You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za ayi ko kunya ba aji ba tunda yanzu ma anfara yin wayar".


Amnah tasa dariya sannan tace"momy kenan".


Sunata aikinsu suna fira sai ga momyn amnah ma ta isa akacigaba da aiki.


Fayal tana zuwa daki ta amsa wayar tare da fadin"Assalam alaika".

Amsard yace"wa'alaiki salam .

Fayal tace"good morning honey".

Amsard yace"morning my princess.
Fatan ranar nan tamiki kyau kamar yadda fuskarki take".

Fayal tace"da ikon Allah mijin kirki
Da fatan dake da"azo domin ina bukatar ganin kyakkayawar fuskar sarkinah".

Amsard yace"uhumm bayan sunce baza azo dani ba uhumm ni kuka ma zanyi".

Fayal tace"uhummm haba sarkina karkayi kuka kayi hakuri kaji kasan me kyau baya kuka".


Amsard yace"uhummm ni a"a sai nayi fah'.

Fayal tace"uhummm uymmm toh muyi tare uhummmm uhummmmm".


Amsard yace"wayyo rufamin asiri sarauniyata karkiyi kuka ai inwani ne ma yazubarmin da hawayenki sai na zubarme da idonma gaba daya".


Fayal tace"toh promise bazakayi kukan ba".

Amsard yace"i promised sarauniyata.


Fayal tace"tanx my sarki.


Alhaji yasa sahala takira amsard tazo tasami amsard nawaya tace"yaya alhaji yana kiranka".


Amsard yamata alama da hannu da nufin yana zuwa.


Amsard yacewa"fayal byeee sarauniyata alhaji nakirana".


Fayal tace"owk byeeee miss you take care".


Amsard yana zuwa alhaji yacemasa gasu alhaji babbanan sun iso kazo kai zakayi musu jagora zuwa jigawan.



Amsard yaji dadin jin hankan sose amman haka yaboye azuciyarsa gudun kar ace yayi rashin abin.




Abangaren fayal kuwa suna gama waya taje kichin aiko ta tarar momyn amnah ta iso.



Momyn amnah tasa fayal agaba sai tsokanarta take.


Fayal kuwa takasa magana gashi amnah da momy sai dariya suke mata.

*PAGE* 52.

-------------------------------------------------------------------------


Amsard ne ke tuka su
Sunyi nisa atafiya sannan yashiha gidan mai domin kara me amotar alokacin ne yama usman text cewa"muna hanya fa dani akazo inmun kusa dan ma magana muhadu agidan su fayal din".


Alokacin daya tura text dai dai da gama sa man da ake hakan yasa suka cigaba da tafiya su Alhaji babba kuwa sai hirarsu suke amota .
Insuka ma amsard magana sai dai yayi murmushi in nabada amsa ne sai yabAsu.




Su momy sun kammala kome hakan yasa sukaje suka kara wanka kowa yaci gaye sannan suka fara shirya abincin acikin flas da dish.


Adai dai wannan lokacin su amsard suka iso .
Usman ma ya iso domin amsard yakara masa text din.



Usman ne yafara shiga yasanar wa da dady sun iso dama shima dady yakira dadyn amnah suna xaune jira kawai su amsard su iso hakan yasa yace"a madallah kushigo mana ".


Su Alhaji babba suka shigo sunyi gesuwa ta mutunci sose da dady kamar sun san juna hakam ba karamin dadi yamusu ba .

Bayan sun gesa ne dady yasa akaturo amnah .
Amnah tana zuwa yace "yauwa damuyi maganene kikai shi bakwon nako dayan falon kwa gesa achan".

Amnah tace"to tare da fadin muje to".

Amsard da usman suka bita tashiga dasu falo.


Sannan ta koma ta sanarwa da momy akan akai musu abinci.

Amnah tace"momy fayal takai wani karamin falo ni dan kai na dady .

Momy tace"owk".

Aka kira fayal takai abinci .

Fayal tace"uhumm momy nifa kunya nkeji".

Momy tace"a basu sanki ba ma".

Fayal tafara shagwaba aiko momyn amnah tace"maza dauka kikai amnah kema dau naki.



Ba musu dukansu suka dauka domin sun san halin momyn amnah atsaye take.



Abangaren su alhaji kuwa
Alhaji babba yanemawa amsard auren fayal kuma dadyn amnah yabasu tare tabbacin ba bata lokaci za ayi bikin.


Sunyi farinciki sose ana cikin hakane amnah takawo musu abinci suka fara ci cikin nishadi.





Fayal tana zuwa kawai taga abin mamaki wai amsard ne zau ne dan ita ko ganin usman m batayi ba.


Ta sake baki kawai tana kallonsu.

Amsard sai murmushi yake mata.
Usman yace"yadai amaryar mu ki karaso mana.".

Sai alokacin fayal tagane ashe ba amsard vane kadai.



Tayi murmushi tare da ajiye basket din abincin.

Sannan tazauna tana fadin"sannun ku dazuwa".
Usman yace"yauwa amaryar mu".

Fayal ta ce"ina hininku".
Amsard yayi sauryn cewa lafiya lau" .
Usman yace"kai mallam adai bary na amsa ko?


Amsard yace"aa barni mallam gwara na amsa abina".


Fayal tace"uhumm wato da kacemin barakazo ba ko?.

Amsard yayi murmushi sannnan yace",ai surprise nakeso namiki neh".



Fayal tace"ysssn zakayi bayani amman dai ga abinci kufara ci".


Fayal ta zuba musu abincin tare da musu bismillah.


Usman yace"toh nidai akwoshe nake uwargida tacikamin ciki da abinci.


Fayal tace"haba dai kaci mana banda fulako fah'.

Usman yayi dariya sannan yace"ai kigodewa Allah akwoshe nake da sai nacinye abincin nan duka.


Fayal tayi dariys tare da fadin lallai kam.


Amsard yace"uhumm nito kizo muci ".

Fayal tace aa nifa nakwoshi.


Amsard yace",uhummm uhummm ni wallahi sai kinzo danci".


Fayal tace"uhymm ni aa kaci".



Usman yabude baki tare da fadin"laaaaaa agaban nawa?
Toh bara nabarku .





Amsard da fayal suka sheke da dariya atare .
Domin sun sunmanta ma dashi awajen.




Niko nace kwaga masoyan asa....



Amsard yace"au mallam daman kana nan nsh"

Usman yace"ai baka tuna dani ba kam.


Ahaka sukata zolayar juna har sukaci abincin.


Su alhaji sun tsayar da auren nan da karshen wata .



Sukayi sallama tare dasaawa akira musu amsard da usman dasu koma gida.


Fayal tunda taji maganar tafiya tafara shagwaba akan amsard ba zai tafi ba.

Usman yace"yoooo kwana nawane?
Ai munkusa hutawa da wamnan shagwabar".


Dakyar amsard yalallaba fayal ta hakura.

*oh su fayal anzama yar love*


Suka rabu cikin farinciki da begen juna.

*PAGE* 53.

------------------------------------------------------------------------

Su amsard suka kama hanyar komawa jigawa.

Ita kuwa fayal tana komawa momy amnah tasa ta agaba tana da anki zuwa amma tunda akaje aka hango ango an labe.


Fayal takasa zama dan kunya.



Ahaka rayuwarsu fayal da amsard takasance arana sai suyi waya sau goma ko fima .



Yau yakasance saura kwana biyu biki.
Dan haka gobe sa lalle kuma za ayi kamu.


Amsard tuni ya iso jigawa gidan usman ita kuwa AmeenAh tuni takoma gidan su fayal domin shirye shirye da hike fayal bata da wasu kawaye Ameenah da Amnah ne sai kuma kawayen amnah na skul da suka gaiyata.





Washe gari
Anata chukuchukun biki
Lokacin tafiya kamu yayi.
Fayal tasaka jan doguwar riga tare da golden din rosil da takalmi tare da pos dinta.


Sukuwa kawayen amarya golden din kaya suka da jan dan kwali.

Amsard ma jan kaya yasa tare da golden din takalmi da hula.

Abokanansama golden din kaya sukasa


Agaskiya abin nasu yatsaru ba sai nabata lokaci wajen muku bayani ba.


Anfara kamu lafiya sannan akasa fayal a lalle tare da amsard .

Ankira amsard da fayal suyi rawa fayal ta kame kam
Shiko amsard yabawa mutane mamaki.
Yadunga tikar rawa sai vedio akemasa wasu kuma na masa manni.


Ahaka aka kammala cikin farinciki.




Washe gari yakasance daurin aure dan haka dun bun mutane sun sheda aure fayal da amsard.




************

Rayuwa suke cikin farin ciki da zaman lafiya tare da annashuwa.
Kowa yana kyautatawa juna akullum suna gundun bacin ran junan su .

Anacikin haka fayal tasamu ciki.
Tasamu kulawa agurin amsard kamar yadawo da cikin jikinsa yake.

Ita kuwa fayal ansamu damar shagwaba sai wadda ta karu.


Anacikin haka fayal ta haihu lafiya tasamu yarta mace.

Wace akasamata sunan hjy momyn amsard
Ana kiranta da *ASHNAH*




*ALHAMDULILA NAN NAKAWO KARSHEN LITTAFINA MAI TAKEN 'BABU RUWAN SO' BANSAN IYA YAWON GODIYA DA ZAN NUNAMA D'UNBIN MASOYANA BA, NAGODE KWARAI DASO DA KAUNAR DA KUKA NUNA MA LITTAFINAN, ALLAH YABARMU TARE........**THANKS ALOT ALL MY FANS.....LOVE YOU SOOOOO MUCH*💋*Godiya ta musamman ga duk 'yan group d'ina, dakuma 'yan uwana writers nagode sosai Allah yasaka da alkairi da zumunci da san da kuka nunamin.*_*Jinjina Gareku ' yan Zamani Writer's Association nagode kwarai Allah ya kara d'aukaka*_My fans sai kunjini a sabon novel d'ina nan gaba me taken *KUCHAKAR KISHIYA*


*Ur"s preety xayeesherth*💖

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment