To kar ki yarda ɗin, ni ina ruwana da wani a addini sai an gani da ido. Sannan da kike wani magana baida imani ya kashe ni mana. Kuma ai itace taja masa, dama na rantse sai na mata abinda bazata taɓa mantawa dani ba.....”
“To amma tunda itace ta maka laifin ka rama a kanta mana ba shi ba. Sannan kai ne wawa, kuma ina ji maka tsoron Daddy ya fitar da maganar nan ta dawo cikin gidan nan kaine zaka sha wahala”.
Tana gama faɗa ta fice a ɗakin. Da kallo ya bita zuciyarsa na wani irin zafi. Sai kuma yay ƙwafa....
Received at 12:31 P ★A ɓangaren Uncle Tasi'u yana kallon video yana faman jinjina kai da sakin murmushi. Jinsa yake rai fess. Dan kuwa ya samu makamin da zai sami abinda yake so gun Adda A'isha. Duk da wani gefen zuciyarsa na gargaɗinsa akan halin Haysam. Amma wadda ke zugashi na dannewa.
Fitowa yay daga cikin videon, kai tsaye ya sayi ticket ta online, dan dole ne ya je ƙasar haihuwarsa. Zuwa na bazata a yau ɗin nan. Daɗi sosai yaji na samu jirgi mai tashi nan da awanni goma. Dan haka babu ɓata lokaci ya hau shiri......

>>>>>>>%<<<<<<

Washe gari safiyar juma'a aka sallamo Lailah mai jego, duk da jiya su Nimrah tun yamma har dare suna asibitin tuni suka rikice da farin ciki. Dan sun tattare inasu-inasu sun koma sashen su Lailah gaba ɗaya. Tunda dai jarirai sun zama biyu sai aka raba rigima kowa ya ɗauki ɗaya.
Sosai farin cikin kasancewa da babys ya kwashe rabin hankalinsu acan. Sai dai wani kaso na tunanin Nimrah nakan Dada ne. Dan tun fitar jiya da yayi bayan ya amshi hotuna a hannunta har yanzu bai dawo gidan ba. Ga Baba Driver ma tun jiyan bata sake ganinsa ba. Abin ya dameta ƙwarai da gaske, batare da ita kanta tasan dalilin yin hakan ba. Bayan sallar la'asar sai ga Mu'azz ya shigo, dawowarsa kenan daga makaranta. Bai ko shiga sashen Mammah ba yayo nan shima. Suna cikin caftarsu Aunty Shariffa na rabon faɗan akai baƙi ƴan barka. Dole suka fito dan basu waje kasancewar suna da yawa.
Mu'azz ne ya takali Ruky sabuwar rigima, hakan yasa ta bishi da gudu. Nimrah uwar zuga ta bisu tana faɗin, “Yauwa Buddy na kada ki raga masa”. Tana maganar ne tana dariya har suka shigo falon. Da yake suna gabanta sun rigata. Ta shigo ta samesu tsaye cak, sai kuma muryar Mammah dake magana kamar cikin ɓacin rai ta daki kunnenta. Itama tsayawa tai dan in kaji Mammah na faɗa an kaita bango ne.
“Nace Tasi'u mi kake nufi?!”.
Furucin Mammah ya sake dukan kunnuwansu. Sai lokacin Nimrah ta fahimci ashe baƙo sukayi a gidan. Ba kuma kowa bane face Uncle ɗin nan da yazo kwanaki kuma Baban su Finga-fiyau kamar yanda Mammah ta sanar musu. Yana zaune a kujera gabansa da abinci da aka jera a Center table. Sai Mammah da itama ke zaunen tana facing ɗinsa. Da waya a hannunta fuskarta kuwa yanayi ne da zasu rantse basu taɓa gani ba...
Gwaggo Khadijah da Gwaggo Alawiyya da suka fito suma saboda tsawar Mammah suka ƙarasa inda suke. Gwaggo Khadijah ta zaune tana riƙo hannun Mammah da faɗin, “Ayi haƙuri Maman Ma'aruff. Mike faruwa ne?”.
Maimakon Mammah ta bata amsa sai Uncle Tasi'u ne ya amsa mata cikin ɓacin rai. “Yaya ki barta, na rasa miyasa Adda bata son gaskiya akan yaranta, dan fa kawai nace mata gyara kayanka, shine zai zama sauke mu raba......”
“Karka kawo min zancen banza zancen wofi Tasi'u”. Mammah ta katse shi a tsawace fiye da tsawar ɗazun da sai da ta saka su Nimrah zabura. Cikin nuna shi da yatsa tare da wurga masa wayarsa dake hannunta ta cigaba da faɗin, “Mika sani akan yarana da har zaka yanke musu hukunci? Dama ka kawo min yaranka gidana dan su dinga saka maka ido akan al'amarin mu.....”
Gwaggo Khadijah da hankalinta ya ƙara tashi ta riƙo Mammah. “A'isha dan ALLAH ya isa haka. Ya kuke abu kamar wasu ƙananun yara, wai mike faruwa ne? Ku fiddani a duhu....”
Kuka sosai Mammah ta fashe da shi, ta nuna wayar Uncle Tasi'u dake yashe a ƙasa. “Yaya Khadijah na gaji da halin Tasi'u wlhy, ki faɗa masa in dai ba alkairi ya dawo dashi cikin rayuwata da zuri'ata ba dan ALLAH ya tattara yaransa su koma. Wai ki duba video cikin yaran nan wani ya ɗauka na Muhammad da Nimrah, shine yazo yana zancen banza akan hakan. Wai Muhammad na neman Nimrah...” babu wanda bai razana ba a falon, Mammah ta cigaba da faɗin, “To bari kaji kai da masu ɗaukar Videon ko zaku dawo cikin hankalinku. Nimrah MATAR Muhammad ce. An ɗaura musu AURE tun tana da shekara bakwai. Sai ka sake wani shirin”.
Received at 12:31 PM
reacted with ❤ Wani irin duka kan Nimrah yayi tamkar an saki irin tsawar nan mai girgiza gari a cikin tsakiyar ruwan da ke sauka da manya-manyan ƙanƙara. Kalaman Mammah suka wani irin sake maimaita kansu a cikin illahirin duk wata ƙofa dake amsa suna ƙofa a cikin jikinta. (Nimrah MATAR Muhammad ce. An ɗaura musu AURE tun tana da shekara bakwai). Ai sai kawai tayi luuuuu zata zube. Da wani irin ihu su Ruƙayya da sukai sumar tsaye dan suma kalmar ta dake su da girgiza su suka zabure kanta. Sai kuma suka tsaya cakk sakamakon ganin Dada da babu wanda zaice ga sanda ya shigo falon, da ga gefensa Daddy Imran ne. Nimrah da ta tafi zata zube ya tare da jikinsa. Yana tsaye ne ƙyam akan ƙafafunsa, hannunsa ɗaya tallefe da bayanta saboda tareta da yayi, ɗayan na cikin aljihu. Sai dai idanunsa da sukai masifar juyewa da wani irin hargitsatstsen yanayi tsaye suke ƙyam akan Uncle Tasi'u da shima ya juyo wajen kamar su Mammah saboda ihun Mu'azz da Ruƙayya...
Tuni Hanoon da Afeef da Dayyan dake laɓe sun fito suma. Ganin Dada da basuyi zato ba tunda sun san tun jiya baya gidan tuni ya firgitasu. Dan Afeef ya jiƙe sharaf da zufa ga icayi na neman kufce mas a wando.........✍️

Afeef tsuntsun da yaja ruwa ba shi ruwa ke doka ba🤣. Ka ragema su Mammah aiki 🥱🚶👌..........A hankali Daddy Imran da shima ke kallon Uncle Tasi'u cike da ɗunbin mamaki dan duk abinda Mammah ta faɗa a kunensu ne. Shigowar su Nimrah babu jimawa suka shigo. Hakan ta faru ne kuma saboda su ta gaba suka shigo, su Nimrah kuwa daga sashen su Ma'aruff ta kofar baya suka shigo. Dan haka basu san da zuwansu gidan ba.
Idanun nasa da shima suka kaɗe ya janye daga kan Uncle Tasi'u ya maida kan Dada. Yasan waye Zakinsa, dan haka ya ɗan sauke numfashi da kai hannu ya akan kafaɗarsa ya ɗan bubbuga alamar lallashi. A hankali kuwa Dada ya juyo ya zuba masa idanun nasa, sai kuma ya lumshe su ya sake buɗewa. Batare da yace ma kowa uffan ba dai-dai Uncle Tasi'u da jikinsa ke rawa na zaburowa da nufin zuwa inda yake lips ɗinsa na motsi alamar magana zai masa kawai Dada ya ɗaga Nimrah dake a sume cak yau wucewarsa.
Ai ba Mammah data san halin kayanta ba hatta su Gwaggo Khadijah sai da suka ɗan waro idanu waje. Dan asalin manna wulaƙanci gangariya da babu gauraye Dadan yay ma Uncle Tasi'un. Imran ya duƙar da kai yana danne murmushin dake neman suɓuce masa da ƙyar. Sai kuma ya ɗan sake ɗagowa ya kalla Dadan dake haura staircase da wani irin salon ainahin jarumai. Sai ka rantse ba mutum ya ɗauka ba, dan babu alamar yana jin nauyinta duk da tana a sume ne....
Da wani irin sauri itama Nabeeha ta dafe kanta dake sara mata, sai kuma tai ƙoƙarin riƙo Ruky dake kusa da ita. Da sauri Ruƙayya ta juyo, hakama kowa na falon da sai yanzu suma suka farga da ita. Ashe itama komai a kunnen nata ya faru, dan su Amima na balcony na sashenta motar su Dada ta shigo, shine Rayhana ta kirata a waya ta sanar mata. Sai ko gata ta fito da hanzari, sanda take fitowa su kuma har sun kusa sashen Mammah. Sun shigo kenan itama ta afko amma taja ta tsaya ganin abinda ke faruwa alamar babu lafiya saboda ganin Mammah na kuka. Sai kuma ga bayani taji kamar yanda kowa ya ji. Zuciyarta na neman tarwatsewa duk da tasan wannan amma sai taji kamar ita Mammah ke ma bitar tunatarwar mijin Haysam mijin Ninrah ne ƴar cikinta da da'ace tana zuwa gidan ta samu ciki zata haifi kamar Mu'azz ne. Dai-dai ta ɗago zata kalla Dada dake gabanta kaɗan kawai taga ya matsa da wani irin zafin nama ya taro wadda keta gabansa kaɗan Da sai da ta faɗa jikinsa sannan taga fuskar Nimrah. Sai kawai taji numfashinta ya ɗauke komai ya tsaya mata cak, shine bata dawo a hayyacinta ba sai yanzu, duk da yanzun ma a wani yanayi ne saboda ganin abinda Dadan ya aikata kuma ko'a jikinsa ya ɗauki ƴar yarinya a hannu a gaban kowa ya haura sama inda kowa yasan ɗakinsa zai kaita.....
___

A dai-dai kuma wannan lokacin cikin hikimar UBANGIJI wani al'amari mai girgiza ƙasar da al'ummar cikinta, dama ɓoyayyun munafukai yay amsa kuwwa. Domin kuwa bayani ne mai girma, mai tsauri, daban al'ajabi ya fita daga fadar shubagaban ƙasa akan sunayen waɗanda aka bama muƙamai masu daraja da kima da zasuyi aiki a wannan gwamnatin tasa.
Akwai manyan ministoci guda takwas da sunansu ya fara fita, sai babban sakatare. Sai NATIONAL SECURITY ADVISOR (NSA) . da CHEF OF STAFF. Ba muƙaman ne suka girgiza ƙasar ba, sunayen mutanen da aka bama muƙaman biyun ƙarshe ne. Mr. Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi is appointed as the (Chief of Staff to the President). & Mr. Imran Abbas is appointed as the National Security Advisor (NSA).

Gan-gan-gan-gan. Wannan fa shine ainahin tashin bomb mai kai goma sha biyu. Shugaban ƙasa kuma na kammala bada umarnin sanarwar dan tun jiya ya rattaɓa hannu a gidansa yau ya ƙaddamar a yanzu kuma ƙarfe huɗu na yamma. Yana badawa kuma yay shigewarsa gida. Gashi yau juma'a ce, za'a shiga hutun weekend.
Wannan fa shine (Tarwatsa wara wari jikan Tafida!, rai ya daɗe rai yayi ma alfarma. Kaga mazan aiki sun zo. Ya cika sittin mai ban mamaki🔥....) Aba Nasiru Sarkin waƙa shawara ya yoma shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida irin wannan waƙar sak ta sarkin Kano shima. (Kai ku bamu kiɗan janaral a sama. Masu gudu su gudu, sai Baba Tafida, sai Baba Tafida. Bana dai janar shine a sama... Amma a KIDA A RUWA..... Masu gudu su gudu.
Received at 12:31 PMKu faɗama shaggun can su ware💃💃🥱😂🤣).

Tabbas Janar ma KIDA A RUWA ne MAI TADA HANKALIN DODONNI

Jama'a to ALLAH ya taroni🥺, sanyi fa ya kankama sai kun haɗa da haƙuri magana ta ALLAH. Yo irin wannan waƙoƙi haka kamar babana ne Janar ɗin🥱😎🥶🧑‍🦯.

•••••••••••••••••

“Amma kai Mole wawa ne, jaki ma dabbul arab. Shine sai yanzu kake gaya min?”.
Wani irin tafasa zuciyar Malam Buba ta shiga yi a cikin ƙirjinsa. Ya kalla Dagger da idanunsa da suka kaɗe jazur saboda yanda kalamansa sukai masa zafi matuƙa. Amma sai ya danne a kan harshe ya furta. “Oga ya kake so nayi?. Tun jiya da Uwa ta faɗa min fa na baro gidan nake nemanka. Yanzu haka kalla jakkata anan na gama yanke binka sansani idan har ban sameka na ƙarshen nan ba. Sai kuma nayi sa'a kaga saƙona kazo.”
Gaba ɗaya Dagger ji yake kamar kansa zai tarwatse dan tashin hankali. Ya dunƙule hannu da masifar ƙarfi ya daki bangon ɗakin Malam Buba yana wani irin ƙaraji daya saka Malam Buba zaro idanu yana kallon ƙofa. Duk da saida ya rufe windows da ƙofar tunda Dagger ya shigo yana tsoron wani yaji ihunsa a gida... “Oga kayi a hankali mana kada wani yaji. A ganina ba rikita kai bane mafita. Tunanin abinda ya dace. Kasan dai tunda Uwa tace taga hoton nan mutumin nan bazai ƙyale mu ba. Dole zai fara bincike akanmu......”
“Shiyyasa nace kai wawa ne Mole. Idan kai jaki ne shi ba irinka bane ai. A zatonka zai mance da fuskata ne har ya zauna wani bincike a kaina? Kaima badan wannan gemu da sajen ɓadda kamar daka sanya ba da wannan fentin da kake ma kanka an gaya maka bazai gane ka ba ne tun a ranar farko? Ko a yanzu na fara tantamar guy ɗin nan bai gane ka ba, ya barka ne kawai a cikin takunsa.”
Tsuttt fitsarin tashin hankali ya zubo jikin Mole. Jikinsa na karkarwa ya ce, “Amma Oga miyyasa baka taɓa faɗa min haka ba?”.
Wata muguwar Harara Dagger ya zuba masa kawai, batare da yace komai ba ya hankaɗesa ya buɗe ƙofar ɗakin ya fice abinsa. Ai gaba ɗaya sai Mole ya sake jin gudawa ma na neman zubo masa ba fitsari ba. Tuni ya zabura ya ɗauki jakarsa da dama ya haɗa komai nashi yabi bayan Dagger. Yana fitowa ya samu

Please Login or Register in order to submit comment