You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da basu san mike faruwa ba hankalinsu ya tashi. Umma da ke a birkice tunda labarin ganin Lulu yazo musu a kunne faruwar wannan abun ya sakata faɗawa dakinta tana dariya dan daɗi ji take kamar ta ciza uwauwanta. Ana can ana haya-haya na al'amarin tana nan tana kiran Hajiya Naqiba suna kwasar dariya. Sai dai fa batun haihuwar Lulu da sai a yanzu suka sani ya taƙaita musu farin cikin nasu...

      Dole aka koma da Lulu gidan Daddy ita da Babynta hankalin kowa a tashe musamman Ammah da Daddy da Abbah. Dan sun sake tabbatar da lallai akwai matsala. Aunty Bilkisu da aunty Amarya da abu yayma tsaye a rai basuyi ƙasa a gwiwa ba suka ja Ammah gefe game da zargin su akan Umma da abinda ya faru bayan tafiyarsu. Mamakin wannan al'amari ya kashe Ammah tama kasa cewa komai sai kallon su Aunty Bilkisu takeyi. Itako mitaima Umma da zafi haka a gidan nan take mata irin wannan ƙiyayyar, duk da basu tabbatar ita bace dole ko suna so ko basa so tana cikin zarginsu tunda tayi abubuwan zargin ciki harda wanda aka gani da ido. Gwaggo Sa'adah da ranta ya ɓaci ce tace zatayi magana ita kam sai dai ayi duk wacce za'ayi. Da sauri Ammah sarkin dattako ta dakatar da ita da faɗin, “A'a Sa'adah ai magana ba tamu bace yanzun. Domin yinta kamar mun fargar da itane ta sake shiri tunda zuciyarta ta riga ta mutu. Fara magance matsalar ya kamata muyi kafin mu ɗauki mataki. Yaran nan na bani tausayi matuƙa, auren kusan shekara ɗaya amma basu taɓa zaman cikakken wata ba a ƙarƙashin inuwa ɗaya gashi harda rabon haihuwa. Muyi ƙoƙarin ganin al'amarin su ya dai-daita sannan muje mataki na gaba dan ita ba komai bace face baiwa ta ALLAH shine zai mana maganinta ta inda batai zato ba.”
      Badan Gwaggo Sa'adah ta so ba ta haƙura. Amma ta ɗauki alƙawarin sai ta wajiga rayuwar Ummah itama....
 
    A wannan yanayin akai taron suna mai ƙayatarwa, dan a zahiri Lulu normal take tsakaninta da Smart da duk abinda ya shafesa ne aka nisanta su, hatta da ƴan uwansa komai normal. Dan yanda ta dinga haba-haba da su aunty Bilkisu da ma duk wanda ya ɗan uwa na Smart abin zai baka mamaki da birgeka. Bama ita ba, hatta ƴan uwanta babu wanda ya wulaƙanta mata dangin miji. Umma ce ma taso kawo gutsiri-tsoma a wajen da ƴaƴanta akan abinda bai ko taka kara ya karya ba. A take Adda Mairo ta taka mata birki da faɗin, “Sufa basa son fitina da ƙananun magana. Alkairi da farin cikine ya kawosu akan gudan jininsu. Dan haka ta kama kanta gaskiya, tunda iya ƙoƙari mutanen nan sunyi da su a wajen taron nan”. Wannan abu ya ƙonama Umma zuciya dan ba haka taso ba. Bata bari sun taho tare ba tayo gaba, babu wanda yabi takanta sai ƴaƴanta. Dan ko Mama cewa tai wlhy bazatama kanta mugunta ba sai anci komai da ita, duk da acan gida ma da suka baro wani taron za'ai.
       Bayan an gama taron suna da ya girgiza sukatan su Umma da har ta fara tunanin abinda tai ɗin kamar yama warwarene ganin ɓarin kuɗin da Smart yayi, dan hatta anan gidan suma Ammah tayi taron suna sai ma kace anan maijego take, yanda aka yanka rago da sa acan gidan su Lulu anan ma ƙaton sa da ragon aka yanka, a cewar Smart basai sun damu dana can gidan su Lulu ba balle a samu masu ƙananun magana duk da yasan su Lulun bazasu ƙi kawowa ba. Alhmdllh mutanen arziƙi sun taru tako ina fiye da zato da tsammani. Yayinda komai ya tafi cikin farin ciki da bajinta dai-dai misalin da baza'a taɓa kallonsa a almabazaracci ba ko nuna fariyya....

        ________★

  A washe garin gama taron suna Alh. Sulaiman ya iso Nigeria a hargitse. Dan a daren jiya labarin tabbatar da Lulu ta dawo Nigeria ya isa garesa. Kamar yanda mahaifinsa ya saka kuwa hakance ta faru, dan tun a filin jirgi jami'an tsaro sukai ram da shi. Wannan lamari ya girgiza zukatan Garko family sosai dama mutane da yawa da ke da alaƙa da uban da ɗan. Dan basu ɗauka Baba Garko bai haƙura ba tunda an samu Lulu. An saki Tajuddeen da ya share wata biyu a hannun jami'an tsaro yau, Baba Garko kuma yabar ƙasar sabgogin gabansa tamkar ba'ai komai ba. Ƴan ƙananun magana sun fara tashi kaɗan-kaɗan a tsakanin al'umma game da wannan cakwakiya tsakanin ɗa da ubansa. Kowa na faɗin albarkacin bakinsa, tun ƴan jarida nayi a ƙumshe har dai zancen ya fara fita a bayyane. Sai dai kowa da abinda yake faɗa akan al'amarin. Wasu suce sace ƴar ƙanwarsa yay ya ɓoye, wasu suce harda azabtar da ita yay saboda bata auri ɗansa ba. wasu suce aure yaje aka ɗaura mata akan aure da ɗan nasa. Magana dai barkatai gata nan, har abin ya fara shan kan Garko family musamman da sukaji ana neman saka waswasi akan AA wai ba'a ma san ɗan mijin Lulu na farko bane kona Tajuddeen.
       Wannan magana ita ta tayarma da Daddy hankali. Ga Uncle Yousuf na tare da Smart acan England. Smart ne ya kwantar masa da hankali ta waya da tabbatar masa ai dama hakan zata faru dole, amma yayma kowa banza sai sun gama cecekuce ɗin nasu sai su san gaskiya. Abinda ke faruwar a yanzu yana cikin shirinsa akan Sulaiman ɗin. Hankalin Daddy ya ɗan kwanta ya samu nutsuwa. Amma yana mamakin wannan wane irin shirine haka da Smart da atashin farko ya ɗauki hanyar tallata abinda ke a ɓoye bayan da kansa yace yaƙin sunƙuru za'ayi. Koda yake bari ya saka masa ido yaga minene manufarsa. ai karan bana shine maganin zomon bana daman.....


Ana tsaka da wannan dambarwa aka dawo da Dada gida Nigeria. Alhamdullah ta samu sauƙi sosai kamar ba itace aka fita da ita ƙasar raga-raga ba. Sai dai ta dawo ƙasarta da tagwayen al'amura biyu masu gogayya da juna zuwa uku. Na farko shine anga Lulu, sai dai tana baƙin ciki da haihuwarta da ɗan talakan nan dai, amma dai bata yarda ta furta ba gudun karta sake ƙullama kanta tsiya ga Baba Garko da tun a sibiti ƴaƴan keta faman kiransa suna bashi haƙuri ya maidata iddarta saura kwanaki ta cika amma yay biris da su. Abu na biyu shine fitowar Tajuddeen da kama Sulaiman kuma. Wannan al'amari ya sake ɗaga mata hankali. Ta kuma sake tabbatar da Baba Garko a shirye yake da kowa kenan, dan haka ta ƙara kama kanta.
     Da ƙyar ta iya bari gari ya waye tasa Uncle Muneer ya kaita gidan su Lulu. Karo na biyu kenan da zata taka Jiƙamshi House a tsohon rayuwarta. Da ga lokacin rasuwar mahaifiyar Lulu sai yau saboda tsabar ƙiyayyar da takema Daddy a baya, koda yake har yanzu ma bawai ta barsa bane, kawai tana dannewa ne saboda Lulu ta nuna mata bazata ɗauki wannan ba ana zagar mata mahaifi. Duk da kasancewar gidane ginanne a tsaye, a kuma anguwar data amsa sunanta anguwa dan kosu da ke a kusa da gidan gwamna sun san a yanzu hotoro G.R.A ɗin ta basu baya. Amma haka tsohuwar nan ta dinga wani yamutse-yamutsen fuska har abin ya bama Uncle Muneer haushi da tabbatar da Dada fa bazata taɓa ta canja ba sai dai a barta da halinta kawai dan ya riga ya shiga jininta ne. Sun sami tarba tautuntawa da ga Daddy da Mommy. Duk da dai Dada na amsa musu gaisuwa sama-sama basu damu ba. Uncle Muneer ne dai ya ware abinsa sunata shan hira da Daddy cikin mutunta juna kamar yanda suka saba. A haka su Amrah dake maƙale da AA akoda yaushe yanzu, ko makaranta sai anyi jan ido suke wucewa suka fito. Yana goye ne a bayan Afrah yana barci, yayinda Amrah ke jiran time ya cika ta kunto mashi dan dole aka koma sakama kowa lokaci har su Naseer da ake korawa makaranta da ƙyar. Dan yau Suhaib harda kukansa shi sai da AA zai tafi kamar wani ƙaramin yaro. Basu ba dake ƙanana hatta Mubeen wataran faɗa ake da shi akan ɗaukar AA. Hakan na saka Lulu farin ciki da jin ƙaunar ƴan ƙannen nata matuƙa. Su twins kansu kullum sukan kirata sama da sau uku suna tambayar ina son ɗinsu. Hotunansa kam ƙa'ida akai masa wanka sai an tura musu. Ra'is da Deen kam ai sun ma dawo nan gidan saboda AA. Mommy kanta na ƙoƙarin gyara kuskuranta akan AA ɗin, dan itace a tsaye kan kula da Lulu da yaronta duk da Iya Tabawa na iya ƙoƙarinta. Dan ana cewa za'a samo tsohuwar da zata kula da Lulu ta ce ita dai a bata dama ta maida alkairi a wannan karon. Duk da dai a tsorace take saboda sanin halin Lulu ɗin. Amma dai ganin kamar ta ɗanyi sauƙi yanzu yasata cewa a bata dama. Bako a samu wata matsalaba kasancewar a yanzu ma ga Ummita kuma, sannan da gaske al'amuran Lulun sunyi sauƙi kam, duk da idan ƴan masifar na kusa takanyi abinta.........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣2️⃣



.......Sai da Mommy ta harari Afrah sannan ta sakko AA a bayanta ta miƙama Uncle Muneer da yay magana. Dada ko tai muƙuy tana satar kallon yaron. Kamar dai kunya ce ta hanata cewa a kunnto mata shi. Amsarsa Uncle Muneer yay yana murmushi da tsokanarsa irin na wasar jika da Kaka Mommy na kare masa suna dariya. Cikin murmushi ya dubi Dada da faɗin, “Dada gafa baƙon duniya kinyi sabon ɗa”.
     Murmushin yaƙe Dada tayi da faɗin, “Aiko ga shi nan bai baro gida ba, ALLAH yasa iya nan ya tsaya bai ɗakko sauran halayyar ba”. Kowa ya fahimci abinda take nufi, wato kamanin AA da Smart. Amma sai duk suka basar da ita. Ganin bata da niyyar cewa a bata ɗan yasa Uncle Muneer miƙa mata shi. A dai-dai nan Lulu da su Afrah suka kaima labarin zuwan Dadan ta fito. Babu kunya ta zabura gabansu ganin Uncle Muneer na miƙama Dada AA. Cikin sauri take faɗin, “Uncle kai dai ɗauki amma dan ALLAH kada ka bata ta faki idanunku ta kashe min yaro.”
        Babu wanda furucin Lulun bai dakarma zuciya ba. Cikin faɗa Mommy ta ce, “Mawaddat mike damunki? Baki gane wacece bane? Dada ce fa!”.
     Babu alamar damuwa ko sassauci da ga Lulun ta ce, “Mommy sarai na gane wace. Ko a cikin dubun mutane bazata layance min ba ai ba! Dada bace?. Kiyi haƙuri Mommy ki fahimceni, tayaya zan yarda ta ɗaukar min yaro bayan tun yana ciki aka haɗa kai da ita wajen nema ganin bayansa a gaɓar da daga ni har ubansa bamu san da shi ba saboda tsabar zaluncinsu. Dan haka barni da tsohuwar nan ni na dawo a rakkiyarta. Shin mima ya kawoki gidanmu? Keda kike zaginmu kuma kin rantse ƙafarki bazata sake taka cikinsa ba saboda Daddy da Mommy sun zalunce ki?”.
       A daburce Dada ta ce, “Kina da hankali kuwa Mawaddat!?”.
    “Sarai nake Dada, kinfi kowa sanin haka kuma. Ko a lokacin da nake shaye-shaye na san abinda nakeyi balle yanzu da nake a cikin hankalina. Yanzu dan ALLAH bakiji kunyar zuwa wai ganin abinda na haifa ba? Abin bai miki wani banbarakwai ba hakannan? Ai nazata ko'a hanya kika ga jinina dana Aliyu kya gudu dan kunya. Baku so ba ALLAH yayi, Aliyu ɗan Aliyu Mawashi ya tabbatar muku shi ɗan halak ne. Kuma ki sanarma ɗayan Mugun ni da shi wasa yanzu zai fara...”
    Rawa jikin Dada ya farayi kamar mazari. Tuni hawaye sun cika mata idanu, muryarta na rawa ta ce, “Mawaddat ni kike ma irin wannan ɗibar albarkar haka? Saboda namiji? Namijin ma da bai damu da ke ba bai taɓa sonki ba sai da akai masa tallarki da sunan auren yarjejeniya. Kin bar gidansa bai nemi inda kike ba...”
         Cikin ƙyaɓe baki Lulu ta ce, “Wannan gurgun tunaninki ne Dada. Shiyyasa kika zabgan ƙarya Aliyu ya sakan ko kunya baki ji ba saboda kina son na auri shashashan jikanki da baida freedom ɗin kansa sai na ubansa. Yo ai ko maza sun ƙare a duniya gara na mutu babu aure dana auri wannan shakatafin da ko ƙirrar mazan ƙwarai babu a jikinsa soƙai-soƙai kamar wani ɗan talo-talo. Aliyu ya soni ko karya soni wannan ba matsalarki bace ba, jeki fara gyara naki matsalar auren da ya rage saura kwanaki hope ɗinki ya kufce inba haka ba wlhy azumin bana sai mun buga miki gwauruwa tashi gari ya waye....”
        “Mawaddat!!”.
   Daddy ya faɗa da ɗan ƙarfi cikin tsawatarwa. Cikin girmamawa ta ce, “Na'am Daddy”.
      Kansa ya girgiza mata alamar ta bari. Harara ta ballama Dada ta ɗauke kanta. Mommy da Uncle Muneer abin ai ya girmi kansu. Yayinda Dada ta saki kuka tana nuna Lulu. “Ni zaki cima mutunci Mawaddat saboda na zo gidanku ganin ɗanki. Ni kike nunama kin haihu kin san zafin ɗa?”.
        Baki Lulu ta murguɗa mata da taɓe baki. Uncle Muneer ya sauke ajiyar zuciya yana sake gyara zaman AA a cinyarsa da yin gyaran murya ya dubi Dada. “Dada ya isa haka dan ALLAH miye abin wani kuka anan. Mawaddat yarinya ce ai, sannan irin wannan ranar nake gudun mana dama shiyyasa nake nuna miki ki daina biyewa Yaya da al'amarinsa. Yarinyar nan itace dai zata zauna da Tajuddeen, tun farko da aka ƙulla tace muku bata so, amma kika damu kanki, kuma godema ALLAH rabon yaron nan na namiji ne, da mace ne wlhy komai zai iya faruwa ciki harda iya rasa rai....”
         “Yanzu dai Manneeru kana sake goyon bayanta ta cigaba da zagina kenan?”. Dada ta faɗa cikin kuka. Da sauri ya ce, “Sam ba haka nake nufi ba Dada. Taya zan giyama Mawaddat baya ta zageki kuma. Amma kuyi haƙuri. Ina son a gyara kuskuren nan ne saboda gaba. Yanzu badan ALLAH ya taƙaita ba yarinyar nan ta kuɓuta a hannun Yaya mi kike tunanin zai faru? Ko kuma data rasa ranta a wajen yunƙurin zubar mata da ciki. Yaya yayi amfani da ke ya barki a ciki. Sannan da mijin yarinyar nan fitinanne kina ganin zai ƙyaleku ne akan yunƙurin zubar masa da ciki har sau biyu? Ga shi kunje kunce mata mijinta ya saketa! Shin aure kan aure kukai shirin mata komi ma wai shin ni na kasa gane muku?”.
       Tsigil Lulu ta ce, “Abinda suka shirya mun kenan Uncle, kuma wlhy a lokacin na ƙudiri aniyar suna ɗaurashi zan kashe Tajuddeen ɗin ne sai dai nima a kashe ni!”.
     Babu wanda bai kalletaba yanzu ma a razane. Itako hankalinta kwance tama miƙe tana hararar Dada da cigaba da faɗin, “Kuma ko yanzu ba haƙura nayi ba. Dan bana barin bashin gaba. Sulaiman sai yamun bayanin alaƙata da shi da ya addabi rayuwata data mahaifina, dan haka ku jira sammacin kotu dan sai munyi shari'a, idan Aliyu ya iya muku haƙuri da kawai ci ni bazan barku ba”. Daga haka tabar wajen fuuuu. Dada ta zabura zata bita Uncle Muneer ya riƙeta yana girgiza mata kai. Sai ta ƙara fashewa da kuka ta maida faɗan a kan Daddy. Wai duk shi ya kitsama Lulu taci mata mutunci tasan Lulu bata da wannan wayon. Daddy dai ko tari baiyi ba, sai Uncle Muneer ne ya shiga mata magana cikin ɓacin rai akan shi da yasan abinda zatayi kenan da bai kawota ba. Yanda yake faɗa zai tabbatar maka ransa ya ɓaci, dan sosai take cima Daddy mutunci da masa gori. Amma ko tari bai mata ba balle aje ga batun ramawa. Su Amrah ne dai suka sake zuwa suka kira Lulu. Aiko sai gata a fusace. Ranta yafi na kullum ɓaci akan abinda Dada kema mahaifinta, atake na ƴan ƙwayar ya motsa ta rufe ido taima Dada tas har sai da ta gudu dan kanta saboda ganin buyagin Lulu fa ya haifi nata. Dan yanda Lulu ke ruwan bala'i zaka rantse bata taɓa sanin Dada ba a rayuwarta balle tuna qlaƙarsu. Uncle Muneer ransa ya kai matuƙar ɓaci, da yasan abinda Dada zatazo tayi a gidan mutane wlhy dabai kawota ba. Aiko ƙin kaita yay gidan Alh. Sulaiman da tace zata duba Tajuddeen shima.
      Lulu kam da bayan fitarsu Daddy ya hauta da faɗa sai ta sakar masa kuka. Dole ya fice cikin ɓacin rai dan duk da yayi shiru kalaman Dada sun matuƙar zafar masa zuciya shima, amma bazai so Lulu ta cigaba da mata tsiwa ba matsayinta na kakarya. Ya danne ne kawai saboda dattako. Lulu na komawa ɗakinta kiran Uncle Yousuf ya shigo mata. Ɗauka tai kawai ta fashe masa da sabon kuka. Ƙirjin Smart yay wata irin harbawa. Dan dama kiran nashi ne bana Uncle Yousuf ba. Haka yake yi sai ya kirata da layin Uncle Yousuf ɗin yaƙi magana. Taita faman sallama yay shiru har sai ta gaji ta katse, wani lokacin tabi kiran wani lokacin ta share. Ko tabi baya ɗauka kuma sai dai ya bama Uncle Yousuf ɗin. Dama shi burinsa jin muryartane, wani lokacin ma yakanyi sa'ar jiyo AA na kuka musamman idan darene a Nigeria kasancewar AA ɗin ya dage da musu kukan dare yanzu. Da ance ɗaya tayi babu sauran zaman lafiya kuma sai anyi sallar asuba. Wani lokacin har Daddy fitowa yake ya ɗaukesa aita masa addu'a da rirriga amma yaron nan ko'a jikinsa. Mommy tayi, Ummita tayi Iya Tabawa tayi. Lulu kam sai dai tayi tagumi kawai yana kallonsu, wani lokacin ma ba'a tashinta sai idan kukan yayi nisa ne sosai ace ta tashi ta shayar da shi. Amma yaron nan ko'a jikinsa, wani lokacin ma dan zuciyar tsiya irin ta uban baya ko kamawa.
      Kasa sauraren kukan nata Smart yayi ya yanke kiran, cikin tashin hankali da damuwa ya nufi Uncle Yousuf kamar zai fasa kuka ya ke faɗin, “Kuka takeyi, ka kira kaji mike damunta Please Uncle”.
         Shima Uncle Yousuf hankalinsa ya tashi, dan yasan duk abinda ya saka Lulu kuka ba ƙarami bane. Wayar ya kira tare da saka Hans-free. Kamar bazata ɗauka ba kuma sai ta ɗauka. Tambayoyi Uncle Yousuf ɗin ke mata cike da kulawa batare da ko jiran sun gaisa ba. Bata ɓoye masa komai ba ta sanar masa. Smart ya sauke nannauyar ajiyar zuciya da lumshe idanunsa da suka kaɗa sosai. Shi dai tunda ba wani abu ne ya sameta ba ai da sauƙi. Lallashinta sosai Uncle Yousuf yay, sannan ya mata faɗa da nasiha akan rashin kunyar da taima Dadan. Ya ce karta sake babu ƙyau hakan. Dada tamkar mahaifiya take a gareta. Ta bashi haƙuri da tabbatar masa bazata sake ba. Amma a ranta fa tasan ita da Dada fa ai haihata-haihata (🤣😂 ALLAH ya ƙyauta su Lulu an san daɗin ɗa🥱🚴👏).
         Cikin tsokana Uncle Yousuf ke duban Smart yana faɗin, “Darun matar nan taka sai kai Aliyu, ni dama nasan wlhy bazata ƙyale Dada ba. Kuma duk a wajensu ta kwaso wannan masifar ai dan mudai a family namu babu mafaɗaci”.
      Murmushi kawai Smart keyi, a ransa yana sake jinjina hali irin na Lulu. Yasan tabbas yaransa sun bani da masifa tunda shima dai ba raga masa ake ba. Wani lokacin idan tana faɗa har mamakin wai kanta baya ciwo yake yi. Tana da tsiwa sosai, ga shi sam babu tsoro a idanunta. Ita dai kawai zaman lafiyarka da ita kada ka shiga gonarta ne kawai..........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣3️⃣



.......Alhmdllh sosai jego yayma Lulu ƙyau, ga Iya Tabawa na mata wani sirrintaccen gyara irin na mutanen da cikakke da ke zama a jikin mace duk da bada kanta ta haihu ba. Gefe kuma Aunty Saliha ta sake kawo wanda sukai mata gyaran aure na nasu suma yanzu. Mommy ma na nata ƙoƙarin. Sai ruwan addu'oi wajen Malam na Yakasai da ake amsowa Lulu na tsarin jikin da yanayin da take ciki game da Smart. Wannan ƙoƙarin Ammah ne da Abbah. Dan ita kanta Ammah kan zauna da kanta tai mata addu'oi a cikin ruwa da ma ruwan zam-zam shima AA ana bashi.
      Sai Daddy da ya kawo mata malama har gida tana ɗora mata karatun addini saboda Ummita zataje ganin gida itama. Da yake Lulu tasa abun a ranta hatta Mubeen zaunarwa take ko su Amrah su ƙara mata karatun. Gefe guda kuma tana ta ciku-cikun yima ƙungiyarta rigester shima da taimakon Daddy da Uncle Khamil na Abuja da shima ya bata goyon baya. Koda wasa bata son tuna Smart, dan ko AA ta kalla babansa yazo mata a rai kanta ya dinga wani irin masifar ciwo kenan dake tayarma kowa na gidan hankali. Inda aka yankata Alhmdllh yana sake warkewa, Aunty Khadijah matar Coach ce ke zuwa dubata kullum babu fashi, idan abinda ya kama taje asibiti ne kuma sai ta shirya Mubeen ya kaita suje suga likitan su dawo. Da Ummita zata wuce shatara ta arziƙi Daddy ya haɗa mata, itama Lulun ba'a barta a baya ba, Uncle Khamil ne da yazo ya wuce da ita duk da dai jirgi sukabi zuwa Abuja tare, dan Lulu ta gargaɗeta zuwa ɓagwai saboda gudun mutanen Alh. Sulaiman kar su cutar da ita ko iyayyenta.

       ★A ɓangaren Ammah tsaye take wajen kaima UBANGIJI kukanta akan dai-daituwar zaman waɗan nan ma'auta. Tare da yawaita sadaka da azumi. Yaranta kaf basu zauna ba har ƴan uwanta kasancewar suna da haɗin kai. Yayinda itama Ummah ta kasa zaune ya kasa tsaye wajen sake lafto sabbin asirai kala da iri akan Ammah da Smart kai harma su Aunty Amaryar ba bari tayi ba. Dan a kwanakin nan da ƙyar suka samo kan Abba da aka nema juyarma da kai. Sai Alhmdllh al'amarin baiyi nisa ba ya sake shi, hakan ya tada hankalin Ummah kam sosai, dan ba ƙananun kuɗi ta kashe a aikin da akaima Abban ba, amma sai gashi ya tafi a banza cikin ƴan kwanaki ƙalilan....

         *_UK LONDON_*

   Hassada ga mai rabo taki ce, sannan duk abinda UBANGIJI ya ƙaddara shi a matsayin naka babu wani mahaluki a duniya da ya isa canja wannan ƙaddarar. Dan kuwa a lokacin da Ummah ke can tana faɗi tashi akan abinda bata iya jayayya da shi ba anan ƙasar England ƙaramin labari ne ke neman canja kansa akan Aliyu Mika'il Idris Mawashi, wato Smart Mawashi zuwa babban gaske gagarumi. Dan fa manyan clubs da ke zawarcinsa ta ƙarƙashin ƙasa sun fara bayyana kansu a fili yanzu. Wannan yasa aketa faman kai kawo da dambarwa tun barowarsu Canada shi da Manager ɗinsa Uncle Yousuf. Sosai ake ta kai ruwa rana da bata kashi a tsakanin Coach's ɗin mayan clubs ɗin. Shi dai Smart ya duƙufa gayama UBANGIJI da neman zaɓinsa. Dan bashi da wani zaɓi sai nashi. Yayi alƙawarin duk inda ya tsinta kansa zaiyi aiki tuƙuru in sha ALLAHU duk da a cikin zuciyarsa yana da club ɗin da yafi so da ƙauna kuma gashi a cikin masu zawarcin nasa. Amma sai bai Zafafa ba ya bar ma UBANGIJI komai

Please Login or Register in order to submit comment