You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

antayo ashariya mai kawuna bakwai ta dire. Balbale Lulu tai da masifa irin wadda bata taɓa mata ba, tare da tambayoyi masu tsaurin gaske da suka saka Lulun ɗan jin nauyi harta gagara cewa komai. Sai da taga ta takura mata tace faɗuwa tayi. Hakan ya ƙara harzuƙa Dada ta fisgeta suka fita, sai dai zafin da take ɗan ji ya sata tirjewa dole Dada ta kamata suka fita cikin lallaɓawa. Anan ne makwafcinsu ya gansu, sai dai ita Lulu bama tasan maƙwafcin nasu bane ba. Lulu ta roƙi Dada suje Court akan case ɗin yarinyar nan da take so a ƙarƙare a yau, inda suka samu alƙali suka juye masa kuɗaɗe akan ya cigaba da riƙe mata mutumin a gidan yari zata bar ƙasar dan bata da lafiya. Da ga court hanyar airport suka ɗauka, suna isa basufi minti arba'in da biyar ba jirgin zuwa Abuja ya shirya tashi, dama Dada tasa a tanada mata ticket tun barowarsu gida. Ita kaɗai ta wuce Abuja Dada ta koma gida. Maimakon gidan Uncle ɗinta Khamil wata mata ce tazo ta tareta, tasan matar tare da Dada da daɗewa, suna kiranta Hajiya Shuwa. A ranar gaba ɗaya ta yini kwance ne da zazzaɓi a gidan Hajiya Shuwa, hakama washe gari dai duk gata nan ne dai babu isashen lafiya tare da ita. A kwana na uku Dada tai kiranta a waya ta tsara mata zance cewar ai Aliyu na nan nata zaginta da cewar wai ta tafi yawon banza ne, dan haka sun saka ƴan sanda sun kamashi a yanzu haka ma kotu zasu kaisa ya bata takardar sakinta. Ran Lulu ya ɓaci matuƙa dajin wai Smart na zaginta har da dangantata da karuwa, dan haka tacema Dada tana son ƴan sandan nan su ƙara wajiga rayuwasa kuma ya saketa. Kwana biyu bayannan da ke zama biyar da barowarta Dada ta kirata nan ma ta sanar mata Aliyu wai ya saketa. Duk da abinda take fata ke nan sai taji wani iri, daga ƙarshe ma ranar yini tai babu lafiya zuciyarta a cunkushe. A ranar ta sanarma Dada tana so tabar Nigeria zuwa America, amma sai Dadan ta bata shawarar taje gidanta na Canada tunda babu wanda yasan da shi, dan Uncle Yousuf yay ikirarin ɗaukarta da kansa ya maida gidan Aliyu ko tana suma tana mutuwa ne. Ran Lulu ya sake ɓaci, ta kuma sake jin ƙwarin gwiwar nisantar ahalinta baki ɗaya. Wannan shine dalilin tahowarta Canada tare da mai aikin da aka haɗota da ita mai suna Ummita. Sai dai tunda sukazo zuciyarta taƙi nutsuwa waje ɗaya, abubuwa da yawa tsakaninta da Smart a ɗan zamansu sun zame mata barazana a barci da ido biyu, wannan ya sata sake buɗe babin shaye-shayen ta sosai-sosai. Ko abinci bai dameta ba da ga shaye-shaye sai barci. A kwanakin da bazasu wuce sati biyun nan ba ne abubuwa suka fara canjawa, idan tasha kayan shaye-shayen ta tana kammalawa zatai amansu, tun tana ɗaukar al'amarin wasa har takai bata son warin kowane irin ƙwayar magani, amma cikin ƙarfin hali take daurewa ta sake gwada sha, ta kuma sake aman nasu. Wannan dalilin ya sata ɗaga ƙafa kwana biyu, sai kuma hankalinta ya fara dawowa jikinta har salla da lokaci yayi kamar wadda aka zabura sai ta tashi tayi. Kwana uku da suka wuce kuma sai zazzaɓi ciwon kai da kasala, ga yawan mafarkin Aliyu kamar wani magic a gareta. Sai duk randa tai mafarkin nashi takan tashi da ɓacin rai har taji buƙatar shan kayanta ko zata manta da shi. Sai kuma dai ta daure taƙi sha dan ko tunawa tai da su sai taji amai. Yau kuwa wayar gari tai cikin wata irin damuwa da kewar wani abu data kasa canka a ranta, sai zuciyarta daketa faman ƙuntata, cikin son kauda yanayin ne ta samu ƙwaya tasha amma ta rantse bata zama a cikinta shine take amayar da ita a yanzu).........✍️

Wannan kenan.

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣



.......Dole da taimakon Ummita mai aikin nata ta gyara jikinta ta kamota ta fito da ita bedroom. Cikin wando dogo da sweater ta shirya tare da Safa mai kauri sosai, ta haye gadon cikin rawar ɗari taja bargo har saman kanta. Tare da bama Ummita umarnin ƙara mata gudun room hitter ɗin ɗakin. Dan wani irin rawar sanyi take har haƙoranta na haɗuwa waje guda. Ga hawaye sun gagara tsayawa (yau fa an taɓo manyan mata🤣🙏).

Yanayin da Lulu ke ciki ya tada hankalin Ummita, number da suke waya da Dada jefi-jefi ta lalubo ta kira, kamar baza'a ɗagaba ma sai kuma aka ɗaga, cikin ladabi Ummita tai sallama da gaida Dada, daga can ta amsa a gadarance da tambayar ina Lulu. Cike da damuwa Ummita ta sanar mata gata kwance babu lafiya, dama kusan kwanakin nan haka take ganinta sama-sama, sai dai rashin tabbatarwa yasa bata faɗa mata ba sai yau. Rai a ɓace Dada ta shiga zagin Ummita ɗin, duk ta rikice dan tana bala'in son Lulu, zamu iya cewa soyayyar mahaifiyarta ce ta dawo kanta. Ita dai Ummita haƙuri kawai take bama Dada kawai. Dan ta tabbatar masifar tsohuwar original ce.

Ba'a rufa mintina goma da katse wayar Dada ba alerm ɗin gidan ya kaɗa, miƙewa Ummita da ke falo tai ta nufi ƙofar, bata buɗe ba kai tsaye ba, ta danna numbers dake jikin ƴar computer ɗin kusa da ƙofar dake manne a bango dan ganin wanene. Baturiyar mace ce tsaye, cikin nuna alamar tana ganin Ummitan da ga wajen itama ta ce, “Hy” cikin ɗaga hannu. Amsa mata Ummita tai itama da “Hy” ɗin. Cikin murmushi matar ta cigaba da magana cikin harshen nasara. “Sunana Doctor Olivia, Nazo nan ne bisa umarnin Mrs Garko”. Yanda ta kira kalmar Garko ɗin taso bama Ummita dariya, amma ta dake da ƙyar sai murmushi da tai mata tare da ɓuɗe ƙofar. Sun sake gaisawa da Dr Olivia, Sannan tai mata rakkiya ɗakin da Lulu ke kwance.

Ganin yanda jikin Lulu yay zafi sosai yasa Dr Olivia cewa dole suje asibiti, a take tai kiran ambulance cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gasu. Lulu na rawar sanyi da faɗin su barta ita bazataje ko ina ba su Dr Olivia suka ɗauketa a ambulance ɗin tare da Ummita suka wuce. Suna zuwa babu ɓata lokaci aka shiga da Lulu ciki tare da rufuwa bata gudunmawar gaggawa.

*_UK_*

Hankalin Dada da ke jiyyar mijinta ya tashi sosai, amma tanata ƙoƙarin dakewa dan kar Alhaji Garko da ya fara samun sauƙin jikinsa Alhmdllh ya fahimta tare da sauran yaransu da sukan zo dubashi. Idan wannan tawaga ta wuce sai wata kuma tazo, abinka da masu hannu da shuni, kallon fita ƙasar ake kamar barin Kano a shiga Katsina ne. Alhaji Garko da bai san halin da ake ciki ba har yanzu dan babu wanda ya sanar masa saboda halin da yake ciki ya zubama matar tasa ido cikin tausayawa, dan shi ya fassara yanayin nata ne da gajiyawa musamman da yake akwai tsufa. Cike da kulawa ya ce, “Hajarah kina buƙatar hutu, ya kamata kije gida haka nan tunda jikina da sauƙi nima, har ma muna sa ran sallama nan da ƙarshen watannan”.

“Haba dai Alhaji ya hankalina zai kwanta kana nan ina can, duk da dai jikinka Alhmdllh amma har yanzu kana buƙatar kulawa. Danni ko sallamarka sukayi bana son ka koma gida Nigeria yanzu har sai ka sake hutawa anan magana ta gaskiya.”

Murmushi yay irin nasu na manya da faɗin, “Hajarah rigima kenan. Yanzu ni da abubuwa ke jirana tari-tari tunda ALLAH yasa da sauran kwanana a gaba mizai sa na kuma sake sabon zama anan ai gara na koma gida ko?”.

“Humm Alhaji wlhy wannan gaskiya ce ba rigima ba. Gara dai ka sake hutawa dan muna komawa can hayaniya ma ta isheka musamman ta ƴan siyasar nan da ba gajiya suke ba. Dan haka dan ALLAH ka yarda kawai sai ka sake hutawa, nima yanzu inaga maimakon tafiya Nigeria bari na ɗan je Canada na huta na kwana biyu kafin a sallamekan ko.”

Ɗan jimm yay na alamar tunani, sai kuma cikin nuna fahimta ya ce, “Shike nan idan hakan kike so uwar garke na. Yanzu yaushe zaki wuce Canadan?”.

“Eh to ko zuwa yamma haka tunda ga su Khamil da iyalansa nan sun iso ko, auta ma yace min zai baro Saudiyya shi da matarsa gobe in sha ALLAH. Kaga dai ai ka sake samun masu kulawa”.

Murmushi yay mata cikin nuna gamsuwa. Dan Dada kam a wajen bama miji kulawa jaruma ce, tsaye take kan abinta ta kankane ko ina tunda ƙuruciya har girma babu wata mace data taɓa raɓar mata miji da sunan kishi. Wannan tsananin kishin nata yasa hatta matan ƴaƴanta take jin kishinsu akan ƴaƴan nata da suma take matuƙar so da ƙauna tamkar ubansu. Babu ɓata lokaci ta hau shirin wucewa Canada, dan ji take kamar ta rufe ido ta isa taga hanlin da ƴar jikarta take a ciki, saboda a nata bahagon tunani babu abinda zuciyarta ke raya mata sai kodai Smart, ko Uncle Yousuf wani ya sakema Mawaddat asiri ne.

Dai-dai lokacin da Lulu ke cika awanni goma sha ɗaya a asibitin su Dr Olivia Dada ke isowa ƙasar ta Canada. Tunda ƙuruciya an riga da an san lungu da saƙo na ko'ina, dan a duk ƙasar da suke yawan zama suna da gidansu na kansu musamman manyan ƙasashen nan masu ji da kansu irinsu England, America, France Chaina, Saudiyya, Dubai, dan da gasken gaske wannan family sunada dukiya, bayan wadda mahaifinsu ya gada a wajen nasa mahaifin ya kuma tara nasa na kansa, su kansu yaran kowanne ba ƙyalan bane wajen kuɗin, dan babu wanda ke zaune kaf ɗinsu a neman na kansu suke. Ko marigayiya Mawaddat mahaifiyar Lulu data kasance mace ɗaya tilo a cikinsu sanda tana raye tsaye take akan neman na kanta saboda haka aka gina musu rayuwa, duk da yana da dukiya kuma ya gada ne shima a wajen mahaifinsa bai yarda yaransa su zama cima zaune ba, suna ayyuka a cikin gwamnatin ƙasarsu da na wasu ƙasashe, suna kuma Business ƴaƴa da iyaye har ma da jikoki. Cab ta ɗauka tun daga airport zuwa asibiti kai tsaye, dan a ƙage take da son ganin halin da jikar tata ke ciki. Wadda har yanzu ana kan tafka rigima akan ɓoyetan da tai dan bayan ita sai Alh. Sulaiman kawai suka san ina Lulun take. Hatta da Tajuddeen sunƙi sanar masa. Ita Dada zuciyarta ɗaya ce game da ɓoye Mawaddat dan kawai ta rabata da Smart ne matsayinsa na talaka jikanta Tajuddeen ya samu. Yayinda shi Alh. Sulaiman ba haka kawai bane a tashi zuciyar, dan a yanzu haka bai fara aiwatar da plan ɗinsa bane akan Lulun sakamakon rasa inda Smart yake da yay shi kuma. Dan tun washe garin da Smart ya baro 9ja yasa malami binciko masa shi amma ƙasa ko sama babu labarinsa. Amsa ɗaya suke samu a bincikensu shine ya ɓoye kansa dan kar ya saki Lulu. Duk da dai suna zargi Uncle Yousuf ne ya ɓoyesa amma a ɗan tsukunnan sun ƙara tsananta bincike kasancewar har yanzu basu sami wani point ba akan hakan. Dan shi Uncle Yousuf ɗin ma ya sake baro Nigeria ɗin zuwa harkokinsa da ya bari bayan yayma Daddy tas da tabbatar masa da cewar ya zare hannunsa akan al'amarin Lulu, dan ya fahimci goyon bayan da Daddyn ke batane a baya ya bata lasisin biyema Dada tabar gidan aurenta. Saboda ya tabbar da babu haɗin kan Lulu Dada bazata taɓa iya ɗauketa a gidan aurenta ba harta ɓoyeta gashi ana neman wata uku kamar wasa.

*_NIGERIA_*

Sosai Daddy yana cikin wani hali na azabtuwar zuciya game da abubuwa da yawa. Na farko shine ɗan uwansa dake fushi da shi. Ƙaunar da yakema Yousuf a zuciyarsa daban ce a wannan duniyar, dan zai iya rantsuwa ko ƴaƴansa baya musu irin wannan ƙaunar har Lulun da ake kallo ya fifita. Na biyu rashin sanin inda Lulu take har yanzu, tun yana ɗaukar al'amarin wasa Dada zata dawo da ita bayan wasu kwanaki har lamarin ya fara bashi tsoro. Lokacin da yaje UK duba Baba Garko har roƙonta yay akan tayi haƙuri Lulu ta koma gida koda bazata koma gidan mijin ba, dan tabar aikinta da mutane ke matuƙar buƙatarta. Amma sai Dada ta murje idanu tai masa tas dole yaja bakinsa yay shiru dan yana ɗaga mata ƙafa kodan darajar sunan uwa da take amsawa. Sannan fa Daddy dama can Uncle Yousuf ya fishi zafi, shi dai barsa da zuciyar tsiya kamar ɗan kuturu. Abu na uku wani salon rainin wayo da Alh. Sulaiman ya ɗan fara kawo masa da nuna shi yanzu a shirye yake da shi akan komai, sai zuciyarsa ta fara bashi anya kuwa bada haɗin kan Alh. Sulaiman ɗin Dada ta ɗauke Lulu ba kamar yanda yay zargi tun farko. Idan ko haka ne to tabbas a wannan karon ya shirya duk wacce ma za'ai ayi shima. Wannan tunanin ne ya zaburar da shi yau daga gida daya fito yace driver ya wuce da shi office ɗin Alh. Sulaiman Sufi Garko. Sanda suka iso ma shi bai kai ga isowar ba, dan haka sukai zaman jiransa. Baifi mintina bakwai ba a tsakani sai gashi shima. Sai da ya shiga da kusan mintina huɗu drivern Daddy ya shiga ya nema musu iso. Alh. Sulaiman da tun shigowar Daddy cikin Companyn aka sanar masa, yana shigowa kuma ya shaida motarsa yay wata dariyar mugunta da bama sakatariyarsa umarnin shigo da shi.

Tunda Daddy ya shigo Alh. Sulaiman da yay wata kishingiɗar iskanci a kujera yana jujjuya kansa ya saki murmushi mai ma'anoni da yawa. Yi Daddy yay kamar bai gansa ba, sai ma ya kai zaune duk da ba'a bashi damar hakan ba. “Ina fatan kana lafiya?”. Daddy ya faɗa a takaice. A gatsine Alh. Sulaiman ya amsa masa da “A office ka sameni ai ba'a gadon asibiti ba”.

“Kuma haka” cewar Daddy a gatsine shima. Batare da ya jira cewar Alh. Sulaiman ɗin ba ya cigaba da faɗin, “Sulaiman ina kuka kai min yarinyata?”.

“Ka shirya ganinta yanzu kenan?”.

Idanu Daddy ya tsurama Alh. Sulaiman cikin ɓacin rai, sai dai kafin yace wani abu Alh. Sulaiman ɗin ya ƙyalƙyale da wata dariyar mugunta yana miƙewa tsaye. Takowa yay inda Daddy yake ya ja kujerar dake kallon wadda yake zaune shima ya zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya. Fuska ya tsuke ya zubama Daddy dake kallonsa cike da tsana idanunsa shima. “Isma'il Ibrahim Jiƙamshi! A da kana ɗaukar duk zantukana matsayin kurari ko? Kana tunanin bazan iya illata rayuwar Mawaddat ba dan kawai tana ɗiyar ƙanwata?. To kayi kuskuren sanin waye ni, dan zamanka da ni na tsawon shekaru bakwai bai maka amfanin komai ba kuwa. Bari kaji wlhy wlhy da ace na san da wannan sirrin a hannun Mawaddat ƙanwata kafin mutuwarta, ni da hannuna zan kasheta bayan na amsa, sai ALLAH ya taimaketa ta mutu a karan kanta kafin na sani ɗin, amma duk da haka bata tsiraba ta barma ƴarta gadon laifinta. Dan haka Isma'il ina maka gargaɗi na ƙarshe, ka bani camara ɗin nan, ka kuma saka a ranka baka taɓa sanina ba har abada, in ba hakaba, a wannan karon saina wargaza rayuwar kaf family ɗinka bata Mawaddat kawai ba. Dan haka zaɓi ya rage naka....”

Murmushi Daddy yay mai ma'anoni da yawa duk da yasan duk abinda Alh. Sulaiman ɗin ya faɗa zai aikata fiye da hakan. Amma cikin nuna halin ko in kula idonsa akansa kyam ya ce, “Sulaiman kenan. Ka manta ni Isma'il ɗin wanene nima. Sannan banda haukarka a tunaninka baka camara na nufin gogewar abinda ka tafka da in kaf family naka sukaji sai sun maka tsanar da sai ka gwammaci mutuwa da rayuwa. To idan ka manta bari na tuna maka, bayan abinda Mawaddat ta ɗauka nima ai nasan komai, ko toshewar basirar taka takai ka manta cewar komai na sani tunda da bakinka ka kirani ka sanarmin abinda kayi kuma na gani da idona, hasalima tare dani ka ɗauki yarinyar ka kai ƙasan gotter ka jefar. ai ba abinda Mawaddat ta ɗauka bane kawai hujjar. Sannan na biyu Sulaiman kada ka manta a tafin hannuna kuke kai da su Alh. Baita, idan yanzu na sanarma duniya su waye ku a ƙasar nan wlhy wlhy ba dukiya ko matsayi ba sai anyi faca-faca da namanku da taimakon mahaifinka dan kafi kowa sanin irin tsanar da yay ma abinda kuke aikatawar. Ai dama na sanar maka tun a waccan ranar, sai na ɗan ɗana ma zuciyarka rayuwa cikin fargaba da zullumi fiye da yanda ƙanwarka ta ɗanɗana min a tsahon shekara ɗaya dana rayu da ita.....”

“Nima ai na tabbatar maka sai dai mu rayu a tare cikin zullumin da fargabar ko ka manta”. Alh. Sulaiman ya faɗa a zafafe cikin katse Daddy. Sai kuma ya ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “Isma'il kenan a tunaninka kaima ban san a yanda ka rayun bane, ko cakake ban san kaima kana rayuwa bane cikin irin yanda kake tunanin ka sani a tsahon waɗan nan shekarun. Ka gaya min inba tsoro ba miyyasa ka ɗauke ƴarka daga Nigeria da ga randa na tabbatar maka saina hukunta rayuwarta bisa laifin mahaifiyarta? Miyasa kaketa kaffa-kaffa da ita fiye da sauran ƴaƴanka?. Amsar itace Tsoro ne! Kana jin tsorona Isma'il!! Hhhhh tabbas wannan tsorone!!”.

Da ƙarfi Daddy ya buga decks tare da miƙewa a zafafe.........✍️

Tofa fagen na manya ne yau🚴🚴🚴

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣



.......“Kai ɗin banza da zanji tsoronka Sulaiman. Ka sannni kaima ai, ni na wuce maka kanwar lasa, sannan ni ƙadangaren bakin tulune a rayuwarka data abokanka ta yanda kuka rasa yanda zakuyi dani. Ƙarshen target ɗinku shine ku kasheni dai, kuma na tabbatar muku a randa kuka kasheni wlhy ko minti ɗaya bazan cika ba da ɗaukewar numfashi kuma duniya zatai muku zafin da sai kun gwammace mutuwa kamar ni, dan sai mutanen duniyar sun san suwaye ku. Idan ba tsoro kuke ji ba miyya hanaku aikatawar a tsahon shekarun nan. Miyasa kuka kasa bayan kunada kowacce irin dama? Miyasa baku aikata bane sulaiman? Ku kashenin mana? Maza ku kashenin idan kun cika ku tsagerane dan ALLAH!!”.
      Matuƙar razana Alh. Sulaiman yayi da kalaman Daddy, cikin ɓacin rai da zafafuwar zuciya ya nunashi da yatsa lips ɗinsa na rawa. “Haka kace ko?”.
          “Haka nace Sulaiman, idan kuma bakaji ba na sake maimaita maka. Kuma wlhy na baka daga nan zuwa ƙanƙanin lokaci ɗiyata ta dawo gareni inba hakaba sai na sakaka nadama irin wadda sai ka gammaci mutuwa da rayuwa. Dan duk inda kasa ƙafa ka sani ni Isma'il ƙaddararka biye nake da kai. Plan ɗinku na gaba shine sakama Yousuf cocaine a kaya yayinda da zai baro ƙasar Chaina zuwa Nigeria. Bance ku fasaba dan ALLAH, amma ku sani wannan shine mabuɗin farko na kiran mutuwarku. Ni Isma'il kallon kitse kukema rogo kawai, dan ko poisining ɗin Baba da kukayi na barku ne kawai bisa wani dalilina na tarkon dana ɗanama rayuwarku. FURAR DANƘO NAKE, A SHEKARA ANA DAMU BANI FARAU-FARAU. Mawaddat kuwa bazan sake cemaka ina take ba, in dai har ita ɗin jinina ce da kanta zata maido kanta gida bisa bigiren bijire muku. Ku muje zuwa wasan a yanzu na shirya masa....”
          Har Daddy yabar office ɗin Alh. Sulaiman da yay sumar tsaye bai iya dawowa a hayyacinsa ba. Sai da Daddyn yay banging ƙofar ne ya zabura wata zufa na feso masa a illahirin jikinsa. Bai ma san sanda ya since hular kansa ya hau fifita da ita ba jikinsa ma wata irin rawar shiga ruɗani da tashin hankali. Ji yake kamar mafarki yakeyi, shin Isma'il da ya sani ne haka wai shin ko canja shi ankayina? wagga al'amari haka kamar a mahwalki. Shiy yasan Isma'il nada zuciya kam tabbas batun yanzu ba, amma bai taɓa tabbatar da zai iya wani yunƙuri ba bayan kafiyar daya sanshi da ita kawai musamman da yaga tunda suka fara ƴar tsamar nan Daddyn nayi tamkar yana shakkarsa a koda yaushe, lallai ya yarda bakatsinan mutum abin tsorone yau. Da ƙarfi ya hankaɗa kayan saman table ɗin nasa da nuna ƙofa a kausashe ya furta “Isma'il You really are playing with fire!!!....”

       (😂Daddy ni kaina ka shayar dani mamaki, ashe jinin katsinawan dai na aiki a jininka) 
                

       *_CANADA_*

       Sosai hankalin Dada ya sake tashi ganin yanda Lulun tai wani masifar ɗashewa ta ƙara haske sosai, ga komai nata ya ciko musamman ƙirjinta. Dan ma zazzaɓin daya tasota gaba ya ɗan saka jikin nata girgiza ƙasa kaɗan kwana biyun nan. Tambaya bayan tambaya Dada ta shiga jeroma Dr Olivia akan mike damun jikar tata haka. Kai tsaye Dr Olivia ta sanar mata Lulu na ɗauke da ciki wata uku da kwanaki biyu. Tamkar an fasa irin ƙaton dutsen nan mai girgiza yanki da gidajen wajen gaba ɗaya haka maganar Dr Olivia taima Dada saukar aradu a tsakkiyar ka. Cikin razani da zabura ta maimaita kalmar “Ciki!”  ɗin zuciyarta na bugawa. Dr Olivia ta sake tabbatar mata da hakane. Wata muguwar ashariya Dada ta lailayo ta dire akan Smart. Tare da faɗin, “ALLAH ya tsinema wannan shegen yaro dangin talauci dangin jaraba. Yanzu nan sai da dai ya ɗirka mata ciki. Amma Mawaddat kema ƴar banzar yarinya ce. Randa na ɗakkoki da ga gidan yaron nan har tambaya naita jera miki akan yanayin dana ganki amma kikace min faɗuwa kikayi ashe-ashe miƙa masa jiki kikai ya lalube”. Sai ga hawaye suna cika idon tsohuwar nan dan ɗaurama kai masifa. Kasancewar da Hausa Dada tai maganar duk sai hankalin Dr Olivia ya tashi ta shiga tambayarta ko lafiya. Rai ɓace Dada tace mata ba komai tana zuwa. Cikin rawar jiki ta fito tana neman lambar Alh. Sulaiman ɗanta...

        *_LONDON_*

       Iya ƙoƙari yana yi wajen ganin ya ajiye matsalolinsa gefe ya fuskanci rayuwarsa ta yanzu da cigaban da ya riskeshi. Sai dai hakan ya gagara matuƙa duk da akoda yaushe yay waya da Ammah ko Abbah ko Uncle Yousuf da Coach shawara suke bashi akan ya dai ƙara daurewa. Ammah kan masa nasiha mai ratsa jiki da tabbatar masa in sha ALLAH komai zai zama labari, kuma in har Mawaddat matar da zai rayu da itace duk abinda za'ai sai ta dawo garesa. Wannan ƙwarin gwiwar da mahaifiyarsa ke bashi kan ƙara ƙarfafa masa gwiwa. Sai dai hakan bai hanashi kasancewa cikin mafarkin Lulu ba a duk sanda zai kai kwance da sunan barci. Al'amarin ma har yana neman zame masa jiki akoda yaushe a koda yaushe cikin wanka yake. Ya kasa manta dare mafi daraja da muhimmanci da ya zama wani babban jigo a cikin zamansu na kwanaki ashirin da shidda. Tunashi kansa yay murmushi ko ƙaramar dariya harma da tausayawa. Duk da ashi kansa yasan darene da bazai iya tantance komai yanda ya kamata ba illa dai yasan a shi kansa yasha wahala balle ita. Amma sambatunta ko neman agaji zai ce na wannan dare ya kasa manta komai.
         Yau ma kamar kullum cikin shiri fita wajen training ya fito daga dogon ginin estate ɗin da masaukinsa yake zaune mai hawa kusan ɗari da hamsin, a hawa na tamanin da biyar yake dan haka ya sakko ta lifter har zuwa block A, sanye yake cikin dogon wando na sport da riga mai dogon hannu itama dai irin wandon ce. Sosai ya canja gaba ɗayansa tamkar wanda dama

Please Login or Register in order to submit comment