You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na minti uku sannan ya miƙa mata alamar ta cigaba da sakawa. Shi kuma ya ɗauki wayarsa.
Bata san waya kira ba, kawai jitai cikin umarni ya furta, “Turo min Ruƙayya”. Daga haka ya yanke kiran.........✍️

Hajja Ninah Ai wanda bai ji bari ba yaji hoi🥱🏃🏼‍♀️.
Received at 12:22 PM
[16/02, 10:58 pm] null: KIƊA A RUWA 3

14

........Anan falo Ammar na ajiye wayar su Aunty Ummi suka shiga masa alamar yaya dai. Dariya yayi, dama kuma ita suke yi tun fitowar Nabeeha da gudu tana kuka da basu san abinda ya korota ba. Tun wucewar Nimrah sama Mammah ta bar falon. Hakan yasa Gwaggo Khadijah da Gwaggo Alawiyya binta, dan sun san dai bai wuce lamarin Nabeeha ne ke damunta ba duk da tana ƙoƙarin ganin ta danne. Amma dai abinda Nabeehan tayi yau rashin kunyar tayi yawa ai.
Wucewar iyayen nasu ciki daɗi yay ma su Ja'afar, dan a take suka shiga amaye abinda ke bakinsu game da Nabeehan suma, kowa cin alwashi yake akan koyama Nimrah abubuwan da zata ƙona Nabeeha da ruwan jikinta. Sai kuma gata ta sakko a kiɗime harma tana kuka. Tsabar wulaƙanci sai suka fashe da dariya a tare har wasu na tafawa. Aiko kamar sun izata, sai ta ƙara gudu tana danne bakinta saboda tahowar wani sabon kuka mai ƙarfi. Suna cikin dariyar ne kiran Dada ya shiga wayar Ammar. Da sauri ya ce, “Kuyi shiru Dada ne”.
Tsitt sukayi ya gama amsa wayar, shine yana yankewa suke tambayar mike faruwa. Abinda Dadan ya faɗa ya sanar musu. Biebah ta ƙwalama Ruky dake kitchen tare da Mu'azz wai suna ma Nimrah special girki kira. Amsawa tai tana fitowa. Saƙon Dada ta gaya mata, da yake bata san wainar da ake toyawa ba ta nufi saman cikin farin cikinta..
Rikicewa Ruky tai da ganin Nimrah kamar tayi kuka. Ta shiga tattaɓata tana tambayar mike damunta. Har sai da Dada daya shagala a kallon su yay gyaran murya. Cikin shagwaɓa Ruƙayya ta kalleshi, kamar zatai kuka ta ce, “Dada Aunty Nabeeha ce ta dake ta?”.
Idanu ya waro waje dan mamaki. Wato dai halin iri ɗaya ne ita da aminiyar tata. Ji wani sharri kuma. Bashi da zaɓin daya wuce girgizama Ruƙayyan kansa, kafin cikin umarni ya ce, “Kamata kuje ta kwanta”.
Kamata Ruky tai, har suka fita yana binsu da kallo, a ransa kam yana jinjina wannan ƙaunar juna. Bayan soyayyar jini, da soyayyar ma'aurata soyayya mafi muhimmanci da ban mamaki ga ƴaƴan adamu itace ta abokantaka da babu alaƙar jini a ciki, lallai duk abokan da sukai tarayya akan soyayya ta gaskiya zasu shiga aljanna suna masu farin ciki da juna. Idan riya ko cin dunduniya ta shigo sai su ƙare da zage-zage da aibanta juna a ranar rarrabe ayyuka. (Ya Rabbi kasa mu rayu da masoya na gaskiya, mu kuma kasance a aljanna tare muna masu farin ciki da juna. Duk wanda zai zo garemu da fuska biyu, ya rabbi kasa shartinsa ya zamewa rayuwarsa bargo akan kansa can ya ƙarata shi kaɗai🙏).
Cahh iyayen nasu suka yo musu da tambayoyi a falo. Sai da Nimrah ta sanar musu abu ne ya faɗo mata a ƙafa sai kuma ta ƙone sannan suka nutsu. Amma da kowa ya hau da tunanin Nabeeha ce. Har sun fara ɗaukar alwashi a zukata. Dariya ce ta nema suɓuce ma Mammah dake ƙoƙarin fitowa. Ta girgiza kai tana gimtsewa. A ranta kam ta fahimci dole tai wani abu kafin waɗan nan iyayen banzar su ɗora Nimrah kan wani layin daban, a haka ma yaya lafiyar kura tunda itama ba ƙyalen bace ƙyallece ita da aminiyar tata Ruƙayya da basa ɓoyema juna sirri....

^^^^^^^^^^^^^^
A ɓangaren Nabeeha kam yanda ta shigo sashen nata ya saka Amima da Rayhana dake cin abinci kallon juna. Sai kuma suka taɓe baki a tare. Amima ta ce, “Lafiya kuwa?”.
“Ƙya tambayeni bayan muna tare”.
Cewar Rayhana fuska a yamutse.
Amimah ta ce “Hummm maybe korota sukai ko”.
“Mtsowww matsalarta ce. Banda zubar da kai ka dawo miji baizo inda kake ba kai ka ɗauki ƙafa ka tafi nemansa. Itafa wannan da cikin aljihun baya aka haifeta muguwar kidahuma za'ayi. Bata gane komai sai son miji.”
“Ikon ALLAH to miye dan taso mijinta Rayhana. Wani kike so taso to ne?”.
Hararar Amima mai maganar Rayhana tayi, cike da takaici ta ce, “Kema fa wawuya ce wani lokacin. Inba hauka ba son miji ne kawai rayuwar aure?. Mijin ma irin Haysam daya san martabar kansa, wlhy sam bata dace da shi ba.”
Received at 12:22 PM Galala Amima tai tana kallonta yanzu kam. Sai kuma tace, “Tofa wata sabuwa. Sai yanzu duk kika san wannan? Toke auren kikai da kika san mima mijin ke buƙata? Anya Rayhana babu wani abu a ranki?”.
“Ubanki ne a raina. Shegiya munafuka”.
Cike da son tura haushi Amima ta kwashe da dariya tana miƙewa da faɗin, “Oh to lallai abin ya girma. Ubana kam ai ubanki ne kema dole ya zauna miki a rai. Adai bi a hankali. Kar wajen tone-tone kaza ta tono wuƙar yankanta. Shi wannan NAMIJIN ZAKI ne ba Mazan club ba. Baya ɗaukar wargi balle shashanci. Itama data samu bata kasance ballagaza bane kuma tana cin darajar Abbanta. Amma kinga matsayarta, balle ke da aka saba leƙe-leƙ...”
Jifan da Rayhana ta wurgo mata da saving spoon ya sata barin wajen da gudu tana dariyar iskanci data sake shaƙe wuyan Rayhana...

••••••••••••••••••••

9:pm na dare Dada daya fita a gidan shi da su Ma'aruff tun bayan sallar magriba suka dawo. Asibiti suka rakashi ya duba Lailah da Baby, daga can suka je duba Daddy Imran gida. Zuwa lokacin su Aunty Ummi duk sun wuce gida. Falon ma babu kowa alamar duk sun shige barci. Baiyi mamaki ba dan yasan masu ƙiriniyar gidan na fama da kansu. Mammah kuwa dama akwai barcin wuri. Su Bilal kuma office gobe. Har ya nufi upstairs sai kuma ya dawo da baya, ƙofar Mammah ya nufa, yay knocking a hankali. A mamakinsa sai yaji tana bada umarnin shigowa.
Koda ya shigo a zaune ya sameta bakin gado tana duba wani littafin addu'oi. Ta ɗago tana kallonsa da amsa sallamarsa. Dai-dai yana kaiwa zaune take faɗin, “Ai har na fara tunanin kiran wayarka. Dan zaman jiranka nake daman”.
Ƙaramin murmushi yay da faɗin, “To Mammah lafiya dai ko?”.
“Lafiya lau. Yaya jikin Imran ɗin?”.
“Alhamdullah ai ba a jigace yake ba. Kawai dai harda razani”.
“Alhamdullah ALLAH ya kiyaye gaba. In sha ALLAHU zan je na duba shi gobe nima.”
“ALLAH ya kaimu”.
“Amin ya rabbi. Shaiɗancin mutanen nan ya fara bani tsoro Muhammad. Tunda har tunaninsu ya fara basu yin amfani da makusantanka domin samun biyan buƙatarsu. Abin akwai haɗari sosai a ciki, idan na farko an tsallake rijiya da baya nan gaba kuma fa?”.
Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, dan shi da farko ma yayi tunanin maganar Nabeeha zatai masa. “Kar ki damu Mammah in sha ALLAHU hakan bazai sake faruwa ba. Wannan ma da suka aikata zasu biya bashinsa harda riba da hannayensu. Akwai shirin da nake yi musamman akan su ƙananun nan. A cigaba da mana addu'a dai. Dan in sha ALLAHU nasara ce ke tunkaro mu. Ko ba komai abinda sukayi yanzu ɗin ya ƙara buɗe min tunani na akan sanin su waye su.”
“Addu'a har mu koma ga UBANGIJI bazamu daina yi muku ita ba, ALLAH ya cigaba da baku kariya. Ya ɗora nasararku akan maƙiyanku. Suma ALLAH ya shirye su su gane gaskiya kafin lokaci ya ƙure musu idan masu shiryuwa ne.”
“Hummm Mammah kenan, to Amin. Amma waɗan nan mutanen basa buƙatar shiriya.”
“A'a ba'a yankema UBANGIJI hukunci akan ikonsa ai.”
“Haka ne kam, ALLAH yasa mu dace. Ranar asabar iyayen Haydar zasu zo a tsaida magana. Kuma ina son ne kawai a saka rana batare da wani jeka ka dawo ba. Lahadi mu kuma sai muyi batun Bilal da Asma'u. Sai dai shima Ammar kawai zan haɗa da shi”.
Murmushin Mammah ya faɗaɗa sosai. Ta ce, “Alhamdullahi ALLAH yasa ayi damu. Ya kuma sanya albarka a ciki. Amma Auta yana da budurwa kuwa?”.
Yanzu kam sai da Dada ya ɗan murmusa. Kai tsaye ya ce, “Zan bashi Ruƙayyana in sha ALLAHU”.
Wani irin farin ciki ne ya daki zuciyar Mammah. Har bama tasan ta zabura ta kamo hannun Dada ba. Ta ce, “Muhammad da gaske? Aiko idan kayi haka ka gama min komai. Wannan tunanin ya daɗe a raina. Tsoron halin ɗan yau yasa na shanye abina. Ya rabbi yanda ka bani wannan farin ciki a wannan dare kaima ALLAH ya faranta maka har ƙarshen numfashinka”.
Received at 12:22 PM “Amin Mammah, tare dake da zuri'armu”.
Sosai take farin ciki, dan har sai da tai sujidar shukur. Bayan ta ɗago ne take masa maganar shima lokaci yayi da Nimrah zata san wanene shi a gareta. Dan ɗazun Imran ya kirata sun tattauna sosai. Shiru Dada yay baice komai ba, itama bata damu da shirun nasa ba ta cigaba da faɗin, “Tunda har sun gaya mata yin shirun mu zai sakata a wasi-wasi. Amma idan mun sanar da ita zata kasance a nutsuwa koda zata shiga ruɗani. Nimrah yarinya ce mai wayo, suna da iliminsu da fahimtar abubuwa gwargwadon iko, idan bamuyi saurin yin hakan ba a yanzu suke tasowa samari na kawo musu caffa, idan sun tsallake tarkon wani bazasu tsallake na wani ba dan zuciya ba'ai mata shamaki ƙo ƙa'idar wanda zata iya so. Makarantar ma idan zata zama damuwa kawai su zana ssce wannan shekarar, maybe idan suka ga kansu a jami'a a samu sauƙin wannan ƙiriniyar tasu”............✍️

Hhuummmm!
Received at 12:22 PM
[16/02, 10:59 pm] null: KIƊA A RUWA 3

15

.........Ya gamsu da shawarar Mammah kam. Dan haka yace, “Hakan yayi sosai. In sha ALLAHU zan duba naga yiwuwar komai Mammah.”
“To ALLAH yay muku albarka. Ka sanar ma Jamilu ne?”.
“Eh, in sha ALLAHU. Yace ma yana tafe ranar juma'a. Sai dai Uncle Naseer zuwa gobe in sha ALLAHU zanje shima muyi maganar. Sai waɗan nan yaran, su basa komai ne a gidansu suka zo nan suka tare?”.
Ta san su Hanoon yake magana. Dan haka tai murmurshi. “To ban sani ba Muhammad. Amma dai nayi waya da Tasi'un ya tabbatar min sati mai zuwa shima zai dawo ƙasar. Amma ina son ka zauna dasu ko sau ɗaya ne ka tsawatar musu akan wasu ɗabi'u nasu marasa ƙyau kodan a taimaki rayuwarsu.”
“Hummm Mammah, nifa akan abinda na isa kawai nake tsawa. Ki bar masa ƴaƴansa a yanda kika gansu yazo ya kwashe abinsa. Ai ya fiki sanin ba'a dai-dai suke ba. Amma ya zaɓi barinsu a haka. Yanzu dai kwanta ki huta. Nima zanje barci nake ji sosai.”
Sarai ta fahimci dan ya kaucewa maganar ne kawai. Dan haka ta ɗan murmusa tana girgiza kanta. Har yay mata sallama ya fice tana binsa da kallo....

Koda ya maida ƙofar ya rufe dole ya ciro wayarsa ya kunna fitila dan an kashe hasken falon gaba ɗaya. Takunsa bai wuce biyar ba yaja ya tsaya gab da fara hawa staircase saboda kamar nishin kuka yake ji. Duk da anayi ne ciki-ciki ƙarfin ji da ALLAH ya bashi ya saka shi ji, ga kuma darene ko ina yay tsitt. Juyawa yay saitin inda yake jiyo sautin. Tabbas a kitchen ne, dan haka ya zubama ƙofar shiga idanunsa tsahon sakanni. Kafin ya ɗaga ƙafafunsa ya nufi wajen cike da takunsa na jarumta da lafiyar jiki irin ta baraden maza masu tsayin gaɓɓai. Hasken wayar ya ɗan rufe da hannu, kafin ya tura ƙofar kitchen ɗin....
Yanda ya shigo a bazata, tare da haska kitchen ɗin da fitilar wayarsa a lokaci ɗaya ya saka Nimrah zabura. Dan zaune take a ƙasa cikin ɗan lungun jikin cabinet, ta saka kanta a tsakiyar ƙafafunta. Fitilar kitchen ɗin ya kunna, ganin wanene ya shigo ya sata miƙewa tsaye gaba ɗaya jikinta na tsuma.
Dada kam idanu ya zuba mata kawai yana kallonta daga sama har ƙasa. Kayan barci ne wando da riga masu taushi a jikinsa. Wandon har ƙasa, sai rigar mai gajeren hannu iya gwiwa. Kanta da hula, sannan ƙafarta da bedroom slippers masu taushi. Tunda tai masa kallo ɗaya ta duƙar da kai bata sake ɗagowa ba. Tana ta dai cuɗa hannun nata cikin juna yanda aka saba....
“Ki dafa lemon tea ki kawo min”.
Ya faɗa kawai yana juyawa abinsa ya fita. Sharr hawaye suka sake zubo mata. Takai hannu ta share tana jan hanci. Batare da tace komai ba ta nufi inda tea pot ɗinsu suke ta ɗauka ɗaya ƙarama. Fanfo taje ta ɗauraye sannan ta saka ruwa dai-dai misali ta nufi gas. Ta ajiye tukunyar tana sake share hawayen da suka ƙi tsaya mata da shashshekar kuka. Abubuwane sun mata yawa a cikin ƙirji, musamman wanda ta gano a wajen mutanen can da wanda aka sanar mata game da zuri'arta da shi kansa Dadan da ƴan uwanta data gani jininta a karo na farko a rayuwarta, bayan labarin mahaifiyarta data rasu babu labarin wanda ta taɓa sani a danginta sai yanzu. Addu'ar da take ta ambato ce kawai ke saka mata nutsuwa da babu abinda zai hanata haukacewa a wannan gaɓar. Lemon tsamin data ɗauka babbar guda biyu ta wanke, tare da ganyen na'a-na'a da lemon grass ta koma wajen tukunyar ta zuba. Lemon tsamin kuma ta yanka ɗaya a ciki, ɗaya a cikin flaks data ɗakko shima....

Dada da yay ɗan jimm a bakin ƙofar kitchen ɗin yana kallo tamkar yana hangota jin ta fara kai-kawon aikin daya sakata, amma tana cigaba da shashshekar kuka sai ya furzar da iskar bakinsa kaɗan yana barin wajen. Sama ya haura abinsa. Sai dai bai wuce ɗaki ba sai da ya leƙa ɗakin su Mu'azz dana su Bilal ya tabbatar sun kwanta, sai Afeef ne ma ke latse-latsen waya, yana jin kuma za'a buɗe ƙofar ya kifeta shima yaja bargo yay likimo. Dan ya tabbatar Dada ɗin ne saboda duk dare haka yake musu..
Received at 12:22 PM Ɗakin sa ya wuce. Bayan ya zube wayoyinsa a saman mirror ya shiga kunce agogon hannunsa. Dai-dai nan Nimrah tai knocking.
“Shigo”.
Ya faɗa a taƙaice. Koda ta turo ƙofar ta shigo da sallama ƙasan maƙoshi saboda muryarta ta ma dishe, bai juyo ya kalleta ba amma ya amsa a lips. Hanyar bayi ya nufa yana rage botiran shirt ɗinsa da faɗin, “Ki jira ni anan” daga haka ya shige ya barta da bugun zuciya da kallon ƙofar bayin. Bata da zaɓin daya wuce bin umarninsa. Dan haka takai zaune a ƙasan carpet tana ɗan wasa da lallausan gashin jikinsa. Sai dai lokaci-lokaci tana share hawayen dake ciko mata idanu amma taƙi bari su zubo...

Ya ɗan jima kafin ya fito, sai dai kayan barci ne yanzu a jikinsa saɓanin kayan daya shiga da su. Tunda tai masa kallo ɗaya ta maida kanta ta duƙar. Shi kam baima kalla inda taken ba kai tsaye gaban mirror ya nufa yana ƙara tsane gashin fuskarsa da ƙaramin towel. Ya ɗan ja mintuna a wajen, dan sai da ya saka turare a jikinsa ya kammala uzirinsa kafin ya nufi gado abinsa. Ɗago kai Nimrah tai a karo na biyu tana kallonsa, a tunaninta koya manta da ita ne, ganin ya hau gadon sosai ya zauna, sai dai ya jingina bayansa da fuskarsa yaja bargo ya rufama ƙafafunsa zuwa ƙungunsa, ya kuma kashe hasken fitilar ɗakin gaba ɗaya sai lamp itama ta side ɗin da yake zaune kawai.
“Bani”.
Ya faɗa a taƙaice yana buɗe laptop daya ɗora saman cinyarsa bayan yasa ƙaramin filo. Shiru Nimrah bata motsa ba, dan batama fahimci da ita yake ba. Sai da ya ɗago ya kalla inda take, tare da faɗin, “Wai bada Nimrah nake ba”.
Ƙirjinta taji ya buga, dan bayan a jeji data gudu sanda bomb zai tashi bata taɓa jin ya kira sunanta ba. Miƙewa tai gaba ɗaya ta ɗauki tray ɗin data saka ƙaramin flaks da tea cups guda biyu, sai tea spoons suma biyu da zuma cikin ɗan wani gora mai ƙyau alamar a haka aka sayeshi. A ƙasan carpet ɗin gaban gadon ta ajiye, daga tsugunne ta haɗa masa komai. Saman bed side drawer tai nufin ajiyewa sai ya miƙa mata hannu batare daya bar abinda yake a laptop ba. Hannun ta kalla, sannan ta ɗan kalla fuskarsa dake ciɗin-ciɗin kamar koyau she. Dole ta matsa sosai inda yake sannan ta miƙa masa. Maimakon amsa da ɗan plate ɗin da kofin ke a kai sai kawai ya kama hannun cup ɗin, ita kuma da ba haka tai zato ba sai taji kamar ya tafi zai ɓare ne, caraf ta kama hannunsa cikin nata hannun.
Idanunsa dake kan screen ɗin yaɗan lumshe tare da buɗewa a lokaci guda kan hannayen nasu. Da sauri ta janye nata tsigar jikinta na tashi batare data san dalili ba. Shima sai bai ce komai ba, ya dai kalleta shaaa ya ɗauke idanunsa. Daga haka ya fara shan shayin yana aikinsa. Ganin lokaci na ƙara jaa yaƙi cewa kuma ta tafi cikin rawar murya ta ce, “Dada na tafi?”.
Shiru bashi da niyyar amsata, bai kuma daina aikinsa ba balle shan shayinsa da yake matuƙar jin daɗinsa. Sai yaji tama fi Ammar iya dafawa. Dan kullum shi yake sakawa ya dafa masa. Ammar daya fahimta ma ko bai buƙata ba sai ya dafa ya kawo ya ajiye a ɗakin in ma baya gidan. Yau ma gaba ɗaya ya shafa'a ne saboda kasancewar su Aunty Mimi a gidan.
“Tashi ki dawo sama”.
Furucin yazo mata a bazata daga bakin wanda bazata iyama jayayya ba. Gadon ta kalla sannan ta kallesa, ganin har yanzu hankalinsa akan aikinsa yake sai taji kamar ta saki kukan da take ta faman dannewa. Bata da zaɓin daya wuce bin umarninsa, dan haka ta miƙe kanta a ƙasa ta ɗofanu acan ƙarshen ƙafafunsa dake cikin bargo. Sai da taja kusan mintina biyu kafin ya ɗago ya kalleta, kallo irin na tsaiii ɗin nan akan mutum dake sakashi yaji rikicewa, sai dai babu damar yin motsi balle yin magana dan anfi ƙarfinka.
“Mike damun ki?”.
Ya faɗa kai tsaye idanun nasa dai a kanta ƙyam. Jitai ta sake daburcewa, dan ta tabbatar dai amsar yake buƙata daga gareta kuma dole ta bashi. Cikin rawar lips da in-inar da yanzu tazo mata ta buɗe bakin zata fara magana...
Received at 12:22 PM “Kar kimin ƙarya”.
Ya katse hanzarinta cikin gizago. Sai kawai taji hawaye sun ciko mata idanu. Lips ɗinta sai rawa suke kuma. Idanunta ta ɗan ɗago kaɗan da nufin satar kallonsa sai taga nashi har yanzu ƙyam a kanta. Da gudu ta risinar da nata. Sai ga hawaye sharrr da take faman riƙewa sun ɓalle. Fuskarsa ya kauda gefe yana furzar da iska. Sai kuma ya janye laptop ɗin gefe, tare da ajiye kofin shayin da har ya shanye a bed side drawer ya miƙa mata hannu.
“Zo nan”.
Kamar dama abinda take jira kenan ta miƙe, gabansa tazo zata durƙusa daga ƙasa ya hana hakan ta hanyar riƙo hannun nata. A bakin gadon ya zaunar da ita tana facing ɗinsa, har jikinta na gogar nashi duk da shi a rufe yake da bargo. Dan haka ta ƙara duƙar da kai sosai..........✍️
Received at 12:22 PM
Viewed 2 times
[16/02, 10:59 pm] null: KIƊA A RUWA 3

16

..........“Yaushe kika zama sha-sha-sha ne da komai kuka-kuka?”.
Yanda yay maganar can ƙasan maƙoshi, da sigar lallashi yana ɗan matsa hannunta dake cikin nashi har yanzu ya sata ɗan jin sassauci. Cikin muryarta dake a ɗashe ta ce, “Dada ina son na Mutu ne?”.
Idanu ya zuba mata sosai, sai kuma ya ɗan motsa lips kaɗan ya ce, “Mutuwa? To idan kika mutu wazai haifa ƴaƴan soja Kiddo?”.
Da sauri ta ɗago tana kallonsa, duk da bawani ta gane zancen nasa ina ya dosa bane ba. Kai ya ɗan jinjina mata alamar tabbatarwa. Ita kuma sai kawai ta tura baki tana janye idanunta daga cikin nashi.
Mitsitsin murmurshin da bai shirya bane ya kufce masa. Sai dai bai bari ta gani ba ya gimtse abinsa. Gyaran murya ya ɗanyi, hakan ya sata sake ɗagowa, sai dai bata yarda sun haɗa idanu ba. Cikin son kamata a wuya ya canja salon sigar tambayar tasa. Dan ya fahimci ɗaya daga halayenta shine kafiya, dagiya akan abu. Idan ba ita taso ba akwai taurin kai. Sannan ya fahimci depression ne ke neman kamata.
“Miyasa kika daina raba damuwarki da ƴar uwarki, aminiyarki? Bayan kuma sanda na dawo ba haka naga kuna yi ba. Kin fara ɓoye mata abubuwa ne?”.
Kanta ta girgiza masa da sauri.
“Magana nake so da baki”.
“Bana ɓoye mata komai. Kawai dai yau ne naji ina son na dawo kitchen ɗin nayi kukan”.
“Ko kuma kiyi mutuwar da kike so ba”.
Shiru tai dan bata da abin faɗa. Kamar ma ya shiga ya karanta abinda ke zuciyarta ne. Shima fahimtar hakan ya sashi cigaba da faɗin, “Shike nan tunda baƙya son Ruƙayya tasan damuwarki itama ta damu. Ni kiyi abota da ni mana. Kinga tunda na riga na ganoki sai mu dinga tattauna matsalar a tare ko? Hakan bazai sa Ruƙayya taji ba balle hankalinta ya tashi kamar yanda baƙya so”.
“Ai Mammah tace babu ƙyau abota tsakanin namiji da mace”.
(Wata sabuwa) Ya faɗa a zuciya. A zahiri kam sai ya ce, “Haka ne gaskiya Mammah ta faɗa. To amma ai ni ne, Mammah bazata hana ba. Bakiga itama da ni take shawara ba. Amma tunda baƙya sona da abokin ai shike nan. Zan nema Ruƙayya mu ƙulla, kar kuma kiga mun ware ki kiji haushi. Dan zanyi duk yanda zan yi na ƙwace miki ƙawa”.


Please Login or Register in order to submit comment