You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya daɗe tambaya nake ko nan aka kawo wata da sukayi faɗa a wani salon sunan ta Hushaima Sahnish Shazeen ".

"Nan ne!, Ya akayi ?".........." Qanin ta ne ni mun ji shuru ne har lokacin tashin su yayi bamu ganta ba, shi ne mukaje muka tambaya aka faɗa mana abin da ya faru da kuma inda aka kawo ta"......... Juyawa ɗan sandan yayi wurin sauran ya ce, "Constable Buhari DPO na nan kuwa?"......... Ɗan shiru Constable Buhari yayi kafin ya ce, "Anya kuwa saidai na duba banajin yana nan gsky".

"To da ALLAH je ka duba in yana nan kace masa ɗan uwar yarinyar nan ne da ke da case dasu Hajiya sulaimiyya"..........Tashi Constable yayi ya wuce ciki can sai gashi ya dawo yana faɗin, "Ya tashi saidai ya dawo gobe".

"To kaji baya nan saidai ka dawo gobe kamar ƙarfe goma haka".

"Yanzu officer ba za'a iya bamu bailing ta ba kenan?"........ Dariya yayi yana kallon Sahnish ɗin kafin ya ce, "Kai yaro baili fa kace? ai bama a fara wannan zancen ba tunda ba'a san halin da yarinyar data fasawa kai take ciki ba, dan har yanzu ance bata farfaɗo ba, kuma ma in zan Baka shawara tun wuri ka fara neman lawyer dan iyayen yarinyar sun buqaci a turasu kotu kuma har an ɗau statement dinsu ma zaa aika so batun baili duk babu shi a yanzu".

Wani irin faɗuwa gaban Sahnish yayi, cikin rawar murya ya shiga roqon su amma ko dubansa basuyi ba ƙarshe ma sai cewa ɗayan yayi, "To kai haka ma ake zuwa baili kamar zakaje karɓar sadakar kunu"......... Cikin rashin fahimta Sahnish ya ce, "Bangane ba ranka ya daɗe"..........." Shikenan tunda baka gane ba juya ka koma inda ka fito, ka dawo goben".

"To officer dan ALLAH ka min alfarma na ganta mana"........ Kallon baka da hankali suka masa kafin ya ce, "Kai baza ka ganta ba ka wuce ka bamu waje ka cika mu da surutu".......... Cikin rawar ƙafa Sahnish yaja hannun Shazeen sukayi waje hankalin sa in yayi million ya tashi, wurin wa zai nufa wa ya sani da zai masa alfarma, sun kusa minti talatin tsaye a bakin police station ɗin kafin ya yanke shawarar kiran baba ilerika. Ɗaga waya yayi ya kira shi........

Baba ilerika ne kishingiɗe a majalisar tasu shi da abokan sa sai tafka muhawara suke akan lamarin siyasar ƙasar Nifaz ɗin, Wani me suna Jarwai ya ce, " Kai ni fa Malam lawan ba zan taɓa yarda cewa ba izinin gomnati a duk wa'annan abubuwan dake faruwa ba, kai ai bani ba ma duk me hankali yasan da wata a ƙasa kawai so ake mu saki sana'ar mu, mu dogara da abubuwan da ake shigo mana dasu daga waje a Matsayin cigaba daga nan kuma mu koma ƙaraƙashin ikon su ya zama su zasu ɗinga juyamu yadda suke so, saboda bamu da ikon sarrafa komai daga ƙasarmu"............ Malam lawan ya ce, "Yanzu miye laifi dan an kawo abubuwan cigaba mun karɓa, ku bakwa ganin ƙasashen da basa ƙarɓar abubuwan cigaba ya suke? Ai basa gaba".

"Ai kuwa sunfi zaman lafiya Malam lawan, shin ka taɓa jin labarin irin wa'annan gurbattatun abubuwan dake faruwa a irin wa'annan ƙasashen? Ai babu. Saboda ta hanyar da ake shigo mana da abubuwan da ake cewa na ƙaruwa ne ta nan ake shigo mana dana cutuwa ma, Kaga ka yarda kawai jarwai ya fika gsky a wannan Maganar, taya ma to za'a ce mu saki kiwo mu saki noma za'a dinga shigo mana da komai ba sai mun wahala ba, in kuma munaso muyi da kan mu za'a shigo mana da Artificial intelligence ɗin da zasu sauqaqa mana kayi tunani fa".

Jarwai ya ce, "Ai qasimu ba dan komai bane kawai dan su rabamu da sana'o'in mu ne, kuma ba zai yiwu ba dan tunda suka fara motsa wannan Maganar to akwai shirin da sukeyi dan haka whl kowa ya nemi sana'ar hannun da ba wata shegiyar gunkin ko engine da za'a sawa battery ace zai iya yi, wannan shi ne kawai abinda zai cecemu".

Shi dai Baba ilerika yana daga kishingiɗen sa yana goga ashuwakin sa yana kallon masu wucewa ba tare da yace dasu uffan ba, wayar sa ce ta Fara ƙara, zarota yayi daga aljihun gaban rigar sa ganin Sahnish ya sashi yin picking tare da karawa a kunne. "Helo Sahnish ya akayi ne?".

"Baba akwai matsala whl".......... Yadda yaji Muryar Sahnish ɗin ya sashi tashi daga kishingiɗen da yake yana faɗin, "Subahanallahi ALLAH ka raba mana hanya da matsala, meke faruwa?".

"Baba Hushaima ce suka samu matsala da wata a wurin aikin su har ta fasa mata kai, to yanzu sun kawo ta police station nazo nayi duk iya bakin ƙoƙarina sun hana ma a ganta ".

"Tooo abinda ya faru kenan, yanzu kai kana ina ? Kuma wani police station ne?".

"Ni muna ƙofar police station ɗin yanzu......." Nan ya kwatanta masa police station ɗin.

"To ku jirani anan bari na ƙaraso, kaik jama'a daga wannan sai wannan Hushaimaaa"....... Ya ƙarashe yana kashe wayar tare da miqewa ya kalli sauran abokan nasa da suke ta faman tabka muhawara sannan ya ce, "To Jarwai mu wata yar camama ta taso, za kuma mu ƙara gaba"....... Dariya Jarwai yayi kafin ya ce, "Shege ilerika bakaso a zauna lpy in dai akwai ci a rigimar"......... Miqewa tsaye yayi yana karkaɗe rigar sa ya ce, "Ahhh to kuwa kaga laifi na ne duk inda ci yake kuma ai kowa yana so "......... "To ko nazo na raka ka ne". Faɗin Malam lawan.

"Makaho ne ni ko kuturu da bazan iya kai kaina ko ina ba har sai na nemi ɗan jagora, ko kuwa ah ah jariri ne ni da sai an ɗaukeni?"......... Girgiza Kai Malam lawan yayi yana Dariya ya ce, "kaga ni fa wasa nake mutumi na, jeka ka dawo".

Qasimu ya ce, "Kaga ilerika jeka abunka rabu da su, kar ma su ɓata ma lokaci harkar ta wuce ka".



-------------------------√



             AURELLON SULTANATE💎


Ziyada ce ta shigo falon da Ummu ke zaune tare da hadiman ta, kowa da aikin da yake wasu kuma suna zaune a gabanta suna mata hira, wasu suna matsa mata ƙafafu, wata tana haɗa mata tea, suna ganin shigowar ziyadan suka fara risinawa suna mata Barka da shigowa duk da a zaune suke. Cikin takun da ke nuna eh ita ɗin jinin sarauta ce kuma sarautar ma ta Aurellon ta ƙaraso, wuri ta nema ta zauna ba tare da tayi magana ba, ganin yanayin fuskarta yasa Ummu faɗin, "Ku tashi kuje kawai sai na neme ku"............" A tashi lpy sarauniyar sarauniyoyi, ALLAH ya ƙara miki lpy"....... Suka haɗa baki wurin faɗa suna miqewa. Wadda take haɗa tea ce ta ce, "Ranki ya daɗe za'a miqo tea ɗin ne ko naje?"......... Hannu kawai ta miqa mata alamar ta bata, duqawa tayi kan guiwowin ta sannan ta miqa mata ɗan ƙaramin mug ɗin na gold dake haɗe da wani ɗan ficicin teaspoon da kuma saucer da aka ɗaurashi akai. Tana karɓa Khadimar ta juya ta bar wurin.

"Meke faruwa ne ziyada?"....... Ummu ta tambaya tana kurbar tea ɗin dake hannun ta .

Kafin ziyada tayi magana Reeslan ya shigo yana gyara zaman band ɗin kansa, sanye yake da wata Black Polo t shirt data fito da kyakkyawar surar jikinsa ta cikakken ɗa namiji sai caramel colour skinny jeans da ya sa, baiyi masauki ko ina ba sai gefen Ummu, ɗan tsukakken bakinsa ya kai bakin mug ɗin dake hannun Ummun ya kurɓi tean, sai kuma ya gyara zamansa tare da sanya dukkan hannayen sa biyu ya karɓe mug din da saucer yana faɗin, "Ummu saidai fa kisa a kawo miki wani, waye ne ya haɗa a cikin khadiman naki?"........... Sakin baki Ummu tayi tana kallon sa kafin ta kai hannu ta riqe kunnen sa ta murɗe, ɗan ɓata fuska yayi amma bai ce komai ba, dungure masa kai tayi tare da faɗin. " Ka nutsu ɗan ALLAH Reeslan, ka ajje duk wani rashin ji a gefe, ka sani kai ne fa magajin kujerar Aurellon, ni kwata kwata na rasa ya zanyi dakai whl".

"A'a Ummu ni fa nace saidai Habiby ya ƙarɓa ko shi ko Sahel dan gaskiya ni bazan iya wata sarauta ba, dan ALLAH ki daina faɗar hakan ma Ummu yana bata min rai whl"........ Ya faɗa yana tsuke fuska kamar bai taɓa sanin wani abu Murmushi ba a duniya. Ajiyar zuciya Ummu ta sauke tana kallon ɗan nata da a ko da yaushe su kayi ƙoƙarin kwatanta shi da sarautar tasu sai ya nuna bacin rai da fushi ko da kuwa Sultan da kansa ne zai masa maganar. "Tohm shikenan naji yanzu daga ina kake?"........ Ba tare da ya kalleta ba alamar ransa ya ɓace da maganar data masa ya ce, "Naje Horse ranch na duba Hirtik ba lpy, sai na biya fada wurin su Abbu ".

"To ka tashi kaje wurin Rouslan domin bayajin daɗi inajin tun fitar ka yake ta amai sai da aka kira Abyan ma yazo ya duba shi, amma Imam ya aiko da ruwan addu'a, kai ma in kaje Ka ganshi kazo ka karɓi naka kasha "..........Tunda ta ambaci Rouslan bashi da lpy ya juyo da mugun sauri, "Ummu bansani ba ai meysa ba'a kirani ba, how za'a kira wani Abyan bayan gani, wai meysa ake min haka ne, shikenan mutum baya kuskure ne, ko shi Abyan ɗin baifi ƙarfin kuskure ba. Ba dan alqawarin da nayi wa Rouhi ba whl da sai na koma kan aiki na saidai duk abinda zai faru ya faru"......... Kafin Ummu tace wani abu ziyada ta ce, "Yah Reeslan ka tarar da abinda ke faruwa da kaje fada".......... Ɗan kallon ta yayi hankalin sa akan Ummu da ita kuma ta juya wurin Ziyada tare da tambayar ta, " Meke faruwa ne ziyada? Tun ɗazu na lura da magana a bakin ki kuma kinzo kin zauna kinyi shuru".

"Ummu Ammu yassar ne akace ya yanke jiki ya faɗi yanzu a fada ".

"Innalillahi wa Inna ilaihir rajuun me ya sameshi haka?" .

Reeslan da ya tashi domin zuwa wurin Rouslan ya ce, "Sai dai haƙuri Ummu, amma Ammu yassar ba zaiyi ba, shi ma mutuwa zaiyi".......... Dafe ƙirji Ummu tayi idanunta na cikowa da hawaye cikin rawar murya ta ce, "Reeslannnn! Innalillahi wa Inna ilaihir raju'un, Reeslan bana hanaka irin wannan maganganun ba meysa bakajin maganata? Meysa Reeslan so kake sai zuciyata ta buga ko?"..........Ta ƙarashe cikin Muryar dake bayyana tsananin tashin hankalin da take ciki, wannan shine karo na uku da irin haka ta faru kuma in Reeslan ya ambaci mutuwa mutum zai yi, to fa mutuwar yake amma Ummu bata taɓa yarda wani ya sani ba ciki harda mai martaba, sai addu'a kawai data dukufa dayi saboda bata so a canfa mata ɗa.

Ita kuwa Ziyada da bata san abinda ke faruwa ba sai cewa tayi, "yah Reeslan me Ammu ya ma da zaka masa fatan mutuwa?"......... Wucewa kawai yayi ba tare da ya bawa ɗayansu amsa ba , Ummu ce ta ce, "Ziyada karki sake naji wannan maganar a bakin wani, yadda akayi ta a nan a barta a nan whl ko da wasa naji ta sai ranki ya ɓaci".........Tana kaiwa nan ta miqe ta bar falon zuciyar ta cike da fargabar abinda zai biyo baya.



*TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.*



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️




___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd sultywrites22



STEP 1



PAGE _______58


Reeslan na shigowa ɗakin su ya tarar da jakadiya dake zaune kan shag rug ɗin ɗakin nasu tana tsiyayawa Rouslan ruwan addu'ar da Ummu tace tazo ta bashi wanda Imam ya aiko, Wani irin ɓaci yaji ransa bai san lokacin da ya katsa mata wata tsawa ba, da faɗin, "Me kikeyi Anan, tashi ki fita kafin na saɓa miki kamanni"......... Take jikin jakadiya ya ɗau rawa har cup ɗin hannun ta na suɓucewa ya faɗi. " ALLAH ya huci zuciyar Maleekh dama Sheikha ce ta buqaci nazo na bashi "..........Ta ƙarashe tana tashi zata fita, ciki ya ƙarasa in da take tsugunne tare da ball da kyakkyawan Jug ɗin yana faɗin, "Su wannan uban wa kika barwa ? tattare tsiyarki ki fita da ita "..........." Habiby p......."

"Kaiiiiii Shut".......... Ya faɗa yana ɗaura yatsan sa kan ɗan mitsitsin lips ɗin nasa. Harara Rouslan ɗin ya watsa masa ta gefen ido yadda shi kaɗai kawai zai gani sannan ya ɗauke kansa, Wucewa jakadiya tayi jikinta na ɓari ta shiga tattare kayan dan Jug ɗin tuni ya tarwatse ruwan addu'ar ya zube, haka ta tsitsince sannan ta nufi ƙofar fita. "Kuma ki turo wadda zata gyara ɗakin nan"........ Ya faɗa Yana matsawa wurin two seater sofa ɗin da Rouslan ke zaune a kai. Zama yayi yana huci kamar wani tafasasshen ruwan zafi. Sai a lokacin Rouslan ya sake cewa, "Haba Habiby ruwan Addu'a ne fa Imam ya aiko kazo ka zubar, ayoyin ALLAH ne fa"........ Wani kallo ya watsa masa Amma baice komai ba shi kuma ya cigaba da faɗin, "Kuma jakadiya ko ba komai tayi ya'ya damu, ka tuna tun bamu fi shekaru huɗu ba a duniya take tare da mu, ya kamata ace kayi limiting actions ɗinka toward her".

Hannunsa ya kai goshin Rouslan ɗin yana faɗin, "Me kake ji yanzu? Ummu tace min bakaji daɗi ba bayan fita ta?".......... Ɗan sauke numfashi yayi dan maganar da yake ma ƙarfin hali ne shi kaɗai yasan me yakeji a jikinsa wani irin turirin zafin zazzaɓi ne kawai ke fita.

"Shi Abyan ɗin da yazo ya baka magani ko kuma kawai iyayi yazo yayi ma? Meysa ma tukunna baka kirani ba har ka bari suka kira wani Abyan"........ Ya faɗa wannan karon a tausashe da kuma kulawa . Lumshe idanun sa yayi ya buɗe kana ya ce, " Ya min Allurai dai, ga sauran can ma ya bari ya ce in kazo sai ka duba yaso ka cigaba da yi min. Kuma banaso ne na tashi hankalin ka a inda kake saisa ban kiraka ba"........ Jijjiga kai Reeslan ɗin yayi tare da tashi ya wuce gaban gadon nasu, bedsheets ɗin dake kai ya cire gabaɗaya sannan ya wuce ya ɗauko wani sabo ya dawo ya shimfiɗa ya canza pillow case ya gyara gadon tsaf tsaf, sannan ya dawo ya kamo hannun Rouslan ɗin kamar wani yaro, miqewa yayi ya bishi har zuwa bakin gadon, nuna mashi kan gadon yayi da faɗin, "Kwanta ka huta".

"Ina zaka ?".......... Rouslan ɗin ya tambaya yana kallon sa. "Ba inda zani wanka ma zan shiga, nima in na fito kwanciyar zanyi na huta ai"........... Rouslan bai Ƙara cewa komai ba ya hau ya kwanta, wata na'ura Reeslan ɗin ya kunna ita kuma iyakarta zagayen gadon kawai zata sanyaya, in kuma sanyi ne zata baka dumi kamar dai Ac amma Ac in Ka kunna duka ɗakin zata game ita kuma wannan iyaka gadon ne kawai. Saida ya seta ta sannan ya sauke wasu ƙayatattun transparent curtain dake zagaye da gadon. Daidai lokacin akayi Knocking, "Waye ?"..........Ya tambaya a daƙile.

"Khadimah Jamila ce jakadiya tace nazo na gyara ɗakin"......... Saida yaja tsaki sannan ya Ƙarasa ya buɗe ya koma tsakiyar ɗakin ya tsaya tare da riqe waist ɗinsa da hannayen sa, "ki nannade rug ɗin ki fita dashi ki canzo wani karki ɓatamun lokaci kiyi sauri"......... Duk wannan maganar yana yin tane cikin faɗa faɗa a qage irin wanda ya ke jira ayi kuskure kaɗan ya kaiwa mutum duka.

Duk da nauyin rug ɗin haka ta nannaɗe shi sannan ta shiga ƙoƙarin ja amma duk da haka bai ga ƙoƙarin ta ba ya ce, "Da ALLAH ki sa ƙarfi kiyi maza ki fice dashi, ki zo kiyi abun dake gabanki, kina abu sai kace wanda ake rainon ku da yunwa"......... Bata ce komai ba sai saka dukkan ƙarfinta da tayi ta ja shi waje sannan ta kira wata khadimar tace ta janye wannan ta sa a ɗauko wani a store yanzu yanzu, Kasancewar sun san aikin Reeslan ɗin yanzu yanzu ne shi bai san wani abu wai sai anjima ba yasa cikin hanzari ta kira wata ta tayata ɗauke wannan ɗin.

Dawowa ɗakin khadima Jamila tayi tana haki ta tattare Wurin sannan tayi mopping, lokacin aka shigo da wani sabon rug ɗin tare suka haɗu ita da wadda ta kawo suka shimfiɗa sannan suka zube a gabansa tare da faɗin, "Ko da akwai abinda za'a yi wa maleekh?".......... Tsaki yaja da faɗin, "Dama ku biyu na kira ne ?".......... Da sauri wadda ta kawo rug ɗin ta tashi zata fita har ta kai ƙofa ya ce, "keehhhhh"......... Datse hakwaran sa yayi tare da kallon gadon da Rouslan ke kai yana bacci, cikin ƙoƙarin yin ƙasa da Muryar sa ya ce, "Nace ki fita ne ko kuwa na sallame ki ne? ba tambaya na muku ba? "......... Jikinsu ne ya ɗau rawa a tare suka ce, "ALLAH ya huci zuciyar Maleekh ".

"Ku bace min da gani kafin nayi pieces da miskinan ƙasusuwan ku"........ Ai kafin ya ƙarasa sunyi waje tare da rufo ƙofar, kwafa yaja sannan ya wuce wurin bedside drawer ya jawo burner ɗin sa ya jona ya wuce ya ɗauko turaren wutar su, dan shi takanas yake zuwa ya kwaso na Ummu daga an haɗa mata sabbi, kaɗan ya zuba dan already ɗakin nasu ya riga ya kama da kamshi dan ko pillown su ka ɗauka in Ka ajje to kai ma kamshin ya kama jikin ka kenan. Bathroom ya wuce domin watsa ruwa ya zo ya kwanta ya huta.




------------------√




Ranar ko da ya tashi bai fita ko falo ba daga ɗakin sirrinsa sai normal ɗakinsa, gyaran ɗakin ma yana ciki akayi, haka abinci a ɗakin yaci sama sama saboda hankalin sa na kan aikin da yake, ko su Ace bai haɗu dasu ba sai Philip da ya sanya ya dubasu ya Kuma tambaye su ko da akwai abinda suke da buqata. Ba abinda yake sai bincike a kan shadow tun 11am yake Abu ɗaya har 3pm Amma ba wani labari domin Shadow Yana da mutane a kowani ƙasa Wanda suke masa safarar mutane, Saidai Kuma a duk binciken sa mutanen nasa ko wuqa zaka sa musu a wuya su faɗa ma inda za'a samu shadow to fa Saidai ka datsa musu wuqar nan bama inda yake ba hatta kamannin sa basu sani ba fari ne? Baqi ne? ah ah yellow ne baza su iya faɗa ba kamar dai yadda BB LALO ya faɗa masa, tashi yayi daga gaban table ɗin yanajin kamar kansa zai kama da wuta, tunda ya fara aiki Matsayin jami'in sirri Ba'a taɓa bashi aiki yayi failing ba hakan yasa ko da aka danqa masa aiki kan Shadow baiji ko ɗar ba dan gani yake kamar ƙaramin aiki ne, tun da ya tashi ko wanka baiyi ba daga shi sai short nicker yake ta dirzar wannan uban aikin. Kai kawo ya shigayi a ɗakin sirrin nasa yana tunane tunane har baisan iya tsawon lokacin da ya ɗauka ba sai jin Kiran sallar la'asar yayi, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya fice zuwa master room ɗin nasa, toilet ya wuce ya ɗauro alwala ya fito, jallabiya ya zira kawai ya tada sallah. Yana idarwa ya miqe ya koma ɗakin sirrin ya sake dasa sabon zama gaban system ɗin ya ɗaura daga inda ya tsaya, Amma still ba wani labari kawai dai matsayar da ya tsaya itace dole wa'anda zasu ɗauki mutanan da zasu basu zasu kaisu inda ake tara mutanan, Kuma dole ne shadow ya kasance a kusa dasu koma ta Ina yake. Da haka ya yanke nasa hukuncin kawai zasu Kira suce musu sun gama aiki su faɗa musu inda zasu Kai musu mutanan, numfashi ya furzar tare da kashe system ɗin da duk wasu abubuwan da ya kunna lokacin da ya shigo sannan ya fita daga ɗakin ya koma master room.

Miqa yayi tare da langwashe hannayen sa baya suka bada sauti ƙas ƙas haka wuyan sa ma, direct bathroom ya wuce tsawon 30 minutes yayi a ciki sannan ya fito lokacin anata kiraye kirayen sallar magrib, wata jallabiyar ya ɗauko ya sanya ya tada sallah, yana idarwa ya cire ya wuce gaban mirror can ma sai da ya ɓata kusan minti ashirin ba dai sai na fada ba kunsan mutumin naku da sluggishness ya fiya lakwai lakwai tu. Tashi yayi ya wuce gaban sip ɗin nasa ya ciro kaya maras nauyi, wani army green cargo shorts da black armless t shirt Mai laushi kamar auduga ya feshe jikinsa da turaren sa me kamshi. Saida ya gama duk abinda zaiyi ciki harda sallar isha Sannan ya fito daga ɗakin.

Haka take a wurin su Kiara tunda suka tashi sukayi wanka suka fita sukayi breakfast Kiara ta koma ɗakin da suka sauka ita da Ash, ta fara aikin binciken Shadow, Ash kuwa Philip tasa ya zagaya da ita gidan ta ɗanyi kalle kalle sannan ta koma ɗaki ta samu Kiara ta tasa system ɗin ta a gaba, itama wucewa tayi ta ɗauko ta ta ta jona a caji tana faɗin, "Kin samu wani info ne Kia?".......... Ba tare data ɗago ba ta ce, "Ash kinsan abinda ke ban mamaki a duk ƙasar da yasa a samo masa mutane to a bakin border wanna ƙasar ake ajje masa wa'anna mutanen".

Cikin alamun rashin fahimta Ash ta ce, "kamar ya kenan ? Ban fahimta ba ?".

Ɗagowa kiaran tayi tare da cire hular dake kanta ta wulla kan gado Sannan ta ce, " Hakan na nufin bashi da takaimemiyar ƙasa, su kawai yaran nasa aikin su su kawo masa mutanen bakin border daga nan Kuma su juya suyi tafiyar su".

"Kenan akwai mutanan sa a bakin kowace border?"........." Yes that's the fact, to Amma yanzu ta Ina kike ganin zamu soma kamashi ?".

Ash na kunna system ɗinta ta ce, "ki daina Abu kamar ba jami'ar bincike ba idan dama taqi sai Abi hagu, zamuyi amfani da na'urar tracker ne kawai".

"Yes yes Ash kin kawo idea, dole idan da tracker a jikin mutanan mu, duk inda sukaje zamu san takunsu da Kuma motsinsu har mu sameshi".

Wata bazawarar dariya Ash tayi hankalinta akan system ɗin ta da take caccaka da zara zaran yatsun hannunta kamar wata typewriter ta ce, "Wai kina tunanin dan munyi amfani da tracker shikenan zamu samu inda shadow yake?"
............"What do you mean? Kin sake sani a duhu?". Kiara ta tambaya tana sake haɗe rai.

"Kinga shikenan daga na haske ki da fitila kema naki shadow zai bayyana".........."Stop joking Ash it's not time for that".

"What I mean shi ne in munyi amfani da tracker zamu San inda ake Kai mutanan, sannan zamu San me akeyi dasu sai muje mu ebe su, dole hakan zai girgiza shi Kuma duk inda yake zai motsa wannan shi ne target ɗin mu, motsin sa muke so daga inda yake kawai,

Please Login or Register in order to submit comment