You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa kuzaku rasa naku rayuwar" juyawa yayi ga abdud Shakur babban nahannun damanshi yace " kaida jakadiya abashiyya amanarta na hannunku ku kareta daga sharrinsu tanzarzar karda kusake waninku yayi gigin fada mata ko ita wacece harse lokacin karfin iko zefara bayyana ajikinta itada kanta zata gano ko ita wacece kuma tabar duniyar bil adama takoma masarauta domin baku kariya " yagama jawabinsa yaname juyawa gasu baba " yace iname nemar afuwarku daku yafemin dan banasan inmutu da hakkinku akaina dan Allah kuyafemin yarku tana cikin kariya babu abinda zesameta sekun tabka wani babban kuskure dazesa sufara farmakanta! Nan ne itakuma zata fara taka matakin rabuwa daku" cikin tsoro baba yace" menene wannan kuskuren dazamu kiyaye " domin su gaba daya sun gama tsorata dasu " budan bakin sarki abdud daar yace " ko wani irin hali zaa shiga karku yarda sarauniya takai dare awaje inkuma hakan yafaru to sukuma zasu fara farmakanta da dukkan karfinsu " jiki asanyaye baba yace zamu kiyaye in sha Allah kallon fuskanta mama sukayi wacce har alokacin kuka takeyi jakadiya abashiyya tace " sumayya kuyi hakuri ku gafarta mana dole zamu kasance daku har tsawon sanda sarauniya zata koma gunmu zamuta bata kariya da rayuwarmu " watsa mata harara kawai mama takeyi itakuwa abashiyya se murmushi takeyi mata ganin lokaci nakurewane yasa sarki abdud daar yace" bakuce kunyafemin ba dan nasan mutuwa zanyi ba lallai musake haduwa ba" hada baki sukayi wajen cewa munyafe maka duniya da lahira murmushi gaba dayansu sukayi, lokaci daya dukansu suka bace batt komawa masarautar sukayi suka samu anmusu taasa sosai shahada sukayi sukaci gaba da yaki cikin rashin saa tanzarzar yayi nasaran kashe sarki abdud daar har lahira, zagaye masarautar sukayi kaff basu samu jaaazana ba hakan yasa afusace sukabar nasminaya.
Bakaramin takaici sukayi ba da mutuwar sarki da matarsa da danshi ba sunji badadi sosai babu abinda yake kona musu rai kaman isukaga kujeran mulkinsa babu kowa akai tunsuna boye musu gaskiya har suka gaji jakadiya abashiyya da abdud Shakur ne suka fito suka musu bayanin kan cewa sarauniyarsu na nan zuwa garesu nan bada jimawa ba sunyi farin ciki dajin wannan maganar haka suka dibi dakaru fiye da dubu zuwa ga gidansu sarauniya domin bata kariya.

Wata bakwai ciff_ciff mama tafara nakuda aikuwa adaren ranan jakadiya ce ta karbi haihuwar ganin fuskan sarauniyarsu dakuma bayanta nadauke da zanen tambarin masarautar su (tattoo dake bayan fanan) yasata shiga cikin farin ciki mara misaltuwa daduk masarautar nasminaya, duk data kasance bakwai ni amma tafi wani dan wata taranma girma dakuma kuzari jakadiya ce tabukaci da abawa sarauniya nata dakin daban saboda suji dadin kula da ita dukda basaso haka suka ware mata dakinta daban ranan suna yarinya taci suna Fatima suka mata lakabi da fanan, ahaka tadinga girma dawasu abubuwan mamaki atare da ita Kuma koda wasa basa yarda tayi nisa da gida dazesa takai mangrib kansu daya da suhaima yar gidan kabiru.
___ tunda takai shekara 10 kuma wayan nan abubuwan al'ajabin suka dena bibiyarta kawarta daya dal itace amira, fanan nada shekara she uku aduniya mama tasake haihuwar ya mace suka samata ilham (auta) time din kuma su usman suka gama makaranta , haka fanan da Amira suka girma harsuka gama secondary school dinsu tare akasamo musu addimission a garkuwa school of health lokacin suna aji hudu a islamiyya, dake 2yrs program ne suka gama dawuri sukayi graduate batare da bata lokaci ba baban Amira yasamo musu aiki a asibitin specialist suka fara aiki, akaxo akayi auren anty firdausi, babban abinda su baba suka fara lura dangane da fanan shine babu wani namijin dayataba tunkararta da sunan yana sonta abun yadaure musu kai Sosai amma haka sukayi shuru.


Wannan shine takaitaccen tarihinmu cewar baba ba karamin girgiza sukayi ba dajin haka abin yabasu mamaki fiyeda yanda baa tunani gyaran murya me martaba yayi yace " tabbas fanan baiwar Allah ce wacce batasan komai ba ta cancanci girmamawa da farantawa kafin tabar duniyarmu domin ni inada labarin nan domin kafin sarki abdud daar yabar duniya Abdud Shakur yasameni yafadamin abinda yafaru dukda bansan waye sarkin nasu ba amma na tausaya musu matuka gashi bamuda hanyar taimaka musu sede nasa akata musu adduo'i! Nasan abdud Shakur ne alokacin da natafi aikin hajji nida iyalaina muka hadu dashi muka fara abokantaka be boyemin komai ba yafadamin shi jinni ne hakan bedameni ba mukaci gaba da zumunci duk sanda yasamu lokaci yakan kawomin ziyara ,ranar wata jummaa ne cikin tsohon dare yazomin amafarki naganshi acikin mawuyacin hali nan ne yake sanar dani abinda suke fuskanta yakuma bayyanamin kancewa sunyi sabuwar sarauniya ashe fatima ce Allahu akhabar " azaad de jinsu kawai yakeyi shidama tunda yaga fanan yagane bawai wani abu bane ajikinta itadince dakanta duk da bawai yayi believing da wayan nan abubuwan bane adduah yadingayi Allah yasa su shashantar da maganar auren. Haka suka cigaba da tattaunawarsu, Abba yace " ai dah nakowane Allah Ubangiji yakareta dakuma al'umman musulman duniya daga sharrinsu" amsawa sukayi da Ameen fara raba goro akayi ganin da gaske sukene yasa azaad cewa " Abba amma kasan dacewa akwai alkawarin aure tsakanina da aneesa " Abba zeyi magana me martaba yarigashi da fadin" karka damu aikana da daman dazakayi hudu" dariyar shakiyanci yaseer yasa. Shuru yamusu yana sake_saken aranshi, haka aka daura auren azaad muhammad mainasara da Fatima muhammad Umar akan naira dubu dari biyu lakadan ba ajalan ba nan take suka fara gaggaisawa da juna suna taya juna murna bakin ciki kamar zekashe azaad afusace yamike yafita a falon bin bayanshi doctor ammar da yaseer sukayi. Su ya Usman kuwa tunda sukaji wacece kanwarsu din gaba daya walwalarsu taragu barinma insuka tuna zata tafi tabarsu wata rana.

Bada umarni me martaba yayi akira mishi matan gidan kiransu ya al ameen yaje yayi suka fito danduk wainar da ake soyawa basu saniba zama sukayi suna gaida me martaba kallon fanan da har time din take kwance akan kafadar ummi yayi gyaran murya yayi yabude taro da sallama " Fatima naji duk wani abinda yafaru daku iname baki hakuri da lefin danmu yashafeki amma kisani kaddara bata canzawa sede tadau lokaci " haka de yamata nasiha me ratsa jiki ita da gaba daya jamaar dake falon daga karshe yace " se abu nagaba yau aka daura miki aure keda azaad domin kutsira daga kazafin da akamuku " dagowa fanan tayi dasauri tana kallon me martaba dan san gasgata maganar daya fada wani azaad din yake nufi ................

Alhamdulillah nan nakawo karshen book 1 da izinin Allah .
via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD











https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe

πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺



Story & Written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹)



Da sunan Allah me rahama mejinkai πŸ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen πŸ₯°πŸ€Ž






Masha Allah mundawo hutu da izinin Allah.






Book two πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š







꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂




&_____________________________________&




Page 3️⃣1️⃣





Dagowa fanan tayi dasauri tana kallon me martaba dan San gasgata wani azaad din yake nufi, gyada mata kai me martaba yayi domin tabbatarwa tunani tafarayi taya hakan ze kasance Mr azaad din da bawai sona yakeyi ba zasuce sun mana aure innalillahi wainna ilaijiraji unnn yah Allah Ina rokon ka daka bani iKon cinye wannan jarabawan. Ummi tarasa farin ciki zatayi ko akasin hakan tayi matukar jin dadin wannan labarin domin dama burinta bewuce fanan tazamo surkantan taba gashi Allah ya amsa adduah ta, amma abin tambayan anan shin fanan zata amince da wannan auren kuwa . Mama kam ji takeyi lamarin kamar amafarki cikin awowin dabasu wuce uku zuwa biyu ba har an tabbatar da fanan amatsayin matar aure lallai baa mamaki da iKon Allah me kowa me komai mai tsara komai ayanda yaso kallon fanan kawai takeyi tana tuna zata koma wani gida tayi rayuwa nan take taji wani irin kewarta yakamata, ganin tayi shuru kanta akasa tana wasa da yatsun hannunta ne yasa baba cewa " Fatima nasani ke yace me biyayya ga iyayenta bakya taba sabama umarninmu shisa akoda yaushe nake matukar alfahari na kasancewarki ya agaremu , wannan auren da akayi bawai anyishi bane dan kuntatawa daya daga cikinku bane ah ah! Anyi wannan auren ne domin kare mutunci da martabanku dakuma namu gaba daya, zaku iya fitowa duniya kununa musu kudin ma'aurata ne hakan shikadai ne ze wanke sunanku a idon duniya! Kuma iname tabbatar muku da sesun nemi afuwarku, auren nan da akayi yana daga cikin kaddarar rayuwarku Allah yariga daya kaddara azaad shine mijinki kema kece matarsa kiyi hakuri ki rungumi wannan auren in sha Allah zakiga alkharin dake cikinsa Allah yamuku albarka "
She's speechless gaba daya kalaman baba sun gama kashe mata jiki tama rasa takamemmen mezatace innalillahi wainna ilaijiraji unnn kawai take iya furtawa acikin ranta ahankali tafara samun nutsuwa.
Gaba daya tausayinta yakamasu Abba ne yace " Fatima kifada mana shin kin amince da hakan dan bazaa taba miki dole ba munsan dole zakiji wannan lamarin awani iri amma munyi hakan ne saboda wanke sunanku" kanta akasa tana wasa da kyawawan yatsunta dasuka kasance chocolate color with her sweet voice tace " na amince " basuyi tsammanin hakan ba amma dasukayi laakari da fanan yarinya ce me biyayya ko da batasan abu bazata taba musawa ba kokuma taki bin umarninsu ba, alhamdulillah sukace atare yaseer ne yace " yanzu abinda zefaru asamu ashawo kan azaad inyaso zuwa gobe se ashirya hira dasu agidan tv " jinjina kai sukayi alamar gamsuwa da maganarshi , cigaba da magana yaseer yayi yana kallon faisal" kashirya appointment da BBC news dakuma NTA domin sun dade sunason hira dashi Allah beyi ba seyanzu da dalili yazo nasan zasuji dadin wannan maganar " " to shikenan zanyi hakan yanzu base anjuma ba " aikuwa yana gama magana ya lalubo wayarsa yayi dialing number customer service na BBC news macece ta daga tace " hi, am Jenifer thank you for contacting BBC news how can I help you?" Maida mata da amsa yayi " by the way my name is Faisal adamu I am azaad the billionaire official secretary luckily I want to inform you that your appointment has been approved " wani irin ihun farin ciki tasa tana " heyyy thank you jesus " bama ita kadai ba hatta sauran ma'aikatan dasukaji labarin murna kawai sukeyi dan abinda suka dade suna jira kenan yin hira dashi bakaramin daraja zedagawa gidan tv suba domin he's the most famous person da kowan ne suke bukatar tattaunawa dashi. Haka faisal yakara kiran NTA yasanar dasu kafin yakashe wayarsa. Duk shuru sukayi suna jiran suji abinda me martaba zece

____ " alhamdulillah abu nagaba danakeso infada duk da kunsani kuma shine! duk yarinyar da aka daura aurenta tana tarewane agidan mijinta a ranar inbawai akwai wani kwakwaran dalili bane zehanata tarewa" yajuwa ga su ummi yacigaba" Aysha yau base gobe ba ku fara shirin daukan amarya banyan sallah isha " daf!daf!daf gaban fanan yatsinke ta shiga uku yanzu ana nufin bazata kwana agidansu ba wani irin rayuwa zatayi atare da Mr azaad. Abinda baba yake tunani yazo daya da abinda mama da su ya Usman suke tunani taya zaayi amarya ta tare batare da iyayenta sun mata kayan daki daduk wani abinda ake bukata ba, suna bukatar abasu ko nan da gobe ne saboda bawai basu dashi bane Allah ya hore musu abinda zasu mata irin na yar gata ma kuwa.
Baba ne ya nisa kafin yace " me martaba agafarceni, banqi ta taka ba domin kai amarya aranar da aka daura aurenta izuwa dakin mijinta bakaramin lada zata samu ba da albarkan aure saboda hakan shine ka'ida ! amma abamu daga yau zuwa gobe wannan auren yazo mana baa kan shiri ba bamu tanadi komai ba in sha Allah daga yau zuwa gobe inyaso se azo adauketa" murmushi irin tasu ta manya me martaba yayi yana kallon yan falon gaba dayansu sannan yace " shin awani ayah ko hadisi kukaji ance kayan dakin mace dakuma duk wani abinda zata bukata agidan aurenta yarataya aka wuyan iyayenta ? To bari kuji abinda kuka manta a musulunce muddin mutum ya auro mata komai yanakanshi daga abinda yakama gida wato muhalli, kayan amfanin gida, tufafinta, shanta da ciyar da ita duk ya tattara akan wuyanka amatsayinka na shugaba agareta! Yanzu ne da zamani yake juyawa yakoma juyi_juyi iyaye suka fara kai yayansu da kayan su gado su setin daki dasauransu amma badole bane wannan kuma yin hakan shike Kara sangarta mazan sukeyin duk abinda suka gadama gadaransu yanzu shine kawai sadaki zasu bada da kayan lefe se gida shikenan amma da su sukeyin komai da komai dakansu bazasu taba kuskuren sakin matansu ba dan haka babu abinda fatima zata tafi dashi gidan mijinta koda kuwa cokali ne " babu yanda su baba suka iya tabbas maganar me martaba gaskiya yafada amma yanzu anawa mata hakane domin gudun reni ko kana nan maganganu.
Abba da ummi kuwa sunji dadin maganar da me martaba yafada domin suma abinda zasu fada kenan yarigasu domin sune da matukar godiya da baba yabasu auren fanan yarinya me hankali da tarbiya babu gidan da bazaayi farin cikin samun yah Kamar taba .
Karfe 5:00 saura Adduah me martaba yayi sosai taro yakare, mikewa yayi rike da sandar shi yana musu sallama su fulani da galadima suma sukabi bayanshi suka tafi, su abba ma fitowa sukayi zasu tafi suka rako su har bakin gate suna musu se anjuma insunzo daukan amarya tare da musu godiya sosai ahaka sukayi sallama . Komawa cikin gida sukayi suna jinjina iKon Allah babu wanda yayi zaton haka awannan lokacin zama sukayi suna dan maida magana mikewa fanan tayi tabarsu afalon bin bayanta sukayi da kallo gaba daya jikinsu babu laka bin bayanta suhaima da amira sukayi dakin akwance suka sameta kanta na kallon saman celling kamar wata me tunani zama sukayi akusa da ita.
Baba ma dakinshi yashiga bayanshi mama tabi dan tanason jin yanda sukayi dangane da fanan.


via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺



Story & Written by..
MRS 🌹 ISHAM 🌹


Page 3️⃣2️⃣





_____ " babansu yakamata kafada musu komai dangane da fanan kar azo daga baya abu yazo yacabe " cewar mama dake zaune tana facing din baba , Maida hankali baba yayi gunta yace " haba sumayya ta taya kike tunanin zan boye musu wani abu dangane da yarmu nafada musu komai domin me martaba Shima ashe yanada labarin amma besan wacece takamemmen sarauniya ba " yafadi hakan ayayin da yake bude wata locker dake jikin wardrobe dinshi kudi yafito dasu akalla sun kai dubu dari hudu " Kinga wannan kudin ki kira firdausi kibatasu taje kasuwa tasiyowa fanan kayan sawa dakuma akwatin da zaa sasu amma banda atamfa shi innaje shago zabayar wa tela yamata dinki " yamika matasu ahannunta karba tayi tana jujjuya kudin ahannunta hawayen dake kokarin zubowa a idonta ta mayar dasu tana fadin " yanzu kenan fanan ayau zatabar gidan nan tun kafin ta tafi nafara kewarta bansan wace irin rayuwa yata zatayi atare da wanda bayason taba " shikanshi baba abin yadameshi amma hakan shine ze samo musu sauki , girgiza kai yayi kafin yace " karki fadi haka aure anriga da anyishi amatsayinki ta mahaifiyarta adduah kawai zaki mata na zaman lafiya agidanta " jiki asanyaye mama tace" hakane Allah yabasu zaman lafiya " ameen.

____ " haba azaad sekace baka da tausayi dan saboda kaine fah wannan abun yafaru da yarinyar nan Yakamata da akayi maganar auren nan kabada goyon bayanka dari bisa dari amma ko kunyar iyayenta bakaji ba afili kace bakason yarsu " cewar yaseer da dawuwansu kenan yashigo part din Azaad, duk wannan maganganu dayakeyi azaad najinshi kalla bece mishi ba shikadai yasan abinda yake damunshi duk bazasu fahimmce shi bane, tashi yayi yazauna yana kwabe fuska yace " yaseer nasani nasan saboda nine sunan yarinyar yabaci kuma am willing to do anything daduk karfina wajan ganin nawanke sunanta amma aiba dole seta hanyar aurenta ba ! Can you imagine wai kamar ni azaad muhammad mainasara the billionaire nizaawa auren dole unbelievable, bana sonta kwata_kwata kuma banajin zan iya sonta saboda she's still kid to me akwai sauran yarinta akanta and tamin karama , duk inda aka ambaci aure yashiga tsakani to andauki amanarta ne anbaka kulawa da ita, lafiyanta rashin lafiyanta dakuma tarbiyanta se adalci nikuma yanda banasanta banajin zan iyayin daya daka cikin wayan nan abubuwan shisa bazan iya zama da ita ba " tabbas abinda azaad yafada haka shin ze iya kula da fanan ne ko baze iyaba mutumin da ko kadan mata basa gabanshi be masan tayanda zekula dasu ba wani irin tausayin fanan ne yakamashi amma yasa aranshi in sha Allah seyayi iyayinshi naganin ya dedeta tsakaninsu da iKon Allah.
_____ " to yanzu de ba wannan ba kashirya ayau zaa kawo maka amaryaka kazama cikin shiri dan acikin daren nan Yakamata ka angonce " cike da shakiyanci yaseer yake maganar dan yasan yanzu ze fusata azaad, uhmmm kawai azaad yafada yana aiyanawa aranshi inya kusanci wannan jaririyar aiseta kusan mutuwa, Yaseer de tashi yayi yabarshi adakin dan yaga azaad inya fusata zasuyi dauki ba dadi.

Anty firdausi ce da mama, suhaima,Amira,auta afalon suna zaune sunata bubbude kayan da anty firdausi tasiyo da kudin da baba yabada kayane nagani nafada akwati biyu masu kyau abaya ne da akalla zasu kai guda ashirin se wasu fitinan nun kana nan kaya nahutawa dakuma liffaya suma sunkai 20 da takalma da jaka se jewelries nagani nafada kaya de masu matukar kyau suna zaune suna kallon kaya ya usman da ya al ameen suka shigo suma hannunsu niki_niki rike da manyan ledoji na kayan cosmetics daga abinda yayi kan turare, kayan make up, lotion,soaps shower gel, shower perfume etc. Shirya kayan akayi duka a akwatu nan se aka fitar mata da wanda zatasa yau suka gama shiryasu tsaf. Ana kiraye_kirayen sallah mangrib mama tace " firdausi yakamata kitashi kuje ki shiryata kinga lokaci natafiya kar babansu yashigo yasamu baa kammala ba" Daukan kayan dazata sa anty firdausi tayi takai dakin tasameta tana kwance tabawa kofa baya zagayowa tayi gabanta idonta biyu ba bacci takeyi ba , hannu anty firdausi tasa tadagota tazauna murya asanyaye tace kitashi kije kiyi wanka tare da alwala inkikayi sallah sena shiryaki " babu musu tamike tashiga wanka, tayi wankan tadauro alwala tafito daure da towel amma ta rame fuskanta fayau dogon rigar jallabiyarta tasa tadau hijab ta tada sallah seda tayi adduah sosai kamin tadan jabaya tajinginu da jikin gadon . Matsowa kusa da ita anty firdausi tayi tarike kafadarta sannan tace " fanan kidena sawa kanki wasu irin tunani ki karbi komai ayanda yazo miki kuma kikara da godewa Ubangiji yasa hakan shine mafi alkhari domin duk abinda kikaga yasamu bawa to muqaddarine daga Allah , nasan tunaninki ya karkata akan wani irin zama zakiyi da mijinki da bayasonki to kisani wannan abu ne me sauki inkika kara mika lamuranki ga Allah sannan ahankali hankali zakike cusawa mijinki sonki azuciyarshi mu mata inde mukaso babu tayanda bama bi da namiji duk yanda kikaso zaki iya lankwasashi domin namiji zumane seda wuta kisa aranki zakuyi rayuwar farin ciki kedashi ko bakuyi ayanzu ba zakuyi nan gaba zanyi duk iya kokarina wajan tallafa miki kina dani kidenajin wani kunya kinji ko " gyada mata kai tayi domin kalamanta sun kwantar mata da hankali tadanji relief, karajin kwarin guiwa tayi.

Jin datayi anshiga sallan isha ne yasa ta tashi ta tada kabbarah bayan ta idar ne anty firdausi tace mata tazauna agaban mirror zama tayi kamar yanda tabukata miko mata wasu mayuka masu bala'in dadi tayi dan tashafa shafawa tayi tana jin kamshin har tsakiyar kanta light make up anty firdausi tamata karkuso kuga fanan yanda tayi kyau da make up din nan, Mika mata wando na jeans dakuma yellow din body hook me dogon hannu tayi karba tayi tasa bakaramin kamata sukayi ba tab sukamata sunzauna ajikinta sosai hips din nan kamar zasu faso wandon sufito , liffaya anty firdausi tadauko fari sol medan touch din yellow ajiki nada matashi tayi mekyau ajikinta ta mata dauri da dolface yellow gashin kanta kuwa dauresu tayi seya zama kamar gammo dan kunne da sarka tasa mata se awarwaro da abin hanci me dan karamin stone rufa mata liffayan tayi ajikinta tako Ina harda fuskanta sannan tafesheta da wasu mayun turare masu kamshi sosai tabata takalmi white color se hand bag dinta,shiryata tsaff tayi wani irin kyau da fanan tayi mara misaltuwa tafito sakk amarya , rikota anty firdausi tayi tazauna akan gadon tana kokarin rufe mata fuska kenan segasu amira, suhaima sunshigo suma sun gama shiryawa cikin atamfa sunyi kyau sosai zama sukayi akusa da ita suna yaba irin kyaun datayi kamar su saceta sugudu duk yanda takai da basar dasu seda suka dan sata dariya, dan dazunma dasuka shigo dakin dataga zasu dameta kawai tasharesu tajuya musu baya.

Anty amina, anty shayida anty Zainab se zeenat ne zasuje dauko amarya su yaseer da fawwaz ne zasu kaisu duk sunci ado abunsu suka nufi anguwarsu fanan motar uku kawai suka dauka dan baason ayi yawanda zaa gane,bayan su isone suka shigo falon mama suka zauna suna Kara gaisawa mikewa anty firdausi tayi tashige dakin tariko hannun fanan da fuskanta yake arufe dakin baba sukayi domin yamata nasiha

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DDπŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺



Story Written by...
MRS 🌹 ISHAM 🌹










Page 3️⃣3️⃣ & 3️⃣4️⃣



Dakin baba suka shiga tazauna akan sallaya fuskanto ta baba yayi kafin yafara magana " Fatima ni nafi kowa sanin halinki kin kasance me hakuri da juriya dakuma sadaukarwa , to ayanzu ne wayan nan halayen zemiki amfani ke yanzu ke bakamar sauran yan mata bace karki dinga hada kanki dasu domin ke yanzu kinzama babba tunda kika zama matar aure kikama mutuncinki amatsayinki ta matar aure , wani shiga shirgin daba naki ba babu ruwanki! Sannan aure yar hakuri ce duk wasu ma'aurata dakika gani dukkansu hakuri suke da juna domin anriga da anzama daya, yazama dolene se anyi hakuri da juna kiga misali da mahaifiyarki yau shekara ashirin da biyar da aurenmu amma dede da musu wannan bata tabamin ba balle bakar magana mara dadi hakurinta yazarce misali itadin matace tagari to zanso kiyi koyi da ita kiyi hakuri da mijinki ako wani irin hali kikasance meyi mishi biyayya kibishi sau da kafa nan ne zakiga ribar auren dakuma hakuri rashin kunya ba naki bane, inyace kiyi , kiyi inyace bari kibari karki tsaya yana fada kina maida masa magana , sannan mudin kika fita zuwa wani wajen batare da izinin mijinki ba duk taku daya mala'ikun Allah tsine miki zasu dingayi ! Wannan gidan bekai gidan mijinki ba domin mace da gidan mijinta take tunkaho duk abinda ze hadaki da mijinki kizama mace me sirri karki yarda sirrin mijinki yafita sede in abinda yakeyi yazarce ka'idan addinin musulunci nan ne zaki kai kara domin neman solution, Karki manta aljannarki na karkashin kafarsa seya daga zaki shiga dan haka kiwa mijinki biyayya karki saba mishi Allah yamuku albarka yabaku zaman lfy zaku iya tafiya" tunda baba yafara magana taketa sheshekar kuka gaba daya maganganunshi ya ratsata sosai rarrafawa tayi har gabanshi tarungumeshi tana kuka bubbuga bayanta yakeyi yana shafa kanta tare da samata albarka . Haka anty firdausi tafito da ita falo tana kuka mikewa su anty Amina sukayi da niyyar tafiya fitowa mama tayi hannunta rike da wata yar karamar box riko hannayen fanan tayi tabude box din awarwaro ne guda hudu aciki na zinari alamun sundade ba design din zamanin nan bane se sheki sukeyi zurawa fanan tayi ahannun kafin tace " wannan awarwaron dakike gani gadon alhalinmu ne kakar kakatace tabawa kakata lokacin datayi aure itakuma kakata tabawa mama na dazatayi aure nima sanda zanyi aure mamana tabani kinsan metace min " dago manyan idonta dasukayi jaa tayi takalli mama ta girgiza Kai, yar murmushin yake mama tayi tacigaba" cemin tayi duk sanda nahaifi yata tayi aure itama inbatasu, ki kula dasu sosai

Please Login or Register in order to submit comment