You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

TAKWAS*
PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️



***Habiba ta yank'are hak'ora zuciya a jagule tana zuba yak'e tace.

"Ayyo! Ni kam da yake ban tab'a ganinki ba shiyasa ban shaida ki ba,na kan ji
Labarin ki dai a wurin yara,kece mai sai da k'osai da safe ko?


An gayu tace.


" Eh wallahi kuwa,k'osai da awara duk ina toyawa da safe,haka nan ina siyar da
gasarar kunu,dafatan kuma za ku zamo d'aya daga cikin kontoma na ku dinga siya"

Habiba ta rik'e baki tace.


"Kontoma kuma?menene kuma kontoma?

Rauda da ba ta saka musu baki ba sai lokacin ta kwashe da dariya ta dubi Habiba
tace.


" Ke ina jin dai Costomer za ta ce ko?"

An gayu ta buga cinya ta k'yalk'yale da dariya da k'arfi,sannan tace.


"Ai kuwa kamar kin sani K'awata,Kastoma nake nufi"


Habiba kam dariya tayi,daga ganin wannan matar shuda ce bata da cikakken
saiti,domin zama tayi ta dinga zuba musu zance soki burutsu,idan tayi wata maganar
sai ta dubi Rauda tace "Hakane ko K'awata?"

Ita kam Rauda sai biye mata take suna shan Shafta da kwasar dariya,domin ta fahimci
An gayu irin matan nanne masu shegen surutun tsiya,komai ya fito bakin su fad'a
suke yi babu tantancewa.

Habiba dai takaici ya ishe ta,An gayu tak'i tashi ta tafi gashi basu gama hirar su
da Rauda ba,karad'in ta kawai ake ji tana buga zance,sai da ta kusan awa d'aya
sannan wani yaro ya shigo yana fad'in "Wai An gayu ta zo in ji Malam Arabi"


Aikuwa da hanzari ta mik'e ta shuri silifas d'in ta tana fad'in.


"Bari naje na amsa kiran maigida,yanzu zan dawo,K'awata ai zan kuma tarar da ke
ko?"

Habiba ta zaro idanu ta fakaici idanun An gayu ta laftawa Rauda Harara,Rauda ta
gane abin da take nufi shiyasa tayi murmushi tace.


"Ah ah ba lallai ki sameni ba K'awata,wataran za mu sake had'uwa ai,ni ma bani da
nisa tsiran mu layi d'aya ne,ina layin makarantar Daren da mijinki yake koyarwa"
Nan An gayu tace Aikuwa za ta kaiwa Rauda ziyara,suka yi sallama ta fice da
sauri,suka bita da kallo Rauda na dariya sai Habiba da take sakin tsaki tana
hararan Rauda.


Rauda tana dariya tace.


"Wai ni me nayi miki ne kika isheni da harara?ni fa bani na sa mijinta ya jibgeki
yayi miki ganda ba balle kice"


Habiba ta sake sakin tsaki ta tofar da yawu tace.


"Wai ke Rauda baki lura da wani curarren tasono da koriyar majina a hancin matar
nan ba,an ya kuwa kanta babu motsi,babba da ita babu gyara ki dinga fitowa haka ana
kallonki,ni wallahi duk ta tayar min da zuciya ma kamar nayi Amai"


"Kika sani ko mura take yi?" Rauda ta fad'a tana tuntsira dariya.


Habiba tace.


"Kin manta Uwar mura take yi,ko in ce miki frinji ne a kanta k'arewa mura,to ko
muran take yi ma ba za ta dinga gyara hancinta ba?ni wannan da abinci nake ci ai ta
haramta min wallahi,kuma wai a haka ance miji na kira ta zabari k'afa ta tafi,taf!
Wannan miji zai yi kyakkyawan gani,ke daga ganin matar nan kin san ladan noma
ce,k'ila Noma malam Arabin yayi wa gyatumin ta aka bashi ladan ta daga
k'auye,wannan aba haka babu fasali"

Rauda ta keb'e baki tace.

"Karfa ki manta kin saba da zama da k'azamai Habiba,babbar aminiyar ki Harira ma ai
k'azama ce ta bugawa a jarida wallahi,kuma koma ladan nomar ce ba shi yaga zai iya
ba"


Habiba ta kama girgiza kai da Hannu ta na cewa.


"Lala lala al mandudu kalas!billahillazi huwar rahmanu duk k'azantar Harira ba zaki
ganta da tasono da mijina a hancin ta ba,ita dai kawai k'asanta ne bata gyarawa
yake d'oyi da wari,sai kuma d'oyin hammata,kuma kwanakin baya kan abubuwan nan su
faru har turaren tsuguno da miski ta siya gun zahra'u,kinga kuwa ai ta d'akko
hanyar gyara ko…!?

Rauda za ta yi magana kenan wayarta ta soma k'ara,ta bud'e Jakarta ta fito da ita
ta na dubawa,Ashe yayarta ce ke sanar da ita sun zo bata nan suna k'ofar gida,nan
Rauda tace su jirata gata nan zuwa,domin bata yi nisa ba tana kusa.

Tana kashe wayar ta fara k'ok'arin mik'ewa tana gyara mayafin kanta,ta dubi Habiba
tace.

" Habiba bari na wuce gida,yaya Abida ce suka zo bana nan,ni ban ma san da zuwan su
ba wallahi,k'ila yayen D'an ta Imamu ta kawo min Dan jiya mun yi waya da Umman mu
tace min an yaye shi yau za a kawo min shi,to ban ma yi zaton da Uwar D'an za a zo
ba"

Habiba ta sauke numfashi tana mik'ewa tsaye ita ma,sannan ta dubi Rauda tace.

"Wai ni kuwa Rauda ya kuka k'are da wannan tsinannen mutumin mijin Abida?haka kawai
ya zamar da ita k'aramar bazawara haihuwa d'aya,amma dai kun maka D'an iska a kotu
ko?

Rauda ta ce.

" Aikam dai yana nan yana zabga nadamar abin da yayi,kullum yana sintiri akan ta
dawo gidan sa ita kuma ta k'i komawa,Yaya Abida ta sha wahalar wannan
mutumin,kullum fa sai ya sha giyarsa yake zuwa ya tanana mata jikinta kamar wani
d'anyen nama,hmmm…bari na wuce Habiba hirar ba zata k'are ba,in muka kuma had'uwa
ma k'arasa "

Rauda ta fad'a tana yin gaba.

Habiba ta bita har Soro tana yi mata rakiya,suka yi sallama,Rauda ta wuce ita kuma
ta juyo cikin gida ta fara k'ok'arin wanke waken kulelen da za ta yi.




**************




Amina Zaune a tsakar gidan Shafa'atu ,ta tasa Shafa'atun a gaba da d'irmemen cikin
ta haihuwa ko yau ko gobe ta zabga tagumi,a hankali shafa ta gyara zamanta kan
tabarmar da take kai ta yatsune fuska,tana D'an jin ciwo kad'an kad'an kamar me
nak'uda,sai da ciwon ya lafa ta d'ago ta dubi Amina tace.


"Wai ni me yake Faruwa ne Amina?duk na ganki ba yadda na saba ganin ki ba,ko dai
har kin fara shan gashi hannun Sunusin ne?waya gayamiki barno gabas take?kina murna
wai ke kinyi Aure zaki sha soyayya ko?an fad'a miki mazan yanzu mutuncine da su?
tattatun y'an iska ne fa wallahi,a waje soyayya kamar za a cinyeki,da zarar kin
shiga kin zama nama,kinga duk k'ibar nan ta ki ko,idan miji ya minnira miki wani
takaicin sai kin dawo kamar falwaya saboda rama"


Amina ta sauke numfashi ta dubi Shafa'atu tace.

"Ni fa Anty Shafa babu abin da ya shiga tsakanina da mijina kike ta wannan
subad'ad'in,muna zaman mu lafiya wallahi,domin idan dad'i da soyayya suka yi mana
yawa har goyani yake yi"


"Ya Goya wa?" Shafa ta ambata tana zabura har k'ugunta na amsawa,sannan ta cigaba
da magana cikin zare idon mamaki.

"Wai Sunusin ne yake goyaki Amina?Sunusin da na sani me baya kamar allon mayya ta
k'ak'a bayan sa zai d'auke ki kina da girman buhun kwaki uku?sake zance dai Amina"

Amina ta b'ata rai ta d'aure fuska jin maganar Shafa'atu, nan da nan Shafa'atu ta
shiga taitayin ta ganin yadda fuskar Amina ta d'aure,kar taje ta haye tsohon cikin
ta ta saka ta haihuwar da bata shirya ba 😂.

Cikin k'ufula Amina tace.

"Ina ganin mutuncinki Anty Shafa, don haka kar ki sake cin mutuncin mijina
gaskiya,nazo ne na fad'a miki damuwata saboda naga kin fi kusa da ni a halin
yanzu,idan kuma ba zaki saurareni ba ne na k'ara gaba"

Shafa'atu ta yi saurin tare ta da cewa.

"Haba haba K'anwata,kiyi hak'uri wallahi zan saurare ki,menene yake faruwa da ya
sanya ki a damuwa?"

Amina ta yi ajiyar zuciya, ta k'urawa Shafa'atu idanu tace.


"Wani tashin hankali ne yake Neman tunkara ta ina zaune lafiya,jiya Sunusi yake
fad'a min wai Harira zata dawo gidan da nake mu cigaba da zama tare,to kin dai san
Halin Harira,kin ma fini sani tunda tare na ganku,Kuma nima kin san kamar zawayi
nake bani da hak'uri,shine nazo ki bani shawarar yadda zan zauna da ita,don gaskiya
ba zan d'auki rainin wayonta ba,ban auri mijinta ba ma ban d'auka ba balle yanzu?
idan tace zata kawon iskanci za mu ci uwar sabada ne ni da ita ……

Wani irin zaro ido Shafa'atu ta yi,cikin ta ya fara k'ululu,Harira zata dawo?tabbas
za a sha drama,musamman da jiya Kamilu yake bata labarin wai Malam Arabi ma ya dawo
layin su gidan da su Zahra'u suka tashi,tabbas BAHAGON LAYI zai k'ara shiga
chakwakiya kenan …….!




Comment
Share
Vote
pls




*BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️


*BAHAGON LAYI*
(SABON SALO)

*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️

HASSANA D'AN LARABAWA

*BABI NA TARA DA NA GOMA*

PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️


*Kar ku manta idan kun zo karatu ku fara yin fitsari saboda kar a samu matsala ya
kufce kuyi a wando kamar wancan karon🤣🤭sannan a tanadi (Jar Kanwa) saboda ciwon cikin
dariya*🤣🤣😆🤪🤪




"Wai da gaske kike yi Amina?da gaske Harira zata dawo layin nan da zama?" Shafa'atu
ta ambata a tsorace.


Amina ta cigaba da kallon ta cikin mamaki,ganin yadda duk ta firgice,ko menene abin
tsoro a wannan maganar oho!dan haka ta k'ank'ance idanu tace.

"Ya naga wai duk kin firgice ne?maganar da nayi ce ta firgitaki ko dawowar
Harirar?"

Nan da nan shafa'atu ta waske tana Sosa k'eya da cewa.

"Ah ah wallahi babu komai Amina,kawai ina tayaki kishi ne,bana son Harira ta dawo
ta takura miki Dan shegiyar kanta ce wannan matar"

Amina ta tab'e baki ta D'an harari Shafa'atu tace.


"Fad'i gaskiya dai,ko dai kike taya ta kishi tunda k'awarki ce?yo ni wata Harira ta
isa ta takura min a gidan mijina?wadda nanan masai ma tafi min daraja a kanta,ai
wallahi ta dawo mu zuba a gani,shege ka fasa,Idan ta kwantar da kanta muyi zaman
lafiya,idan ta zo da akasin hakan kullum zata dinga cin na Akuya ne a hannu
na,domin ba saurara mata zan yi ba"

Shafa'atu ta rik'e hab'a tana girgiza kai tace.

"Ah ah kar ki fad'i haka Amina,ta ya ya zan taya Harira kishi Dan a cutar da ke?kar
fa ki manta ke K'anwar mijina ce,ita kuwa ba dangin iya ba na Baba sai had'uwar
layi kawai,kinga kuwa ba zan tab'a barin ki Dan na bita ba,kuma insha Allahu ma
lafiya k'alau zaku zauna,Harira ai taga ishara,bayan dahuwar ganda da kika yi mata
ga dahuwar ragadada da yallab'ai me tiyagas yayi mata,ko in ce yayi mana,kinga kuwa
dole ta hankalta ku zauna lafiya"

Amina ta mik'e tsaye tana sab'a mayafin ta tace.


"Atoh dai wannan ya rage na ta,ni dai a shirye nake tsaf da makaman ya k'i na,haka
nan na tanadi nukiliya Wanda zan tarwatsa duniyar ta muddin tace zata yi ya k'i da
ni,amma in ta zo da zaman lafiya ta yiwa kanta k'iyamullaili"
Shafa'atu ta amsa da cewa.

"In sha Allahu ma da zaman lafiyar za ta zo,ina da yak'inin hakan" sannan ta zarce
da cewa.

"Wai gida zaki koma ne naga kin mik'e?"

Amina tace.

"Eh gida zan koma,zan yi wa Sunusi wanki ne?"

"Wanki kuma?yanzu har wanki kike wa Sunusin?cewar Shafa'atu cikin mamaki.

Amina ta jijjiga kai tare da cewa.

" k'warai kuwa,to ba mijina ba ne?ai babu abin da na zan masa ba,kamata yayi na
share masa hawayen sa da suka dad'e suna zuba a dalilin rashin samun mace ta gari"

Shafa'atu tayi murmushin yak'e tace.

"Tabbas haka ne kuwa,Dan kuwa Harira ko D'an tofi bata tab'a wankewa Sunusi ba,wai
bata ga yadda za a yi ta wanke kayan gardi me d'auke da guntun kashi ba"

Takaici ya kama Amina,ta saki tsaki tana cewa.

"Don Allah ni daina yi min maganar wannan dabbar,danni Harira bambancin ta da
dabbobi kad'an ne,jaka jahila kawai"

Shafa'atu tayi muk'us ganin Amina ta fusata kar ta huce a kanta,daga nan suka yi
Sallama Amina ta wuce gidan ta tana cewa Shafa'atu "Allah ya raba lafiya,sai mun ji
kyakkyawan labari don da alamun nak'uda kike yi" ta bar shafa'atu da bin ta da
kallo tana hango yadda zaman Harira da Amina zai yiwu a muhalli d'aya,tashin
balagar D'an tsako kenan….!




******************




Da Sallamar ta ta shigo tsakar gidan,daga can cikin d'aki ta ji ana amsa mata,Dan
haka ta d'aga labulen rumfar ta shiga tana k'ara wata sallamar.

Umman Saratu da ke zaune a tsakiyar Rumfar ta sake amsawa tana fad'in.

"Maraba lale da Hajiya Maimuna, sannu da zuwa"

Hajiya Maimuna ta nemi gefen Umman Saratu ta zauna tana kallon k'afarta da aka
shafe ta da garin magani,cikin tausayawa ta amsa da .

"Yawwa Fatsima sannun ki,ya kika k'ara ji da k'afar ta ki?"

Umman Saratu ta ce .

"Sai godiyar Allah,ga k'afa nan muna lallab'awa tak'i takuwa,kullum Malam yana
hanyar k'auyuka karb'o min magnguna,ban da rubutun da kullum yake min ina sha,to
kin san an ce ciwo farat d'aya yake shiga,sauk'i kam sai a hankali"

Cikin jimami da tausayawa Hajiya Maimuna tace.

"Tabbas hakane Fatsima,to Allah ya mayar kaffara ya baki lafiya,Allah ya yaye miki
wannan ciwon k'afa"

"Ameen Ya Allah" Umman Saratu ta amsa,sannan ta zarce da cewa.

"Baki ga Malam d'in a zaure ba ko?ai baya nan sun tafi wani gida yin saukar
alk'ur'ani,sabon gida ne shine me gidan ya gayyace su shi da almajiran sa domin ayi
karatu a gidan"

Hajiya Maimuna ta gyara zaman ta tace.

"Aikuwa dai ban ganshi ba,sai dai wasu almajiran da suke karatu,yaushe Baba Laminde
tazo daga k'auye Fatsima?na ganta a tsakar gida kan tabarma kamar tana bacci"

Umman Saratu tayi kasak'e,sai can ta dubi Hajiya Maimuna tace.

"Baba Laminde kuma?a gidan nan?

" Eh mana Baba Laminde dai ta k'auye,ba ita ce kwance kan tabarma a tsakargida tana
bacci k'uda na bin bakin ta ba?"

Girgiza kai Umman Saratu tayi,cikin takaici tace.

"Ni rabo na da Baba Laminde tazo garin nan ai an jima,Saratu ce fa take bacci,kama
tayi miki da Baba Laminden ne?"

A zabure Hajiya Maimuna ta dafe k'irji tana fad'in.

"Wace Saratun?kina nufin Saratunki ce ta mommole ta zama tsohuwa haka?bata da
lafiya ne?ko dai cutar k'yanda take? Ta jero tambayoyi cikin gigita.

Umman Saratu ta girgiza kai cike da damuwa tace.

" Yo ban da abin ki Hajiya Maimuna manyan mutane suna k'yanda ne?k'yanda ai sai
yara,lafiyarta k'alau kawai duniya ce take ladaftar da ita,tak'i zaman Aure sai
iskanci iri iri takewa mijin,shi kuma ya gaji ya sako ta,gashi nan har iddarta ta
cika amma ya k'i ya maida ita d'akin ta "

Hankalin Hajiya Maimuna a tashe tace.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, wallahi bani da wannan labarin Fatsima,da
yake na jima bana gari ina Maiduguri ziyarar y'an uwa,amma banji dad'in wannan
magana ba,me yasa kuka bari Saratu take cikin wannan yanayin,na rantse da Allah na
zaci Baba Laminde ta k'auye ce,tana yarinyar ta da ita amma duk tsufa ya sakko
mata,nifa kamar har furfura na gani a gefen kanta,daman an ce tashin hankali yana
kawo furfura Ashe da gaske ne?"

Umman Saratu tayi murmushi tace.

"Haba dai furfura?tatar Koko ta gama yi min,ina ji k'ullun ne ya shafe ta kika ga
kamar furfura,ni kaina da bana tausayin ta saboda ta b'ata mana rai,amma yanzu har
na fara tausaya mata wallahi, haka kawai ma fa tana kwance sai kiji tana ihu kamar
mahaukaciya,dukan da ta sha a hannun mahaukaci yana dawo mata a k'wak'walwar kanta"
"Wane mahaukaci kuma?" Cewar Hajiya Maimuna.

Nan Umman Saratu ta kwashe labarin komai ta fad'awa Hajiya Maimuna, takaici kamar
ya kashe ta Dan Haushi,ga kuma dariyar da ke cinta,Umma bata kammala rufe baki ba
suka jiyo ihun Saratu daga tsakar gida tana zambarwa tana fad'in.


"Ku zo ku cece ni Mahaukaci zai kashe ni,Salisu kana ina ne?ka taimaken jijjib'in
mijina,D'an lukutina abin alfaharina,inna fatahna laka fathan mubina,na shiga uku
mahaukaci zai kashe ni"

A zabure Hajiya Maimuna ta mik'e tana Neman wajen b'uya,domin ihun ya gigita
ta,bata san lokacin da ta take k'afar Umman Saratu ba,umman ta zuba wani mahaukacin
ihu saboda azaba,ihun ya k'ara razana Hajiya Maimuna ta kifa akan cinyar Umman
Saratun,da azaba ta ishi Umma kawai sai tasa bakin ta ta dank'o wata Tsoka da ke
gefen wuyan Hajiya Maimuna dai dai k'eyar ta,ta sakar mata cizo a wajen.

Hajiya Maimuna ta zabga ihu,a dai dai lokacin da Saratu ta fad'o d'akin da gudu
tana ihu.




Comments
Share
Vote
pls




*BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️



*BAHAGON LAYI*


(SABON SALO)


*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️

HASSANA D'AN LARABAWA
*BABI NA GOMA SHA D'AYA DA NA GOMA SHA BIYU*


PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️




***Hajiya Maimuna ta ruk'unk'ume Umman Saratu jikinta na rawa tana ganin kamar
kanta Saratu za ta yo,k'eyarta na zugi da rad'ad'i sakamakon hak'oran Umma da suka
kaiwa naman k'eyar ziyarar bazata😂,ita kam Saratun tana shigowa zata nufo su cikin
k'arfin hali Ummanta ta saki naman k'eyar Hajiya Maimuna ta kwaye murya ta daka
mata tsawa da k'arfi tana zazzare idanuwa.

"Ke Saratu !Dan ubanki dakata nan kar ki k'araso nan,shiga taitayin ki ki dawo
nutsuwarki kafin ki sa na kirawo Malam yanzun nan yayi min maganin iskancinki".

Chak! Saratu ta tsaya jikinta na rawa tana k'ik'k'ifta idanuwa, ta daina ihu da
surutan da take yi,Umman ta k'ara dubanta tace .

"Nemi waje ki zauna a nan in da kike kuma ki nutsu".

Aikuwa sai Saratu ta zame ta zauna a inda take tsaye,sai kallon Hajiya Maimuna take
yi wadda tayi ragajeje kwance a cinyar Umma,gabad'aya gab'ob'inta sun sage ta kasa
mik'ewa tsabar matsanancin tsoron da ya rud'a ta,sai lokacin Umman Saratu ta dubi
Hajiya Maimuna ta D'an yamutsa fuska cike da takaici ta ce.


"Don girman Allah Maimuna ki d'agani,ina fama da jinyar k'afafuwana amma duk kin
taushe min su"

A hankali Hajiya Maimuna ta ja jiki ta d'aga Umman Saratun,ta koma gefe ta rakub'e
tana satar kallon Saratu k'irjinta na tsananin bugawa tana sauke numfashi,gabad'aya
a tsorace take,Dan ita tunanin ta Saratun Haukacewa tayi ta shigo za ta lode su,sai
da ta gama mayar da Numfashin tsoro da jigata sannan ta dubi Umma tace.

"Kiyi hak'uri Umman Saratu,domin ni ban san ma lokacin da na haye kan k'afafun ki
ba wallahi,na tsorata da ihun da take zabgawa ne k'warai da gaske,amma dai gaskiya
ya kamata a kai ta asibiti a duba k'wak'walwar kanta,kar fa wata matsalar ta samu
daga haka,wannan ai ba k'aramar sukutar masifa ba ce".

Umma ta sauke numfashi ta dubi Hajiya Maimuna ta ce.

"Ni ma nayi wannan tunanin,amma da na fad'awa Malam sai yace min wai babu asibitin
da za a kaita, tsabar iskanci ne kawai take ji da shi shiyasa take mana wannan
ihun,rannan fa da tana yi kinga dukan da yayi mata?ni gashi ba k'afafu ba balle na
tashi na k'wace ta,sai da yayi mata lilis,kuma yace duk randa ta kuma wannan ihun
da surutai wai zai sa gardawan almajiransa su d'aga ta sama ya Zane ta ciki da
bai, ni kam mamaki ne ma ya kamani da jin lafazin sa,shiyasa na dube shi nace da
shi.

" Malam da girmanta za a sa gardawa su d'aga ta a zaneta"

Sai ya ce min wai in bari ta sake yi d'in a gabansa zan ga aiki da cikawa,to in
tak'aice miki labari muddin yana nan yanzu bata yi,amma da zarar taga ya fita zata
addabeni da ihu da surutai,hakan yasa na tabbatar da maganar Malam cewa Saratu
iskanci ne abin na ta,don taga ni ban da k'afar da zan tashi na luguiguita mata
jikinta ne kawai".
Hajiya Maimuna ta ja ajiyar zuciya ta kalli Saratu da ke rakub'e jikin bango sai
zare ido take,fuska duk ta yamushe kamar ta Akuya,kamar ta da Baba Laminden k'auye
ta k'ara fitowa rad'au,ta girgiza kai a Zuciyar ta ta na ce wa.


"Amma kin cuce ni fad'uwar gaban da kika sakani Saratu,ba Dan ina jin tausayin ki
ba har gaban abada ba zan yafe miki ba"

A fili kuma sai ta dubi Umman Saratun ta ce.

"Lallai kam bata kyauta ba in dai haka ne,amma ina ganin damuwa ce tayi mata yawa
fa,ya kamata a nemi Salisu a bashi hak'uri a daidaita su ta koma d'akin ta,zamanta
haka kara zube babu fa'ida,tabbas Saratu tayi ba dai dai ba amma ayi mata Afuwa,na
tabbatar ba zata sake aikata irin hakan ba in sha Allahu ,saboda bala'in da ta gani
kad'ai ya isheta ishara a rayuwa"

Umman Saratu ta ce.

"Hmmm!yaushe rabon wani Salisu da gidan nan,sai fa yayi wata d'aya bai zo ba,sannan
kuma ko yazo a waje yake tsayawa su gaisa da malam ya wuce,baya shigowa gidan nan
ko don ma kar yaga Saratun, ai Salisu yayi fushi sosai kan abin da ya faru,Kuma ni
banga laifinsa ba,tunda a gabansa har uwar sa take ambatowa ta zaga,tana ambatar ta
iya me ido d'aya,kinga kuwa duk d'a na halak ba zai jure cin mutuncin iyayensa ba
Hajiya Maimuna".

Hajiya Maimuna ta girgiza kai cike da takaici ta ce.

"Tabbas haka ne,ban da abin Saratu ma iyan da tuni ta riga ta mutu menene na
ambatota?Allah dai kawai ya kyauta,abin da ya faru ya riga ya faru,sai a guji gaba
kawai,yanzu dai zan samu nayi kiran Salisun gidana tunda mutumina ne,lokacin da
yayi almajiranci a gidana yayi aikin wanke wanke da shara da wanki,har yanzu kuma
yana ganin mutuncina yana zuwa ya gaisheni,Yanzu ma Dan nasan bana gari ne shiyasa
baya zuwa,amma zan sa a kirawo min shi ko na kirashi a waya mu tattauna akan batun
in sha Allah,kuma za a samu mafita da yardar Allah"

Umman Saratu ta ji dad'i Sosai da maganar Hajiya Maimuna, ta dinga yi mata
godiya,domin ita kanta ta gaji da zaman Saratun tare da ita,burinta ta koma gidan
mijinta.




******************


Har soro ta rako shi ta na tafiya da k'yar,sai da suka zo soron k'arshe sannan ya
tsaya ya waiwayo yana duban ta cike da tausayawa a fuskar sa,yayi murmushi ya ce.

"Sannu kinji ,Allah ya raba lafiya,koma ciki ki huta don ni fa bana son naga kina
Aiki da yawa,tausayin ki nake ji Zahra'u na"


Zahra'u tayi murmushi tana langab'e wa ta kalli K'asimu ta ce.

"Haba maigida,kullum fa naje awo likitocin suna fad'a mana mu dinga motsa jikin
mu,idan nak'uda ta zo mana za mu samu sauk'in haihuwa,kuma ba za mu yi doguwar
nak'uda ba,shiyasa kaga bana son zama na jab'e,nafi son in ganni a tsaye ina aiki
ko wani abin"

Ya D'an matsa kusa da ita ya d'aga rigar yana k'arewa cikinta kallo,Wanda yayi
tirtsetse kamar y'ay'a biyu ne a ciki,shafa cikin yayi yana washe baki ya ce.

"Allah yasa ki haifo min mace in sa mata suna Zahra'u, ko domin riritani da kike yi
kamar wani k'wai"

Zahra'u tayi Y'ar dariya,sannan ta rik'o hannun sa ta ce.

"Ina so in anjima yarinyar mak'otan nan Nana zata rakani nan bayan layi gidan
kitso,kaina duk ya dameni so nake ayi min kitso,kasan kuma tun dawowar mu unguwar
nan Atika ce take min,ita kuma kwana Ashirin da Auren ta kenan,na rasa wata
budurwar da zata dinga zuwa tana yi min,shine Nana tace min akwai wata mai yin
kitso a bayan layin nan kuma ta iya,sai dai ita matar Aure ce bata zuwa gidan mutum
tayi masa sai dai mutum ya taka yaje da k'afafuwan sa"

Sai da K'asimu ya kammala sauraronta sannan ya sauke ajiyar zuciya, ya kalleta ya
ce.

"Kina ambatar gidan kitso sai da na tuna da BAHAGON LAYIN mu da muka taso,ni dai ba
don an rasa mai kitso ba babu dalilin da zai sa na k'ara barinki zuwa gidan wani
kitso,matattarar y'an iskan mata da gulmace gulmace,wace irin gwagwarmaya ce ba a
sha gidan Harira mai kitso ba?abubuwa da yawa sun faru wad'anda ko tuna su bana
son yi,sai da Harira ta wargaza layin nan sannan hankalin ta ya kwanta,shiyasa naji
dad'in Auren da Sunusi yayi,har na bashi gudummawa mai Tsoka, sai yanzu zai san
yayi Aure,domin da ba Aure yake ba wasan yara kawai yake da shirme"

Zahra'u ta jijjiga kai tana sauke numfashi, tabbas sun shuka tsiya a BAHAGON
LAYI ,har bata son tunawa da abubuwan da suka faru,musamman dukan da suka sha a
hannun ofisa,wannan rana ba zata tab'a mantawa da ita ba,shiyasa tun da suka bar
BAHAGON LAYI suka dawo wannan unguwar bata tab'a sha'awar shige shigen mak'ota
ba,kuma ita ma kulle k'ofarta take yi bata bari a shigo mata in dai ba yara ba,suma
d'in ba ko yaushe ba,Yarinya d'aya ce ta san sun yi Sabo sosai,kuma tana aikenta
cefane ko siyo wani abin,ita ce( Nana),yanzu babu Ruwan ta da rayuwa irin ta
BAHAGON LAYI, ba zata sake biyewa irin su Harira su Habiba su kaita su baro
ba,domin ba don tayi sa'a mijinta yana sonta ba da tuni sun gurgud'e mata Aure,
yanzu ga Saratu can gidan iyayen ta,tana girbar abin da ta shuka.

K'asimu ne ya dawo da ita daga tunanin da ta afka,ta hanyar rik'o hannayen ta,ta
sauke ajiyar zuciya ta dubeshi ta ce.

"Ni kaina bana son zuwa gidan kitson mijina, duk da dai ba kowane gidan kitso ne
zai kasance irin na Harira ba,kuma in sha Allahu zan tsare maka kaina da
mutuncina,har naje na dawo babu abin da zai faru"

Ya ji dad'in maganarta,ya shafa kumatun ta yana murmushi ya ce.

"Yawwa y'ar Albarka, haka nake son ji,don Allah ki kula min da kanki,kinga dai
tsohon ciki gare ki,ni ina ganin ma zuwa zan yi na koyo yadda ake kitson,sai na
dinga yi miki a gida ba sai kin fita ba ko?"

Zahra'u ta shek'e da dariya,K'asimu na taya ta dariyar,daga nan suka yi sallama ya
fita zuwa kasuwa,ita kuma ta juya ta shige cikin gida tana takawa da k'yar saboda
yadda cikinta yayi girma haihuwa yau ko gobe.
***************


Salisu zaune a shagon Babalalo,shi kuma Babalalon yana yi masa aski,suna D'an tab'a
hira kan yadda shagon askin ya k'one,lokaci guda Salisu yaji wayar sa na k'ara
alamar kira,Hannu ya saka cikin aljihun sa ya zaro ta,yana dubawa sai yaga sunan
uwar d'akin sa ce wato Hajiya Maimuna…..

Da hanzari ya d'aga wayar ya kai kunnen sa ya rafka sallama cike da girmamawa.




Comments
Share
Vote
pls




*BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️



*BAHAGON LAYI*

(SABON SALO)


*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️

HASSANA D'AN LARABAWA


*BABI NA GOMA SHA UKU DA NA GOMA SHA HUD'U*

PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️




***Kamar yana gaban ta haka ya D'an russuna yana gaishe ta cike da girmamawa,saboda
ganin k'imarta da girmanta da yake,yayin da Babalalo ya koma

Please Login or Register in order to submit comment