You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karfe takwas na safe

"zuwa azahar wani malaminsu Ustaz Abdulsalam wanda Allah ya daurawa kaunar Amina (ba kauna ta soyayya ba), bayan ta bada haddarta ya daga kai ya dube ta tana harhada takardunta don komawa gida ba tare da an yi addu ar tashi ba."

"Ya ce,  Amina Mas ud, zauna ki jira ni in gama da  yan uwanki, akwai maganar da za mu yi ."

"Ba da son ranta ba Amina ta koma bencinta ta zauna tana ta sake-sake cikin ranta,  Ban daura abincin rana ba, na san yanzu daga Goggo har Baba sun dawo daga asibiti ba su samu na dafa komai ba&  Sai hawaye sharr-sharr."

"Ustaz na lura da Amina, kawai sai ya ji zuciyarsa ta karye, ya fahimci tsayar da ita din da ya yi ne ya sa ta kuka. Shi kuma so yake ya ji me ta ke yi wa sauri haka da har ya shafi hazakarta a kan karatu? Tana daga cikin daliban da ya sanya sunansu za su halarci gasar karatun alqur ani mai tsarki ta duniya (International competition of"

Holy Qur an) wadda za a yi a kasar Misra wannan shekarar.

"Bai nuna ya ga tana kuka ba, har ya gama da dalibansa uku da suka rage masa. Ya isa har gaban bencinta ya ce,"

 Aminatu Mas ud!

"Ta dago jajayen idanunta ta dube shi, a zuciyarsa ya ce,  Subhanallahi Ahsanul Khaliqeen . A fili kuma ya ce,  Me ke damunki ne a  yan watannin nan? "

"Ta share hawaye da bayan hannunta,"

 Babana ne ba shi da lafiya .

"Cikin tausayawa Ustaz ya ce,  Allah sarki, me ke damunsa? "

 An ce wai ya samu (stroke). Amma yana samun sauki .

" Allah ya kara wa Baba lafiya, ki dinga karanta fatiha kafa bakwai a ruwa, ki karanta suratu Yaseen ita ma kafa bakwai, ki ba shi ya sha, a kuma shafe masa jikinsa, insha Allahu zai kara samun sauki ."

"Amina ta ce,  Zan yi insha Allahu . Ya dube ta na  yan sakanni, sannan ya"

ce.

" Ni da har na ba da sunanki matsayin wadda za ta wakilci jihar Bauchi a  International competition a kasar Masar, ban san halin da ki ke ciki ba ke nan ."

"Amina cikin girgiza kai,  Ba zan iya zuwa ba Ustaz, don Allah ka cire sunana, ban sani ba ko nan gaba, idan na ga Babana na takawa da kafafunsa ."

"Ustaz ya jinjina kai, ko nawa ne  ya yan da suka damu da iyayensu haka irin AMINA? Yana rokon Allah ya ba shi  ya ya mata masu albarka irin Aminatu, domin an ce akasarin  ya ya mata masu jin kan iyaye ne."

" Zo ki tafi Aminatu, kada ki manta da addu ar da na gaya miki, Allah ya kara masa lafiya, ya albarkaci rayuwarki ."

"Ta kuwa suri jakarta ta fito, da ta tabbatar ta yi wa Ustaz nisa, sai ta kwasa da gudu. Ustaz ya girgiza kai domin yana kallonta."

"To haka a boko ma, kullum cikin makara ta ke, a yi ta yi mata bulala da horon da ake yi wa  yan makara, amma ba"

"ta damuwa. Don ba ta fita sai ta tabbatar ta gama komai na ayyukan gidan, tun asuba in ta tashi ba ta komawa za ta share gidansu tsaf! Da ganyayyakin bishiyar umbrella ke batawa; ta share dakunan Goggo da na Baba, ta yi wanke-wanke, ta dora sanwa, ta dama musu koko, ko kunu, ta yi musu dumame na abin da aka ci daren jiya. Sannan ta yi wanka ta yi shirin makaranta a iya shekarunta goma sha biyu."

"Haka Goggo za ta yi ta saka mata albarka don ko ta ce ta bar mata in ta gama hidimar babanta za ta yi, Amina ba bari za ta yi ba. A zuciyarta cewa ta ke,  Don wa nake karatun? Ai don in tallafi rayuwarku ne watarana, to kuma Baba ba shi da lafiya, in na rasa shi ko ke Goggo me ye amfanin karatun nawa? "

"A shekarar Amina ta shiga karamar sakandire, da kyar da sudin goshi, domin duk abin da suke samu a sana ar Goggo a maganin Babansu da abin da za su sanya a bakin salati yake karewa, an tattaro"

"Tantabarun babanta na kasuwa an jibge musu a gida, ita ke kula da su."

"Wani zubin sai ta zauna tana mamakin Kawu Sule, tunda ya yi kudi ko gaida Yayan nasa da jiki ya daina, matarsa Atika ita ma halinsu daya, daga su sai  ya yansu uku suke rayuwarsu, ya manta da nakasasshen dan uwansa, wanda shi da ya samu nasa rufkin asirin sai ya dauko shi ya kawo maraya, ya yi masa silar tsayawa da kafafunsa. Ko takardar magani aka ba su a asibiti in magungunan masu tsada ne ta kai masa, ya soma lissafo mata matsalolin da suke ciki ke nan shi da nasa iyalin, dole suka hakura suka daina kai masa."

"Tana aji biyu na sakandire, mai yanke buri da soyayya ta yanke tsakaninta da mahaifinta. An ce idan ajali ya yi kira babu makawa sai an tafi, wannan haka ne, amma mutuwar Malam Mas ud rashin kulawa da rashin magani, ko gashin kashi da ake masa gagara ya yi, ta abin da za su ci kawai suke. Goggo sai dai ta tayar da shi ta ba shi abinci, ta kwantar. In ya yi lalura ta tsaftace"

"shi, hannun ma da kafa da suka soma warkewa bayan barinsu gadon asibiti daina motsin suka yi saboda rashin magani da (contineous treatment). Allah ya jiqan Malam Mas ud."

"Misalta halin da Amina ta shiga na rashin mahaifinta ba zai fadu ba, kwananta bakwai tana zazzabi mai tsanani, Goggo ta dage da yi mata addu a ba dare ba rana, kada rashin ya yi mata yawa, ba ta da kowa a Nigeria sai su, domin tuni iyayenta suka koma kasarsu Sirrleone. Da taimakon Allah Amina ta samu, amma fa da kullaci a ranta na kanin Babanta Alhaji Sulaiman, da kawun mahaifinta Malam Bilya, wanda ko gaisuwa bai zo musu ba, a cewarsa ba ruwansa da bakin haure, Mas udu lokaci ya yi ko daga can inda yake ya yi masa addu a Allah zai karba."

"Kafin rasuwar mahaifinta ne Allah ya hada Goggo da maraya Ilya, sun yi zaman mutunci da iyayensa kafin Allah ya dau ran mahaifinsa, har yanzu kuma mahaifiyarsa Zulai suna mutunci da Goggon, shi ya ba ta"

"shawarar ta kara wata sana ar bayan itace da kananzir tunda yanzu lokacin zafi ne kuma tana da freezer katuwa, shi zai rinka kai mata makarantu. Ta shiga wani shiri na koyon sana o i da gwamnatin Bauchi ta shirya karkarshin ma aikatar ci gaban mata, tsawon wata guda aka ba su jari mai tsoka, da shi ta sayi freezer din, ta kuma ja jarin zobo da kunun ayarta masu shegen dadi da tsafta. Duk unguwar ma a wajenta ake saye bayan makarantu da ake kai wa da sauran wuraren hadaka na mutane, Ilya ya samu taimakon wasu yaran guda biyu inda suke raba kafa. A gefe kuma sana ar itace da kananzir ita ma tana nan. Dakin soro wanda Sule ya zauna a nan Ilyan Goggo (kamar yadda Amina ke kiransa), nan Goggo ta bar masa yake kwana domin ta yarda da hankali da amanarsa."

"Wani lokacin Amina in suna tadi da Goggonta ta kan ce,  Goggo da fa a ce ni likita ce, kuma na karanci lalurar Babana, da fa yanzu bai mutu a gida cikin ciwo ba,"

"zan dinga samun albashi in sai masa magani, in kuma dinga duba shi da kaina ."

"Goggo kan ce,  Kul Amina! Kada ki yi sabo, kullu nafsin za ikatul maut, in sa i ya yi dole sai an tafi, likita bai isa komai ba ."

"Amina kan ce,  Haka ne Goggo, amma insha Allah zan yi karatu mai zurfi Goggo, zan karanci lalurar da Babana ya yi domin jinyarta sai mai hakuri, imani, juriya da sadaukarwa. Idan na tuna yadda kullum Baba ke sa miki albarka, da roka miki aljannah, sai bakin cikina ya ragu domin hakika kin rabauta. Goggo za ki taimaka min in yi karatun? Ba za ki ce aure za ki yi min ba? "

"Goggo ta yi murmushi,  Karatu ai ba ya hana aure Amina, sai dai ki ce sai in mijin bai zo ba, in kuma ya zo to za mu yi sharadi ko da gaban alkali ne, zai barki ki ci gaba ."

"Amina kan zumburo baki,  Ba sai na kula su ba balle su zo din? "

"A zuciyarta ta ke fadin hakan, don a dabi arta ba ta ja-in-ja da Goggon nata. In"

"ta fadi abu wanda bai yi mata ba shiru ta ke yi, hatta Goggon ta gane hakan."

"Amina an gama aji uku na karamar sakandire suna jiran fitowar sakamako, (double promotion) aka yi mata saboda kokarinta, ta zana (placement) tana shekara sha uku. Jarrabawar ta fito, ta ci makarantar  yammata ta gwamnatin tarayya da ke Bajoga (Gombe)."

"Amina ba ta samu tafiya makaranta a shekarar ba, saboda ana kashe kudi matuka ba kamar ta gwamnatin jiha inda ta yi ba. Ita ba ta ma san ya akai aka tura Amina wannan makarantar ba, maimakon ta gwamnatin jiha inda ta ke, wannan kuma kokari ne da Malaman Amina suka yi don a cewarsu ba a barin masu (Extraordinary talent) irin Amina su yi ta bata lokaci a kan karatu. Goggo ta daure ta kai ta can din, in har tana da hali."

"Goggo da Ilyanta suka zauna suna shawara, Goggo ta ce,  Ka gani fa Ilya, ni fa tarin aure nake mata in na ce wannan makarantar mai tsada zan kai ta me za mu"

tara? Ga shi da alama ita ma ta makala zuciyarta a kan makarantar .

"Ilya ya ce,  Goggo hakura da tarin auren ki ba ta ilmi, ba abin da ilmin da za ta yi ba zai saya mata ba na auren, ki bar maganar auren a hannun Allah. Ko da mun san Kawu Sule ba zai yi ba, ni na gaya miki Allah zai kawo wata hanyar daban. Sannan ga wata shawara, dazu wani abokina yana da kanti a cikin jami ar Tafawa Balewa ya gaya min in shawarce ki, ko za ki iya a dinga yin cincin mai nama (meat pie) da kek (cake) mai kyau mu dinga kai wa  joints na cikin jami a, kunun Aya da zobo a dinga durawa a tsaftacciyar robar lemuka, in har za a jura wallahi akwai samu sosai. Shi zai rarraba musu in na kai, da an siyar in karbo kudin ."

"Goggo ta ce,  Ga shi Amina makarantar kwana za ta tafi balle in samu mai taimaka min ."

"Ilya ya ce,  Mai aiki za mu dauka babba, ni ma zan shiga cikin aikin, kuma in mun yi mai yawa ba kullum za mu yi ba sai"

bayan kamar kwana uku-uku in an karbi kudin wanda aka sayar .

"Goggo ta ce,  To ka gaya wa Zulai, (tana nufin mahaifiyarsa) ta cigita mana mai aikin ."

"Cikin sati daya Zulai babar Ilya ta samo wa Goggo mai aiki, bazawara ce mijinta ya rasu ya barta da yara hudu sunanta Talatu, neman aikin aikatau ta ke ruwa a jallo, suka hadu suka fara aikin tare, har Ilya shi ma ba a barshi a baya ba, in ka ganshi ya takarkare yana murjin (Meat pie) a injin taliya sai ya ba ka dariya, duk don Aminarsu ta samu ta yi karatu mai kyau."

"Baba Talatu na da dadin sha ani, ga labarai na ban dariya a cikinta, suna aiki tana ba su labarai, Amina na shan dariya, tasu ta zo daya don Amina akwai son jin labarai don haka ba ka raba ta da rediyon Goggo kullum, ta murdo nan ta murdo can, tana jin me duniya ke ciki."

"Sana ar ta Goggo sai sam-barka, ta fara da hannun dama, ba ta ajiyar kudi a gida, adashi ta ke zubawa. Bayan ta fidda"

"hakkin Ilya da Talatu da sauran yaran da Ilya ya samo suke taimaka masa. Amina na kula da Tantabarunta don yanzu aiki ya yi musu sauki, tun bayan samun Baba Talatu. Ita ta ke wanke-wanke da shara, har wankin kayan Goggo da Amina ta ke yi, don haka Amina ta samu isasshen lokacin karatun islamiyyarta, shekara guda ke nan ba ta makarantar boko, Goggo na tarin abin da za ta dauki nauyin karatun da shi."

"Amina na son Tantabarunta, don suke debe mata kewar babanta, ko dubu nawa ka ce za ka siya ba za ta sayar maka ba, ga su nan cikin daki guda masha Allah sai hayayyafa suke."

"Ilyan Goggo kan tsokane ta,  Amina da Tantabaru za ki tafi gidan mijinki halan? "

"Duk lokacin da ya ce mata hakan ba za su kara shiri ba sai an yi kwanaki, don inda abin da Amina ta tsana a rayuwarta to a yi mata zancen aure ko miji, don ta dauke su  as an obstacle (matsayin shinge) ga ci"

gaban rayuwarta da kudirin da ta ke da shi a zuciyarta.

"Akwai wata rana da wani dan unguwarsu Danladi ya biyo ta tana tafiya ta dawo daga ajin haddarta, ba ta san ita yake bi ba sai da ya yi mata magana."

" Aminatu, dan tsaya mana, magana nake so mu yi ."

Amina ta tsaya cak! Sannan ta juyo da manyan idanunta ta galla masa harara.

" Amina kin dade kina burge ni, don Allah ki ba ni dama mu shirya kanmu in nemi aurenki, don Allah Aminatu ."

"Su Amina aka yi wani irin tsaki kamar tsaka,  Na yi kama da ire-iren  yammatan da za ka aura ne? ko na yi kama da matar karen mota mara arabi da boko? Ahir dinka da kula ni, wallahi ka kara tare ni a hanya sai na tula maka kasa, ba kai ba ni ka ji na gaya maka, ba kai kadai ba mai aurena ba a haife shi ba wallahi, don haka ka fita hanya ta ka ji na gaya maka ."

"Kalamanta sun yi wa Danladi ciwo,"

 Ashe ba ki da mutunci? Don kin samu an

"so ki? Banza! Wadda ubanta bai bar mata gadon komai ba sai Tattabara, kin yi kadan ki ci min mutunci, insha Allahu sai mijin aure ya gagare ki, da ni ki ke zancen ."

"Amina ta murguda baki ta yi wucewarta ta rabu da shi yana ta masifa, har da kumfar baki. A ranta ta ce,  Ai gara in rasa mijin auren. Ni ina ruwana da wani aure? Duk abin da zai raba ni da Goggona neman tsari nake da shi ."

"Can kuma ta yi kwafa, ta girgiza kai,  Wai ubana bai bar min komai ba sai Tattabaru, ya bar min komai kuwa tunda ya sanya ni a turbar neman ilimi, Tantabaru kuma arziki ne na gode wa Allah, na gode wa Babana da ya bar min su a matsayin gado, wani me nasa uban ya bar masa? "

"Tana nufin Danladin, Amina fa akwai tsiwa ta rashin arziqi in dai a kan za a ce ana sonta ne. in ban da wannan za ku zauna lafiya cikin kwanciyar hankali. Ko Goggo ba ta gaya wa yadda suka yi da Danladi ba, don ta san fada za ta yi mata."

*** *** ***

"A yau Goggo ta dau adashinta na kudi naira dubu dari da hamsin. Ta soma sayayyar kayan abinci wanda dan makarantar kwana ke bukata, ta shake (Ghana Must Go), Amina ta shirya kayanta, Ilya ya yo musu shatar taxi su uku har da shi, wadda za ta kai su har cikin FGGC Bajoga."

"Da suka shiga suka nemi ofishin Principal ta lokacin, Hajiya Aishatu Dukku. Suka mika takardun

Please Login or Register in order to submit comment